Showing 24001 words to 27000 words out of 186776 words

Chapter 9 - TAIMIYAH Book Complete Document by Ayshat Dansabo Lemu .txt

15 Dec 2024

6571

da faran-faran ba,tana da raunin zuciya da saurin kuka,musamman idan ana kwaikwayon tafiyanta ko kiranta da suna gurguwa,yanzu zata fashe da kuka tana kaiwa Iya ƙara........✍🏻






#Ɗansabo ce#
[12/14, 10:04 PM] +234 703 769 7050: *TAIMIYYAH*❤️


©️Ayshat Ɗansabo Lemu ✍🏻

*Page 11*


TAIMIYYAH a lokacin da suka girma suka kai matakin gama Secondary School,tun a sannan ta sake gane irin tsanan da Umma tai mata bana wasa bane,da irin huɗuban da takewa Zuhrah da Basma akanta, tana cusa musu tsana da kishin TAIMIYYAN a zuciyansu,ko da yaushe tana nuna ma Zuhrah da take babba cewa,kakarsu Iya tafi son TAIMIYYAH ne kasancewan Abie Baban TAIMIYYAN yafi Baba Sani kuɗi,abinka da huɗuban uwa tun yaran basa maida kai akan zantukan ta a hankali suna girma suna sake wayo,har Zuhurah ta fara gasgata hakan tana jin kishin TAIMIYYAN a zuciyanta da jin haushin yadda TAIMIYYAN ta fita kyawun halitta,a islamiyan da suke kowa TAIMIYYAH yafi so ba ita ba,haka a dangin su Baba Sani duk idan sun je can Rimi Family House ɗinsu kowa TAIMIYYAH yafi ja ajiki da yaba kyawun halittanta,hakan ya sake jefawa Zuhurah ƙin TAIMIYYAH ta ɗauki ɗabi'an ƙuntata zuciyan TAIMIYYAN ta hanyan kyaranta a bainar jama'a,tana sukan nakasanta da kiranta gurguwa musaka,wanda ta gama gane hakan shine weakness ɗin TAIMIYYAN,domin bata iya daurewa a duk lokacin da sukai mata gorin halitta takan ji wani irin ƙunci da ɗaci har ƙasan zuciyanta,wanda take kasa controlling kanta har sai ta zubar da hawaye,tun Iya bata farga da irin rayuwan da ƴan uwan junan suke ba,har ta gama gane yadda su Zuhuran ke cin fuskan TAIMIYYAN ko agaban waye,abinda ya fusata zuciyan Iya har watarana ta haɗa Zuwairan da su Zuhurah tai musu wankin babban bargo,tare da hana su Zuhuran takowa zuwa sashin ta sai da wani dalili me ƙarfi,itama kuma TAIMIYYAN Iya tai mata iyaka da shiga Sashin Baba Sanin,sai idan ya dawo taje gaida shi ko ita Iyan ta aiketa ta fito,amma sam ta hanata zuwa ta zauna bare har su samu daman cigaba da muzantata,wanda hakan ya sake janyowa TAIMIYYAH wani sabon tsanan a zuciyan Umma da Zuhurah,Alhaji Sameer da TAIMIYYAH ke kiransa Abie bai taɓa banbanta TAIMIYYAH da Zuhurah a wajen siya musu tsadaddun Situru na xamani ba,amma sam Umma da Zuhurah basa gani gani suke a komi TAIMIYYAN sai ta zarta Zuhurah tunda Iya tafi son ta ,ko kaya me tsada aka sai ma Iyan sai ta ce TAIMIYYAH ta ɗauka ta ɗinka,da kuɗinta ma take siyawa TAIMIYYAN duk abin da tai sha'awa ta kuma ji tana son TAIMIYYAN da shi,a kwana a tashi su TAIMIYYAH suka kawo lokacin girma suka shiga shekaran gama secondary skull,zuwa lokacin duk wani kyawu da cikar halitta da Allah yai mata baiwansa ya gama fitowa fili,Yah Sadeeq lokacin yana shekaran ƙarshe a jami'an NILE Abuja,wanda