Showing 132001 words to 135000 words out of 186776 words

Chapter 45 - TAIMIYAH Book Complete Document by Ayshat Dansabo Lemu .txt

15 Dec 2024

6580

Iyah tayi,Iyah ta sanya Babah Ladi ta kawo masa lemu amma sai ya miƙe yana cewa tafiya zai yi.


Hakan yasa Iyah yi masa fatan alkhairy,ya isa wajen da take zaune ya aje mata kuɗi masu yawa,duk kuma yadda Iyah tayi da shi akan ya ɗauke kuɗinsa ƙi yayi.
Hakanan Iyah tayi masa godia da sanya albarka,suka fice Zuhurah na biye da bayansa kamar jela.


Suna fita TAIMIYYAH ta miƙe tayi shigewarta ɗaki,don bata ma so Iyah ta ɗakko wani zance akan Ameerun, wanda ita kallon farko da tayi masa sam bai kwanta mata ba.Bata kuma hango dacewarsa da ƴar uwar nata ba sam,amma sai tayi musu fatan alkhairy cikin zuciyarta,tare da addu'an Allah yayi mata zaɓi itama mafi alkhairy cikin nata rayuwar.


Har suka zauna cin abincin dare TAIMIYYAH taƙi tanka Iyah akan zancen Ameeru,wanda Iyah ke ta faman mitan ita dai yaron yai mata kama da irin mazannan marasa kamun kai.TAIMIYYAH sai tayi murmushi kawai tana cewa Iyah, "Ke dai Iyah kiyi fatan alkhairy kawai tunda dai an riga an sanya lokaci,kuma ita shi ta ga yayi mata,shi take so kin ga kenan koma ya yake tana son kayanta."


"Hakane kuma Zainabu,miye nawa a ciki yaran da basa ganin ƙimarka da darajarka a matsayin wacce ta kawo ubansu duniya,ai sai suyi tayi Allah bada sa a ya sanya alkhairy."


TAIMIYYAH tayi saurin amsawa da, "Ameen." Tana ɗaurawa da faɗin, "Iyah ya maganar xuwa gidan Mamar Gonan Ganyen?"


Iyah tayi saurin duban TAIMIYYAH tana cewa, "Oh! Ni Iyah wallahi kaman kinsan abinda nake ta tunani a raina kenan,ina ga za mu zuwa sati me xuwa Insha Allah,so nake yi ki ɗan yi ko irin cake ɗinnan na ƴan takaddu da Doughnut ɗinnan me laushi sai akai mata ko baƙi ta dinga ba."


TAIMIYYAH ta jinjina kai tace, "To shikenan Iyah Allah shi kaimu lafiya,sai ayi mata ai tunda weekend ne za mu Insha Allah."


Daga haka suka cigaba da hira da Iyah,har sai da agogo ya buga ƙarfe tara sannan TAIMIYYAH tayi wa Iyah sai da safe,ta shige zuwa ɗakinta.


Bata kwanta ba sai da ta gama karanta sabon novel ɗin da ta siya me suna NAHUCE,na Sumayyah Abdulƙadir Takory, (Gwanata kenan a kaf marubuta littafan Hausa,Allah ya ƙara ɗaukaka Anty Takory).


Bayan ta kammala ne ta miƙe ta ɗauro alwala ta zo ta kwanta,tana jin wani irin shauƙi na kewaye zuciyarta,bata jima da kwanciya ba bacci ya saceta ba tare da ɓata lokaci ba.


___________


*GRA,Zaria.*
*09:48am*


Maleek Ado ne zaune cikin falonsa na ƙasa yana karin kumallon safe,wanda Hajjah ce ta shiryo abincin Shehu ya kawo masa.


Yana cin abincin ne suna vid call da Suhailah,wacce ke ta faman narke masa wai bata da lafiya,ta tashi da zazzaɓi ne gashi tace masa bata ma sha magani ba.


"Please wife ya isa haka kukan,ki tashi ki sha magani idan bai yi ba,ki wuce asibiti da driver kin ji ko?"


