Showing 138001 words to 141000 words out of 197828 words
Chapter 47 - IDAN BA KE 1 TO 2 COMPLETE By Na'ima Suleiman Sarauta Nimcey luve .txt
rabauta da ribar dake cikin zamantakewar aure Zawja? So ki ke na zama Ayuu!?"
Ya yi shiru da nufin ko zata tanka masa amma tai mursisi dole ya tsuguna ya lashe aman da ya yi mai datti da wari, daman tabarmar kunya da hauka ake kwashe ta.
"Na yi miki al'ƙawarin idan akan taɓa jikin ki da nake ki ke wannan kumfar bakin, to na haƙure zuwa lokacin da ranki zai fari, bana son ki ƙaura cewa Idanuna, IDAN BA KE ba san ya nake b" sai lokacin ta kalle shi ta ce.
"YAA SHEIKH" Ganin kamar da gayya ta faɗi sunan na shi ya sa kawai ya bita da Idanu, yanzu ta dai na bashi mamaki, kallon mara tausayi wacce bata amsar uzuri yake mata.
Ta kalle shi ta ce "Ba jikina ne bana so ka taɓa ba, so nake ka haƙura dani na tsayin shekarun da suka rage maka a rayuwa, ka yi zuciya ka bani takardar sakin daka furta kuma ka ayyana a ranka YAA SHEIKH ALIYU" cikin rawar murya YAA SHEIKH ya ce
"ƙarya na ke, iya laɓɓa kawai na furta haka, IDAN BA KE babu wata rayuwa da zan iya" dariya ta so kama Halisa amma ta danne tana dafe ƙirji ta ce "Asstagafirullah, Allah na tuba ka manta ƙarya haramun ce?" Bai ƙasa a gwiwa ba wajan furta.
"Ni ba Manzo ba, ni ba sahabi ba, ni bawa ne na Allah, a koda yaushe zan iya kauce hanya!"
Ta ware hannunta irin "Anyway, is not problem"
Ya langwaɓe kai ya ce
"Kin yarda IDAN BA KE babu numfashin Aliyu" ta nuna shi da hannu ta ce
"Wallahi ba zan koma gidanka ba, idan har ni ce kwanciyar hankalinka to ka shirya tafiya lahira da kwanan kabari" tana faɗin haka ta juya tana kaɗa masa ƙugu wanda suke ƙara sanya YAA SHEIKH cikin wani hali wanda shi kan shi ba zai iya furta ko fasalta yadda ya ke ji ba.
Ya zube akan kujera yana dafe kan shi, bakinsa ɗauke da addu'ar samun sassauci da rahamar Ubangiji. Ya miƙe a sanyaye tare da nufar part ɗinsa yana zuwa ya nufi bathroom ya sakarwa kan shi shower da ruwa mai sanyi, ya daɗe tsaye yana mayar da numfashi. Ya ɗaura alwala yana fitowa ya saka Jallabiya Viridian green mai ƙaramin hannu, ya ɗauki hirami ya ɗora a kan shi tare da ɗaukan prayer mat ya shimfiɗa.
Sallah ya yi raka'a biyu raka'ar farko ya karanta Fatiha da Surah Kafiroon, ta biyu ya yi Fatiha da Surah Al Ikhlas. Cikin sujjadar ƙarshe ya shiga faɗin.
