Showing 108001 words to 111000 words out of 186776 words
Chapter 37 - TAIMIYAH Book Complete Document by Ayshat Dansabo Lemu .txt
nufi wajen da wayar take aje tana ɗauka, ta kai kunni bayan tayi receiving tana cewa, "Yah Nass har ka iso ne,ok gani nan fitowa yanzu." Daga haka ta aje wayan ƙirjinta na faman dokawa,cikin hanzarin ta ɗauki veil ɗinta me shara-shara ta yafa, ta fito daga ɗakin nasu ta nufi ƙofan fita.
Naseer wanda tun isowarsa ƙofar gate ɗin gidan memories ɗinsu da TAIMIYYAH ya shiga dawowa kwanyarsa.Sai ya dinga jin wani zumuɗi da shauƙin son ganin kyakykyawan face ɗin TAIMIYYAH da yayi missing tsayin lokaci.
Sabida Basmah ta yaudare shi da cewa idan ya zo,ita ce zata san yadda za a yi ta jawo masa TAIMIYYAH zuwa sasan su, ba tare da Iyah tama san ya zo gidan ba.
Ya cigaba da jingina da jikin motarsa hannunwansa duka biyu harɗe saman ƙirjinsa,ya kafe ƙofar gate ɗin da kallo yana jiran ganin me fitowa daga ciki.
Basmah ta buɗe ƙofar ta fito cikin wani irin taku na ɗaukar hankali,take nufowa inda Nass yake tsaye.
Nass ya dinga bin ta da kallo yana ji kansa ya fara wani irin sarawa,tun lokacin da ya ɗaura idanunsa akan Basmah.Ta ƙariso tana kashesa da wani irin murmushi,da har haƙoranta suka bayyana,kafin tayi magana cikin narke murya tana cewa, "Sannu da zuwa Yah Nass mu je daga ciki ko."
Nass da gaba ɗaya kansa ke wani irin juyawa, sai yayi saurin dafe goshinsa da hannu yana cewa,
"Okey toh."
Daga haka Basmah tayi gaba shi kuma yana biye da bayanta,idanunsa na yawo akan jikinta yana kallon yadda take motsa albarkatun jikin nata cike da gayya,take wani irin baƙon abu ya fara tasowa daga cikin zuciyarsa yana mamaye ilahirin jinin jikinsa,kansa ya yi masa wani irin nauyin da bazai iya misaltawa ba.
Har suka isa part ɗin su Basmah ya rasa abinda ke masa daɗi.Basmah kuwa sai wani rawar jiki take yi ta rasa inda zata tsoma ranta, sabida murnan ganin Nass ɗin a gabanta.
Gabaki ɗaya wankan da ya shawo cikin wani dark gray ɗin gezner ya gama tafiya da zuciyarta,ta zauna kusa da shi idanunsu na sarƙewa cikin na juna.
Nass ya ji wani irin yanayi na ratsa shi har cikin ɓargonsa,ya kai hannu yayi saurin dafe kansa da ke sara masa, yana son karanto addu'a amma ya kasa.
Basmah da ke lura da yana yinsa sai ta saki murmushi tana cewa, "Bari in zuba maka lemu ka sha kafin in je in taho maka da TAIMIYYAH."
Tayi maganan tana tsare shi da ido don son ganin reaction ɗin da zai nuna.
Ga tsananin mamakinta kuwa sai gani tayi, ya ɗago yana mata wani irin kallo,kafin yayi magana cikin sanyin muryarsa yana cewa,
"No Basmah karki kira ta please! Ni ba ita nazo gani ba, yanzu zan koma gidama kaina ciwo yake me tsanani,tunda ke na ganki its okey please!"
Basmah da taji kamar ta saki ihun murna ta taka rawa,sai ta maze ta wani haɗe face tana cewa, "Ban gane zaka wuce yanzu-yanzu ba,bayan ba ka ga sahibar taka ba."
