Showing 48001 words to 51000 words out of 186776 words

Chapter 17 - TAIMIYAH Book Complete Document by Ayshat Dansabo Lemu .txt

15 Dec 2024

6589

mata a ɗazu ɗin.Ta sauke ajiyan zuciya a hankali,lokacin da kiran ya yanke ba tare da ta ɗaga ba.Sai dai wani kiran ne ke sake shigowa,hakan yasa TAIMIYYAH ta zubama Screen ɗin ido, bata da alamun zata amsa kiran.Saukar muryan Anty Laurat taji cikin kunnuwanta tamkar daga sama,tana faɗin "TAIMIYYAH kiyi picking call ɗinki mana ha'a." TAIMIYYAH ta zunɓuro baki kaɗan cike da shagwaɓanta na sabo take faɗin "Anty ɗazu fa muka gama waya,miye kuma na kira yanzu please!"


"And so what? Na ji min sakarci irin na ƴan fari,wallahi TAIMIYYAH so kike aji kanmu akan wannan Nass ɗin.Dama ɗazu a chart ya kawo min ƙaran kin yanke masa waya alhali shi bai gama jin muryanki ba.Oya pick the call my Friend."
Anty Laurat tayi maganan tana zubawa TAIMIYYAH harara.Gaba ɗaya sai TAIMIYYAH ta sake kwaɓe fuska, ganin yadda duk attension ɗin Zuhurah ya dawo kanta.Ga kuma wayan nata dake cigaba da Blinking alamun kira ne ke ta shigowa yana yankewa,sai kawai tayi receiving call ɗin tana kai wayan kunni.


Da shagwaɓaɓɓiyar muryanta take faɗin "Hello!" Sam ita bata san yadda salonta ke kassara zuciyan Nass ɗin bane.Watakila data rage narke masa murya da shagwaɓa haka,koda yake da alamu ita bata ma san tana yi ba.Tunda yin shagwaɓa sabonta ne kowa ya santa da shi,wasu har cewa suke duk laifin Iya ne ita ce ta ɓata TAIMIYYAN.


Nass daga ɓangarensa ya sake gyara kwanciya bisa lallausar Bed ɗinsa.Har wani lumshe idanu yayi tasirin muryan da shagwaɓar na zagayawa har tsakiyan kwanyansa.Wani irin zazzafar soyayyan TAIMIYYAN yake ji tamkar ana sake kunna zuciyansa da jan hankalinsa zuwa gareta ne,abin har ya fara bashi tsoro don bai taɓa jin son mace kaman yadda ya ke ji akan TAIMIYYAN ba.Duk da cewa ya taɓa soyayya da wata Muneerah suka rabu,amma sam bai ji yadda yake ji irin haka ba sai daya haɗu da TAIMIYYAN, "My luv shi ne sai kin ja aji kafin ki amsa kiran nawa.Allah sarki bawan Allah Nass ina shan wahala da wannan Babyn tawa,ina ga sai nazo gaban Anty Laurat na zubda hawaye,sannan zata sake ƙoƙarin ganin ta kafa gwamnatina a zuciyanki ko Baby?" Cewan Naseer ɗin shi ma cikin shagwaɓe tasa muryan,salon daya wanzar da kyakykyawan murmushi saman fuskan TAIMIYYAN.Ta yi magana cikin ƙasa da muryanta sosai take faɗin "No bama sai hakan ya faru ba,ina yini." ta kai ƙarshen kalamin da gaisar da shi,ya amsa cikin salon barkwancinsa yana kwaikwayon muryanta,hakan ya sake sanya TAIMIYYAH sakin murmushi sosai,har Beauty point ɗinta na lotsawa.
Naseer ya cigaba da janta da hira yana sake mata bayanin yadda ya ƙagu yai aure,don ya gama kammala gininsa a sabuwar GRA ɗin Zaria yanzu,wata anguwa da ake cewa Gonan Ganye.Tuni har lefe duk ya kammala haɗawa sai abinda ba'a rasa ba,don haka dama shi matar yake jira sai kuma ga TAIMIYYAN Allah ya haɗasu.


