Showing 126001 words to 129000 words out of 197828 words
Chapter 43 - IDAN BA KE 1 TO 2 COMPLETE By Na'ima Suleiman Sarauta Nimcey luve .txt
furta wani abun to zata faɗin abin da ba shi kenan ba, wanda zai sanya yaji kunyar Idanun mutane ukun nan da suke kan shi
"Amma shi yana son ki ne?" Tayi saurin faɗin
"Ehmn da yawa ma, yana bani darasin littafin Alhayat alzawjia" Abba Hakimi ya sunkuyar da kan shi ƙasa jin al'amarin ya shahara ya shige tunaninsa. Umma A'isha ta janye kanta can zuwa wani waje tana mmkin yau ɗaya bakin yarinyar ya buɗe, Mother ce tayi ƙarfin halin cewa
"Daughter jeki huta ɗakin ki, yanzu dai bakin amince kina son cikin,kuma kina son Yaa Sheikh ba?" Cikin sanyin muryarta ta ce "Eh, Mother". Mother ta ce
"To tashi ki ke anjima Dadarki zata zo kafin ta shige Sokoto" nan da nan farin ciki ya mamaye fuskar Halisa zuciyarta yayi fes ta juya tana faɗin "Abba, Abba Hakimi ya fasa kada zuciyarka ta damu.."
Wayam! Ko inuwar Yaa Sheikh babu tun a sakin layinta na biyu ya sulale yabar parlourn gudun abin da zata iya faɗa anjima, su kansu ba ita ba sunyi mmkin yadda ya bar wajan ba tare da kowa ya lura ba.
Ta miƙe tsaye tare da nufar bedroom ɗinta, Mother ta bita da idanu ganin yadda jikinta ya sauya, ƙirjinta ya ciko sosai fatar jikinta ta ƙara haska sosai fiye da baya har wani yellow take, gabaɗaya sauyin shigar sabon ciki ya bayyana a jikinta. "Yanzu ya za ai da wannan lamarin na Zahrah?" Abba Hakimi ya ce "Dole iyayenta za tabi da zarar sun zo, tunda Engineer yaƙi yiwa yaron huɗuba zan saka Yaa Sheikh ya yi masa" Mother da take jin maganar na dokan ƙaho zuciyarta sosai ta ce
"Mene haɗin Yaa Sheikh da wannan yaron kuma? Ni wallahi banga amfanin zamanta a gidan nan ba"
"Kada ki zama mai son ki Maryama, ke macace ya kamata ki fahimci zafin da yarinyar ke ji a ranta, laifinta ƙanƙani ne cikin wannan lamarin" Idanun Mother ya sauya ta ce
"Abba kasan babu macan da za aiwa haka ranta ya yi ɗaya, idan naga yarinyar da abin data haifa zafi na keji, zuciyata babu daɗi" Abba Hakimi ya miƙe tsaye yana kallon hanya ya ce
"Yaro baya da laifi, nasan daman za kiji zafi amma laifin mijinki ne" ran mother ya ƙara ɓaci sosai ta ce "Ni ba mijina bane, nakai ƙara court ma dole ya ƙarasa saki na" Abba Hakimi bai ƙara cewa komai ba ya nufi ɓangaren shi, domin Mai martaba da Dada suna asibiti wajan El-bashir.
Yaa Sheikh na zaune daga shi sai Jallabiya hannunsa riƙe da azkar yana dubawa, a hankali ya dubi lokaci ya ga rana ta kusa faɗuwa an kusa kiran magriba
Kamar ance ya ɗago kan shi ya hangota a bakin ƙofa tana leƙen shi suna haɗa idanu ta koma ta ɓoya tana dafe ƙirji,gani take kamar Abban nata an sauya mata shi, idan ba kuskure tayi ba gani tayi furfura gemun shi ta sake yawa ainun.
Ta ƙara leƙowa taga kan shi a ƙasa yana duba littafin hannunsa ta bishi da idanu tana jin son shi da ƙaunar shi na ƙara ninkuwa a zuciyarta, SO mai tsanani ya ƙara mamaye ko wacce ƙofa dake zuciyarta.
Kamar daga sama taji saukar kamilalliyyar muryarsa mai kamala ya ce "Zonan Haliyserh"
Ya faɗa a taushashe har lokacin bai ɗago kan shi ba. Ta ƙarasu bakinta ɗauke da sallama sanye da hijabi har ƙasa kamar ma daga wanka ta fito ko shiryawa ba tai ba, ta nufo wajan na shi.