A.Maleek yayi maganar idanunsa akan face ɗin Suhailah,ta sake zararo hawaye lokacin da ta yaye duvet ɗin da ta rufe jikinta dashi.Take kuma fingilwan rigar da ke jikinta ya bayyana,hakan yasa Maleek sake manna idanunsa bisa allon screen ɗin wayarsa,yana kallon yadda ƙirjinta ya bayyana sosai a waje.Yayi magana cikin low voice yana cewa, "Baby kina son sani a damuwa ne ko? Bayan kinsan a matse na taho nan ɗin,kin yi tsarki ne?"


Suhailah dake duban face ɗin Maleek ta share hawayen da ke zuba,tana gyaɗa masa kai tace, "Yes my Maleek ɗazu na yi wanka,goben za ka dawo ko sai jibin?"


Maleek ya ɗan lumshe idanunsa sabida yadda Suhailah ke son kunna shi,gaba ɗaya ta riga ta san lagonsa babu abinda ke saurin tada sha'awarsa kamar ya ga breast ɗinta a waje.Ya buɗe idanun ya sauke akan inda yake ɗaukar hankalinsa,sannan ya buɗe baki yace, "No sai jibi daga wajen meeting zan ƙariso gida,na sanar miki zamuyi meeting da Minister jibi,please wife ki tashi ki je ki sha magani."


Maleek yayi maganar yana haɗe face yadda Suhailah ba za ta yi masa musu ba,ta kuwa ɓata fuska tana dubansa tace, "Korata kake yi Baby bayan nima nayi missing ɗinka."


"Suhailah kina son in shiga wani hali ne alhali bama kusa bare in rage zafi,please ki je ki sha magani za mu yi waya anjima kaɗan, yanzu nima wanka zan yi akwai baƙin da zan gani kafin na wuce zuwa gidan Hajjah."


Daga haka ya kashe wayar kawai don yasan idan ya biye mata za ta yi ta kunna shi ne kawai,Ya cigaba da cin abincin yana jin kewarta me yawa na lulluɓe zuciyarsa.


Lokacin da ya kammala cin abincin direct sama ya nufa,ya since kayan jikinsa ya wuce zuwa toilet don yin wanka.
Koda ya fito cikin sauri-sauri ya shirya cikin manyan kaya da suka amsa jikinsa,ya feshe jikinsa da tutaren AMOUAGE daddaɗan ƙamshinsa ya cika ɗakin.


Kiran wayarsa da akayi yasa shi isa inda ya zube wayoyin nasa,ya ɗauki wanda kira ya shigo ciki ya kai kunni.
Maganar minti ɗaya yayi ya aje wayer yana nufan wajen wata drawer, ya ciro kuɗaɗe masu yawa ya zura cikin aljihu,sannan ya kwashi wayoyinsa ya fito don sauka zuwa falon ƙasa inda zai gana da mutanen da ke jiransa.


Da wani mutum da zai ba kwangilar kai abinci gidajen marayu ya fara ganawa,ya sallameshi bayan ya turo masa kuɗi ta account.Daga nan ya fara ganawa da mutanen da ke jiransa daga waje,yana sallamansu da kuɗi kamar yadda ya saba,in dai ya shigo gari aka san yazo to shikenan fa bai da sauran sukuni,mutane ƴan maula da masu tarin matsaloli ne za su yi ta zuwa,shi kuma baya gajiya da bayarwa.Shiyasa shi ma tunda Ubangiji ya yi masa arziƙi bai taɓa gajiya da bayarwa ba,kuma Allah bai taɓa nuna masa ranan da za a zo a tsaya masa yace ya rasa abin badawa ba.


Bai samu kansa sai kusan ƙarfe ɗaya na rana,shiyasa bai ma tsaya cewa zai jira yin sallah a masallacin da dake jikin ƙaton gidan nasa ba,ya wuce kawai don zuwa gidan Hajjah.




