Showing 114001 words to 117000 words out of 186776 words

Chapter 39 - TAIMIYAH Book Complete Document by Ayshat Dansabo Lemu .txt

15 Dec 2024

6605

tama kasa kuka,sai idanunta da ta lumshe tana jin wani azaba na ratsa hannunta da ta durƙushe akansa.Sama-sama take jin maganganun wanda ya kaɗetan da muryar wata mata da ke faman salati tana cewa, "Shehu maza ku ɗauke ta zuwa mota wannan jinin da take zubarwa yayi yawa."


Babu ɓata lokaci Shehun ya kwashi TAIMIYYAH zuwa mota,wacce jikinta ke faman rawan ɗari sabida ruwa ake sheƙawa har lokacin.Dama ga shi ita ba mai son ruwa ya taɓa lafiyar jikinta bace, shiyasa kafin kace kwabo haƙoranta har sun fara karo da juna,ga jinin da yaƙi tsayawa wanda ke zubowa daga gefen wuyarta da ya tsage sosai.


Hajiya Aysha da ke riƙe da ita a jikinta salati kawai take yi tana ƙarawa, cikin tsantsar tashin hankalin wannan tsautsayi daya gitta musu.Shehu ne ya miƙo jakar TAIMIYYAH daya ɗakko daga bakin kwalbatin ya aje kusa da Hajiyan,ya zagaya ya koma mazaunin driver ya tashi motar yana tambayar Hajiyar wani asibiti za su nufa? Hajiya Aysha dake riƙe da TAIMIYYAH wacce Hajiyar ta sanya ɗankwalin kan TAIMIYYAH ta ɗaure wajen da jinin ke zubowa tayi saurin cewa Shehu, "Muje ABU tudun wada kawai Shehu don gara a kaita asibitin da za a duba ta da kyau."


Tana maganan ne cike da tashin hankali musamman yadda taji jikin TAIMIYYAN ya fara ɗaukan zafi.Har lokacin jikinta rawar sanyi take yi, haƙoranta na faman dukan juna,suna isa asibitin Shehu yai farking motar lokacin ruwan ya ɗan tsagaita babu laifi.


Cikin ƙanƙanin lokaci aka zo aka ɗauki TAIMIYYAH don ta kasa tafiya sabida yadda jikinta ke faman rawa,sai a lokacin kuma Hajiya Aysha ta kula da cewa tana lalurar ƙafa ma.Hakan yasa tausayin halin da yarinyar ke ciki ya ninku a zuciyarta,bata samu nutsuwa ba sai da aka baiwa TAIMIYYAH gado tare da bata kulawar gaggawa don tsaida jinin dake zuba har lokacin........✍🏻












#Ɗansabo ce#
[12/14, 10:11 PM] +234 703 769 7050: Littafin TAIMIYYAH paid book ne,ga duk wanda ta tsincesa a kowani irin group ne,kiji tsoran Allah karki karanta sai kin biya 500 naira only.


Za ku iya min magana ta wannan number ɗin 08167768704, ko kuma ku turo kuɗin ku kai tsaye ta wannan account ɗin 0504192664 aisha ibrahim dansabo GTbank.*


*Sai ku tura shaidan biyanku ta wannan line ɗin 08167768704.*


Masu turo credit za ku turo katin MTN na 500 ta wannan line ɗin 08167768704.




_Ina ƴan kasuwa masu buƙatar a tallata muku hajar ku? Maza ku garzayo da kuɗi ƙalilan a tallata muku kayan siyarwanku sai dai kawai ku ji ana kiran waya don buƙatan sayan kayan ku,ku tuntuɓeni ta layina kamar haka 08167768704._


*48*


Lokacin da Likitan ya kammala baiwa TAIMIYYAH duk wata kulawa da ta dace,sai ya yi mata ɗinki a wajen daya tsage daga gefen wuyarta na hagu inda jinin ke zuba,sannan ya yi mata allura tare da ɗaura mata drip.


