Showing 165001 words to 168000 words out of 186776 words

Chapter 56 - TAIMIYAH Book Complete Document by Ayshat Dansabo Lemu .txt

15 Dec 2024

6619

ita ta hanyar kiran sunanta, 'Zaynabb' Hakan yasa TAIMIYYAH dakatawa daga tafiyar da fara tana dafe da guiwar ƙafarta. Maleek ya yi taku uku ya cimmata yana yin ƙasa da muryarsa yadda koni me ɗakko muku rahoto, ban ji me ya ce ba, ya furtawa TAIMIYYAH wasu ƴan kalmomi, da suka sanyata saurin rufe fuskarta da Hijab ɗin dake sanye a jikinta. Wani irin feeling ta ke ji na zagaye jinin jikinta, yana sake narke zuciyarta da dilmiyata a ƙaunar Maleek ɗin me tsanani. Ta buɗe face ɗin tana ƙin juyowa ta kallesa kamar yadda yaci buri,ta sake shagwaɓe murya tana cewa, "Ni dai babu ruwana Yah Maleek Bye! Ka gaida min da Hajjah." Daga haka ta fara takawa ta nufi hanyar komawa Sasan Iyah,Maleek ya bi bayanta da ido yana ƙarewa yanayin tafiyarta da ke bashi tausayi kallo.Zuciyarsa na sake jin feeling me tsanani akanta,har sai da ta ɓacewa ganinsa ya juya zuwa wajen motarsa.
Yusuf ya iso da sauri ya buɗe masa back seat ya shiga ya zauna,yana ji tamkar zai bar wani ɓari na farin cikin rayuwarsa ne daga cikin gidan......✍🏻










#Ɗansabo ce#
[12/14, 10:14 PM] +234 703 769 7050: Littafin TAIMIYYAH paid book ne,ga duk wanda ta tsincesa a kowani irin group ne,kiji tsoran Allah karki karanta sai kin biya 500 naira only.


Za ku iya min magana ta wannan number ɗin 08167768704, ko kuma ku turo kuɗin ku kai tsaye ta wannan account ɗin 0504192664 aisha ibrahim dansabo GTbank.*


*Sai ku tura shaidan biyanku ta wannan line ɗin 08167768704.*


Masu turo credit za ku turo katin MTN na 500 ta wannan line ɗin 08167768704.




_Ina ƴan kasuwa masu buƙatar a tallata muku hajar ku? Maza ku garzayo da kuɗi ƙalilan a tallata muku kayan siyarwanku sai dai kawai ku ji ana kiran waya don buƙatan sayan kayan ku,ku tuntuɓeni ta layina kamar haka 08167768704._


*65*


Umma na isa cikin falonta ta zube a cikin kujera tana faman sauke numfashi,zuciyarta na mata wani irin suya da ƙona. Su Zuhurah da Basmah da ke zaune suna magana akan tsarin bikinsu suka ɗaga kai a tare suka dubi Umma suna haɗa baki wajen faɗin, "Umma har kun dawo,lafiya duk ki ka fita hayyacinki haka?"


Umma ta ɗago ido ta dubi su Zuhurah ta ce, "Zuhurah ina cikin tashin hankali da firgici,ji na ke yi tamkar zan yi hauka wallahi, wannan hatsabibin Bokan da muka dawo daga wajensa wallahi ya fi Maharazu shaiɗanci, don ya sanar da ni abinda ya fi gaban auren waccar gurguwar tashin hankali,don aure ya ce babu fashi sai an ɗaura shi don haka yanzu babu su cikin lissafina,maganar auren Ubanku yanzu shi ne babbar tashin hankalina."


Umma ta kai ƙarshen maganan tana ji tamkar numfashinta zai sarƙe,Hajiya Barirah da ta ƙariso cikin falon ne ta dubi Umma ta ce, "Hajiya Zuwairah wannan tashin hankalin duk ba shi ne mafita ba,sha'ani ne a gabanki nan da ƴan kwanaki za ki fara tara mutane,yakamata a ce kin sanya nutsuwa cikin lamuranki don kaucewa surutun mutane. Ki nutsu a kammala wannan hidiman kafin ki kwantar da kai ki binciko wace ce ke shirin kutso kai cikin rayuwarku ke da mijinki."