Nass da ke ji wani irin duhu na lulluɓe zuciyarsa,yayi saurin duban Basmah yana cewa, "Yes bana jin ganinta ne kawai,tunda na ɗaura idanuna akanki na ji cewa bama sai na ganta ba,tunda dama Mum tayi Allah ya isa idan har na cigaba da bibiyarta,please kar ki dage akan sai na ganta Basmah."
Yadda ya kira yi sunan Basmah ya sake narkar da zuciyarta,ta wani yi masa fari da ido tana cewa, "Okey Yayana na fahimceka,yanzu dai sha wannan sai mu ɗan taɓa hira kafin ka wuce ɗin."
Tayi maganan tana miƙa masa cup ɗin da ta cika masa da lemun zoɓon,wanda da aka dafa shi da ruwan magani.
Nass ya amsa ya kai baki yai masa kurɓa biyu ya aje,sabida uban sugar da aka cika, wanda yaji zaƙin har hawa masa kai yake yi.
Cikin kissa Basmah ke jansa da hira yana biye mata, duk da irin ciwan kan da yake ji amma sai yaji tamkar wanda aka ɗaure da igiya, sam baya son barinta hasalima muryarta ne yake ji na rikiɗe masa yana komawa tamkar na TAIMIYYAH.Shiyasa ya sake sakin jiki tana cigaba da hilatarsa da hira, har zuwa sanda Zuhurah ta shigo suka gaisa da Nass ɗin,ta fita ta basu waje bayan sun haɗa ido da Basmah sun sakarwa juna ƙayataccen murmushi..........✍🏻
#Ɗansabo ce#
[12/14, 10:11 PM] +234 703 769 7050: *Littafin TAIMIYYAH paid book ne,ga duk wanda ta tsincesa a kowani irin group ne,kiji tsoran Allah karki karanta sai kin biya 500 naira only.*
*Za ku iya min magana ta wannan number ɗin 08167768704, ko kuma ku turo kuɗin ku kai tsaye ta wannan account ɗin*👇🏻
0504192664 aisha ibrahim dansabo GTbank.
*Sai ku tura shaidan biyanku ta wannan line ɗin 08167768704.*
Masu turo credit za ku turo katin MTN na 500 ta wannan line ɗin 08167768704.
_*Ina ƴan kasuwa masu buƙatar a tallata muku hajar ku? Maza ku garzayo da kuɗi ƙalilan a tallata muku kayan siyarwanku sai dai kawai ku ji ana kiran waya don buƙatan sayan kayan ku,ku tuntuɓeni ta layina kamar haka 08167768704.*_
*46*
Lokacin da Basmah da Nass suka fito daga part ɗin Baba Sani ta ƙofar waje, dai-dai lokacin ne TAIMIYYAH da Shukurah suka fito daga sasan Iyah, TAIMIYYAH za ta yiwa Shukurah rakiya zuwa bakin gate.
Shukuran ta kawowa TAIMIYYAH ziyara ne don sun rabu da haɗuwa da juna,sabida TAIMIYYAH ta daina zuwa islamiya, sai haddah kawai take zuwa.
Sam ita TAIMIYYAH bata kalli sashin part ɗin Baba Sanin ba,don haka bata kula da fitowan su Basmah da Nass ba,sai ita Basmah ce ta hangi su TAIMIYYAH da suka nufi hanyar gate.
Ta wani saki murmushi tana jin sabon nishaɗi na kewaye zuciyarta.
Har suka isa bakin gate ɗin Basmah na faman zubawa Nass hira,wanda gaba ki ɗaya shi Nass ɗin hankalinsa baya ma kanta,sabida yadda ciwan kan da yake ji ke sake tsanani.
Sun ƙariso bakin gate ɗin ne dai-dai lokacin da TAIMIYYAH ta juyo don komawa cikin gida.Caraf! Sai sukai ido huɗu da Nass wanda ke tahowa, cikin wannan takun nasa da ta sani, me cike da nutsuwa.
Idanun TAIMIYYAH suka sake girma,tana sake waro su waje cike da ɗimbin mamakin ganin Nass shi da Basman,waɗanda ke tahowa Basmah na binsa agindi-agindi tamkar kafaɗunsu za su yi gogayya juna.
