Showing 3001 words to 6000 words out of 197828 words
Chapter 2 - IDAN BA KE 1 TO 2 COMPLETE By Na'ima Suleiman Sarauta Nimcey luve .txt
ƙasan ƙwayar yana rufe idanu da buɗewa ya ce "Gasu can" ta durƙusa ta ɗaga ƙwayar sai ga kuɗi da gudar dubu ɗaya da ɗari biyar guda biyu sai ƴan ɗari guda goma. Zaro idanu tai waje jikinta na rawa ta ce "Kai ɗan Almajiri mai ƙarya wannan kuɗin duk na kindirmona ne? Ai aradu kuɗin yai yawa" hannunsa dake harɗe a ƙirji ya wara tare da ɗaga kafaɗa ya ce "haka suka bayar ai" "su waye?" Shiru yai mata yana ƙoƙarin juyawa ta ce "Mene wannan a ƙafarka?" Zaro idanu waje yai tare da yin baya ganin tana ƙoƙarin zuwa inda yake yasa yai saurin faɗin "ke fillo bayanki" juyawa tai da sauri amma babu kowa a wajan tsaki taja tana kakkaɓe zanin jikinta ta ce "Mai ƙarya dai ɗan wuta" ta ƙare zancan tana ɗago kanta babu Almajirin kamar yadda ta raɗa masa suna babu ko inuwarsa sai wani farin Zomo data gani kyakkyawa dashi ya ƙura mata idanu, itama kafesa tai da idanu kamar zata kamasa sai kuma ta ɗauki ƙwayarta ta nufi bakin hanya inda zata samu motar da zata kaita Njoɓoli. Da idanu Zomon ya bita har tayi nisa sosai yana kallon sanda ta samu abin hawa, girgiza yai yana kaɗa kunnuwansa sai gashi ya koma mutumin ɗazo wanda take ce masa Almajiri mai yagaggun kaya. Murmushi yai mai kyau a kuma fili ya furta "Danejona"
Da gudu motar mai ƙirar Toyota Rav 4 ta Ƙarasa shiga cikin compound na Abti American University Yola (AUN). A hankali akai parking motar a tsakanin jerin motocin da suke cikin harabar. Buɗe murfin motar tai cikin faɗa faɗa ta ce "No! I mean I lost my eye sight for a while, my Mom slapped me and i was very shouked da marin, Sbd kawai wancan banzan ya kai ƙarata gida i hate him wallah ai babu dole cikin aure ko? I'm 29 years mene ya sa za ana damuna akan wani aure?" Yanayin yadda take maganar kaɗai zai sanya kasan ranta ya ɓaci har buga kan motar take sbd zafin zuciya tsaki tai ta ce "No am okay nazo ganin Zahrah ne, i will catch you later" kashe wayar tai baki ɗaya tana fitowa daga cikin motar tunawa da yadda Yarinyar ɗazo da yadda ta firgita ya sanya tai Murmushi tana nufar hanyar wani office. Office ɗin ba kowa sai some of things da suke saman table zama tai tana danna number Zahrah.
Zahrah na tsaye cikin hall ɗin da take lecturing wayarta tai ringing ta san babu wanda zai kirata at this time sai Surayyerh da sauri ta kalli students ɗin dake hall tana faɗin "Ok guys Conservation biology has two central goals 1. to evaluate human impacts on biological diversity and 2. to develop practical approaches to prevent the extinction of species (Soulé 1986, Wilson 1992)" tana faɗin hakan tace "You get it?" Gaba ɗaya suka ce "Yes Maaa" jinjina kai tai tana taɓe baki idanunta akan wani matashi da sauri kuma ta juya hannunta riƙe da Ink pen ta nufi wajan bord da sauri ta shiga rubuta.