Tana zuwa ta nemi zama kan cinyar shi, ya yi saurin riƙe hannunta tare da ɗago kanshi idanunsa ya sauka akan fuskarta idanunsa ya sauka tsakiyar nata tayi saurin janye nata, saboda kaifin na shi idanun. A hankali ya ajjiye littafin yana jawota tare da zaunar da ita saman ƙafafuwan shi tayi saurin juyawa suka fuskanci juna!
Ya dubi bakinta ganin kamar tana cin abu tare da saka hannu ɗaya ya tallafo haɓarta tare da saka hannu ya buɗe bakin nata, ya buɗe idanunsa akan ta, tare da mayar da idanunsa cikin bakin tayi saurin riƙe hannun ta ce
"Abba ina so, kada ka cire" ya kame fuska tare tsare ta da idanu a hankali ya zare raguwar ƙanƙarar dake bakinta "leƙe ko? baki san mijin naki ba ne" tayi murmushi ta ce "Abba naga ka ƙara babba, kayi kyau shi ne fa" ta ƙare maganar tana son ƙwace ƙanƙarar daga hannu shi.
Shiru ya yi hakan ya sa ta ce "Ka bani to, yawuna duk ya tsinke" ya ƙara haɗe fuska ta ce "Don Allah, wallahi zan maka amai idan baka ban ba"
Ya sauke numfashi yana juya idanu a hankali ya ce "Me ya sa? sanyi zai miki illa fa?"
Ta saƙalo wuyan shi hannunta ɗaya tana shafa sajan shi zuwa dugun gemun shi ta ce
"Kawai naji ita nake so, bana son komai sai ita"
ganin da gaske ice ɗin take so, gashi nan tana ƙoƙarin kakarin amai ya yi saurin zura mata a baki, taka duguwar ajjiyar zuciya idanunta na lumshe duk ta narke a hannun shi.
A hankali ta ji saukar hannunsa a flat ɗin cikinta ya shafa kaɗan, tayi saurin kallon shi, Yaa Sheikh soyayyar abin da ke cikin matar malam ɗin ya mamaye zuciyar shi, yana ƙara yiwa Ubangiji godiya daya azurta matar da zuciyarsa ke so fiye da komai, da samun cikinsa jininsa ke kwance a ƙasan mararta.
"Allhamdulillah!"
Ya faɗa a taƙaice. Halisa ta ce "Abbana mene?" A daidai kunnanta ya ce "My kankanaty, baki san azumi nake ba? Ohya ɗaga ni" ta ce
"Azumin me Yaa Sheikh?" Halisa Said while playing with his beard.
Ya ɗaga ta daga jikinsa yana nufar bathroom ya ce "lokaci, sallah" yana ƙoƙarin shiga cikin toilet ɗin yaji ta rungome shi ta baya hannunta bakiɗaya ta saka ta riƙe ƙugun shi, ƙirjinta dake gogar bayan shi ya sanya tsigar jikinsa ta shi, ya rufe idanu a fili ya ce
"Yasubuhanallah! Ya Rasulullah! Zaki ɗauki hakki" ta saki dariya sosai ta ce "hakin me zan ɗauka Abba?" Yana ƙoƙarin magana yaji saukar hannunta inda bai yi tunani ba, ya zare hannunta daga marar shi kamar zai kuka, duk ya ɗan birkice ya kame fuska tare da juyawa ya ce "Burinki ki karya azumi? Allah ya takaita mini wahala an kira sallah na yarda mata shaiɗanu ne wannan ɗaukan hakƙi ne Zawja"
Ya yi saurin turata baya tare da tura ƙofar tana dariya ta ce
_“I love you Yaa Sheikh Ya shehin malamina”_ Ya girgiza kai kawai kamar yadda Ummul ke yi idan abu ya bata mamaki, ya daɗe tsaye yana mai da numfashi, ya tabbatar da kafin a kira sallah tai masa haka to ya yi wahalar banza babu inda azumin za shi.
