Showing 78001 words to 81000 words out of 186776 words
Chapter 27 - TAIMIYAH Book Complete Document by Ayshat Dansabo Lemu .txt
baki."
Suhailah tayi maganan suna jerawa da juna zuwa cikin falon,sukai masauki bisa 3 seater baki ɗayansu lokacin da Meenah ke faɗin, "Ke rabani da wata harkar online inba Business zan fara ba.Ni sam wallahi chart bai dameni ba Suhailah bare yanzu da hidiman yara kawai nake ganin ya isheni banma da time sosai.Ku dai har yanzu amarci kuke ci baku ƙare ba bare ku bamu Babies ko?" Meenah tayi maganan cike da barkwanci idanunta akan Suhailah.
Suhailah ta saki murmushi tana faɗin,"Wani amarci Meenah ana neman gud 6yrs da aure ke dai kawai Allah ya kyauta akwai labari sosai gara da kika shigo,dama na rasa da wa zan tattauna damuwan da ke cikin zuciyata,yanzu dai bari ina zuwa insa akawobmiki wani abu."
Daga haka Suhailah ta miƙe ta nufi hanyar corridor da zai kaita kitchen.Meenah tabi bayanta da kallo kafin ta fara ƙarewa falon kallo tana jinjina irin daular da qawartata ta samu.Tun tarewan su Suhailan a gidan sau ɗaya tazo sabida aure da ya kai ita Meenan nesa,tana tare da mijinta ne a Bauchi sai sun zo gari take samu ta zo ayi zumunci.Tunda itama close friend ɗin Suhailah ce sosai tun suna Secondary skull har zuwa jami'a suna tare.Daga baya ne su Zuby da suka shegewa Suhailah har hakan yasa ita Meenah ɗan ja baya, sabida tafi kowa sanin sheɗancin Zubaida Halliru tunda kusan anguwa ɗaya suke basu da nisa sosai.
Suhailah ta fito daga kitchen ɗin Ameena mai aiki na biye da bayanta ɗauke da ƙaton tray, da aka shaƙo shi da abubuwan motsa baki.
Ameena ta aje tray ɗin a gaban Meenah tana durƙusawa ta kwashi gaisuwa,kafin ta miƙe ta bar falon bayan Meenah ta amsa gaisuwan da yi mata sannu.
Suhailah ta zubawa Meenah ido tana ganin yadda ta aje uban ƙiba abinta.Ta saki murmushi tana faɗin, "Meenah haka kika zama wata big madam shi Asheerun ya barki da wannan jikin?:Ai da Maleek ne kin bani da mita sai ya ga kin sauka zai sama miki lafiya baya son ƙiba shi sam a wajen mace.Yafi so ya ganka dai-dai misali kai ba rama kuma babu ƙiba me yawa,so miye labari ina kika baro yaran?"
Meenah ta saki dariya tana faɗin, "Yara suna Bauchi wajen kakarsu ban taho da kowa ba sabida jibi zamu juya. Biki muka zo yi fa wallahi Suhailah nima bani son ƙibar amma ya zan yi ina shan maganin sliming yaƙi amsa ta,na gaji na watsar shima yayi mitansa ya gama wallahi,ai fa ke gaki nan gunin sha'awa kin zama wata chubby abinki ke ba ƙiba kikai sosai ba kuma baki da rama so cute."
Meenah tayi magana tana ɗaukan plate ɗin da aka zubo dambun nama ta fara ci a hankali, lokacin da Suhailah ke cewa, "Amma gaskiya baki kyauta ba da kin zo koda Khalil ne shi da yake ƙarami."
"Ke rabani da wahala tunda na samu inda za a kula da su na aje su haka yafi min." Cewan Meenah tana gyara zama ta fuskanci Suhailah sosai.Suhailah ta aika mata harara tana faɗin, "Ai kin kyauta yanzu miye labari?"
Meenah ta cigaba da tauna dambun data cika baki da shi tana faɗin, "Labari na wajen ku manyan mata masu duniya,ai sai kawai mu ka ji anbaiwa Maleek Babban muƙami haka gaskiya na yi murna Allah sanya alkhairy Suhailah,yanzu Lagos za ku wuce kenan ko kina nan dai sai dai ya dinga zuwa?" Suhailah ta girgiza kai tana faɗin, "Abuja zan koma ina ga zuwa next week ma idan ya juyo daga Lagos zamu wuce.
