Showing 111001 words to 114000 words out of 186776 words

Chapter 38 - TAIMIYAH Book Complete Document by Ayshat Dansabo Lemu .txt

15 Dec 2024

6608

tare da Nass ɗin, da yadda ta shiga ruɗu duk sai da ta sanar musu,ta ƙare maganan tana sheƙewa da dariya.


Zuhurah ma ta saki dariya tana cewa, "Ai ni dama na san dole sai ta shiga shock!Sabida ita duk a tunaninta bamu san komi akan rabuwarsu da Nass ɗin ba.Ga maganganun da ki kai mata Basmah,dole zuciyarta ta kusa bugawa,tamkar fa amanarta za ki ci tunda dai tsakani da Allah dole ce ta raba su, ba son ransu bane yasa ba za su mallaki juna ba,dole da tsananin ciwo ace ƴar uwarta ta jini kuma ta koma sun jone da abinda zuciyarta ke so,gaskiya ta ɗan bani tausayi tsakani da Allah."


Zuhurah ta ƙare maganar tana ɗan ɓata fuska,don da gaske ta ji tausayin TAIMIYYAH,sabida tana hango da ita a kaiwa hakan da bata san irin tashin hankalin da za a yi da ita ba.


Umma ta zabgawa Zuhuran harara tana faɗin, "To sarkin tausayi,sai ki bar mata Ameerun naki ki share mata hawaye,tunda ta baki tausayi."


Basmah ta amshe da cewa, "Barta kawai Umma tunda tafi son ta dani, aiko sai ta bar mata Ameeeun mu gani idan zata iya mitsuww...!!!"


Basmah ta ƙare maganan da jan dogon tsaki,tana faman hararar Zuhurah,wacce nan da nan ta haɗe fuska tana cewa, "Easy please Basmah,abar zancen kawai haka,Allah ya barki da Nass ya juyo da zuciyarsa gareki shikenan ko?"


Basmah ta sake sakin tsaki tana cewa, "Eh shikenan kuwa kin gama magana,zuciyarsa kuma kaman na samu na gama tunda ya riga ya shigo hannu ko Umma?"


Umma ta jinjina kai tana faɗin, "Sosai kuwa,yanzu ma zan kira Boka Maharazu in sanar masa da duk abinda ya gudana,in so samu ne itama gurguwar a yi abinda zata ji ko sunansa bata son ji,a danne zuciyarta a kuma rufe mana bakin jarababbiyar kakar taku,yadda ko magana yai nisa tsakaninki da yaron,ba za ta iya taɓuka komi ba sai dai ma ta goyi bayan abin."


"Yauwa Umama wallahi har na ƙara jin ƙaunar ki a raina, i luv u so much." Cewan Basmah tana rungume Umman suka saki dariya,ita dai Zuhurah sai ta tashi ta basu waje kawai,can ƙasar zuciyarta danƙare da tausayin TAIMIYYAH.


Umma da Basmha ko cigaba suka yi da tattaunawa akan yadda za a saito musu da zuciyar Nass ɗin, ta yanda sai abinda suka ce zai yi.




TAIMIYYAH koda ta sha maganin sai ta kwanta,kan kace kwabo kuma zazzaɓi ya rufar mata,hakan yasa hankalin Iyah ya sake mummunan tashi.
Babu shiri ta sake ɗakko mata maganin zazzaɓi ta bata ta sha,ta rufa mata bargo tana faman jera mata sannu.


Sai gabda magriba TAIMIYYAH ta iya tashi,da yake tana off ne sai ta nufi toilet ta sakarwa kanta ruwan ɗumi,tayi wanka ko za ta ji ƙarfin jikinta tunda zazzaɓin ya sauka.