Ita dai TAIMIYYAH jinsa kawai take yi tana ganin komi kaman a film.Wai itace yau take waya da saurayi da sunan yana son ta,har yana maganan suyi aure? Saurayin ma kuma ba gurgu irin ta ba.Muryan Nass ɗin ya katse zaren tunaninta lokacin da ya ke faɗin "Baby please allow me to call u Vid Call please!" TAIMIYYAH tayi saurin girgiza kai kaman yana ganinta,kafin ta narke murya tana faɗin "No please! Bani kaɗai bace fa ina cikin mutane ne,kuma ma ni bana jin zan iya Vid Call."
"Meyasa Baby?" Cewan Nass a ƙagauce,amma sai TAIMIYYAH tai shiru bata ce komi ba har sai daya sake nanata tambayansa,kafin ta furta "Bakomi kawai bana ra'ayi ne shiyasa."


"Gaskiya Baby dole ko ki canza wannan ra'ayin indai muna tare.Yanzu to ki amince inzo har gida in sake ganin kyakykyawan face ɗin Baby na please!" Nass yayi maganan cike da magiya,hakan yasa TAIMIYYAN satan kallon Anty Laurat,amma a maimakon idanunta su sauka akan Anty Laurat ɗin,sai idanunta suka sauka akan fuskokin su Zuhurah da Basmah.Waɗanda gaba ɗaya attension ɗinsu ya koma kan TAIMIYYAN baki ɗaya.Abinda yasa TAIMIYYAH tayi saurin ɗauke kanta daga dubansu,tana zagayawa da idanunta ko zata ga Anty Laurat ɗin,amma wayam! Babu ita da alamu ta bar cikin falon,ba tare da ita TAIMIYYAN ta ankara ba.Ganin hakan sai kawai TAIMIYYAH ta miƙe tana dafa ƙafanta ta fara tafiya,tana faɗin "Please kar kace haka,bazan iya fitowa ba koka zo.Sabida na gaya maka ina da baƙuwa,kuma mun jima bamu haɗuba so muna buƙatan time.Gashi ma sai cinye mana lokacin hira ka ke." TAIMIYYAH ta kai ƙarshen maganan cike da narke murya,wanda bata san irin tasirin da muryanta ke yi a zuciyan Nass ɗin ba.


Daga can ɓangaren Nass ɗin sake lafe wayan yayi a kunni yana ji tamkar da bata kai aya ba.Don bai gaji da jin wannan sweet voice ɗin nata ba.
Amma sai ya daure shima cike da salon narke mata murya yake faɗin "To naji Baby amma idan kina so karna zo,don Allah ki yadda in ga face ɗinki ta Vid call please! Hakan kaɗai zai samar da nutsuwa a zuciyata har inji zan iya fasa zuwan,please kar kice no Baby!" Yadda ya kai ƙarshen maganan cike da magiya yasa TAIMIYYAH sauke numfashi a hankali,tana jinjina kalan rigima irin na Nass ɗin da shegen wayansa.Don ta gama gane duk ta inda ta ɓullo masa yasan shima ta yadda zaibi tai masa abinda yake so.
Hakanan ba don tana so ba ta amince ya kira vid call ɗin,tana daga zaune bisa wani table da ke nesa kaɗan da cikin falon.


Tai receiving vid call ɗin tana gyara zaman Hijab ɗin jikinta.Bata wani bari ya jima yana magana ba tai hanging up! Duk kunya na rufeta sabida rashin sabo,su ko su Zuhurah gaba ɗaya sun rasa nutsuwa.Hankalinsu gaba ɗaya na kan TAIMIYYAH duk da cewa ta basu waje,amma hakan baisa hankalinsu ya bar kan TAIMIYYAN ba.Ita Zuhurah tsaban mamakin yadda TAIMIYYAN take wani shagwaɓa da narke murya take yi,wani kishi da haushi na kasheta.Don a ganinta salon daya kamata ace ita ta iyane TAIMIYYAN keyi,amma da yake ita buɗaɗɗen murya take da shi sam muryan nata baya yin irin na TAIMIYYAN.Ita ko Basmah tsabagen takaicin yadda har TAIMIYYAN da take a gurguwanta ta samu saurayi,ita ko babu wanda ya taɓa cewa yana sonta shine takaicin da yasa ta kasa ɗauke idanunta daga kan TAIMIYYAN. Har TAIMIYYAH ta gama amsa call ɗin hankalinsu na kanta, Yasmeen dai na zaune tana kuma ankare da yadda suke bin TAIMIYYAN da kallo.Wani dariya na cinta a rai amma tana dannewa,har TAIMIYYAH ta dawo cikin falon ta zauna mamaki bai daina kashe Zuhurah ba.Zaman TAIMIYYAN keda wuya Anty Zuhurah ta dawo cikin falon,wayane kare a kunninta da alamu tana amsa call ne.