Ai Hajjah ba za ta so mu koma Lagos ba kinsan ta tsani garin tunda aka kashe mata Miji a can shikenan ta tsani jin ko sunan garin,yanzu haka ita bata yi wani murna da wannan muƙamin ba,tunda aka ce zaman Maleek zai fi yawa a Lagos ɗin.Shiyasa kawai sai ya sayi gida a Abuja sai ya dinga zuwa duk weekend Abuja ɗin,amma fa ni nama fi so ya bar ni anan ni kaina bana son yin nesa da Hajjata."
Suhailah ta kai ƙarshen maganan tana wani narke fuska,har ga Allah ita da gaske take yi bata son komawa wani Abuja.Meenah tayi dariya tana faɗin, "Ai qawata gara dai ki koma ɗin yanzu fa an daina sakacin barin miji sakaka babu kulawa,gara ko'ina kana nane da abinka ko can Lagos ɗin ya gayyaceki kar ki sake ki nuna baki son zuwa, bi abinki ki ga halin da yake ciki a can ɗin.Idan ki kai sanya wasu na nan daga gefe suna jiran su shigo ne,don haka ki aje wannan sakarcin dana sanki da shi a baya ki kama mijinki gam ki riƙa kula da shi.Ki fita harkan qawaye Suhailah don na ga suke ɗauke miki hankali kina shirme,wai shin ma ya labarin ta hannun damar naki Zuby,har yanzu bata yi wani auren ba?"
Meenah ta ƙare maganan da jefawa Suhailah tambaya,idanunta akan Suhailan wacce tayi saurin taɓe baki kafin ta fara cewa, "Hmm! Meenah kenan wallahi ni har kinsa gabana ya faɗi da kiran sunanta ma,don sam ko sunan Zuby yanzu bana son inji an kira min."
Da tsananin mamaki Meenah ke kallon Suhailah jin furucin da ke fitowa daga bakinta,kafin ta buɗe baki tana cewa, "Suhailah duk irin amintar da ke tsakaninku shine zaki ce baki son jin ko sunanta,meyafaru ne tsakaninku haka?"
Suhailah ta ja numfashi ta sauke tana duban Meenah ta fara bata labarin yadda Zuby ta fara cusa mata ra'ayin fara shan Pills.Har kawo shawaran data bata bayan an sanar da su mahaifarta ta samu matsala,da yadda Zubaidan ta amshi number ɗin Maleek har zuwa kan makircin da Zubyn ta so shirya mata a wajen Maleek ɗin.Da irin textses ɗin da take aiko masa na son ya aureta ta ƙare maganan da cewa,
"Meenab ai Zuby ta gama sire min ta fita araina kwata-kwata,na daɗe da yin blocking ɗinta ma bani bata har abada.Dama ansha gaya min shu'uma ce amma lokacin idoma ya rufe tsakanina da Allah son ta nake da zuciya ɗaya,ashe ita bada zuciya ɗaya take tare da ni ba."
Meenah da sam bata ji wani shock akan duk labarin da Suhailah ta bata ba,don ta riga ta san wacece Zuby za ta aikata fin hakan ma.Bare tana ganin irin daulan da Suhailah ta samu da irin mijin da Allah yai mata baiwa da shi.Ita dama tunda ta ga yadda Zuby ke kwantar ma Suhailah da kai ta san ba a banza ba, akwai wata manufan da take da shi ashe ko hasashenta ya zama gaskiya.Meenah ta saki murmushin takaici kafin ta dubi Suhailah tana cewa, "Suhailah kenan dama kece baki san haƙiƙanin wacece Zubaida Halliru ba,ai zata yi fiye da haka don ita bata ɗauki cin amana a bakin komi ba.Na zura miki ido ne kawai ke da ita don na san sai irin wannan ranan ta zo Allah ma ya taimakeki da kika samu mijin da ya fargar da ke wautan da kika tafka cikin sauri.Amma Suhailah kinyi sakarci da wauta da kika biye mata har kika aikatawa kanki irin wannan Babban kuskuren.Ta ya baki taɓa haihuwa ba zaki fara shan maganin hana ɗaukan ciki inba wauta da sakarci ba....."
