Showing 57001 words to 60000 words out of 186776 words
Chapter 20 - TAIMIYAH Book Complete Document by Ayshat Dansabo Lemu .txt
Sadeeq da TAIMIYYAH babu uban da ya isa hanawa,shi ma kuma Sanin xai zo ya sameni." Daga haka Iyah ta juya ta koma Sasanta,ta bar su Umma tsaye carko-carko.Umma ta dubi Zuhurah tana faɗin "Don ubanki sai ki sanar dani abinda kika ga suna yi." Zuhurah ta zunɓuro baki tana faɗin, "Wallahi Umma rungume fa na ganta a jikinsa,shi kuma sai wani faman shafata yake yi ko kunya."
Umma ta saki salati tana faɗin "Shi Sadeeq ɗin kika gani da Gurguwan a haka? Aiko zan ci ubansa a gidannan,inma iskancin ne ya rasa wacce zai dinga bi sai Gurguwa Musaka? Koda yake ba laifinsa bane itace take cusa masa kanta,tunda tasan da wuya ta auro gara ta bashi yai ta kwasan banza,amma zanyi maganinsa zai san cewa da gaske na tsani yarinyar."
Umma ta ƙare maganan cikin tsananin fishi,tana nufan ɗakinta don ɗaukan waya ta kira Sadeeq ɗin.
Basmah ce bayan shigewan Umma ta dubi Zuhurah tana faɗin "Don Allah Yah Zuhurah da gaske kike yi abinda kika faɗi,ba sharri ki kai musu ba?"
Basmah tayi maganan idanunta akan Zuhurah.Ita kuwa Zuhurah tsaki ta ja tana faɗin "Eh! Sharrin nai musu tunda ke banza ce,kina tunanin bazai iya neman nata bane,yana ganin nono da ɗuwawu available."
Yadda Zuhurah ta kai ƙarshen maganan ne yasa Basmah kwashewa da dariya.Kafin ta furta "No wonder abu kullum sake cika suke,ashe suna samun taki ne bamu da labari,amma Gurguwarcan akwai ƴar rainin wayau,kullum zulum-zulum da Hijab ashe shu'uma ce.Shi kuma Yah Sadeeq da shegen kwaɗayi da son banza,miye na bin Gurguwa inma iskancin zai yi ta bakin Umma mitsuuww...!" Basmah ta ƙare maganan da jan tsaki.
Daga ɓangaren Iyah kuwa bayan ta koma Sasan nata,zaunar da TAIMIYYAH tayi ta sake mata faɗa akan yadda kullum take kyale su Zuhurah,na cin kasuwansu akanta ba ta iya maida musu martani.Daga ƙarshe tai musu faɗa da nasiha daga ita har Yasmeen akan muhimmancin kare mutumcin kai,ko da wasa kada su bari kowani namiji yai anfani da kusancin da ke tsakaninsu har yace zai dinga kai hannunsa jikinsu.
Daga Yasmeen har TAIMIYYAN maganganun Iyah sun ratsa jikinsu,hankalin TAIMIYYAH sai ya kwanta sosai.Amma duk da haka da zaran ta tuno yadda Zuhurah ke gwaɓa mata magana,sai ta ji zuciyarta ta taɓu.
Duk wannan bidirin da akayi sam Anty Laurat bata da labari,don bata gidan abin ya faru ta je can samaru kai ɗinki,wajen wani sabon telan da su Zuhurah suka samu.
Yasmeen ce ke bata labarin komi,sanda ta shigo Sasan Iyah da yamma,aiko itama ranta ya ɓaci sosai da abinda Zuhuran tayi.Hakan yasa tace ta cire hannunta akan yin abincin dasu Zuhuran xasu tarbi Ameerun dashi,don tuni ma ya ƙariso garin inji Zuhuran.Ya yi masauki a hotel ne ya ɗan huce gajiya,sai zuwa dare zai ƙariso nan gidan.