Ta nufi wajen TAIMIYYAH kanta tsaye tana faɗin "TAIMIYYAH ga Amore ɗina zaku gaisa." TAIMIYYAH tw miƙa hannu ta amshi wayan tana kaiwa kunni,cikin sanyin muryarta me cike da nutsuwa take gaida saurayin Anty Laurat ɗin,ya amsa da kulawa yana tambayarta ya Zarian? Ai yana nan zuwa kawo wa gimbiyar tasa ziyara shima yaga gari.TAIMIYYAH dai murmushi tayi kawai tana furta "To shikenan Allah ya kawo ka lafiya." Daga haka ta miƙa ma Laurat ɗin wayan,tana maida duban ta kan Yasmeen da hankalinta a yanzu yake kan chart.Ta furta "Yasmeen mu je ko,na fara jin bacci kinsan halina da saurin bacci gashi har gobe Friday ma sai mun je skull."


Yasmeen ta miƙe tana faɗin "Okey muje ai an gaisa,saura kuma gobe kar in ga ƙeyan ku a Sasan Iya anzo min hira." Yasmeen ta ƙare maganan idanunta akan Zuhurah tana aika mata harara.Zuhurah ta saki murmushi tana faɗin "Haba waneni ai dole ma in shigo,kada ki zauneni da waɗannan ɗuwaiwukan naki.wai ni Yasmeen yaushe kikai wannan ƙiban haka ne?" Zuhurah tayi maganan cike da iskanci,hakan yasa Yasmeen dalla mata harara kafin ta furta "Ban sani ba ƴar rainin wayo,sai kace kema ba ƙiban kika narka ba.TAIMIYYAH ce kawai ta fimu jiki me kyau,ita ba lukuta can ba kuma babu siranta a tare da ita,ko'ina dai a cike da kayan alatu kaman zasuyi magana.Wallahi nafi son irin wannan jikin amma ya zanyi tunda jikin ƙiban aka bani." Yasmeen tayi maganan tana wani watsa hannuwa alamun yata iya ɗinnan....Zuhurah sai baki ya mutu ƙus! Jin an yabi TAIMIYYAH.Ta wani taɓe baki tana faɗin "Sai da safe jeki abinki saina shigo goben,in rigimamiyar tsohuwar can ba ta koroni ba,tace na zo taɓa ƴar gwal."


Tuni TAIMIYYAH ta jima da yin gaba abinta.Tana jiran Yasmeen ɗin daga bakin ƙof,amma tana jin duk abinda suke faɗi.Yasmeen ɗince ta baiwa Zuhuran amsa dai-dai da ita tana faɗin"Eh kam kinsan zata iya kuwa,don yadda take jin TAIMIYYAH a ranta ai ina ga tafi gwal.Sai dai lu'u lu'u,kai gud night ɗinku kunji." Daga haka ta nufo wajen TAIMIYYAH suna jerawa da juna suka fito daga Sasan,suka nufi Sasan Iyah.


Ita Anty Laurat na can suna shan soyayyah da saurayinta ta waya.Sam bata san ma suTAIMIYYAN sun tafi ba,sai bayan sun ɗan jima da fita ne ta fito falon ta ga wayam! Sai ta zauna tana maida hankalinta kan TV itama.Zuhurah ce tai zaraf tana duban Anty Laurat ɗin take faɗin "Anty wai ni kam mutumiyanki babban kamu tayi haka,take zuba wannan uban shagwaɓan da iyayi a waya? Nifa mamaki ya gama kasheni ɗazu da take waya.Wanene shi ko wannan da yake biye mata haka?"


