Showing 138001 words to 141000 words out of 186776 words
Chapter 47 - TAIMIYAH Book Complete Document by Ayshat Dansabo Lemu .txt
dake cikin tray ɗin da Babah Ladi ta kawo ta ke cewa, "Waɗannan kuɗin fa,waya aje su cikin nan?"
TAIMIYYAH ta kwaɓe fuska tare da watsa hannu baya ta ce, "Ina ganin shi ne ya aje su kafin ya tafi,don dama yace zai aje saƙo a baiwa Babah Ladi da ta kai masa lemu da ruwan."
Iyah sai ta jinjina kai tana kai hannu ta ɗakko kuɗin, ta miƙawa TAIMIYYAH tana cewa, "Irga mu ga yawansu ,sai ki kai ma Ladin Allah anfana, na ɗauka ke ya ajewa in ce meyasa zaki amsa kuɗinsa,amma tunda kyauta ce ya yi da sunan Ladi, sai a bata abarta Allah anfana ya yi albarka."
TAIMIYYAH dai bata ce komi ba,sai kuɗin ta amsa ta fara irgawa,ƙamshin AMOUAGE na dukan hancinta,tare da tsirga wani baƙon yanayi cikin zuciya,har ya zuwa gangar jikinta,tayi saurin kammala irga kuɗin, wanda suka kai naira dubu sha biyar.Ta miƙawa Iyah tana cewa, "Iyah 15k ne bari a ba ta ɗin."
Daga haka ta fita zuwa ɗakin Babah Ladi ta kai mata kuɗin,Babah Ladi tayi godia suna fitowa a tare da TAIMIYYAH, zuwa ɗakin Iyah don tayi godian kuɗin.Ita dai TAIMIYYAH ɗaki ta koma ta kwanta, zuciyarta na cigaba da tunanin Maleek, da yadda lallausar hannunsa ya tallabo fuskarta.
Ta ɗaga hannu ta shafi face ɗinta, tana ji har lokacin kamar hannunsa ne akan fuskar nata bai cire ba,tayi saurin lumshe idanunta wani baƙon yanayi na lulluɓe zuciyarta,kamar yadda sunansa ke amsa kuwwa cikin kunnuwanta.Ta buɗe baki a hankali cikin siririyar muryarta ta furta sunan a zahiri ' _Maleek Ibrahim Adoo...',_ ta ja ƙarshen sunan akan harshenta, tana jin wani abu na tsirgawa cikin kanta.
___________
A ɓangaren Maleek Ado kuwa,lokacin da suka isa gidan Hajjah, tun Shehu bai ida gama parking ba,Maleek ya ɓalle murfin motar ya fice.
Yana taku ne cikin sassarfa da zafin jini, har ya dangana kansa da falon Hajjan,ya yi sallama cikin muryarsa me cike da ginshiri,lokacin da yake sanya kansa cikin falon.
Hajjah da ke zaune tana duba littafin Hisnul Muslim,idanunta sanye cikin farin gilashi, ta ɗago ta dubi Maleek ɗin tare da amsa sallamar tasa.
Ya fara takowa zuwa cikin falon a gaggauce, har ya iso kusa da ita ya yi masauki a ƙasan carfet.Kansa ya ɗaura bisa guiwar ƙafarta ya sauke wani zazzafar ajiyar zuciya,yana ji sai yanzu ne zuciyarsa ta numfasa,tun bayan ido huɗu da suka yi da TAIMIYYAH.
Hajjah ta aje littafin da ke hannunta tare da zare gilashin idanunta,tana duban Maleek ta ce,
"Maleek lafiya ka ke ta faman sauke numfashi kamar wanda ya yi tsere,kun je ɗin ko wani wajen ka je daban ne?"
Hajjah ta jefa masa tambayar, tana me ɗago kansa daga guiwarta ƙafarta,inda Maleek ya kwantar da kansa a kai.