Bakin TAIMIYYAH har wani rawa yake wajen furta kalmar,
"Nass...!!!"
Yadda ta faɗi sunan murya a waje sosai ya sanya Nass da shi ma ya zuba mata ido, kansa na sake sarawa tamkar zai rabe gida biyu,yayi saurin rintse idanunsa yana ji tamkar kansa zai bar gangar jikinsa.
Ganin yadda Nass ɗin ya rintse ido, yasa Basmah isa gaban TAIMIYYAH tana cewa,
"Yah TAIMIYYAH miye hakan daga ganinsa zak kira sunansa cike da ɗaga murya haka?Nass ɗinki ne dai da kuka rabu ba gizo yake miki ba,don haka in mamaki kike yi ki daina."
Basmah ta ƙare maganan tana aika mata wani mugun harara,tana me komawa kusa da Nass tana faɗin, "Sorry my Nass,har yanzu ciwan kan ne dai?"
Nass da idanunsa har lokacin yake a rintse kansa na juyawa,ya buɗe idon yana sauke su akan TAIMIYYAH da tai mutuwan tsaye, ta kasa koda ƙwaƙwƙwaran motsi sabida shiga shock da tayi.
Nass yayi saurin buɗe baki yana faɗin,
"Zay..na.b!"
A rarrabe ya faɗi sunan zuciyarsa na mamayewa da wani irin duhu, ya wuce su TAIMIYYAH fuu..!!! Tamkar wanda aka dannawa remote control.
Hakan yasa TAIMIYYAH bin bayansa da kallo, zuciyarta na wani irin shaking a ƙirjinta.
Wani irin gagarumin tashin hankali take ji na rufto mata,sai tayi gaggawar maida dubanta ga Basmah,cike da son jin ƙarin bayani daga gareta.
Kamar Basmah ta san nufinta sai ta tako har xuwa gaban TAIMIYYAN, wacce zuwa lokacin dukkanin jikinta ya ɗauki rawa,tana dafe da guiwar ƙafarta me laluran.
Basmah ta murmusa tana kai hannu zata dafa kafaɗan TAIMIYYAH, amma sai TAIMIYYAH tayi saurin yin baya tana jingina da jikin gate ɗin.
Tana ji ƙafafunta na neman gaza ɗaukar nauyin gangar jikinta.Basmah ta sake sakin murmushi tana cewa, "Yah TAIMIYYAH kiyi haƙury, na san ba za ki taɓa jin daɗin tarayyata da Nass ba,amma am sorry to say zuciyata ta jima da kamuwa da son abinda zuciyarki ke so,sai kuma akai sa a baku dace da juna ba tunda ke Allah ya yoki gurguwa,shi kuma Nass lafiyayyan namijin da ya mallaki duk abubuwan da mace za ta buƙata a wajen ɗa miji."
Basmah ta ɗan dakata da maganar, tana sake shigar da idanunta cikin na TAIMIYYAH,wacce zuwa lokacin wani irin zufa ya fara wanke fuskarta.Basmah ta cigaba da cewa, "Tun randa na fara ganinsa a wajenki na faɗa kogin soyayyarsa,amma sai nai ta dannewa sai a yanzu dana bibiyesa na gane cewa,uwarsa ta raba ku don kasancewarki gurguwa,ba zai yiwu ɗanta ya aure kina a gurguwa ba,shiyasa ni kuma naga bazan iya bari mu rasa shi duka mu biyu ba......."
Yadda TAIMIYYAH ta jefo mata wani mugun kallo ne ya saka Basmah kasa cigaba da maganarta,kamar yadda TAIMIYYAH itama ta kasa cewa komi, sai hannu da ta kai ta dafe saitin zuciyarta tana jin wani irin zafi da ƙuna.
Kanta ne yai wani irin sarawa tana jin duniyar gaba ɗaya na juya mata,cikin sauri ta fara takawa tana nufan hanyar komawa sasan Iyah.
Basmah tabi bayan TAIMIYYAN da kallo wani abu na motsawa cikin zuciyarta,amma wani sashin na danne tasirin abinda ke tasowan,sai ma tayi saurin juyawa ta fice daga gate ɗin gidan, ta nufi wajen motar Nass da ke fake daga waje.