Lokacin da ta fito sai ta kintsa kanta tana zura rigar baccinta me kauri, ta sanya hula akanta ta fito zuwa falo don cin abinci,har lokacin zuciyarta na mata ciwo,bata kuma fasa ganin komi kaman a cikin mafarki yake faruwa ba.......✍🏻














#Ɗansabo ce.#




_To masu karatu sai mu je zuwa don ganin yadda wasan zai kaya,amma fa sai da tausayin TAIMIYYAH ya sani hawaye_ 😰










#Ɗansabo ce#
[12/14, 10:11 PM] +234 703 769 7050: *Littafin TAIMIYYAH paid book ne,ga duk wanda ta tsincesa a kowani irin group ne,kiji tsoran Allah karki karanta sai kin biya 500 naira only.*


*Za ku iya min magana ta wannan number ɗin 08167768704, ko kuma ku turo kuɗin ku kai tsaye ta wannan account ɗin*👇🏻
0504192664 aisha ibrahim dansabo GTbank.


*Sai ku tura shaidan biyanku ta wannan line ɗin 08167768704.*


Masu turo credit za ku turo katin MTN na 500 ta wannan line ɗin 08167768704.




_*Ina ƴan kasuwa masu buƙatar a tallata muku hajar ku? Maza ku garzayo da kuɗi ƙalilan a tallata muku kayan siyarwanku sai dai kawai ku ji ana kiran waya don buƙatan sayan kayan ku,ku tuntuɓeni ta layina kamar haka 08167768704.*_


*47*


*2 Weeks Later*


Cikin biyu ɗinnan da suka wuce abubuwa da yawa sun faru ciki har da sanya ranan auren Zuhura da Ameeru da aka yi,an sanya watanni uku masu zuwa za a sha biki.
Sai Yah Sadeeq shi ma magana yai nisa har an kai kuɗin gaisuwa ana so nan da lokaci kaɗan a sanya rana.


Ta ɓangaren Basmah da Nass kuwa tuni sun gama samo kan Nass ɗin,don wani irin azababbiyar soyayya suke gwadawa juna.Basmah gaba ɗaya ta sake matowa a kansa ta kuma gama saki cewa asiri gaskiya ne,tunda gashi yayi aiki akan Nass har ya tsunduma a kogin sonta cikin ruwan sanyi.
Duk da cewa tun daga randa ya zo suka haɗu da TAIMIYYAH bai sake zuwa sunyi ido biyu ba,sai dai ta waya kawai suke shan luv ɗinsu kaman sun shekara da furtawa juna kalmar so.
Umma lokacin da ta ji wajen da Nass ɗin ke aiki a Abuja,sai taji duk ta ƙosama a sanya ranan auren Basmah da Nass ɗin,don tana saka ran lokaci kaɗan Nass ɗin zai taka wani babbar matsayi.
Gashi binciken da suka yi akansa sun gano cewa Babansa ya rasu ya bar musu ƙaddori sosai,tsaban kuɗi ne bai bari sosai ba ,duk sai Umma suka sake rikicewa akan son Basmah ta mallakesa a matsayin miji.


Ta ɓangaren TAIMIYYAH kuwa sati biyunnan tayi shine cike da ƙarfin zuciya, sabida ba ƙaramin wahala ta sha ba kafin ta iya danne zuciyarta akan cin amanan da Basmah ke son gwada mata.Iyah ce kullum ke tasa ta a gaba tayi ta mata nasiha akan tayi haƙury ta manta da komi,ta kuma yi addu'a Allah ya yaye mata dukkanin ƙuncin da take ji a cikin zuciyarta.
Tasirin nasihar da Iyah ke mata da ƙarfin addu'a da tsayuwar dare da take yi,tana kaiwa Allah kukanta akan ya cire mata duk wata soyayyar Nass da ya rage a zuciyarta,shine ya ƙara taimakawa wajen samar mata da nutsuwa.


A kuma cikin waɗannan kwanakin ne aka kammala raba gadon Abie gaba ɗaya,aka fitarwa kowa da kason sa da Allah yace a bashi.
Hatta Baba Sani da Guggo Bilki suma sun shiga cikin magada sabida Abie bai bar ɗa namiji ba sai TAIMIYYAH ita kaɗai.
Hankalin TAIMIYYAH da na su Iyah ya tashi sosai a ranan,don TAIMIYYAH kusan a kwance ta yini tana kuka,tare da tsunduma cikin tunanin yadda rayuwa ke juya mata daki-daki da tarin abubuwa masu taɓa zuciya.


