Showing 30001 words to 33000 words out of 197828 words
Chapter 11 - IDAN BA KE 1 TO 2 COMPLETE By Na'ima Suleiman Sarauta Nimcey luve .txt
zai isa komai na lefen" Sheikh ya ware idanu jin wai 2.5m kuɗin lefen yarinyar da ko sanin kamarta bai ba,baya buƙatar kuma ya sani ɗin.
Cikin kyakkyawan lafazi Sheikh ya sake furta "2.. 2.. 2.5m A aaaa Abba yai yai yawa fa?" Abba Hakimi ya girgiza kansa yana mmkin yadda Sheikh babu abin da ya sani dan gane da rayuwar mace.
"Meke sani Sheikh Aliyu? Kasan kayan mata da tsada, ko kai Alkyabbar nawa kake siya? Duk Alkyabbar ka tafi nawa kuɗi sosai, kuma a arziƙin da Ubangiji ya yi maka dan an taɓa 2.5m har wani abu ne?" Shafa gemunsa zuwa sajansa kawai Sheikh ya yi bai damu da auren ba, amma yaji daɗin yadda Abba Hakimi ke nuna kulawarsa ga duk abin da ya shafe shi.
Abba Hakimi bai nunawa Sheikh ya san komai ga Bankunan da yake shirin buɗewa ba, dan haka sai ya ce "Ka tashi kaje can gidan, kuɗi kuma daman hakƙina ne na aurar da kai daga nan har sadaki" jin Sheikh yaƙi cewa komai ya sanya Abba Hakimi ɗago kansa ganin Sheikh ɗin ya yi zaune jingine jikin kujera ya dafe kansa da hannu bibbiyu zufa na yanko masa tsakanin gashinsa jikinsa na rawa kaɗan kaɗan.
Girgiza kai kawai Abba Hakimi ya yi tare da jawo rubutun da ya yi da safe ya tsiyaya a cup ya zuba zuma a ciki ya juya kaɗan tare da ajjiyeta gefe guda zuwa lokacin da Sheikh ɗin zai daidai a hankali shi kuma yaci gaba da duba wani littafin Tafsir.
Mother na zaune tana girgiza ƙafa cikin damuwa take kallon tilin kayan lefen dake parlourn, da sunan kayan lefen yarinyar da Sheikh zai aura. Yaya Halima ta ce.
"Na daɗe banga kayan lefe mai yawan haka ba, shi Sheikh ɗin har nawa ya bada?" Motar ba ta ce komai ba sai Dr A'isha data kalli kayan da kyau ta ce. "Kalli fa Yaya iya gold guda biyar ne, Wallahi sai na ɗaukar wa su Maimoon kowa ɗaya abar shegiya da ɗaya kawai" Mother ta kalli Dr A'isha ta ce. "Tsinke na kayan nan babu mai ajjiye mini cikin gidan nan, balle su Maimoon su saka ba su rasa komai ba, a barwa wacce aka siyawa". Dr A'isha ta ce "Amma Barrister kalli kayan fa? Ni dai sai na ɗauka dukiya ai ba hauka bane" cikin faɗa Mother ta ce "Wai meke damunki haka A'isha akwai abin da kika rasa ne balle kayan nan su dameki idan su kike let me know I'll buy it for you" a sanyaye Dr A'isha ta cewa yayat tata "Am sorry Yaya"... "Sai haƙuri Barrister" cewar Yaya Halima wacce take babba a cikinsu. Miƙewa kawai Mother tai tana faɗin "Idan ban yi haƙuri ba kashe kai na zan? Ina nan dai wlh sai na aurawa Sheikh wata macan ya haɗa mata biyu" Dr A'isha ta ce "Wai ya kaga Sheikh da mata biyu" Dr A'isha ta kalli Yaya Halima ta ce "Nifa ina da shawara Yaya Halima, mai zai hana mu kai kayan lefen nan da kanmu zamu ƙara ganin ita Zahran da ake faɗa sai mu ganu tarbiyyar ta" Yaya Halima ta ce "Gulma zamu kenan? Maza ke kaiwa a bari su kai kawai?" Dr A'isha ta ce "Please mana Yaya Please" da ƙyar Yaya Halima ta amince ta ce zata nemi Engineer domin tasan yadda Mother ta ɗauki Al'amarin ba lallai tai magana ba.