“What is Bachelor of Science in Conservation Biology?" Dake tana ɗaukar su course ɗin Conservation Biology Under Faculty of Sciences ne. Shiru duk sukai suka kasa bata amsa hakan yasa Zahrah sakin tsaki a file ta ce "Is an assignment, ba zan wasting time ɗina wajan yi muku explanation ba, i have so much work to do bye" wani daga cikin students ɗin ne ya miƙe yana dariya tare da ƙwaiƙwayar yadda Zahrah ke tafiya ya tsaya gaban ɗaliban ya ce "I have so much work to do bye... Big Maaaa The arrogant one I hate this woman. But i like her style" gaba ɗaya Students ɗin suka saka dry ba kuma kowa ke ƙaunar Zahrah ba, wulaƙanci da disga mutane ya mata yawa, kuma idan ta shiga hall babu wanda ya isa ya shiga ga bada Assignment da shegen text da Attendance. Zahrah na fita ta nufi Office a nutse take tafiya cikin takun isa da gadara tana sanye cikin wata atamfa Amarya collection mai tsada ɗinkin riga da skert ya kama jikinta sosai, idanunta sanye cikin farin cat eyes wanda ya ɗan haska ɓakar fatar jikinta she's classes and educated ƴar wanka ce ga tsafta da tarin ilimi. Ƙafarta dake sanye cikin Derby shoes ta tura cikin office ɗin tana ya tsona fuska ta ajjiye handbag ɗin L.v akan kujera idanunta akan Surayyerh ta ce "Lafiya dai?" Surayyerh taja tsaki ta ce "ina lafiya? Can you imagine yau Mom ce ta mareni sbd wancan banzan?" Buɗe idanu Zahrah tai kamar ba zatai Mgn ba sai kuma tace "mene abin damuwa?" "Zahrah mari fa? Wallahi ba zan ƙara ɗauka ba idan aka sake marina, Look at me am 29 going to 30 ace Mom bata bar marina ba?" Girgiza kai kawai Zahrah tai ba tare da ta ce komai ba. "Ina magana Kinyi shiru, wannan miskilancin naki na tsana fa" "uban me kike son nace maki Surayyerh? Your mother has been slapped you sbd kinyi kuskure sai nace bata kyauta ba? Babu abin da zaki iya sbd Uwa ce dole ki hqr" Zahrah ta faɗa cikin ɓacin rai. "i can't bazan iya jurewa ba" cewar Surayyerh "ok zaki rama kenan? Are you going to beat your mother?" Surayyerh ta girgiza kai cikin damuwa ta ce "A'a kawai zan faɗa mata kada ta kuskura ta sake marina, Nasan Uwa tace kuma sai tai ta dokana akan wanne dalili, ɓacin rana nake gudu" Kallon Surayyerh kawai Zahrah keyi kafin taja numfashi ta ce "Ina cikin damuwa Surayyerh na fara tsorata fa" Surayyerh ta ce "Damuwa akan me?" Hannu Zahrah ta ɗora akan cikinta ta ce "Am pregnant Surayyerh ina da ciki wata uku, kuma na gaji da zubar da ciki wallahi" zare idanu Surayyerh tai tana faɗin "Pregnant? ciki na huɗu kenan fa Zahrah? Kina da hankali kuwa? Wannan karan dole ki yafe cikin kin manta mai Dr yace miki ko?" Ajjiyar zuciya Zahrah ta sauke kafin ta kalli Surayyerh da kyau ta ce "I'm not ready for this, kin san ba aure gareni ba, idan na bar cikin na haihu me zance a gida? Me zan faɗawa Mimi? daman Kullum cikin faɗan naƙi aure take wai na girma da yawa, karatun boko ya buɗe min idanu yanzu kusan shekaruna 31 ne Surayyerh" Surayyerh ta numfasa ta ce "Me kike jira? Ki kira Deen mana kuyi magana ya turo iyaye kuyi aure, Mimi nada gaskiya Kinyi primary, secondary, N.c.e, degree, kinyi masters to what are you waiting for wanda ya shige kiyi aure, haba ai ta boko ai ta boko nifa idan yanzu ne wlh ba zan wata boko ba, shekara 31 ana abu ɗaya sai zallar iskanci kawai da kike kina zubar da ciki a banza, sai kin gama zubar da ƙwayayen da Ubangiji ya baki matsayin zuri'a a banza wlh" Tsaki Zahrah tai "wani lokacin wlh ke Mahaukaciya ce, ni kike tunanin zan iya auren Deen yanzu? Inda a yanzu nasan rayuwa nai boko naje ƙasashe kala-kala da ace ko secondary schl ban rufa ba shi ne zan iya auren Deen amma yanzu kam i can't, zanje hospital a cire cikin, da kike maganar haihuwa waye ya faɗa miki daman ina son raya da haihuwa da yawa ne? Abeg ta shi muje Madam am not in the mood" Surayyerh ita dai mamakin Zahrah take bata, ta rasa ita da Zahrah waye yafi laifi, ita tana ganin mahaifiyarta na takura mata domin har kusan zaginta take a zuciya, ta hanata jin daɗin rayuwa komai sai ta ce wai taji tsoran Allah, ita kuma Zahrah iyayenta sun sake mata duk abin da zatai babu me cewa dan me gidansu gidan boko ne a waye suke gaba ɗaya, hakan yasa Zahrah keta aikata alfasha hankali kwance. "Kinzo da mota ne?" Surayyerh na miƙewa tsaye ta ce "E, kefa?" Zahrah ta ce "A'a, ba zan iya driving ba wannan cikin duk ya sauyani muje kiyi dropping nawa gida" "ok let's go" Fita sukai Zahrah da Surayyerh aminai ne duk faɗan da za suyi har abada babu mai ji, su gama fushi su shirya. Mota suka shiga Surayyerh na driving Zahrah na gefe a haka suka bar cikin Abti America.
