Showing 27001 words to 30000 words out of 197828 words
Chapter 10 - IDAN BA KE 1 TO 2 COMPLETE By Na'ima Suleiman Sarauta Nimcey luve .txt
zaki samu lafiya" ta faɗa hawaye na wanke mata fuska gaba ɗaya ta ƙara zama wata kala damuwar ciwon Dada ya sata gaba, gashi yanzu Hamma Yabi baya yini gida sbd neman kuɗin zuwa asibitin burni. Jigum tayi tana kallon yadda kumfa ke fita ta bakin Dadar amma bata san me zatai mata ba, bata da wanda zata kira a cikin bukkar. Shatu dake rakuɓe ta kalli Danejo ta ce "Dada mutuwa zatai ko?" Girgiza kai Danejo tayi ta ce "Waya faɗa miki? Babu inda Dada zata yafi ta barmu aradu muna tare da ita" wata ƙara da Dada tayi tana sanƙamewa ya sanya Shatu fashewa da kuka, da gudu kuma Halisa Danejo Rome tayi waje. Karo sukai da Hamma Yabi wando ya shigo hannunsa riƙe da ƙwayar magani daya amsu, ya riƙe Danejo da kyau wacce take ƙoƙarin fita daga hayyacinta. "Hande en boni, Danejo lalashewa ya sameka me ya samu Dada?" Gaba ɗaya ta rikice sai ƙanƙame hannun Hamma Yabi take ganin bata hayyacinta ya jata ciki yana zuwa ya kwantar da ita yana rufe mata fuska shiru tayi har lokacin cikinta bai bar rawa ba, domin gani take kamar Dada tabarta kenan ta mutu ta tafi. Ya girgiza yana komawa wajan Dada tare da ɗagata ya bata maganinsu ya shafa mata zuwa fuska da wuya Ajjiyar zuciya ta sauke tana buɗe idanunta, hannun Hamma Yabi ta kama da kyau tana son tambayar shi mene ya samu Halisarta amma ta kasa, a haka barci ya ɗauke ta cikin mayuyacin hali. Washegari kamar kullum Danejo ta tatsi nono a ƙwayar, tun kafin gari ya yi haske ta fita kiwo da shanunsu, sai da ta ɗauki awa uku ta dawo cikin sauri tana tafe tana kaɗa naggen bayan ta ɗaure su ko abinci bata ci ba ta nufi cikin burni kawai tsaye zuwa Abti America. Yadda taje haka ta dawo babu wanda ya sanya kuɗi ya sai nonon balle su samu na abinci, a wahale ta shiga Rugar idanunta na rufewa ta kafa baki a nonon wata nagge ta shiga sha sai da cikinta ya ɗago taja Ajjiyar zuciya tare da nufar bukkarsu.
Sheikh Aliyu haydar na kwance saman makaken gadonsa idanunsa akan screen ɗin laptop ɗinsa yana sauraran abin da ake faɗa ta cikin laptop ɗin. Can dai ya ja tsaki ya girgiza kai, speaking calmly ya ce "Ni ni niii da dddddd dama zaka zaka zaka sauya labarin nan naka Khalil, in anyway banga amm am am amfaninsa ba..." Dry sosai wanda aka kira da Khalil ya yi ganin yadda Sheikh ke runtse idanunsa yana buga kai duk dan ya kare kansa "To ai ni yana da amfani a wajena tun da abin da ya shafi Sheikh Aliyu haydar Aliyu ai shafi Khalil Ahmad Sarki, look Sheikh don Allah cire son zuciya ka faɗa mini mai mata sukai maka? Let me know" Sheikh ya shafa lallausan gashin kansa wanda yake kwance gwanin sha'awa, cikin son cire damuwar father a ransa ya dage yake hira da Khalil duk da yana shan wahalar magana ya jima bai magana mai tsayin haka ba, idanunsa lumshe ya ce "kakaka....ka kasan me?" Sheikh ya faɗa yana buga kansa jikin pillow yana riƙe ɗaya hannunsa sbd In-ina. Kallonsa kawai Khalil yake yana jiran jin abin da Sheikh ɗin zai faɗa, a wahale cikin In-ina wacce yake son ya saba magana da ita ya mirgina kaɗan yana riƙe kansa da hannu bibbiyu ya ce "man ta ta manta kawai, ya ya yaushe za za kazo?" Murmushi Khalil ya yi cike da ƙaunar Sheikh Aliyu haydar ya ce "Zamu zo da mai martaba wajan Hakimi, I think I will spend my two weeks vacation with you in Kano" jinjina kai kawai Sheikh ya yi ba tare da ya ce komai ba. "You are just afraid of women because you see yourself as a Sheikh, women are the happiness of a man, try and see" Girgiza kai kawai Sheikh ya yi ba tare da ya ce komai ba ya kashe vedio call ɗin.
