Showing 102001 words to 105000 words out of 186776 words
Chapter 35 - TAIMIYAH Book Complete Document by Ayshat Dansabo Lemu .txt
na jigata a aiki,amma indai za a aje min komi waje ɗaya inyi aikina daga zaune shikenan."
Ummie ta saki murmushi tana kai yam balls ɗin ɗaya baki, ta gutsira tana cewa, "Allah sarki duk da haka dai ke ɗin ba mai kyuiyan aikin bace kawai,gashi ko yayi daɗi sosai egg ɗin ya kama jikinsa.Za ki yi mana a nan sasan wataran in ga yadda kike yi yake yin daɗi haka."
TAIMIYYAH tayi ɗan ƙaramin dariya tana cewa, "To shikenan Ummie duk sanda kika so a yin sai kiyi magana."
Daga haka suka ɗan taɓa hira kafin TAIMIYYAH ta baro sasan Ummie.
Ta shiga sasan Iyah kenan ta zauna, saƙon text message ya shigo wayarta,da wani baƙuwar lambar na daban.
Sai ta buɗe text ɗin ta fara karantawa,tana gama karanta saƙon, ta fahimci daga Yah Emran ne,yana mata magiya ne akan tayi picking call ɗinsa,sai ta share text ɗin baki ɗaya,ta sake tayi blocking wannan line ɗi daya turo saƙon da shi.
Memakon ta cigaba da zaman falon sai ta nufi ɗaki kawai ta kwanta,tana jin wani ɓacin rai na taso mata,don ta kasa gane me Yah Emran ke son ɗaukarta da har yake tunanin zata iya saurararsa,bayan duk irin tozarcin da yayi mata.
Ta lumshe idanunta tunanin Nass na kutsowa cikin kwanyarta,haka kawai taji wasu hawaye masu ɗumi na sauka suna biyo ƙuncinta.
Soyayyarsa da ke can ƙasan zuciyarta ke son tasowa baki ɗaya,sai ta rintse idanunta sosai tana tunanin, 'Ko a wani hali yake yanzu,shikenan Mum ɗinsa tayi nasaran tarwatsa duk wata soyayya da ta gudana tsakaninsu kenan?"
Ta kai hannu tana share hawayen dake zubowa daga idanunta,tana jin zuciyarta na wani irin ƙuna da shiga ƙunci me tsanani.
Ta gama sallamawa cewa ta rasa Nass har abada, tunda mahaifiyarsa bata sonta sabida kawai ta kasancewa gurguwa.
TAIMIYYAH ta jima tana kuka da hawaye kafin ta rarrashi kanta tayi shiru,tana faman sauke ajiyar zuciya, kewan Abie na taso mata.Tana hasaso cewa da yana raye da ta kira shi taji koda muryansa ne,amma ya riga ya tafi inda bazai dawo ba.
Wani kuka me ƙarfi ya sake kwace mata lokacin da take tuno sautin amon muryar su Nahar,da yadda suke yawan yin vedio call suna ɗebe mata kewa,yau gashi duka babu ko ɗaya a cikinsu.
Sai kawai ta kifa kanta a jikin pillow tana rushewa da kuka,tamkar za ta haɗiyi zuciyarta ko za ta huta da jin irin ƙuncin da take ji a yanzu.
Bayan ta rarrashi kanta tayi shiru daga kukan,sai ta zame tana gyara kwanciyarta bisa bed,bata jima ba sai bacci ya yi nasaran ɗaukar ta,bata kuma farka ba sai la'asar........✍🏻
#Ɗansabo ce #
[12/14, 10:10 PM] +234 703 769 7050: *Littafin TAIMIYYAH paid book ne,ga duk wanda ta tsincesa a kowani irin group ne,kiji tsoran Allah karki karanta sai kin biya 500 naira only.*
*Za ku iya min magana ta wannan number ɗin 08167768704, ko kuma ku turo kuɗin ku kai tsaye ta wannan account ɗin*👇🏻
0504192664 aisha ibrahim dansabo GTbank.