Da idanu Dada take bin kuɗin da Danejo take bata, a sanyaye ta ce "Duk wannan?" "E, Dadana ɗan Almajirin mai yagaggun kaya ne yace mini aradu duk kindirmo ake siya dasu, kuɗin da yawa" Dada ta jinjina kai ba tare da tace komai domin magana bai dameta ba, tun bayan rasuwar Baffansu Danejo ta zama shiru-shiru sanadin hakan ciwonta ya sake yin tsamari. "Dadana nawa ce wannan?" Danejo ta tambaya tana nunawa Dada gudar dubu ɗaya, girgiza kai Dada tai bayan ta tsurawa dubu ɗayar idanu ta ce "Ban san sunanta ba, ki bari Hamma Yabi ya zo sai ki tambayeshi ko?" Miƙewa Danejo tai ta ce "Bari naje wajan Shatu na tayata irga Naggenmu" fita tai a hanya taci karo da Hamma Yabi, da sauri Hamma Yabi ya kama hannun Danejo ya shiga duba Funa, Fobbina, Wayla, Hirna. Ma'ana Gabas, Kudu, Arewa, da Yamma, ganin ba kowa yasa Hamma Yabi faɗin "Mun shigesu Danejo, gobe ake bikin gasar wasa da maciji, wanda Sarkin ruga yake sawa, kuma yau za'a zaɓi wanda za'ai wasan dashi" fararen idanunta ta juya sosai cikin rashin damuwa ta ce "Hamma mene abin damuwa, ni Dadana kawai nakeso ta samu lafiya ina ta mafarki wani kala" girgiza kai Hamma Yabi yai kaifn ya kama Danejo sosai ya ce "Baka iya wasa da Mashiji ba Danejo, kuma Sarkin ruga zai iya zaɓarki matsayin wacce zatai wasan, idan baki iya ba Mashijin zai iya saranki ki mutu murus, ko baki mutu ba idan baki iya ba Sarkin ruga zai iya korar mutum daga cikin Rugar Rome" cike da tsoro Danejo ta zaro idanu waje ta ce "Mi boni Hamma Yabi yaya zanyi?" "Yanzu shai mu jira muga wa za'a zaɓa, kije ki ɗauki kindirmo mai man shanu ki bawa Dada gobe zamu koma ashibiti" kai ta ɗaga alamar to Hamma Yabi ya nufi cikin jejin nemo wani sassaƙen magani ita kuma ta nufi wajan garke a nan ta samu Shatu ta kama bakinta a nonon Nagge tana ta sha hankali ƙwance. Zama tai kan wani Leggal (Icce amma kututture) samun kanta tayi da tunani wanne kalar Mashiji za'ai wasan dashi? Meyasa idan taje Birni take ganin wasu mutanan ba irinsu ba komai nasu daban ne, meyesa birni ta banbanta da Rugar Rome?. Ajjiyar zuciya ta sauke tana murza yatsun hannunta da sauri takai dubanta zuwa ga ƙadamin yatsarta idanunta ya sauka akan zoben dake maƙale da yatsar da tsananin mamaki take kallon hannu yaushe wannan abun ya zo hannunta? Mene sunansa ita bata taɓa ganin abu mai kama da zobe ba sai yanzu, ga wani zane a tsakiyar zoben kamar tambarin abu amma bata san ko mene ba, ƙoƙarin zare zoben take amma ta kasa hakan yasa dole ta hqr. Suna zaune a garken suka ji ana shelar Sarkin ruga yana neman jama'ar Rugar Rome baki ɗaya. Da Shatu da Halisa suka kalli juna zuciyarsu cike da zullumi amma Danejo tai ta