Showing 147001 words to 150000 words out of 186776 words

Chapter 50 - TAIMIYAH Book Complete Document by Ayshat Dansabo Lemu .txt

15 Dec 2024

6613

credit, ki gaida ƴar uwarki da Mamarku."


Basmah ta miƙa hannu ta amsa kuɗin tayi godia, tana duban Iyah da ke faman doka mata harara ta ce, "Iyah ki taya ni godia."


Iyah sai ta saki murmushin yaƙe, tana takaicin halayyar jikokin nata da suka gada wajen uwarsu,ta dubi Hajjah tana cewa, "Hajiya har da wani ɗawainiyar bata kuɗi,to an gode Allah saka da alkhairy ya ƙara arziƙi."


"Haba Hajiya Fatima miye na godia,ai jikata ce itama inda kara."


Cewar Hajjah lokacin da Basmah ta juya don komawa zuwa sasansu,jikinta har ɓari yake yi don ƙosawa ta isa ta kaiwa su Umma gulma.Iyah su kai sallama da Hajjah ta shiga mota, Shehu ya ja suka nufi gate. Hajjah ta sake zuge bakin jaka ta baiwa Tukur dubu biyu,ya amsa yana ta godia da yaba kirki da mutuncin matar, har suka fice daga gate ɗin gidan.


Iyah ta juya don komawa cikin gida, zuciyarta cike da tunanin wannan abin alkhairy da Hajiya Aysha ta zo musu da shi,don me ƙaunar ka ne zai so haɗa jini da kai,ba tare da ya duba fifikon ɗaukaka da ratan da ke tsakaninka da shi ba,don daga labarin da Hajjah ta basu ta gane cewa sama da ƙasa,su Hajjah sun yi musu rata me tarin yawa,duk da cewa su ma suna cikin sahun masu rufin asiri ne kawai,amma arziƙi na wajen su Hajjah idan har za a duba fifikon da ke tsakani kuwa,za ta iya cewa Maleek ya fi ƙarfin ajin TAIMIYYAH ko ta wani fanni.Sai dai daga labarin da Hajjah ta bayar,na irin mafarkin da ya dinga yi yasa jikin Iyah yin sanyi,har take ji a zuciyarta cewa,addu'a shine kawai abinda lamarin ke buƙata,don ba su san me Ubangiji ya ɓoye ba.Har ta isa cikin sasanta tunane-tunane kawai take yi a cikin zuciyarta.
__________


"Yah Zuhurah! Yah Zuhurah! Kina ina ne?"


Basmah ta dinga ƙwalla kiran sunan Zuhurah,lokacin da ta sanya kanta cikin falon na su,Zuhurah ta fito daga ɗaki tana cewa, "Basmah lafiya wannan kira haka?"


Basmah ta zauna tana kaɗawa Zuhurah sabbin ƴan 500 da ke hannunta tana cewa, "Zuhurah kalli ki ga, wannan Hajiyar da muka gaisar ranar walimar TAIMIYYAH,ita ce ta bani su. Ke kin ga danƙareriyar motar da take hawa kuwa? Hmmm! ni wallahi na rasa inda Iyah ta samo wannan hamshaƙiyar Hajiyar."


Basmah ta yi maganar fuskarta na nuna alhini me tarin yawa,Zuhurah ta zurawa kuɗin ido tana cewa, "Wallahi ni ma na rasa ina ta samo matar,daga gani kin san akwai kuɗi a wajen Hajiyar, ko daga yanayin skin ɗinta zuwa suturar da ta saka a ranar."


Basmah ta gyaɗa kai tana faɗin, "Gaskiya kam matar tayi ga kyauta da fara'a ,amma baki ga yadda Iyah ke faman zabgamin harara ba, daga na je mun gaisa da matar,Allah kaɗai yasan kuɗin da matar ta baiwa ƴar gaban goshin Iyar ai,ke kina ganin ko ranar walimar ƙananun kuɗi ta baiwa TAIMIYYAH? Ai Allah ne kawai ya sani sai su da suka dafa,wallahi Iyah akwai baƙin hali,ba don na fita Allah ya yi zan wafci rabona ba da shikenan,ba za ta taɓa cewa ta shigo sasan mu, ba tunda mune bata ƙauna."