Hakan ya sanya shi zubawa Hajjah manyan idanunsa, kafin ya buɗe baki ya ce, "Can muka je Hajjah,na ganta,na ga gurguwarki Hajjah,sai dai tunda na yi ido huɗu da ita zuciyata bata huta ba,na shiga ruɗani da tsoro ba kaɗan ba Hajjah."
Yadda Maleek yake magana cike da sanyi, yasa Hajjah dafa kansa tana cewa, "Me ka gani a tattare da ita, da har ya jefaka a ruɗani irin haka Maleek,sanar dani meke faruwa ne wai?"
Maleek ya sake sauke numfashi, tare da furzar da zazzafan huci,kafin ya dubi Hajjah yana faɗin, "Hajjah ko kin san wannan Zaynabb ɗin itace na ke mafarki da me irin idanunta, wacce na taɓa baki labari watannin baya,har na ke sanar da ke ina yawan mafarki Yarinyar ne tana kuka,sai dai idanunta kawai ake nuna min, ban taɓa ganin zahirin fuskarta da kammaninta ba,sai dai manyan idanunta masu haske, da nake gani suna zubar da hawaye,a lokacin ina ɗauka cewa ko dai aljana ce ke bibiyata a cikin bacci,sai yau nayi ido biyu da irin waɗannan idanun da nake gani cikin baccina akan fuskar Zaynabb, hakan yasa na gane cewa itace na ke mafarki da ita Hajjah."
Maleek ya ƙarisa maganar yana duban yadda Hajjah ta tsura masa ido with shock,sai ya maida kansa ya kwantar a jikinta tamkar ƙaramin yaro.
Hajjah ta jinjina kai tana cewa, "Maleek da gaske ka ke yi ko dai kana tsokanata ne kawai?" Maleek da ke sauraran Hajjah bai ɗago kansa daga jikinta ba ya ce, "Hajjah ke ma kinsan ban iya ƙarya ba,duk abinda zan faɗi to hakan yake,sabida haka kika horeni,wallahi irin idanun da nake gani cikin mafarki,shi na gani akan fuskar wannan gurguwar Hajjah,kuma tunda na ɗaura idanuna akanta nake ji kamar ana uzura zuciyata da wani irin baƙon yanayi a kanta.Na jima ina ji ajikina cewa,akwai wata ƙaddara dake cikin yawan mafarkan dana dingayi watannin baya,sai dai ban tabbatar da hakan ba sai a yau, da na yi tozali da waɗannan idanun da siffar Yarinyar,ban san me ƙaddara za ta zana tsakanina da ita ba Hajjah."
Yayi maganar yana jin yadda zuciyarsa ke cigaba da dokawa akan TAIMIYYAH,shi karan kansa ba zai iya fassara yanayin da yake ciki,akan ganin TAIMIYYAH da yayi yau ɗaya ba.Yana jin lokacin da Hajjah ta kai hannunta tana shafa sumar kansa,amma ya kasa ko da motsi kamar yadda itama Hajjah ba ta ce komi ba,suka ɗauki tsawon lokaci a haka,kafin Hajjah ta fara da cewa, "Abdulmaleek idan har TAIMIYYAH ta kasance,ita ce ake nuna maka wani ɓangaren na siffarta a cikin baccinka,to tabbas akwai wani ɓoyayyen al'amari da Ubangiji ya barwa kansa sani,jikina yayi matuƙar yin sanyi da jin hakan, kamar yadda wani sashi na zuciyata ke farin ciki da jin hakan,ka duƙufa da addu'a sannan kuma mu yi istikhara, mu nemi zaɓin Allah akan wannan lamari,duk abinda Ubangiji ya hukunta sai mu amsa a matsayin zaɓinsa ba na mu ba."
Maleek ya ɗago kansa daga jikin Hajjah,yana me zuba mata manyan idanunsa,kafin ya jinjina kai yana cewa, "Hakane Hajjah,amma baki ji yadda nake ji a cikin zuciyata ba,ba kiji yadda ƙirjina ke bugawa da wani yanayi da baki ba zai iya miki bayani ba Hajjah,koma miye zai faru na rigama na sallama, ina kuma ji ajikina da wuya ƙaddaran aure bai haɗani da Zaynab ba,don yadda zuciyata ke doka mata ban taɓa jin irin hakan akan kowace mace ba,zan aure ta, zan kuma zauna da ita har ƙarshen numfashi na Hajjah."