maza ta kama hannun Shatu suka nufi wajan. A tsaye suka samu mutane wasu na sanye da fararen kaya na Fulani wasu kuma Kuraye yawancin su gaba ɗaya farare ne, amma sam babu cikakken addini ga rashin tsafta. Sarkin ruga ya gyara tsaiwa yana faɗin "Kamar yadda kowa ya sani, a gobe ne zamu gabatar da gasar wasan Mashiji, za'a zaɓi mutum ɗaya ya buga wasa da ƙaton Mashiji kamar yadda muka saba, idan mutum ya kashe Mashiji akwai kyautar Nagge da kuma ƙwayar nono guda hamsin, idan Mashiji ya kashe mutum Shi kenan wasa ya zo ƙarhe, idan mutum bai mutu kuma za'a kuresa daga Rugar Rome baki ɗaya, don haka yanzu zamu fito da alƙalin wasa ya zo ya zamu wanda za'ai wasan da shi" Shatu ta ƙankame hannun Danejo ita ko kalmar Mashijin bata so taji an faɗa balle ta gansa a gabanta. Dajeno kam shiru tai kanta a ƙasa tunani fal ranta domin gaba ɗaya ma hankalinta baya wajan. Alƙalin wasa ya fara zagaye mutane har ya shige kan Danejo gama dubawa yai sannan ya gyara murya ya ce "Mun zaɓi Halisa Dajeno Rome a matsayin wacce zata fafata da ƙaton Mashijin mu a gobe....
#Sarautar marubuta
#True life story*🌈 IDAN BA KE 🌈*
Nimcyluv sarauta
*_Arewabooks@Nimcyluv_*
3.
"Na shiga uku ta ya ya zan iya wasa da maciji? Wallahi kashe ni zai yi" Danejo ta faɗa a fili cike da tsora wanda ya sanya har ta kusan sakin fitsari gaba ɗaya ta firgita. Shatu ta ce "Ki faɗa masa ba zaki iya ba a zaɓi wata, idan Mashijin ya kashe ki na shiga uku na lalashe aradu" da sauri Danejo ta fito tsakiyar fili idanunta akan Alƙalin wasan muryarta na rawa ta ce "A yi mini afuwa Alƙalin wasan ba zan iya wasa da maciji ba aradu sarata zai yi" Alƙalin wasan ya kalli Danejo sosai, shi ya ɗan jima bai ganta ba, ta ƙara girma da wayo sosai ta zama ƴar budurwa irin girman ƙauyen nan dai. Sai rashin tsafta da addini dake ɗawainiyya da ita duk da ana ƙoƙarin ganin an magance hakan a cikin Rugar Rome. Murmushi alƙalin wasan ya sake yi cikin kulawa ya ce "Zaki iya mana? Ai Baffanki ya ƙware wajan iya sarrafa maciji, a wasan ƙarshe kuma macijin ya zama silar mutuwarsa, ki yi wasan ko dan ƙarasa cikawa Baffanki burinsa na zama gwarzo a Rugar Rome. Tabbas zaki iya Halisa Dajeno Rome" girgiza kai tai da sauri idanunta cike da hawaye ta ce "Ba zan iya wasa da maciji ba, mene ya sa sai ni? Baffana daban ni daban kalleni ƙarama ga maza nan da yawa a zaɓi wani daga ci" Sarkin rugar yai saurin faɗin "Ke aka zaɓa, kuma dole kiyi domin ba zamu taɓa sauya ra'ayinmu ba, ya zame miki wajibi muddin kina cikin Rugar Rome" a tsorace Shatu ta ce "Hande en boni, yau mun shiga uku" kasa cewa komai Danejo tai domin gani take kamar ma ta mutu ne lokaci kawai take jira.