Daga Zuhuran sai Basmah da masu aiki,su kai kiɗansu su kai rawansu a Sasan Baba Sanin.Don Anty Laurat ƙin komawa ma Sasan tayi,don kar ma Umman ta sata shiga ta taya su aikin,sai da akai kiran Sallar Magriba ta bar Sasan Iyan ta nufi nasu.
Su TAIMIYYAH kowacce sai ta tashi ta nufi ɗaki don ɗaura alwala.
___________
Maleek Ado ne zaune daga ƙasan carfet ɗin Babban falon da ke down stairs,yana sanye cikin ƙananun kaya mafiya tsada.Dawowansa daga masjid kenan bayan an idar da sallan Isha'i,sai yayi masauki anan falon ƙasan don hutawa.
Yau ko kaɗan baiyi nesa da gida ba,wajen Hajjah kawai ya je ya gaidata ya dawo gida.
Hatta wayoyinsa yau ɗin a kashe suka yini sai da yamma ya kunna su.Bai wuce minti biyar da zama ba Suhailah ta sakko daga sama,tana nufo wajensa direct cikin takunta me cike da yauƙi.
Tunda ta doso shi idanunsa ke zube a kanta,tana sanye cikin Straight Gown na English Wears,rigan yabi jikinta ya lafe sosai tare da fitar da suranta.Bakinta ya sha jan lipstick Red kalan rigan data sanya ɗin,hannunta riƙe da wayanta tana faman taunan cingam ɗin Orbit me shegen qamshi.
Lokacin data iso hannu ya miƙa mata ta sanya nata ciki,yana me janyota gaba ɗaya tai masauki a jikinsa.Ya ɗaga manyan idanunsa ya sauke akan ƙirjinta,kafin ya kai hannnu saman lips ɗinta yana shafa janbakin daya zauna raɗau akan lips ɗinta.
"Yah Maleek ko a kawo abinci nan ne?" Suhailah tayi maganan tana sake lafewa a jikinsa.Maleek ya sanya idanunsa cikin nata,murya can ƙasa cike da ƙasaitannan nasa yake faɗin "Yes akawo nan Wife,amma ba sai anyi wahalan sauko da su duka ba,just ki zubo min iya abinda kika san zan ci,ina fata kinyi min haɗin Fruit Salad ɗinnan?" Ya ƙare maganan da jefa mata tambaya,yana saketa ta miƙe tsaye,sai ta gyaɗa masa kai tana faɗin "Nayi tun ɗazu yana cikin fridge bari sai a haɗo har da shi."
"Alright! Luv thank u." Cewan Maleek cike da basarwa,yana ɗauke ganinsa daga gareta lokacin da ta nufi hanyan hawa stairs ɗin.
Lokacin da Suhailah ta sakko ɗauke da Tray ɗin da ta ɗauro abincin da tai sarving ɗin Maleek ɗin,sai ta aje agabansa tana faɗin, "My Maleek ga abincin."
Ya ɗago manyan idanunsa ya sauke akanta,yana nuna mata inda zata kawo masa abincin nan gabansa sosai.Ta ɗauki Tray ɗin ta matsar gabansa,tana zama kusa dashi ta fara ciyar da shi da kanta.
Bai ci wani da yawa ba yace ta bashi Bowl ɗin Fruit Salad ɗin,ta miƙa masa tana sake mannuwa da jikinsa.Qamshin turarenta na shiga hancinsa sosai,yana sake saukar da nutsuwa a zuciyansa,har ya gama shan Fruit Salad ɗin bai yi magana ba,kamar yadda itama Suhailah ta kame bakinta,don tasan halin ƴan kayanta sarai.Bai faye son yana cin abinci ana damunsa da hira ba,shiyasa itama sai ta maida hankali akan chart ɗin da take yi da Zubaida Halliru.Wacce ke tambayanta cewa Maleek ɗin ya dawo ne? Suhailah ta aika mata da amsan cewa eh! Ya dawo gasu ma tare yana kusa da ita.