Maleek ya yi maganar yana duban yadda wani irin abu ya haska a idanun Hajjah,kafin fuskarta ya washe da wani irin faffaɗan murmushi,wanda ya jima bai ga irinsa akan fuskar Hajjar ba.Ta cigaba da kallonsa da tsananin mamaki da murnan jin kalaman da suka fito daga bakinsa,ta kamo hannunsa ta riƙe tana cewa, "Maleek daga gani ɗaya da ka yi wa TAIMIYYAH har ka yanke cewa zaka iya aurenta,da gaske ka ke yi za ka iya aurenta ka zauna da ita a yadda take babu cutarwa? Bana so ka yi gaggawa har sai ka tabbatar da irin ƙaunar da kake mata a zuciyarka,bana so ka ji tausayin nakasanta ka ce za ka aureta don hakan,ina so ka aureta da zuciya ɗaya ne,kuma kana me jin so da ƙaunarta, ba wai don tana gurguwaba sai don ɗabi'u da kyawun tarbiyyyah da nagartarta.Don haka kamar yadda na faɗi ne ka je kayi istikhara ka nemi zaɓin Allah, duk abinda ka cigaba da ji akanta ka sanar dani,ni kuma na yi alqawarin nema maka aurenta da gaugawa,Allah shi kaɗai yasan abinda yake nufi da haɗuwata da wannan Yarinyar,don ina jinta a zuciyata fiye da yadda zan iya misalta maka Maleek."
Hajjah tayi maganar cike da nuna irin ƙarfin ƙaunar da take ji akan TAIMIYYAH,ta cigaba da cewa, "Ina fata baka sanar da ita wanda ya tura ka xuwa gareta ba,don bana so su san cewa kai ɗana ne,har sai ka ji da gaske kana ƙaunarta, za ka kuma iya zama da ita tsakaninka da Mahaliccin sammai da ƙassai,sannan idan har Zaynab ba ta aminta da kai ba, to zamu haƙura da ƙudirinmu don ba zan so ai mata dole ba."
Kalaman Hajjah na ƙarshe ne suka girgiza zuciyar Maleek Ado,har yayi saurin ɗagowa ya dubi Hajjah, da wani yanayi akan fuskarsa ya ce, "A'a Hajjah ki daina faɗin hakan don Allah,ban fara jin irin wannan yanayin da nake ji akanta don in daina ba,tun kafin na yi tozali da ita a zahiri in ga irin idanun da nake gani a cikin baccina,na ke shiga wani yanayi kafin in koma da walwalata,a yau dana gansu a zahiri saman kyakykyawar wannan halittar, ba na ji zan sake samun sukunin zuciya da cikakkiyar nutsuwa,ba tare da na mallaketa gaba ɗayanta ta dawo a ƙarƙashin ikona ba,don haka don Allah ki daina fatan ba za ta so tilon ɗanki ba please!"
Yadda Maleek ya ƙare maganar cike da magiya,abin har al'ajabi ya bai wa Hajjah.Ta jinjina kai tana sake sallamawa ƙudiran Ubangiji,don bata taɓa tunanin ganin irin abinda take gani a yanzu akan fuskar Maleek ba.
Hajjah ta dafa kansa tana faɗin, "Shikenan Maleek ka kwantar da hankalinka, In sha Allah alkhairi zai biyo bayan wannan lamarin."
Maleek sai ya tashi daga ƙasan carfet,ya nufi kan doguwar kujeran Hajjah ya zauna,yana me zamewa kaɗan bayansa ya ginjina da jikin kujeran sosai,sannan ya lumshe idanunsa.