Baba Sameer da yai kuɗi sosai zuwa time ɗin shi ya ɗauki nauyin karatunsa zuwa can ɗin,abinda ya faranta ran Baba Sani matuƙa tare da sake jin ƙaunar Yayan nasa,TAIMIYYAH ta fito da result me kyau tare da samun manyan kyautuka a ranan Grad ɗin nasu,sai dai lokacin da suka zo zana Jamb sai akai rashin sa'a bata samu makin da ake nema ba,domin burin ta shine tana son zama Nurse ko cikakkiyar Lawyer,domin tarihin mahaifiyanta da taji wacce tana shekaran kusa da ƙarshe ta kammala nata karatun ta haifeta ta rasu,hakan ya dasa mata son maye gurbin marigayiya TAIMIYYAH,sai dai du ka Allah bai xana hakan a goben TAIMIYYAN ba sai ta bige da shiga Federal Collage of Education da ke Zaria,kwalejin da suke kusa sosai aka bata Course ɗin ENGLISH/ECONOMICS course me wuya amma TAIMIYYAH ta dage akan cewa ya kwanta mata zata yi shi komin wahalansa,don a ganinta idan batai karatun ba bata san me zatayi ba,musamman a lokacin da take jin kanta cikin wani irin kaɗaici na rashin abokanan hira a gida,tunda ƴan uwanta na jini da xata raɓe su taji daɗi sun juya mata baya,tsakaninsu da ita sai kyara da hantara daga su har uwansu,hakan yasa daga kallo sai kallo sai kuma wayan da Abie ya kawo musu kyautan sa a wani tafiya da yayi xuwa UK,ya zo musu dashi ita da Zuhurah iri ɗaya samfurin Iphone 12Pro Max,to tunda ta buɗe shafukan sada zumunta nasu Instagram,Whatsapp,Twitter da sauransu sai suna ɗebe mata kewa sosai,musamman da Maryam Salis tasa akai adding ɗinta a groups na littafai,sosai take jin daɗin karance-katance especially idan ba Skull ranan,suna hiran su da Iya sosai domin komi nata kai tsaye take tinkaran Iya,sabida haka ta hore ta dashi,don riƙon uwa tai mata bana kaka ba,sai dai ita TAIMIYYAH ba hakan tafi so ba,tafi sha'awan ta jita cikin tsararrakinta,a skull ita ba gwanar tara qawaye bace,daga Maryam Salis,Murja Gubuci,sai Fatima Lawal, ko kaɗan TAIMIYYAH bata taɓa fuskantan kyara ko gorin halitta a skull ba,duk da yadda take kame kanta sam bata son shiga cikin mutane sabida gudun gori ko kyara akan kasancewanta me laluran ƙafa,lokacin da suke primary ne ma take samun irin yara masu tsokananta suna kiranta da gurguwa-gurguwa,ko yara suyi ta binta suna kwaikwayon tafiyanta har sai Teachers sun gani sun tsawatar,domin TAIMIYYAH zama take tai ta kuka idan ana tsokananta,ta sha cewa Iya akaita a gyara mata ƙafanta ko za'a daina kiranta da gurguwa,amma tunda ta ƙara wayau ta sanya dangana ko an kwaikwayeta bata kuka,duk qawancen da suke yi da su Maryam ɗin dukkaninsu Iya bata taɓa bari taje gidajensu ba,sai sau ɗaya ne taje gidan su Maryam Salis dake Gaskiya Layout,su dai sun zazzo nan musamman Murja da Maryama suna matuƙar son TAIMIYYAH sosai,sai wata ƴar islaminyansu Bushira wacce suke layi ɗaya,amma itama ɗin Iya bata cika bari taje gidansu ba,a cewanta bata son yawan bin qawaye gara su su biyoka gida,Yah Sadeeq tun da TAIMIYYAH ta