Showing 93001 words to 96000 words out of 186776 words
Chapter 32 - TAIMIYAH Book Complete Document by Ayshat Dansabo Lemu .txt
yana sake jinjina baiwar kyawu da Allah yayi wa TAIMIYYAN.
amma
Sai dai kasancewarta gurguwa yasa yake jin bazai taɓa iya bata zuciyarsa ba.Wani tunani ne ya haska cikin kwanyarsa sai ya juya da sassarfa don fita daga gidan, jin za a tada sallah a masallacin dake kusa dasu inda suke sallah anan.
TAIMIYYAH dai bata san ma yana yi ba,don ita haushin kallonta da ya tsaya yine ma ya kamata.Ta dinga mita a zuciyarta ita kaɗai akan me zaisa ya tasata da kallo haka kaman wani ɗan iska.
A fili ta furta, "Mutum sai shegen girman kai da baƙin hali,ga shegen kallon matan tsiya kaman maye."
Ƙasa-ƙasa tai maganan iya kunnuwanta,shiyasa Yasmeen da ke gefe tana cire Abayar jikinta sam bata ji me TAIMIYYAN ta faɗi ba.
Yau ɗinma da lokacin yin Dinner yayi TAIMIYYAH ƙin fita tayi.Sai ta fake da cewa Yasmeen zata ɗan yi tilawa ne sai zuwa can anjima zata ci abincin.
Hakanan Yasmeen ta fita ta bar TAIMIYYAN a ɗaki wacce ta ɗakko Qur'ani ta fara karantawa.Bata bar karatun ba har sai da Yasmeen ta shigo hannunta riƙe da ledan gasasshen nama ta ajewa TAIMIYYAH tana cewa, "Gashinan inji Yah Anas kuma Guggo Bilki tace kiyi maza ki bar karatun haka ki fito kici abinci,don ta kula da gangar kike ƙin fita falo yanzu."
TAIMIYYAH sai ta aje Qur'anin tana duban Yasmeen take faɗin, "To sarkin karaɗi ai dama yanzu zan fita ɗin don na fara jin yinwa,ɗakko naman muje dashi can ɗin sai muci kilama shi kawai zan ci in sha madara ya wadaceni."
Yasmeen ta saki dariya tana cewa,"Ai nan kika fi kauri dama, kwaɗayi da son cin nama kamar wata kura,duk Iyah ce ta sangartaki haka wallahi,yarinya sai shagwaɓa kamar wata babyn goye."
TAIMIYYAH ta juya ta bankawa Yasmeen harara tana faɗin, "Na dai ji wani ma ya koyi shagwaɓar idan zai iya mana." Daga haka suka jera da juna zuwa falon.Sun samu babu kowa su Yah Anas ɗin sun kama gabansu zuwa part ɗinsu.
Guggo Bilki kuma da alamu tana ɓangaren Abbah,sai kawai su TAIMIYYAH suka baje naman suna ci a tsakiyar falon saman carfet.
Yasmeen ce ta ɗakko musu kwalin Hollandia milk cikin fridge ta haɗo da cup suka zuba madaran suna korawa da shi,suna cin gasasshen naman da yaji kayan haɗi sai qamshi kawai ke tashi.
Koda suka kammala TAIMIYYAH ta riga Yasmeen isa ɗaki don kwanciya bacci,ita Yasmeen ta tsaya kallo sai wajen 11:30pm ta shigo lokacin tuni TAIMIYYAH ta jima da yin bacci.
Washegari ya kama ɗaurin aure da yini baki ɗaya.Duk iya yadda Guggo Bilki ta matsama TAIMIYYAH akan ta tashi ta shirya su fita zuwa gidan bikin tare amma ta ƙi,dama ita Yasmeen tun safe ta bar gidan bayan ta tashi TAIMIYTAH su wuce tare taƙi tashi.
Hakanan Guggo Bilki ta fice zuwa gidan bikin ita kaɗai.Sai ta bar TAIMIYYAH da masu aiki dake can baya suna hidimansu.
