Showing 177001 words to 180000 words out of 186776 words

Chapter 60 - TAIMIYAH Book Complete Document by Ayshat Dansabo Lemu .txt

15 Dec 2024

6621

ta yi maganar very serious ya sanya ƙirjin Suhailah bugawa,ta yi saurin duban Anty Safiya ta ce, "Don Allah Anty ki bar wannan maganar,wannan ba magani bane fa wani abu ne kawai."


"Wani abu bai da suna ne Suhailah? Wallahi sai mun ga ko mene ne ki ke wa wannan uwar sufan da kika yi wajen ɗauke shi daga kan gadon.don haka tun muna shaida juna ki aje sa kawai mu ga ko miye."


Suhailah ta dubi Anty Rady cikin mummunar tashin hankali, jikinta har ya fara rawar rashin gaskiya. Ta yi magana muryarta na rawa ta ce, "Don Allah Anty Rady ku barni wallahi ba zan iya nunawa ba."


Anty Safiya da jikinta ya gama bata cewa koma miye ba abu me kyau bane shiyasa Suhailah ke ɓoyewa, sai ta dubi Rady ta ce, "Radiya taso ki gani mu danne ta mu amsa tunda ba fin ƙarfin mu za ta yi ba."


Suhailah ganin da gaske su Anty Rady danneta za su yi,sai kawai ta saki ledar layun ƙasa. Anty Safiya tabi ta ɗakko su daga ƙasa cike da zallar tsoro da firgici, ganin layu ne take gani da idanunta ta dubi Anty Rady ta ce, "Radiya gane min ko idanuna ne basa gani daidai,waɗannan layu ne nake gani ko kuwa?"


Anty Safiya ta ƙare maganar tana miƙawa Radiya manyan layun guda biyu. Anty Rady ta amsa tana dubawa cike da firgici ita ma akan fuskarta ta ce, "Da gaske layu ne Safiya ba gizo idanunki ke yi ba,Suhailah a gidan uban wa ki ka samo layu,yaushe ki ka fara bin Bokaye ba mu sani ba?"


Suhailah da zuwa lokacin ta ke zube akan bed tana kuka,ta ɗago idanunta ta sauke akan Rady. Wani irin firgici da tashin hankali na sake danne zuciyarta,muryar ta na rawa ta ce, "Wallahi Anty Rady sharrin shaiɗan ne da kuma zigar Jawahir,amma ni ban taɓa zuwa wajen Boka ba.Na rasa nutsuwata ne Anty sabida zafin kishin da na ke ji akan Maleek. Shi ne ta ziga ni ta ce wannan hanyar ita kaɗai ce mafita da za a tarwatsa auren bayan an ɗaura,don Allah ku rifa min asiri kar ku gayawa Hajjah da Inna Dije,don na san kasheni ne kawai Inna Dije ba za ta yi ba."


Suhailah ta kai ƙarshen maganar tana sake rushewa da wani irin kuka mai cin rai. Dukkanin jikinta rawa yake sabida shiga ruɗu da tashin hankali,ga yunwa da ke sake kwakular hanjinta na sake taimakawa wajen sanya jikinta ɗaukar rawar.


Anty Rady da ranta ya gama ɓaci ta dannawa Suhailah wata uwar ashar! Kafin ta ce, "Suhailah da iliminki na addini akai da komi ki ke kauce hanya, sabida kawai za a miki kishiya? Lallai idan baki farga kin dawo hayyacinki ba kwanan nan za a fara kiranki da suna bazawara. Don ina sahun farko da zan ziga Hajjah ta raba aurenki da Maleek tunda kin ɗakko hanyar zama ibilishiya mushrika. Uban wa ya taɓa gaya miki cewa Boka ya isa ya hana Allah ida nufinsa akan bayinsa?"


Anty Rady ta jefawa Suhailah tambayar cike da tsawa,don ita irin mutanan nan ne masu saurin ɗaukar zafi. Suhailah ta faɗa jikin Anty Safiya wacce mamaki ya daskarar da ita ta saki kuka tana cewa, "Don Allah Anty Rady ki yi haƙuri ba zan sake ba wallahi tun a yanzu na yi nadama,sharrin shaɗain ne da zafin kishi ya kai ni ga biyewa huɗubar Jawahir."