"اَللَّهُمَّ إِنِّي أَسْتَخِيرُكَ بِعِلْمِكَ، وَأسْتَقْدِرُكَ بِقُدْرَتِكَ، وَأَسْألُكَ مِنْ فَضْلِكَ الْعَظِيم، فَإِنَّكَ تَقْدِرُ وَلا أَقْدِر، وَتَعْلَمُ وَلا أَعْلَم، وَأَنْتَ عَلاّمُ الغُيوبِ، اللّهُمَّ إِنْ كُنْتَ تَعْلَمُ أَنَّ هَذَا اْلأَمْرَ
Idan zama da Halisa matsayin matata shi ne alheri
- خَيْرٌ لِي فِي دِينِي وَمَعَاشِي وَعَاقِبَةِ أَمْرِي، عَاجِلِهِ وَأَجِلِهِ فَاقْدُرْهُ لِي وَيَسِّرْهُ لِي ثُمَّ بَارِكْ لِي فِيهِ، وَإِنْ كُنْتَ تَعْلَمُ أَنَّ هَذَا اْلأَمْرَ شَرٌ لِي فِي دِينِي وَمَعَاشِي وَعَاقِبَةِ أَمْرِي، فَاصْرِفْهُ وَاصْرِفْنِي عَنْهُ وَاقْدُرْ لِي الْخَيْرَ حَيْثُ كَانَ ثُمَّ أَرْضِنِي بِهِ."
Bayan ya kammala Sallar Istihara ɗin ya jingina da jikin gado idanunsa rufe, barci ya ƙaura cewa Idanunsa tare da yi masa hijira, ƙaramar yarinya na son Jan shi a ƙasa ya zama kamar bita zai-zai, bai taɓa mafarkin zata ƙaurace masa har haka ba,bai ɗauka bayan shi zata damu da ganin wasu nata ba, ya ɗauka iya shi ɗaya ya ishe ta a rayuwa. Ya ɗauka ba zata nemi soyayya mai zafi daga gare shi ba, sai gashi tunaninsa ya saɓa zaton shi. Har aka kira Assalatu yana zaune, rabon shi da cin kyakkyawan abinci har ya manya. Ya miƙe yana ɗaukan casbawa tare da yin waje. A harabar gidan yaci karo da Abba Hakimi da kuma Umar-khan da Ishaq-Hakim sun fito zasu nufi Masjid. Suka jera ba tare da kowa ya yi magana ba,cikin takun shi mai kama dana wahainiya, nutsuwa,kamala, kwarjini da tarin Ilhama dake kwance saman fuskar YAA SHEIKH ALIYU HAYDAR ALIYU ya shiga wajan liman tare data kabbarar harama, karatu ya fara a sanyaye cikin rashin sautin murya saɓanin da, gabaɗaya suka rasa meke damun shi yana yi yana rafkanwa, bayan ya sallame ya yi sujjada bayan sallama. (Sujjadar ba'adi). Wa'azi ya fara akan gudun duniya da duk wani kayan kyale-kyale dake cikinta.
Misalin 10 na safe Abba Hakimi da Mother da kuma Umma A'isha na zaune saman kujera Halisa fito sanye da ƙaton hijabi har ƙasa, ta durƙosa har ƙasa ta gaishe su.
"Matar ya ya akai ne?"
Ta sunkuyar da kanta ƙasa ta ce "Jon wuro makaranta nake son na koma Please" ya daɗe yana kallonta yana jajanta lamarin kafin ya ce. "An shige ki da yawa, wanne mataki ki ke kafin ku dawo?" Ta ce "Jss2 zan shiga" ya ce "Tab, yanzu Kinyi girma sai dai a biya ki zana weac da neco, bana jin kuma zaki iya karatun University"
Da sauri ta ce "Zan iya Jon wuro, Allah ina da ƙoƙari ko karatun Alkur'anin da ka ke mini haddace shi nake, gashi yanzu ina izu talatin da biyar" ya ce.
"Na gamsu, duk da ina mamakin kaifin tunaninki da basirar da Ubangiji ya baki Halisa" Mother tai murmushi ta ce "Duk wanda ya zauna da YAA SHEIKH ai ba zai taɓa zama daƙiƙi ba,balle kuma wanda ya rena" walwalar fuskar Halisa ta ɗauke ta ce "Ai da ƙoƙarina Dada ta haifeni"
Mother ta ce "Haka fa" ita dai tai shiru
Abba Hakimi ya ce "Tambayi mijinki, shi ne zai baki iznin idan ya amince zan bawa Umar-khan ya yi komai"
Tamkar zatai kuka ta ce
"Ni bani da wani miji, ka dai na haɗani da kowa don Allah Jon wuro" daga bakin ƙofa aka ce.