*Sai ku tura shaidan biyanku ta wannan line ɗin 08167768704.*
Masu turo credit za ku turo katin MTN na 500 ta wannan line ɗin 08167768704.
_*Ina ƴan kasuwa masu buƙatar a tallata muku hajar ku? Maza ku garzayo da kuɗi ƙalilan a tallata muku kayan siyarwanku sai dai kawai ku ji ana kiran waya don buƙatan sayan kayan ku,ku tuntuɓeni ta layina kamar haka 08167768704.*_
*44*
_____________
Kwanakin TAIMIYYAH shida da kenan da dawo daga Kano,ya kama ranan Saturday.
Ta dawo daga makarantar haddah kenan a gajiye,tana shigowa falon Iyah hancinta ya shaqo mata ƙamshin turaren SAUVAGE DIOR.
Sai tayi tsaye daga bakin ƙofar bayan Iyah ta amsa sallamar da ta yi cikin sassanyar muryar ta.Manyan idanunta ta ɗaga a hankali, tana me sauke su akan bayan Emran da ke zaune yana facing Iyah,don haka ita da take tsaye daga bakin ƙofa ya bata baya.
Cikin slowly ta dafe ƙafarta ta cigaba da takowa zuwa cikin falon,jikinta ya gama bata koma waye a zaune tun kafin ta ga face ɗinsa ma.
Emran da tun fara takowan TAIMIYYAH cikin falon ya zubo mata ido,sai ya cigaba da kallonta har ta ratso tsakiyan falon ta isa wajen Iyah tana cewa, "Iyah na dawo,Yah Emran barka da zuwa." Daga haka sai ta miƙe ta cigaba da takawa har zuwa ɗakinta.
Tana jikinta na jin tasirin kallon da Emran ya biyo bayanta da shi,zuciyarta ta ji ya ɓaci tunda ta ci karo da face ɗinsa,ga kuma wani fargaba da zullumi da ke dukan ƙirjinta.
Tambayoyi masu yawa suka dinga kutsowa cikin zuciyarta,tana tambayan kanta, 'Me Yah Emran Zaria? Don tafi kowa sanin haka kawai, ba kasafai suka cika yo tafiyayya zuwa Zaria su gaida Iyah ba,sai in da wani dalili suka fi zuwa daga shi har su Yah Anas ɗin,da wacce ya zo,kar dai a ce tafiyayya ya yo sabida ita?" Waɗannan su ne tarin tambayoyin da suke addabar zuciyarta TAIMIYYAH har ta gama cire Hijab ɗin da ke jikinta,ta aje Qur'aninta saman drawer.
Shigowar Iyah ɗakin nata ya saka TAIMIYYAH ɗaga manyan idanunta ta sauke akan Iyah,tana me amsa sallamar da tayi.Iyah ta tako zuwa cikin ɗakin tana kallon TAIMIYYAH cikin ido,tare da cigaba da nazartan yadda duk tayi wani sanyi daga ganin Emran da tayi.
Ta ɗan tsuke fuska kaɗan tana cewa, "Zainabu sai ga Emran kaman daga sama ya biyo sahunki,yace yana ta kiran wayarki kin rufe shi baya iya samunki,meyasa zaki haka TAIMIYYAH? Ke da ɗan uwanki don ya nuna yana da ra'ayi a kanki sai ya zama abin wulaƙantawa? Ya gaya min komi, yace sabida ya bayayyana miki cewa yana son ki, shine dalilin da kika matsa sai kin dawo,to maza ki canzo kaya ki fito ki samesa ni yanzu zamu fita da Sani,zani Rimi amma zan dawo kafin ya wuce,na saka Ladi a shirya abinci sai ki shiga ku yi aikin tare, ki ɗan masa wani abin na birgewa cikin girkunan zamani da kika Iyah."