Yana juya ya yiwa Hajiya Aysha bayani akan dole admiting ɗin patient ɗinta za a yi ta samu kaman kwana ɗaya da yini, sabida buguwan da tayi a hannunta na dama,da kuma ciwan kai da take kuka da shi.


Hajiya Aysha sai ta gyaɗa masa kai cike da gamsuwa tana faɗin, "Okey! Babu damuwa." Tayi maganar lokacin da take ƙarisawa bakin gadon da TAIMIYYAH ke kwance, idanunta a lumshe amma hawayene ke zubowa daga idanunta yaba sauka a kan kyakykyawar face ɗinta.


Sai lokacin ne ta samu daman kuka dukkanin inda ta bugu na mata tsananin ciwo,ga kanta da take ji tamkar xai rabe gida biyu ne.


Muryar Hajiya Aysha da ta jiyo daf da ita yasa ta buɗe idanunta da sukai mata nauyi, ta sauke akan kyakykyawar face ɗin matar da bata san ko wacece ita ba, Hajiyan ta dubi TAIMIYYAH da ta zuba mata ido tace, "Sannu Zainab." Don taji lokacin da TAIMIYYAH ke sanar da likita sunanta.


TAIMIYYAH ta maida idanunta ta lumshe bayan ta amsa sannun can ƙasan maƙoshinta, ta sake buɗe baki a hankali tana cewa, "Don Allah a ɗauki wayata a kira min Iyah."


Hajiya Aysha ta jinjina kai tana cewa, "Nima tunani na kenan,sannu Allah ya baki lafiya kiyi haƙury komi ya farune bisa tsautsayi da ƙaddara ,don tuƙin ganganci ba halayyar Shehu bane da alamu ke ce kika shiga titin cikin ruɗu ba yadda ya dace ba,Allah ma ya auna arziƙi da ba wani mummunar rauni kika ji ba, buguwace kawai inji likitar sai ɗinkin da akai miki a inda kika sami rauni."


Ita dai TAIMIYYAH jin Hajiyar kawai take yi sama-sama don bacci ya fara rinjayar idanunta, sabida alluran da akai mata.Hajiya Aysha ta nufi in ta aje jakan TAIMIYYAH kusa da nata,ta buɗe tana ciro wayarta tai swiping sai ta ga babu lock,hakan yasa ta sauke ajiyar zuciyar tana shiga contact kai tsaye don lalubo sunan Iyah data ji TAIMIYYAH ta ambata.
Cikin sauƙi ta gano sunan ta kuma dannawa layin kira, kasancewarta wayayya da ta saba anfani da manyan waya na zamani.


Bugu biyu muryar Iyah ya shiga kunnuwarta lokacin da take faɗin, "Salamu alaikum! Zainab kina ina ne har kika bari yamma tayi miki a waje?"


Hajiya Aysha tayi saurin cewa, "Barka da yamma Hajiya ba mai wayar bace,wallahi ta haɗu da tsautsayine gamu nan a asibitin ABU da ke Tudun Wada Zaria."


Tana jiyo yadda Iyah ta rafka salati kafin ta furta, "Subhanallahi! Amma dai da sauƙi ko baiwar Allah?"


Hajiya Aysha tayi ma Iyah bayani yadda hankalinta zai kwanta,kafin suyi sallama Iyan na sanar da ita gata nan bisa hanya yanzu Insha Allah.Sai Hajiya Aysha ta sauke wayar daga kunni tana maida shi cikin jakar TAIMIYYAH ta koma bakin gadon tayi tsaye, tana ƙarewa kyakykyawar face ɗin TAIMIYYAH wacce barci yai nasaran ɗaukarta kallo.
Hajia Aysha ta dinga yaba kyawun yarinyar cikin zuciyarta, tare da jin tausayinta me tsanani lokacin da idanunta ya sauka akan ƙafafun TAIMIYYAH,wanda ɗaya ya sirance sai lafiyayyen dake da ƙibarsa.


