Showing 120001 words to 123000 words out of 186776 words

Chapter 41 - TAIMIYAH Book Complete Document by Ayshat Dansabo Lemu .txt

15 Dec 2024

6626

Allah bai sa haka suke ba,mata ce me mutunci da sanin darajan ɗan adam,duk arziƙinsu bai sa ta kasance me wulaƙanta halittan Ubangiji ba."


Umma da tuni ta fara jiyo ƙamshin jirwaye cikin maganar Iyah sai tayi saurin ɗaukar basket ɗinta tayi gaba tana cewa, "To Iyah Allah ƙara sauƙi bari in miƙa kwandon ciki nima fita zanyi na ga dawowar ku nace bari in tsaya mu gaisa."


Iyah ta taɓe baki tana cewa, "To madallah." Daga haka tayi gaba abinta Sani na biyo bayanta da kayan zuwa ciki.


Tuni TAIMIYYAH ta isa ɗaki bayan sun gaisa da Babah Ladi da tai mata ya jiki,tana isa kan gado ta nufa ta zauna tana sauke numfashi.
Bacci-bacci take ji a idanunta shiyasa ta miƙe ta jona wayarta a caji ganin a kwai wuta,ta baro wajen tana nufan wajen kayanta ta ciro wata doguwar riga me taushin jiki,ta cire na atamfar jikinta ta sanya wanda ta ciro ɗin.
Direct sai ta nufi gado ta kwanta ba a ɗauki lokaci ba kuwa bacci ya sace ta.


Iyah da ta kammala kintsa kayan da suka dawo dasu sai ta nufi ɗakin TAIMIYYAH, tana son sanar da ita abubuwan arziƙin da ta gani cikin kulas ɗin da Hajiya suka kawo,sai ta tadda TAIMIYYAH tayi bacci hakan yasa ta fitowa ta nufi ɗakinta itama don ta huta.


Koda Ummi suka shigo gaida TAIMIYYAH sun samu daga ita har Iyah suna bacci,sai Babah Ladi kawai suka tadda da ke ta hidiman ɗaura girkin lunch.
Ummie sai ta koma sasanta ta bar Inna Larai za ta taya Babah Ladi aiki,don wataran idan ta shigo ta kan shiga kitchen suyi aikin tare, tunda Iyah ce take zuba musu abinci ana kuma sanya musu daga sasan Baba Sani ma,duk da cewa babu abinda ba a aje musu na kayan abinci a sasan su ba ,sabida idan sunyi ra'ayin dafa abinda ran su ke so su girka abinsu.


TAIMIYYAH da Iyah sai azuhur suka tashi daga bacci,kai tsaye TAIMIYYAH wanka ta shiga ta fito ɗaure da alwala tana jin daɗin jikinta sosai.
Kanta sayau take jinsa duk ciwan kannan ya tafi sai dai mura dake son damunta kaɗan,shima ta san tana shan maganinsa da aka haɗo mata daga asibiti za ta samu sauƙi.


Bayan ta idar da sallah ne ta fito falo don cin abinci ta kuma sake shan magani, lokacin ne kuma ita ma Iyah ta fito daga ɗaki.Hakan yasa Kusan a tare suka isa wajen cin abincin, wanda Babah Ladi ta aje har kulolin abincin da suka dawo da shi daga asibitin.


TAIMIYYAH ta fara da bubbuɗe kulolin don ganin abinda ke ciki, sai ta ga su chips ne da akai wa haɗin sauce na musamman da liver,sai farfesun naman kaza da gasasshen naman rago da akai raping ɗinsa cikin foil paper,wani irin gashi da yayi romo-romo sai azaban ƙamshin spices ke tashi.
Nan take TAIMIYYAH ta ji gashin naman ya shiga ranta,ta ɗauki plate ta zuba kaɗan tana ɗaura jallop ɗin shinkafan da Babah Ladi tayi akai.


Iyah ganin naman ragon da ɗan yawa yasa ta zuba itama, suna ci suna santin daɗinsa,TAIMIYYAH na yabawa duk wanda yayi wannan gashin naman da cewa ƙwararrene.


Tana kammala cin abincin ɗakinta ta koma ta kunna wayarta,don tasan tabbas an nannemeta anji wayarta a kashe. Aiko tana kunna wayar bada jimawa ba kiran Yasmeen vid call ya fara shigowa,TAIMIYYAH ta ɗauka tana zama daga gefen gado ta fara da cewa, "Besty sai yanzu zaki nemeni kiji lafiya ta gaskiya nayi fishi."