Da daddare duk suna zaune a parlour Mother, Yaya Halima, Dr A'isha dasu Maimoon da auta Fattoumah. Motar Sheikh tai parking a gidan da gudu Fattoumah ta miƙe yana faɗin "Yaa Lee Mother ta Yaa Lee nan" murmushin jin daɗi Mother ta yi ba tare da ta ce komai ba. A hankali ya fito da ƙafafuwansa waje kasancewar shi kaɗai ne da kansa ya yi driving hakan ya sanya gajiya ta saukar masa, yana fitowa Fattoumah na zuwa wajansa da gudu ta ce "Wlcm Yaa Lee" lumshe idanunsa ya yi tare da buɗewa, ganinta ƙarama kuma autarsu ya sanya ya sassauta fuskarsa tare da sunkuyawa ya ɗauke ta da hannu ɗaya, ɗaya hannun kuma ya rufe motar. Gemunsa taja ta ce "Yaa Lee ina kake zuwa muna ta missing naka" ya ware idanu bai ce komai ba sai hancinta da yaja kaɗan.
Da idanu suka bisa yana sanye da shadda ruwan madara babbar riga da jamper bai saka hula ba sai hirami daya rufe kansa da shi fuskar shi mai ɗauke sanje zuwa gemu ta bayyana ta cikin hiramin daya gewaye fuskar. Ƙamshin Roja tuni ya mamaye parlourn da ƙamshi, Maimoon da Zeefa duk suka miƙe tsaye suna sakin murmushi a tare suka ce "Sannu da zuwa Yaa Lee" bai kalle su ba ya tattara hankalinsa gaba ɗaya ga Fattoumah dake masa surutu, bayan ya zauna saman kujera ya daidaita nutsuwarsa da kyau cikin ƙasa da murya ya ce. "Barka" ya faɗa kai tsaye ba tare da In-ina ba, Dr A'isha da Yaya Halima suka kalli juna. "Dani ka ke ko Yaya Halima?" Bai kula Dr A'isha ba ko kallonta bai ba domin yasan nemen magana ce. Tai dry ta ce "Ka gama kame fuska duk girmata da kayi dole ace da mijin iya baba, ko yanzu goma ta faɗi tafi biyar albarka dole na amsa sunan uwa a gare ka" miƙewa yai da Fattoumah ganin Dr A'isha na neman fasa masa kai da surutu. Kai tsaye Upstairs ya nufa ɓangaren father domin amsa kira. Yaya Halima tabi bayan shi da kallo ta ce "Sannu Dr da tsaurin ido, lallai karanki ya kai tsako Sheikh kike faɗawa haka? Sai da Barrister Maryam ta yi aure ta haifi Sheikh da shekaru huɗu ba aka haifeki?" Dr A'isha tai dry ta ce "Wallahi yaya ƙarfin hali ne kawai, amma ba ƙaramin kwarjini ya yi mini ba, gashi ko inuwata bata samu albarkar kallo balle Ni" dry gaba ɗaya sukai. a zaune Sheikh ya samu Father hannunsa riƙe da jarida idan kaga Sheikh da Father ba zaka taɓa cewa Sheikh ne ɗa ba, domin yafi cika idanu da jiki tsayi faɗi uwa uba fuskar Sheikh data samu sumar ƙwarai ta ƙara fidda asalin shi. A kan carpet ya zauna yana sauke numfashi kansa a ƙasa bakinsa na rawar gaida Father ya yi saurin ɗaga masa hannu ya ce. "Bani da lokacin jin faa kakkkkka yayyyya, na kiraka domin ka shirya zuwa Yola wajan Zahrah kafin akai lefe jibi, umarni na baka Aliyu ba shawararka nake nema ba" Jinjina kai kawai Sheikh ya yi bai ce komai ba. "Tashi kaje idan ka zauna ba zaka amfane ni da komai ba, zan bawa Saif-wazir address ɗin" miƙewa tsaye Sheikh ya yi sai da yaje bakin ƙofa Father ya ce "Ka kwana a nan, ban amince ka koma gidan Hakimi ba daga nan har ɗaurin aure" Sheikh ya juya da sauri ya kalli Father wato ya fahimci duk abin da yake masa baya damunsa shi yasa ya sanya Abbansa cikin al'amarin. Juyawa ya yi kamar yadda ya ce ya nufi Part ɗin nasa yana tattare babbar rigarsa.
