Showing 153001 words to 156000 words out of 197828 words

Chapter 52 - IDAN BA KE 1 TO 2 COMPLETE By Na'ima Suleiman Sarauta Nimcey luve .txt

12 Dec 2024

9342

unborn child"
Ya zame jikinsa tare kallon fuskarta da yake ganinta tarwai a idanunsa ita kuma ta lumshe idanunta, ya sumbaci goshin da kuncinta daga nan bata sake sanin meke faruwa ba, sai farkawa tayi taga ƙarfe 5:15 na yamma.
Ta farka a tsorace da ƙyar ta iya addu'ar tashi daga barci, ji tayi duka gabɓanta ciwo suke, ta saka hijabi tare da kunna hasken bedroom ɗin
ta shiga ƙarewa ɗakin nata kallo babu komai sai ita ɗaya,ta dafe ƙirji ta ce "Ya Allah meke shirin damuna ne? Me ya sa nake ganin Abbana?" Ta dafe kai tana zama bakin kujerar.
Mother data buɗe ƙofa ta shigo ta ce "Halisa?" Tai firgigit ta buɗe ido a rarrabe kamar mara gasky ta ce "na.. na'am"
"Meke damunki, ɗazo na shigo na sameki kina ta barci zuwana na uku kenan, yanzu kuma ina sallama shiru"
Ta juya ta kalli bedroom ta ce "Mother ba kiji ƙamshin Modibbona ba?" Ta saki baki ta ce
"Wanne irin ƙamshi ni Maryamu, ƙamshin kuma na Yaa Sheikh bayan kin san baya ƙasar"
Ta saki kukan tsoro, shagwaɓa hadda rigima ta ce "shi na gani, yanzu ya shigo muna tare har barci ya ɗaukeni"
Mother ta saki tsaki ta ce
"Kin fara samun matsala, ki tashi kiyi wanka da sallah kici abinci, ina son duba lafiyarki"
Ta goge idanu tare da yin kicin-kicin da rai.
"Meye kika haɗa fuska, ba zaki mini wannan sangarta taki da kukan rashin abinyi ba"
Ta ƙara haɗa fuska ta ce
"Allah ya baki haƙuri, naga dai Abbana Dr ne, kije kawai zai duba ni"
Mother ta ce
"To sannu ƴar Abba ba kiji kunya ba? Bayan kin gama yi masa ɗiban Albarka, baki duba girman shekarun shi da gemun shi, da ilimin da Allah ya bashi kika watsawa idanunki toka kika ce bakya son shi ya sake ki?" Ta marairaice fuska tana tura baki ta ce
"To yanzu na cire tokar shikenan? Nifa ina son Abbana ko ya yi sakinma wallahi ban sako ba"
Mother ta saki baki gudun kada ta sake magana, Halisa ta sakar mata layi ta ce
"Uhm ki fito ina jira" ta ce "To, amma idan kin san zaki mini wannan allurar wallahi bana so" ita dai Mother ba ta ce komai ba, sai da taje ƙofa zata fita Danejo ta ce
"Mother wallahi idan Father yazo ki bisa zama babu miji babbar masifa ce kuma jarrabawa uhm"
da sauri Mother ta fice daga cikin bedroom ganin tsakani da Allah ita Halisa shawara take bawa Mother ɗin. Wanka tayi tai sallah tare da yin Istigifari na makarar da tayi, ta shirya cikin wata light blue ɗin abaya mai stones da flowers tana da faɗin wuya hakan yasa rigar ya zauna sosai a ƙirjinta wanda ya ƙara cika da sauyi, babu rama a Jikinta domin kullum ƙara buɗewa take musamman waje biyun nan, da hips da brest ta fuska ne ta fayau Idanun ya faɗa sai dogwan hancinta kawai.