Su Zuhurah gaba ɗaya sai kan su ya kulle da maganganun su Umma, Zuhurah ta dubi Hajiya Barirah cike da tarin son ƙarin bayani daga bakin Hajiyan ta ce, "Anty kun samu a duhu wane ne zai yi auren? Kuma meyasa ba za a iya fasa bikin TAIMIYYAH ba,wallahi Anty ina cikin baƙin ciki tun daga sanda na san waye za ta aura hankalina ya tashi,bamu sake sarewa da lamarin ba sai da aka kawo lefenta,wanda hakan yasa babu shiri muka soke kawo namu lefen don kunya kawai za mu sha,sabida gaba ɗaya babu wanda zai dubi lefenmu da gashi,don duk wata dukiya an gama zube ta ana waccar shegiyar gurguwar,don Allah Anty a san duk yadda za a yi a fasa bikin ta rasa shi kowa ya huta."


Zuhurah ta yi maganar idanunta akan Hajiya Barirah,wacce ta ke ta faman murmushi kafin ta dubi Zuhurah ta ce, "Zuhurah wannan auren ƙaddararren aure ne da babu mahalukin da da zai iya hana a ɗaura shi,don haka ku yi haƙury ku yi fatan idan ta shiga kada ta samu zaman lafiya da abokiyar zaman,amma aure kaman an yi an gama in ji Kallah,yanzu abinda za ku fuskanta ya fi gaban wannan matsalar na ita gurguwar,don Ubanku aka ce zai ƙara aure nan ba da jimawa ba,kuma a cikin auren na shi akwai zazzafan rabo da zai gitta wanda hakan shi ne silar mutuwar mijin matar da zai aura ɗin,babbar tashin hankalin shine ba a bayyanawa Boka wace ce matar ba,kun ga kenan Ummanku na cikin matsala da ku kanku,don ba ku san wata jarabar za a kwaso a kawo muku ba."


Basmah ta danna wata uwar ashar lokacin da Hajiya Barirah ta kai ƙarshen maganarta,kafin ta maida dubanta kan Umma ta ce, "Umma yanzu sabida Allah da gaske Baba sai ya iya miki kishiya? Lallai ko wace ce sai ta ci ubanta idan ta shigo gidannan kuwa,don Allah ki kwantar da hankalinki a gama wannan bikin, mu samu nutsuwa a ɗakin mazajenmu daga baya sai mu maida hankali wajen gano wace ce wacce zai aura ɗin,ita kuma TAIMIYYAH In sha Allah ba za ta taɓa samun kwanciyar hankali a gidan aurenta ba,ba dai arziƙi su ke mawa ba to ga ta ga guy ɗinnan,don wallahi yafi ƙarfin ajin ta kawai Iyah ce da uwarsa suka haɗa abun kamar yadda na ji labari."


Umma ta dubi Basmah ta ce, "Basmah in ji ubanwa ya ce miki auren haɗi ne? Kin ko ga yadda ya ke kallonta kamar zai cinyeta,yanzu fa muka wuto su a waje ta yo masa rakiya,kun ga haɗuwar mutumin kuwa? Motar da ya zo a cikinta kanta abin hankali ya tashi ne idan ku ka ga haɗuwa da girmanta, don ina ga kuɗinta zai iya siye duka motocin da mazajenku ke hawa,wallahi ina cikin baƙin ciki da wannnan ƙaddararren auren na TAIMIYYAH,yanzu ne na ke jin tsanarta har cikin ƙashi da ɓargona domin ban taɓa tunanin musaka kamarta za ta iya taka matsayin auren attajiri irin wannan mutumin ba,babban tashin hankalina shi ne ta haihu da shi don ance bai taɓa haihuwa ba,kun ko ga idan ta haihu shikenan sun fara mamaye dukiyarsa don akanta zai talike,ina cikin tsaka me wuya Hajiya Barirah,na rasa da wanne zan ji? Auren ubansu da Boka ya ce zai tabbata ko kuwa baƙin cikin auren wannan Yariyar dana tsana tun tana tsumman goyo?"


Umma ta ƙare maganar da jefawa Hajiya Barirah tambayar idanunta na tara ƙwallan baƙin ciki, zuciyarta na mata wani irin nauyi tamkar an ɗauki bulo an ɗaura mata a ƙirji.