"Anƙi ɗin, bayan duniya ta gama shaidawa Gadanga shi ne mijinki kuma shi ne gatanki"
Jadda ta ƙarasa faɗa tana shigowa ciki, Maimoon ta biyo bayanta. Daga tsaye Jadda ta ce "Halisa ki ke meye ne? Ke kam ba a nonon Khadijah ki sha wannan mugun halin ba, uwarki ba haka take ba, ta san halarci ta san kuma wanda ya yi mata, tun wuri ina baki shawara ki bi mijinki dau da ƙafa, kafin wata can tayi ciki tashi, ni Alkur'an da zai aure mata uku ma da ya kyauta mini, ai lafinki ne da ki ka sake masa jiki yana lugudan da ya yi niyya da shi, har ya banka miki ciki, waya faɗa miki ana yi wa namiji haka? Ai basu da kunya ta wannan ɓangaren kuma tunda kuka fara dole ku ƙare tare, balle namiji kamar Malam wanda ya karanta yaji komai a Muslunci"
Wani takaici ya kama Halisa ta ce.
"To ya yi auren mana, ni daman ai bana son shi" Jadda ta dungure mata kai ta ce "Laa! Ji tsinanniyar ƙarya, mai ƙarya a ƙona shi a wuta yasin, gashi nan kin cika kin yi fam! Alamar kin son buƙatar mijinki mayya kema ɗin fitinanniyya ki yi ta lalata ɗan jama'a yanzu ki guje shi" ta juya kan Abba Hakimi ta ce "Can fa naci karo da shi, wallahi sai dana zubar masa da ƙwalla, ni na ɗauka ma da wani ɗan ganyen nai karo kai Allah ya sa mu gama da duniya lafiya, wai Malam ne soyayya ta rugurguza shi haka, huhuhu! Ke kam ba zaki taɓa gamawa da duniya salamun ƙaulin ma idan har baki rungomi mijinki da hannu bibbiyu ba, idan ba yara ki ke so kina samun cikinsu akan titi ba" ba wanda ya kulata can ta nisa ta ce.
"A to meye ma ruwana, wannan rayuwar kowa yaji da abin da yake gaban shi, Allah ya sa ba wata tsiyar na ce ba, amma dai ƴar mutan Rome kinci amanar malam" Umma A'isha ta ce "Amana kam ta ci" Jadda ta muskuta ta ce
"To Ubangiji ya san yadda zai da lamarin, ko kuma kawai ya saki ƴar banza mai zubin zabiya, ni da ƴata ce da tuni na haɗa mutin a gaban kowa zai ɗaga mata nono" ta jinjina kai ta ce "Allah ya san yadda zai da lamarin" Halisa ta haɗe fuska sosai ta ce
"Idan auren a hannunki yake yanzu ki sake mini shi, ko ki je ki sanya ya sake ni ki ga idan zan mutu masifaffiyar mata kawai" Jadda tai mitsi mitsi da idanu ta ce
"Kiga masifa akan Mai rawani Wlh shi ne azababbe, meye nawa da zan raba haɗin Allah?" Mother ta shiga cikin zan can ta ce.
"Rabo da Jadda kin ji daughter, gidan Aliyu ne ba zaki koma ba" Ta kalli Abba Hakimi ta ce
"Jon wuro makarantar?" Ya numfasa ya ce "A'a, ba ruwana jeki nemi izini wajan mijinki,kafin ya ce baƙin ciki nake masa"
Ta miƙe zuciyarta babu daɗi bata son duk abin da zai sanya ta shiga sabgar shi. Bayan tafiyarta Jadda ta ce
"Maryam haƙuri nazo baki, ki daina gani na kamar tsohuwar banza nasan me nake, Yaran da Ubangiji ya azurtaku dasu zaki duba, kada rayuwar su ta ƙare a haka" Mother ta ce.