girma ta xama budurwa sai ya sake ninka kulawan da yake bata,yana janyota a jikinsa sosai tayi sabo da shi ta yadda har yake iya sanin wasu damuwoyinta,shi kuma duk a lokacin danne Soyayyanta da yake ji yake,har ta kai ta kawo abin ya fara fin ƙarfinsa,tuni Umma ta lura da irin shaƙuwan da ke tsakanin TAIMIYYAN da Sadeeq ɗin,watarana ta sa akai mata kiran TAIMIYYAN tai mata kyakykyawan gargaɗi akan ta fita mata daga harkan ɗa,xagi da cin mutunci ranan TAIMIYYAH ta sha har ta gode Allah,haka ta baro Sashin ta koma wajen Iya tana kuka sosai,Iya batai ƙasa a guiwa ba bayan ta tirke TAIMIYYAH taji yadda sukai da Umma,taje tai mata wankin babban bargo,TAIMIYYAH sam bata damu da zuwa Lagos wajen Abie ba,domin a shekaran da ta shiga FCE a wannan shekaran ne Abie ya samu canjin wajen aiki aka maida shi Lagos,can Port-authority a kuma babban matsayi aka kai shi wajen,sai ya ɗauke Samha daga Kaduna suka koma Lagos ɗin da zama,a lokacin an haifan ma TAIMIYYAH qanni biyu duk mata Raudha da Maryam da ake kira da Nahar,yaran sun shiga ran TAIMIYYAH amma rashin samun fuska a wajen Ummie matar Abie ɗin yasa sam bata jin daɗin zuwa wajensu ko ta samu hutu,ta gwammace tai zamanta da Iya duk sanda su suka zo sai ta ga qanninta wanda suma suke tsananin son ta,sabida yadda take jansu a jiki idan sunzo garin,sau ɗaya ta taɓa zuwa Lagos ta ga inda su Abie ɗin suke,tai Sati biyu Iya ta matsa akan a dawo da ita,dama Abie ɗin tabi a jirgi lokacin da zai koma,da zata dawo ma a jirgin ya haɗo ta da wani abokin aikin sa da zai zo Zaria,tun daga lokacin bata kuma zuwa ba har ta kammala karatun NCE ɗinta baki ɗaya,ita kuma Zuhurah ta kammala Diploma da tayi a ABU Congo inda ta karanci Public Administration.Lokacin da Yah Sadeeq ya ga sun kammala karatun ne,ya fallasawa TAIMIYYAH sirrin zuciyansa akanta,amma sai TAIMIYYAN ta nuna masa rashin yiyuwan abinda yake muradi,ba ƙaramin ƙiyayya Umma take mata ba,TAIMIYYAN
Duk da kasancewanta nakasashshiya hakan bai hanata cika burinta na samun ingantaccen ilimi ba,matsi da ƙuncin rayuwa tare da gorin halitta da take fuskanta daga ahalinta su Zuhuran,duka bai raunata zuciyan TAIMIYYAN ba bare har taji cewa ita ɗin kasashshiyace har ta kasa maida hankali akan karatun ta.Abu ɗaya ta sawa ranta shine Allah shi ke halittan bawa ta yadda duk yaso ya gansa,ta kuma sawa zuciyanta cewa nakasan halittan bawa baya tashi abanza domin ubangiji yai mata baiwa da tarin ni'imomi cikin rayuwanta.Wanda a yanzu ne take sake ganin cewa lokaci yayi da zata bi shawarwarin Iya wajen dake zuciyanta,ta nuna ma su Zuhuran cewa a yanzu duk wani gori da cin fuskansu ya daina damunta,zata maida hankali wajen inganta rayuwanta da ilimi ta kowani fanni,domin tana sha'awan takai wani matakin da zata dogara da kanta har ta tallafi nakasassu irin ta,waɗanda basu da gata tunda ita Alhamdulillah cikin gata da kyakykyawan rayuwa ta tsinci kanta .