Zuhurah ta kyaɓe baki tana cewa, "To ai ta yi banza tunda mu ma dai gidan arziƙin za mu shiga, duka kwanaki nawa suka rage,sai su yi ta zama ita da gurguwar tata."


Suka saki dariya ita da Basmah,Basmah na miƙewa ta ce, "Bari in je in dawo kin ji,dama gulma ya dawo dani,ga 1k ke ma ki shaida."


Basmah tayi maganar tana miƙawa Zuhurah kuɗin,Zuhurah ta amsa Basmah ta fice don tafiya inda za ta.


Daga can ɓangaren sasan Iyah kuwa,lokacin da ta isa cikin falonta sai ta wuce zuwa ɗakin TAIMIYYAH direct. Ta samu TAIMIYYAH a kwance ta yi zurfi cikin tunani,sai ta zauna daga gefen gadon tana cewa, "Zainab tashi mu yi magana."


TAIMIYYAH ta yinƙura ta tashi zaune, tana duban Iyah fuskarta a narke,Iyah ta dubi TAIMIYYAH tana cewa, "Zainabu kin ji dai da maganar da Hajiya ta zo mana da shi ko? Bana so ki zafafa ko ki hana kanki sukuni da yawan tunani,ki fawwala Allah lamarin mu kuma yi addu'a, don bamu san abinda Allah ke nufi da haɗamu da waɗannan bayin Allah a rana tsaka ba,jikina ya yi sanyi da bayanin da Hajiyar ta yi akan mafarkin da ya ke yi da me irin idanunki,kar ki damu kanki da yawan tunani kamar yadda Hajiyar ta ce, ki saurare shi mu kuma yi addu'a, Allah ya zaɓa mana mafi alkhairy,idan mijinki ne za ki aure shi ko muna so ko bama so,don haka tun daga yau ki dage da addu'a, mun rabu da ita akan cewa zan saka Babanki Sani yayi bincike akan su,duk abinda muka ji zan sanar da ita sai a turo manyansa,don nema masa izinin fara zuwa zance wajenki sabida ku fahimci juna,ina fata ko don ƙaunar da ta nuna akan ki,ba za ki guji jininta tilo ɗaya da ta mallaka ba,matuƙar mun same sa da kyawawan halayya,Allah ya duba maraicinki ya yi miki zaɓi mafi alkhairy."


TAIMIYYAH da duk jikinta yake a sanyaye ta amsa da cewa, "Ameen Iyah amma ni tsoro nake ji, ina ganin kamar sun fi ƙarfinmu, kuma kar ki manta yana da mata ,kuma jininsa ce matar Iyah,ni dai gaskiya tsoro nak....."


"Zainabu kar kice za ki ja da yin Allah,ki yi addu'a ne kamar yadda na faɗi,kasancewarsa me mata ba abin damuwa bane, don Allah ya fiki sanin komi amma kuma ya kawo shi cikin rayuwarki,Allah ya fi mu sanin abinda yasa ya ƙaddari silar haɗuwarki da mahaifiyarsa,har sanadi yasa ya gane cewa ke ce yarinyar da ake nuna masa cikin baccinsa,wannan kaɗai ya isa yasa ki nutsu ki barwa Allah ikon sa,mu jira mu ga abinda Allah zai hukunta kinji ko?"


