Showing 81001 words to 84000 words out of 186776 words
Chapter 28 - TAIMIYAH Book Complete Document by Ayshat Dansabo Lemu .txt
Dattijiya da zata kusa sa'ar Iyah.
Guggo Bilkice ta fito daga ɗaki tana musu sannu da zuwa tare da rungume TAIMIYYAH a jikinta.TAIMIYYAH ta gaida Guggo Bilkin tana faman zuba mata shagwaɓar cewa ta gaji.
Guggo Bilki ta dube ta cike da kulawa tana faɗin, "To ai sai ki je ki watsa ruwa yanzu zaki ji duk gajiyan ta ware, sai ku fito ga abinci can yana jiranku a dining,idan kun kammala duka da abincin sai ku sameni a part ɗin Abban su Yasmeen, ku gaishe sa kun san yau weekend yana gida."
TAIMIYYAH ta jinjina kai cike da gamsuwa tana cewa, "To Guggo Bilki bari in fara da wankan wallahi na gaji sosai."
Kafin Guggo Bilki tace wani abu Sani ya shigo ɗauke da jakunansu.Ya gaisa da Guggo Bilki yana aje jakunan anan cikin falon,tai masa barka da iso lafiya tana me ɗaga murya ta kira ɗaya me aikin nasu me suna Ramma.
Bayan Ramma ta ƙariso ne Guggo Bilki ta bata umurnin zuwa ta buɗewa Sani ɗakin baƙi,akai masa abinci da komi da komi.Sani yai godia yana juyawa ya fice daga falon.
Ita TAIMIYYAH tuni har ta isa ɗakin Yasmeen,ta fara da cire kayan jikinta don shiga wanka.
Lokacin data fito wankan har Yasmeen ta kawo musu abincin nan ɗaki.TAIMIYYAH ko mai bata tsaya shafawa ba ta nufi wajen akwatinta ta ciro wata gown mara nauyi na Material ta saka.
Yasmeen ma wankan ta shiga itama.Lokacin data fito ta samu TAIMIYYAH ta zuba abinci tana ci,wayanta na hannunta riƙe tana chart da Zee dake tambayarta cewa ko sun isa Kanon? TAIMIYYAH ta bata amsa da cewa gatanan ma har tayi wanka tana cin abinci ne.Yasmeen ce ta dubi TAIMIYYAH tana faɗin, "Sis manya ina fata dai har kin kira Iyah don hankalinta ya kwanta mun iso lafiya."
"Oh God! Gara da kika tuna min wallahi ita nake da niyyan kira,sai kuma hannuna ya kunna data na hau online,Zee ta tasani da surutunta bari ki gani in kira ta yanzu kuwa."
Daga haka TAIMIYYAH tayi dialing number ɗin Iyah,aiko bugu biyu ta ɗaga suka gaisa. TAIMIYYAH ta sanar mata cewa sun iso lafiya basu jima sosai suna magana ba TAIMIYYAH tayi hanging up.Tana shirin aje wayar saƙo ya shigo har zata yi banza taƙi duba saƙon.Sai kuma ta ga lambar Nass ne data kasa sharewa a wayarta,hakan yasa ta buɗe saƙon,zuciyarta na ingizata ta buɗe message ɗin message ɗin ta ga ko me ke ciki.
Aiko lokacin data buɗe saƙon ta fara karantawa,bata san lokacin da hawaye suka fara zarya a face ɗinta ba.Wani irin tausayin kansu da soyayyar Nass ɗin da take ƙoƙarin dannewa na tasowa baki ɗaya.
Kalamai ne yayi anfani da su masu nuna zallan kewanta da shiga cikin mummunan yanayi da yayi a sanadiyyar ta daina kula shi,ta daina ɗaukar wayarsa bare ya samu darajan da zata maida masa reply, na saƙonnin daya dinga turo mata.
Daga ƙarshen saƙon ne ya furta kalaman da suka sanya ta zubda hawaye.Sakamakon sanar da ita cewa Mummynsa tayi masa Allah ya isa,ta kuma ce idan bar rabu da ita ba sai ta tsine masa.