Sai da taci kuka sosai ta gode Allah kafin ta sanyawa zuciyarta dangana,tayi musu kyakykyawar addu'a kamar yadda Iyah tayi mata nasiha akan yin hakan,lokacin da ta tadda TAIMIYYAR a ɗaki tana kukan.


__________


Yau ya kama Sunday tun safe TAIMIYYAH ta sanarwa Iyah da maganar zuwan ta Gaskiya Layout gidansu Zee,kwana biyu kenan da Zee ɗin ta kirata ta sanar mata cewa bata da lafiya sosai.


Hakan yasa TAIMIYYAH ke son zuwa ta duba jikin Zee ɗin,don har ma ta sanar da Sani cewa ya zo ya kaita idan anyi sallar zuhur,in yaso idan za ta dawo gida sai ta dawo a Napep.


Misalin ƙarfe sha ɗaya da rabi ta kammala shiryawa cikin wata atamfarta kalar dark coffee,wanda akaiwa ado da milk and gray.Ɗinkin ya zauna a jikinta sosai tare da yi mata kyau ba kaɗan ba,ta ɗaura ɗankwalin kayan yadda Hijab zai zauna akai sosai,bata shafa ko powder a face ɗinta ba illah man baki da tozali kaɗai data sanya.


Ta zura hijab ɗinta bayan ta gama feshe jikinta da turarenta na GIORGIO PINK,ta nufi wajen da take aje takalmanta ta ɗakko wani flat shoe ta zura.
Ƙaramar hand bag ɗinta ta ɗauka ta jefa wayarta a ciki sannan ta fito zuwa falon,don jiran ƙarisowan Sani su wuce.


Iyah da Ladi ne zaune a falon suna hiran su cike da raha,TAIMIYYAH ta ƙariso cikin falon tana me zama kusa da Iyah take cewa, "Iyah na shirya Sani kawai nake jira ya iso mu wuce,me xaki bayar a kaiwa Zee ɗin?"


Iyah da dubi TAIMIYYAH tana jinjina kyawun da ta yi duk cewa Hijab ta saka,ta buɗe baki tana faɗin,
"Masha Allah Zainabu kin ko fito fes kamar a sace ki a gudu,wannan kalar na kula yana miki kyau ƙwarai,ki tashi ki shiga ɗakina zaki ga kuɗi a saman madubi, ki ɗauki dubu biyu ki kai mata kice ta sayi lemu,idan kuma za ku tsaya da Sanin ne ku siya mata duk ba laifi."


TAIMIYYAH ta tashi tana aje bag ɗinta akan kujera tace, "Toh Iyah aiko ta gode,ina ga kawai a bata kuɗin kin san mara lafiya da ai masa kyautan kayan dubiya gwara an kai masa kuɗin,komin ciwan da yake sai kin ga yayi murna."


TAIMIYYAH tayi maganan cike da raha tana dafe ƙafarta ta fara takawa don zuwa ɗakko kuɗin,tana jiyo Iyah da Babah Ladi na dariyan zancen nata.


Tana fitowa Sani na shigowa cikin falon suka gaisa da Iyah, yana sanar da TAIMIYYAH cewa gashi ya iso.


TAIMIYYAH ta dubesa tana cewa, "Okey mu je kawai Sani ka ga rana tana yi."


Daga haka yai gaba bayan yai sallama da Iyah,itama TAIMIYYAH tayi wa Iyah sai ta dawo ta fito riƙe da bag ɗinta,ɗaya hannunta kuma na dafe da ƙafarta.


