Showing 96001 words to 99000 words out of 186776 words

Chapter 33 - TAIMIYAH Book Complete Document by Ayshat Dansabo Lemu .txt

15 Dec 2024

6603

a goben,ta dubi Yasmeen tana cewa, "Sorry Babyn Aliyu,da gaske hankalina yayi gida ne."


Yasmeen ta taɓe baki tana faɗin, "To ni bari na koma tunda naga kin ji sauƙi,ko kawai ki tashi ki shirya mu koma tare,ke kanki idan kika shiga cikin mutane za ki ji daɗi."


Babu musu ko TAIMIYYAH ta tashi, har abin ya so baiwa Yasmeen mamaki,amma sam bata kawo komi cikin zuciyarta ba illa bin TAIMIYYAH da kallo da tayi,lokacin data isa wajen kayanta tana ciro rigan da zata saka.
Wani haɗaɗɗen doguwar rigan Swiss Excelsior ta sanya,kalan maroon and milk da akaiwa touch da black kaɗan-kaɗan a jikin kwalliyar.Kalan yayi wa TAIMIYYAH kyau sosai kasancewarta fara,gashi ɗinkin ya zauna a jikinta wanda ya kasance yankan A-shape ne.
Ta nufi wajen mirrow tana ɗaukan powder ta murza kaɗan,sai tayi lining manyan idanunta da eye liner.Take fuskarta ya ɗauki wani irin kyau da ƙyalli don ma idanun nata sun ɗanyi ja sabida kukan data sha,amma duk da hakan tayi kyau ba kaɗan ba, musamman lokacin data kafa ɗaurin ture kaga tsiya,tai ɗan baya dashi kaɗan bai cokaro gaban goshi sosai yadda wasu ke yi ba.


Yasmeen data zuba mata ido ta buɗe baki tana faɗin, "Masha Allah,wannan irin kyau haka TAIMIYYAH gaskiya kullum ki dinga wa Allah godia wanda ya kyautata halittarki,Masha Allah! Masha Allah! Da wannan kyakykyawar halitta."


TAIMIYYAH ta ɗan harareta kaɗan tana faɗin, "Zaki fara ba,godia kam kullum cikinta muke Yasmeen,muje don Allah ni karki tasani kina faman yabon kyawu kaman baki taɓa ganin kyawawaba sai ni."


Yasmeen data miƙe tana ɗaukan mayafinta ta yafa,sai ta dubi TAIMIYYAH tana faɗin, "Ke dai kawai ayi shiru yanzu dai saka Ɗan-kunni mu wuce,hakan zai sake fito da kwalliyarki, ke baki son saka Ɗan-kunni."


TAIMIYYAH ta ɗauki wasu Ɗan-kunninta da ke saman mirrow ɗin ta sanya,aiko nan da nan kwalliyarta ya sake haskawa.
Ta ɗauki wayarta bayan ta yafa gyalen daya shiga da kayan jikinta,ta dubi Yasmeen tana cewa, "Muje Yasmeen kin tsaya sai kallona kike yi." Yasmeen ta saki murmushi tana yin gaba TAIMIYYAH ta biyo bayanta.


A falo sukai arba da Yah Emran zaune daga ɓangaren dining,ya sauya shiga daga farar shaddar ɗazu zuwa ƙananun kaya.
Kallo ɗaya TAIMIYYAH taiwa wajen da yake zaune, ƙirjinta ya buga da wani irin ɓacin rai,da sauri-sauri take dafa ƙafarta me laluran tana tafiya har ta fice daga falon,yanayin da suka kasance ciki a ɗazu na dawowa kwanyanta.


Emran da Yasmeen ta tsaya yi masa magana yabi bayan TAIMIYYAH da kallo,yana jin wani yanayi na sake taso masa,don wankanta ya cijesa matuƙa.Cikin zuciyansa yake faɗin 'Gaskiya Yarinyar akwai body da laushin jiki,ga kyau babu ƙarya kawai nakasanta shine illarta."