Yasmeen da ke kallon fuskar TAIMIYYAH tar a wayarta ta saki murmushi tana faɗin, "Sorry Tawan kece ai kika kashe wayarki ni kuma ban kira ta line ɗin Iyah ba.Ya jikin naki ina fata dai babu wani matsala? Kawai sai muka ji wannan tsautsayi Allah ya tsare gaba TAIMIYYAH."


TAIMIYYAH ta amsa da cewa, "Ameen Yasmeen,ai abun ya zo da sauƙi ma tunda ban ji wani rauni me yawa ba,kuma nayi dace wallahi matar da driver ɗin nata ya kaɗeni me kirki ce,su suka kaini asibiti yauma kuma ta sake dawowa duba ni, baki ga abincin data zo da safe ta kawo ba,kuma har sai da aka bani sallama sannan ta tafi, gaskiya Hajiyar tana da mutunci sosai."


TAIMIYYAH ta cigaba da baiwa Yasmeen labarin yadda abin ya faru,Yasmeen ta jinjina kai tana cewa, "Allah sarki haka ne dama sai ki ga Allah ya haɗaka dana gari wani lokacin,amma ta kyauta sosai tayi abinda ya dace." Yasmeen ta cigaba da cewa, "TAIMIYYAH dama abinda ya faru tsakaninki da Yah Emran kenan shi ne baki sanar min ba,sai jiya Mamie ke bani labari kin kyauta kenan ?"


TAIMIYYAH ta ɓata fuska don ita sunansa kawai da Yasmeen ta kira sai da ranta ya ɓaci,ta shagwaɓe murya tana faɗin, "Yasmeen to ni banga anfanin sanar miki bane tunda ba abin arziƙi ne ya faru ba,wallahi ni am sorry to say na tsani jin ko sunansa ba don yana jinina ba.Ai Iyah ta sanar min wai Guggo Bilki tai masa cin mutunci sosai har da Abbah ta haɗa shi ma."


Yasmeen ta saki tsaki tana cewa, "Hmm! Wallahi abin ya matuƙar bani mamaki da ɗaure min kai,kinsan bamu taɓa sanin bad side ɗinsa ba sai da hakan ya faru, ashe shi Yah Anas dama ya san Yah Em ɗin na neman matansa,amma shi kansa cewa yayi bai san abun nasa yayi riƙan da har ke zai iya cewa zai ketawa mutunc ba,kiyi haƙury TAIMIYYAH ki yafe masa don gaskiya yayi nadama daga baya,har ni jiya ya sama da daddare yace in sake baki haƙuri wai duk kinyi blocking line ɗinsa,kiyi haƙuri ki yafe masa maganar soyayyace dai koni ban goyi baya ba,don Abbah cewa yayi ma kar ya sake jin maganar."


TAIMIYYAH ta sauke numfashi tana cewa, "Shikenan ya wuce Yasmeen,ni bama abinda ya sake ɓata min rai irin yadda ya lallaɓo yazo ya tsara Iyah wai sona yake da gaske."


Yasmeen ta saki murmushi tana cewa, "Ina ruwan shegen kaya ai ya iya tsari da kike ganinsa a miskilinnan,to ai Mamie tai masa tas tace in ma son ne na gaske ya kama zuciyarsa sai dai ya kashesa, kada ma ya sake nufo ta da maganarki tunda shi baida mutunci."


TAIMIYYAH ta ɗan saki murmushi tana faɗin, "Wayyo Guggo Bilki kice dai an masa taron dangi ne, don Iyah itama tace ta kira shi ta zazzagesa tas!"


Suka saki dariya a lokaci guda Yasmeen na cewa, "Wai ni kam ina mutanenki ne ashe Zuhurah kuma an sanya lokaci to Allah ya kaimu da rai da lafiya,ita ma Basmah ance ta samu wani za a zo a sanya lokaci ayi bikin duk gaba ɗaya ko?"


TAIMIYYAH da idanunta ke kan fuskar Yasmeen ta cikin wayarta,tayi saurin ware ido tana jin wani abu na sukar zuciyarta.Cike da dauriya tai magana tana cewa, "Haka kika ji Yasmeen? Ai ni bamma sani ba nasan dai ta samu wanin ,amma bansan maganan cewa za a sanya lokacin ba,Allah ya sanya alkhairy toh."


Yasmeen ta amsa da Ameen tana noticing yadda mood ɗin TAIMIYYAH ya canza,hakan yasa ta cewa, "TAIMIYYAH lafiya ya dai mood ɗinki na ga kaman ya canza?"