TAIMIYYAH ta dubi Iyah a sanyaye tana me gyaɗa kai, ba tare da tace komi ba. Iyah ta cigaba da yi wa TAIMIYYAH ƙarin bayani, akan labarin Maleek ɗin da Hajjah ta dinga bata, da irin yadda tun ganinsa da TAIMIYYAH ya kasa nutsuwa.Ita dai TAIMIYYAH jin Iyah kawai ta ke yi ,tana kallon komi kamar mafarki ko almara,tunaninta ya hasko mata yadda suka kwashe da shi ɗazu a waya,da yadda har ya fara kiranta da wife ɗinsa, kamar wanda akai wa albishir da cewa an basa ita,wani baƙon yanayi ya doka acikin zuciyarta,idanunta na hasko mata kyakykyawar miskilalliyar fuskar Maleek Ado ɗin,da yadda yake furta kalamansa cike da ƙasaita. Har Iyah ta gama bayananta ta tashi ta fice daga ɗakin,zuciyar TAIMIYYAH bata huta daga tunanin Maleek Ado ba..........✍🏻
















#Ɗansabo ce#
[12/14, 10:13 PM] +234 703 769 7050: Littafin TAIMIYYAH paid book ne,ga duk wanda ta tsincesa a kowani irin group ne,kiji tsoran Allah karki karanta sai kin biya 500 naira only.


Za ku iya min magana ta wannan number ɗin 08167768704, ko kuma ku turo kuɗin ku kai tsaye ta wannan account ɗin 0504192664 aisha ibrahim dansabo GTbank.*


*Sai ku tura shaidan biyanku ta wannan line ɗin 08167768704.*


Masu turo credit za ku turo katin MTN na 500 ta wannan line ɗin 08167768704.




_Ina ƴan kasuwa masu buƙatar a tallata muku hajar ku? Maza ku garzayo da kuɗi ƙalilan a tallata muku kayan siyarwanku sai dai kawai ku ji ana kiran waya don buƙatan sayan kayan ku,ku tuntuɓeni ta layina kamar haka 08167768704._


*59*


Washegari TAIMIYYAH ta dawo daga skull ne kawai,ta tadda danƙareriyar motar Hajiya Aysha fake a cikin compound ɗin gidansu.
A hankali take takowa daga bakin gate ɗin zuwa ciki,sabida gajiyan da tayi a skull ɗin yau,har za ta wuce motar sai ta hangi Shehu daga ciki yana zaune,hakan yasa ta nufi wajen motar suka gaisa,sannan ta wuce zuwa sasan Iyah .


Da sallama ta isa bakin ƙofar shiga falon Iyah,Iyah daga ciki ta amsa sallamar da TAIMIYYAH tayi,hakan yasa TAIMIYYAH kutsa kanta ciki,idanunta suka sauka akan Hajiya Aysha da ke zaune cikin falon,an cika gabanta da kayan cima,don tun jiya da TAIMIYYAH ta sanar da Iyah cewa Hajiyan za ta zo,Iyah ta tashi yau da shirin tarbanta ita da Babah Ladi.


TAIMIYYAH ta isa cikin falon fuskarta na blushing, ta ƙarisa kusa da kujeran da Hajjah ke zaune,ta durƙusa ta kwashi gaisuwa.Hajjah ta amsa gaisuwar cike da kulawa idanunta akan TAIMIYYAH da tayi mata kyau sosai, cikin hijab ɗin jikinta kalar maroon,TAIMIYYAH ta dubi Iyah tana cewa, "IYah ina yini,na dawo".


Iyah ta amsa da cewa, "Lafiya lau, barka da dawowa Zaynab,ai tun ɗazu Hajiya ke tamabayar yaushe za ki dawo,don tace zuwar naki ne sai ki maza ki shiga ciki, ki kintsa ki fito ki ci abinci."


TAIMIYYAH sai ta dubi Iyah da sauri tana cewa, "Tuh Iyah bari in shiga daga ciki, sallah zan yi sai in fito."