Maganan da Yasmeen tayi ne ya dawo dashi daga zancen-zucin daya tafi,tana cewa, "Yah Emran ina magana,nace zan samu 5k ɗin ne ko mu wuce kawai?"


Ya sauke manyan idanunsa akan Yasmeen ɗin yana cewa, "Bani da cash a jikina yanzu, amma zan miki transper ki turo min details ɗinki har dana Zaynab zan saka muku kuɗin." Daga haka ya maida idanunsa akan abincin da ya zuba bai sake duban Yasmeen dake masa godia ba.


Itama ganin hakan yasa ta fice ta cimma TAIMIYYAH a waje tana tsaye jingine da jikin gate tana jiran fiwowan Yasmeen ɗin.
Lokacin da Yasmeen ta ƙariso sai da TAIMIYYAH tayi mata mitan daɗewan da tayi bata fito ba.Yasmeen ta sanar da ita abinda ya tsaidata,sai kawai TAIMIYYAH ta taɓe baki bata kuma magana ba har suka samu abin hawa suka isa gidan bikin.


Basu dawo gida ba sai dare don tara da rabi ma ta wuce suka shigo gida.Tun a gidan bikin dama TAIMIYYAH ta sanar da Guggo maganan tafiyarta a goben.
Da Guggo Bilkin tace tayi haƙury har zuwa monday su dawo kai Kausar Amarya,wacce za a kai Katsina amma sai TAIMIYYAH tace wa Guggo Bilki ai har sun gama magana da Iyah, gobe da wuri Sani zai zo su wuce.


Tunda Guggo Bilki ta ji cewa Iyah za ta turo Sani tasan zance ya ƙare,hakan yasa ta amsawa TAIMIYYAH da cewa Allah ya kai su goben lafiya.


Yanzu da suka dawo daga gidan bikin sai kawai TAIMIYYAH ta hau haɗa kayanta.Yasmeen na taya ta tana mitan yadda TAIMIYYAN ta dage,sai ta tafi kaman wata wadda akai alluran tuburewa.


Ita dai TAIMIYYAH jin Yasmeen kawai take yi,don ba za ta iya sanar da ita irin halin ƙuncin da zuciyarta ke ciki, akan tozarcin da Yayansu yai mata a ɗazu bane,shiyasa kawai taja bakinta ta ɗinke.Suka cigaba da kammala shirya kayanta cikin akwati,Yasmeen ɗin ta fice daga ɗakin ta bar TAIMIYYAH na yin waya da Maryam Sanusi.


Washegary da wuri TAIMIYYAH ta tashi sukai sallama da Yah Anas da Ahmad kafin su fita wajen aiki.Kowannensu sai da ya bata kuɗi tai musu godi,mutumin nata Emran ne kawai basu haɗu ba.
Lokacin data je gaida Abbah shi ma kuɗin ya bata dubu goma yace ta sayi kayan kwalliya,ta amsa tai godia tana fitowa daga ɗakin Abban.


Ta sanyo kai don fitowa kenan Emran da zai shiga ɗakin na sanyo kai, saura kaɗan suyi karo TAIMIYYAH tayi saurin yin baya ta bashi hanya.Ya shige yana barin mata qamshinsa na turaren SAUVAGE DIOR.


Ta wuce cikin sauri tana jin daga ƙamshin har mamallakinsa ta tsanesu tsana me tarin yawa.Koda ta isa ɗaki lokacin Yasmeen ta fito wanka tana shafa ne,TAIMIYYAH ta zauna daga bakin gado tana zube kuɗin da ke hannunta.


Ta toilet direct itama ta yo wanka ta fito,cikin sauri ta gama shirinta tsaf cikin wasu riga da skat na atamfa.Suka fito tare da Yasmeen sukai breakfast TAIMIYYAH na ji cikin ranta duk ta ƙosa Sanin ya iso.


Ƙarfe tara da rabi Sani ya iso garin Kano.Bayan an kai masa abin karyawa ya ci ya huta, wajen 11 suka kamo hanya da TAIMIYYAH,bayan su Yasmeen da Guggo Bilki sun yo mata rakiya har bakin mota.
Yasmeen har da kukanta lokacin da TAIMIYYAH ke ɗaya mata hannu,itama kanta TAIMIYYAH sai data share hawaye.