Ta sauke numfashi tana kai hannu ta gyara mata rigar jikinta da kyau ya rufe ƙafafun sosai, ta isa ta zauna a kujeran da ke ɗakin tana sauke zazzafar numfashi.
Shehu driver ne ya shigo yana tambayar jikin TAIMIYYAH Hajiyar ta bashi tabbacin da sauƙi sosai,tunda buguwace kawai sai ɗinki da akayi a wajen daya tsage.


Shehu ya yi fatan samun sauƙi ga yarinyar yana komawa waje ya zauna cikin mota, kamar yadda Hajiyar ta bashi umurni tare da sanar da shi zasu jira Mamar TAIMIYYAH ta zo kafin su bar asibitin.


Mintuna talatin da biyar sai ga Iyah sun iso asibitin tare da Sani da ya kawo su ita da Babah Ladi.


Iyah ta ɗaga waya ta kira layin TAIMIYYAH sai Hajiya Aysha ta ɗauka, tana sanar da Iyah gata nan fitowa ta taho da su,ta kashe wayar tana fitowa kai tsaye zuwa waje, cikin sa'a sai ta hango Iyah da Babah Ladi daga can nesa su na faman dube-dube.Ta isa wajensu suka sake gaisawa da jajanta abinda ya faru,kafin su ƙarisa zuwa ɗakin da aka kwantar da TAIMIYYAN.


Iyah da Babah Ladi suka isa bakin gadon suna kallon TAIMIYYAH dake kwance,hannunta ɗaure da drip sai bacci take yi sadidan.Iyah ta sauke numfashi tana kai hannu ta taɓa goshin TAIMIYYAH tana cewa, "Sannu Allah ya baki lafiya Zainab." Ta cigaba da cewa "Nifa na ji shirun yayi yawa wallahi,sai na ɗauka cewa ruwan da aka yi yasa ta tsayawa bata koma gidan ba,tunani ma sai ya tafi akan cewa watakila daga gidan ƙawartata ce za a maidota a mota ashe tsautsayi ne ya gitta,Allah ma ya auna arziƙi babu karaya ko mugun buguwa dama gata da lalurar ƙafa dana shiga uku ni Iyah"


Iyah ta ƙare maganan cike da damuwa me tarin yawa,Hajiya Aysha ta sauke numfashi tana cewa, "Wallahi nima inda na godewa Allah kenan da babu wani mugun rauni data ji me ɗaga hankali,sai a godewa Allah buguwa ce kaɗan da tayi a hannu sai kanta da take kukan yana mata ciwo,shima kuma likitan ya bada tabbacin tana samun bacci me tsawo zuwa lokacin da za ta farka za ta samu sauƙi,sai kuma inda akai mata ɗinki da ta zubar da jini sosai amma ɗinkin ma bamai yawa bane bari ki gani."


Hajiyar ta ƙarisa da Iyah wajen gadon tana nuna mata inda akai ɗinkin daga gefen wuyar TAIMIYYAR an rufe da plasta.Iyah ta jinjina kai tana cewa, "To Allah ya bada lafiya ku kuma Ubangiji ya saka muku da alkhairy da kuka kawota asibiti baku gudu kun bar marainiyar Allah a titi ba."


Hajiya Aysha tayi saurin duban Iyah tana cewa, "Haba Hajiya wallahi babu komi hakkine akan mu ai kawo ta asibitin, tunda mune muka kaɗe ta,maganan guduwa kuma ai wannan sai mutanen da basu san darajan ɗan adam ba,amma taya zaka yi sanadiyyan kaɗe mutum kace kuma ka gudu ka barsa babu tsoran Allah,Allah ya yi mana tsari daga aikata hakan."


Iyah da Babah Ladi suka haɗe baki wajen amsawa da, "Ameen." Iyah na ɗaurawa da faɗin, "Duk da haka dai mun gode Hajiya Allah saka miki da mafificin alkhairy."