_To masu karatu mun ji miye asalin TAIMIYYAH da yadda ta taso,yanzu labarin zai fara inda zamu ji cikakken ya rayuwan TAIMIYYAN zai cigaba da kasancewa da ƴan uwan ta su Zuhurah? shin burikan ta zasu cika,wani me rabon ne zai yi nasaran shi ga zuciyan TAIMIYYAN har ya cire mata duk wani tsoro da shakku da take ji akan aure,gurgun ne ɗan uwanta zata samu kaman yadda su Umma ke faɗi,ko kuma wani ne na daban ubangiji zai jefo shi cikin rayuwanta? Duka zaku ji amsoshin idan kun cigaba da bibiyan alqalamin Ɗansabon,_




Assalamu alaikum! My peoples duka anan na kawo ƙarshen free pages da zan iya baku,ga duk wacce take buƙatan karanta cigaban labarin TAIMIYYAH sai ki biya kuɗin ki ta wannan asusun kai tsaye kamar haka👇🏻




Zaki tura 500 kacal ta wannan account ɗin 0504192664 Aisha Ibrahim Dansabo GTbank,sai ki turo da shaidan biyan ki ta wannan layin 08167768704.


Masu turo Credit zaku turo ta katin MTN na 500 ta wannan layin 08167768704 shaidan biyanku ma ta layin zaku tura.


Masu Account da Arewa Books ga yadda zaku sayi littafi👇🏻






*_AREWABOOKS LINK kai tsaye_*


https://arewabooks.com/book?id=620032232dff83519bbad5a3


*DANNA LINK DIN NAN KASHA KARATU👆🏽👆🏽👆🏽*


*_YADDA ZAKA SIYA LITTAFI A AREWABOOKS_*👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾


*Recharge* - inda ake shiga domin saka kudi cikin account.


*Balance* - Zai nuna kudin account dinku da zaku iya sayayyan littafai cikin kasuwar ArewaBooks.


*Credit/Debit Card* - Hanyar farko kuma mai dadi wajan Recharge din account dinku.


A inda (Enter your amount) za'a saka kudin da akeson Recharge din sai a taba "Proceed". Zaibude muku inda zaku saka bayanan katin banki, kuna gamawa kudinku zaishiga account dinku kaitsaye (instant).


--------


Akwai wasu hanyoyin saka kudi a ArewaBooks account kamar:


*Bank Transfer*
*Airtime Transfer*


Saidai su ba kaitsaye bane (instantly) sai ArewaBooks ta tabbatar da Transfer din, amman bayakai 1hour za'a gansa a Balance.




*Bank Transfer* - kamar yadda akwai bayani a sama da kuma account number ArewaBooks.


_Account No_ - *1220077999*
_Account Name_ - *Arewa Books Publishers*
_Bank_ - *Zenith Bank*


Bayan anyi Transfer dinne sai a cike wannan Form din:


Amount Paid: - Nawa aka tura?


Name used for transfer: - sunan da aka saka wajan turowa


Transferred time: - lokacin da aka turo


Name of bank: - sunan bankin da aka turo dashi


Deposit date: - ranar da aka turo


Sai ayi SUBMIT.


*Airtime Transfer* - muna bada shawaran ayi amfani da *Debit Card* kokuma *Bank Transfer* akan *Airtime Transfer* , amma idan yakama babu mafita saishi tau muna amsar:


MTN,
9Mobile
Glo
Airtel


Amma kamar yadda akayi rubutu a sama afara tuntubar ArewaBooks a WhatsApp domin akwai percent da ake cirewa na canji(convert) kafin kudinka yashiga Balance.