Wanka ya yi sosai kana ya ɗaura alwala, ya fito jikinsa na zubar da ruwa ƙamshin Lifeline skin care pro plus shower Gel na fita daga Jikinsa ya shirya cikin wata white Embrodiery design jallabiya, ya ɗora hirami tare da rufe kan shi sai fuskar shi da gemunsa dake bayyane, direct fita ya yi ƙamshin Roja ya sanya Abba Hakimi da Mai martaba kallon direction ɗin duk da sun riga san waye, bai magana ya nufi Masjid. Bayan yaja sallah ya dawo gida kai tsaye part ɗin shi ya nufa, Mother na zaune ita ma idar da sallarta kenan ta kammala shirya wa Yaa Sheikh kayan buɗe baki. Ta kalli Halisa data fito sanye da blue ɗin hijab ta ce "Daughter ga Abincin Yaa Sheikh maza zo ki kai masa" kafin Halisa tai magana Abba Hakimi ya ce "Ba dai ita ba, ki kai masa da kan ki, idan kin kai kice ina buƙatar ganin shi da zarar ya gama" Halisa bata ji daɗi ba, amma ta kasa cewa komai ganin Abba Hakimi ya haɗe fuska sosai. Mother ta kai masa ta kuma sanar masa umarnin Abba.
Suna zaune duka a parlour Dada ta fito wani ihu Halisa tayi tare da rungome Dada idanunta cike da hawaye ta ce
"Dadata nai ta jiran ganin ki" Dada tai murmushi sosai wani daɗi ya kamata ta ce "Ke kam baki girma" Umma A'isha ta ce "Ba batun girma, ni dai abin da ke tare da ita nake ji, garin tsalle tsallen nan zai a zubar da shi" Mother ta ce
"Ah Allah ya ki yaye Umma, na lura wasan jika da kaka ki kewa Daughter" ita Halisa hankalinta na wajan Dada ta ce "Ina ki kai shiga, Dadata nayi missing naki da yawa" Data ta zauna tana cewa "Munje wajan El-bashir duba jikin shi" Annurin fuskar Halisa ya sauya jin ance El, bata mance abin da ya yi wa Abbanta ba, kuma ita ma ba zata taɓa son shi ba. Ta zauna tana cewa
"Ina Shatu?" "Tana Rugar Rome, za a kawota gobe idan Allah ya kai mu" Halisa ta miƙe ta ce
"Bari na faɗawa Yaa Sheikh kin zo ko?" Ba walwala a fuskar Abba Hakimi ya ce
"Kada naga ƙafar ki a part ɗin shi" tayi saurin cewa "To me ya sa, bayan lada zan samu" Mother ta ɗauke jin za a fara halin, Umma A'isha murmushi kawai take, Dada kuma tai shiru dan ba huruminta ba ne.
"Haka na ce, muddin ki ka je ki tabbata zaki bi iyayenki Masarauta" ta haɗe fuska idanunta na kawo ruwa cikin rawar murya ta ce
"To a gasky Jon wuro ban gane ba, gwara kawai mu koma makka zaman can yafi daɗi tunda babu saka idanu" Abba Hakimi maganar ta dage shi, yasan kuma da iyakar gaskiyar ta take faɗa. "Tashi kibar wajan nan Dajeno" cewar Dada ta miƙe tare da yin bedroom ɗinta ta ce "Mutum da mijinta"
Gabaɗaya sukai kamar basu ji me ta ce ba, Abba Hakimi ya tura a kira Zahrah ba jimawa ta fito ɗauke da jaririn. Zamanta kenan ƙamshin Roja ya daki hancinta, tayi saurin lumshe idanunta nutsuwa na saukar mata, ta tsare Yaa Sheikh da idanu shi kam bai kalli inda take ya nemi waje ya zauna saman kujera yana rufe.
"Aliyu na kira ka domin kayiwa Yaron Zahrah huɗu ba" Ya kalli Abba Hakimi na wani lokaci kana ya jinjina kai, da sauri Zahrah ta miƙawa Yaa Sheikh babyn da yake ta barci gwanin sha'awa ya ƙara girma, a hankali ya ɗora bakinsa a kunnen bbyn tare da yin Bisimillah kana ya yi masa huɗuba da suna.
MUHAMMAD.
