Showing 60001 words to 63000 words out of 186776 words

Chapter 21 - TAIMIYAH Book Complete Document by Ayshat Dansabo Lemu .txt

15 Dec 2024

6591

harshensa,suka fara ba juna wani irin deep kisses.Wanda ya sake motsa duk wani kafa da Maleek ɗin yabi ya adana kewanta da yake ji,hannunsa ya kai yana ƙoƙarin sauke botiran riganta ta gaba,amma sai tayi saurin dakatar da shi ta hanyan raba jikinta da nasa.Ta ɗauki jakunan daya watsar tana masa sighn da ido, alamun su ƙarisa daga sama,sannan komi da zai faru sai ya faru...
Maleek da gaba ɗaya jikinsa ya saki da wani irin zazzafan sha'awanta dake sake taso masa.Sai ya rufa mata baya zuwa saman,inda Suhailah bata tsaya a ko'ina ba sai ɗakinsa.


Lokacin da Maleek ya sanyo kansa cikin ɗakin,wani daddaɗan qamshine ya ziyarci hancinsa.
Ko'ina a gyare yake tsaf! Kaman yadda yake muradin gani,sai ya fara da cire rigan shaddan dake jikinsa yai jifa da ita saman gado.Suhailah data ƙariso wajen ita ce ta ɗauke rigan tana ninkewa,kafin ta kai dubanta kan Maleek ɗin da ke binta da kallon da ita kaɗai tasan ma'anansa.Saita shagwaɓe fuska tana faɗin "Wanka first Darling sannan abinci please!"


Tuni Maleek ɗin ya gane inda magananta ya dosa,amma baiyi magana ba sai miƙa mata hannunsa da yayi.Babu musu ta ƙarisa kusa da shi yai mata masauki a jikinsa,yana kai bakinsa kunnuwanta ya raɗa mata wasu kalaman da suka sanyata sakin ƙaramin dariya,tana saurin ɓoye fuskarta a ƙirjinsa.


Daƙyar ta lallaɓashi ya yo wankan ya fito,ta taya shi ya shirya cikin farar jallabiya suka fito zuwa falo.Suhailah ce ta isa wajen dining ta fara sakko da kulolin data shirya masa abinci,tana jera su a ƙasan carfet don ba koda yaushe yake cin abinci a sama ba.Fovourite Food ɗinsa tai masa na tuwan semo miyan ɗanyar kuɓewa,wanda ta wadata shi da naman shanu da ganda aciki.Sai haɗin chicken salad da yaji salad cream da kayan haɗi,sai qamshi ke tashi lokacin data ke zuzzuba abincin cikin plate.
Idanun Maleek ne ke yawo a jikinta ko'ina,tunda ta fara kai-kawo na kwaso kayan abincin,har zuwa yanzu data gama zuba masa abincin cikin plate.Da kanta ta ciyar da shi itama tana ɗan cin haɗin salad ɗin kaɗan-kaɗan.
Bai wani ci tuwan da yawa ba sabida dare ne baya son cika cikinsa da abu me nauyi sosai,shiyasa yafi cin salad ɗin da ɗan yawa sosai,kafin ya kauda kai alamun ya ƙoshi,hakan yasa Suhailah aje plate ɗin ta tsiyaya masa ruwa da lemun Pineapple da tayi masa,sai ya amshi cup ɗin lemun ya fara sha da kansa.Ganin hakan yasa Suhailah tashi ta nufi ɗakinta don sauya kayan jikinta,ta maida wata fingilwan Vest wacce tsayinta da kaɗan ya wuce guiwa.Babu komi a jikinta illa Vest ɗin kaɗai,wacce ba ta da maraba da ba-bu sabida yadda tabi fatan jikinta ta lafe,tare da bayyana duk wani suran jikin Suhailan.