Sannan bata amince ya cigaba da bibiyan TAIMIYYAN koda ta waya bane.Ya kai ƙarshen kalamansa da cewa,
" _Zaynab zan barki ne ba don zuciyata ta daina son ki da ƙaunar ba.Sai don gudun kada fushi da tsinuwar mahaifiya ya tabbata akaina.Ina so kisa a zuciyarki ni Naseer Aliyu Ƙwarbai da soyayyarki zan mutu,sabida ina miki son da koni bansan adadinsa ba.Don Allah Zaynab ki taya ni da addu'an Allah ya bani juriya da danganan rabuwarmu da juna,domin ina cikin wani hali da baki bazai iya furtawa ba,ina miki fatan alkhairy tare da samun masoyin da zai fini sonki da ƙaunarki,ina fata zan ji koda kalma ɗaya ne tak! Daga gareki bayan kin gama karanta saƙona,_
_Ur Nass Aliyu Ƙwarbai."_
TAIMIYYAH na kaiwa ƙarshen saƙon ta saki wani irin kuka me cin rai.Tana kai hannu ta dafe bakinta don gudun sautin kukan kada ya janyo hankalin Yasmeen.Wacce ke can gaban Drawer ɗin kayanta,tana cire kayanta daga akwati tana jere su a ciki.
Tayi kuka me yawa kafin ta samu ƙwarin guiwan tura masa da reply masu ɗauke da taƙaitattun kalmomi na fatan alkhairy.Daga ƙarshe bayan ta tura saƙon,sai ta samu kanta da goge dukkanin lambobinsa biyu dake cikin wayarta baki ɗaya,ta tashi a hankali ta isa kan gadon ɗakin Yasmeen ta kwanta tana ji wani sabon kukan na zuwar mata. Ta saki kukan da ƙarfi wannan karon,don ji take yi tamkar ta sanya hannu ta ciro zuciyarta daga ƙirjinta ta cire duk wata soyayyar Nass dake danƙare a ciki.Amma bata da wannan damar shiyasa ta saki kukanta me sauti,wanda hakan ya janyo hankalin Yasmeen tayi saurin aje kayan dake hannunta.Ta iso wajen TAIMIYYAH tana tambayanta abinda ke faruwa,memakon TAIMIYYAH ta bata amsa sai ta sake rushewa da kuka.
Cikin kukan take sanar da Yasmeen saƙon Nass ɗin,ta ƙare maganan da cewa, "Yasmeen ba ina kuka bane don mahaifiyarsa tace ya barni ba,ina kuka ne sabida zafi da takaicin dalilin ƙina da take yi da Nass ɗin,sabida kawai Allah ya mayar dani gurguwa.Yasmeen zuciyata zafi take yi idan ina tuna irin cin fuskan da tai min.Meyasa mutane suka daina duba kyawun halayya da nasaba me kyau,suka koma duba zubin halitta da ƙyalƙyalin duniya? Miye aibuna a hakan Yasmeen don na zamo gurguwa...?"
TAIMIYYAH ta sake sakin kuka me cin rai ji take yi ina ma da itace tabi Abie suka bar gidan duniya ko zata huta da cin fuska da isgilancin da take fuskanta daga wajen wasu mutane,da suke ɗaukarta a maƙasƙanciya sabida kawai Allah ya jarabceta da zama Gurguwa.
Yasmeen da tausayin TAIMIYYAH ya gama cika zuciyarta har ƙwalla na taruwa a idanunta,tayi saurin zama kusa da TAIMIYYAH tana fara rarrashinta da kalamai na kwantar da hankali.
Bayan Yasmeen ta ci nasaran tsaida kukan da TAIMIYAH keyi ne sai ta lallaɓata akan ta wanko face ɗinta.Lolacin da TAIMIYYAH ta fito daga toilet bayan ta wanko fuskarta,sai suka sanya Hijab suka fito don zuwa Sashin Abban su Yasmeen ɗin su gaishe shi.