Hajiya Aysha ta murmusa tana jin zuciyarta na sake kwanciya da waɗannan mutane,kafin ta furta cewa, "Babu komi fa ki bar godia mu ne ya kamata muyi ta bada haƙury Allah ya tsare gaba,sai dai ai mata faɗa ta ringa kula sosai lokacin da za ta shiga titi." Ta cigaba da sanar da su Iyah yadda tsautsayin ya faru.


Iyah ta jinjina kai tana cewa, " Ai matsalar TAIMIYYAH shine ruɗewa da zaran ta ga hadari in dai tana waje ne to shikenan hankalinta zai tashi,sabida bata son dukan ruwan sama ko kaɗan tun tana ƙarama, yana sanya mata zazzaɓi da mura me zafi,shiyasa ina ga duk ta kiɗime har wannan tsautsayin ya faru,kuma dai Allah ma ya aiko da hakan ne amma da tunda ta ga hadarin tayi zamanta gidan ƙawar idan ruwan ya ɗauke ko Sani sai ya je ya ɗakkota."


Iyah ta kai ƙarshen maganar idanunta na kaiwa kan gadon da TAIMIYYAH ke kwance bata ma san me suke ciki ba.


Hajiya Aysha ta jinjina kai tana cewa, "Ai kinsan ance ƙaddara ya rigayi fata,Allah ya riga ya rubuto hakan sai dai fatan Allah ya kiyaye gaba,ina ga ni zamu zo mu wuce zuwa goben da safe Insha Allah zan zo na sake duba jikin nata,nasa Shehu ya biya kuɗin komi babu abinda za a nema Insha Allah,idan ta tashi a sake mata sannu Hajiya."


Hajiya Aysha tayi maganar tana miƙewa tsaye tareda ɗaukan jakanta dake kan kujera,hakan yasa Iyah ita ma tashi tana sake mata godia sosai.


Iyah ta raka Hajiya Aysha har waje sannan sukai sallama da juna, Iyah ta dawo ciki tana jinjina kirki da karamcin matar har cikin zuciyarta.


"Ladi gaskiya matar nan akwaita da kirki na yaba ƙwarai da karamcinta,Allah yasa da alkhairy ya tsare gaba."


Iyah ke wannan maganar lokacin da ta sake isa bakin gadon da TAIMIYYAH ke kwance,Ladi ta furta, "Gaskiya Hajiya nima na ga karamcinta,da wasu ne guduwa zasu yi abinsu musamman da suka ga ruwama ake yi sanda tsautsayin ya faru."


Iyah ta kai hannu tana taɓa jikin TAIMIYYAH don taji ko da zazzaɓi tana cewa, "Hmm! Ke dai bari kawai Allah ne ya duba yadda TAIMIYYAN take ya taimaketa suka dubeta da idon rahama har suka kawota asibiti me inganci kuma."


Daga haka suka cigaba da tattauna abinda ya farun.Sai daf da kiran magriba sannan Iyah tace Babah Ladi ta zauna ita Sani zai maida ita gida ta ɗakko musu abubuwan buƙata ta dawo,sai ita Babah Ladin ta koma Iyah ta kwana da TAIMIYYAH.


Bayan Iyah ta koma gida ne ta ɗaga waya ta sanar da Baba Sani da ke gari tsautsayin da ya faru da TAIMIYYAH,tare da sanar da shi cewa yanzu haka TAIMIYYAN na can asibiti sai zuwa gobe za a sallameta.


Baba Sani ya jinjina lamarin yana faman faɗan cewa a daina barin TAIMIYYAH kwata-kwata tana fita ita ɗaya a motar haya.Sai dai idan za ta dinga ɗaukan drop duk inda za ta adinga kaita ana komawa a ɗakko ta idan shi Sani na da uzuri lokacin,Iyah dai dake sauraransa har ya gama maganar sai cewa tayi, "Kai dai kawai mu doge Allah da abin yazo da sauƙi,amma duk yadda muka kai da kiyayeta bamu kai Ubangijin da ya halicceta ya kuma jarabeta da lalurar ba,ni a kullum bana so ta dinga ji a ranta tana da wani nakasan da zai hanata kai kawo yadda kowa ke yi,tunda dai ba a nannaɗe take ba Allah yasa tana takawa da ƙafafunta da taimakon dafa guiwar da take yi,idan muna nuna mata cewa komi sai an mata zata dinga jin babu daɗi cikin zuciyarta tunda ita me ƙoƙarice da son yin komi da kanta a hakan."