Ta fito Main parlour tana rolling vail ɗin abayar hannunta riƙe da waya. Ba kowa a parlourn kai tsaye ta shige kitchen ta samu salad da tumatir da albasa ta haɗe waje guda fal cikin plate, ta zuba white oil da yaji kaɗan ta saka maggi, ta haɗa da lemon tsami yawonta har tsiyaya yake sbd wani irin kwaɗayi daya taso mata, daman ta jima ba taci komai ba, sai abincin da Ummul ta bata. Ta fito da kwaɗon salad ɗin da lemon citta data haɗa ta daka ice ya yi wani irin sanyi na shige misali. Zama tayi saman kujera ba tare data lura da wanda ke zaune ba, hannu baka hannu ƙwarya ta dinga cin salad ɗin, fisgewa taji anyi kamar tai hauka ta ce
"Wane mai son ɗaukan zunubin ne" ta faɗa tana miƙewa Idanunta ya sauka akan Khalil Ahmad Sarki ta saki murmushi tana tsalle tare da rungome shi ta ce
"Oyoyo my prince my hamma" ya watsa mata harara ya ce "Princess wannan yajin is not good for your health" ta marairaice ta ce
"Please Hamma ka bani wallahi ji nake kamar zan amai idan banci ba" Umma A'isha ta ce
"Kada ka damu babu abin da zai mata" ya watsa hannu ya ce "daman dai fushin Yaa Lee nake jiye mana" Halisa bata sake cewa komai ba sai cin salad take, tana gamawa ta ɗauki ruwa mai sanyi tasha. "El-bashir karɓo mini ruwan nan" El-bashir dake zaune kusa da Halisa bata sani ba,ya ware idanu ya ce "ki barta mana" cikin tsawa ta ce "Mubasshir ka kawo mini nace ko?"
Halisa na tsaka da shan ruwan sanyin wanda take jin daɗin shi taji an ƙwace ta juya da sauri suka haɗa idanu da El-bashir cikin masifa ta ce "Waye kai? Meye haɗinka dani da zakai mini shisshigi cikin lamarina?" El ya kasa ce mata komai sai Dada ce ta ce "Ni zakiwa rashin kunya ba El-bashir ba, kuma ba a taɓa sauya tuwo suna" Halisa ta miƙe duk da taji daɗin ganin mahaifiyarta amma hakan bai hana ɓacin ranta bayyana ba ta ce "Ba zan taɓa son shi tunda baya ƙaunar Abbana ya nemi kashe shi" tana magana faɗin hakan tai bedroom idanunta cike da ƙwalla. Dada ta miƙe zata bita El-bashir ya ce "Please Mom u hve to understand her feelings komai tayi daidai ne, ni ne mai laifi nima kuma bisa kuskure amma dani da ita ba a san wanda yafi son Yaa Lee ba"
Dada ta ce "Duk wannan bai zama dalilin da zata wulaƙantaka kuma ta tsaneka ba" Khalil ya ce
"Be patient Mom, I'll talk to her tana da zafi da riƙe abu ne" ya lallaɓa Dada ta zauna shi kuma ya nufi wajan Halisa..
Washegari Halisa ta shirya ta nufi makarantar Ibadur-rahman.
Zahrah na zaune gefen gado Dr yana ƙara dubata domin yau za a sallameta daga asibiti ya ce "Allahamdulillah jiki da sauƙi, kici gaba da shan magani" tai murmushi ta ce "Thank you Dr, da baka taimaka mini ba, ba zan taɓa samun farin ciki da auren Yaa Sheikh ba, naji daɗi yadda plan ɗinmu na ciwon Cancer ya tafi daidai babu matsala" Dr ya ce
"Imagine da gaske ace kina da Cancer" ta ce "Please daina faɗa ban shirya tafiya lahira na bar Yaa Sheikh ba, burina naga ranar aurenmu amma sai nan da wata uku ai thank God an kawo kuɗi dai" Dr ya jinjina kai ya ce
"Congratulations, yanzu kin daina sharholiyya kenan?" Ta ce "Har abada babu ni ba ita, daman can tsautsayi ne balle yanzu dana fahimci Yaa Sheikh tsanar da ya yiwa kalmar Zina, sai naji na tsaneta nima, ina son shi kamar zan mutu ina buƙatar soyayyar shi da kulawar shi, wannan dalilin yasa nace ka faɗa masa ina da ciwon Cancer it was all my plans" Surry dake bakin ƙofa riƙe da Muhammad ta dafe ƙirji a ranta ta ce
"That's means she's lying to him? ba wani ciwon Cancer" tai murmushi tana girmama ƙarfin son zuciyar Zahrah. ta juya ba tare data shiga ba, Dr ya sallami Zahrah suka koma gida ta fara shirye-shiryen biki a karo na biyu duk safiyar Allah sai ta kira Yaa Sheikh wani lokaci ya ɗaga wani lokaci ya share, tun tana dannewa harta fara yi masa complain shi kuma ya ɗan fara sassauta yanayin sbd condition ɗin da take ciki.