Lokacin data sake fitowa falon samun Maleek ɗin tayi yana kallo.Ya ɗago manyan idanunsa ya sauke akanta,yana jin wani irin feeling na taso masa,na zallan sha'awan ta da ya tara.Domin sati biyu har da kwanaki biyu ba wasa bane a wajen lafiyayyan namiji kamansa,don haka baƙaramin tara sha'awanta yayi ya adana a ƙasan zuciyansa ba.
Don haka a yanzu da take gabansa sai komi ya kwance masa,Suhailah ko tun daga nesa ta hango yadda ya kasa ɗauke idanunsa akanta.Shiyasa tana ƙarisowa sai tayi masauki a laps ɗinsa,tana kwantar da kanta a ƙirjinsa murya can ƙasa take faɗin, "Sweet wannan kallon fa?"


Maleek da ya sauke ajiyan zuciya me ƙarfi sai ya aje remote ɗin dake hannunsa,yana sake shigar da ita cikin jikinsa sosai.Gaba ɗaya qamshin da ke tashi a jikinta sake kwance notikan sha'awanta sukeyi akansa,ya cusa kansa tsakanin wuyanta yana faɗin, "Wife ina tsananin buƙatarki oya muje Bed ki bani magani." Daga haka ya miƙe da ita ajikinsa,yana takawa kaman ya ɗauki Baby suka wajen kayan kallon da ke aiki,ya yi anfani da hannu ɗaya wajen kashe kayan kallon.Ita dai Suhailah sake maƙalƙalesa tayi tana faman bashi kiss a saman face,har suka isa ɗakinsa yai mata masauki akan tsakiyan gadonsa,yana sakkowa ya nufi toilet don wanko bakinsa.


Lokacin daya fito kai tsaye light off yai musu yana nufan kan gadon,tare da janyo Suhailah zuwa jikinsa. wacce ta cire masa rigan jikinta gaba ɗaya sabida sauƙaƙa masa wahalan cirewa......


To sai in ce asuba ta gari Maleek Ado tunda na ga,wannan karan da soyayya ka dawo lol.


____________


Tun misalin takwas da rabi na safe,TAIMIYYAH ta gama shirinta tsaf na zuwa haddah.Sanye take cikin riga da plain zani na wata atamfar Chiganvy,kalan Green da akaiwa adon manyan zane da Milk and Red kaɗan,ɗinkin yayi mata kyau sosai tare da zama ajikinta ɗas! Fuskanta kaman ko yaushe babu komi akai sai man leɓe,yau ko kwallin ma bata sanya ba.Cikin sauri-sauri take komi don bata ma so Yasmeen ta motsa ta ganta,wacce take kwance tana baccinta sadidan.Ta ɗauki dogon Hijab ɗinta na skull ɗin ta sanya,tare da nufan wajen takalmanta ta zura flat shoe me hanci, don sune irin takalman da take iya tafiya dasu.Qur'aninta ta ɗauka tana fitowa zuwa falo,ganin babu kowa yasa TAIMIYYAH nufan ɗakin Iyah,sai dai nan ɗinma Guggo Bilki ce kawai akan gadon Iyan tana bacci.Jin motsin ruwa daga bayi yasa TAIMIYYAH gane cewa Iyah wanka ta shiga,sai kawai ta juyo tayi fitowanta don tafiya makarantan.


Daga waje suka haɗu da Ladi ta fito daga ɗakinta.TAIMIYYAH ta gaisheta tana faɗin, "Saina dawo Babah Ladi,idan Iyah ta fito kice mata sauri na ke yi na wuce,kuma a aje min abin kari na saina dawo zan karya." Babah Ladi ta amsa da faɗin, "To ƴar gidana adawo lafiya,zan sanar da Iyan Allah bada sa'a da ilimi me anfani."


TAIMIYYAH da tai gaba ta amsa da "Ameen." Tana fitowa daga Sasan Iyah ta nufi Compound na gidan,tana fata kar ta haɗu da kowa har ta bar gidan.Cikin sa'a kuwa bata haɗu da kowan ba sai Tukur da suka gaisa ta fice abinta.Tana tafe ne zuciyanta na tariyo mata abinda ya faru tsakaninta da Yah Deeku a daren jiya.Ta wani ɗan lumshe ido ta buɗe hankalinta na kan hanyan da take bi,sanyin safiyan na kaɗa Hijab ɗinta yana ratsa jikinta.Har ta isa makarantan bata bar tunanin da wani ido zata kalli Zuhurah ba,ba kuma ta san ta yadda za ta yi ta iya dakatar da Nass ba, kaman yadda Yah Sadeeq ɗin ya buƙata.