Hajjah ta nufi ɓangaren dining,inda aka aje wani ƙaramin fridge,ta ciro goran ruwa me matsakaicin sanyi,ta nufo wajen da Maleek ke zaune idanunsa a lumshe.Ta ɓalle murfin goran ruwan tana miƙa masa ta ke cewa, "Maleek karɓi ka sha ruwan sanyi,ko ka dawo cikin nutsuwarka sosai."
Maleek sai ya buɗe idanunsa yana kallon goran ruwan da Hajjah ke miƙo masa,kafin ya kai hannu ya amsa goran yana cewa, "Thank u Hajjah." Daga haka ya kai goran ruwan kan bakinsa,ya fara sha sanyin ruwan na ratsa maƙoshinsa,ya sha fiye da rabin ruwan sannan ya aje goran daga ƙasa yana sauke numfashi.
Ya dubi direction ɗin da Hajjah ke zaune ta tsura masa ido,ya jefeta da murmushi me sanyi.Hajjah ta maida masa da martanin murmushin,sannan ta yi magana cike da tsokana ta ce, "Maleek ashe dai karon ka da gurguwar Hajjah me zafi ne,tunda gashi haɗuwa ɗaya duk ka fita hayyacinka,da kai ka ɗauka aljanace kake gani da idanun bil'adama a cikin baccin naka?"
Maleek ya jinjina kai yana cewa, "Seriously Hajjah ba za ki gane me nake ji akan wannan yarinyar ba yanzu, ki taimaka ki bani numbarta zan yi magana da ita zuwa anjima."
Hajjah ta saki murmushi me faɗi,kafin ta tashi ta ɗakko wayarta ta miƙawa Maleek.Ya amsa yana dubanta da fuskar shagwaɓa yace, "Hajjah to wani suna ki kai saving numbar da shi?"
Hajjah ta aika masa harara tana cewa, "TAIMIYYAH." Daga haka ta koma ta zauna murmushi na blushing saman fuskarta.Maleek ya shiga contact ɗin wayar Hajjah, ya lalubo sunan TAIMIYYAH,yana lode lambobin cikin wayarsa wani irin yanayi na kewaye zuciyarsa.
Ya tashi ya isa inda Hajjah ke zaune, ya aje mata wayar a kusa da ita ya ce, "Hajjah Allah ƙara girma zan fita yanzu,amma zuwa anjima zan dawo kafin in wuce GRA,ina fata zuwa lokacin an yi min soup ɗin dana ce."
Daga haka sukai sallama da Hajjah,ya taka yana barin cikin falon,gabaki ɗaya yana ji tamkar ana ingiza zuciyarsa,akan son sake ganin waɗannan idanun a saman fuskar TAIMIYYAH.
Da ƙyar ya iya controllling zuciyarsa, har ta iya haƙura da kiran TAIMIYYAH vid call,ya haƙura sai zuwa dare idan ya koma can gidansa,ya nutsuwa akan gadon baccinsa sannan sai ya kira ta.
Ya karya kan motarsa da ya ɗauka a gidan Hajjah, ya kamo hanyar shiga cikin City,don zuwa wajen wani old friend ɗinsa da ke Unguwar Alƙali cikin Zaria City........✍🏻
#Ɗansabo ce#
[12/14, 10:12 PM] +234 703 769 7050: Littafin TAIMIYYAH paid book ne,ga duk wanda ta tsincesa a kowani irin group ne,kiji tsoran Allah karki karanta sai kin biya 500 naira only.
Za ku iya min magana ta wannan number ɗin 08167768704, ko kuma ku turo kuɗin ku kai tsaye ta wannan account ɗin 0504192664 aisha ibrahim dansabo GTbank.*
*Sai ku tura shaidan biyanku ta wannan line ɗin 08167768704.*
Masu turo credit za ku turo katin MTN na 500 ta wannan line ɗin 08167768704.