Meenah ta rufe ido taiwa Suhailah tatas akan irin sakarci da wautan data aikata da tare yi mata gargaɗi akan hattara da biyewa ƙawaye. Musamman a wannan zamanin da mutane suka maida cin amana ba komi ba,ta cigaba da cewa, "Suhailah ke ce baki san yadda zamani ya sauya ba sabida bakya shiga cikin mutane.Allah kuma ya yoki da kyakykyawan zuciyar da kike iya sakin jiki da kowa,to ki sani zamani yayi sauyawan da babu wata wacce zaki iya sakin jiki da ita 100% kice ba za ta iya cin amanarki ba,ko da ace ko ciki ɗaya kuka fito sabida muna cikin wani irin zamani da hassada da son kai yayi yawa a cikinsa.Ɗan uwa sai ya ci amanan ɗan uwansa sabida abin duniya,ƙawa ta ci amanar ƙawarta sabida kuɗi da son duniya.Don haka baka saurin sakin jiki da kowa yanzu bare har ka dinga buɗe cikinka a wajen wata ƙawa ta san sirrinka da na gidan aurenka,wallahi Zuby idan ta samu Maleek irin ƴan duniyan mazan nan ne ina tabbatar miki da cewa cikin ƙanƙanin lokaci za ta janye miki hankalin miji.Ko bai aureta ba suyi ta watsewarsu a waje tunda ba kamun kai gareta ba,ki godewa Allah Maleek na son ki kuma shi ɗin ɗan halas ne da ya samu kyakykyawar tarbiyyah.Wanda ruɗin zamani da giyan arziƙi bai sanya ya shiga hanyan banza ba,don haka idan zaki tashi ki kama mijinki da kyau ki tashi,magana zai ƙara aure ko wani abu duk ki barwa Allah komi,kuskure kin riga kin yi Suhailah kuma baki da hujja a yanzu ko dalilin da zaki iya hana shi ƙaro aure kamar yadda ya faɗi.Bama na miki fata ina miki fata ki samu lafiya ki haihu tamkar kowace mace,sai dai idan ƙaddaranku ce sai ya ƙaro auren kiyi addu'a ki barwa Allah komi,Insha Allah ko ya ƙaro auren sai ki ga hakan ya zame miki wani alkhairyn na daban.Amma ki aje duk wani son jiki da sakarci a gafe guda ki kama mijinki kiyi masa biyayya,yana son ki kuma shi jininki ne bazai taɓa juya miki baya akan duk wata ƙaddaran da zata sameki ba,amma batun Zuby ki bi duk hanyar da zaki bi ki ga cewa ta daina zuwa inda kike ma bare har ta sake samun fuska a wajenki,ke garama ki tattara ki bar garin kawai a huta."
Meenah ta ƙare maganan cike da ɓacin rai domin tun farko tayi takaicin yadda Suhailah ta sakarwa Zuby fuska,har take zuwa gidanta taci karen ta babu babbaka.
Suhailah ta saki ajiyan zuciya tana sake jin nadama da danasanin sakarwa Zuby fuska da tayi tun farko na ƙona zuciyarta.Ta furzar da iska me zafi daga baki tana cewa, "Meenah nagode ƙwarai da shawarwarinki tabbas ku ne qawaye nagari da kuke tsagewa mutum gaskiya komin ɗacinta.Haƙiƙa na cuci kaina na tafka wauta da sakarci hakama Hajjah ta gaya min amma Insha Allah na ɗauki Babban darasi, har abada bazan sake maimaita kwatankwacin kuskuren da nayi a baya ba.Kuma Zuby na bar ta kenan har abada na gaya miki ko sunanta bana son ji sabida idan ina tuna irin maganganun da take aikowa Maleek ji nake zuciyata tamkar zata ƙone sabida baƙin ciki....."
Suhailah ta cigaba da bayyanawa Meenah irin gadar zaren da Zuby ta dinga ɗaura ta akai,ba tare da ita ta gane cewa cutar da ita take son yi ba sai daga baya.Meenah ta jinjina ma sakarcin Suhailah sosai don ita ta ɗauka tunda Suhailah tayi aure ta fara hankali,don tun farkon Suhailah ita irin ƴan farin yarannanne masu wauta da sakarci,don ma Hajjah tayi mata riƙo irin na jajirtattun iyaye masu baiwa ƴaƴa ingantacciyar tarbiyyah da ba a san irin wauta da sakarcin da Suhailah za ta dinga yi ba.
Sai wajen ƙarfe biyu da rabi na rana bayan sun yi Lunch sannan Meenah tai shirin tafiya.Suhailah ta haura zuwa sama ta haɗo mata abin arziƙi har da su uban choculate da bata rabo da su sabida shan zaƙinta,duk ta zuba cikin leda tace akaiwa yaranta.
Meenah tayi godia me tarin yawa kafin Suhailah ta kira wayan Kabeeru driver ya zo ya maida Meenah gida.Kabeer ɗin shine driver ɗin da Maleek ya bar mata don ya dinga fita da ita unguwa,amma ita Suhailan ta fi ganewa yin driving da kanta.Sai idan bata jin yin tuƙin ne ta kan kira shi sai yazo su fita tare.