Anty Rady ta ɗaga hannu za ta ɗauke Suhailah da mari,Anty Safiya ta yi saurin tarewa ta ce, "A'a Rady wannan ba shine mafita ba yanzu dai ta tashi ta kintsa ta ci abinci,don da alamu ko karin safe bata yi ba,idan ta gama sai mu yi magana da ita cikin tsanaki."


Anty Rady da ke huci ta gyaɗa kai cike da gamsuwa da maganar da Anty Safiya ta yi ta ce, "Suhailah maza tashi ki kintsa kafin ki sanar da mu wanda ki ka taɓa gani a zuriyar mu yana bin Bokaye don neman biyan buƙatarsa."


Suhailah jiki na rawa tabi umurninsu wajen tashi ta kintsa jikinta,har lokacin amma kuka ta ke yi hawaye sun kasa daina zuba akan fuskarta. A haka ta gama shiryawa ba tare da ta iya yin wata aba wai kwalliya ba,ta dai sanya wani haɗaɗɗan lace mai nauyin kuɗi. Kalar lace ɗin gray ne da akaiwa ado da red and milk colour, sosai kalar lace ɗin da yanayin ɗinkin boubou da akaiwa rigar na zamani ya amshi jikin Suhailah. Ta sanya ɗankunni manya da suka sake fiddo kyawunta.
Anty Rady ce ta miƙa mata kwalli tace ta sanya a idanunta,ta kuma tsaida waɗannan hawayen hakanan. Suhailah ta amshi kwallin ta sanya a idanunta da zuwa lokacin sun kumbura sosai,ta aje kwallin tana tashi daga gaban mirrow ɗin ta nufi kan sofa ta zauna. Jikinta a sanyaye yake da tarin nadama da firgicin halin da za ta shiga idan Hajjah ta ga waɗannan layun,kuma aka ce wai ita Suhailah ce ta amso su don ta binnesu da mugun nufi.Wasu hawayen masu zafi suka sake zubo mata,ta bar su sukai ta zuba ba tare da tayi yinƙurin share su ba.


"Amshi maza ki ci ki shanye ruwan tea ɗin tas! Empty plate da cup kawai na ke son gani."


Anty Safiya ta yi maganar tana miƙawa Suhailah plate ɗin da ke hannunta,me ɗauke da zazzafan Noodles da ta dafo mata. Ta soya mata wainar egg a sama tare haɗa mata ruwan tea me kauri.
Suhailah ta amsa ta aje daga kan sofan,ita kuma Anty Safiya ta aje cup ɗin tea ɗin ta juya zuwa bakin gado ta zauna.


Anty Rady na zaune daga can gefe guda tana kallon Suhailah cike da takaici,don bata ga dalilin da Suhailah za ta tashi hankalinta haka don Maleek zai sake aure ba.Sabida bata ga abinda ta nema ta rasa ba,sannan duk wannan haukan kishin da take yi bama waje ɗaya za ta zauna da kishiyar ba,hasalima ba gari ɗaya za su rayu ba to a wani dalili ne Suhailar za ta damu kanta har haka,har tana ƙoƙarin jefa kanta a halaka?


Ita dai Suhailah da ƙyar take tura Noodles ɗin sabida gaba ɗaya bata cikin nutsuwar zuciya da ta gangar jikinta.Hakanan dai ta dinga turawa tana kora ruwan tea ɗin,sai ga shi ta tada plate ɗin Noodles ɗin baki ɗaya. Ta aje cup ɗin tea ɗin bayan ta shanye tana me yin hamdala,tare da ɗaga ido ta saci duban su Anty Rady da hankalinsu ke kanta,ta maida kan ƙasa tana ji tamkar ƙasa ta tsage ta shige,don su kansu kunyar haɗa ido ta ke yi dasu bare kuma su Hajjah.


Anty Safiya ce ta taso daga bakin gadon ta dawo kusa da Suhailah ta zauna,hannunta riƙe da waɗannan layun biyu ta dubi Suhailah ta ce, "Suhailah kin ga dai daga ni har Rady babu bare a nan,don haka ki ji tsoran Allah ki sanar damu gaskiyar yadda aka yi waɗannan layun suka zo gare ki,kuma wani ƙudiri ku ke dashi akan birne su?"