Washegari tunda ya yi sallar asuba bai koma ba, sbd wani irin mafarki da ya yi, abin ya tsaya masa yana son neman fassarar mafarkin wajan Abba Hakimi amma ya kasa, baya son mafarkin ya dangancin wani jinsi wanda ba nashi ba. Ƙarfe 7 daidai ya shirya cikin Milk ɗin shadda gezner bai saka babbar riga ba, sai golden ɗin Alkyabba daya sanya ya ɗora golden ɗin hirami, da ƙyar ya yi breakfast ɗin da Mother ta kawo masa shi ma sai da ta zauna ya gama jan ajinsa yaci kana ta fita ganin ko ƙala bai ce mata ba. Yana gamawa shirya wa Saif-wazir ya jashi zuwa garin Yola da taimakon Map. Sai da sukai nisa sosai sun ma bar Commission Quarter's ɗin sun nufi wani waje kamar daga Sama Saif-wazir yaji Sheikh yai gyaran murya kaɗan alamar ya tsaya. Waje ya nema ya yi parking gurin kamar jeji kamar ƙauye kuma. Cikin nutsuwa ya fito yana gyara zaman alkyabbar jikinsa, a hankali ya fara bin wata hanya hannunsa goye a bayansa. Sai da ya yi nisa sosai kana yaja ya tsaya. Kwance ya ganta kanta kife a ƙasa jini na zuba kaɗan a goshinta sai ƙwaryar kindirmon dake gefe guda hannunta guda riƙe da cikinta, da sauri ya zame idanunsa daga gare ta sbd kansa da yaji ya sara yana ƙoƙarin barin wajan wasu ƴan Fulani riƙe da Sanduna suka gewaye shi ɗaya ya ce "Aradu mun kama masu fyaɗen yara" Sheikh ya ware idanu amma bai nuna komai ba, wani ya ce "Wannan kamar kidnama waye kai?" nan ma shiru ya yi bai ce komai ba, Labo da yafi su iskanci ya kalli inda take kwance ganin jini a kanta ya ce "Aradu fyaɗe ya yi mata, kuma tunda kayi mata fyaɗe dole doka ta hau kanka" Sheikh trying to explain amma harshe ya sarƙe. "Kai ku saurara" Saif-wazir wanda hankalinsa bai kwanta da yadda Sheikh yabar motar ba, ya faɗa yana nufu wajan. Ƴan Fulanin suka tsaya ya kalle su sosai ya ce "Kuna hauka wanne irin fyaɗe mai yasa baku da tunani ne, yayi muku kama da wanda zai aikata haka?" Labo ya ce "Alkur'an sai na raɗeka da wannan sandan, ga jini nan muna gani ya kwantar da ita, dole kawai ya amshi hukunci" Saif-wazir ya ce "Wanne irin hukunci kuma?" Labo ya ce "Kai maza kira mana Giɗaɗo" abu kamar wasa kafin kace wani abu kusan gaba ɗaya ƴan Fulanin Rugar Bello suka zagaye Sheikh. Giɗaɗo ya kalli Sheikh kana ya kalli Labo ya ce "Zaro mana zoben hannunsa daka gani mai tsaida ne" Labo ya kama hannun SHEIKH tare da zare zoben, kusan mutuwar tsaye Sheikh ya yi yama rasa me zai ce, sai gumi dake yanko masa ya shigo ne domin tsinkar wani ganyen magani kalli yadda tsautsayi ya rutsa da shi. Kamar daga sama yaji Giɗaɗo na faɗin "Allhamdulillah mun riƙe wannan zoben matsayin sadaki" Saif-wazir ya ce "What sadakin me?" Giɗaɗo ya ce "Ai yanzu muka aura Wannan Balaraban aure da yarinyar nan, ni ne waliyin yarinyar Labo kuma waliyin Balaraban hakan shi ne hukuncin duk wanda ya yi wa wata fyaɗe a Rugar Bello, yanzu da shi da ita mata da miji ne halak ɗin sa ce....
Free pages yana gab da ƙare wa biya kuɗin ka domin shiga Paid book tuni sun yi nisa da karatu😂🤷🏾♀️.... Biya 500 ta Wannan account ɗin 6850917335 Na'ima Shu'aibu Sulaiman fidelity bank. Shaidar biya 08119237616. Ƴan nijar sun yi mini magana.*🌈 IDAN BA KE 🌈*
_*Nimcyluv sarauta*_
15....