TAIMIYYAH da tunda Iyah ta fara magana ta shiga shock...Sai ta ɗaga manyan idanunta ta dubi Iyah,tana ma rasa abinda zata ce,don tsananin mamaki da tsoran maganan da Yah Emran ɗin ya shiryawa Iyah,ya gama daskarar da ita a zaune.Amma sai tayi ƙarfin halin cewa Iyah, "Toh shikenan Iyah za a yi duk yadda kika ce,sai kin dawo ma yi magana,amma ni ba sabida shi na dawo ba wallahi."
TAIMIYYAH ta ƙare maganan cike da shagwaɓa da raunin murya,wanda ya saka Iyah hararanta tana cewa, "Koma dai miye ki tashi maza ki same shi bari in je nasan kila Sani na waje ya ƙariso."
TAIMIYYAH ta bi bayan Iyah da kallo lokacin da take ficewa daga ɗakin,ba tare da ta jira cewan TAIMIYYAH ba.
TAIMIYYAH ta sauke wani zazzafar ajiyar zuciyar, tana ji tamkar ta saki kuka ko zata ji sanyin takaicin da ya tokare maƙoshinta.Ta cigaba da zama daga bakin gadonta bata da niyyan tashi ta fito zuwa wajen Emran ɗin, kamar yadda Iyah ke buƙata don ita ya riga ya gama sire mata, ta kuma tsane shi tsana me tarin yawa,sai dai ta sani tunda ya riga ya tako zuwa nan ɗin,dole ta fuskancesa ta ji da wacce ya zo?
Sai ta miƙe ta isa bakin mirrow ta tsaya, bayan ta dogare ƙafarta da jikin stool ɗin.Kallon kanta tayi daga sama har ƙasa, tana sanye ne da doguwar rigan material me irin Silk ɗinnan,anyi masa ɗinkin boubou da yai mata kyau sosai a jiki.
Fuskarta babu komi sai man leɓe da ta goga tun safe da zata fita zuwa haddah,ta juyo zuwa wajen kayanta ta ɗauki ƙaramin Hijab ta sanya, ta fita zuwa falon Iyah fuskarta babu ɗigon annuri ko kaɗan.
Tunda ta fito Emran da ke zaune ya kafe ta da ido,ya ji zuciyarsa na amsawa da tarin begenta da tsananin soyayyarta da ke fisgan zuciyarsa.
Sai dai ya fi kowa sanin zallar sha'awarta ne ke haifar da zazzafar soyayyarta da yake ji a cikin zuciyarsa,ya cigaba da kallonta har ta samu waje ta zauna cikin kujeran da ke nesa da shi.
Shiru ya ratsa a cikin falon sai sautin TV da ke kunne ke tashi a hankali,ko kaɗan TAIMIYYAH ba tayi gigin kallonsa ba,tana dai jin tasirin na shi idanun a jikinta, kafin amon muryarsa ya ratsa kunnuwarta inda yake cewa, "Zainab gani na biyoki tunda rashin kunyarki har ya kai,ki sanya duka numbers ɗina a black list ko?"
TAIMIYYAH ta kwaɓe fuska tana me sake jin tsanansa na mamaye ruhinta,ta ɗago manyan idanunta ta sauke akansa,sai lokacin kuma ta kula da shigan da ke jikinsa.Yana sanye ne da wani haɗaɗɗen Filtex material na maza,kalan Blue Black da yai masa mugun kyau,don yana da hasken fata ba za a kira shi baƙi kai tsaye ba, sai dai a kira shi da wankan-tarwaɗa.
Ta ɗauke kai daga dubansa, ganin irin kallon da yake bin ta da shi kamar tsohon maye,tayi magana cikin sanyin murya tana cewa, "Rashin kunya kuma Yah Emran?"