Kafin ya ƙarisa cikin Gonar Ganye ɗin sai da ya tsaya ya samu jam'i a masallacin dake bakin titin shiga kwanar gidan Hajjah ɗin.
Bayan an idar ne ya ƙarisa zuwa gidan Hajjah yayi horn mai gadi ya buɗe masa gate ya shige.
Sai lokacin da yake tinkaran entrance na shiga cikin gidan,zuciyarsa ta tunasar da shi alqawarin da ya yiwa Hajjah na zuwa ya ga gurguwarta.Wani abu ya taɓa zuciyarsa yana jin gaba ɗaya jikinsa na mutuwa,don tun daren jiya yake neman hanyar da zai iya sillewa Hajjah amma ya rasa,ya riga ya amsa mata zai je ɗin dole ne kuma ya cika wannan alqawarin.


Ya samu Hajjah tare da wasu baƙi biyu lokacin da ya shiga,hakan yasa suna gaisawa da baƙin ya wuce zuwa cikin ɗakin Hajjah.


Akan gadonta ya zauna yana aje wayoyinsa,ya wani lumshe ido yana furzar da iska daga bakinsa,kafin ya ɗauki wayarsa ɗaya ya shiga neman layin Suhailah.


Bugu biyu ta ɗaga wayar ya fara da tambayarta jikinta,yayi ɗan jim kafin yayi magana cikin isarsa da ƙasaita yace, "Alright! Sai ki shirya ku wuce zuwa asibiti,ki yi haƙury Suhailah bana son wannan kukan kina ɗagamin hankali,zan dawo gobe na fasa kaiwa jibin okey."


Ya sake yin jim kafin yace, "Okey sorry zai tafi Insha Allah,ku dai je asibitin in kun isa ki kirani bye Allah ya baki lafiya."


Daga haka ya yi hanging up yana maida idanunsa ya lumshe,dai-dai lokacin da Hajjah ke sanyo kanta cikin ɗakin.Ta sauke idanunta akan Maleek ɗin tana cewa, "Maleek lafiya dai?"


A.Maleek ya buɗe manyan idanunsa ya sauke akan Hajjah,kafin ya ɗan saki murmushi kaɗan yana cewa, "Lafiya lau Hajjah,Suhailah ce ke son dagulamin lissafi zazzaɓi take yi taƙi kuma shan magani sai kuka,kin san halin ciwanta da raki da shagwaɓar tsiya,yanzu nace lallai su wuce asibiti tunda ga driver nan a gidan."


Hajjah ta zauna bakin gado tana cewa, "Subhanallah! Allah ya bata lafiya,ai Suhailah ita ciwanta ban haushi ne da shi,bata son sha magani to ina ko za a samu sauƙi da sauri,gara dai ka matsa mata su je asibitin a duba ta,zazzaɓin ake tayi ko'ina sai dai fatan Allah yaye wahala kawai."


Maleek ya jinjina kai yana cewa, "Hakane Hajjah,karki damu na sanar mata su wuce asibitin yanzu,da zaran sun isa za ta kira ni,akwai fura ne a fridge Hajjah?"


Hajjah ta dubesa tana gyaɗa kai take cewa, "Akwai bata da yawa amma,mu je daga falo sai Lubah ta ɗakko maka,baƙin sun tafi ai."


Suka fito tare da Hajjah zuwa cikin falon nata,ta ciri murya ta kira Lubah tare da bata umurnin ɗakkowa Maleek Furan da bata da rabo da shi cikin fridge.Lubah ta kawo furan ta aje tana kwasan gaisuwa,kafin ta miƙe ta bar wajen tana jinjina halin tilon ɗan Hajiyar,wanda suke gulmarsa akan cewa ya cika miskilanci,sai dai yana da kyauta don suna dafa kuɗaɗe duk idan zai wuce sai ya musu rabon kuɗi.