A round 10:30am aka tashe su daga skull ɗin,TAIMIYYAH suka jero da wata ƴar ajinsu me suna Bilkisu.Suna tafe suna magana akan yadda waliman yayensu zai kasance,wanda bazai wuce nan da wata biyu ba zasu kammala haɗe haddansu baki ɗaya.Sun zo dai-dai kwanan da TAIMIYYAH za ta nufi hanyan gida sannan sukai sallama da Bilkisun.Sai ya zamana TAIMIYYAH ita kaɗai ke takawa zuwa cikin layin nasu,kanta a ƙasa take tafiya kaman yadda ta saba.Wani irin ciwan kai take ji na ɗan taso mata kaɗan-kaɗan,ta kuma san hakan baya rasa nasaba da fitowan da tayi bata karya ba,har ta ƙariso gida bata haɗu da kowa data sani a layin ba.


Lokacin da ta sanyo kanta cikin compound ɗin gidan,tun daga nesa idanunta suka hango mata Baba Sani da Yah Sadeeq a tsaye suna magana.Hakan yasa tafiyanta ya sake komawa very slow,don sam bata so haɗuwa da Yah Deeku ba sam,so tayi har ya gama weekend ɗinsa ya koma ba za ta bari su sake haɗuwa da juna ba.Babu yadda ta iya haka ta karya kwana zuwa wajen da suke tsayen,don ta san dole za su ga wucewanta,kuma gashi dama bata je sun gaisa da Baban ba ta tafi haddah.


"Salamu alaikum!
Ina kwana Baba."


Cewan TAIMIYYAH lokacin data ƙarisa gabansu Baba Sanin,tana me tsugunawa har ƙasa ta gaida shi.Ya amsa da matuƙar kulawa yana faɗin "Zainab har kin dawo daga haddan,ya dai tabbata ke kaɗaice ke maida hankali,waɗancan shashashan basama zuwa kenan? Aiko zanci ƙaniyansu sosai." Baba Sani yayi maganan cike da nuna ɓacin rai,ita dai TAIMIYYAH na tsugunne.Sai daya kai aya sannan ta miƙe tana satan kallon Yah Sadeeq,da take jin tasirin idanunsa ajikinta.Don tunda ta ƙariso wajen jikinta ya bata kallonta yake yi,ta gaishe shi cikin sanyin murya tana juyawa ta fara takawa don barin wajen,ba tare data jira ya amsa ba.


Tana dafda shiga Sasan Iyah ta jiyo muryansa yana faɗin "Wait! Zaynab." Sai TAIMIYYAH ta tsaya cak! Har ya ƙariso inda take,sannan ta ɗaga manyan idanunta ta sauke akansa,yana sanye da riga da wando ne irin masu kaurinnan na bacci,da alamu ko wanka baiyi ba kenan.
Ta ɗauke idanunta daga gare shi lokacin da yake matsowa daf-da ita sosai,har tana jin saukan numfashinsa akan face ɗinta.Abinda yasa tai ɗan baya kaɗan tana sake dubansa da fuska a shagwaɓe.
Shi kuma sai ya saki ƙaramin smile yana faɗin "Matsoraciya miye na wani saurin yin baya kaman kin ga dodo,wato shine kika kashe waya tun jiya ko?" Ya jefawa TAIMIYYAH tambayan idanunsa akanta yana kallon yadda ta sake wani narke fuska,kafin ta dubesa tana faɗin "Ni mantawa nayi ban kunna ba,sabida da wuri na tafi Haddah."


Yadda TAIMIYYAN tayi maganan cike da shagwaɓan daya riga ya santa da shi,yasa shi sake matsowa gabanta sosai,cikin ƙasa da murya yake faɗin "Alright! Jiya kin manta baki ɗauki kuɗin da saurayinki ya baki ba,ki ka barmin a ɗakina saura kaɗan in yayyagasu sabida kishi." Ya ƙare maganan yana wani tsuke fuska alamun har zuciyansa da gaske kishin yake ji.TAIMIYYAH tayi saurin dubansa tana sake kwaɓe face take faɗin "Kai! Yah Deeku to ba kaine duk ka janyo hakan ba,ni har yanzu zuciyata ta kasa nutsuwan cewa Zuhurah ba za ta sanar da Umma a yadda ta gammu jiya ba."