Wannan shine bayanan.
[12/14, 10:04 PM] +234 703 769 7050: *TAIMIYYAH*❤️


©️Ayshat Ɗansabo Lemu ✍🏻


*Page 12 to13*






*CIGABAN LABARI.*


________Kaman yadda TAIMIYYAH ta sanar da Baba Sani ran Monday za ta yin Registration,hakan ya kasance misalin ƙarfe Sha biyu da rabi na rana,ta shirya cikin Riga da zani na tamfar Holland.Ɗinkin yai mata ɗas a jiki duk da babu kwalliya akan fuskanta ta yi kyau matuƙa,manyan idanunta farare tas masu wani irin turuwan baƙin ƙwayan ciki sai haskawa su ke da ƙyallin baƙin kwalli da ta zizarawa idanun.Ta ɗakko gogaggen Hijab ɗinta kalan Milk wanda ya shiga da atamfar jikinta ta sanya.Wayanta ta ɗauka don neman layin Zuhurah ta ji ko ta amsa kuɗin Form ɗin kafin Baba Sani yadda yace Zuhuran ta tuna masa.Wayan na fara ringing ta koma ta jinjina da jikin gadon da take zaune,ba za ta iya cewa yaushe rabon ta da ɗaga waya ta kira layin Xuhuran ba,asalima ta ɗauki numbern su awayan Yah Sadeeq ne ko don watarana,kada wani abu ya sameka aso kiran layin ƴan uwanka na kusa ka ce ba ka da shi.Ba don haka ba ba ta ga anfanin ma aje number ɗinsu cikin wayanba,sai ko irin wannan ranan wanda sam ba ta son shiga Sasan na su ne bare wani cin fuskan ya biyo baya,tunaninta ya katse ne a lokacin da muryan Zuhuran ya ratsa kunnuwanta,daga yadda ta amsa call ɗin TAIMIYYAH ta gane ba ta da number ɗinta ba ta san waye ya kirata ba.Sabida yadda ta wani lanƙwasa murya wajen faɗin "Hello!" TAIMIYYAH da murmushi ya kwace mata ta amsa da faɗin "Salam Zuhurah TAIMIYYAH ce,kin amsa kuɗin form ɗinne mu wuce tare? Don ni yanzu zan wuce shi ne na ce bari in kira ki inj......"


Kafin ma TAIMIYYAH ta kai ƙarshen maganan ta ji ɗinɗinɗin...!Zuhurah ta kashe wayan,hakan yasa TAIMIYYAH bin wayanta da kallo tana taɓe baki,ko kaɗan abin bai ba ta haushi ba don a ganin ta Zuhurah kan ta taiwa ba ita ba,Skull ɗin ma in ba ta yi ba duk don kanta tunda ita dai ta sa ka kanta kuma za ta yin ko da Zuhuran ko ba bu,don haka sai kawai ta miƙe tana dafa ƙafanta ta fara takawa,ta isa wajen da take rataye jakunanta ta ciro wata ƙaramar jakan LV.Ta buɗe ta cilla wayanta ciki,bayan ta tabbatar duk kuɗaɗen da za tai anfani da su suna ciki.Wajen Drawern Bed-side na gado ta nufa ta buɗe tana janyo ledan Sweet da na Dabino ma su kyau da ba ta rabo da ajewa sabida yawan bada sadaka da ta ke yi,ta ɗiba ta watsa a jaka tana mai da Drawern ta rufe,ko da ta fito Ladi ta samu a falon,suka gaisa da TAIMIYYAH sannan ta wuce Ladi ta isa ɗakin Iya.A kwance ta samu Iyan ba ta jin daɗi sosai wai kanta na ciwo ta sha magani shine ta ɗan kwanta,tai mata sannu da sanar da ita zata yin Registration ɗin ta dawo.Iya tai mata fatan dawowa lafiya daga haka TAIMIYYAN ta fito daga ɗakin,tana takawa a hankali cikin yanayin tafiyanta da sai ta dafe ƙafanta me lalura.Wanda yanayin tafiyan na ta bai hana a ga ne irin nutsuwan da ke tattare da ita ba,sannu-sannu ta ke takowa layin nasu idan ta haɗu da wanda ta sani sai ta tsaya su gaisa,a haka har ta iso bakin titi inda xa ta tari Napep ya ƙarasa da ita can gaban Congo kaɗan.Inda nan ne wajen Computer Training Center ɗin yake,bata wani jima sosai ba a wajen ta gama abinda zatai ta fito wajen.Da ƙafanta ta dinga takawa tana miƙe titi,har sai da tayi tafiya me ɗan nisa kafin ta tsaida Napep ta hau,ita kaɗai ya ɗauka tunda har ƙofar gida take buƙatan ya kaita.Kuɗin da ya ambata lokacin da su ka iso ƙofar gate ɗin shiga gidan ta zuge jaka ta ciro masa,har zata shiga gida ta hango wasu yaran almajirai biyu zasu wuce ta tsaida su.Ta ba su sadakan Sweet da Dabino,har da raguwan canjin da ke jakanta ƴan goma goma ta ba su,su ka amsa su na godia ita kuma ta nufi ƙofan shiga gate ɗin gidan ta tura ta shige,zuciyanta na tuno mata da Baba Megadi wanda Umma ce tai maƙarƙashiyan da Baba Sani ya kore sa ga shi har yanzu ba'a samo wani Sabon Megadin ba,har ta isa Sasan Iya bata haɗu da kowa a Compound ɗin gidan ba,hakan kuma ba ƙaramin daɗi yai mata ba,tana isa ƙofan shiga falon na su ta fara jiyo muryan Maryam Salis.
Lokacin da ta sanya kanta cikin falon bayan Iya ta amsa sallaman da tayi,idanunta akan Maryam ɗin ya fara sauka.Ta saki wani irin murmushi tana ƙarawa takunta sauri,cike da murnan ganin Maryam ɗin ta fara faɗin "Lallai ne Maryama kin iya bazata,shi ne jiya da mu ke magana a chart ba ki sanar da ni zaki zo ba."