Tana isa ta samesa cikin motar ya haɗe kansa da styering motar idanunsa a rufe ruf! Ta saka hannu ta buɗe front seat ta shiga ta zauna, tana kiran sunansa cikin narke murya.
Nass ya ɗago idanunsa da suka rine zuwa ja,ya sauke akan fuskar Basmah yana ji tamkar ya fasa ihu ko zai dawo cikin hayyacinsa,ya gano meke shirin faruwa da shi amma ya kasa.
Ya zubawa Basmah ido zuciyarsa na cigaba da dokawa, tamkar za ta yi tsalle daga ƙirjinsa ta fito waje,Basmah dake ta faman kallon yanayin da ya shiga, sai tayi ƙasa da murya tana faɗin, "Sorry My Nass kanne dai har yanzu,kayi haƙury ka ƙarisa zuwa gida ka samu magani ka sha, zuwa anjima sai muyi waya ko?"
Nass daya zama tamkar wani gunki sai ya samu kansa da gyaɗa mata kai,yana maida idanunsa ya sake lumshesu,kafin ya sake buɗe su akanta yana cewa, "Okey Basmah, but don Allah meke shirin faruwa da ni ne?"
Basmah ta aika masa harara ƙasa-ƙasa tana cewa, "Kamar yaya Yah Nass?"
Nass ya cije lips ɗinsa yana kai hannu ya dafe kansa yake cewa, "Basmah zuciyata ciwo take yi,ga kaina da nake ji tamkar zai rabe gida biyu tunda na iso ƙofar gidannan,gaba ɗaya na rasa dukkan nutsuwata,a yanzu kuma da nayi ido biyu da Zaynab,ina ji tamkar zuciyata zata yo tsalle daga ƙirjinane ta fito waje,raina zafi yake yi Basmah meyasa zan ji hakan alhali ina son ta so me tsanani?"
Yadda ya tsare Basmah da idanunsa da suka sauya kala,yasa Basmah taɓe baki ta sake kwantar da murya tana cewa, "Naseer bazan iya gane komi ba, tunda nima a haka na ganka sanda ka iso,amma karka damu yanzu kana buƙatan ka je ka huta, ka sha magani sai muyi magana zuwa anjima, Allah ya baka lafiya my bro."
Nass ya jinjina kai kawai a lokacin da Basmah ke ficewa daga motar,ta juya don komawa cikin gida,tana Allah-Allah ta isa zuwa sasansu don baiwa su Umma labari.
Nass ya bi bayanta da kallo zuciyarsa na ɗarsuwa da wani irin feeling da bai taɓa jin irinsa ba,ya rintse ido tare da cije lips ɗinsa tamkar zai fasa shi,yana me dafe kansa yana furta kalmar, "La'ilaha'illallah!"
Ya cigaba da zama cikin motar har lokacin hannunsa na dafe da kansa,sai da ya ɗauki lokaci me tsawo kafin ya iya tada motar ya bar ƙofar gidan.
A ɓangaren TAIMIYYAH kuwa,ikon Allah ne kawai ya ƙarisar da ita zuwa sasan Iyah,sabida ta turguɗe a tafiyarta babu adadi kafin ta isa cikin sasan.
Gaba ɗaya jikinta da ko'ina ma rawa suke yi, tsabagen shiga shock da tashin hankalin ganin Nass ɗinta tare da Basmah.
Lokacin da ta iso cikin falon Iyah sai kawai ta zube akan kujeran farko, tana sakin wani irin kuka me tsuma zuciya.
Iyah da ke zaune ta taso da sauri ta nufo wajan TAIMIYYAH tana faɗin, "Lafiya Zainab, meke faruwa haka zaki shigo ki xube min kina kuka, daga rakiyar ƙawa maza sanar dani me yafaru?"
TAIMIYYAH sai ta sake rushewa da kuka,tana kama hannun Iyah ta kai saitin ƙirjinta tana cewa, "Iyah danne min ƙirjina ina kamar zai fashe,zuciyata zafi take yi Iyah kamar numfashina zai ɗauke."