TAIMIYYAH ta kai ƙarshen maganan komi yana dawo mata,shi ko Yah Sadeeq sai ya tsura mata ido yana ji tamkar ya sake rungumanta ajikinsa irin na jiyan,ya wani lumshe ido ya buɗe akan fuskan TAIMIYYAN.Yana ɗan sakin smile yake faɗin "And so what! To idan ta faɗi Baby, Zina ta ganmu muna yi ko babu kaya a jikinmu ta ganmu?" Yah Sadeeq ɗin yayi maganan yana ƙoƙarin su haɗa ido da TAIMIYYAH.
Amma sai TAIMIYYAH tayi saurin ɗauke kai,wani uban kunyan maganan da Yah Deekun ya ɓaro na lulluɓeta.Bai bari tace komi ba ya sanya hannu a aljihunsa yana ciro kuɗin da Nass ya bata jiya yana miƙa mata,ta sanya hannu ta amsa amma taƙi bari su haɗa ido har lokacin.Cike da kishi yake faɗin
"Ki tabbatar Iyah kika ba kuɗinsa ta aje masa,kar ki sake ki anfani da su kinji na gaya miki Baby." Yayi maganan bilhakki idanunsa akan TAIMIYYAN data ɗan zumɓuro baki,kafin ta furta, "Ai da ma ita zan ba ni bance zan kashe ko sisi ba,kuma ma ai shine ya aje yai tafiyansa,amma tunda ya bani nace masa bazan amsa ba."
Tana kaiwa ƙarshen maganan ta juya zata bar wajen,amma sai Sadeeq yayi saurin riƙo Hijab ɗinta.Saura kaɗan hannunta ya goce akan guiwanta da take dafe dashi,tayi saurin sake dafe ƙafan me laluran.Tana ɗago manyan idanunta ta sauke akan Yah Deekun,ya wani haɗe fuska yana faɗin "Shine zaki tafi na ce na gama magana dake ne?"


"Yah Sadeeq don Allah ka saki Hijab ɗin to,kada wani ya fito ya ganmu.Yinwa nake ji ban karya ba na fito don Allah ka barni in ƙarasa ciki please!"


Yadda tai maganan kaman zata sanya masa kuka,yasa ya sake mata Hijab ɗin yana faɗin "Alright! Baby jeki ki karya amma ki kunna wayanki zamuyi magana."


Kai kawai TAIMIYYAH ta gyaɗa masa tana juyawa ta shige,shi kuma Yah Sadeeq ya juya ya nufi part ɗinsa,zuciyarsa ba sake cika da soyayyan TAIMIYYAN,da yake ji kaman ƙara shi akeyi a zuciyarsa kullum.


Da sallama TAIMIYYAH ta shiga falon Iyah,idanunta na sauka akan Yasmeen da Guggo Bilki da ke zaune cikin falon.Luggage ɗin Guggo Bilkin ne agabanta tana shirya kaya,TAIMIYYAH ta ƙarisa wajen tana gaida Guggo Bilkin.Ta ɗago tana amsa gaisuwan TAIMIYYAN kafin ta ɗaura da faɗin "TAIMIYYAH shine kika tafi makarantan baki ko tsaya kin karya ba,zaki ci faɗan Iyah kuwa don sai mita take yi tun ɗazu." TAIMIYYAH ta saki murmushi tana faɗin "Iyah kenan,dama na san za ta yi faɗa kam.Guggo Bilki wai da gaske tafiya zakiyi yau ɗin? Gaskiya zamuyi kewa."


TAIMIYYAH ta ƙare maganan cike da nuna irin missing ɗin da za su yi na Guggon nasu,don babu ruwanta da hayaniya akwai ta da sauƙin kai sosai.
Yasmeen ta dubi TAIMIYYAH tana faɗin "Aike wallahi baki da kirki, kin san za kiyi sammakon fita makaranta amma baki tasheni ba,ki kai tafiyanki."