Emran ya dannan mata harara yana cewa, "Yes rashin kunya mana da raini,sabida kin fahimci cewa tunda na ga halittarki kin tafi da zuciyata,to gani na biyoki har inda kike.Kuma na zo ne in baki haƙury akan kalaman da nayi a kanki,da abinda ya faru tsakaninmu a Kano, yanzu son ki nake ji sosai cikin zuciyata Zaynab,don haka ki amince da soyayyata mu yi aure, dama shine burin Mamie.Ta son ganin na yi auren zumunci kuma ke ta zaɓa min,zaki amince da Yayanki ya zama mijinki Zaynab?"
Yadda ya kai ƙarshen maganan cike da narke murya na zallar iya yaudara,yasa TAIMIYYAH saurin kallonsa with so much shock...! Bakinta har wani rawa yake muryarta na harɗewa lokacin da take faɗin, "Soyayyah Yah Emran,kana nufin ni kake so a yanzu wai? Kamanta cewa ina nan a gurguwata har yanzu, wacce ba za ka iya nuna ta a matsayin matarka abokanka su raina ka ba.Ina nan a musakata ban warke ba, ba kuma zan warke ba har abada idan haka Ubangiji ya so ganina,don haka ba ni kake so ba Yah Emran tun wuri ma ka gyara kalamanka,kuma kada ma ka cigaba da yaudaran zuciyarka a kaina,kace kawai jikinki nake so Zaynab amma bani kake so ba."
TAIMIYYAH na maganar ne hawaye na fara sauka a saman kyakykyawar fuskarta,hakan yasa Emran tashi zai isa inda take zaune, amma sai TAIMIYYAH tayi saurin dakatar da shi,cikin tsananin ɓacin rai take cewa, "Karka kuskura ka ƙariso inda nake Yah Emran,in ba haka ba wallahi zan maka ihu Babah Ladi ta fito,don bamu kaɗai bane a gidan, karka ɗauka don Iyah ta fita zaka maimaita irin akuyancin da kai min a Kano."
Yadda TAIMIYYAH tayi maganan cike da gargaɗi tana ɗaga masa murya,yasa Emran daskarewa a tsaye yana kasa koda motsi,sai idanu da ya zuba mata kawai yana ji tamkar ya nufeta ya rungumeta da ƙarfin tsiya,kalmar akuyancin da ta furta cikin kalamanta na ƙona zuciyarsa.
Kaman TAIMIYYAH ta san tunanin da ke ransa sai ta miƙe don bashi waje,sabida zuciyarta wani irin tafarfasa kawai take yi da zallar tsanan Emran ɗin.
Emran ganin da gaske TAIMIYYAH tafiyarta za ta yi ta bar shi, yasa shi cire murya ya kira yi sunanta Zaynab! Ya ɗaura da faɗin,
"Don Allah ki tsaya ki saurareni Baby wallahi da gaske son ki nake yi,ina sonki a gurguwan da kike Zaynab,kuma nayi kuskuren sakin kalaman dana furta miki wancan lokacin, amma kiyi haƙuri a yanzu zuciyata azabtuwa take yi da ƙaunarki me tsanani Sis Zaynab."
TAIMIYYAH da tayi tsaye jingine da jikin kujera, ta ɗaga manyan idanunta tana jifansa da wani mugun kallo,ta buɗe baki tana faɗin, "Yah Emran please ka daina furta kalmar kana sona,hakan na sake ƙona zuciyata ne da kimsamin tsananka me tsanani.Ka ɗauka ban ji duk yadda kuka yi da Mamie akaina bane? Tana roƙonka ka so ni amma kana nuna cewa faɗuwar aji ne lafiyayye kamarka ka auri gurguwa,har kana faɗin me zaka sanar abokanka idan ka auri gurguwa? Naji komi Yah Em babu abinda zaka yaudareni da shi, gurgu irina shi yafi cancanta in mallaka masa soyayyata da zuciyata baki ɗaya.Kada ka ƙara cewa kana sona ko furta wasu kalamanka na yaudara a kaina,wallahi summa billahi Yah Emran bazan taɓa ƙaunarka ba, sai dai ƙauna irin ta jini shima bazan ɓoye maka ba a yanzu tsananka nake ji matuƙa,don haka ka daina yaudaran kanka in dai ni Zaynab ce to banzan taɓa son ka ba,kuma ba zan taɓa aurenka ba Insha Allah."