Yadda take maganar tana rishin kuka ya ɗaga hankalin Iyah,tayi saurin zama cikin kujeran tana ɗago TAIMIYYAH zuwa jikinta tace, "Subhanallahi! Ni Fatima meke shirin faruwa da marainiyar Allah,Zainab sanar dani meke damunki? yanzu-yanzu sai Ubangiji ,lafiya kuka fita da Bushira kuna hiran ku abin sha'awa fa."
Iyah tayi maganar hannunta akan ƙirjin TAIMIYYAH, tana jin yadda zuciyarta ke bugawa tamkar zai fito daga ƙirjinta.
TAIMIYYAH ko cigaba tayi rasgar kukanta, hannunta na damƙe da ɗaya hannun Iyah,tana ji tamkar zuciyarta ta fito waje ko zata samu sauƙin abinda take ji.
Iyah data rasa abin cewa sai kawai ta fara janyo duk addu'ar da ya zo bakinta tana tofawa TAIMIYYAH,suka ɗauki lokaci me tsawo a haka kafin TAIMIYYAH ta tsaida kukan,amma har lokacin taƙi bari Iyah ta cire hannunta daga kan ƙirjinta da yai masifar yi mata nauyi.
Da ƙyar da kuma rarrashi Iyah ta ciyo kan TAIMIYYAH ta sanar mata da abinda ya faruwa a waje.
Tun daga kan ganin Nass da Basmah da tayi har zuwa kan maganganun da Basmah ta gaya mata,bata rage komi ba ta zayyanewa Iyah ta kai ƙarshen maganar tana kuka me tsuma zuciya.
Iyah da itama tai mugun shiga tashin hankali da ruɗu,sai tayi saurin furta kalmar, "Hasbunallahu wani'imal wakil!" Sannan ta cigaba da cewa, "Yanzu har lalacewar Zuwaira ya kai haka,wace iriyar ƙiyayyya suke miki da suke so lallai sai sun tozartaki sun ci amanarki har haka? Kiyi haƙuri Zainab!kiyi haƙury! Shine abu na farko da zan fara gaya miki,sannan ki kwantar da hankalinki ki baiwa zuciyarki ƙwarin guiwar ɗaukar dukkanin ƙaddaranki na rayuwa.Na sani da ciwo amma ki daure ki barwa Allah komi,ki kuma zuba musu ido bana so ki nuna komi, koda ace za a kai matakin da Basmah za ta auri Naseeru,dai-dai da rana ɗaya karki bari su gane cewa sun ƙuntata zuciyarki,karki bari su ga damuwa akan fuskarki Zainab..."
Iyah ta dakata kaɗan tana ji tamkar itama ta taya TAIMIYYAH kukan,ko zata ji sauƙin baƙin cikin da ya lulluɓe zuciyarta itama.Amma memakon hakan sai ta ƙarfafi zuciyarta ta cigaba da cewa, "Tunda dama uwarsa bata son ki,ina so ki danne zuciyarki Zainab,ki zuba musu ido in dai cin amanace su yi da kyau, Allah zai nuna musu iyakarsu ya kuma yi miki sakayya sabida sun yi hakan ne don su tozartaki...."
Iyah ta sake dakatawa daga maganar,zuciyarta na tsananin ƙuna,kafin ta cigaba da faɗin, "TAIMIYYAH ita duniya idan kina cikinta,to har ki barta ba za ki daina fuskantar ƙalubale, da ganin tarin abubuwan mamaki da ruɗu ba,musamman da muke cikin wani irin zamani,da tsoran Allah ya yi ƙaranci a zukatan al'umma,don haka ki ɗauki wannan bakomi ba,in dai cin amanace ban taɓa ganin wanda ya aikatashi yaci riba sai dai faɗuwa.Ki taimakeni ki sanya haƙury a cikin zuciyarki, ki roƙi Ubangiji ya cire Naseeru daga zuciyarki,ya musanya miki da mafi alkhairy,ina me baki yaƙinin cewa idan har kinyi hakan, Allah ba zai wofintar da ke ba Zainab, zai amsa miki buƙatar ki cikin rahamarsa da tausayinsa,su kuma ina musu addu'ar Allah basu sa'a,ya kuma yi miki kyakykyawan sakayya,yadda suka ɗakko hanyar cin amanarki da cin zarafinki, suma Allah ya kawo wanda zai ci nasu amanan."