A hankali yake tafiya kan shi a ƙasa yana gyara zaman alkyabbar jikinsa fitowar shi kenan daga zaman tattaunawar da sukai akan aikin hajjin da za a fara nan da kwana goma. A yau ɗin kuma yake son barin Madina zuwa Makka, amma yana da muhimman wajan da yake son ya ziyarta ya kaiwa Allah kukan shi, ya kuma karkato da hankalin Saif-wazir zuwa gida. Daga nan masallacin juma'a ya nufa yaja jam'i kana ya yo gida. Umar-khan dake zaune ya ce
"Ka samu kira, da saƙwanni" ya jinjina kai idanunsa rufe a taushashe cikin gajiyawa ya ce "Kayi magana ko?"
Umar-khan ya ce
"Abubuwa da yawa sun ƙare a kamfanin sarrafa shinkafa, munyi magana da Manager Khalil dole za a tura wani Chaina"
Yaa Sheikh ya yi shiru ya
ware idanu ya ce
"El-bashir" Umar-khan ya ce "I don't have his number" da ido kawai Yaa Sheikh ya kalli Umar-khan ya ce, da sauri cikin ladabi ya miƙa masa wayar a hankali kamar mara lafiya ya zuba number El-bashir a wayar ya danna kira tare da saka handsfree.
Lokacin El-bashir yana tare da Abba Hakimi da Dada tare da sauran family wayarsa ta fara kaɗa Algaita, ganin sunan da bai taɓa tunani ba da sauri ya ɗauka yana faɗin.
"Assalamu alaika"
Yadda ya amsa wayar with so much respect yasa sukai tunani Mai martaba ne. Yaa Sheikh ya amsa kafin ya ce
"You're alone?" El ya ce
"Many people" lokacin Halisa ta shigo hannunta riƙe da Alkur'ani fuskarta rufe da liƙab El-bashir ya ce "Include your wife" Halisa kamar wacce ta fahimta tayi saurin ƙwace wayar Jikinta na rawa ta kara a kunnenta ta ce "Abbana" Ya runtse idanunsa zuciyarsa tai kyakkyawan bugawa gabaɗaya Jikinta ya ɗauki sautin muryarta wacce ya yi kewa da jinta , ya rungume hannayensa a ƙirji, ganin haka ya sanya Umar-khan miƙewa tare da fita yasan yanzu ba lallai ayi maganar kamfanin ba. Yadda taji anyi shiru ta ƙara tabbatarwa Abbanta ne akan layi ta zame wayar daga kunnenta ta ɗora a bakinta ta sakar matsa kiss ta ƙara sakar masa wani kiss ɗin
"Muu'ah... Muu'ah" Abba Hakimi ya yi ƙasa da kai, Dada ta miƙe tabar wajan, mother ta saki baki da hanci Umma A'isha dake kakace tayi murmushi kawai, Khalil Ahmad Nuran Sarki ya kalli Halisa yana yabawa rashin ta indonta.
Mubasshir El-bashir Ahmad Nuran Sarki ya kalli kyakkyawan ƙanwar ta shi mai tsananin kama da shi, komai nasu iri ɗaya ne so da ƙaunar Princess Halisa Ahmad Nuran Sarki kuma Halisa Danejo Rome uwa uba Matar Malam Halisa Yaa Sheikh Aliyu haydar Aliyu ya wanzu a zuciyarsa. Ta buga tsalle tama mance da cikin Jikinta tana sakin dariya hawaye na zubu mata ta fasa ƙara da ihu wanda ya karaɗe parlourn bakiɗaya ta ce
"I love You Abbana, I miss you Modibbona, ina sonka Yaa Sheikh ina sonka ina sonka zan cinyeka da soyayya Mijina mai gemu" tuni Khalil ya ɗora Camerar iphone ɗinsa akanta. Yaa Sheikh ya nutse cikin lallausan kujerar da yake yanayin da yake ciki ba zai barshi yayi magana ba, bai sai adadin ke yake ji akan wawta da ƙuruciyar ƴar fillo ba. Ƙit ya kashe wayar yana fesar da numfashi ya faɗaɗa fuskarsa daga kamewa yana jan gemunsa ya ce.
"Bbyn Abba, Matar Malam" wayarsa tai haske ya duba.
"Check Your WhatsApp"
Number Khalil da ita aka turo saƙon.