Ita kam TAIMIYYAH ko ajikinta ta gwammaci tayi zamanta ita ɗaya, data je gidan biki ta shiga taron jama'a daga me cewa Allah sarki dubi gurguwa sai masu yaba kyawunta.
Ko wanka bata tashi yi ba sai wajen 12 na rana.Gidan yai tsit babu kowa don har mazan duk suna wajen reception tunda ɗaurin auren sha ɗaya na safe ne,shiyasa babu motsin kowa sai su Ramma masu aiki kuma duk suna ta can baya.
Lokacin da TAIMIYYAH ta fito wanka tana ɗaure ne da towel da tsayinsa ya zarce guiwanta.Ta nufi wajen madubi tana jan stool ta zauna don fara shafa mai.
Tana tsaka da shafa man aka turo ƙofar ɗakin aka shigo.Sam ita bata damu ba ta cigaba da shafanta tana cewa, "Yasmeen kin dawo ɗaukan wani abu hal....."
Maganan ta ya katse ne a lokacin da idanunta suka bango mata wanda ke tsaye daga bakin ƙofa ta cikin mirrow.
Yah Emran ne ta hango tsaye ya zubo mata manyan idanunsa yana kallonta babu ko ƙiftawa.
TAIMIYYAH take ta ji wani matsanancin faɗuwar gaba da takaicin yadda ya risketa babu kaya ajikinta.Ta rintse idanunta tana rasa ma me zata yi,ita dai ba zata iya tashi a haka ta nufi wajen da Hijaban sallansu yake ba.Sai ta gwammace ta cigaba da zama a hakan tunda a zaune take da a ce ta tashi neman abun rufa ya ganta daga ita sai towel.
Ta buɗe idanunta a lokacin da ya gama sanyo kansa cikin ɗakin tare da maida ƙofan ya rufe.Ya murza key yana zaresa daga jikin ƙofar ya cilla a aljihun dakakkiyar farar shaddar gezner dake jikinsa.
Ganin hakan yasa TAIMIYYAH dubansa a firgice tana faɗin, "Lafiya Yah Emran zaka shigo ɗaki babu neman izini,baka ga a halin daka sameni bane? Please ka fita ka bani waje zan shirya tunda kai ba muharramina bane."
Yadda TAIMIYYAH take magana cike da zallar ɓacin rai,jikinta har wani rawa yake na tsananin tsoro yasa Emran sakin wani makirin murmushi.
Idanunsa na cigaba da bin jikinta da wani mayen kallo.A hankali ya fara takowa zuwa inda take zaune ba tare da ya bi umurninta na fita daga ɗakin ya bata waje ba.Ganin yana tahowa wajenta ne ya sake jefa zuciyar TAIMIYYAH cikin matsanancin fargaba da tsoro.Ta kai hannuwanta duka biyu tana sarƙesu a ƙirjinta tare da maida idanunta ta rintse,tana nanata kalmar Innalillahi daga farkonsa har ƙarshe.........✍🏻
#Ɗansabo ce#
[12/14, 10:10 PM] +234 703 769 7050: *Littafin TAIMIYYAH paid book ne,ga duk wanda ta tsincesa a kowani irin group ne,kiji tsoran Allah karki karanta sai kin biya 500 naira only.*
*Za ku iya min magana ta wannan number ɗin 08167768704, ko kuma ku turo kuɗin ku kai tsaye ta wannan account ɗin*👇🏻
0504192664 aisha ibrahim dansabo GTbank.
*Sai ku tura shaidan biyanku ta wannan line ɗin 08167768704.*
Masu turo credit za ku turo katin MTN na 500 ta wannan line ɗin 08167768704.
_*Ina ƴan kasuwa masu buƙatar a tallata muku hajar ku? Maza ku garzayo da kuɗi ƙalilan a tallata muku kayan siyarwanku sai dai kawai ku ji ana kiran waya don buƙatan sayan kayan ku,ku tuntuɓeni ta layina kamar haka 08167768704.*_
*41*
Emran ya cigaba da takawa zuwa wajen da TAIMIYYAH ke zaune idanunsa akanta,ya tsaya daga bayanta yana kai hannuwansa duka ya dafa kafaɗunta.