Zuhurah tayi tambayan bil hakki idanunta akan Anty Laurat.Wacce ta saki dariyan rainin hankali, kafin ta dubi Zuhuran cikin ido tana faɗin "Wani Handsome ta samu in gaya miki Daughter.Don ba kiga haɗuwansa ba,komi yaji gashi ɗan gaye da yasan kan miye iya saka sutura a jika.Kuma ba ƙaramin matowa akanta gayen yayi ba,sai kinga yadda yake roƙona da safe akan inje in duba miya hana ta kunna waya.Ai nasha gaya muku ku bar ganinta gurguwa kuna rainata a haka,wallahi TAIMIYYAH matar manya ce.Domin yarinyan ta mallaki Qaulities ma su yawa a tattare da ita."


Anty Laurat takai ƙarshen maganan tana ji kaman ta saki shewa.Ganin yadda annurin kan fuskan su Zuhurah da Basmah ya ɗauke,cikin zallan nuna kishi da hassada Zuhurah ke faɗin "Hmm! Anty amma ke kina ganin ba wani abu ya kawo sa gareta ba?Maza yanzu da suka zama duk ƴan iska.In kin bibiya wallahi kyawunta da dirin jikinta ya janyo hankalinsa kanta,yana gama mata wayo ya amshi abinda yake so zai yi gaba abinsa.Ahaf! Nawa akayi kuma wani Guy ne irin wannan zai wani liƙewa gurguwa musaka,sai dai idan da manufan da ya kawos......"


"Keh! Daughter ki iya bakinki,bana son wannan baƙin halin na ku.Shikenan don tana gurguwa sai akace bazata yi haɗaɗɗen saurayi ba? Ko kuwa ita ɗin ba mutum bace da Allah ba zai kawo mata duk irin namijin da yaso ba?Nakasa aiba kasawa bace kune kuke na ku shirmen.Ki faɗi alkwairy ko kiyi shiru mana haka Annabi yace,amma duk kun bi kun sanyawa baiwar Allah ido kuna hasada da ita.To wallahi ku kula ni kam ba ruwana,don ni bazan biye muku ba ubanku zanci wallahi akanta.Don banga abinda ta tare muku ba,kuka ɗauki karan tsana kuka ɗaura a kant....."


Maganan Anty Laurat ɗin ya katse ne lokacin da Umma ta bayyana a wajen.Fuskanta a haɗe babu rahama take duban Laurat ɗin a fusace tana faɗin "A she ko kema zanci ubanki Laurat.Akan waccar banzar musakan ne zaki tasa min ƴaƴa kina musu irin wannan tijaran,sai ka ce basu ne jininki ba?Uban me kika haɗa da ita musakar da har zaki dinga zaƙewa a kanta? Dama kallonki kawai nake yadda kike wani shige mata sai kace sa'ar ki sabida asara.To ahir ɗinki wallahi ki fita idona ko ki tattara ki koma gida,indai zaki dinga matsa musu akan wata gurguwa can,aikin banza kawai."


Umma ta ƙare maganan a fusace tana yin gaba ta wuce ɗakinta direct.Ranta a masifan ɓace yake da yadda qanwar nata ke son TAIMIYYAH,har tafi damuwa da ita akan su Zuhurah.


Anty Laurat da ke can falo itama ranta ya gama ɓaci sosai.Hakan yasata tashi fuu...! ta bar falon,zuwa ɗakin da ke kusa da nasu Zuhuran.A nan take sauka dama duk idan tazo ,duk da dai ta jima ma bata zo garin ba sai wannan karon.Haka ta zauna daga bakin Bed tana dafe kanta,zuciyanta na tsananin ƙuna da takaicin baƙin hali irin na yayar ta.
Suko su Zuhurah dariya suka sheƙe da shi bayan shigewan Anty Laurat ɗin.Basmah na faɗin "Ke kiji ƙarfin hali gun Anty dai,ta wani zaƙe sai zuba take akan wata musaka.Waya sani ma ko ita ke cusa kan nata wajen Guy ɗin,shi kuma yana biye mata don yaji daɗin kwasan banza yaga Body.Ni inyi saurayin mana Yah Zuhurah." Basmah ta ƙare maganan suna sake bushewa da dariya,Zuhurah na faɗin "Hmm! Ai zamu zuba ido mu ga waye Guy ɗin,badai yanzu ga Yasmeen tazo ba kwantar da kai zamu yi,mu riƙa zuwa Sasan da sunan hira daga nan zamu gano komi ai,har ma muci nasaran ganinsa idan ya zo."