A.Maleek da ya ture Bowl ɗin gefe guda bayan ya shanye haɗin Fruit Salad ɗin,sai ya sauke manyan idanunsa akan Suhailah da hankalinta ya ɗauku akan chart ɗin da take yi da Zuby.Bai yi magana ba sai hannu daya kai a bazata ya zare wayan daga hannunta,idanunsa na sauka akan chart ɗin su,ganin sunan Zuby yasa shi tuno da tarin saƙonnin da take damunsa da turowa,don ma yayi Blocking ɗinta shine ya samu mafita.
Ya aje wayan daga gefe yana duban Suhailah cikin ido yake faɗin,
"Waye Zuby ,wani matsayi take da shi a wajenki da har zaki ɗauki number ta ki ba ta?"
Ya jefawa Suhailah tambayan yana tsareta da idanunsa,face ɗinsa babu alamun sassauci ko kaɗan.Hakan yasa Suhailah ɗauke idanunta akansa tana faɗin "Aminiyata ce tare muke a skull tun daga level one,har muka gama tana da kirki sosai fa Yah Maleek.Kuma ai na bata numbern ne sabida tace zata tayani baka haƙury ,tunda itace ta bani shawaran fara anfani da Pills ɗin da suka janyo min matsala." Suhailah tayi maganan tana duban fuskan Maleek,wanda yake jifanta da wani irin mugun kallo,kafin ya buɗe baki yana faɗin,
"Okey! Tuh ina so kisani in dai zamana kike yi a gidannan,na kuma isa da ke to na soke duk wani Ƙawancen da ke tsakaninki da ita.Ba ki ba ita, kuma karta sake tako ƙafanta cikin gida na kinji na gaya miki?"
Suhailah tayi saurin ɗago idanunta da ke nuna zallan kaɗuwa da kalaman Maleek,ta furta "Haba Yah Maleek me yai zafi har haka,me Zubaidan tai maka?" Tayi maganan tana kallon yadda ya ke jifanta da harara kafin ya sake jefa mata wata tambayan cikin kaushin murya, "So kike yi kisan me ta yi min kafin ki bi umurnina Suhailah?"
Yadda ya tsatstsareta da manyan idanunsa yasa Suhailah kasa magana,sai gyaɗa masa kai da tayi kawai tana jin wani irin haushin kalamansa.
Maleek bai sake magana ba shima,sai wayansa daya ɗauka ya shiga ma'adanan saƙonni yana miƙa mata wayan,tare da tsare ta da idanunsa da ke kiɗima ta.
Suhailah ta amsa wayan tana sauke idanunta akan numbern Zuby da ta turo saƙon.
Ta fara bin rubutun tana karantawa cikin sauri,amma tun kafin ta yi nisa a karatun wani irin tashin hankali ya ziyarce ta.Ta ɗago ido ta saci duban A.Maleek da nasa idanun ke kanta,ya watsa mata wani banzan kallon da yasa ta saurin mai da dubanta kan wayan,tana ƙarisa karanta saƙon da ya gigita tunaninta.Don bata yi zaton ko da wasa Zubyn data ɗauka a matsayin aminiya za ta iya shirya mata wannan makircin da sharrin a wajen Maleek ɗin ba.
Hankali tashe Suhailah ta sake matsawa jikin Maleek ɗin,bayan ta aje wayan tana dubansa cikin rawar murya ta fara faɗin "Wallahi dukkanin abinda ta faɗi sharri ne Yah Maleek,ita ce duk ta bani shawaran fara planning tana nuna min cewa kada na bari na fara haihuwa tun ban mori ƙuruciyata ba,ni kuma ganin lokacin ina tsaka da karatu sai na dinga bin shawaranta,har na fara anfani da maganin hana ɗaukan ciki,wallahi bance bazan haihu da kai ba Yah Malee....."