Ta ƙare maganan lokacin da ta ke isa kujeran da Maryam ɗin ta ke zaune.Maryaman ta saki murmushi itama tana faɗin "TAIMIYYAH kenan ai na fi so in miki bazatan tun da ke ba'a ganinki sai dai a Chart ɗin,ai ban jima da shigowa ba Iya ke sanar min kin je ki dawo."


"Wallahi bari kawai wani Computer Training na shiga in gaya miki,shine na je yin Registration zuwa next week zan fara zuwa."


Cewan TAIMIYYAH har lokacin murmushi yaƙi barin face ɗinta,ta waiwaya wajen Iya tana faɗin "Iya na dawo,ya ciwan kan na ki ina fata dai ya kama gabansa?"


Iya ta murmusa tana faɗin "Ya kama gabansa kam Alhamdulillah.Na ga ai kin yi saurin dawowa da har na ce ko za ta kira wayanki,tace a barki dai muna ɗan taɓa hira kin ga gashi har kin dawo ɗin."


Iya tayi maganan tana tashi don komawa ɗaki,ganin hakan yasa TAIMIYYAH miƙewa tana cewa Maryam "Mu je ɗaki Besty,gaskiya yau kin biya ni na ji daɗi sosai da wannan ziyara."


Maryam ta saki murmushi tana biye da bayan TAIMIYYAN har zuwa ɗakin ta,Hijab kawai TAIMIYYAH ta cire ta aje jakanta ta fito zuwa Kitchen don kawowa Maryam wani abu.Duk da ta ga Iya ma tasa Ladi aje ma Maryam ɗin ruwa da lemu,amma ita tana da raguwan Samosa a Fridge shiyasa zata soya mata kafin Ladin ta gama abincin Lunch.Cikin minti goma ta gama soya Samosan ta juye shi a kyakykyawan mazubi,ta ƙara ɗaukan ruwa da lemu ta ɗaura a madaidaicin Tray ta nufo ɗakin.Maryam ce tayi saurin tashi tana amsan Tray ɗin a hannun TAIMIYYAH tana faɗin "Haba qawata shine ba zaki kirani in ɗakko ba."


Ta aje Tray ɗin daga saman gadon,idanunta akan TAIMIYYAH da ta saki dariya tana faɗin "Haba dai zan iya ai, ba gashi na kawo lafiya ba,ke ni fa abubuwa da yawa ba na jin wahalan yin su,amma ku sai kuita ganin kaman ajigace

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login