Wayar Zee ta kira lokacin da suka shiga dai-dai kwanar da Zee ɗin tai mata kwatance.Bugu biyu Zee ɗin ta ɗaga tana sake kwatantawa TAIMIYYAH layin da zasu shiga,basu wani sha wahala ba suka isa ƙofar bate ɗin gidan nasu Zee.


TAIMIYYAH ta sauka ta sallami Sani ya juya ita kuma ta nufi bakin gate ɗin tana bugawa,ba a ɗauki lokaci ba mai gadi ya buɗe mata ƙofa ta shige bayan ta sanar masa wajen Zainab ta zo.


Da fara'a Mamar su Zee ta taryi TAIMIYYAH lokacin da tai sallama a bakin ƙofar shiga falon nasu.


TAIMIYYAH ta durƙusa har ƙasa ta kwashi gaisuwa, kafin tayi masauki akan seater ɗin da Mamar Zee ɗin ke nuna mata.


Zee ce ta fito daga wani corridor tana faman murmushi cike da murnan ganin TAIMIYYAH take faɗin, "Oyoyo besty ashe kun gane kwatancen haka da sauri ba ku wahala ba,welcome dear tashi mu shiga daga ciki."


Ta ƙare maganan tana kama hannun TAIMIIYAH ta miƙar da ita tsaye,ita dai TAIMIYYAH sai blushing take kafin ta furta, "Zee kenan ya jikin naki?"


"Naji sauƙi sosai namcy sai jiri da nake fama da shi ance jinina yayi ƙasa."
Zee tayi maganar tana yin gaba zuwa ɗakinta TAIMIYYAH na biye da bayanta har suka isa ɗakin Zee ɗin.


TAIMIYYAH ta samu gefen gado ta zauna tana faɗin, "Kai namcy ki ce kina fama da abu me wahala jiri bai da daɗi sam wallahi,nayi fama da matsalar wani ciwo da nayi ban ji da daɗi ba ,sai kin ta shan ORS shi ma yana maganinsa sosai."


Zee ta marairaice fuska tana faɗin, "Ke dai bari kawai TAIMIYYAH wallahi ina jin jiki yanzu haka ɗan tafiyan nan dana yi baki ji yadda kan ke juya min ba,shiyasa bani son jirgawa ko'ina ina kwance a ɗaki."


Cike da zallar tausayin Zee ɗin TAIMIYYAH ke faɗin, "Ayyah! Sorry ai dama ba ki fita ba kin bari an nuna min ɗakin ni sai na shigo da kaina,sannu Allah ya baki lafiya namcy."


Zee ta amsa da "Ameen." Dai-dai lokacin da wata ƙaramar budurwa ta shigo hannunta ɗauke da tray ta aje gaban TAIMIYYAH.


Ta durƙusa ta gaida TAIMIYYAN cike da ladabi, daga gani ka ga ƴar aiki me hankali da tarin nutsuwa.


TAIMIYYAH ta amsa gaisuwan da sakin fuska sannan yarinyar ta miƙe ta bar ɗakin.


Hira suka fara da Zee wacce ta jingina da jikin gadon sosai sabida jirin da ke damunta,cikin hiran take tambayar TAIMIYYAH Nass, sabida ita sam bata san da maganar rabuwar TAIMIYYAH da Nass ɗin ba.


TAIMIYYAH ta ɗan ɓata fuska tana fara baiwa Zee labarin zuwansu dubiyan Mum ɗinsa da abinda ya biyo baya,har kawo kan yadda Nass suka yi da Iyah akan cewa rabuwarsu da juna shi yafi alkhairy, tunda uwarsa ta riga ta furta ba zai auri gurguwa ba.


Zee da abin yai matuƙar bata mamaki da takaici ta buɗe baki tana cewa, "Kai amma ko wannan Mum nasa jahila ce sai kace ba mace ba,har ta iya kallon tsaban idanunku taci fuskar ku haka,gaskiya da dani aka je asibitinnan da taji maganganu,amma gaskiya TAIMIYYAH ban ji daɗi ba wallahi,sabida kun dace da Nass ga shi yana son ki sosai,yanzu shikenan kun rabun da gaske kenan ko waya ba kwa yi?"