Akwai Wi-Fi gidan yana shiga vedio ya shigo, milk ɗin hijabi idanunsa ya gane masa, ya yi downloading vedion da sauri ya miƙe idanunsa akan Halisa dake tsalle na muryar jin muryarsa ya katse ya kira number Mother tana ɗauka, a karo na farko cikin zafin murya harshensa na riƙewa ya fara faɗa da masifa ta inda ya shiga bata nan yake fita ba, don me za'a barta tana tsalle bayan ansan ba ita ɗaya bace if something happens to her fa? Yana gama faɗan ya kashe wayar ba tare daya bar Mother tayi magana ba. Ta riƙe haɓa ta ce
"Yau zafin zuciyar Aliyu Gadanga ya motsa masifa kenan" jikin Halisa ya yi sanyin ganin yadda Yaa Sheikh ya yi mata banza ko dai da gaske bashi bane kamar Yadda El-bashir ya faɗa?...
*_3 month later_*
Gabaɗaya harabar filin da ake saukar Alkur'anin da bikin hafizan mahaddata a cike yake da manyan baƙi, iyayen yara da ɗaliban saukar. Kimanin ɗalibai 100 ne cif sai hafizai guda 35 sanye suke da fararan hijabi tas sun san rufe fuska da liƙab, hannunsu sanye da safa haka ƙafarsu, wanda sukai saukar kuma milk ɗin hijabi ne a jininsu, makarantar matan aure ce amma ba'a taɓa sauka wacce takai wannan ba acikin shekarar. Ɗaya bayan ɗaya aka dinga kiran sunan hafizan suna karatu daga ƙarshe aka ce "Halisa Sheikh Aliyu haydar Aliyu" a sanyaye ta miƙe tana ƙara buɗe hijabinta sbd cikinta daya fara tasawa na kimanin wata huɗu zuwa biyar. Yau ta ƙara tabbatarwa Abbanta Yaa Sheikh ya gujeta rana mafi muhimmanci da zai tayata murna amma babu shi a wajan ko wacce mace mijinta na tare da ita, amma banda ita. Tayi ƙasa da murya tana sauke numfashi a hankali cikin sautin murya mai amo! Wanda duk wanda yasan yadda Yaa Sheikh yake ƙira'ar Alkur'ani yaji karatun Halisa zai san cewa rainon shi ce, cikin fidda tajweed da makarijin huruf ta fara karatun cikin suratul Nisâ'i. Wajan ya yi shiru aka shiga tasa Camera a kanta duk da ba a ganin fuskarta wani irin karatu take mai cike da nutsuwa. A hankali ya juya fararen idanunsa akanta yana mai yabawa da karatun nata farin cikin da yake ciki ya ninka nata, shi ne maƙo na musamman da sarkin Kano amma har ya bata Alkur'ani da certificate da allo bata san shi ne ba, tana gama karatun ta saki kuka wanda an ɗauka na farin ciki ne, ita kuma zallar damuwa ke damunta na rashin ganin nata gwanin ko ta ce tsohon mijinta. Aka dinga basu kyaututtuka anan aka Shaida akwai muhawarar Alkur'ani ta ƙasa da ƙasa wacce hadda sunan makarantar a wacce za a fara karawa ta cikin gidan kafin a samu gwarzuwar da zata tsallake matakin ƙarshe.
Taro ya tashi Halisa taci kuka ta ƙoshi Mai martaba ya dinga alfahari da Princess haka Dada, Ummul ta rungome Halisa jin hadda zazzaɓi a Jikinta,cikin kuka ta ce
"Ummul baya so na da gaske, na shiga uku Ummul zuciyata" Ummul ta ce "kada ki damu kanki, akwai gajiya da zazzaɓi tare da ke" kafin Halisa tayi magana suka ji ance "Assalamu alaikum" ƙamshin turaren Roja ya ƙara bayyana mai sallamar Halisa ta juya da sauri tana cire liƙab ɗin fuskarta sukai idanu huɗu da Yaa Sheikh dake tsaye cikin wata dakakkiyar shadda fara tas ya ɗora Alkyabba mai tsananin kyau da tsada ya fito a Yaa Sheikh ɗin shi. Hawayen fuskarta ya ƙasa tsayawa,Ummul tai murmushi a hankali ya shiga takawa har zuwa inda take tsaye ta haɗe fuska kamar ba ita ke kukan rigima ba, yana zuwa ta juya zata gudu ya saka tattausan hannunsa ya kama nata tare da dawowa da ita baya, a hankali cikin wani kyakkyawan yanayin ya juyawa su Ummul baya yana mai shigar da Halisa cikin Alkyabbar shi ya zagaye ƙugunta da hannunsa duk biyun suka manne da juna, ya ranƙwafa daidai wuyanta ya sumbaci kuncinta da bakinsa mai tsafta tare da hura mata iska a kunne cikin raɗa ya ce.