Yasmeen ta ƙare maganan tana zabgawa TAIMIYYAH harara.Kafin TAIMIYYAN tace komi Iyah ta fito daga ɗaki,hannunta riƙe da wayanta ta dubi TAIMIYYAH tana faɗin "Kin kyauta fita babu karin safe,bayan kin san kina da ulcer." Iyah tayi maganan cike da mita tana hararan TAIMIYYAH data cire Hijab ta aje saman kujera,kafin ta dubi Iyan tana faɗin "Allah baki haƙury Iyah,sauri nake yi amma kin san bana fita ban karya ba ai.Ina kwana mun tashi lafiya?" Ta ƙare maganan da gaida Iyah,wacce ta amsa tana faman taɓe baki,hakan yasa Yasmeen sakin dariya tana faɗin "Iyah wallahi wajenki TAIMIYYAH ke course ɗin iya harara da shagwaɓa,ke ma da alamu lokacin ƙuruciya kin taɓa shagwaɓa son ranki." Yasmeen ta ƙare maganan suna kwashewa da dariya ita da TAIMIYYAH,Iyah ta aikawa Yasmeen daƙuwa tana faɗin "Kin ci gidanku ƴar nema." Guggo Bilki dai na jinsu tana dariyan draman su Iyah da jikokin nata da bai ƙarewa.TAIMIYYAH ce ta nufi wajen cin abinci don karyawa,koda ta gama sai ta wuce ɗaki tana ɗaukan wayanta ta kunna.
Haka kawai take son jin muryan Nass ɗin,don tasan yayi ta kiran wayan da safe ya jita a kashe.Aiko wayan na gama Booting saƙonni suka fara shigowa.Sai ta nufi inbox ɗin don karantawa,biyu daga MTN ne sai guda ɗaya daga Nass ɗin,ta buɗe na Nass ɗin tana karanta tsararrun kalaman daya turo mata na gud morning text.Wanda baya fashin turowa duk safe.Daga ƙarshen saƙon yai mata ƙorafi akan ya kira wayanta a kashe,amma idan ta ga saƙonsa ta kira shi please!


TAIMIYYAH ta saki smile a lokacin data gama karanta saƙon,tana nufan call log tayi dialling number ɗinsa.Yana fara ringing zuciyanta ya shiga bugawa,har zuwa lokacin da yai cuting call ɗin ya biyo bayan kiran.Sai ta gyara zamanta daga bakin Bed ɗin lokacin da sassanyar muryansa ya shiga kunnuwanta.Ta gaida shi cike da salonta dake sake narkar da zuciyanta Nass ɗin.Sun ɗauki kusan 15minutes suna waya kafin suyi sallama,Nass ɗin na sanar da ita tuni har ya isa Kd ma.


Bayan TAIMIYYAH ta aje wayan sai ta miƙe tana cire kayan jikinta.Ta maida wata doguwar riga mara nauyi,sabida bata faye son zama da kaya masu nauyi idan tana zaune a gida ba.


Yasmeen ce ta shigo ɗakin lokacin da TAIMIYYAH ta ɗakko System ɗinta zata kunna.Yasmeen ɗin ta sauke idanunta akan TAIMIYYAN tana faɗin "To Malama sai ki tashi ki fito mu raka Mamie don yanzu zata wuce." TAIMIYYAH ta ɗaga manyan idanunta tana duban Yasmeen take faɗin "Yanzu da wuri haka,kai ita ko Guggo da-dai ta bari sai gobe kawai." Yasmeen ta jefa mata harara tana faɗin "To Abbah bai ga dama ba,yace yau-yau yake son ganin ta koma gida,nima da ƙyar ya amince in ƙara one week."


Tare da TAIMIYYAN suka fito zuwa falon Iyah,dukansu sanye da Hijab a jikinsu.Tuni Guggo Bilki har an kai Luggage ɗinta mota,Driver ɗin da zai tuƙata zuwa Kanon ma iya so ashe tun safe.