TAIMIYYAH dake ƙoƙarin danne abinda take ji na taso mata daga zuciya, sai tayi saurin duban Yasmeen ɗin tana cewa, "Yasmeen tsakaninmu babu wani maganan ɓoyo kinsan waye Basmah ke tare da shi har ake maganar za a sanya musu rana kuwa?"


Yasmeen ta girgiza kai cikin sauri, kafin ta furta, "No bansani ba waye shi ɗin ni naji abun yazo da gaggawa ne ai, ita dake complain kullum akan rashin masu kulata,waye guy ɗin da yazo cikin gaggawa haka?"


TAIMIYYAH da ke ji har hawaye ya fara taruwa a idanunta, sabida tsananin ɗacin da take a cikin zuciyarta tayi ƙarfin halin fara faɗin, "Yasmeen Nass ne fa,Nass nawa da muka rabu shine ya dawo yana son Basmah,na kasa gaya miki ne tun ranan da mu kai ido biyu da shi yazo wajenta.....


TAIMIYYAH ta kwashe yadda aka yi tana kuka ta sanarwa Yasmeen,har ta kai ƙarshe hawaye na zuba a idanunta tana jin ciwan wannan cin amana da Basmah za ta yi mata na ƙona ranta.Yasmeen da gaba ɗaya ta shiga shock! Sai ta yanko wani irin zagi tana cewa, "Kutumar ubancan kayyasa! TAIMIYYAH ko dai idon ki ne ya gane miki me kama da Nass ,amma ba dai shi Nass ɗinki dana sani ba?"


TAIMIYYAH sai tayi murmushin yaƙe cikin raunin murya take faɗin, "Wallahi Yasmeen shi na gani ganin idona ba labari aka bani ba,ni yanzu duk abinda aka ce min mutum zai yi ya daina bani mamaki,sabida na gama gane halayyar mutane yadda ta lalace kawunansu kawai suka sani,ba a maida cin amana abakin komi ba, kullum na tuna yadda dama ba sona suke ba sai inji mamakina ya ragu,amma abinda ke ɗaure min kai shine ta ina har suka haɗu da Basmah suka jone har soyayyah ya shiga tsakaninsu? Koda dai ta gaya min dama tun randa ta fara ganinsa ta ji ta kamu da sonsa,sai na tuna irin kallon da take binsa da shi tun a wancan lokacin,amma maganar gaskiya Yasmeen abin na tsananin min ciwo a zuciyata."


Yasmeen da gaba ɗaya ranta ya gama ɓaci tana ji kamar tayi tsuntsu ta zo Zaria,ta saki wani ashar ta dannawa Basmah tana cigaba da faɗin, "Kar ki damu kiyi haƙury Besty Allah zai miki kyakykyawan sakayya ne soon Insha Allah,ita kuma ƴar banzar mara kunyan ki zuba musu ido kamar yadda Iyah ta faɗi ne,aure indai na cin amana ne wallahi babu inda yake zuwa,ko yayi ƙarƙo to zaki ga ana fuskantar tarin matsaloli a cikinsa.Kuma tabbas ina ji ajikina ba haka kawai suka barsa ba, da asiri suka nemesa ko rantsuwa nayi bana ji zan yi kaffara akan hakan,haba abin da ɗaure kai amma koma miye zai fito fili komin daren da daɗewa,za mu zuba ido mu sha kallo don Allah ki cire damuwa ki barwa Allah komi, in sunyi ne don su ci amanarki su tazartaki to kansu zasu ci amana da yardar Ubangiji, ai Allah baya bacci ya kuma san manufan da ke zukatan dukkan bayinsa."


TAIMIYYAH ta sauke zazzafar numfashi tana kai hannu ta share hawayen da suka zubo mata tana me cewa, "Hakane Yasmeen wallahi ina iya bakin ƙoƙarina wajen ganin na manta cewa mun taɓa soyayya da shi,amma na kasa daina jin ciwo a cikin zuciyata duk sanda na tuno wai Basmah ce xata min haka,amma bakomi koma miye ina musu fatan alkhairy, Allah yasa rakiya tayi nisa,ni kuma Allah ya bani ƙarfin zuciyar fuskantar kowace irin jarabawa,amma soyayya ya gama fita daga kaina Yasmeen bana sha'awar in sake ɗanɗanarta."


Daga haka suka cigaba da tattaunawa akan irin yadda ƴan matan wannan zamanin suka kware wajen iya cin amana.