Sun ɗakko hanya da Sani wanda ke tuƙinsa cikin salama da ƙwarewa.Idanun TAIMIYYAH suka sauka akan wajen ATM machines da ake cire kuɗi.
Tace wa Sani ya tsaya daga bakin hanya ta bashi ATM card ɗinta,ta gaya masa pin ɗin tace ya ciro mata duka dubu sha biyar ɗin da Yah Emran ya tura musu ita da Yasmeen a jiya.


Sani ya ciro kuɗin ya dawo suka kama hanya bayan ya baiwa TAIMIYYAH kuɗin da ATM card ɗinta.Sai ta sanar da shi cewa tana son ya kaita inda zata iya ganin nakasassu masu bara akan hanya,zata basu sadaka ne.


Sani ya kai ta inda yasan masu nakasa suna zama,kama daga gurugu har ma da makafi da kutare.
TAIMIYYAH ta rabar musu da duka kuɗin sannan suka kamo hanyar Zaria.Tana ji zuciyarta na rage zafi da raɗaɗin baƙin cikin da Yah Emran ɗin ya kimsawa zuciyartata,amma bata ji memory ɗin abinda ya yi matan zai goge daga kwanyarta har abada.


Ta kai bakin gyalenta ta ɗauke hawayen da suka ziraro mata..........✍🏻
















#Ɗansabo ce#
[12/14, 10:10 PM] +234 703 769 7050: *Littafin TAIMIYYAH paid book ne,ga duk wanda ta tsincesa a kowani irin group ne,kiji tsoran Allah karki karanta sai kin biya 500 naira only.*


*Za ku iya min magana ta wannan number ɗin 08167768704, ko kuma ku turo kuɗin ku kai tsaye ta wannan account ɗin*👇🏻
0504192664 aisha ibrahim dansabo GTbank.


*Sai ku tura shaidan biyanku ta wannan line ɗin 08167768704.*


Masu turo credit za ku turo katin MTN na 500 ta wannan line ɗin 08167768704.




_*Ina ƴan kasuwa masu buƙatar a tallata muku hajar ku? Maza ku garzayo da kuɗi ƙalilan a tallata muku kayan siyarwanku sai dai kawai ku ji ana kiran waya don buƙatan sayan kayan ku,ku tuntuɓeni ta layina kamar haka 08167768704.*_




*42*


*Zaria,Gonan Ganye.*


Motar Suhailah ce ta faka daga cikin parking space na gidan Hajjah.Ta fito sanye cikin lafaya me asalin kyau tsada ta yane jikinta daga sama har ƙasa,kai kace irin kanuri ɗinnanne dangin shuwa.


Kalar Lafayar wani irin Blue ne da akaiwa ado da kalan Red and Black haɗe Silver ajiki.Tayi kyau da shigan sosai hannunta riƙe da key ɗin motarta da hand bag ta nufi cikin gidan.
Da sallama ta isa cikin falon Lubah me aiki ta amsa sallamar tana ma Suhailah sannu da zuwa,Hajjah ta fito daga ɓangaren kitchen kenan tayi arba da Suhailah.
Sai ta saki murmushi tana faɗin, "Ashe ma gaki kin iso yanzu muka gama maganarki a waya da Antinku Raliya,tana gaya min kin biya kinyi mata sallama tun ɗazu."


Suhailah ta aje bag ɗinta saman kujera tana ƙoƙarin zama take cewa, "Wallahi Hajjah saloon na biya shiyasa,da tun ɗazu na iso nan ɗin,kuma na tadda har mutum biyu a wajen shiyasa na daɗe."