Jikin TAIMIYYAH ba inda baya rawa lokacin da ta ji saukan hannuwansa a kafaɗunta.
Tayi saurin buɗe ido tana kallonsa ta jikin mirrow ɗin, jikinta na rawa hawaye na fara wanke fuskarta. Emran shi kuma ya juyo da ita gaba ɗaya suna fuskantar juna.TAIMIYYAH ta ware idanunta tana magana cikin rawar murya tace, "Yah Emran please miye hakan kake yi,don girman Allah ka fita ka bani waje,baka ga babu kaya a jikina bane daga ni sai towel,ko kai bakasan haramcin yin hakan bane?"
Yadda take magana cikin nuna zallan fusata yasa Emran kai hannu ya bige bakinta da ƙarfi.TAIMIYYAH ta saki kuka tana ture hannunsa daga jikinta,ta yinƙura don ɗakko Hijab ko wani abu ta suturta jikinta da shi,sai dai tana ƙoƙarin tashi daga kan stool ɗin Emran ya kai hannu ya ɗagota gaba ɗayanta zuwa jikinsa.
Kafin tayi wani yinƙuri ya kai bakinsa bisa kunninta yana faɗin, "Ashe baki da kunya ni kike wa tsawa haka? To bari in tabbatar miki da cewa bani da ilimin sanin haramcin."
Yadda yayi maganan yana ƙoƙarin kai ɗaya hannunsa kan towel ɗin dake ɗaure a ƙirjinta yasa TAIMIYYAH buɗe baki zata saki ihu...Kamar yasan shirinta kawai sai ya kai bakinsa ya rufe bakinta ruf!
Take bugun numfashin TAIMIYYAH ya tsaya cak! Jikinta ya ɗauki wani irin rawa.Hakan yasa Emram ɗagata gaba ɗayanta ya kai kan gado,har lokacin bakinsa na manne da nata, ƙamshinsa na turaren SAUVAGE DIOR gaba ɗaya ya gama buɗe hancin TAIMIYYAH.
Ta kai hannu ta fara dukan ƙirjinsa da yai mata rumfa da iyakan ƙarfinta,amma Emran bai yi ko gezau ba har sai da yayi nasaran tura harshensa cikin bakinta,cikin sa a TAIMIYYAH ta samu ta gantsara masa cizon daya sa shi sakinta babu shiri.
Tayi wani irin hantsalawa gefe guda tana damƙo zanin gadon dake shinfiɗe ta rufe jikinta,wani matsanancin kuka na ƙwace mata har lokacin jikinta rawa yake kaman mazari.
Emran da yai tsaye yana bin ta da kallo, zafin cizon da taiwa harshensa na ratsa shi,sai ya saki ƙwafa yana binta kan gadon baki ɗaya ,ya damƙota ita da zanen gadon data cimimiye jikinta da shi.
Ya fara ƙoƙarin zaro ta daga cikin zanin gadon yana cewa, "Allah yau tunda kika cijeni sai na nuna miki cewa ni ɗin ba kanwar lasa bane."
Cikin kuka TAIMIYYAH ke masa magiyan yayi haƙuri ya barta amma ina...! Sam bai saurareta ba sai da yayi nasaran rabata da zanin gadon da ya zama sutura a gareta.
Ganin towel ɗin dake ɗaure a jikinta na son kwancewa, yasa TAIMIYYAH kai hannu ta damƙesa tana sakin kuka me sauti,dukkanin jikinta na sake ɗaukan rawa, zuciyarta tamkar ta fashe sabida baƙin cikin wannan tozarci da Yah Emran ke shirin aikata mata.
Hannunsa ya kai yana kamo siririn ƙafarta mara lafiyan ya riƙe a hannunsa, yana kallon yadda zanen jan Lallin da akai mata ya zauna a farar ƙafartata.Ya cigaba da bin ko'ina na jikinta da kallo sha'awanta na sake fisgar zuciyarsa,musamman da yaji yadda jikinta ke da wani irin laushi.