Hajiya Barirah ta dubi Umma cike da jin tausayinta ta ce, "Hajiya Barirah haƙury kawai za ki yi amma tunda Boka ya furta miki hakan,to ki sawa ranki hakan ne don bai taɓa faɗin abinda ba zai tabbata ba. Yanxu dai mu kammala da hidiman da ke gabanmu,sannan kada ki sake ki nunawa Sani cewa kin ji wani magana akan zancen zai ƙara aure,ki zuba masa ido har a ƙare bukukuwan nan da ke gabanmu. Na tabbatar ko ma wace ce za ta bayyana mana cikin sauƙi idan har ki ka iya riƙe kanki,ki ka kuma iya danne duk wani kishi da baƙin cikin da ke ta so miki. Sabida rayuwa duka da kike ganinta iya siyasa ce da kissa na zaman duniya,wanda suka iya suke da riba wanda basu iya ba kuma sai mu yi ta bulayi muna walagigi ba tare da mun gano bakin zaren ba,don haka ki adana duk wasu lassafinki akan Sani da waccar gurguwar. Ki fuskanci auren ƴaƴanki da yadda za ki ɗaurasu akan hanyar da za su mallaki mazajen na su a tafukan hannayensu,wannan shi ne kawai mafita ba nuna damuwa da baƙin cikinki a fili ba."


Hajiya Barirah ta ƙare maganar idanunta akan Umma, Umma ta dubi Hajiya Barirah ta ce, "Hajiya Barirah tashi mu je daga ciki mu tattauna da kyau,don gabaki ɗaya kaina a kulle yake bana gane komi."


Daga haka suka rankaya zuwa ɗakin baccin Umma,su Zuhurah na biye da bayansu da ido,kafin Basmah ta saki wani mahaucin tsaki,tana jin zafin maganar ƙarin auren Baba Sani da Boka ya faɗi na taɓa zuciyarta. Ita ko Zuhurah gaba ɗaya baƙin cikin irin mijin da TAIMIYYAH za ta aura , shi ne abinda yafi damunta da ɗaga hankalinta fiye da komi,sabida tunda wani course mate ɗinta ya yi mata bayani akan waye Maleek Ado, da irin tarin arziƙin da ya mallaka da muƙakamin da ya ke riƙe da shi a yanzu,shikenan ta ji duk duniya ta ji babu wanda ya dace da Maleek ɗin irinta. Ta ɗaga ido ta dubi Basmah ta ce, "Basmah yanzu muna ji muna gani wannan gurguwar za ta shiga gidan daulan da ya zarce tunaninmu? Wai anya ko Bokayen nan ba wasa da hankalin su Umma suke yi ba kawai,amma ta ya za a ce ba za a iya hana wannan auren ba?"


Basmah ta ja tsaki tana duban cikin idon Zuhurah ta ce, "Zuhurah don Allah mu aje maganar TAIMIYYAH a gefe,don ni ji na ke yi kamar zuciyata za ta kama da wuta,aikin gama ya gama tunda dukkanin Bokayen bakinsu ya zo ɗaya,sun ce aure dole sai an yi babu fashi,kuma an riga an kawo lefen da ya tabbatar mana da cewa da gaske ta riga ta yi mana zarrah,baki ji yadda Yasmeen ke koɗa irin tsaruwan gidan da za a kaita a GRA bane? Zuhurah bamu da abin yi yanzu da ya wuce mu rungumi na mu mazajen ,tunda su ma ba baya bane suna da kuɗinsu daidai su. Ita kuma kishiya kaɗai ta ishe ta, don ba za ta haɗa kanta da dakariyar matarsa ba don Ubanta. Ba dai kwaɗayi ba to mu zuba musu ido shi ma guy ɗin kyawunta ne ya ruɗesa kawai,da zaran ya kwanta da ita shikenan ya gama da ita,don haka ki aje batunta a gefe mu cigaba da shirya yadda za mu ƙawata yinin mu kawai,kinsan Anty Laurat zuwa nan da 4 days za ta iso,so nake kafin ta iso mun gama da komi don na san wajen waccar gurguwar za ta tare."


Zuhurah ta jinjina kai cike da gamsuwa da maganganun da Basmah ta yi ta ce, "Hakane kam,amma dai ba yadda rai yaso ba, a ce wai gurguwa ta zarce mu a samun miji na nunawa sa'a, wannan babbar faɗuwa ce a gare mu wallahi."


Basmah ta sake jan tsaki suka cigaba da tattaunawa akan auren nasu,da kuma shirin yadda za su fuskanci bikin wanda ya rage saura kwanaki goma kacal masu zuwa.


____________


"Babyn Maleek Ado har ya wuce da wuri haka?"