Hajjah da itama ta nema waje ta zauna ta jinjina kai tana faɗin, "Ai Maleek yace tafiyan ma ba gobe ba sai jibi,amma dai angama miki duk abubuwan buƙata har garin kunu dana ɗan-wake duk an gama,ni kaina har na gama shiri amma na sanar masa kwana ɗaya zanyi na gama ganin wuri sai a dawo dani,bazan iya wata guda a cikin yara ba kamar mara faɗi haka kawai ba haihuwa ba bakomi ba."


Suhailah sai ta zumɓure baki tana cewa, "Kai Hajjah don Allah karki ce haka,ni wallahi ji nake yi kamar kada na koma indai ba za ki yadda ki bimu kiyi wata a can ba,ki daure Hajjah please!"


Hajjah ta girgiza kai tana cewa, "Wallahi bada ni za a yi wannan haukan ba,sai dai ki fasa bin nasa wannan matsalarku ne ke da shi,au kinga na manta jiya ƙawarki ta zo nan gidan,take tambayata wai ko kun bar gari ne ta je gidanku yafi sau uku mai gadi na hana ta shiga,baki ga abin arziƙin data kawo min ba gashi can a ɗaki banma juye su daga ledan ba."


Suhailah taiwa Hajjah ƙuri zuciyarta na ɓaci da jin kalmar sunan Zuby da Hajjah ta faɗa,ta ja tsaki tana faɗin, " Hajjah ita Zubaidan ce tazo har gidan nan ɗi? Lallai ne wato tanan zata ɓullo sabida nayi blocking duk wata hanyar haɗuwata da ita,to wallahi tayi kuskure kamar yadda Maleek yasa ai mata iyaka da shiga gidansa,haka zai sa ai mata iyaka da xuwa nan ɗin ma, banza kawai maciyiya amana."


Yadda Suhailah take magana cike da ɓacin rai yasa Hajjah sakin baki tana kallonta har ta kai aya.Kafin ta buɗe baki tana duban Suhailan take cewa, "Lafiya me kuma yafaru tsakaninki da ita,yadda naga kina jida wannan Zubaidar,me tai maki nacin amana ni Hajjah?"


Suhailah nan take ta zayyanewa Hajjah duk yadda suka yi da Zuby,har kawo ɗaukan numbern Maleek data yi ta ba Zubyn,da irin saƙonnin iskancin da Zubyn ta dinga tura masa bata rage komi ba ta zayyanewa Hajjah,ta kai ƙarshen maganan da cewa, "Shine yanzu don an toshe kafan da zata dinga shiga min gida,ni kuma nayi blocking line ɗinta shine zata zagayo ta ɓangarenki sabida tana son cusa kai a wajen Maleek taci amanata."


Hajjah da tsananin mamaki da takaicin Suhailah ya rufeta,ta ballawa Suhailah harara tana cewa, "Ai bai birgeni ba Maleek ɗin da bai amsa tayin aurenta ya aureta ba,tunda ke kin maida kanki sakarya shashasha..!! Na rasa wani irin wauta kike dashi Suhailah,an gaya miki yanzu ana wani amintane yadda xamani ya lalace da cin amanan juna,hatta ɗan uwanka na jini baka tsira da ya ci amanarka ba indai akan abin duniya ne.To wallahi ki kuka da kanki tun wuri ki aje duk wani sakarci ki kama kanki da mijinki,me ma ya kaiki aminta da Bazawara kamarta da idanu a tsatstsaye na fitsara,to ai yanzu kinga ta fito miki da halinta dama ba sabida Allah ta shiga jikinki ba tana da manufa.To kurwanta kur akan ku daga ke har Maleek ɗin,Allah yai min tsari da haɗa zuri'a da irin su,tsaye kyam nake akanku ba dare ba rana,musamman Maleek da yake namiji sabida ina jiye masa ruɗin zamani da sharrin kuɗi,domin yanxu idon mutane da yawa na kansa maza da mata,shiyasa daga ance miki ƙarfe uku tayi na gama bacci kenan,ina kan sallaya ina miƙama Ubangiji kuka na akan ya tsaremin gaba da bayansa,ya karesa daga dukkanin sharrin zamani da ruɗinsa,duk wacce xai saukar dashi akan hanya Allah ya shiga tsakaninsa da su.Don haka ina da yaƙini Ubangiji yana jina kuma yana amsa buƙatuna,daga ke sai shi nake kallo a matsayin sanyin idanuna Allah yai muku tsari daga dukkan sharrin na mutum da aljan."