_Ina ƴan kasuwa masu buƙatar a tallata muku hajar ku? Maza ku garzayo da kuɗi ƙalilan a tallata muku kayan siyarwanku sai dai kawai ku ji ana kiran waya don buƙatan sayan kayan ku,ku tuntuɓeni ta layina kamar haka 08167768704._
*57*
Basmah da qawayenta,Amna da Sharifa ne zaune cikin ɗakin baccin su Basman.Sharifa ta dubi Basmah tana cewa, "Besty ni fa wallahi na yi matuƙar mamakin jin cewa, wai an sanya miki ranar aure kamar daga sama,shi ko wannan wani guy ne ya zo da zafinsa haka,a ina kuka haɗu?"
Basmah ta saki ƙayataccen murmushi tana duban cikin idanun Sharifa ta ce, "Ke dai bari kawai ƙawata,da zafinsa ya zo kam amma maganan long story ne,bari in baku labarin yadda muka haɗu...."
Basmah ta zayyane ma su Sharifa labarin tun farkon ganinta da Nass tare da TAIMIYYAH,har kawo yau da ake zancen aurensu,nan da watanni uku masu zuwa.Ta kare maganan tana cewa, "Friends wallahi ni kaina ganin abin na ke kamar a dream da,amma tunda Umma ta je Yobe ta kai sunansa wajen oga teacher,shikenan komi ya tafi yadda muke so,kar ku so ku ga yadda Nass ke nuna min so a yanzu,kamar dama can ni zuciyarsa ta fara so ba wata gurguwaba."
Ta kai ƙarshen maganar tana kwashewa da dariya, su Amna na taya ta.Kafin su tsaida dariyan Sharifa na faɗin, "Ke bamu mu ga pics ɗinsa inga kalarsa ,da har kika iya rufe ido ki kai wa ƴar uwarki ta jini ƙwacensa,gaskiya Basmah ba ku da kyau. Ni har tausayin baiwar Allah ya kamani,da ace uwarsa bata raba alaƙar dake tsakaninsu ba, ahakan zaku farraqa tsakaninsu ki auresa babu tsoran Allah?"
Sharifa ta ƙare maganar da tambayar Basmah, tana tsare ta da ido.Basmah tayi saurin haɗe fuska tana dannawa Sharifa harara ta ce, "Eh...! Lallai Sharifa Salis, yaushe kika fara wa'azi bani da labari? Ke idan ana maganar wanɗanda suka san kan snatching har kya yi motsi ma,kar ki ɓata min rai please! Bari dai in nuna miki kalar haɗuwarsa,sannan sai ki san cewa ko ke ce, za ki iya yin komi don ya zama mallakinki."
Basmah tayi maganar tana danno pic ɗin Nass,wanda ya yi azabar kyau.Ya ɗauki pic ɗin ne sanye da ƙananun kaya,a wani haɗaɗɗen wajen cin abinci a garin Abuja.Ta miƙawa Sharifa wayar tana cewa, "Amshi ki gani ƙawata."
Sharifa ta miƙa hannu ta amsa wayar Basmah,tana ɗaura idanunta akan screen ɗin wayar,idanunta suka sauka akan kyakykyawar fuskar Nass Aliyu.Take ta ji wani dumm..! Cikin kanta,ta sake tsurawa hoton idanu tana sake hango tsantsar kyawunsa da haɗuwarsa,tabbas bata ga laifin Basmah da ta ruɗe akansa, har suka shiga suka fita za ta mallakesa ya zama nata ba.
Ta ɗauke idanunta daga duban hoton, ta mayar kan Basmah dake ta faman blushing,idanunta akan Sharifan. Sharifa ta miƙawa Amna wayar tana cewa, "Ungo Amna ki gani,gaskiya guy ɗin ya haɗu ba karya wallahi."
Amna ta amsa wayar ta kalli pic ɗin per seconds,sannan ta miƙawa Basmah wayarta tana cewa, "Gaskiya ya haɗu ba karya Basmah,banga laifinki ba don ko ni na samu dama zan iya yin wuff da shi."
Basmah ta warce wayarta daga hannun Amna, ta tsuke face ta ce, "Ban son iskanci ƙawata, a gabana ki ke faɗin hakan?"
Sharifa ta amshe da faɗin, "To miye aciki ke ma ai ƙwacensa ki ka yi ƙawata,bare ma wasa Amna take yi miki,Allah ya sanya alkhairy ya kaimu lokaci,mu ci uwar sabada a ranar."