"Enough! Please." Maleek ya katse Suhailah daga maganan data ke yi cikin fushi,da nuna zallan ɓacin ransa.Ya ɗaura da faɗin,
"Sabida ke ɗin sakaryace shine kika dinga biye mata tana shirya miki gadar zare ko? To ai yanzu kin fara fahimtan inda ta dosa.So take ta kashe aurenki ita ta shigo don ta samar da abinda ke kika kasa samarwa,don haka bana son sake jin sunanta ma a bakinki bare har ta sake tako min cikin gida.Idan ko hakan ya faru to ki fara shirin amsar ta a matsayin kishiya,tunda ke sakarya ce mara zurfin tunani,da har zaki ɗauki numbern mijinki ki baiwa qawar ki.Qawar taki ma ƴar iskan da ta fiki buɗewan ido sabida ke shashasha ce!" Ya ƙare maganan yana ture Suhailah da ke jikinsa,amma sai ta sake ƙanƙameshi tana sakin kuka me tsuma zuciya.
Dana sani da kuma nadaman biyewa Zuby da tai tayi a baya na mamaye zuciyanta.Cikin kuka take baiwa Maleek ɗin haƙury tare da roƙonsa yai Blocking layin Zubaidan ma baki ɗaya a wayansa,don kalamansa na cewa zai iya auren Zubyn idan ta cigaba da Aminta da ita ba ƙaramin kiɗimata ya yi ba.
Maleek dake sauraren magiyan da Suhailah ke masa,sam baice uffan ba har sai data ɗago tana duban fuskansa,da idanunta da yai kace-kace da hawaye,ya balla mata wani harara yana faɗin "Yanzu kin amince zaki rabu da ita ko kina sha'awan ta shigo ku zauna tar......"
Kukan da Suhailah ta saki tana kai hannu ta rufe bakinsa,shi ya hana shi ƙarisa kalamansa,wani irin dariya ke taso masa yana dannewa.
Cikin muryan kuka Suhailah ke faɗin "Wallahi zan bar ta Yah Maleek,bari na har abada ma kuwa tunda ita ɗin maciyiya amanace,ba sona take tsakani da Allah ba,don Allah ka daina cewa za ka iya aurenta zuciyata bugawa za ta yi." Suhailah ta kai ƙarshen maganan tana sake cusa kanta a ƙirjinsa ta saki kuka,hakan yasa Maleek sakin ƙaramin murmushi yana kai hannu bisa kanta.Ya zame hulan data sa ya shiga yamutsa lallausan gashinta,kafin ya fara maganan cikin ƙasaitacciyar muryansa,yana faɗin "It's okey! Kukan ya isa haka,kinga yanzu sai ki fara ɗaukan darasi akan sakarwa qawaye fuska,bama ita wannan kaɗai ba duk wata qawa kiyi hankali da sakin mata fuska, bare har ta san wani sirrin abinda ya shafi gidan aurenki da mijinki,har ki iya ɗaukan numbern mijinki ki bata.Karki sake min irin haka ko da wasa kin ji ko?" Suhailah dake sauraransa ta gyaɗa kai kawai don bama zata iya magana ba,sabida yadda baƙin cikin Zuby ke kashe zuciyanta.
A Maleek ɗin ya cigaba da faɗin "Nan da 5 days na ke saka ran Visa ɗinki zai fito,zamu tafi Egypt kaman yadda na sanar da Hajjah,ni nawa har ya fito Visan don haka sai ki addu'a Allah sa asamo mafita,idan kuma mafitan bata samu ba kaman yadda na faɗi a baya dole ne zan ƙara aure Subailah.
Zan ƙaro aure ba don na daina son ki ko zan daina ba,sai don kawai ina da buƙatan ganin jinina na yawo a doran ƙasa,ina buƙatan haihuwa sosai da sosai Suhailah, shiyasa abinda kika yi ya taɓa zuciyata matuƙa.Ba don dangantaka ta jini me ƙarfi da ke tsakanin mu ba,wallahi da gida zaki koma har sai kin nemi lafiyan da mahaifanki zata iya ɗaukan ciki.Sannan zaki dawo gida na tunda lokacin da ki kai ma mahaifar illa ba da izini na kika aikata dukkanin abinda kika yi ba."