Yasmeen ta yi maganar idanunta akan TAIMIYYAH,wacce ta shigo cikin ɗakin tana me zare Hijab ɗin jikinta. Ta ɗaga manyan idanunta ta sauke akan Yasmeen kafin ta ce, "Wallahi ya wuce Yasmeen,wai sauri ya ke yi zai ga wani mutum a can gidan Hajjah, a she tare suka iso da matarsa wai tana gidan Hajjah ɗin. Ni fa wallahi haka kawai na ke jin tsoron haɗuwar mu da ita,don ban san da wani ido za ta kalle ni ba? Ya sha faɗa min akwai ta da tsananin kishi akansa,ni kuma gashi gurguwace na san za ta tsaneni sosai domin a matsayinsu da irin ratar arziƙin da ke tsakaninmu,gani za ta yi tamkar zubewar aji ne a haɗa ta kishi da gurguwa kamata. Wallahi Yasmeen duk sai in ji jikina ya yi sanyi idan ina tuna hakan,Allah ya sa dai ba gida ɗaya za mu rayu tare ba da bansan yadda zan yi da fargaba ba."


TAIMIYYAH ta kai ƙarshen maganar cikin sanyin murya da raunin xuciya,hakan yasa Yasmeen dubanta da fuskar tausayi ta ce, "Ki kwantar da hankalinki TAIMIYYAH babu komi,babu abinda zai kasance tunda ba tare za ku zauna ba,sannan wannan raina kan naki da ki ke yi bana ƙaunarsa ko kaɗan,don haka kada ki sake ki nunawa kishiya kasawarki ko gazawarki akan mijinku. Sabida kawai kina da wata lalura da Ubangiji ne yaso ganinki a hakan,idan ta gane rauninki ta nan ɓangaren xa ta yaƙe ki ta dinga miki gori. So kada ma ki sake ki dinga nuna cewa nakasanki na damunki tunda dai mijinki na ƙaunarki a hakan, yana kuma ɗokinki da son kasancewa da ke miye matsalarki da kishiya? Ki cire ta aranki ki fuskanci abinda zai ɗaga darajarki a zuciyar Maleek ne. Sannan ki tabbatar masa da cewa nasaka ba kasawa ba ce, wajen bashi dukkanin soyayyah da kulawar da zai dinga mantar da shi cewa ke ɗin me lalurace. Kada ki bari wannan son da yake miki ya tafi a banza, ba tare da ke ma kin yi hoɓɓasa wajen mantar da shi kowa a zuciyarsa idan kuna tare da juna ba."


Yasmeen ta ƙare maganar tana kashewa TAIMIYYAH idanu,hakan yasa TAIMIYYAH sakin murmushi ta ce, "Yasmeen baki da dama fa,ni idan kina waɗannan kalaman kunya ki ke bani ba kaɗan ba. Amma fa gaskiya Maleek yana son a nuna masa so a zahiri,shi irin mazan nan ne masu daraja soyayya da son a nuna musu ko agaban waye.Wallahi idan yana wasu maganganun yanzu har ji na ke yi kamar na narke sabida kunya,amma shi ko a jikinsa zaro kalamansa ya ke yi kai tsaye ba tare da jin wata kunya ba."


TAIMIYYAH ta yi maganar cike da zallar shagwaɓa,zuciyarta na sake hasaso mata wasu tarin kalamai masu nauyi da Maleek ɗin ke faɗi idan suna vid call. Yasmeen ta saki murmushi me faɗi tana cewa, "Hmm! Ai akwai show wallahi a gaba,don ni har na ƙosa in ga yadda zai maida ke wata tantiriya a fagen iya luv,dama ke ma ɗin munafuka ce irin ku ba ƙaramin iya nunawa miji luv ku ka iya ba. Don wannan shagwaɓar kaɗai ta isa ma ta dinga narkar da shi, bare kuma ki buɗe shafukan litattafan da kika adana don gwada masa madarar ƙauna a zahiri,don na san duk wannan shagwaɓar ta munafurci ce, waya sani ma ko duk kin ƙosa a ɗaura ki fara bashi pepe."


Yadda Yasmeen ta kai ƙarshen maganar cike da tsokana da shaƙiyanci ne yasa TAIMIYYAH sake shagwaɓe fuska,kafin ta buɗe baki cike da shagwaɓa ta ce, "Allah ya isa da wannan sharrin da ki ke Yasmeen. Wallahi ni babu ruwana ban tanadi wasu littafan da zan buɗe shafukansu akan ko wani namiji ba,ko kin manta ni ɗin ustaziyaciyace ku ma alarammiya,wacce bata san komi ba sai karatunta,don haka ni ki daina min sharri in ba haka ba zan sanar masa kina min sharri."