Anty Safiya ta yi tambayar tana tsare Suhailah da idanunta babu ko kiftawa,Suhailah da kanta ke ƙasa ta sake dankwafar da kanta hawaye na zuba daga idanunta. Takaicin kanta da kanta na sake lulluɓe zuciyarta,ta yi magana cikin muryar kuka ta zayyane musu duk irin huɗubar da Jawahir ta dinga mata akan auren Maleek ɗin,har kawo kuɗin da ta baiwa Jawahir ɗin ta je mata wajen Boka ta amso mata asirin,ta ƙare maganar da cewa, "Wallahi Anty Safiya ba ni ce da kaina na amso su ba,hasalima ban taɓa zuwa wajen kowa neman taimako ba,ita ce ta je ta amso ta kuma sanar da ni yadda za a birne su bayan an ɗaura auren,ku taimake ni ku rufa min asiri kar ku sanar da Hajjah,wallahi ba zan sake ba na tuba na yi nadama wallahi."


Suhailah ta yi maganar tana kuka sosai cike da magiya,amma sam hakan bai sa su Anty Rady jin tausayinta ba,sai ma tsawa da Anty Rady ta daka mata tana tambayarta wacece Jawahir? Suhailah ta dubi Anty Rady jikinta har rawa ya ke yi wajen bata amsa ta ce, "Makwafciyata ce a can Abuja."


"Suhailah wai meyasa ke baki da hankali ne,baki san inda duniya ta sanya gaba ba,baki san illah da sharrin biyewa ƙawaye da ɗaukar huɗubobinsu na sharri ba ko? Uban wa ya gaya miki ƙaunar ki take yi da har za ta ɗauraki a irin wannan layin ke kuma ki hau kai? Ba ƙaunarki ta ke yi ba so ta ke yi ki rasa aurenki don ubanki."


Anty Rady ta yi maganar tana ji tamkar ta taso daga inda take zaune ta kwaɗe Suhailah da mari. Anty Safiya ta amshe maganar da cewa, "Suhailah kina da wauta gaskiya,kuma baki da wayau ne ke a rayuwarki ko kaɗan. Shirme da sakarci kawai ki ka sanya a gaba sai zafin kishinki na banza da wofi,sabida duk zafin kishin mace ba ya hana namiji ƙara aure sai dai idan bai so ba,ko kuma Allah bai zana masa cikin littafin ƙaddararsa ba.Don haka ki dawo cikin hankalinki ki yi gaggawar tuba zuwa ga Mahaliccinki, ki gane cewa ƙarin auren da Maleek ya yi bai yi don ya daina son ki ba. Kuma ba don ba ki haihu bane haka Allah ya rubuta masa cikin littafin ƙaddararsa,sannan ki gane cewa Hajjah ba za ta taɓa goya baya ayi abunda da zai cutar da rayuwarki ba Suhailah,domin Hajjah Uwace a gareki da ta baki dukkan gata,ko kaɗan bata cancanci mummunar butulci daga gare ki ba. Wanda har za a ɗauraki akan layin da za ki iya cutar da gudan jininta,kuma da yake ke ɗin sakaryace da banzan kishi ya rufe idanunki,ki amince ki bi wannan turbar. To ki sani cewa kamar Inna Dije da Hajjah sun ga waɗannan layun,don ni ban amince da nadamar da ki ke cewa kin yi ba,dole su zama shaida don idan wani abu ya faru da tilon ɗan ta ko ƴar mutane ke za a fara tuhuma."