A.Maleek ya kai ƙarshen maganan kunnuwansa na jiye masa azababban kukan da Subailah ke yi.Me asalin motsa zuciyan me saurare wanda hakan ya raunata zuciyansa,har ya sake matseta a jikinsa sosai,yana jin ɗumin hawayenta da ke jiƙe gaban rigansa.
Bai sake magana ba kamar yadda Suhailah itama bata fasa kuka ba,domin kalamansa ba ƙaramin rugurguza zuciyarta yayi ba.Wani irin soyayya take wa Maleek ɗin da ya haifar da azababban kishinsa a zuciyarta,shiyasa kalmar ƙarin auren da yake ambata ta ke jin tamkar yana soka mata mashi ne a ƙahon zuci.
Shafa lallausan gashin kanta ya cigaba da yi,har zuwa lokacin da Subailah ta yi shiru don kanta.Tana faman sauke ajiyan zuciya akai-akai,ya ɗago fuskarta daga jikinsa yana tsura mata ido,kafin ya fara share mata hawayen da yaƙi tsayawa,murya can ƙasa yake faɗin "Ya isa haka kukan Suhailah,na sanar da ke gaskiyan abinda ke zuciyata ne don bazan iya miki ƙarya ba.Ina son ki wife ke ma kinsan hakan,sai dai soyayyar da nake miki ba zai sa in iya zuba miki ido mu rayu babu haihuwa ba.
Musamman yadda na nake jin zafin cewa kece ki kai wa kanki illa,ko da zan ƙara aure ina so ki sawa ranki zanyi hakan ne ba don son da nake miki ya ragu a zuciyata ba.Kuma nayi miki alqawarin kare duk wani martabanki,i luv u wife,i luv u so very much! Kuma ina fata in cigaba da sonki har ƙarshen numfashi na Suhailah."
A.Maleek ya kai ƙarshen maganan yana haɗe fuskokinsu waje guda,kafin a hankali ya haɗe bakinsa da nata ya fara bata wani irin kisses da suka tsaida gudun hawayen Suhailah cak! Ta wani sake shigewa jikinsa tare da ƙanƙamesa tamkar zata shige cikin ƙirjinsa.Gaba ɗaya Maleek yayi nisa wajen nuna wa Suhailah tarin ƙaunanta dake cikin zuciyansa,lamarin da bai tuƙe a ko'ina ba sai a gadon baccin su.
Don Maleek ɗaukanta yayi cak! Suka haura zuwa sama,ba tare da sun bi takan wayoyinsu dake zube a falon ba,ban sake jin ɗuriyan su ba sai da komi ya dai-dai ta,sannan Maleek ya zare jikinsa yana nufan toilet ya tsarkake kansa.
Lokacin da ya fito Suhailah na kwance shame-shame bisa bed ɗin,dukkanin jikinta da zuciyanta sun gama galabaita da tarin ƙaunar da Maleek ya nuna mata.Kallon ta yayi cikin ido yana nuna mata hanyan Bathroom da hannu,alamun ta tashi ta je ta tsarkake jikinta ita ma.
Bai kuma jira cewan ta ba ya nufi hanyan fita ɗakin,don sauka down stairs ya kwaso musu wayoyinsu.
Suhailah ta fito daga wanka agogo na buga ƙarfe 1 dot na dare,sanye ta fito da rigan wanka kanta na ɗigan ruwa.Direct ɗakinta ta wuce don busar da gashinta sabida gudun kwana da lema akai,don hakan na sanyata Mura.
Bayan ta busar da gashin,sai ta sanya ƙaramar Vest a jikinta bayan ta fesa Body mist me sanyin qamshi.Ta fito ta nufi ɗakin Maleek ɗin,ta same shi kwance bisa Bed idanunsa a rufe,hakan yasa ko da ta hau kan godan sai ta nufesa tana shigewa cikin Duvet ɗin,yai mata masauki a ƙirjinsa yana ya rungumeta.Hancinsa na shaqo masa sassanyan qamshin Body mist da Suhailan tai anfani da shi,ita ko Suhailah luff tayi a faffaɗan ƙirjinsa,tana kai fuskanta zuwa nasa ta bashi light kiss,murya can ƙasa ta furta "Luv u my Maleek."