Da sauri ta juya idanunta cike da hawaye ta nufi cikin bukkarsu zuciyarta cike da zullumi da kuma fargabar abin da zai je ya dawo. A haka ta shiga cikin bukkar Idanunta akan Dada wacce take kwance cikin halin ciwo, domin a kullum ciwon nata ƙara tsanani yake. "Dada Alƙalin wasan ya zaɓi Danejo matsayin wacce zatai wasa da maciji a gobe" da sauri Dada tana jan numfashi ta kalli Danejo cikin damuwa ta ce "Mene ya sa baki cewa masa ba zaki iya ba?" Shatu tai saurin faɗin "Sarkin ruga ya ce wai dole tayi domin cika muradin Baffanmu" Dada ta miƙawa Danejo hannunta cikin kulawa ta ce "Waye yace muku Baffanku wasan maciji shi ne burinsa?" Danejo ta kasa magana sai ajjiyar zuciya take saukewa Shatu ce tai ƙarfin halin cewa "Sarkin ruga ne ya faɗa" Murmushin taƙaici Dada tai bata taɓa ganin zalunci irin haka ba, ta rasa me suka tsarewa Sarkin ruga da yake shirin ƙarar dasu ta hanyar kashesu da maciji wanda wasu suka tabbatar macijin tsafi ne. Cikin ƙonar zuci ta ce "Baffannku bai taɓa sha'awar yin wasa maciji ba, halima babu wannan al'adar ta wasa da maciji a Rugar Rome, daga baya Sarkin ruga ya samar da ita, bayan ya samar da ita ya zaɓi Baffanku matsayin wanda za'ai wasan dashi" shiru tai sbd tarin daya sarƙe mata numfashi, da sauri Shatu ta ɗauki ruwa ta bata, numfashi ta sauke kafin ta ce "Bisa dole Baffanku ya amince, yasha wahala kafin ya kashe macijn bayan ya samu raunuka wanda ya sa ya kwanta jinya, da shekara ta zagayo aka ƙara zaɓar Baffanku abin mamaki shi ne babu bambanci tsakanin macijin shekarar data shige da kuma wanda aka fito da shi, Baffanku ya tsorata, gashi idan ya ce ba zai ba to za'a kuresa daga Rugar Rome, tun daga wannan shekarar Baffanku ke gabatar da wasan Maciji, har zuwa shekarar da maciji ya kashe shi wanda kuma anyi hakan ne domin aga bayansa. a ruɗe Danejo ta ce "Kenan kashe Baffa akai Dada?" Dada ta girgiza kai ta ce "Ba zance ba, bani da hujja akan haka koma mene hukuncin na wajan Allah".
Danejo taja numfashi cike da raunin murya na rashin sanin mafita zuciyarta cike da tarin zullumi ta kalli Dada ta Shatu ta ce "Dada ba zan iya ba, ina jin tsoro" "Halisa idan ba kiyi korarki za su yi daga cikin Rugar Rome, ni kuma ba zan jure hakan ba, Ubangiji na tare dake. Dole kiyi wasan imma ki mutu ko kiyi rai Kinji ko?" Kafin Danejo tai magana Hamma Yabi ya shigo da sauri idanunsa akan Danejo yana faɗin "Tashi mu tafi Danejo daman nasan bayanki suke son gani kamar yadda suka kashe Baffa" kallo Hamma Yabi Danejo tai idanunta ya kumbura sbd kuka ta ce "Hamma ina zamu?" Muryarsa na rawa ya ɗaga ta tsaye ya ce "Zanje na ɓoyeki sai an gama wasan zaki dawo, zan nuna ban san idan kike ba" Dada tai saurin cewa "A'a Yabi, kada ai haka kamar Halisa tare damu, idan ta tafi to Shatu ce zata maye gurbinta kasan haka ai" zama yai sosai ya ce "Yanzu haka zamu zauna? Ke baki da lafiya ita kuma muna kallo maciji ya kashe ta?" "Akwai Allah" Dada ta bashi amsa tana rufe idanunta. Halisa kasa bacci tai ga yunwa ga tsoro can cikin dare ta tuna ai ha tayi sallar issha ba, da sauri ta fito daga bukkar gaba ɗaya rugar shiru babu kowa sai wutar da aka kunnawa ko wanne garke dake ci hankali. Can bayan bukkarsu ta nufa tai tsari a wajan tai alwala babu ko shafar kai ta kwararan ruwan ta dawo. Sallar ma dungure tai Fatiha kawai ta iya cikakkiyar babu gyara. Yadda taga rana haka dare, dab da Asuba ta nufi garke tare da tatsar nono, tana