Suka sheƙe da dariyar shaƙiyanci,Basmah na cigaba da basu labarin yadda tsare-tsaren bikin zai kasance.Sai can yamma shaƙiƙan ƙawayen Basmah na tun secondary skull,wato Sharifa Salis da Amna Muktar suka bar gidansu Basmahn,bayan ta yo musu rakiya har bakin gate.
__________
TAIMIYYAH da tunda ta shige ɗaki bayan tafiyar Maleek Ado,ba ta fito ba sai bayan sallan isha'i.Direct kuma wajen cin abinci ta nufa don yin dinner,ta zauna bada jimawa ba Iyah ta iso wajen,tana ɗaura idanunta akan TAIMIYYAH ta ke cewa, "Au ashe kin fito,da yanzu ai nake shirin zuwa ɗakin naki inga ko lafiya,daga tafiyan mutum sai ki ƙule a ɗaki kina faman tunane-tunane,to ni dai babu ruwana bana son kina sanyawa kanki damuwa akan abinda bai kai ya kawo ba.Ki yi addu'a a duk abinda kika ga ya shigo cikin rayuwarki,Allah baya taɓa jarabtar bawa sai akan abinda zai iya ɗauka,don haka ki dinga sanyawa kanki salama don Allah Zainabu."
TAIMIYYAH ta ɗaga kai ta dubi Iyah da manyan idanunta kafin ta ce, "Hakane Iyah nima ba tunani nake yi ba,kawai na ɗanyi karatu ne sai na tsaya duba wasu littafai,ganin lokacin sallah yayi yasa na tsaya na gabatar da sallar magriba, na jira akai isha'i sannan na fito cin abinci."
Iyah ta zauna tana faɗin, "To da dai yafi miki Zainabu kar kiji tsoran komi, In sha Allah koma waye alkhairy ne ya kawo sa ba sharri ba."
Daga haka suka zuzzuba abincin suka fara ci,suna hira kaɗan-kaɗan har suka kammala cin abincin.TAIMIYYAH ta koma daga cikin falon Iyah ta zauna,tana ɗaukar remote ta sauya tasha zuwa Bollywood.So take yi ta hana zuciyarta yawan tunanin mutumin ɗazu,ta ƙura ido akan TVn ba don tana da tabbacin zata fahimci komi ba.Ta rasa meyasa tunaninsa yaƙi fita daga zuciyarta,ya yi mata tsaye a rai, da ta rufe ido hannuwansa take ji a fuskarta,ta yi saurin sake manna idanunta akan screen ɗin TV, tana kallon fuskar fararen fatar dake gilmawa a ciki,ba tare da ta san kan film ɗin ba, bare ta fara fahimtan ina aka dosa ma.
Ƙaran shigowar saƙo cikin wayarta,yasa ta ɗaga ido ta kalli agogon dake manne jikin bango,inda ya nuna ƙarfe 8:49pm (Takwas da mintuna arba'in da tara na dare).
Sai ta maido dubanta kan wayarta,tana me kai hannu ta yi swiping screen lock ɗin wayar.Idanunta ya sauka akan baƙin lambobin da aka turo saƙon,sai ta samu kanta da buɗe saƙon don ganin daga waye?
_"Salam Zaynabbb! Hope u are fine,please zan kira vid call in the next some minutes,ki yi picking call ɗin please!_ "
Waɗannan sune kalaman dake rubuce cikin saƙon.TAIMIYYAH ta karanta saƙon a ƙallah kusan sau uku, amma brain ɗinta bai kawo koda wasa cewa daga Maleek bane,don ta san har suka rabu bata bashi numbarta ba, 'To ko dai Yah Emran ne?', Tunaninta ya haska mata hakan, tana jin wani abu na taɓa ranta.Sai dai kafin ta sake wani dogon tunani, kira ta vid call ɗin ya shigo wayarta,ta tsurawa wayar ido tana ji haka kawai zuciyarta