Anty Safiya na kai aya Suhailah ta sake rushewa da matsanancin kuka,ita kuma Anty Rady ta ɗaura da cewa, "Yo in banda abin ta ma ni da nake da kishiyoyi har biyu ta taɓa ji ko ganin koda wasa na ce zan bi hanyar bin Boka ko Malaman tsubbu? Ban taɓa ba kuma bana fata Allah ya nuna min ranar da zan siyar da imani na sabida ɗa Namiji.Ki nutsu Suhailah ki maida lamuranki zuwa ga Allah shi kaɗai! Ki kuma gode ma ni'imar da ya yi miki na samun miji nagari kamar Maleek. Ke ƴar gata ce Suhailah da Ubangiji ya yi miki ni'imomi da dama cikin rayuwarki. Kar ki manta cewa akwai mata da yawa da basu fi ƙarfin ci da sha ba ma a gidajen aurensu,amma a hakan mazajensu ke zuwa su jajibo auren kuma su zauna da kishiyoyin dole, basu da yadda suka iya. Ke kuwa kina cikin daula da gatar uwar mijin da ta raineki da hannunta,ta baki dukkan gata da kulawar da ko iyayenki na raye ba lallai ki samu hakan daga gare su ba. Sannan bata barki a haka ba sai da ta ɗauki tilon ɗanta ƙwaya ɗaya da ta mallaka,ta baki shi a matsayin miji ya kuma amshe ki da hannun bibiyu,tare da baki soyayyarsa da dukkan gata da kulawa. Ya mallaka miki zuciyarsa da yardansa tare da mayar da ke tauraruwa a idon mata ƴan uwanki,domin Maleek bai rage ki ta ko'ina ba har kawo yau da aka ɗaura masa aure, bai nuna gazawa akanki wajen rarrashi da son ganin kin kwantar da hankalinki ba. A she wannan kaɗai bai isa yasa ki danne duk wani zafin kishi ki rungumi ƙaddara ba Suhailah? Kina tunanin Hajjah za ta iya cutar da ke ko cutar da gudan jininta ne? Ki ji tsoron Allah wallahi Suhailah. In kuwa ba haka ba za ki zo kina nadamar da ba za ta anfana miki komi ba sai danasani,domin kishi idan ya yi wa mace yawa babu inda ya ke kaita sai ga halaka,daga ƙarshe idan ta cika matsawa ma da nuna haukar kishin sai dai mijin ya sake ta. Don haka ya rage naki ki shiga hankalinki ki watsar da ƙawanyen banza ki kama mijinki,ko kuma ki cigaba da biyewa ƙawar bariki ta kai ki ta baro.kin yi ilimin addini kin san hukuncin wanda ya mutu yana haɗa Allah da waninsa,don haka ba sai an sake miki dogon wa'azi ba,idan za ki dawo cikin hankalinki ki dawo kawai,kishiya ba kanki farau ba kuma ba za a rufe ƙofa daga kanki ba. Don haka ki rungumi ƙaddaranku ke da shi domin ku zauna lafiya,daga ƙarshe ina miki fatan Ubangiji ya rage miki wannan zafin kishi da wautar da ke damun kwanyarki."


Anty Rady ta kai ƙarshen maganar idanunta a kan Suhailah, wacce ke ta faman kuka maganganun Anty Rady na shiga jikinta, tare da motsa zuciyarta matuƙa,dukkanin jikinta ya yi wani irin sanyi nadama na lulluɓe zuciyarta.


"Yanzu sai ki tashi mu ɗunguma baki ɗaya zuwa gidan Hajjah,don a nuna musu wannan layun kafin a ƙona su tunda Ubangiji da bai kasance me zalintar bayinsa ba, bai baki ikon aiwatar da mummunar ƙudirinku ba, ya jefo mu gidan muka ga abinda ki ke shirin birnewa. Don haka maza ki tashi ki ɗakko mayafi mu wuce,dama ni na tuƙo mu a motar Hajjah don haka sai mu ɗunguma mu koma can,ki zauna a can gidan ma kawai har a ƙare hidimar komi Amarya ta tare a ɗakinta,kafin ki tattara ki bar mata garin baki ɗaya. Saura idan kin koma cam ki cigaba da baiwa ita ƙawar taki fuskar da har za ta sake nufo ki da zancen zuwa wajen Boka. Don Allah ki biye mata kar ki fasa Suhailah,ina me tabbatar miki da cewa sai kin yi biyu babu in dai kin ce ke huɗubar ƙawaye za ki riƙa ɗauka."


Suhailah dai ba baka sai kunni kuka kawai ta ke ta rafsawa,a haka ta tashi ta ɗakko mayafinta suka fito tare da su Anty Rady. Bayan sun ɗaukar mata kaya kala biyu da duk abinda za ta buƙata,sun sanya shi cikin ƙaramar Luggage. A hankali Suhailah ke biye da bayansu suna tako stairs ɗin benan don sauka zuwa ƙasa,hannunta riƙe da wayarta da ke faman vibrate alamun shigowar kira amma ta kasa koda kallon wayar bare ta ga me kiran. Zuciyarta dai na raya mata cewa Jawahir ce ke kira ta ji ko ta birne layun kamar yadda suka rabu za ta birne ɗin,shiyasa ta kasa duban wayar ma bare har ta ɗaga kiran.


Sun sakko downstairs ɗin kenan shi kuma Maleek Ado yana shigowa cikin falon,hannunsa riƙe da babbar rigarsa da ya cire don ba ma'abocin sanya babbar riga bane shi tun fil-azal ɗinsa.