Umar-khan ne ke driving a hankali idanunsa akan titi amma hankalinsu na kan Sheikh dake manyan mota cikin wata dakakkiyar shadda fara tas ya ɗora golden ɗin Alkyabba sai rawanin daya ƙarawa fuskarsa kyau da haiba ya yi wani irin kyau kamar Balarabe ƙamshin Roja ya cika motar sosai. Yana ki shingiɗe a bayan motar tunani yadda zai sauya ya koma kamar yadda father yake buƙata, a haka suka ƙarasa Wani Restaurant mai kyau da tsari mara hayaniya, Umar-khan ya yi parking kasancewar fitar sirri ce yasa babu wasu masu take masa baya, cikin sauri ya buɗe Sheikh mota a nutse ya fito yana gyara zaman alkyabbar jikinsa tare da goya hannunsa a baya cikin kamala ya yi gaba Umar-khan na biye da shi zuwa cikin Restaurant ɗin. Zama Sheikh ya yi tare da kallon mutanan da zasu tattauna dasu, bayan sun gaida Sheikh ya ɗaga musu kai suka shiga nuna masa zanan bank ɗin daya buƙata na reshe uku, kaduna, Abuja, da Lagos. Baya cewa komai sai da Umar-khan suke tattaunawa gani ya yi zanan bai masa ba, domin babban bank yake so wanda ba a taɓa yin mai girman sa ba. Hakan ya sa ya amshi carbon paper da pen a nutse ya zana yadda yake so, zanan ya bawa ma'aikatan mamaki abin da basu sani ba, kaɗan kenan daga cikin baiwar Sheikh duk abin da ya sanya ransa yana gwadawa yake yi daidai. Sallama sukai bayan anyi musu transfer miliyoyin kuɗi domin fara aiki gadan-gadan. Ɓangaren Kamfanin sarrafa shinkafa ma tuni aiki ya yi nisa, ya yi ordern injina masu kyau daga Chaina. A gajiye ya dawo gida idanunsa na rufewa kansa ya sakarwa shower lokacin 1:30 ya saba barci tsakanin azahar zuwa sallar asr, fresh milk ya tsiyaya a cup tare da zuba honey ya sha kaɗan ya wanke baki, yana kwanciya barci ya ɗauke shi daman ya riga daya saba.
Washegari ya kama weekend Sheikh bai san meke faruwa ba, sai daya farka yaji labarin tun 7 su Uncle Haroon da Abba Hakimi tare da Baffansa suka nufi garin Yola nema masa aure. Ko ajikinsa bai ɗauki auren matsayin wani abu, shi dai ya san ko farcen mace bai taɓa sha'awa ba balle ya birgensa. Da yamma su Abba Hakimi suka dawo cikin jin daɗin an basu auren Zahrah nan da sati mai kamawa za a ɗaura aure. Kasancewar yau Friday ne ya sanya Sheikh ya shirya cikin wata bugaggiyar shadda fara tas da ita mai ɗinki jamper da babbar riga, bai sanya hula ba sai hirami daya saka a saman sumar kansa ya ɗauki zagayayyen abun nan na larabawa Black colour ya ɗora saman hiramin, shekarunsa suka bayyana a jikinsa, domin kowa ya kalli Sheikh Aliyu haydar ya san ba yaro bane, girma ya fara hawa jikinsa babu mamaki ya yi aure a same shi da yara biyar haka, shekaru 34 ba wasa bane ba. Kai tsaye babban masallacin juma'a ya nufa sai da ya yi huɗu ba sosai mai ratsa jiki akan tsaida sallah a lokacin ta, tunda duk In-inar Sheikh inda karatu zai yi yana farawa ake nemanta a rasa. Bayan idar da Sallah ya nufi zaga gidan marayu kamar yadda ya saɓa idan yana ƙasa, a hankali yake tafiya hannunsa goye a bayansa kansa a ƙasa fitowar su kenan daga gidan marayu zasu shiga mota yaje gida wajan