Iyah ta kai ƙarshe tana ƙoƙarin maida hawayen tausayin TAIMIYYAH da suka cika idanunta,ganin TAIMIYYAH sai cigaban da kukanta take yi,yasa Iyah cigaba da cewa, "Don Allah kiyi haƙury Zainab, ki zuba ido ni da ke in dai da rayuwa to zamu ga yadda ƙarshen abun zai kasance,kisa a ranki idan Basmah ta auresa dama can mijinta ne haka Allah ya rubuta,amma kada ki sawa kanki damuwar da zai illata zuciyarki Zainabu,ki taimakeni ki taimaki maraicinki, ki sanya dangana cikin zuciyarki don girman Allah."
TAIMIYYAH dai har Iyah ta kai aya kuka take yi ahankali,tana jin dukkanin kalaman Iyan da suka shiga kunnuwarta suna sake karya zuciyarta.
'Tabbas tana cikin ruɗu da tashin hankali me tsanani,kamar yadda tsantsar mamakin Basmah ke sake lulluɓe zuciyarta,ta lumshe idanunta tana cigaba da sauraren nasihun Iyah da suka fara rage mata zafin da zuciyarta ke yi.
Tun hawayen na cigaba da xuba daga cikin idanunta,har suka tsaida kansu sai ajiyar zuciya kawai da take saukewa akai-akai,har kuma lokacin tana lafe a jikin Iyah ne, ta kaso koda motsawa.
Iyah ta cigaba da shafa kan TAIMIYYAH,tana jin tausayinta me tsanani sake kassara zuciyarta, ta shiga taɗin zuci tana cewa 'Ta sani da ciwo hakan a wajen ƴa mace, ka ga wata da abinda kai kake so,koda ace ƙaddara ta rabaku dole sai ka ji wannan kishin,bare TAIMIYYAH da duka-duka basu ma daɗe da rabuwa da Nass ɗinsa ba,sannan rana tsaka ta tsincesa da ƙanwarta a matsayin masoya,dole abin ba zai zo mata ta sauƙi ba,kuma ko rantsuwa tayi ba za ta yi kaffara ba har da haɗin kan uwarsu Zuwaira ,suka shirya hakan don cin amana da son lallai sai sun nunawa duniya cewa su shaiɗanu ne."
Iyah ta kai ƙarshen maganar zucinta lokacin da TAIMIYYAH ta tashi daga jikinta, tana miƙewa tsaye ta dafa ƙafarta,cikin sanyin murya irin na wanda yaci kuka ya ƙoshi,TAIMIYYAH ta dubi Iyah tana cewa, "Iyah zan shiga ciki kaina ciwo yake min ki kawo min magani in sha don Allah."
Daga haka ta fara takawa a hankali ta nufi hanyar ɗakinta,Iyah tabi bayanta da kallo hawaye na ciki idanunta,na tsananin tausayin TAIMIYYAH.
A cikin zuciyarta take cewa ' Allah ka kawo ma marainiyarka ɗauki,ka bata ikon cinye waɗannan jarabawoyi da suke kutsowa cikin rayuwarta,Allah kai mata sakayyah da alkhairy tare da miji nagari, wanda zai ƙaunaceta ya so ta a yadda take."
Ta kai ƙarshen maganar da tayi a zuci tana amsawa da "Ameen." A sarari kafin ta share hawayen da suka zubo mata, tana miƙewa don zuwa ta ɗakkowa TAIMIYYAH magani ta kai mata ɗaki.
_________
A can Sasan Baba Sani kuwa Basmah ce ta zauna tana zayyanewa Umma da Zuhurah komi daya faru,har kawo kan ganin da TAIMIYYAH tayi musu