Suhailah ta amsa da cewa, "Ameen ya hayyu ya qayyum Hajjah,Allah yaja kwana ya barmu tare har abada,yadda kike tsaye akanmu Allah ya bamu ikon yi miki biyayya har abada."


Hajjah ta amsa da cewa, "Ameen." Sannan ta cigaba da yiwa Suhailah faɗa da Nasiha akan ta kula,ta kuma yi hattara da sharrin ƙawayen zamani,ta kama mijinta da kyau ta aje duk wani sakarci,maganan haihuwa kuma ta dage da addu'a sai ta ga Allah ya kawo mafita cikin sauƙi,idan ma har ƙaddara zai sa Maleek sake aure duk ta barwa Allah ikonsa,tayi addu'a Allah ba zai kawo wacce zata cutar da ita ba.


Suhailah dake sauraren Nasihar Hajjah da kunnuwan basira duk sai jikinta ya yi sanyi.Wani irin ƙaunar Hajjah da ba zai misaltuba na sake mamaye zuciyarta,ta sani Hajjah uwa ce ta gari a wajenta wacce bata da tamkarta har abada,kuma tayi mata dukkanin gata da ko uwarta na raye iyakan gatan da za ta yi mata kenan.
Hajjah ta cike mata gurabe da dama cikin rayuwarta ta zame mata uwa kuma uba duk a lokaci ɗaya.Sannan bata barta haka ba sai da ta ɗauki aurenta ta baiwa nagartaccen tilon ɗanta,wanda duk duniya ba za ta iya haɗa soyayyarsa da kowa ba.


Hawaye suka cika idanun Suhailah a lokacin da zuciyarta ya tuna baya,tun daga kan tashinta a hannun Hajjah tun tana ƴar shekaru biyar,har kawo kan aurenta da Maleek wanda akayi lokacin ba wani son ta yake a zuciyarsa ba.Ya dai amsheta ne sabida Hajjah da kuma soyayyar da ke tsakaninsa da mahaifiyarta da yake kira da Anty Hauwa.
Itace kaɗai ke masa wata irin azababbiyar soyayyah a lokacin, wanda hakan yasa Hajjah jajircewa har sai da Maleek ya amince da aurenta.Bayan anyi auren ne a hankali shi ma zuciyarsa ta kamu da ƙaunarta me ƙarfi.
Ta isa kusa da Hajjah tare da kifa kanta a jikinta tana faɗin, "Hajjah naji dukkanin nasihar ki kuma ina baki tabbacin zan gyara kusa-kurai na,Hajjah har abada ke ɗin ta dabance cikin zuciya da ruhina.Allah ya cigaba da bani ikon yin biyayya ga dukkanin umurninki har a zare numfashina daga gangar jikina."


Hajjah ta rungume Suhailah sosai a jikinta,tana shafa kanta take cewa, "Kar kiyi kuka Suhailah kome nai miki a rayuwa kaina da ƴar uwata nayi mawa,abinda kawai nake so dake a ko yaushe ki zama me haƙuri da yawan ibada,tare da riƙe sirrin mijinki komin rintsi kada ki bari aji kanku,ki kula da mu'amalarki da mutane sabida lalacewar zamani.So da yawa maƙiyanka sune na jikinka wanda kafi kusanci dasu,dariya ba ƙauna bace Suhailah kar ki ga wasu mutane na buɗe miki haƙora a waje ki ɗauka ƙaunace.Bance kar kiyi ƙawance ko hulɗa da mutanen arziƙi ba,amma ki kula kisan wa zaki dinga tarayyah da su,musamman a yanzu da zaki garin masu buɗewan ido sai fa kin dage kinyi kaman kina yi wajen sake janyo zuciyar mijinki,Allah yai muku albarka duniya da lahira."