Saif ya ce "Aure kuma? waya ɗaura, dawa kuma?" Sheikh gyara tsaiwa ya yi zufa na yanko masa ta cikin naman jikinsa,kalmar auren ta gigita masa tunani dama lissafi baki ɗaya. Labo ya kalli Saif-wazir ya ce "Aradu aure aka ɗaura musu, babu wanda ya isa ya warware shi sai ikon Rabbi.. kai Giɗaɗo maza jawo mana su cikin Rugar Bello" cikin gargaɗi Saif-wazir ya nuna Labo da hannu ya ce "Saurara fillo kake kowa, an faɗa maka aure wasan yara ne? Kuma wanda kake cewa zaka aura masa ita already yana da aure wajan matar shi ma zamu, don haka babu wani aure idan ma kunyi sai ku warware auren yanzu nan" Labo ya ɗaga sanda sama gaba ɗaya sauran Fulanin suka ɗaga sanda sama tare da zagaye su Sheikh "ƙarya kake Aradu ina shemeka na sheme banza Alqur'anin Allah, aure kuma dole ne hukuncin duk wanda ya yi fyaɗe ko ya nemi lalata ƴar mutane ke nan, ku shige muje Rugar Bello" Saif-wazir zai magana Sheikh yaja numfashi da ƙyar yana girgiza masa kai domin sarkin yawa yafi sarkin ƙarfi musamman da yake ɓangaren Fulanin suka shigo tsaf za su yi musu gayya. And he doesn't want that to happen. "But Sheikh....," Sheikh ya ware idanu wanda suke ɗaukan hankali kamar ba zai ce wani abu ba sai kuma ya yi ƙasa da murya kamar wanda aka ɗauke wa In-inar ya ce. "Saif-wazir" kallon Sheikh kawai Saif-wazir yake cikin mamaki.
Suna ƙoƙarin tsallake ta su shige Labo ya yi saurin faɗin "Waye zai ɗaukar maka matar ka? yadda ka kawo ta nan haka zaka ɗauke ta mu ƙara sa Rugar Bello" a fili Saif-wazir ya ce "Tab..." Domin yasan that's the first thing da Sheikh can't do it ba zai taɓa ɗaukan ta ba. A hankali Saif-wazir ya sunkuya zuwa inda take kwance zuciyarsa ta buga da ƙarfi lokacin da idanun shi ya sauka akanta. A ruɗe ya juya ya kalli Sheikh Aliyu haydar Aliyu wanda ya tattare Alkyabbar jikinsa idanun shi rufe lokaci guda jijiyoyin kansa suka fito hakan kuma tabbaci ne na zuciyar shi na kusa, tashin hankalin da Saif-wazir ya shiga lokacin da idanun shi ya sauka akan fuskar Halisa Danejo Rome yafi ƙarfin tashin hankalin da Sheikh Aliyu haydar Aliyu yaji akan batun auren nashi da suke ƙoƙarin ƙaƙaba mishi. Saif-wazir ya daidaita nutsuwarsa wani kuzari na zuwar masa mmkin abin da idanun shi ke nuna masa ya cika masa zuciya. Ɗaukan ta ya yi daidai lokacin da Sheikh ya runtse idanunsa yana juya baya da ɗan sauri bakinsa ɗauke da sunan Allah. Saif-wazir na gaba ɗauke da Danejo Sheikh Aliyu haydar Aliyu na binsa cikin nutsuwa da daddako haɗi da kamala yanayin yadda ya kame kansa yake tafiya zaka ɗauka sarki ko Hakimi ne. Gaba ɗaya ƴan Fulanin suka mara musu baya har zuwa Rugar Bello lokacin tuni saƙo ya isa wajan Arɗo gaba ɗaya sun fito tare da yin shimfiɗa a gaban wata bukka wacce ta cika da yalwar inuwa, tun daga nesa Arɗo ke kallon Sheikh Aliyu har cikin ransa bai na'am cewa zai aikata abin da Giɗaɗo ya faɗa ba, amma ya kasa fahimtar mene ya sanya yaji auren shi ne mafita a gare shi dama su baki ɗaya?. Saif-wazir na zuwa ya kwantar da Danejo wacce har lokacin bata farka daga suman da take ba, jini kuma bai daina zuba daga goshinta ba. Arɗo ya kalli Sheikh cikin mutumtaka ya ce "Ka zauna mana?" Ko inda yake Sheikh bai kalla ba balle ya ama shi, sai ma tsaiwa daya gyara yana ɗan duba time fuskar shi tai jajir. Arɗo ya jinjina kai yana ƙara samun ƙarfin gwiwar abin da zuciyar shi ke ayyana mishi. Cikin nutsuwa ya