Cikin disasshiyar murya yake faɗin, "Zaynab kina da kyau da diri daya kamata ace na mallakeki,sabida kin mallaki duk abinda nake so a jikin mace,cikas ɗaya ne zai hanani amincewa da ƙudirin Mamie wannan laluran ƙafar daya mayar dake gurguwa.Ba don hakan ba da gudu zan amince na aureki ko don in more albarkatun jikinnan naki da kyau,amma ko a yanzu bazan iya barinki ban ɗanɗana koda kaɗan bane naji yadda daɗinki yake ko Babe?"
Yana maganan ne duka hannunsa na yawo a jikin TAIMIYYAH,wacce ke faman rasgar kuka jikinta na cigaba da ɗaukan rawa ,kaman wacce zazzaɓi ke shirin kamawa.
Kalaman Emran suka haɗu da tsananin ƙunan da zuciyarta ke yi suna neman tsaida gudun numfashinta.
Ta saki wani gigitaccen ihu a lokacin da taji ya fisge towel ɗin jikinta yayi jifa da shi.
Emran ya kai hannu ya danne bakinta yana ƙoƙarin haɗata da jikinsa ,amma hannun da TAIMIYYAH tasa ta kai mishi wani nushi a ciki yasa shi sakinta babu shiri,yana me ɗauketa da wani gigitaccen mari da hannu ɗaya.Wanda ko kaɗan TAIMIYYAH bata ji zafin marin ba, ta yinƙura tai wani irin tsalle sai gata a bakin toilet.
Jikinta na wani irin kakkarwa ta buɗe ƙofan ta shige tana murza key.Dai-dai lokacin da Emran da ke dafe da cikinsa ya ƙariso wajen yana cizon yatsa.
Har lokacin hannunsa ɗaya dafe yake da cikinsa,don bada wasa naushin ya shigesa ba,wanda ya haifar masa da ɗaurewar mararsa a lokaci ɗaya.
Yana jiyo kukan da TAIMIYYAH ta saki daga cikin toilet ɗin,ya juya yana takawa a hankali ya isa bakin ƙofa.
Da hannu ɗaya ya yi anfani wajen ciro key ɗin dake aljihunsa ya buɗe ɗakin ya fice.Zuciyarsa na cike da ɓacin rai da jin zafin yadda bai samu nasara akan TAIMIYYAN ba.
Yaso koda kaɗan ne ya murji jikinta koya rage zafi koda ace bai shigeta ba,sai gashi ta shammacesa da wannan nushin ta kufce masa.
Ya cije lips ɗinsa yana girgiza kai cike da takaici,har ya fice daga falon hannunsa ɗaya na riƙe da cikinsa, ya nufi ƙofan fita daga sashin baki ɗaya zuwa nasu part ɗin.
TAIMIYYAH dake cikin bayi tana rasgar kuka tana jin lokacin daya fice daga ɗakin.Hakan yasa ta fitowa da hanzari ta nufi ƙofar ɗakin ta kulle tana me barin key ɗin a jikin ƙofar.
Kuka take yi sosai jikinta kuma bai daina ɓari ba,ta faɗa kan gadon Yasmeen tana sake rushewa da wani sabon kukan.Bata taɓa tunanin Yah Emran ɗin tantitin ɗan iska bane sai yau da yake ƙoƙarin tazartata,duk don kasancewarta gurguwa da yake ganin zai iya cin banza akanta.
Hankalinta taji ya yi mummunan tashi, gaba ɗaya sai taji hankalinta ya koma gida,zaman Kanon ya isheta hakanan,ba kuma taji zata iya wuce gobe bata ganta a gaban Iyah ba.
Ta share fiye da mintuna talatin tana rasgar kuka kaman ranta zai fita.
Da ƙyar ta iya tashi tana layi dafe da ƙafarta me laluran ta nufi toilet tana me sakarwa kanta shower,ruwa me sanyi na ratsa tsakiyan kanta yana gangara a jikinta.