A.Maleek ya lumshe ido yana mayar mata da martanin kalamanta,ta sigan da zata fi fahimta ba da baki ba........✍🏻
Littafin TAIMIYYAH paid book ne,ga duk wanda ta tsincesa a kowani irin group ne,kiji tsoran Allah karki karanta sai kin biya 500 naira only.
Za ku iya min magana ta wannan number ɗin 08167768704, ko kuma ku turo kuɗin ku kai tsaye ta wannan account ɗin 0504192664 aisha ibrahim dansabo GTbank.*
*Sai ku tura shaidan biyanku ta wannan line ɗin 08167768704.*
Masu turo credit za ku turo katin MTN na 500 ta wannan line ɗin 08167768704.
#Ɗansabo ce#
[12/14, 10:05 PM] +234 703 769 7050: *Page 29*
*Friday, 8:49pm.*
Suhailah ce ke ta faman kai-kawo a cikin falonta da ke upstairs,tana jiran isowan Maleek Ado, wanda ya shaida mata goslow ne ya riƙe su a Kaduna tun ɗazu.
Sanye take cikin wata english straight gown,da ya amshi jikinta sosai tare da fiddo suranta.Make-up sosai tayi wa fuskanta wanda hakan ne ya sake qawata kwalliyan,ta sanya manyan ɗan kunni da sukai mata kyau matuƙa,qamshin Turarukan ta masu asalin sanyi da daɗi ke fita daga jikinta.
Tana shirin nufan ɗakinta don ita har ta fara gajiya da jiran isowan nasa.Sai kuma taji buɗe gate hakan yasa ta isa wajen window,ta zuge labulen dake jiki don ta samu daman kallo harabar compound ɗin gidan daga waje.Take idanunta suka sauka akan ƙatuwar motarsa da ke shigowa cikin compound ɗin,kafin a tsaida motan Yusuf na saurin fitowa ya buɗe masa back seat ya fito.Yana sanye cikin manyan kaya da suka fito da cikar kamalansa,da kyawun da Allah ya basa.Suhailah ta saki labulan window ɗin tana sauke ajiyan zuciya a bayyane,wata iriyar zazzafan ƙaunar sa na sake narke zuciyanta,duk ta ƙosa ya ƙariso ciki tai hugging ɗinsa ko zaciyanta zata samu relief,daga azaban kewansa da ta yi.
Lokacin da Maleek ya iso cikin falon gidan,hannunsa riƙe da brief case da kuma wata ƙaramar jakan hannu.A bakin matakalan benen da zai kai shi sama su kai kacibus da Suhailah data sakko don tarbansa.Ya sauke manyan idanunsa akan lips ɗinta da ya sha pink ɗin janbaki raɗau! A hankali duk wani gajiyan da yake ji ya fara warwarewa,kewanta da ya yi na sake mamayesa.
Suhailah bata jira komi ba ta rungume shi ,tana masa sannu da xuwa cikin salon da ta san yana motsa zuciyansa.Aiko take ya saki duka abinda ke hannunsa,yai mata wani irin kyakykyawan runguma,yana sanya kansa tsakanin ƙirjinta da ke fitar da wani irin qamshi me motsa zuciya.Murya can ƙasa-ƙasa yake faɗin,"I really miss u wife." Yayi maganan yana ɗago kansa daga wajen ya kai fuskar nasa wani muhalli na daban.
Suhailah cikin low voice ita ma take faɗin, "Miss u too my Maleek,duk na ƙagara ku iso tun ɗazu." Suhailah ta kai ƙarshen maganan da kai bakinta saman nasa ta haɗe,cikin salon da ke birkita lissafin Maleek ɗin take labuban