TAIMIYYAH da taji zuciyarta ta ɗan motsa tayi saurin girgiza kai tana cewa, "Wallahi Zee ba ma yi ni hakan ma yafi min akan mu cigaba da mu'amalar da bai da wani anfani, tunda ba bari za ai manufa me kyau ya tabbata ba,ina ga ma yanxu ai ya samu matar aure."


"Ki bar wannan maganar namcy wa ya gaya miki har ya manta ki da har zai yi sabuwar budurwa nan kusa? Koda yake ba abin mamaki bane idan akai la'akari da mazan wannan zamanin,amma ko idan hakan ya tabbata xan yi mamaki sabida yadda ya mato a kanki."


Zee tayi maganan idanunta akan TAIMIYYAH wacce ke faman sakin murmushin yaƙe,kafin ta dubi Zee ɗin cikin sanyin murya tana faɗin, "Allah da gaske nake yi Zee ya samu wata wacce ba gurguwa ba,ai kin san dama shi aure yake son yi da gaske babu ɓata lokaci,kin ga don ya samu wata cikin gaugawa ba abin mamaki bane."


Yadda TAIMIYYAH tayi maganan muryarta na ɗan rawa na bayyana raunin da ke cikin zuciyarta yai bala'in taɓa zuciyar Zeee, wani irin tausayin TAIMIYYAH ya lulluɓe zuciyarta,don ita shaida ce akan cewa TAIMIYYAH ta kamu da soyayyar Nass ɗin sosai,kuma ko a yanzu ta sani ƙarfin hali kawai TAIMIYYAR take yi.


Ta miƙa hannu ta kamo na TAIMIYYAH tana magana cikin lallashi take cewa, "Sorry ƙawata ki yi haƙury haka rayuwa take cike da tarin jarabawa da kuma ƙalubale,ki ɗauka cewa kawai Nass ba alkhairy bane a gareki tunda har hakan ya faru,Allah xai kawo miki mafi alkhairy soon, ni ina ji ajikina Allah ba zai barki haka ba zai yi miki blessing da abu mafi daraja wanda duk masu rainaki sai sun sha mamaki.Don haka ki yi haƙury Zaynab Allah sa haka shi yafi alkhairy."


TAIMIYYAH ta sake sakin murmushi cikin ƙarfin halin ɓoye damuwa da raunin da take ciki,tayi magana cikin dakiya tana cewa, "Hakane Zee rayuwa na cike da abubuwan mamaki da jarabawa kala-kala,Allah ya bamu ikon cinye ko wace irin jarabawa me daɗi ko marar daɗi."


Zee ta amsa da "Ameen namcy Allah ya ƙara miki ƙarfin imani da ƙarfin zuciya."


Daga haka suka cigaba da hiran rayuwa, koda wasa TAIMIYYAH bata sanar da Zee ɗin cewa Nass wajen Basmah ƙanwarta ya koma ba.Ta rufe wannan sirrin don tana ganin kaman tonawa kai asiri ne da tozarta ƴar uwarta idan ta kwashe abinda Basmah tayi mata ta sanarwa Zee ɗin.
Hakan yasa har suka gama hiran samari da irin ƙalubalen da mata ke fuskanta a soyayya, sam TAIMIYYAH ta kasa sanar da Zee ɗin abinda Basmah ta aikata mata,duk da irin yadda abin ke cin zuciyarta amma ta danne bata gaya mata Zee ba. ( _Ƙalubale gare ku marasa sirri da ƙiris kuke jira abu ya faru daku ku je kuna yayatawa ƙawaye,ba ko wani irin sirri bane zaka dinga sanarwa ƙawa,musamman abinda ya shafi family issue,kun dai ga yadda TAIMIYYAH tayi ƙoƙarin rufe aibun ƴar uwarta alhali ita ƴar uwartata cin amanarta tayi, amma bata buɗe sirrinta a waje ba,sabida komin lalacewan jininka jininka ne dai da baka da tamkarsa sai mu kula please!_ )