Lokacin da suka kammala yin vid call ɗin da Yasmeen,TAIMIYYAH sai ta aje wayarta tana sauke zazzafar numfashi,cikin zuciyarta take al'ajabin yadda rayuwa ke juya mata daki-daki,tare da fatan Allah ya bata ikon cin jarabawa,amma sam soyayya ya fita ranta baki ɗaya.


Tana cikin duba messages da ke shigowa ta online kiran Zee ya shigo wayarta.
Sai ta kashe data tana receiving call ɗin suka gaisa da Zee,TAIMIYYAH na sake tambayar Zee ɗin jikinta.


Zee ta sanar da ita cewa ta samu sauƙi,ta ɗaura da yiwa TAIMIYYAH complain akan kashe wayarta da tayi,don ta kira ta bata sameta ba.


TAIMIYYAH ta sanar da Zee ɗin tsautsayin da ya sameta bayan barowanta gidansu,Zee ta saki salati tana godewa Allah da TAIMIYYAN bata ji rauni me girma ba.Su kai sallama da juna Zee na sanar da TAIMIYYAH cewa da zaran ta sake samun sauƙi za ta zo ta duba ta.


TAIMIYYAH ta aje wayarta saman gado tana tashi ta ɗakko system ɗinta ta jona a wuta don yin chargy.Tunawa da tayi cewa Ummie ta shigo gaidata tana bacci yasa ta yanke shawaran zuwa Sasan Ummie ɗin,ta fito bayan ta zura hijab akan shigar jikinta, tama sanar da Iyah cewa za ta Sasan Ummie ta dawo.
Iyah tai mata a dawo lafiya ,TAIMIYYAH ta fito tana tafiya cikin takunta a hankali cike da tarin nutsuwa har ta isa sasan Ummien.


Bata baro sasan ba sai bayan ta idar da sallar la'asar,cikin tafiyar a hankali take takowa don komawa zuwa sasan Iyah.Kamar an ce ta ɗaga kai ta dubi sashin gate ,sai ta hango shigowar Nass cikin compound ɗin gidan daga wajen gate .
Yana sanye cikin ƙananun kaya da sukai masa mugun kyau.TAIMIYYAH sai ta tsaya cak! Kamar wacce aka saka remote control aka tsaida ta,kirjinta ya shiga bugawa da ƙarfin gaske lokacin da Nass ɗin ke cigaba da takowa zuwa cikin compound ɗin.


Akan idanunta suka gaisa da Tukur mai gadi Nass ɗin na ɗaga waya ya kai kunni alamun kiran waya zai yi. Sam hankalinsa bai kai kan inda TAIMIYYYAH ke tsaye dafe da ƙafarta ta zuba masa manyan idanunta tamkar wacce aka dasa a wajen,gaba ɗaya ta kasa koda ƙwaƙwƙwaran motsi sabida yadda take ganin komi tamkar a mafarki,so take yi ta sake tabbatarwa kanta wajen Basmah yazo a wannan karon ma ko kuwa?


Sai dai ko mintuna biyar ba a yi ba ta hango fitowar Basmah daga Sasan su, tana nufan wajen da Nass ɗin ke tsaye cikin taku na ɗaukar hankali.Nan da nan TAIMIYYAH ta ji kanta ya fara juya mata, ta shiga nanata kalmar Innalillahi wa'inna'ilaihirraju'un! Ta dinga nanata kalmar, tana ji a hankali ƙafafunta na yin sanyi lokacin da Basmah da Nass ke neman ɓacewa ganinta,suna takawa jere da juna suka nufi cikin Sasan Baba Sani.


TAIMIYYAH sai tsinci kanta da silalewa daga tsaye zuwa tsugunne ,tana jin saukar wasu irin zafafan hawaye daga idanunta zuwa kuncinta.
Ta jima haka a tsugunne bata san ma wani irin tunani zata yi ba, zuciyarta na tsananin zafi da ciwon wannan lamari da take fata Ubangiji yasa mata ƙarfin zuciyar iya haɗiye abinda take ji a cikin zuciyarta.


Da ƙyar ta iya tashi tsaye tana ji kanta na mata wani irin ciwo,ta kai hannu ta dafa guiwar ƙafarta ta fara takawa don isa sasan Iyah,bayan ta tabbatar babu ɗigon hawaye ko kaɗan akan fuskarta. Sabida bata so Iyah ta sake ganin raunin zuciyarta akan wannan issue ɗin na Nass da Basmah.