"Ma sha Allah, Rabbi ya raya Muhammad" cewar Umma A'isha Dada ta amshi yaron, hawaye ne ya dinga sauka daga idanun Zahrah ji take kamar taje ta rungome Yaa Sheikh ta ɗora kanta a shoulder ɗin shi tayi kuka mai yawa ko zai tauyasa mata, ta goge hawayen ta ce "Na gode Yaa Sheikh, don Allah kayi haƙuri ka yafe mini"
Kamar daga sama su kaga Father ya faɗo parlourn hannunsa riƙe da Zeefa ya fita hayyacinsa ya zube gaban Mother ya ce
"Maryam ashe zaki iya kai uban yaranki ƙara court?" Tai masa Shiru idanunta akan Auta Fattoumah ta miƙa mata hannu da sauri ta nufi mother tana zuwa ta rungometa, Maimoon na tsaye taci kuka ta ƙoshi komai ya daina yi mata daɗi. "Ki tausaya mini ki janye wannan ƙarar" tai wani irin dariya tana kaɗa ƙafa ta ce
"Wallahi Allah kaji na rantse maka Engineer Aliyu sai ka sakeni wannan cikon ɗayar da Jadda ta hanaka ita nake buƙata yanzu" kamar zai kurma ihu ya ce
"Wallahi ba zan taɓa rabuwa dake ba Barrister sai dai mu zauna daga ni harke ba aure" Mother ta ce "Ka zauna dai? Amma ni aure babu fashi wata ɗaya ya yi yawa banda darajar idda, kuma banda abinka baga uwar shegen ɗanka nan ba sai ka aureta kuci gaba daga inda kuka tsaya"
Da sauri Auta Fattoumah ta ce "Mother bana son babyn na tsane shi ba ɗan uwanmu bane" Mother ta ce "He never been your brother Mamana, tafi bedroom ki kwanta" Father ya yi saurin janye Auta Fattoumah ya ce "Ta tafi ina? Ƙafata ƙafar yarana idan kin damu da su ki dawo gare su, na shirya shi ga Court duk abin da zaki kiyi amma ba zan taɓa sakin ba" ya ɗauki Auta Fattoumah tana rusa ihu ya saka hannu ya kama na Zeefa da Maimoon sukai waje.
Da sauri ta miƙe zata bi bayan shi Abba Hakimi ya ce "Kada ki fara" takaici ya sa tayi bedroom tana sakin kuka. Abba Hakimi ya kafa ya tsare daga Halisa ta fito yake fatattakarta bedroom, Ogan da kan shi ya fito yana fitowa suka haɗa idanu da Abba Hakimi, bai ce masa komai har Yaa Sheikh ya gama zaman shi ya koma part ɗinsa, ya kasa barci ɗumin jikin matar dana gudan jinin shi kawai yake so yaji, gashi gobe Alhamis zai ta shi da azumi still, ya miƙe da ƙyar ya nufi bathroom ya saukarwa kansa ruwa mai sanyi ko zaiji sauƙi, ɓangaren Halisa kusan haka ne, cikin dake Jikinta ya ƙara mata muguwar sha'awa ta buƙatuwa fiye da kima, gashi ita babu damara ta dinga malelekuwa a kan gado, da ƙarshe ta miƙe zaune tare da fashewa da kuka, su duka sai bayan sallar asuba barci ya ɗauke su.
Washegari parlourn Abba Hakimi ya cika da mutane har wanda Yaa Sheikh bai zata ba, Uncle Haroon, Uncle Bashir, Mahaifin Zahrah da Mimi, tare da Surry, Mother, Umma A'isha, Dada, Yaya Halima, Dr A'isha. Sai Ummul dake zaune gefe guda cikin wani white lace mai kyau da tsari, ƙamshin Roja da taji yasa ta ɗago kanta zuwa inda jarumin ɗan nata yake tsaye, Yaa Sheikh mamakin yadda duk mutanan suka zo lokaci guda yake, ya nemi waje kusa da Ummul babu ko kunya ya zauna. Aka buɗe taro da addu'a Kafin Abba Hakimi ya kalli Uncle Haroon ya ce "Haroon ɗan fito mini da dairy ɗin nan" Uncle Haroon ya miƙawa Abba Hakimi, shi kuma ya buɗe wajan deal ɗin su da Yaa Sheikh da saka hannu da komai. A hankali ya miƙewa Yaa Sheikh ya daɗe kafin ya saka hannu ya amsa. Abba Hakimi ya ce "Ka duba deal ɗin nan, ka yanke hukunci tsakanin ni da kai ga shaidu a gabanmu, ka riƙe amana? Ko dai kaci Amana? Kai inama zaka ci wata mana bayan baka son ta, ba zaka taɓa son ta ba har abada...._*Ga masu buƙatar yi musu tallah su yi magana 08119237616, har kullum Idan ba ke na kuɗi ne akan ₦500 🫰🏽1k for Special*_