Daga haka TAIMIYYAH ta miƙe tana dafa ƙafarta, ta fara takawa don isa zuwa ɗakinta,zuciyarta na cike da mamakin kalaman Iyah na cewa wai Hajiya wajenta ta zo.
Har ta cire hijab ɗin jikinta ta nufi toilet, tunani abinda zai sa Hajiya ta yo takakki zuwa wajenta take yi,haka nan dai ta yi uzurinta ta ɗauro alwala ta fito ta tada sallah.


*20 Minutes Later.*


Hajiya Aysha ce ta fara da baiwa su Iyah labarin cikakken asalinta in da da soma cewa,


" Sunana Ayshatu Aliyu,haifaffiyar jihar Katsina,mahaifina Alhaji Aliyu shine Magajin Garin Katsina a wancan lokacin,mahaifiyar mu Hauwa ita kaɗai ce matar mahaifin mu har suka bar gidan duniya, bai sake wani aure ba kuma mu uku kaɗai suka haifa a duniya,Hadeeza itace Babba,sai ni Ayshatu sai Autar mu Hauwa'u. Na yi karatuna tun daga kan primary har ya zuwa jami'a,na kuma yi aure ina da shekaru sha tara a duniya, lokacin ina shekarar ƙarshe a jami'ar Ahmadu Bello da kenan Zaria,na karanci course ɗin Libarary Science ne.
Mijina marigayi Alhaji Ibrahim Ado haifaffen garin Zaria ne, a wata Unguwa da ake kira Lowcos cikin lardin birnin Zazzau. Mun haɗu da shi ne a cikin jami'ar Ahmadu Bello, watarana ya kawo ziyara cikin makarantar, a matsayinsa na tsohon ɗalibin jami'ar. Ba mu jima da haɗuwa ba soyayyah me ƙarfi ya ƙullo tsakaninmu, har ta kai ga manya sun shiga ciki an sanya mana ranar aure."
Hajjah ta cigaba da cewa,
" A lokacin Ibrahim Ado yana aiki ne da hukumar Custum, inda har ya fara taka matsayi me girma a lokacin,don irin mazannan ne da ke tsayawa su samu ilimi me zurfi kafin su yi aure.Mun haɗu da watanni uku aka yi bikin mu ni da shi,aka ɗakkoni daga Katsina aka kawo ni Zaria,cikin sabon gidan da ya gina a cikin Unguwar Tukur-Tukur.
Cikin shekaru goma da aurenmu na haifi adadin ƴaƴa biyar,amma duk suna mutuwa sai daga ƙarshe Ubangiji ya raya min Abdul-maleek, wanda na haife shi muna da shekaru sha biyu da aure. Hakan yasa ni da mahaifinsa muka ɗauki son duniya muka ɗaura akansa,sai dai hakan bai hana mu ba shi ingantacciyar tarbiya ba. Gata da kulawar da yake samu hatta daga wajen kakarsa wacce ta haifi Ubansa, bai sa ya taso a sangarce ba,sabida jajircewata wajen ganin ya samu tarbiya me kyau. Sam bana nuna masa so a zahiri yadda zai sangarce,yana da shekaru goma muka tattara muka koma Lagos da zama,sabida lokacin mahaifinsa ya kusa zama Asistant Controler na ƙasa. A can Lagos Maleek kamar yadda muke kiransa,ya kammala karatunsa na primary,daga nan ya wuce secondary skull, lokacin ne kuma Autar mu Hauwa ita ma aure ya kawo ta garin Lagos,na yi farin ciki da hakan a lokacin, domin dama ban san kowa a Lagos ba lokacin da muka koma. Cikin ƙanƙanin lokaci Maleek ya yi wani irin sabo da Antynsa Hausa,shaƙuwa ya shiga tsakaninsu sosai,duk idan ya dawo skull zai matsa sai driver ya kaisa gidanta.yana SS 2 ma ya iya driving sosai abinsa, uban kuma ya ɗaure masa gindi ya siya masa sabuwar mota,sai ya zamana da ya dawo skull zai ɗauki mota ya wuce gidan Anty Hauwa. Kominsa ita ce hatta abu idan yana so, sai ya fara sanar mata kafin ni in sani.Bayan ya kammala karatun Secondary ne mahaifinsa ya fita da shi England, a can ya haɗo deegree ɗinsa na farko da na biyu, duk a fannin da ya shafi siyasa wato 'Political Science'