Da sallama suka shiga cikin falon nasa yana zaune kusa da Guggo Bilki dake gefensa.Sun maida hankali wajen kallon TV Guggo Bilkin ce ta amsa sallaman nasu, Yasmeen ta nufi wajen Abbanta da sauri tana faɗin, "Abbah i miss u." Abban ya shafa kanta yana faɗin "Miss u too my Auta kun iso lafiya ko? TAIMIYYAN Iyah barka da zuwa Kanon Dabo."
TAIMIYYAH ta isa ta durƙusa a gabansa ta gaishe shi,tana me faɗin, "Lafiya lau Abbah mun sameku lafiya?"
Abbah ya saki murmushi yana bata amsa da cewa, "Lafiya lau Zaynab barkan ku da zuwa." Daga haka TAIMIYYAH ta tashi ta fito daga falon ta bar Yasmeen a can tana zubawa Abban shagwaɓa,don tasan ita ɗin ta gaban goshinsa ce sosai.
Fitowan TAIMIYYAH zuwa main-parlor ɗin yayi dai-dai da shigowan big bros ɗin su Yasmeen ɗin me suna Emran.TAIMIYYAH ta ɗaga manyan idanunta ta sauke akansa lokacin da shima idanunsa ke sauka akanta.Sai ta ɗan saki fuska sosai tana cewa, "Sannu da zuwa Yah Emran ina yini."
Emran ya amsa a taƙaice da faɗin, "Lafiya lau Sis barka da xuwa." Daga haka bai sake cewa komi ba ya nufi hanyar da zai kaishi kitchen.
TAIMIYYAH tabi bayansa da kallo tana taɓe baki,don batun yau ba ta san shi ɗin miskili ne na gaske.
Sam baida hayaniya da kula mutane fuskarnan kullum a cuskule yake.
Memakon ta zauna a falon ma sai kawai ta yanke shawaran komawa ɗakin Yasmeen tai kwanciyarta tana ɗaukar wayarta ta hau online.
Yasmeen data shigo ta ganta a kwance sai ta nufeta tana cewa "Ke yada kwanciya a ɗaka kamam wata baƙuwa,ki tashi mu fita falo mana ga su Yah Anas can sun shigo ku gaisa."
TAIMIYYAH sai ta tashi zaune tana taɓe baki take cewa, "Ni rabani da wani fita falo wannan Yah Emran ɗin yaita ma mutane kallon banza.Baki ga fa dana gaida shi yadda amsa gaisuwan a wani wulaƙance,shi dai akwai baƙin hali wallahi."
Yadda TAIMIYYAH tayi maganan tana faman kwaɓe fuska yasa Yasmeen sakin dariya tana faɗin, "Ke sai kace baki san hali ba TAIMIYYAH da har zaki wani damu don ya yi miki hakan,shi fa kowa ya san halin miskilncinsa.Shiyasa gashi nan ko budurwa ya kasa yi har ansawa Yah Anas rana ashe ina can Zaria,amma shi kin ga ko budurwa bana ji yana da ita,don Allah ki tashi mu je falo nasan ma bazai zauna ba ya fita abinsa zuwa part ɗinsu."
Ba don TAIMIYYAH taso ba haka tabi Yasmeen suka fita xuwa falon.TAIMIYYAH da fuskan mutumin nata Yah Emran ta fara cin karo,yana nan zaune babu wani inda ya je.
Sai ta haɗe fuska tana ɗauke kai daga duban sashin da yake zaune.Ta ƙarisa kusa da kujeran da Yah Anas ke zaune wanda tun fitowan su TAIMIYYAH yake sakar mata murmushi,kafin ya riga ta da faɗin "Wow! Sis barka da xuwa yau wace rana Iyah ta barki kin shigo Kano,welcome dear Sisi."
TAIMIYYAH itama sai ta sakar masa murmushinta me kyau tana faɗin," Thank u Yah Anas na sameku lafiya,ashe kuma an sanya lokaci to Allah ya sanya alkhairy yasa za a yi muna raye,kace kafin inbar gari za a kaini inga irin zaɓen da kai mana ta Sis in-law."