Uncle Bashir ya ce "Abba Hakimi da anyi masa afuwa, hakan ma kaɗai ya isa yaji nauyinka" Abba Hakimi ya kalli Yaa Sheikh yana jinjina ƙarfin hali da zurfin cikin shi ya ce "Anya Bashir? Ai Aliyu bai ɗauki hanyar da zamu shirya ba, basshi ya faɗa mini saka hannun waye wannan a cikin dairy ɗin?" Yaa Sheikh ya rufe ido ya buɗe, yana mai ta'ajujin abin a ran shi, gabaɗaya ya manta da batun wani deal a tsakanin shi da Abba, shi bai ga abin ɗaga zancan ba idan ba so Abban yake ya kunyata shi gaban sirikan shi ba. "Sa hannuna ne"
Ya faɗa a taushashe yana mai daidaita zaman shi babu tsoro akan idanunsa, cikin nutsuwa ba kwanakwana ya shaidawa Abba Hakimin haka. "Hakan na nufin kaci amana kenan Yaa Sheikh?" Yaa Sheikh ya yi shiru he refuse to answer the question. Ya ƙara cewa "kamar ba babban malamin da ya yi magana akan al'ƙawari da muhimmancin shi ba?" Yaa Sheikh ya zare nauyin Abba Hakimi da yake ji cikin ladabi ya ce
"Abba na fa ce maka ba zan iya ba? Ka manta ne?" Dr A'isha tayi saurin cewa "Ba zaka iya riƙe amanar ba?" Ko inda take bai kalla ba, amma yadda ya kame fuska waje guda zaka san mganar ta, sam ba tayi masa ba, kuma bai fiya son shisshigi ba a rayuwar shi.
Abba Hakimi ya yi murmushin manya ya ce "To ka amsa mata mana?" Yaa Sheikh ya harɗe hannunsa a ƙirjin tare da yin baya idanunsa rufe, Ummul kanta a ƙasa ba ta ce komai ba, amma ita kanta zurfin cikin Yaa Sheikh yana damunta kuma a shirye take da huran da Abba zai masa
"Kada na sake tambaya kayi mini shiru Aliyu" Yaa Sheikh ya ce.
"Abba nifa na nemi aurenta, taya zan riƙe wannan deal ɗin?....," Dr A'isha ta ƙara cewa "hakan nuni da cewa kana son Halisa? Ko dai har yanzu kallon ƴar raino ka ke mata kuma ƴar ka?" Bai kulata ba, daman tasan ba zai tanka taba ɗin kamar yadda ta tsammata
Kamar daga sama kuma taji ya ce "Zan rayu da ita, daga nan har sanda zan numfashin ƙarshe a kafaɗunta" maganar Yaa Sheikh ta girgiza dukkan jama'ar parlourn musamman Zahrah wacce zuciyarta tai masifar bugawa, kenan ta rasa Yaa Sheikh? Ba zai taɓa son ba har abada? A ɓoye ta dinga shassheƙa kuka tana gogewa duk abin da take akan idanun Mimi
Uncle Haroon ya yi murmushi sosai wanda Yake nuna jin daɗi ya ce
"Kamar Aliyu ya kawo ƙarshen dramar ko Abba, yana son matar shi, matar shi na son mijinta" kai tsaye Abba Hakimi ya ce "He must pay for what he did" ya gyara zama sosai fuska babu walwala ya ce "Yaa Sheikh Aliyu haydar Aliyu, ko ka ce Dr Aliyu haydar Aliyu, kai mutum ne mai daraja, ni kuma ba mutumin banza bane, akan idanun jama'a na soka da alheri kai kuma ka bijire mini? Ba damuwa nasan alkairi ce ita a rayuwarka ko yanzu, am happy for her data samu namiji kamar ka, amma kafi dace da samun kamarta,ita ɗin macan sirri ce, mai nuna soyayyar mijinta a ko wanne lokaci,
Na fahimci son da ka ke mata tun kwanaki a waya, So ba ƙarya bane, gaske ne, kuma tsararren abu wanda yake zane a zuciyar ko wanne bawa, amma ka sani..,"
Ya yi shiru na wani lokaci can ya ce "Za ai muku sabon aure da Halisa, dukkan wani abu da ake a biki dole kayi da arziƙin da Ubangiji ya baka, kuɗin na gani ina so, kayan lefe komai da komai, kafin lokacin auren ka gyara sabon gidanka dake G.R.A, kafin zuwan wannan ranar kada na sake ganinka a gidan nan balle inda Halisa take, a wannan karan ka tsallake umarnina zaka sha mamakins, zaka san waye ni" tunda Abba Hakimi yake magana Yaa Sheikh yake kallon shi, a ran