Hajjah ta sake ɗan numfasawa sannan ta cigaba da cewa,
"Ya dawo ƙasar Nigeria ya cidda an baiwa mahaifinsa, muƙamin Assistant Controler na ƙasa baki ɗaya,wanda wannan babban muƙami ya janyowa mahaifinsa tsana a wajen ƴan adawa sosai.
Maleek ya dawo ƙasar bai fi da shekara ɗaya ba,ya fara aiki da Port ɓangaren Shiffing Board aka aje sa, sabida ƙafa da ubansa ke da shi a gwamnati, tunda aiki a manyan gurare irin wannan sai ƴaƴan masu faɗa aji a ƙasar,da waɗanda suke da babban matsayi a siyasar ƙasar, ko suke kusa gwamnati sosai.
Ya fara aiki cikin sa a kuma yana taɓa Businees tun yana England,ya kan turo kayayyakin gina-gine ana sayar masa,lokacin da ya fara aiki bai daina ba, sai ma abin ya ƙara haɓaka ya fara ordern manyan kaya ana shigo masa dasu ta jiragen ruwa, shi kuma yana sararwa ƴan kasuwa masu harkan sayar da kayan gina-gine na zamani.
Maleek miskiline sosai da sam ba yi da son hayaniya,ba yi da yawan magana sosai, sannan yana da isa da ƙasaita tamkar shine jinin sarautar, ba ni mahaifiyarsa da nake matsayin ƴar Magajin garin Katsina ba. Duk da miskilancinsa mutum ne me tsananin tausayin na ƙasa da shi,me yawan kyauta da alkhairy ga mabuƙata, kamar yadda ya ta so ya ga mahaifinsa na yi.Yana da son aba shi girma kuma baya ɗaukar raini tun yana da ƙarancin shekarunsa, tun da ya dawo ya fara aiki burina ya tafi akan son ya yi aure,amma shi sam ba ya ma so na ɗakko zancen,sai ya ce shi aure lokaci ne idan lokacinsa yayi zai yi.
Shekaru biyu da bai wa mahaifinsa muƙamin Assistant Controler,Anty Hauwa ta haifi ƴarta ta farko wacce aka sanyawa suna Suhailah,daga kanta kuma ba ta kuma haihuwa ba sai dai ɓari da tai ta yi akai-akai.
Suhailah na da shekaru biyu,ranar wata juma'ar da ba za mu taɓa mantawa ba, aka kashe mahaifin Maleek,wato Alhaji Ibrahim Ado a garin Lagos da daddare, akan hanyarsa ta dawowa gida,lokacin ya dawo daga duba wani abokin aikinsu da bashi da lafiya,a she makasan na biye da motarsa ba tare da shi ya sani ba,har ya kusa isowa gida suka buɗe masa wuta tare da harbesa har lahira."