Anas ya saki dariya yana faɗin, "Karki damu Sis kisa a ranki kin ganta kin gama."
TAIMIYYAH ta maida masa martanin dariyan da yayi ƙasa-ƙasa.Tana maida dubanta kan ɗaya Yayan su Yasmeen ɗin me suna Ahmad tana faɗin, "Yah Ahmad ya kake?"
Ahmad da idanunsa ke kan TAIMIYYAH ya amsa da faɗin, "Lafiya lau aina ɗauka ba za ki gaishe ni bane sai Anas kawai kika sani." Yadda yayi maganan yana hararanta yasa duka suka saki dariya a tare.TAIMIYYAH na faɗin, "Sorry ai abin step by step ake bi,yanzu ba gashi mun gaisa ba ashe kananan dai kuna buga kishi da juna da Yah Anas ɗin."
Ahmad ya sake aika mata harara yana faɗin, "To ya za a yi kinsan saƙo da saƙo ai." Suka sake sakin dariya TAIMIYYAH sam bata sake duban inda Yah Emran ke zaune ba.Wanda ya harɗe ƙafa gaba ɗaya hankalinsa na kan TV amma kunnuwansa na jiyo masa duk abinda akeyi cikin falon.
Hiransu suka yi sosai da su Yah Anas ɗin,Yusuf ne kawai baya nan wai yayi tafiya tare da wani Cousine ɗinsu xuwa Niger.Sai da aka kira Sallar Magriba sannan suka watse,mazan suka nufi masallaci su kuma su TAIMIYYAH suka shige ciki don yin nasu sallar.
Kwananta biyu da zuwa Kanon ta ware sosai a gidan Guggo Bilkin.Tana jin daɗin yadda ƴan uwanta su Anas ke ji da ita,don duk idan zasu dawo daga wajen aiki shi da Ahmad sai sun shigo mata da Ice Cream da su Shawarma.
Yah Emran ne kawai babu ruwanta da shi daga gaisuwa sai gaisuwa ke haɗa su.
Yasmeen ta kan fita zuwa can gidan da za su yi bikin cousine Sis ɗin tasu.Kasancewar gidan babu nisa da gidan su Yasmeen ɗin layi ɗaya ne ya raba su,shiyasa da ƙafa ma Yasmeen ke zagayawa ta je.
Ita dai TAIMIYYAH ko sau ɗaya bata taɓa bin Yasmeen ɗin ba don ita sam bata son shiga cikin mutanen da bata saba dasu ba.Guggo Bilki tayi mita akan su dinga zuwa ana shirin bikin da su tare, amma TAIMIYYAH tayi biris taƙi zuwa.
Yauma tun safe Yasmeen ta gama shiri bayan sun karya kumallo.Ta sanar da TAIMIYYAH cewa zata fita zuwa gidan Babansu Lawal ɗin,don yau Thursday za a yi lalli.
TAIMIYYAH da ke daga kwance sai kawai ta sake gyara kwanciya tana faɗin, "Yasmeen ni wallahi bana son shiga mutanen da ban sani ba.Dama mun saba da Amaryar ce sai na je to amma ban santa ba itama ba sanina tayi ba,kawai sai aganni ana nuna ni ana cewa waccar gurguwan kuma daga ina?Gaskiya ba za ni ba ni ko ranan yinin ma ni kaɗai zaku bari a gidan don ba zuwa zanyi ba."
Yasmeen data gama jin haushi ta ballawa TAIMIYYAH harara tana cewa,"Ai ke kina da damuwa wallahi TAIMIYYAH.Inba haka ba miye na kawo wannan maganan,don Allah ki taso muje kema ai miki lallin mana,ko ja ne zai miki kyau sosai wallahi."
Da ƙyar ta ciyo kan TAIMIYTAH ta yadda zata bita itama ai mata lallin amma a hannu kawai.Ta tashi ta shirya cikin wata doguwar rigan atamfa da ɗinkin yabi jikinta sosai.Kamar yadda kalar atamfar me duhu ya haske farar fatarta,ta sanya Hijab irin me kamar riga ɗinnan,wanda zaka zura hannuwa kai ta sabgarka babu takura.