Mother, kamar daga sama wata budurwa kyakkyawa ajin farko ta tsaya a gabansu da sauri Umar-khan da Saif-wazir suka sha gabanta tun kafin securities su ƙarasu bakinta na rawa ta ce "Don Allah ku barni nayi magana da shi, na jima ina son haɗuwa da shi" Umar-khan ya daka mata tsawa ya ce "Baya buƙatar ganin kowa, kuma a mu'amalar shi baya yi da mata ki nemi wani wajan" A nutse Sheikh ya dakata tare da juyawa idanunsa zuwa inda budurwar take, waro fararen idanunsa waje ya yi yana mamakin abin da ya haɗa shi da bayin Allan nan da suke bibiyar shi. Murmushi mai laushi ya yi ba tare daya bari kowa ya gansa ba, yana mai ƙarewar budurwar kallo musamman ƙafarta. "Ka taimaka mini daga yanzu ba zan sake zuwa inda yake ba" Umar-khan ya yi mata wani ban zan kallo ya ce "Ke ko mayya ce ke baki isa kije inda Sheikh yake ba, kunne masu ƙullawa mutane sharri ko?" Sosai taji zafin maganar Umar-khan sai kawai ta juya kamar zata kifa sbd sauri. Tana barin wajan Umar-khan ya dafe kansa Saif-wazir ya ce "Are you okay?" Ya ce "Kai na ke ciwo, zazzaɓi nake ji" Umar-khan ya faɗa bakinsa na rawa kafin kace wani abu wani zazzafan zazzaɓi ya rufe Umar-khan. Girgiza kai kawai Sheikh ya yi domin ya san za a rina waya aiki Khan musayar yawo da aljani?.
Da sauri Hamma Yabi ya shigo bukkarsu hannunsu ɗauke da kuɗi ya kalli Danejo wacce take sumar kanta ya ce "shai Alhmd kuɗi shun samu gobe zan kai Dada asibitin burni" murmushi Danejo tayi wanda ya ƙara fidda kyanta na fili ta ce "Kai Allah abin gdy Dadata zata samu lafiya yau ba zan barci ba sbd farin ciki aradu" Hamma Yabi ya kalli Dada dake kwance kamar haka cikin farin ciki ya ce "Insha Allah, da sassafe sai burni" fita ya yi farin ciki ya cika zuciyar Danejo Dada zata tashi su koma yadda suke rayuwa a baya. Hamma yabi bai dawo ba sai dare riƙe da ƙullin buduri da ƙosai mai zafi wanda ake a can wajan gari. Sai dai ko zama bai ba suka fara jiyo harbi ta ko wanne waje alamar ƴan fashi ne suka shigo cikin Rugar Rome. "Bone Hamma harbi harbi....," Bata ƙarasa faɗa ba suka ji an shigo bukkarsu wani mutum mai riƙe da bindiga ya kalli Hamma Yabi yana faɗin "Kuɗi,kawo kuɗi bamu da lokaci" jikin Hamma Yabi na rawa ya ce "Ba kuɗi bamu da shi" mutumin ya yi wata dry sosai ya ce "Babu? idan na bincika na samu duk hukuncin dana ɗauka akan kai ka sani" yana faɗin hakan ya fara bincike bukkar daga can waje harbi ake ta ko wanne sashe, cikin rashin sa a mutumin yaga kuɗin da Hamma Yabi zai kai Dada asibiti "Aradun Allah kuɗin asibiti ne, kayi mini ka taimaka Dada zamu bawa lafiya.....," Harbin da akaiwa Hamma Yabi a ciki ya sanya ya fasa ƙara tare da faɗuwa ƙasa ihu Danejo ta fasa ganin yadda jini ke zuba a jikin Hamma Yabi tana ƙoƙarin zuwa inda yake mutumin ya ƙara sakarwa Hamma harbi a tsakiyar kansa......
Wannan littafin na kuɗi zaka samu book 1, 2 akan ₦500 daga farkon labarin har ƙarshe ka tura ta wannan account ɗin 6850917335 Na'ima Shu'aibu Sulaiman fidelity bank shaidar biya 08119237616.*🌈 IDAN BA KE 🌈*
*_Arewabooks@Nimcyluv_*
14......