Ta jima a durkushe ruwan na jiƙe dukkanin jikinta,kafin ta ɗauro wani towel ɗin ta fito daga bayin,jikinta na ɗaukan wani sabon rawar kamun zazzaɓi.
Ta isa wajen kayanta ta zaro wata riga mara nauyi ta saka, ko bra da pant bata tsaya sakawa ba ta naɗe akan gado tana sake ɓallewa da kuka.
Nan da nan jikinta ya ɗauki matsananci zafi kanta na wani irin ciwo.Ta janyo wayarta da ƙyar tana kiran layin Yameen,bugu biyu Yasmeen ta ɗauka.
Da ƙyar TAIMIYYAH ta iya ce mata, "Yasmeen don Allah ki dawo gida banda lafiya." Daga haka tayi jifa da wayar ba tare da ta tsaya kashewa ba,sai Yasmeen ce tayi hanging up daga ɓangarenta.
Ta dubi ƙawayensu da suka cika ɗakin da suke zaune ta miƙe tana cewa, "Friends ku bani awa ɗaya zan je gida na dawo TAIMIYYAH ce bata jin daɗi Firdausy."
Yasmeen ta kai ƙarshen maganan tana duban Feedoh,kafin ta ɗauki mayafinta don fita lokacin da Feedoh ke cewa, "Ayyah..! Ki gaisheta please, zuwa anjima zan zo nima idan muka gama da jama'a,Allah ya bata lafiya."
Yasmeen ta amsa da "Ameen." Tana saurin ficewa daga ɗakin ta nufi waje,lokacin data fito daga gidan Baba Lawal sai taci mugun sa a wani mai adaidaita ya sauke wata,kawai sai ta shige tana sanar masa cewa can layin zai zagaya da ita.
Lokacin da suka ƙariso gidan ta bashi kuɗinsa a guje ta shige,bata ja birki a ko'ina ba sai bakin ƙofan shiga ɗakinsu.Ganin ƙofar a kulle yasa ta fara bugawa tana faɗin, "TAIMIYYAH gani na dawo taso ki buɗe ƙofar,in banda abinki ma ya za a yi ki rufe kanki a ɗaki bayan kuma baki da lafiya." Ita dai TAIMIYYAH dake daga cikin ɗakin jin muryan Yasmeen ne yasa ta tashi da ƙyar ta dafo ƙafarta tazo wajen ƙofan ta buɗe.
Yasmeen da idanunta suka sauka kan fuskar TAIMIYYAH tayi saurin sakin salati tana faɗin, "Na shiga uku ni Yasmeen kinga idanunki kuwa TAIMIYYAH,duk ciwan ne yasa ki kuka har idanunki suka kumbura haka,amma kika kasa kirana sai yanzu?"
TAIMIYYAH gaba kawai tayi ta nufi gado ta kwanta,cikin sanyin murya take cewa, "Yasmeen please bani abinci da magani kawai, ki aje duk waɗannan question ɗin,jiri nake gani wallahi."
Tayi maganan wasu hawaye masu zafi na sake ɓalle mata.Yasmeen ta juya da sauri don zuwa ta kawo mata abinci da maganin kamar yadda TAIMIYYAN ta buƙata.
Lokacin data dawo hannunta riƙe da plate ɗin data zubowa TAIMIYYAH Jallop ɗin shinkafa,wanda ya ji busassshen kifi da nama aciki,sai ta aje plate ɗin akan gado tana cewa, "Ga abincin ki tashi ki ci bari inje in ɗakko miki magani a ɗakin Abbah."
TAIMIYYAH ta tashi ta zauna tana fara cin abincin a hankali.So take ta ƙarfafa kanta ko zata samu nasaran barin garin a gobe,don ta san idan ta cigaba da nuna bata da lafiya to Guggo Bilki ba za ta taɓa bari ta tafi a goben ba.