Suka fito sai faman zuba qamshi suke yi.Sallama sukaiwa Guggo Bilki wacce taji daɗin yadda yau TAIMIYYAH ta yadda zasu fita zuwa gidan Bikin da Yasmeen.
Tayi musu a dawo lafiya suna jerawa da juna suka fice daga gidan.
"TAIMIYYAH bari kawai mu ƙarisa bakin layin shigowa nan zamu sama Ɗan-sahu,sai mu hau ya zagaya damu layin gidan Baba Lawal don gaskiya zan wahal dake idan nace mu taka a ƙafa."
Yasmeen tayi maganan idanunta akan TAIMIYYAH da ke dafe da guiwar ƙafarta suna takawa a hankali.Lokacin da suka ƙarisa bakin titin basu wani daɗe ba suka tare Napep suka shige,ya zagaya dasu xuwa gidan Baba Lawal ɗin,suka sauka Yasmeen ta biya shi kuɗinsa suka shige zuwa cikin gidan.
A falon gidan suka tadda Anty Kareema matar Baba Lawal tare da wasu baƙi.Suka gaisheta ta amsa da fara'a idanunta akan TAIMIYYAH take cewa, "Yasmeen ina kika samo kyakykyawar budurwa haka,ko itace naji kina cewa kun zo daga Zaria tare?"
Yasmeen ta saki murmushi tana faɗin "Itace Ummah sunanta TAIMIYYAH,bata son shiga mutanene yanzu ma da ƙyar ta amince ta biyoni,Kausar ɗin na ɗaki ne?"
Anty Kareema dasu Yasmeen ke kira da Ummah,ta dubi Yasmeen ɗin tana bata amsa da cewa, "Allah sarki wallahi kyakykyawa da ita,Kausar na daga ciki ku ƙarisa mana na san ai sun gama shiri gara kuje wajen lallinnan da wuri." Daga haka su Yasmeen suka wuce zuwa don ƙarisawa ɗakin ƴan matan gidan.Anty Kareema da baƙuwarta suka bi bayan su TAIMIYYAH da kallo baƙuwar na cewa, "Oh! Yarinya kyakykyawa da ita amma ta nakasa wannan da ba gurguwa bace da anga zallar diri da kyawun halitta,wallahi sai naji duk tausayinta ya kamani."
Anty Kareema ta jinjina kai tana cewa, "Ke dai bari Raliya kin riga ni da baki ne,wallahi yarinyar ta birgeni a ganin farko,haka Allah ke ikonsa."
Duk wannan maganganun dasu Anty Kareema ke yi akan kunnin TAIMIYYAH ne.Wacce ke bin bayan Yasmeen a hankali zuwa ƙoafr shiga ɗakin ƴan matan,don haka akan kunninta sukai maganan.
Ta shige cikin ɗakin daga ƙarshe tana jin wani iri cikin zuciyarta.Ire-iren waɗannan maganganun da bata rabo da jin su suna ɗaya daga cikin abinda yasa bata faye son shiga mutane ba.Sabida yawan tanka kyawunta da tausayawa Nakasanta da mutane ke yawan yi,wanda hakan na taɓa zuciyarta da jefa mata rauni da tausayin kanta da kanta.
Lokacin da suka shige cikin ɗakin ƴan matan wanda su biyu ne ma suka rage ba su yi aure ba.Yasmeen ce ta nunawa TAIMIYYAH gefen gado tana cewa, "Ga waje TAIMIYYAH zauna,Kausar ga TAIMIYYAH na janyo muku ita yau zamu tafi Lallin tare."
Daga Amarya Kausar har ƙanwarta me suna Firdausy suka zubowa TAIMIYYAH idanu.Firdausy na riga Kausar da faɗin, "Sannu da zuwa TAIMIYYAH,Yasmeen gaskiya ƴar uwar taki kyakykyawace ga sunanta unique, sam ni ban taɓa jin mace da suna TAIMIYYAH ba."