Daga haka ta juya tana tafiya cikin tsarin yadda Ubangiji ya nufeta da takawa,hannunta dafe da guiwar ƙafarta na hagu ta nufi hanyar shigewa ɗakinta,hawaye na sintiri a fuskarta har ta isa cikin ɗakin tayi banging ƙofar da ƙarfi.
A kan gado ta zube tana cigaba da kuka sosai, hawayen baƙin cikin jin kalmar soyayyah daga bakin Yah Emran ɗin na sake ɓalle mata.
Ko duka jikinta kunnuwa ne ba za ta taɓa aminta da cewa sonta yake yi ba,don ta san ba son gaskiya da amana zai mata ba, sai dai so irin na sha'awa,tunda bai fara son nata ba sai a lokacin da ya tozartata ya gama ganin kyawun surarta a zahiri....."
Kukan da ya taho mata ne yasa ta kai hannu tana dafe bakinta,tana ƙoƙarin maida kukan da ke son kwace mata.
Ta cigaba da sharan hawaye tana jin kewan Nass da Soayyyarsa, na sake kassara duk wata gaɓa da ke motsi a cikin zuciya da gangar jikinta....
Muryan Iyah data jiyo daga can falon alamun har ta dawo daga unguwar da ta fita,yasa TAIMIYYAH saurin share hawayenta,ta koma da baya ta kwanta akan gadonta, tana me lumshe idanunta baki ɗaya tamkar me bacci.
Iyah ta shigo cikin ɗakin kai tsaye tana nufan wajen gadon da TAIMIYYAH ke kwance,ta kai hannu ta shiga bubbuga ƙafar TAIMIYYAH tana cewa, "Maza ki tashi tun raina bai ɓaci ba Zainab,ya mutum zai taso takanas saboda ke, ki dinga wulaƙantasa haka kamar ba jininki ba,wato har yanzu kinƙi cire son wanda uwarsa ta gama tozartaki ta nuna bata ƙaunarki,tace ɗanta ba zai aureki ba sabida ke gurguwace ko? Shiyasa zaki dinga wulaƙanta ɗan uwanki na jini da zai ƙaunace ki fiye da duk wani bare,to maza-maza ki je ki zubo masa abinci don ransa ya gama ɓaci,yace kin gaggaya masa maganganu marasa daɗi,shiyasa kika dawo nan kika kwanta.Yaushe kika koyi rashin kunya Zainab da har zaki kalli Emran kina gaya masa magana? Sabida kawai yace yana sonki shine raini zai shiga tsakani, to wallahi ki kiyayi fushina a wannan karon,kuma baki da miji sai shi don ni naji daɗi da wannan maganar da yazo da it......"
Kukan da TAIMIYYAH ta sanya ne ya hana Iyah ƙarisa kalamanta,tayi sakato da baki tana duban TAIMIYYAH babu ko ƙiftawa.
TAIMIYYAH ta cigaba da rusa kukanta tana cewa, "Iyah wallahi Yah Emran bani yake so ba,tsaraki kawai yazo ya yi amma ko Qur'ani akace in dafa akan cewa ƙarya yake bani yake so ba zan dafa,don Allah Iyah kar ki yadda da zancensa, kuma ni bazan sake fita wajensa ba zuciyata zafi take yi,in dai ba so kike hawan jini ya kamani ba,don girman Allah ki daina cewa banda miji sai shi,ki je kawai ki gama da shi ni kuma idan ya tafi zan waraware miki komi."
Iyah da ta kafe TAIMIYYAH da ido sai ta kasa cewa komi,ta juya ta fice daga ɗakin ranta a ɓace matuƙa.Amma tana isa falo sai ta yi ƙoƙarin saita kanta, ta fuskanci Emran tana bashi haƙury akan karya da gaskiyar da ya kitsa mata na cewa TAIMIYYAH tai masa rashin kunya.