Sai da TAIMIYYAH ta idar da sallar la'asar sannan tayi shirin tafiya gida.
Zee sabida jirin da take fama dashi ba za ta iya yowa TAIMIYYAH rakiya ba,sai ta haɗata da Rahane me aiki don tayi mata rakiya zuwa bakin hanya, inda za ta samu Napep cikin sauri,sai godia take wa TAIMIYYAH akan kuɗin da Iyah ta bayar abata,wanda TAIMIYYAH ta haɗa da kuɗinta dubu uku ya zama dubu biyar ta baiwa Zee ɗin tace ta sayi lemu.


Mamar su Zee ta bai wa TAIMIYYAH wasu fashion masu kyau,TAIMIYYAH ta amsa tayi godia sannan suka fito da Rahane da za tai mata rakiya.


Sai da suka fito waje sannan TAIMIYYAH ta kula da hadarin da ke haɗuwa a garin,nan da nan sai hankalinta ya tashi don bata son dukan ruwa sam!


A hankali suke takowa daga cikin layin gidan su Zee ɗin har suka iso ainihin kan titi inda zata iya samun abin hawa. Zuwa lokacin hadari ne sosai ke sake haɗuwa a garin,TAIMIYYAH sai ta sallami Rahane tace ta koma gida kawai bayan ta buɗe jaka ta bata ɗari biyu, Rahane ta amsa tayi godia tana juyawa don komawa gida.


Ita kuma TAIMIYYAH sai ta ɗan gangara zuwa wajen wani dutse,ta jingina da shi tana sauke numfashin gajiyar da tayi sabida da ɗan nisa daga gidan su Zee ɗin zuwa bakin titin.


Ta jima a tsaye ƙafarta ɗofane a jikin dutsen don jin daɗin tsayuwa amma bata samu abun hawa ba.
Duk Napep ɗin da zai zo a cike zata gansa da mutane a ciki, ga kuma hadari da ke sake haɗuwa sosai har garin ya fara cida, alamun ruwa na gab da sauka,hakan yasa hankalin TAIMIYYAH ya kai ƙololuwa wajen tashi.


Wani Napep ne ta tsaida daga can tsallaken titi ta yadda dole sai ta tsallaka titin za ta shiga,gashi motoci da mashina sun ƙi tsagaitawa bare ta tsallaka ta daɗi,zuwa lokacin har yayyafi ya fara sauka hakan yasa me Napep ɗin fitowa don ya tsallako ya tsallaka da ita, dai-dai lokacin ne kuka ruwan ya sauka me ƙarfin gaske.


Ita kuma TAIMIYYAH da sam hankalinta bai kai kan me Napep da ke ƙoƙarin tsallakowa wajenta ba,ganin kamar mota da mashin ɗin dake tahowa a nesa suke,sai kawai ta nufi titin gadan-gadan tana dafe da ƙafarta don tsallakawa,sai da ta shiga tsakiyan titin ta kula da me mashin ɗin daya taho a guje,sai tayi baya don komawa ɗaya ɓarayin ba ta san mota ta taho ba, kawai ji tayi an wantsakali da ita can gefen titin kanta ya bugu da dakalin kwalbatin bakin hanya.
Lokaci guda ita da me Napep ɗin da ya taho don taimakonta suka saki ihu,me motar da ya kaɗe ta yayi saurin gangarewa gefen hanya ya faka motar suka nufo inda TAIMIYYAH take a yashe shi da matar da ke cikin motar.


TAIMIYYAY da ke yashe a gefen kwalbatin sai zubar da jini take, da alamu wani waje a fuskarta ko gefen wuyarta ne ya tsage ko ya fashe shiyasa jini ke zuba sosai.
Gabaki ɗaya kanta yayi wani irin nauyi gingirin,sabida ba ƙaramin bugawa tayi ba

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login