Shiyasa lokacin da Yasmeen ta kawo mata maganin ciwan kai da zazaɓin,sai ta amsa ta shanye tana aje cup ɗin ruwan dake hannunta ta dubi yasmeen ɗin tana cewa, "Alhamdulillah! Har na ɗan ji ciwan kan ya fara sauka,in gaya miki Mamienku na fita ba sai ciwan kai ba,na fara jin sanyi alamun zazzaɓi shine fa naje na tara kaina a shower ina fitowa kuma sai rawar sanyi ba,na kifa ciki nai ta kuka ashe ƙarawa kaina wahala nake, kaina ya ɗauki wani irin ciwo,gaskiya gobe sai gida don na kula kaman zaman garinnan ciwo zai sani in kwanta,na gaji hakanan gobe gida zan koma gaskiya."
Yasmeen data tsurawa TAIMIYYAH ido ta balla mata harara tana cewa, "Aiko baki isa ba sai next week zaki tafi,ba wani ciwan da zaki kwanta in Allah ya yarda.Ke ɗince kin cika raki abu kaɗan duk ki narke ki ta faman kuka,ni wallahi har kin bani tsoro da na ga yadda idanunki suka kumbura."
TAIMIYYAH ta narke face cike da shagwaɓa take cewa, "Seriously Yasmeen hankalina yayi gida,ai nayi ƙoƙary yau fa sati na ɗaya kuma dama ai sati ɗaya nace zanyi, monday zamu koma skull don haka ni da gaske nake yi gobe zan koma, zan ma kira Iyah in sanar mata a turo Sani da wuri ya ɗauke ni,tunda ku ma kai Amarya za ku tafi goben."
Yadda Yasmeen ta ga TAIMIYYAH tayi maganan da serious sosai yasa ta gama gane rigimi take ji,kuma da gasken take yi hankalinta ya yi gida.Sai ta dubi TAIMIYYAH tana cewa, "To shikenan bari Mamie ta dawo sai aji me zata ce."
TAIMIYYAH ta wani kwaɓe fuska take cewa, "Oho! Ni dai babu wani daɗin bakin da za a min gida zan tafi gobe Allah kuwa."
Kafin Yasmeen tace komi sai ga kiran Iyah ya shigo wayar TAIMIYYAH,ta ɗauka cikin sauri tana faɗin, "Hello! My Iyah kaman kin san ke zan kira yanzu wallahi,ina yini dafatan kuna lafiya?"
Daga ɓangaren Iyah ta amsa da cewa, "Lafiya lau Zainabu ina fata goben dai zaki dawo ko? Duk kewanki ya dameni ɗazu ma Ummien ku da ta shigo take tambayan yaushe zaki dawo." Iyah ta dakata tana sauraran me TAIMIYYAH zata ce daga nata ɓangaren,TAIMIYYAH ta sauke ajiyan zuciya tana cewa, "Eh gobe zan dawo Iyah Insha Allah,maganan ma muke da Yasmeen kika kira yanzu,sai ki ma Sani magana tun yau ,gobe idan Allah ya kaimu sai ya taho da wuri mu dawo."
Iyah daga ɓangarenta ta jinjina kai kaman TAIMIYYAH na ganinta kafin ta furta, "Hakane zan masa magana yanzu ma muna gama wayan da ke,ina su Bilkin suna ta biki tace ke kinƙi shiga cikin mutane,nace mata to ina ta ga kina zuwa bare ki saki jiki da mutane dama,gara ki yi dawowarki gida hakanan,dama ai kwana bakwai kika ce za ku yi ku koma makaratar da kike zuwa ɗin ko?"
TAIMIYYAH ta jinjina kai cike da shagwaɓa take cewa, "Eh Iyah wallahi duk na ƙosa in dawo nayi kewarki sosai." Daga haka suka ɗan taɓa hira da Iyah kafin suyi sallama da juna akan cewa Iyan zata kira Sani,gobe da wuri sai ya kamo hanya.Yasmeen da ke zaune tana jin wayan TAIMIYYAH da Iyah ta zabgawa TAIMIYYAH harara tana cewa, "Ai saiki ta tafiya goben kifi ruwa gudu ma idan kin so."
TAIMIYYAH ta saki wani murmushin yaƙe, tana jin relief a zuciyarta da Iyah ta goya mata baya ta koma