Baba Sani da ke sauraren Iyah daga ɓangarensa sai ya jinjina kai cike da gamsuwa da bayanan Iyan yake cewa, "Hakane kuma Iyah to Allah ya kyauta gaba,bani gida na fita amma da zaran na dawo zuwa bayan sallar Isha zan ɗauki Zuwairah mu taho asibitin."


Daga haka sukai sallama da Iyah bayan ta sanar masa gata ma a gida tazo ɗaukar musu kaya,Babah Ladi ta bari da TAIMIYYAH kafin ta koma asibitin ita.


Cikin sauri-sauri Iyah ta kammala haɗa musu duk abinda za su buƙata waje ɗaya,ta nufi kitchen ta dafa ruwan zafi cikin ƙaton flask ɗinta,sannan ta zuzzuba abinci cikin kuloli ta dama kunun gyaɗa ta haɗa da kayan shayi, duk ta zuba cikin ƙaton kwandon ɗaukar abinci.


Sai bayan sun yi sallar magariba daga ita har Sani sannan Sanin ya shigo ya kawashi kayan zuwa mota,Iyah ta fito ta kullo sasan ta nufi sasan Ummi ta sanar mata abinda ke faruwa.Ummie tayi ma Iyah Allah ya sauƙe ita da Inna Larai,kafin Inna Larai ɗin ta tashi tana sanar da Iyah cewa bari ta ɗauko mayafi su koma tare ta dubo jikin TAIMIYYAN,sai su dawo tare da Babah Ladi tunda Iyah ta dage ita zata kwana da TAIMIYYAN.


Lokacin da su Iyah suka isa asibitin har lokacin TAIMIYYAH bata farka ba,a haka Inna Larai ta isa bakin gadon ta dubata tare da yi mata fatan samun sauƙi.
Sun ɗan taɓa zama kaɗan kafin su yiwa Iyah sallama ita da Babah Ladi suna ma TAIMIYYAH fatan samun sauƙi cikin gaggawa,Iyah ta raka su har wajen barandar fita ɗakin sannan ta juyo zuwa ciki.


Ƙarfe takwas da rabi su Baba Sani suka shigo asibitin,Iyah ce ta fita ta zo dasu zuwa ɗakin da aka kwantar da TAIMIYYAH.Har kuma lokacin TAIMIYYAH bata farka ba likitan kuma yace kar a tasheta, abarta ta samu isasshen hutu ta yadda idan ta tashi ciwan kan da take kuka da shi zai tafi.


Umma da Baba Sani suka isa bakin gadon suna duba TAIMIYYAH tare da yi mata fatan samun sauƙi,Umma sai wani yatsina take yi tana kallon Iyah a fakaice tana taɓe baki.
Duk kuma abinda take yi Iyah na kula da ita sarai, tare da jinjina halayyar Umman da sam ba masu kyau bane.
Iyah sai ta maida kai wajen baiwa Baba Sani labarin duk yadda abin ya faru,da karamcin Hajiya Aysha na yadda suka kawo TAIMIYYAH asibiti.
Baba Sani ya ji daɗin shi ma yadda su Hajiya Ayshan suka nuna kulawa, basu gudu a lokacin da abin ya faru sun bar musu marainiyar Allah a titi ba.


Sun ɗan taɓa zama kaɗan kafin su tashi tafiya Iyah ta rakasu bakin ƙofa sukai sallama,ta juyo ta dawo cikin ɗakin tana ɗauke ledojin fruit da gasashshen naman kaza da Baba Sanin ya kawo.