"Ayya Jadda kin yi mini adalci kuma ki fahimci ni, wallahi a yanzu bana son Engineer ko kaɗan, zaman court kawai nake jira ya sawwaƙe mini kuma ya bani ƴaƴana..." Mother ta dinga faɗa ta inda ta shiga bata nan take fita ba. Jadda ta fashe da kuka ta ce.
"Azaba, daga nemen taimako sai zagi Maryam?" Dr A'isha data shigo yanzu ta ce.
"Babu batun zagi, Gasky ce kawai ya bata raguwar sakin ya je ya yi rayuwa da sauran karuwai" Mother ta kalli Dr A'isha haka kurum kalmar ƙarshe ta ɓata marai har taji zafin Dr A'isha ɗin. "Ya je ya yi rayuwar da sauran karuwai" hausawa sun yi gaskiya da suka ce ba a shiga tsakanin miji da mata, duk lalacewar mijinki dole a kira shi da uban ƴaƴanka, bare kuma _first love_
Jiki a sanyaye Jadda ta fito daga gidan, Engineer dake cikin mota gaban shi ya faɗi ganin yadda mahaifiyar ta shi ta fito, gabaɗaya Ƴan-uwan shi suƙi saka baki cikin matsalar.
Dr A'isha ta miƙe ganin Mother bata tanka ta ba, ta nufi bedroom ɗin Halisa ta shiga bata kyakkyawan darasi akan ƊA-NAMIJI ta ɗora ta akan tubalin da zata ka Yaa Sheikh hankali kwance duk ta nunawa Dr A'isha ita bata ra'ayin Yaa Sheikh yanzu, karatu kawai take so. Ta rantse da abin da zai kasheta ba zata koma gidan shi ba, balle auren shi.
Dr A'isha ta bata sabuwar waya mai kyau tare da sim, ta buɗe mata komai WhatsApp, Arewabooks, wattpad. Ta nuna mata yadda ake karatun littafin duk ta iya Hausa harda ɗan turanci. Kana ta sakata cikin wani shahararren group na MU MA MATA NE.
Ta ƙara yi mata gargaɗin kada ta kuskura ta ƙara barin Yaa Sheikh ya taɓa koda hannunta ne.
Kiran Ummul a waya ya sanya Yaa Sheikh shiryawa cikin wata dakakkiyar shadda mai kyau da ɗaukan idanu, fara tas ya ɗora hirami idanunsa maƙale cikin sirirn farin Glasses photochronic and faɗawar da kwayar idanunsa tayi. Kasancewar ranar juma'a ne ya ɗora Alkyabba mara nauyi, ya fito a babban malami mai ɗaukan ƙaddara a ko wanne lokaci da yarda da ita, ba zai iya driving ba haka ya sa Umar-khan ya yi driving nasa zuwa grandparents house ɗin shi. Ya fito a nutse bakinsa ɗauke da zikirin ranar juma'a ya ɗaga idanunsa ganin garin a lullume alamar hadari ne a ƙasa, ya ɗauke yana shigewa ciki.
Wacce ya gani zaune a parlourn ya bashi mamaki ainun, yaushe ta zo? da izinin wa ta fito? Ƙarar shi ta kawo wajan Ummul ɗin shi ko ya ya?
Ya yi sallama bashi da tabbacin da amsa, amma yana da yaƙinin zata amsa ɗin, kafin ya zauna Ummul ta fito hannunta riƙe da plate na wainar fulawa da lemon kankana, suka haɗa idanu ta ce.
"Sai yanzu?" Ya zauna gefenta yana jinjina kai ta ce "Daughter ga wainar nan, ɗan malalen kuma ba a ƙare ba" Halisa ta yi murmushi ta ce "Thank you Ummul ɗina" Maimoon ta ce "Zan ci ni ma" Halisa ta shagwaɓe fuska idanunta cike da ware tana buga ƙafa ta ce.