"Abdul-maleek ina fata kana sane da zancenmu na jiya,ƙarfe nawa ka yanke shawaran za ku je ɗin? Ga dai Shehu driver nan da shi zaku don shi ya kaini gidan,amma kamar yadda na sanar maka bana so ka je da babbar motarka,sabida wasu dalilai don haka a ɗauki ƙaramar motata ta da,wacce ke aje cikin rumfa yanzu sai a sanar da Shehu ya fito da ita ya goge,so nake ka je ka ganta ido na ganin ido ba,ba sai da daddare ba."


Maleek dake sauraren Hajjah ya jinjina kai yana cewa, "To shikenan Hajjah duk yadda kika ce haka za a yi."


Yadda yayi maganar very low yasa Hajjah gane Maleek na cikin damuwa,amma sai ta share ta dubesa tana cewa, "To bari a sanar da Shehun ya fito da motar zuwa la'asar idan kun yi sallah ba sai ku je ba kawai,ko akwai inda zaka ne?"


Maleek yayi saurin girgiwa Hajjah kai ba tare da yayi magana ba,sai ta miƙa hannu ta ɗauki wayarta ta shiga kiran Shehu,don sanar masa ya ciro motar ya goge."


Duk Maleek na zaune yana jin abinda Hajjah ke cewa har ta kammala wayar.Ta dubi Maleek da yayi shiru ba shi da alamun tanka ta,ta murmusa kaɗan tana cewa, "Maleek ka kwantar da hankalinka bafa dole zan maka akan Yariyar ba,cewa nayi kawai ka je ku ga juna,duk abinda ka ji game da ita ka sanar dani,idan tayi maka ka kuma ji a ranka za ka iya zaman aure da ita zan fi kowa farin ciki,idan kuma ba tayi maka ba zan maka dole ba,sabida ina mata son da bazan so ta auri wanda baya son ta ba,ko wanda zai ji a ransa an tirsasa shi ne ya aureta don tana da lalura,don haka ka sanya zuciyarka a inuwa."


Maleek ya dubi Hajjah yana murmushi kaɗan,sabida yadda yake mamakin duk duniya ita kaɗaice wacce take karantar abinda ke zuciyarsa ko bai furta ba.Ya yi magana cikin shagwaɓe murya kamar ƙaramin yaro,yana cewa, "Hajjah cewa nayi hankalina ya tashi dama?"


Hajjah ta zabga masa harara tana cewa, "Bansani ba ɗan rainin hankali." Maleek ya saki murmushi me faɗi a wannan karon,ba tare da yayi magana ba amma.


Kiran Suhailah da ya shigo wayarsa yasa shi ɗagawa cikin sauri,suka jima suna magana kafin ga miƙa wa Hajjah wayar.


Hajjah tayi wa Suhailah ya jiki suka ɗan jima suna magana,sannan Hajjah ta miƙawa Maleek wayarsa.


Bayan ya gama da Suhailah a waya ne aka kawo masa lunch nan tsakiyar falon Hajjah.


Da kansa ya zuba abinda zai ci cikin abinci kala biyun da aka shirya a gabansa.Yana cin abincin ne amma hankalinsa na kan yadda zai je ya ga gurguwar Hajjah.
Zuciyarsa na hasaso masa ko wace irin gurgurwace Hajjah ke nufi? Don bata sanar da shi yanayin yadda TAIMIYYAH take tafiya ba.Shiyasa yake ji duk ya ƙago ya je shi ma ya ga wacece wannan gurguwar data sace zuciyar Hajjah,har take so ta ɓallo masa rigimar da bai san ta yadda zai iya ɗauka ba,don koda yake ma Suhailah zancen ƙarin aure bai yi tunanin Hajjah za ta iya jajibo maganar aure nan kurkusa ba.


Har ya kammala cin abincin ya kasa samun nutsuwar zuciyarsa,shiyasa abincin ma bai wani iya ci da yawa ba.


Hajjah dake zaune duk tana kula da yanayinsa, sai tayi murmushi kawai tana dubansa cikin ido tace, "Maleek yanzu har ka ƙoshi kenan ka ke nufi?"