Babah Ladi ce ta fito ta aje tray me ɗauke da drinks da abinci a gabansa,suka gaisa sannan ta juyo ta koma zuwa kitchen don ƙarisa aikinta.
Sai around 1:05pm Emran yai sallama da Iyah akan cewa zai koma,yaso ƙwarai Iyah tayi forcing TAIMIYYAH ta sake fitowa ya ganta, amma hakan bai samu ba.
Hakanan ya ajewa Iyah dubu goma saman kujera, yai mata sallama ya fice zuciyarsa cike da jin zafin, yadda TAIMIYYAH ta nuna da gaske ƙinsa take yi har cikin zuciyarta.
Lokacin da Iyah ta samu TAIMIYYAH a cikin ɗaki bayan tafiyar Emran.A kwance ta ganta har lokacin sai faman sharan hawaye take yi,hakan ya sanyayar da jikin Iyah tasan cewa lallai akwai wani abu, ba banza TAIMIYYAH zata dinga kuka haka don kawai Emran ya zo ya fallasa cewa yana sonta ba.
Ta nemi bakin gadon ta zauna, tana kai hannu ta ɗago TAIMIYYAH daga kwaciyar da tayi tana cewa, "Ta shi Zainabu kukan ya isa haka,sanar dani abinda ya faru,ko yake faruwa tsakaninki da ɗan uwan naki Emran."
TAIMIYYAH ta kai hannu ta share hawayenta, cikin sanyin murya da nutsuwa ta zayyane ma Iyah duk abinda ya faru a Kano tsakaninta da Yah Emran ɗin.
Bata ragewa Iyah komi ba har hiransu da Guggo Bilki da ta ji duk bata ɓoye komi ba ta sanar da Iyah,ta ƙare maganan da cewa,
"Iyah wallahi jikina yake so nina gama gane hakan,tunda tun farko ga abinda yace sannan ga yadda yaso ya tozartani ya keta mutuncina,to taya za a yi a yanzu yazo yace wai in amince son gaskiya yake min zai aureni,wallahi ƙarya ne ba son gaskiya yake min ba, don Allah Iyah ki kashe wannan maganan kada ma ya je ya yaudari Guggo Bilki ta ga kaman yayi na'am da ra'ayinta ne, alhali yaudarace yana da manufarsa akaina ne kawai,ba soyayyar gaskiya yake min ba ta sha'awace Iyah,don haka don Allah ki rufa min asiri ki dakatar da shi daga duk wani yinƙurinsa wallahi na tsanesa ya gama zube min,ni soyayyar da kowama ya fita kaina a barni inyi facing karatuna kawai,duk randa Allah ya kawo min gurgu irina sai afara min maganan auren please Iyah!"
Yadda TAIMIYYAH ta kai ƙarshen maganan cike da magiya tana kuka,yasa Iyah rungumeta a jikinta tana jin matsanancin tausayin TAIMIYYAH na keta zuciyarta.Wani irin ɓacin ran abinda Emran yayi wa TAIMIYYAH na keta zuciyar Iyah.
Cikin murya me cike da rarrashi Iyah ke kwantar da hankalin TAIMIYYAH,har tayi nasaran tsaida kukan da TAIMIYYAH take yi.
"Kiyi haƙuri Zainab bansan abinda ya faru kenan ba,da ko ganinki ma bazai kuma yi ba bare har na matsa sai kin je wajensa,zan kuma kira ita Bilkin in sanar da ita komi ta fara cimin mutuncinsa kafin mu gauraya ni da shi,ashe ina masa kallon kamamme shi ɗin watsatstsene daya ɓata wayonsa,idan yana iskancinsa a waje sai ya iya keta alfarmanki inda ya samu galaba akanki? Lallai zamani ya lalace da rashin tsoron Allah,Ubangiji ka shirya mana zuriya dana