"Very gud idea,Yah Zuhurah hakan ko za'ayi wallahi." Cewan Basmah daga haka suka mai da kai akan wayoyinsu kowacce na chart da friends ɗinta na online.....✍🏻






Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/FAuxFVUMsQhHYfF5qiGklY




Littafin TAIMIYYAH paid book ne da zai zo akan 500 naira only,ga masu buƙatan yin payment zakui min magana ta wannan number ɗin 08167768704, ko kuma ku turo kuɗin ku kai tsaye ta wannan account ɗin 0504192664 aisha ibrahim dansabo GTbank.*


*Sai ku tura shaidan biyanku ta wannan line ɗin 08167768704.*




_Masu account da Arewa books,zaku dinga siyan sabbin shafuka dalla-dalla akan farashi me sauƙi,ga yadda zaku siya pages a arewa books kamar haka_ 👇🏻


https://arewabooks.com/chapter?id=62d29e11aa5f8f19bc9621cb


*DANNA LINK DIN NAN KASHA KARATU👆🏽👆🏽👆🏽*


*_YADDA ZAKA SIYA LITTAFI A AREWABOOKS_*👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾


*Recharge* - inda ake shiga domin saka kudi cikin account.


*Balance* - Zai nuna kudin account dinku da zaku iya sayayyan littafai cikin kasuwar ArewaBooks.


*Credit/Debit Card* - Hanyar farko kuma mai dadi wajan Recharge din account dinku.


A inda (Enter your amount) za'a saka kudin da akeson Recharge din sai a taba "Proceed". Zaibude muku inda zaku saka bayanan katin banki, kuna gamawa kudinku zaishiga account dinku kaitsaye (instant).


--------


Akwai wasu hanyoyin saka kudi a ArewaBooks account kamar:


*Bank Transfer*
*Airtime Transfer*


Saidai su ba kaitsaye bane (instantly) sai ArewaBooks ta tabbatar da Transfer din, amman bayakai 1hour za'a gansa a Balance.




#Ɗansabo ce#
[12/14, 10:04 PM] +234 703 769 7050: *TAIMIYYAH* ❤️


©️Ayshat Ɗansabo Lemu✍🏻


*Page 27*


________________
*Lagos,Nigeria.*
*8:35pm*


Kwance yake bisa kafaren gadonsa da ke cikin haɗaɗɗan Bedroom ɗin,wanda komi na cikinsa kalan White and Blue ne.
Daga gefen bedside na gadon Mug ɗin ruwan Coffee ne na tiriri.Hannunsa riƙe da wayansa da yake faman duba saƙonnin da suka cika inbox ɗinsa ta Gmail,wanda rabin saƙonnin daga friends ɗinsa ne, da ke taya shi murnan wannan sabon muƙami da ya samu,wanda aka rantsar da shi satin da ya wuce a Abuja.


Yana sanye ne cikin fararen Pajamas da suka haska farar fatarsa sosai.
Ya ɗaga kai ya dubi babban agogon da ke manne jikin bangon ɗakin,kafin ya kai hannu ya ɗauki ɗaya wayansa dake aje daga gefensa.
Ya shiga dialing wata number,tsayin seconds ya ɗauka kafin ayi picking call ɗin.Ya fara magana cikin harshen nasara, inda ya ɗauki tsayin a ƙalla mintuna biyar kafin yayi hanging up!Yana maida wayan ya aje inda ya ɗakko.