TAIMIYYAH sai wajen tara da rabi na dare ta farka,tana buɗe idanunta ta sauke akan Iyah dake zaune saman dadduma da ta shinfiɗa.Ta yinƙura tana son tashi bakinta na furta wash...!!! Hakan ya jawo hankalin Iyah tayi saurin tashi tana nufowa wajen TAIMIYYAH tana faɗin, "Sannu TAIMIYYAH kin tashi,ina ke miki ciwo yanzu ?"


TAIMIYYAH ta ɗan ɓata fuska cikin sanyin murya take cewa, "Kaina ne Iyah amma yayi sauƙi yanzu hannuna ne ya yi min nauyi."


Iyah ta taimaka mata ta tashi zaune tana jin yadda hannunta ke mata ciwo sosai,Iyah ce ta fita kiran likita ba a jima ba suka shigo tare da likitan ya cire drip ɗin,yana tambayar TAIMIYYAH inda ke mata ciwo ta sanar da shi.
Sai ya juya ya fice daga ɗakin ba a jima ba ya dawo yana sake gwada BP ɗin TAIMIYYAH,ganin komi normal yasa shi juyawa yana ma Iyah bayani akan yadda zata bata magungunan da ke aje daga gefen drawern kusa da gadon da TAIMIYYAH ke kai.


Bayan likitan ya fita ne Iyah ta nufi toilet ta haɗawa TAIMIYYAH ruwan zafi sosai,sannan ta dawo tana riƙe da hannunta zuwa bakin toilet ɗin, sannan ta barta ta shige don ta yo wanka ta gasa jikinta.


Sosai TAIMIYYAH ta gasa jikinta da ruwan zafin tayi wanka tare da ɗauro alwala ta fito,tana jin daɗin jikinta sosai don duk inda ke mata ciwo ya saki,hatta da hannunta da ada yai nauyi yanzu da ta gasa shi da ruwan zafi taji daɗinsa.


Ta tadda har Iyah ta fito mata da kayan baccin da ta ɗakko mata daga gida,riga da wando ne masu kauri sosai sabida ruwan da aka yi yasa garin yayi sanyi sosai.


Sallah TAIMIYYAH ta fara gabatarwa bayan ta sanya kayan baccin,lokacin da ta idar har Iyah ta zuba mata abinci a plate tare da kunun gyaɗan da ta dama don ta san TAIMIYYAH naso.


Da ƙyar da rarrashi sannan TAIMIYYAH taci abincin kaɗan,amma ta sha kunun gyaɗan da ɗan yawa kafin Iyah ta buɗe mata naman kazan da Baba Sani ya kawo musu.
Da yake TAIMIYYAH akwai son naman kaza taci ba laifi sannan Iyah ta kawo mata magungunanta ta sha.


Kiran wayar TAIMIYYAH da aka yi yasa Iyah ɗakko wayar ta kai mata,ganin sunan Yah Deeku yasa TAIMIYYAH ɗauka ta kai kunni.


Cike da shagwaɓa take gaida Yah Deekun, ya yi mata sannu da jiki yana faman faɗa akan meyasa take fita ita kaɗai ba za ta kira Sani ya kaita ba? Ita dai TAIMIYYAH shiru tayi masa bata ce komi ba har ya gama faɗansa ya koma kuma yana tambayarta yadda take jin jikinta.


TAIMIYYAH cike da shagwaɓa take sanar da shi cewa taji sauƙi,sukai sallama yana sake mata fatan samun lafiya sabida yana KD wannan week ɗin bai samu shigowa weekend ba.


Suna gama wayar TAIMIYYAH ta kashe wayarta baki ɗaya ta aje kusa da ita,tana zamewa daga zaune ta kwanta tare da lumshe idanunta.


Sama-sam TAIMIYYAH ke sauraren Iyah dake ta bata labarin kirkin Hajiyar da suka kaɗe ta,tare da sanar ita cewa Hajiyar tace zata dawo gobe ta sake

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login