"Congratulations Hafizata.... Ruhin Aliyu" ya faɗa yana lashe gefen kunnenta...Halisa ta ɓata fuska tare da yin kicin-kicin da ranta, Yaa Sheikh ganin idanun jama'a baya kansu ya saka tattausan hannunsa tare da tallafo fuskarta ya ɗora fuskarsa saman nata idanunsa na yawo a fuskarta yana son ta sanya nata idanun cikin nasa, ko ya fahimci rigimar ta yanzu ta mece? Duk da yasan ya yi laifi mai yawa har bai san ta ina zai fara ba?.
Yadda gangar Jikinta tayi kewar shi haka zuciyarta, ta kasa jurewa yanayin musamman ƙamshin turaren dake sauya mata yanayin da take ciki.
Ta ɗago Idanunta a hankali ta zuba cikin nasa gently ya lumshe nasa gajiyayyun idanun yana jin abu na fisgar shi kamar ya jawota ya rungume na tsayin lokaci
Ganin nata ya fara kassara masa jiki da son sauya masa yanayin da yake ciki
Ya rufe ido ya buɗe a hankali ya zameta daga jikinsa ba tare da ya ce komai ba ya juya daidai lokacin Umar-khan ya yi parking da mota, kai tsaye ya shiga suka bar wajan da sauri.
Tabi motar da kallo tana jin kamar ya tafi da zuciyarta ne, tsoro ya kamata ta shiga addu'ar Allah ya sanya ba tafiya ya sake yi ba a karo na biyu?. "Hankali ya kwanta?" Cewar Mother dake tsaye cikin wata atamfa ta ɗora mayafi akai murmushi Halisa tayi ta ce
"Ni daman a kwance yake" Mother ta riƙe baƙi ta ce "Ba shakka, to zan sanar masa kada ya dawo" tayi saurin ɓata fuska ta ce
"Allah ya sa ba cewa nayi bana son shi ba" Yaya Halima tayi murmushi ta ce "Faɗa mata dai daughter kisan zaman da zaki da ita" kamar jira Halisa take ta ce
"Wallahi Anty Halima duk wanda baya so na da Modibbo na sani, kawai rabuwa nake dasu"
Ummul dake tsaye hannunta riƙe da key car tana sanye cikin Abaya wacce kallo ɗaya zakai kasan bata ƙana nan mutane bace, tayi rolling vail a kanta ba zaka taɓa cewa ita ta haifi Yaa Sheikh ba.
Ta murmusa ta ce "Rabu dasu Daughter, yau ranar farin cikinki ce, kin zama hafiza, Modibbo ya dawo kuma yau zaki tare a gidan mijinki kekam waya kai ki sa a?"
Halisa ta ƙara wajan Ummul ta ce "Ai ina haihuwa sunanki zan saka, kinfi kowa so na, idan Abbana ya kuma yi mini wani cikin sai na saka sunan Abbana mijina Aliyu"
"Yau mun shiga uku da mara Kunyar yarinya" cewar Mother. Ummul ta ce "Gold setting ke aiki, let her do" Ummul ta duba agogon dake hannunta ta ce
"Ya Allah, bari naje am getting late, sai kunzo" ta kalli Halisa ta ce
"Congratulations once again Matar Malam ta zama Malama, your gift is waiting for you"
Danejo tayi kyakkyawan murmushi wanda ya ƙara fidda kyanta, tana ƙaunar Ummul na gartar matar ta kai harta shige samun uwar miji kamarta a yanzu sai an bincika.
"Allah ya tsare Ummul"
Ummul ta murza key tare da tayar da motar cikin nutsuwa take driving harta bar wajan.
Yaya Halima ta ce
"Matar nan tana birgeni iliminta ya yi rana, tasan yadda ake mu'amala da mutane" mother ta ce
"Wallahi" motoci suka shiga zuwa gida domin gabatar da sauran abubuwa tuni an tashi wajan saukar.
Baƙin motocin da Halisa ta gani a parking lot ya bata mamaki sai ba ta ce komai ba, ta nufi cikin gidan fuskarta ɗauke da farin ciki tayi zaton zata samu Yaa Sheikh ciki
Turus! Tayi ganin Surry riƙe da Muhammad matar da bata taɓa tunanin zata sake ganinta ba, Surry ta miƙe tana faɗin.. "Su ƴar fillo manya, kin zama babar mace kamar ba mai tallan Kindirmo a Rugar Rome ba?"
Halisa smiling, ta zauna

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login