Maleek ya shagwaɓe face tare da tsukesa yana cewa, "Na ƙoshi Hajjah kin san yau banyi karin safe da wuri bane,amma anjima ina so amin farfesun Kifi asa yaji sosai da garlic."


Hajjah ta jinjina kai tana cewa, "To Allah ya kaimu anjiman za a yi."


Daga haka sai Hajjah ta kamo wani zancen me muhimmanci suka shiga tattaunawa akai.
Basu tashi daga cikin falon ba sai da akai kiran sallar la'asar,sannan Maleek ya tashi ya fice don gangarawa zuwa wani ƙaramin masallaci,wanda ke gaba kaɗan da gidan Hajjah.


Ita kuma Hajjah ta shige ciki don gabatar da sallar itama,zuciyarta cike da addu'an Allah ya jefa son TAIMIYYAH a zuciyar Maleek ɗin.


Lokacin da Maleek ya dawo masallaci sai ya sanar da Hajjah cewa zasu wuce,zuwa gidansu gurguwanta.Hajjah ta jefa masa harara tana cewa, "Kul! Na sake jin kalmar gurguwar nan,sunanta Zainab TAIMIYYAH sai ka zaɓi na faɗi aciki ba ka kirata gurguwaba."


Maleek ya taɓe baki yana cewa, "Hajjah wai yaushe kika fara son wannan Yarinyar har haka ne?"


Hajjah ta sake manna masa harara tana cewa, "Babu ruwanka da wannan kai dai kawai ku je Allah haɗa zukatanku ni shine fata na."


Maleek ya juya ya fice daga falon Hajjah,yana jin zuciyarsa na wani irin dokawa da addu'an da Hajjah tayi daga ƙarshe..........✍🏻
















#Ɗansabo ce#
[12/14, 10:12 PM] +234 703 769 7050: Littafin TAIMIYYAH paid book ne,ga duk wanda ta tsincesa a kowani irin group ne,kiji tsoran Allah karki karanta sai kin biya 500 naira only.


Za ku iya min magana ta wannan number ɗin 08167768704, ko kuma ku turo kuɗin ku kai tsaye ta wannan account ɗin 0504192664 aisha ibrahim dansabo GTbank.*


*Sai ku tura shaidan biyanku ta wannan line ɗin 08167768704.*


Masu turo credit za ku turo katin MTN na 500 ta wannan line ɗin 08167768704.




_Ina ƴan kasuwa masu buƙatar a tallata muku hajar ku? Maza ku garzayo da kuɗi ƙalilan a tallata muku kayan siyarwanku sai dai kawai ku ji ana kiran waya don buƙatan sayan kayan ku,ku tuntuɓeni ta layina kamar haka 08167768704._




*55*


Lokacin da Maleek ya fita har Shehu ya gyara parking cikin tsohuwar motar Hajjah na da,wata baƙar Vibe wacce har yanzu da kyanta ba wai tayi wani abu bane.


Shehu ya buɗe masa back seat yana masa barka da fitowa,Maleek ya shiga ya zauna yana amsa Shehu a taƙaice.


Shehu ya rufewa Maleek murfin motar tare da zagayawa ya buɗe driver seat ya shiga,ya tada motar suka nufi wajen gate.
Bilya ya buɗe musu gate ɗin yana musu fatan dawowa lafiya,zuciyarsa cike da mamakin yau kuma ubangidan na su ƙaramar mota yake jin hawa.


"Shehu Gyallesu muka nufa,gidan wannan Yarinyar da Hajjah tace kun kaɗeta da mota kwanakin baya."


A.Maleek ya yi maganan lokacin da suka hau kan kwalta,Shehu ya jinjina kai cike da nuna gamsuwa yace, "An gama ranka-ya-daɗe Hajiya ta sanar dani."


Daga haka motar ya ɗauki shiru kafin kiran Suhailah ya shigo wayar Maleek,yayi receiving call ɗin yana jingina da jikin seat ɗin sosai don ya ji daɗin amsa wayar.