Suhailah ta amsa da, "Ameen Hajjah,nagode Allah ya ƙara girma da tsawancin kwana me albarka Ameen."


Daga haka suka cigaba da hira da Hajjah gami da tattaunawa akan matsalolin rayuwa,da lalacewar zamani da irin yadda mutane suka ɗauki cin amana ba a bakin komi ba.Sosai Suhailah ke sake ɗaukan tarin ilimi a maganganun da Hajjah take yi,wanda rabi hannunka me sanda take sake yiwa Suhailah.Tana sake tsoratar da ita akan sauyawar zamani, cikin hikima ta yadda zata zabure ta zama irin macen da take mata fatan zama a wajen mijinta,sabida wautan Suhailah na son yin yawa ta gama lura tana da sakaci wajen kama miji a hannu,ita kuma ba kasafai take son ta dinga zaƙewa akan nunawa Suhailah ga yadda zata dinga yiwa Maleek ɗin ba,sabida kada watarana sharrin zuciya ya kimsawa Suhailah cewa tana matsa mata ne don kasancewan Maleek ɗin jininta tilo da kowa ya san tana son sa fiye da komi cikin rayuwarta.Shiyasa take kawaici da kauda kai a wasu tarin abubuwan da Suhailah ke sakaci dasu, tafi yin mata hannunka me sanda ko jirwaye cikin hikima.


Sai can yamma sosai Suhailah ta baro gidan Hajjah, bayan ta kammale duk abubuwan da zasu wuce dashi Abuja na anfanin yau da kullum.Sabida jibi da wuri zasu wuce har da Hajjah da zata je ganin inda zasu tare a Abujan,duk da cewa taƙi amincewa ta zauna dasu koda na wata guda ne a can ɗin,kafin ta dawo Zaria kamar yadda Maleek ya faɗi.


___________


Tunda TAIMIYYAH suka iso ta gama gaisawa da su Iyah,shikenan sai ta shige ɗakinta tai wanka tayi sallah ta kwanta bacci.


Bata tashi ba sai yanzu da agogo ke buga uku da kusan rabi.Ta nufi toilet tayi uzurinta tare da ɗauro alwalan sallan la'asar da aka kusa kira.
Koda ta fito sai data jira aka kira sallah tayi kafin ta fito falo don cin abinci,sabida da wata irin mahaukaciyar yinwa ta tashi,sabida bata tayi lunch ba ta kwanta bacci.


Tana tsaka da cin abincin Iyah ta fito daga ɗaki cikin shirin fita unguwa.Ta ƙariso wajen cin abincin nasu tana cewa TAIMIYYAH, "Zainabu zan ɗan je can tudun wada gaisuwan wani rashi da aka yi,jikan Babah Rabi ƙawata ne suka zo ganin gida ashe ajalin nasa na nan,zani musu gaisuwa in dawo in kin gama cin abincin sai ki tafi wajen Ummienki ta san cewa kin dawo."


TAIMIYYAH ta ɗaga manyan idanunta ta sauke akan Iyah tana cewa, "To Iyah adawo lafiya Allah yai masa gafara,dama yanzu nake so idan na gama in shiga can ɗin."


Daga haka Iyah tai tafiyarta ta bar TAIMIYYAH na ƙarisa cin abincinta,koda ta kammala wayarta kawai da Hijab ta ɗauka ta nufi sasan Ummie.
Da sallama ta shiga cikin sasan, idanunta suka fara sauka akan Inna Larai ,dake waje tana gyara kayan miya.
TAIMIYYAH ta gaisheta cike da ladabi,Innar ta amsa da fara'a tana ma TAIMIYYAH sannu da zuwa.


TAIMIYYAH ta wuce ta zuwa ciki tana doka sallama daga bakin ƙofar shiga falon gidan.Ummie da ke daga zaune cikin falon ta amsa sallamar da cewa, "Oyoyo Zaynab ashe yau ɗin dai zaki dawo."


TAIMIYYAH ta shiga da fara'a saman fuskarta take cewa, "Wallahi ni

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login