ce "Sannunku, an kawo ƙarar an kama wancan yana ƙoƙarin aikata abin da Rugar Bello ta hana, wasu sunce ya aikata ga yarinyar nan kwance, bisa doka duk wanda ya yi hakan muna ɗaura masa aure da ɗiyar wannan ya sanya zamu aura masa yarinyar nan a yanzu ba tare da ɓata lokaci ba" Sheikh dai jin abin yake kamar ta tsuniyar yara ko damuwa bai ba, auren Zahrah ba bai taɓa damunsa ba balle na wannan ƴar tayin yarinyar. Saif-wazir ya ce "Amma wannan kuskure ne, idan mutum baya so ba, kuma ai ba haka ake ɗaukan doka ba, shigowarmu garin kenan fa suka fara ihun ya yi me ne kamar wasu marasa ilimi?" Giɗaɗo ya ɗaga sanda zai makawa Saif-wazir Arɗo ya yi saurin cewa "A'a Giɗaɗo, ko ma dai yaya ne kuyi haƙuri aure babu fashi" Modibbo da tun ɗazo bai magana ba ya ce "Sai a karɓi sadaki wajansa ai babu lokaci" Labo ya ce "Ga wannan a wajansa muka amsa" ya miƙawa Modibbo zoben gold ɗin da suka amsa wajan Sheikh. Sai a lokacin Saif-wazir ya ƙara cewa "Ga kuɗi a bada zoben, yana da tsada sosai kuma yana da muhimmanci ga mai shi" Modibbo ya yi murmushin jin daɗi ya ce "Daman abu mai daraja muke buƙata ai" abu kamar wasa akan idanun Saif-wazir da kunan Sheikh aka ɗaurawa Sheikh Aliyu haydar Aliyu aure da Halisa Danejo Rome akan sadakin zoben gold. Modibbo ya zama waliyin Danejo Arɗo ya zama waliyin Sheikh. Mutane kusan ashirin suka shaida daga ciki harda Saif-wazir.
Shiru wajan ya ɗauka Saif-wazir ya rasa ta ya ya zai kalli idanun Sheikh ya ce da gaske Danejo matarsa ce? Zai amince da auren ne ko ya ya? Kamar gilmawar walƙiya haka Sheikh ya juya yana gyara Alkyabbar jikinsa kai tsaye baki n titi kuma ya nufa,ganin haka ya sanya Saif-wazir miƙewa da sauri Arɗo ya ce "Ina zaka baka ɗauki yarinyar ba?" Saif ya juya ya kalleta rauni ya bayyana a fuskar shi har baya son kallon yarinyar gani yake kamar idanunsa ke masa gizau da abin da yake gani ɗin. Da sauri ya ɗauke ta ya marawa Sheikh baya yana zuwa titi ya samu Sheikh zaune acikin mota ya dafe kansa da hannu bibbiyu hayaniyar duk ta sauya masa lissafi baki ɗaya, Saif na shirin saka Danejo cikin motar Sheikh ya ce "N...n.. No!!!!" Ya faɗa cikin tsawa da faɗa idanunsa na fitowa waje sosai da kyau, a tsorace ya ce "Jini na zuba a jikinta kada ta samu ƙarewar jini kuma ba zamu je da ita gida haka ba sai mun fara zuwa asibiti" kallon da Sheikh ya yi masa ya sanya Saif yin shiru yana ƙasa da ƙansa. "Please Yaa Lee Matarka...." Kafin Saif ya ƙarasa Sheikh ya yi wa motar key cikin wani irin azababban gudu ya juya kan motar tare da cillata titi ya nufi hanyar da zata mayar da shi Kano ba tare daya ƙarawa wajan Zahrah ba..
Baki Saif ya saka cike da mmkin zafin zuciya irin ta Sheikh Aliyu da alama za a sha fama kafin Sheikh ɗin ya amince da batun auren Danejo ɗin. Mota ya tsayar ya ce masa asibiti mafi kusa don Allah. Kai tsaye aka kai shi Specialist Yola dake Jimeta. Yana shiga reception yaci karo da wata cikin sauri ya ce "Oh sorry it was a mistake.." Tsaki ta ja ta ce "mistake ko rashin hankali Malam? Kana tafiya kai a sama" kallonta kawai ya yi shi bashi da lokacin ta ma, Saurayina ta ce "Banza kawai" Zahrah da hankalinta ya yi gida sbd zuwan wanda yake shirin zama mijinta ta ce "Wai Surayyerh har lokacin cacar baki gareki ne? Tunda muka zo asibitin nan ki ke neman faɗa" Surayyerh ta ɗaga hannu ta ce "Saurara Zahrah ke tunda kika samu cikin nan kike