Hajjah ta kai hannu ta share hawayen da ya zubo mata,na tuna da mummunan ranar da ba za ta taɓa mantawa da shi, a tarihin rayuwarta ba,ta cigaba da cewa,
"Faɗin irin tashin hankali da giginta da muka shiga ma ɓata baki ne.Mun ɗauki tsayin lokaci kafin mu dangana,har mu cigaba da rayuw ba don zuciyoyinmu, sun daina jin zafi da raɗaɗin rashin mutum irin Alhaji Ibrahim Ado ba.
Kuma wannan shine silar tsanata da garin Lagos,ta yadda ko sunan garin aka kira sai na ji zuciyata ta motsa da ɓacin rai me tsanani.Maleek shi ne ya gina min Sabon gida bayan fitana takaba,na tare a cikinsa a Gonar Ganye,a lokacin ne kuma aka kammala tattara dukiyar da Ibrahim ya bari aka raba mana gado,in da ni da tilon ɗana muka lashe kaf dukiya da kadarorin da marigayin ya tara,sabida lokacin iyayensa sun ɗan jima da rasuwa, a dalilin mummunar gobara da ya tashi a sabon gidan da Ibrahim ɗin ya gina musu, suka bar cikin Family House ɗinsu.Wannan rabon gado shi ya janyo mana wata irin tsana daga danginsa,da ƙanninsa maza biyu da suka ci burin ina ma mace Ibrahim ya haifa,sabida su ma su samu shiga cikin magada,amma sai Allah ya ƙaddara cewa namiji ya bari. Har a yau da na ke muku wannan maganar, dangin uban Maleek basa ƙaunarsa,suna matuƙar nuna adawa da irin arziƙin da ya gada,ga kuma na shi ɗaukakan da kullum cigaba ya ke.
Arziƙi sai dai muce Alhamdulillah! Don ba mu san rashi ba indai na kuɗi ne.Shekaran Ibrahim uku da rasuwa aka sake rafka min wani rashin me asalin ɗaga hankali, Anty Hauwa ƙanwata da muka baro a Lagos itace ta rasu,sanadiyar haɗarin mota za su zo wani biki da za mu yi a Katsina a wancan lokacin, tana cikin mutum na farko da ta fara amsa kiran Ubangiji a cikin motar, ƴar ta Suhailah kaɗai ta rayu a cikin motar, lokacin ta fara tasawa tana da shekaru biyar a duniya.


Mutuwar Hauwa ya gigitamu ni da Maleek fiye da yadda zan misalta.Don shi Maleek sun yi waya da ita a lokacin da motarsu ta taso,take sanar da shi gasu cikin mota sun ma taso,don shi mijinta yace ta bari sai ana gobe bikin su biyo jirgi, amma sai ta nuna tafi son zuwa tun wednesday. Ta matsa masa sai ta taho,sai yayi mata irin gatsennan yace sai dai ta biyo mota,to da yake ajali na kira sai ta amince, shi kuma ganin ta nace ya biya mata kuɗin motar suka kamo hanya.
Mu dai sai gawarta aka isa da shi can Katsina,ƴan uwa da dangi suka shiga cikin mummunan yanayi.Maleek lokacin da muka bar Zaria muka isa Katsina ko magana ba ya yi sai kuka.Don mutuwar ya gigita shi matuƙa barin ma da muka isa, ya tadda yadda Suhailah ke faman kuka kamar tasan uwar ta tafi kenan har abada.
Bayan anyi kwana bakwai da rasuwar Hauwa, aka yi bikin da aka ɗaga sabida rasuwartata. An yi bikin da kwana biyu na haɗo kan mu har Suhailah muka ta ho Zaria, bayan na roƙi mahaifinta akan ya bani riƙonta,yace in ɗauka amma idan ya yi magana uwarsa bata amince ba, to zai biyoni har Zaria ya amshi abarsa. Cikin ikon Allah ma sai uwar tasa bata hana ba,hakan shine silar da riƙon Suhailah ya dawo hannuna tana da shekaru biyar a duniya.
Hajjah ta cigaba da cewa,
"Maleek shi ba mazauni bane, don yana can Lagos ɗinsa sai duk ƙarshen wata ko bayan sati uku yake zuwa Zaria, ya yi kwanaki biyar ko sati ɗaya ya juya inda ya fito, har kuma lokacin bai taɓa cemin yana da budurwa ba bare ayi maganar aure. Shekarunsa kuma kullum ƙaruwa suke yi don har ya shiga shakaru 26 a lokacin,ni kuma bani da burin da ya wuce ya yi auren ,amma shi ko a jikinsa,tun ina magana har na gaji na koma yi masa addu'a.
Suhailah ta taho cikin

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login