Ya kalli su Anty Safiya lokacin da ya ƙariso cikin falon ya ce, "Sis ki ce ku Hajjah ta turo dannar ƙirjin?"


Ya yi maganar cike da barkwanci idanunsa na kan Suhailah,wacce ta samu gefen hannun kujera ta zauna,sabida ciwan da kanta ke yi me tsanani. Anty Safiya sai ta saki murmushi tana cewa, "Ango ka sha ƙamshi,sai yanzu ku ke dawowa daga wajen Reception ɗin? Ai mu Hajjah ta turo mu danne ƙirjin wannan sakaryar uwargidan taka mai ban haushi, gashi kuma ƙirjin ba zai dannu a nan ba sai mun dangana da gidan Hajjah ba."


Maleek ya saki murmushin da ba kasafai ake gani akan fuskar ba,har lokacin idanunsa na kan Suhailah wacce ta kasa dubansa, ya ɗan taɓe baki kaɗan kafin ya ce, "To fah! Ki ce har yanzu dai babyn tawa ta ƙi ta ji rarrashi, sai ku je can ɗin ai watakila Hajjar tata ta iya mata tunda ni ma dai anƙi aji nawa rarrashin."


Maleek ya kai ƙarshen maganar yana takawa don isa wajen Suhailah,suna kuma gaisawa da Anty Radiya da ke faman jifan Suhailah da harara. Sai kawai su kai gaba abinsu zuwa waje Anty Safiya na sanarwa Suhailah cewa, ta same su a mota idan sun gama da Maleek ɗin,daga haka suka fice daga cikin falon baki ɗaya zuwa waje.......✍🏻












#Ɗansabo ce#
[12/14, 10:14 PM] +234 703 769 7050: Littafin TAIMIYYAH paid book ne,ga duk wanda ta tsincesa a kowani irin group ne,kiji tsoran Allah karki karanta sai kin biya 500 naira only.


Za ku iya min magana ta wannan number ɗin 08167768704, ko kuma ku turo kuɗin ku kai tsaye ta wannan account ɗin 0504192664 aisha ibrahim dansabo GTbank.*


*Sai ku tura shaidan biyanku ta wannan line ɗin 08167768704.*


Masu turo credit za ku turo katin MTN na 500 ta wannan line ɗin 08167768704.




_Ina ƴan kasuwa masu buƙatar a tallata muku hajar ku? Maza ku garzayo da kuɗi ƙalilan a tallata muku kayan siyarwanku sai dai kawai ku ji ana kiran waya don buƙatan sayan kayan ku,ku tuntuɓeni ta layina kamar haka 08167768704._




*69*


Maleek ya ƙarisa wajen da Suhailah ke zaune yana me zama cikin seater ɗin,ya miƙa hannu ya janyota zuwa jikinsa baki ɗaya ya rungumeta. Take wani irin daddaɗan ƙamshi ya bugi hancin Suhailah,wani irin ƙamshi wanda daga ji kasan daga jikin mace aka same shi,hakan yasa zuciyarta bugawa da ƙarfin gaske. Wani irin kibiyar kishi ya soke ta a ƙahon zuci, sai ta fara kici-kicin raba jikinta dana Maleek ɗin amma ta kasa,sabida wani irin riƙo ya yi mata da ba za ta iya ƙwatar kanta ba. Ganin hakan sai ta sanya masa kuka tana jin wani irin haushinsa na lulluɓe zuciyarta, shi ko Maleek sai ya ɗaura kansa bisa kafaɗunta tare da kai bakinsa saitin kunnin Suhailah na dama ya ce, "Please! Wife calm down mana, ki taimakeni ki kwantar min da hankalinki Suhailah. Har cikin zuciyata bana jin daɗin ganinki kina wannan kukan,duk kin bi kin tsangwami kanki kin ɗaga hankalinki,duk sabida na yi aure Suhailah? Wa ya gaya miki don na yi aure wani abu ya ragu a zuciyata game da yadda na ke ƙaunarki? Ban ƙara aure don in sanya ki a damuwa ba Suhailah,kuma ba don na daina son ki da ƙaunarki bane sai don haka ƙaddara ta zana min,dukkaninku ina son ku kuma zan rayu da ku har ƙarshen numfashi,don haka ki kwantar da hankali ki bani goyan baya ne wajen ganin na tabbatar da adalci a tsakaninku kin ji wife?"


Maleek ya yi maganar cikin murya me cike da rarrashi da nuna

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login