TAIMIYYAH ta sakar musu murmushi suka gaisa cikin fara'a, Yasmeen na cewa Feedoh, "Haka kowa ke cewa bai taɓa jin sunan ba a wajen mata.Kuma asalin suna TAIMIYYAH mata aka fi samawa don ko Abul Barakat da Abul Abbas da ake ce musu Ibnu TAIMIYYAH.Toh su TAIMIYYAN sunan wata kakarsuce na can sama amma macece,sai dai a wajen su labarabawa ba kowanne irin mutum suke kira da suna TAIMIYYAH ba.Sai wanda ya shahara da ko dai kyau ya zama mutum kyakykyawaneshi na buga misali,ko kuma irin budurwarnan wacce take da kyawawan ɗabi'u da iya zama da mutane me haƙury sosai to sai su kirata da suna TAIMIYYAH.Amma galibi bakasafai suke kiran mutum TAIMIYYAH ba se wanda yake da siffofi da ɗabi'u masu kyau abun yabo."
Yasmeen ta kai ƙarshen bayaninta,tana sakin murmush ganin irin hararan da TAIMIYYAH ke aika mata.
Kausar ta furta, "Wow! kice idan na haifi ƴata mace kyakykyawa zan sanya mata suna TAIMIYYAH kuwa,sai in mata fata ta taso da dukkanin siffofi ababen yabo.Yadda za ta cika sharuɗan cinye suna TAIMIYYAH,don wannan Sis ɗin taki Yasmeen da alamu ita ta cinye sunan,don ga kyau nan ga kuma alamun nutsuwa a tare da ita."
Yasmeen ta saki dariya ita da Feedoh suna haɗa baki wajen faɗin, "Amma wannan Amarya baki da kunya tun kafin ma a ɗaura har kin fara zancen haihuwa,eh lallai gara ayi-ayi mu miƙaki tun kafin kifi ƙarfin mu."
Wannan karon har da TAIMIYYAH aka saki dariya,kafin su Feedoh su kammala shirinsu Kausar ta kira wanda zai kaisu wajen yin Lallin.
Lokacin da suka fito jere da junane su Kausar suka kula da yanayin tafiyar TAIMIYYAH.Suka gane ashe gurguwace me laluran ƙafa,take suka ji wani tausayinta ya kama zuciyarsu,Feedoh tai ƙasa da murya tana cewa Kausar, "Wayyo Yah Kausar dubi yadda sai ta dafe guiwa take iya tafiya,ina ma Allah bai jarabceta da laluran ƙafa ba,wannan ai da baƙaramar haɗaɗɗiyar mace za a yi a wajennan ba.Sabida Allah ya bata kyau da dirin jiki,dama shiyasa ake cewa ɗan Adam tara yake bai cika goma ba.Duk abinda kake taƙama da shi sai an rageka ta wani fannin toh ita dai da gurgunta aka jarabceta,amma fa wannan matar manyace gaskiya akwai body da kyau masha Allah."
Kausar ta jinjina kai tana faɗin, "Wallahi kuwa Feedoh,Allah dai yasa mu dace amma naji tausayinta ya kama zuciyata."
TAIMIYYAH dai tayi gaba abinta bata san wainar dasu Kausar ke toyawa akanta ba.Don lokacin da suka fito wajen motar wanda zai kai su kiran Zee ya shigo wayar TAIMIYYAH.Don haka tai receving call ɗin tana kaiwa kunni lokacin da Yasmeen ta buɗe mata murfin back seat ta shige ta zauna.Itama Yasmeen da Kausar back seat ɗin suka shiga sai Feedoh ne ta kame agaba. Yellow yaja motar suna barin layin,har lokacin TAIMIYYAH na amsa wayar Zee dake bata labarin tayi sabon Saurayi.
Lokacin da suka isa gidan Lallin Amarya Kausar ita aka fara yiwa ja a ƙafa.Sannan akaiwa TAIMIYYAH a hannu don tace bata son baƙi iya ja kawai za a mata.
Da ƙyar su kausar suka ja ra'ayinta ta yarda ai mata