Yasmeen ta kwashe da dariya tana duban TAIMIYYAH cikin ido ta ce, "Allahu Akbar! Ustaza Alarammiya Zainab Maleek Ado,dama ai Ustazai kun fi kowa iya tsula tsiya. Kina san masa kira'a ne kina narkar da shi a duniyar da bai taɓa tunanin zai je ba. Za dai mu yi kallo idan an ɗaura, kafin zuwa nan da wata tara mu dawo ɗaukar ɗan Alarammiya TAIMIYYAH da Sheikh Maleek Ado ko?"


Yasmeen ta jefawa TAIMIYYAH tambayar cike da tsokana,hakan yasa TAIMIYYAH yin dariyar da bata shirya ba ta ce, "Kin fi ƙarfina Yasmeen,sai dai in miki fatan shiriya wallahi."


Suka saki dariya a tare daidai kuma lokacin Iyah ta shigo ɗakin, tana sauke manyan idanunta akan TAIMIYYAH ta ce, "Zainabu idon ki kenan? Ba cewa na yi yana tafiya idan kin shigo ki sameni a ɗaki ba,shine ki ka zo nan kuna ta dararraku da wannan lukutar Yarinyar ko?"


TAIMIYYAH ta dubi Iyah tana shagwaɓe fuska ta ce, "Iyah yanzu fa na shigo ban wani jima ba."


Iyah ta taɓe baki ta ce, "To na ji maza mu je ki shanye ki bani kofi na. Yarinya ana miki gata kina botsara ki shiga hankalinki da ni wallahi kin ji na gaya miki,kuma Hajjah ta bugo waya ta ce me gyaran da za ta turo,za ta fara zuwa ne ana saura kwana bakwai biki,so na ke yi kafin ta zo kin gama shanye magungunan sanyin nan dana haɗa miki,da kuma tsumin da Hajiya Rabi ta aiko,mu je ki sha yanzu a kan idona."


Iyah ta ƙare maganar tana yin gaba TAIMIYYAH na biye da bayanta,Yasmeen ta raka su da ido tana dariyar yadda TAIMIYYAH ke ta faman zunɓure baki.


____________


Ana saura kwana bakwai biki aka tafi Bauchi yin jeren Zuhurah. A kuma ranar ne me gyaran jikin da Hajjah ta ɗakko takanas daga Maidugury ta iso don cigaba da gyare Amarya TAIMIYYAH,wacce ta sake wani irin fresh da kyau na ban mamaki,sabida gyaran da ta amsa daga wajen Iyah da aminiyarta Hajiya Rabi.


A ɓangaren Ummie aka sauke Yakurah mai gyaran jikin, mace me fara'a da sanin darajar mutane. Sosai ta fara aikinta na gyare TAIMIYYAH ciki da wajenta,kamar yadda Hajjah ta buƙata,ta kuma biya uban kuɗi domin kwalliya ta biya kuɗin sabulu.


Babu irin gulma da surutun da su Umma ba su yi ba,lokacin da suka ji cewa wai uwar Angon ce da kanta ta turo mai gyaran. Yasmeen da Anty Laurat tare da su Maryam Sunusi, sune kan gaba akan komi na shirye-shiryen yadda yini da Bridal shower ɗin da suka shirya zai kasance. Ba ƙaramin kuɗi suke fatali da shi wajen gudanar da shirye-shiryensu ba, wanda zuwa lokacin da ya rage one week sun kammala komi tsaf!


Ranar Wednesday ne Anty Mardiyyah da wasu daga cikin dangin Mamar TAIMIYYAH suka iso Zaria. Sun samu kyakykyawar tarba daga Iyah,aka sauke su a sasan Ummie wacce ta kammala duk wani shirinta na ganin ta tarbi baƙi yadda ya kamata.


A kuma ranar ne aka gudanar da Bridal shower ɗin TAIMIYYAH, wanda aka gudanar bayan isha'i . Sun cakare sun cake Amarya kuma ta sha kyau na ban mamaki,sabida duk yadda ta zamewa abin ta kuma nuna bata so ko kwalliya ai mata hakan bai samu ba,don ƙwararriyar me kwalliyace tayi mata make-up ɗin. TAIMIYYAH ta yi kyau fiye da yadda alƙalamina zai misaltawa me karatu,duk in da ta gitta sai an kashe mata ruwan flash,su Yasmeen ƙirazan biki su ma sun sha kyau har sun gaji. Sun yi bidirin su iya son ransu ita dai Amarya na daga gefe a kame a zaune waje ɗaya inda aka ƙawata da decoration. Su Zuhurah su Kamu suka yi a can wajen

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login