Cikin ƙaramin lokaci ƴan Rugar Rome suka shiga cikin tashin hankali musamman wajan su Danejo. Ko kuka ta kasa ta kafe gawar Hamma Yabi da kallo sai Ajjiyar zuciya take, shatu na gefe ta ƙanƙame jikin Dada wacce ke sanƙame bata san meke faruwa ba sbd halin da take ciki. Bata taɓa ganin anyi kisan kai a gabanta ba, yaushe gashi an kashe mata yaya wanda ke kula dasu shi kaɗai ya rage musu. Halisa Danejo Rome ta shiga halin firgici ita kaɗai tai ta razana har lokacin idanunta bai motsa daka kan gawar Hamma Yabi ba a haka Asuba ta risketa. Sarkin ruga da Giɗaɗo ne suka shigo bukkarsu Danejo ba neman iso domin basu damu da cewa Dada matar da za a nemi aminci a wajen ta bace. "Allahu Akbar Allahu ya jiƙan Yabi shai abu bai kyau ba sam" Sarkin ruga ya girgiza kai ya ce "Allah sharki aradu harbi har biyu dole ya mutu" da sauri Danejo ta miƙe jikinta na rawa ta kama hannun Giɗaɗo ta ce "Da gaske Hamma Yabi mutuwa ya yi? Da gaske ba zan sake ganin Hamma ba?" Ta faɗa cikin rauwanin muryar kana ganinta kasan damuwa ta jima da kama zuciyarta ta samu waje ta zauna. "Ya mutu mana kamar yadda Baffanku ya mutu ba zai dawo ba" ƙurr ta kafe Giɗaɗo da idanu kafin taja numfashi mai tsayi sai kuma ta sulale a wajan ta faɗi babu numfashi.
A hankali take buɗe idanunta wanda sukai mata nauyi, hannunta ta kai tare da dafa kanta wanda yake mata ciwo sbd barcin data daɗe ta nayi. "Sannu kin farka Danejo?" Shatu ta furta cikin murnar ganin Danejon na motsi bayan suman da tayi. Danejo ta juya tana kallon Shatu kafin a hankali ta buɗe baki ta ce "Ina Hamma Yabi? Ya tafi da Dada asibitin burni?" Shatu tayi saurin faɗin "Hamma Yabi ya mutu ai kuma har an rufe shi a ƙasa" zuciyar Danejo ta buga da ƙarfi tana runtse idanunta sosai tsoro da fargabar makamar rayuwarsu ta dirar mata a zuciya, yaya za tayi da Dada? Ina zata samu kuɗin asibiti ko shanu zata siyar? Mai Hamma Yabi ya yiwa wannan mutunan da shi kaɗai kawai suka kashe cikin Rugar Rome?.
Juyawa tayi ta sake kallon Dada wacce kawo yanzu ko motsi ba tayi ruwa ma idan aka bata ta gefen baki yake zubewa, hawayen da take maƙalewa suka sakko daga cikin idanunta Shatu wacce ke shirin yin kuka ta ce "Kuka ki ke Danejo? Me akai miki ba ga Dada ba muna tare da ita?" Danejo ta goge idanunta da kyau ta ce "Ba kuka nake ba, ki zauna wajan Dada bari naje wajan sarkin ruga na dawo" miƙewa tayi jikinta sanye da fararen kaya na Fulani sumar kanta ta naɗeta da wani zare mai ɗauke da kuran duwatsu masu kyau. Kanta a ƙasa take tafiya cikin sanyin jiki kamar ko yaushe a haka ta ƙarasa bukkar su Sarkin ruga ta tsaya daga waje tana neman iso. Matar Sarkin ruga ta ce "A'a Danejo ne bismillah shigo" kamar ba zata shiga ba sai kuma ta shiga ta samu Sarkin ruga zaune yana shan kindirmo a diririce ta ce. "Jamɓanduna. _Ina kwana_" Ya ce "Jamni.. _lafiya_" zata sake yi masa wata gaisuwar ya dakatar da ita da faɗin "mene ya kawo ki?" Kanta a ƙasa tana wasa da yatsunta ta ce. "daman cewa nayi ko zaka sayi nagge guda biyar daga cikin garkenmu?" Kallon tsaf ya yi mata yana sakin murmushi kafin ya ce.