"Ummul kin ganta ko?" Ummul ta ce "Maimoon bar mata, taci tai ƙiba" Yaa Sheikh ya tabbatar gangar jikinsa ce kawai ke tare da shi, amma gabaɗaya tunaninsa, zuciyarsa, ruhinsa yana gare ta, bai taɓa ganin yadda aka so uwa kuma aka tsani ɗan ta ba.
Ummul ta juya kan Yaa Sheikh ta ce.
"Ina son ka bawa Daughter dama ta koma makaranta" kafin Yaa Sheikh ya yi magana Alhaji Farouk ya faɗo cikin parlourn...Alhaji Farouk bai gama sanin Ummul ba, amma nutsuwarsu da ta zo ɗaya da Yaa Sheikh ya sa kai tsaye ya gano ta, ya yinda da ita Ummul ɗin ganin farko ta wayi fuskar shi sbd kamar da suke da Zahrah, ba tare da nuna wata damuwa ba kasancewar ta wayayyiya ta ɗauke kai daga duban shi.
Yadda ya faɗo musu parlour without everyone's permission ba sallama ba komai shi ya ɗan sosa mata ranta.
Halisa ma ɗauke idanu tayi haka kawai ta ji zuciyarta na buga Jikinta ya mance murus.
Yaa Sheikh bai kalli Alhaji Farouk ba, bai kuma yi mmkin zuwan na shi ba, a irin gane-ganen shi ya gano kusan dalilin zuwan Alhaji Farouk ɗin.
Alhaji Farouk ya zube saman carpet bakin shi na rawa ya ce.
"Am sorry na shigo without permission, ayi mini afuwa" Ummul ta ce
"Ba damuwa,idan har lafiya?" Ya girgiza kai ya ce "wallahi ba lafiya ba Hajiya Ummul-khairy, ina cikin tashin hankali, damuwar da kuɗin da nake da shi bai isa ya siye ta ba, ko ya biya mini ita ba" Ummul tai jim
Kafin ta ɗauke numfashi idanunta can akan plasma ta ce
"To! Ubangijin al'arshi ya yi mana magani" Alhaji Farouk ya kasa cewa komai, sbd wani irin nauyi da Ummul ta yi masa a cikin idanunsa, wani kwarjininta na musamman ya mamaye shi har ya gaza cewa komai, gabaɗaya kalaman shi suka ɗauke tare da yin hijira daga cikin bakinsa.
Ummul ta fuskance shi tana girgiza ƙafa ta ce
"Alhaji Farouk ko? Ya akai ne ka same mu cikin uzuri mu ma"
Ya goge zufar data yanko masa, Ummul ta kalli Umar-khan daya shigo ta ce "Umar-khan ƙaro mana A.cn nan ko?" Ya ce "To! Ummul!"
Alhaji Farouk ya rusuna sosai tare da yin zaman ƴan bori ya ce
"Taimako nake nema Hajiya Ummul, ki dobi girman Allah dana Manzon shi, kada ki dubi girman laifin da Zahrah ta wanzo tana aikatawa a gareki, wallahi ke kaɗai ce matakin da zanbi wajan ceto ran ƴata dake gadon asibiti, cikin halin rayuwa ko mutuwa...,"
Ummul ta tari numfashin shi da cewa
"Kamar Alhaji Farouk ya yi makkowa, Ubangiji ke da rayuwa shi ke da mutuwa, kuskure ne haɗa wannan da wani bawa" ya jinjina kai ya ce
"Haka ne, na ji na ƙara samun ƙarfin gwiwar faɗa miki komai, na fahimci ba iya ɗanki ke da ilimin addini da sanin Allah da yarda da ƙaddara ba, hadda ke kan ki" Yaa Sheikh gabaɗaya a takure ya ke jinsa, duk kalma ɗaya da ake faɗa har tsakiyar kan shi yake jinta, shi ya sa ya yi baya a hankali tare da yin lamo jikin kujera yana riƙe hannun Ummul.