Sun jima suna magana kafin ya yi hanging up yana maida wayar ya aje gefe guda.
Motar ya sake ɗaukan shiru zuciyar Maleek cike da tunanin yadda zai yi ido huɗu da gurguwar Hajjah,ya ɗan saki murmushi kaɗan,lokacin da ya tuna yadda Hajjah ta harare shi don ya kira Yarinyar da suna gurguwa.


Har suka iso Gyallesu suka ratso kwanar shiga layin gidan su TAIMIYYAH,Maleek na amsa call ɗin wani abokin aikinsa ne.Hakan yasa Shehu faka motar daga gaban gate ɗin gidan kaɗan,ya kashe yana jiran Maleek ɗin ya kammala amsa wayar ya ji yadda za a yi.


"Shehu fita ka sanar da mai gadin ya je ya yi mana sallama da Yarinyar, a ce tana da baƙo a waje,sunanta Zainab in ji Hajjah."


Maleek yayi maganar lokacin da ya sauke wayar daga kunni,Shehu ya amsa da faɗin, "To ranka-ya-daɗe." Daga haka ya buɗe motar ya fice yana nufan ƙofar gate ɗin gidan direct.


Bayan sun gaisa da Tukur ne ya sanar masa yana so ne ya yi musu sallama da Zainab,Tukur ya amsa yana nufan sasan Hajjah don isar da saƙo.


Shehu sai ya samu waje ya zauna kan dogon bencin da Tukur ke zama daga bakin gate ɗin,yana jira Tukur ya dawo ya ji me zai je ya cewa ubangidansa Maleek da ke mota yana jira.


Daga cikin sasan Iyah kuwa,lokacin da Tukur ya yi sallama suna zaune tare da TAIMIYYAH ne cikin falon Iyan,tana ma Iyah kitso suna hiransu gunin ban sha'awa.
Sallamar Tukur ɗin ya sanya Hajjah amsawa tana tambayarsa abinda ya ke so?Tukur ya buɗe baki daga waje yana cewa, "Ranki-ya-daɗe baƙo ne aka yi yace a yo masa sallama da Zainab,yana daga can waje."


Hajjah tace, "Baƙo kuma da yamman nan Tukur?To badamuwa abinda za a yi, je ka maza sasan Samha ka ce mata na ce a buɗe falon marigayi ta waje,sai ka kai baƙon ya shiga ya zauna ga Zainab ɗinnan fitowa."


Tukur ya amsawa Iyah yana juyawa don zuwa ya sanar da Ummie saƙon Iyah,kafin ya koma ya sanar da Shehu yadda ake ciki.


Lokacin da Shehu ya sanar da Maleek cewa ya shiga daga ciki,sai da ya yi ɗan jim yana ɓata fuska,kafin ya zuru ƙafafunsa zuwa waje ya fito daga cikin motar.Cikin takunsa me cike da aji yake takawa zuwa cikin gate ɗin gidan,suka gaisa da Tukur a taƙaice,sannan Tukur ɗin ya yi masa jagora zuwa falon Alhaji Sameer marigayi.
Falon kullum a gyare yake tsaf tunda Ummie ta dawo, kullum ake sharewa a gyara shiyasa yake fes da shi,sai tashin qamshin turaren da ake sawa ɗakin kullum ke tashi.


Maleek ya samu kujeran 2 seater ya zauna,yana ƙarewa falon kallo tare da jinjina tsaftan masu gidan,don ƙamshi da ƙyallin da ko'ina ke yi, zai tabbatarwa mutum cewa masu gidan sun san darajar tsafta.


Daga can sasan Iyah kuwa TAIMIYYAH ce kewa Iyah ƙorafi tana cewa, "Iyah yanzu daga cewa ga baƙo sai ki ce a kaisa falon Abie,meyasa ba za a ce ya zauna a waje kamar ko yaushe ba?"


Iyah ta fige kanta daga kitsa goran ƙarshe da TAIMIYYAH ke yi,ta aika mata wani kallo tana cewa, "Haka na ga ya dace kuma ina da dalilina na cewa ya je can,kiyi maza ki tashi

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login