"Yabi bai faɗa miki ɗan cewa gaba ɗaya ba naggenku bane? Kiwo kawai aka baku?" Cikin rashin fahimtar maganar Sarkin ruga Danejo ta ɗaga kanta da sauri ta kalle shi tana faɗin "Dada ta sanar mini gaba ɗaya garken na Baffanmu ne, shanuwan sa ne, kuma kowa ya sani Hamma Yabi ma yasan da haka" Ya ce "E, to buɗe kunne kiji kaf cikin garken naggen nan guda biyu ne naku, sauran duk mallakina ne kuma yanzu zan ɗauka aje kasuwar burni a siyar dasu, idan kina buƙata sai a haɗa da guda biyun naku a siyar daga nan sai ku biyawa Baffan naku bashin da ake binsa ma" kasa cewa komai tayi ganin ƙarfen ƙafa da ake shirin yi musu, wanne irin son zuciya ne Wannan? A nagge sama da hamsin ace guda biyu ne nasu? Me ya sa Hamma Yabi bai taɓa cewa naggen Sarkin ruga bane? Da gaske nasa ɗin ne ko ba haka bane?. Jiki a saɓule ta dawo gida zazzaɓi na rufeta sbd fargaba. Kenan tana ji tana gani Dada zata sake mutuwa ta barsu basu da kowa a duniya?.
Sheikh Aliyu haydar Aliyu na zaune yana duba yadda ginin bankunan guda biyu suka ɗauki harami cikin ƙaramin lokaci tare da kamfanin sarrafa shinkafa. A nutse cikin kulawa da haibarsa kamar kullum ya miƙawa Umar-khan Album ɗin. "Ina fatan komai ya yi yadda kake so?" Kallo ɗaya Sheikh ya yi wa Umar-khan a hankali ya juya kansa yana mai jinjina shi a nutse alamar "Ya yi" Umar-khan yai murmushi kaɗan yana jinjina halin Sheikh da yawan lokaci ba tare da ya ce komai ba ya juya ya fita. Ɓoyayyiyar Ajjiyar zuciya ya sauke yana mai miƙe ƙafafuwan shi saman table a hankali ya fara tunanin yadda zai gina rayuwar shi wanda zai sanya father farin ciki duk ƙoƙarin shi na gano abin da ke sanya father yaji zafin shi har haka ya rasa, da yawan lokaci abubuwan na damun shi nunawa ne kawai ba ya yi. Zuciyar shi na shiga tunani na tsayin lokaci. Miƙewa ya yi cikin kulawa ya shiga takawa a parlourn na shi, ƙarar wayar shi ta dakatar da shi daga tunanin da yake jin ringtone ɗin is different ya sanya ya fahimci mai kiran na shi. Farar Alkyabbar shi mai fidda ƙamshin Roja ya ɗauka tare da ɗorawa saman jallabiyar jikinsa banda dole ko hannun shi bai son a gani sbd tsarin halittar jikin na shi. Kansa a ƙasa ya nufi Main parlour babu kowa sai Hajjir bai ko kalle ta ba ya nufi sashin Abba Hakimi. A zaune ya same shi saman ladduma gabansa ɗauke da kayan marmari sai ƙwaryar zuba da kuma ta fura da nono. Zama ya yi yana fuskantar Abban na shi cikin mutunci bakin na motsa wa alamar gaisuwa Abba Hakimi ya yi murmushi ya ce. "Ba sai kace ba, Allhamdulillah" Sheikh Aliyu a lumshe idanunsa yana mamakin yadda Abba Hakimi ke fahimtar zuciyarshi da yawan lokuta.
"Naga baka shirin auren naka, kamar dai you're not ready if i not mistaken?" Sheikh ya buɗe idanu da kyau akan Abba Hakimi cikin mantuwa domin gaba ɗaya ya manta da batun komai cikin In-ina yana riƙe Alkyabbar dake jikinsa da kyau tare da karkatar da kansa yana rufe idanu ya ce. "A...a...au au aure kuma A a Abba?" "E, Aure mana Sheikh haka za ka yi ta zama babu aure ni ma da kaina ban goyi bayan hakan ba, kayi aure kamar yadda Engineer ya buƙata ko dan samun kusanci da shi" Sheikh zai magana Abba Hakimi ya ƙara ɗaga masa hannu ya ce.
"Kada kai musu, ka amince Allah ya sanya albarka, Engineer ya buƙata ka tura kuɗin lefin ita yarinyar tun da ba auren kake so ba, yi maka za ayi na fanshe ka na bada kuɗin lefen kamar yadda suka ce 2.5m