Alhaji Farouk ya ɗora da faɗin "Nasan idan na faɗi abin da yake rai ka, za kuga kamar na zama mara kunya, na sani duk wani uba dole zai so abin da yarinyar shi ke so, irin son nan na mutuwa wanda zai iya kaita lahira, ki kwatanta hakan matsayin ke ce mahaifiyar Zahrah, zaki iya zuba idanu ta mutu akan soyayyar wani babban Malami, masanin addini, a faɗin nahiyar nan tamu ta wajanta baki ɗaya, malamin da yake da nagarta wanda ake sauraran tafsirin shi fiye dana sauran Malaman da muke da su, malamin daya mallaki bankununi adadin wajan biyar, reshen, Kano, Kaduna, Abuja, Katsina da sauran su, wanda ya mallaki kamfanin sarrafa shinkafa domin ra gewa talakawa farashin yadda suke siye wajan wasu, malami na farko da aka samu ya buɗe gidan marayu yake ciyar da su, da kuɗin shi, yake basu karatu, malamin daya raya makarantun tsangayoyi zuwa na zamani, ina nufin YAA SHEIKH ALIYU HAYDAR ALIYU" Cak Halisa ta ajjiye wainar data ɗakko da zummar kaiwa bakinta, daman tunda aka kawo bata ci ba, tana ƙoƙarin ci Alhaji Farouk ya shigo.
Bayanan shi suka sanya ta kasa ci sai yanzu da take shirin ci ta ji abin da ya nemi tarwatsa mata zuciya da sanya ƙaramar kwakwalwarta cikin halin troma, wani irin masifaffan kishi ya ta so mata, ƙirjinta ya yi mata nauyi, numfashinta ya tsaya cak wanda ya sanya ta shiga kokawar dawo da shi amma abin ya gagara idanunta ya shiga rufewa kamar mai shirin suma, hawaye na fitowa daga cikin idanunta da sukai jajir.
A firgice Maimoon data ankara ta ce "Anti Halisa me ne ya sameki, lafiya innalillahi Ummul Yaa Sheikh Anti Halisa suma take wallahi"
Yaa Sheikh ya buɗe gajiyayyun Idanunsa wanda kwana biyu barci ya ƙaura ce daga cikinsu, yana yunƙurin ta shi Ummul ta girgiza masa kai tare da yi masa nuni daya koma ya zauna
Ya bi umarnin ta, ya zauna yana mai riƙe kan shi, a zuciyar shi tsoro da fargabar abin da ya jefa Zawjan shi cikin wannan yanayin yake, yanzu ƙwayar idanunsa suka hangota lafiya lou yanzu kuma ta rikice kamar wacce ke farfaɗiyya ko wacce Aljanu suka bugar.
Ummul ta tallafo Halisa Jikinta tare da amsar ruwa mai sanyi daga wajan Maimoon ta shiga shafa mata a fuska, a hankali ta shiga bata ruwan, Maimoon na murza hannunta zuwa tafin ƙafarta.
Duguwar ajjiyar zuciya ta ja a wahale idanunta na buɗewa da ƙyar, wani irin zafi da raɗaɗi take ji a ƙasan zuciyarta wani abu na yi mata yawo.
"Sannu Daughter, ƙwarewa ki kai hala?" Maganar Ummul ta ƙara dawo da ita daidai, ta ɗauka it was a dream ganin Alhaji Farouk zaune ya sa ta runtse idanunta muryarta na rawa ta ce. "Zuciyata zafi take Ummul gida zani" ta faɗi hakan ta biyu, tunaninta ko Yaa Sheikh zai tashi hankalinsa har yazo gareta ta sauke masa masifar dake damunta, sai taga ko inda yake bata kallo balle yasan meke damunta, hakan ya ƙara tunzurta wani baƙin ciki ya ƙara ninkuwa sosai fiye da sosai ta fashe da kukan sanin abin da yake damunta. "Mene na kukan kuma?" Ta shagwaɓe fuska tare da basarwa ta