Ba a ɗauki mintuna talatin ba ya iso gidan. Suhailah tai wa Meenah rakiya har bakin mota ,sannan sukai sallama da juna kowacce na ɗagawa ƴar uwanta hannu har Kabeer ya fice daga gate ɗin gidan.
Sannan Suhailah ta juya zuwa cikin gida tana jin zuciyarta wasai cike da tarin nutsuwa.Domin ta jima tana neman wacce zata tattauna da ita akan abinda Zuby ta yi mata amma tana tsoron ai mata Allah shi ƙara.Sai gashi Allah ya jefo mata ƙawarta me son ta Meenah Waziri sun tattauna har ta ji sirrikan shu'umancin Zubyn wanda bata ma san da su a baya ba.
___________
Misalin ƙarfe ɗaya da rabi su TAIMIYYAH suka kammala shirin su tsaf.
Har ma an fitar da Luggages ɗinsu zuwa falon Iyah ƙarisowan Sani kawai suke jira, wanda shine zai kai su Kanon ba motar haya zasu bi ba,shiyasa ma har suka bari suka kai rana haka.
TAIMIYYAH tana sanye ne cikin wani Black and Red ɗin Laces wanda yai asalin amsar farar fatarta.An mata ɗinkin half gown da straight skat da ya zauna a jikinta,duk wanda ya kalleta daga zaune ko daga tsaye babu wanda zai ce tana da wata lalura sai idan ta fara tafiya tana dafa guiwa ne za a san tana da Nakasa....
Yasmeen ita tana sanye ne cikin wata doguwar rigar atamfar Holland.Wanda ɗinkin yai mata kyau ya zauna a jikinta sosai, sai ta yafa gyalen da ya shiga da kalan kayan nata,gaba ɗaya ƙamshi ke fita a jikkunansu me sanyi da daɗi.
Iyah ce ta fito daga ɗakinta hannunta riƙe da kuɗi ta miƙawa TAIMIYYAH tana faɗin, "Ungo ki riƙe wannan kuɗin ko da za ku dinga fita ki ga wani abin kina so sai ki siya,don tafiya ba kuɗi babu daɗi."
TAIMIYYAH ta ɗaga manyan idanunta tana duban Iyah kafin ta miƙa hannu ta amshi kuɗin tana faɗin, "Nagode Iyah amma ina ma fa da kuɗi cikin account ɗina,irin wanda Abie kan turo min duk ƙarshen wata bana wani kashewa, zan dai amsa wannan ɗin idan na ga abinda kike so in siyo miki."
Iyah ta jinjina kai tana faɗin, "Ni dai bance ba kena ba,ita ma kuma Yasmeen ga nata nan zan bata." Iyah tayi maganan tana miƙawa Yasmeen nata kuɗin,Yasmeen ta amsa kuɗin tayi godia,kafin su miƙe tsaye suna sanar da Iyah zasu Sasan Ummie su yi mata sallama,daga can zasu shiga har Sasan Baba Sani Yasmeen tai musu sallama.
Da Sasan Ummie suka fara ta baiwa Yasmeen kuɗi da wani turare.Yasmeen ta amsa tai godia ita kuma TAIMIYYAH ta sanar da Ummien zata bi Yasmeen sai sun dawo.
Ummie ta dubi TAIMIYYAH tana faɗin, "Amma dai ba za ki daɗe ba ko?"
TAIMIYYAH ta gyaɗa kai tana cewa, "Insha Allah Ummie bazan wuce one week ba zan dawo."
Ummie da Innarta sukai musu fatan Allah kiyaye hanya,sannan suka fito suka nufi Sasan Baba Sani don yi musu sallama.
Bayan Yasmeen tayi wa Umma sallama ne suka fito gaba ɗaya tare dasu Basmah da za su yi musu rakiya zuwa wajen mota.
Zuhurah na riƙe da ledan da Umma ta baiwa Yasmeen turmin atamfa.Ita dai TAIMIYYAH ta riga yin gaba abinta don sam bata so su jera dasu Zuhurah bare su gaya mata wata magana mara daɗi,don tana ankare da yadda Basmah ke wani binta da wani irin kallo tunda suka shiga Sasan nasu.
Sun tadda Sani har ya iso yama sanya jakunansu a Boot,hakan yasa sallama kawai suka shiga su kaiwa Iyah da Babah Ladi.