Sai dai yana ajewa kiran Suhailah ta vid call na shigowa, ta ɗaya wayan nasa.
Ya tsurawa screen ɗin wayan idanu, yana tuna saƙon aminiyarta da ya shigo masa a ɗazu.


Kaman bazai ɗaga kiran ba sai kuma ya ɗaga.Idanunsa ya zuba mata,lokacin da fuskanta ya bayyana a allon screen ɗin wayansa.Ya wani lumshe ido yana amsa gaisuwan da take masa, kafin ta ɗaura da faɗin "My Maleek wai yaushe zaka dawo ne? Kace 2 weeks kawai za ka yi gashi yau har kwananka 15.Please dear come back i miss u so very much." Suhailah tai maganan tana faman narke masa.Hakan yasa Maleek tsura mata ido,kafin ya ɗan ɓata fuska yana faɗin "U miss me, but idan na dawo banda ciwan kai me kike bani Suhailah? Any way tomorrow tunda Friday ne, insha Allah ina bisa hanya." Ya ƙare maganan yana kallon yadda murmushi ya bayyana a face ɗinta.Cike kuma da shagwaɓa take sanar masa,da yadda tai missing nasa.
Daga ƙarshe tai masa albishir ɗin dawowa ya samu babban tarba daga gareta.


Lokacin da suka gama wayan,gyara kwanciya Maleek yayi yana me lumshe idanunsa.Zuciyansa na sake tuno masa da saƙon da Zuby ta turo masa,sai ya buɗe idanunsa yana janyo wayansa ya sake shiga ɓangaren adana saƙonnin.Ya buɗo saƙon yana sake bitan karanta shi, kaman me son haddace dukkanin kalaman dake rubuce cikin saƙon.


Wani irin takaici da mamakin halin sakarci irin na Suhailah,na sake kama shi.Ko kaɗan yasan ita Suhailah ba za ta taɓa tunanin cewa,wannan qawar nata za ta iya shirya mata dukkanin abinda ta rubuto masa ba.Sabida gaba ɗaya daga yadda ya karanta saƙon,da irin kalaman da Zubyn tayi anfani da su,ya fahimci kome Suhailah ke yi da goyan bayan wannan qawartata take yi.
Ba tare da ƙaramin kwanyanta ya fahimtar da ita cewa wauta take aikawata ba.
Ya lumshe idanunsa a karon farko zuciyansa na kisima masa wasu tarin lamura masu girma da za su iya biyo baya.


Mafarkinsa na jiya ya shiga kutsowa cikin kwanyansa,kaman a lokacin ya farka daga mafarkin da yayin.
Idanun yarinyar masu wani irin haske na sake gilmawa ta cikin idanunsa.Kamar yadda sautin kukan da take yi cikin mafarkin, ke dawo masa tamkar a yanzu ne yake jiyo sautin kukan.
Ya sake maida idanunsa ya lumshe kansa na sake kullewa.Da yadda duk mafarkin da ya ke yi da yarinyar cikin baccinsa,bai taɓa ganin zahirin fuskanta ba.
Ya rasa meyasa a duk sanda yai mafarkin ya kan jima mafarkin bai bar zuciyansa ba.Abin har ya fara zama sabo a gareshi,don baya kwana biyu baiyi mafarkin wannan yarinyar ba.Ko yace aljana! Don bai taɓa ganin fuskanta ba sai idanu kawai.
Wani lokacin yakan ga tana miƙo masa hannuwanta,tana kuka.
Amma ba ya ganin fuskanta da gangar jikinta.Abinda yasa yafi yardarwa kansa cewa aljana ce! Kila ba dai mutum ba.Gashi kuma ya kasa gayawa kowa yawan mafarkin da ya ke yi da yarinyar.Sai Hajjah kawai da ya taɓa mata zancen a kwanakin baya.


Ganin zai matsawa kansa da tunani,yasa ya tashi ya nufi mamakeken toilet ɗinsa.Bai jima a ciki ba ya fito yana komawa ya zauna akan Sofa,yana ɗaura ƙafa ɗaya kan ɗaya ya kunna TV don kallon labarai.


______________


*Zaria.*

Yau da yake ranan ya kasance

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login