Har da Ladi me aiki aka rankaya zuwa wajen compound ɗin gidan,don yiwa Guggo Bilki rakiya wacce ta nufi Sasan Baba Sani don yi musu sallama.TAIMIYYAH da Yasmeen dai na tsaye jingine da jikin Motar Guggo Bilkin basu bi ta Sasan su Umman ba,mintuna kaɗan sai ga Guggo Bilkin sun fito tare dasu Zuhurah,sunyo mata rakiya har zuwa wajen mota.Ta shiga motar su TAIMIYYAH na ɗaga mata hannu,har Motar ta bar cikin compound ɗin suka juya don komawa cikin gida.


Zuhurah ce tayi saurin biyo bayansu tana kiran sunan Yasmeen.Hakan yasa su TAIMIYYAH dakatawa daga tafiyan suna jiran ƙarisowan Zuhuran,koda ta iso idanunta akan TAIMIYYAH yake wacce tayi saurin ɗauke kai,don bata son ma su haɗa ido da Zuhurah.Tuni Zuhuran ta gane abinda yasa TAIMIYYAH take ɗauke mata kai,sai ta saki murmushi kawai tana faɗin "Yasmeen yau fa Ameeru zai iso,shine nace me kike ganin zamu shirya masa na tarba?"


Yasmeen da idanunta ke kan Zuhurah,sai ta juya tana nunawa Zuhurah TAIMIYYAH tana faɗin "Ga wacce zaki tambaya nan,don ita ce gwanan sanin abubuwan kwaɗayi da Girkunan zamani."


Zuhurah da takaicin maganan Yasmeen ɗin ya ɓata ranta,sai ta maze bata nuna ba.Sai ma tayi taku biyu tana tsayuwa daga gefen da TAIMIYYAH ta juyar da kanta,murya can ƙasa yadda bama lallai Yasmeen data zama a gefen Zuhuran taji me zata iya faɗiwa TAIMIYYAN ba.Zuhuran ke faɗin "Ya da ɗauke kai ƴan matan Yah Sadeeq,ko kuma karuwansa zan ce? Don naga alamu ya gama amshe budurcin tunda har kike kai kanki garesa kina bashi kayan daɗin har ɗaki.To ya? Zaki taimaka ki samarma saurayin nawa abinda zamu tarbe shi da shi ɗin ne Babyn Yah Deeku?"


Zuhurah ta ƙare maganan tana sakin dariyan iskanci.Tuni TAIMIYYAH ta gama muzanta da jin kalaman da Zuhurah ta jefeta da shi,kalmar karuwa data jingina ta dashi yafi komi ɗaga hankalinta.Tayi saurin ɗago kanta don ganin ko Yasmeen ta ji abinda Zuhuran tace,amma cikin sa'a sai ta ga Yasmeen ɗin tama yi nesa dasu tana amsa waya.Hakan yasa TAIMIYYAH sauke manyan idanunta da suka fara tara ƙwallan baƙin ciki a kan Zuhurah,tana faɗin "Zuhurah ni kike kira da karuwan Yah Sadeeq,sabida kawai kin ganmu riƙe da hannun juna?" Tai tambayan tana ji hawayen da take son dannewa na son kwacewa su zubo akan fuskanta.Zuhurah ta dubi TAIMIYYAN tana sakin dariyan rainin hankali take faɗin "To da wacece ke? Karki rainawa kanki wayau mana,ko daga yadda na ganshi a wani susuce nasan magiya yake miki lokacin,yana so ku shiga daga ciki ya jisa ajikinki,ke kuma kina wahal dashi irin sai ya gama shiga uku kafin ki bashi abinda ya saba karɓa,ni dama na san soyayyan da yake miki ba banza ba.Jikin yake so da can ƙasan tunda an sakar masa komi yaji daɗi shiyasa yake nacin ki zama mallakin nasa baki ɗaya,kuma wallahi idan kikai wasa kaman na sanar da Umma abinda na gani."


Zuhurah na kai aya TAIMIYYAH tayi saurin juya baya dafe da ƙafanta ta fara tafiya.Kuka take son yi amma ta danne tana jin wani irin tashin hankali na rufto mata,ga tsananin zafin kalaman da Zuhurah tai

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login