Iyah ta rako su har waje tana musu fatan isa lafiya.TAIMIYYAH ce ta shiga baya ita kuma Yasmeen ta kame a gaban motar suka fice su Zuhurah na ɗagawa Yasmeen hannu.......✍🏻
_To su TAIMIYYAH ƴan Kano sai muce a isa lafiya._
*Salamu alaikum! Ina ma'abota son ƙamshin su ke ne? Uwargida da Amare masu shirin shigewa daga ciki kai har ma da ƴan mata ma'abota son ƙamshi da ƙamsasa suturunku* *.To ga dama ta samu don kuwa shahararriyar mai saida turarukan wuta me asalin kyau da inganci wato RUUSCOLLLECTIONS ta zo muku da turarukan wuta na sawa a ɗaki wanda tun daga kunna shi baza ki taɓa jin ƙauri ba daga farko har karshensa.*
*Bata tsaya anan kaɗai ba don kuwa akwai jerin gwanon kalolin turarukanta masu ƙamsasa jiki da gida haɗi da ɗakuna ma baki ɗaya kamar haka* 👇🏻
*Akwai oil koleccha,da cream koleccha,Body butter, white humra,attraction humra, Mehlab humra, Dufr humra, brown humra, oil humra, golden humra da yellow humra,*
*Turaren wuta dinta kuwa Arabian black bakhoor mai kamshin harami, yemani bakhoor, hemani flakes, sandal rose, sandal flakes, Arabian spices, Senegalese kajiji, Couscous, special kajiji, Golden sand, wardrobe balls, Ruus Remix, Exclusive Dufr, cotton candy, Queen of the night, Bukhur, Alajab.*
*Akwai airfreshner, morphing mist, shampoo, hair cream, Vaseline.* *Harma da su atamfofi, less, shadda, takalma da mayafai duk zaki same su a wajen RUSS COLLECTION .*
Za ku sameta a Garin Kano ta wannan adireshin:- No:221 sarari koki quaters.
Ko ku nemeta a garin Kaduna a Unguwar kanawa.
ga handle ɗinta na Instagrm kamar haka👇🏻
@ Ruuscollections
Ga kuma lambar wayarta don kiranta kai tsaye 👇🏻
07025393114
#Ɗansabo ce#
[12/14, 10:06 PM] +234 703 769 7050: *Littafin TAIMIYYAH paid book ne,ga duk wanda ta tsincesa a kowani irin group ne,kiji tsoran Allah karki karanta sai kin biya 500 naira only.*
*Za ku iya min magana ta wannan number ɗin 08167768704, ko kuma ku turo kuɗin ku kai tsaye ta wannan account ɗin*👇🏻
0504192664 aisha ibrahim dansabo GTbank.
*Sai ku tura shaidan biyanku ta wannan line ɗin 08167768704.*
Masu turo credit za ku turo katin MTN na 500 ta wannan line ɗin 08167768704.
_*Ina ƴan kasuwa masu buƙatar a tallata muku hajar ku? Maza ku garzayo da kuɗi ƙalilan a tallata muku kayan siyarwanku sai dai kawai ku ji ana kiran waya don buƙatan sayan kayan ku,ku tuntuɓeni ta layina kamar haka 08167768704.*_
*39*
*Kano.*
Ƙarfe huɗu da wasu ƴan mintuna motar Sani ya faka daga bakin gate ɗin shiga gidansu Yasmeen dake Unguwar Nasarawa GRA Kano.
TAIMIYYAH da bata saba da zaman mota ba sabida rashin sabo tafiye-tafiye da bata cika yi ba.A gajiye ta zuro ƙafafunta zuwa waje daga cikin motar,bayan ta yiwa Allah godia da ya iso dasu lafiya.
Yasmeen ce ta baiwa Sani umurnin shiga da motar daga cikin Compound bayan mai gadi ya buɗe gate ɗin.
Suka rankaya ita da TAIMIYYAH zuwa cikin gidan nasu Yasmeen wanda zuwan TAIMIYYAH na huɗu kenan zata ce sabida Iyah sam bata son ta ga ta matsa daga kusa da ita.Sai da wani dalili me ƙarfi,tun ƴan uwa da dangin mahaifiyar TAIMIYYAH na mita har sun gaji sun bari.
Da sallama ɗauke a bakinsu suka isa ƙofar shiga Babbar Main parlor na gidan.Mai aikinsu Yasmeen Kuluwa itace ta amsa sallaman tana musu barka da zuwa. TAIMIYYAH ta gaida ta cike da ladabi kasancewarta