Har ta isa sasan Iyah bata daina jin nauyin da ƙirjinta yayi na damunta ba.Shiyasa tana shiga ciki bata tsaya a falo ba ta shige zuwa ɗakinta ta kwanta,tafi mintuna sha biyar tana jinyar zuciyarta kafin ta kai hannu ta janyo wayarta,ta shiga wajen da ta adana karatun Qur'ani ta kunna suratul Rahman,tana fata Ubanjigin rahama da tausayi ya sanyaya zuciyarta cikin gaggawa,idanunta a lumshe suke lokacin da daddaɗan kira'ar Abdullahil Maɗrooth ke ratsa kunnuwanta.
Hawaye suka fara sauka a hankali daga idanunta suna jiƙe pillow ɗin da kanta ke kai,a haka ta fara jin nauyin da zuciyarta yayi na raguwa a ƙirjinta ta fara taji tarin nutsuwa na shigarta, bakinta ya buɗe ta fara bin karatun a hankali cikin muryarta da yai ƙasa sosai sabida yadda zuciyarta babu daɗi ko kaɗan ........✍🏻




_Allah sarki TAIMIYYAH Insha Allah alkhairy me girma na tafe cikin rayuwarki da gaggawa.....Irin wannan cin amanar bashi da daɗi ko daga bare ne bare ɗan uwanka na jini.Allah ya baki juriya da haƙuri Zainab TAIMIYYAH inji Ɗansabo_ 😰




*Hello! Readers what about dis chapter? kun ji tausayin TAIMIYYAH ko bayan Basmah ku ke bi? Sai na ji tarin comments daga gareku son so domin Allah.* ❤️














#Ɗansabo ce#
[12/14, 10:11 PM] +234 703 769 7050: *Littafin TAIMIYYAH paid book ne,ga duk wanda ta tsincesa a kowani irin group ne,kiji tsoran Allah karki karanta sai kin biya 500 naira only.*


*Za ku iya min magana ta wannan number ɗin 08167768704, ko kuma ku turo kuɗin ku kai tsaye ta wannan account ɗin*👇🏻
0504192664 aisha ibrahim dansabo GTbank.


*Sai ku tura shaidan biyanku ta wannan line ɗin 08167768704.*


Masu turo credit za ku turo katin MTN na 500 ta wannan line ɗin 08167768704.




_*Ina ƴan kasuwa masu buƙatar a tallata muku hajar ku? Maza ku garzayo da kuɗi ƙalilan a tallata muku kayan siyarwanku sai dai kawai ku ji ana kiran waya don buƙatan sayan kayan ku,ku tuntuɓeni ta layina kamar haka 08167768704.*_


*51*


"Basmah yanzu duk wannan uban kayayyakin Nass ɗin ne ya kawo miki?"


Zuhurah ke wannan maganar tana faman zaro wasu haɗaɗɗun riguna ready made daga cikin wani bag, me tambarin sunan wajen da aka sayi kayan.


Basmah ta jinjina kai cike da tsananin murna take faɗin, "Ke dai bari wallahi duk nawa ne guda 2 na zaɓa na tura masa, kawai sai da ya zo naga ashe har guda 4 ya saya min,ai gaskiya za a je da Cweety ɗinnan nawa Yah Zuhurah,don na ga alamu har ya fi Ameeru hannun kyauta."


Zuhurah da take taji zuciyarta ya sosu sai tayi saurin tamke fuska tana faɗin, "Abin kuma har da cin fuska Basmah,ke fa baki faye kunya ba wallahi."


Basmah ta saki dariya tana cewa, "Sorry Sis ai gaskiya na faɗi amma, bayan kayannan da zai wuce 10k ya aje min,ni ganin abin nake kaman a mafarki wai ni ce namiji kewa rawar ƙafa haka?Gaskiya ko nawa Maharaxu Boka yace a biya shi bamu faɗi ba don aiki fa yaci ba kaɗan ba,wallahi ba kiga yadda duk yake susucewa idan ina kusa da shi ba,cewa yayi duk ya ƙosa ayi aurennan ko xai hutawa zuciyarsa,ranar Saturday dai magabatansa zasu zo Insha Allah."


Basmah ta kai ƙarshen maganan tana wani blushing cike da tarin farin ciki.Umma da ta fito daga ɗaki ne ta iso inda su Basmah ke zaune a falon, idanunta akan bag ɗin da Zuhurah ta zazzage kayan ciki take cewa, "Basmah har Naseer ɗin ya wuce ne,wannan kayan kuma fa?"


Basmah ta dubi Umma tana faman washe baki tace "Umma waɗannan rigunan dana ga ana tallah a IG ne nace miki na turawa Nass nace ya siya min,to shine ya zo min dasu wannan zuwa weekend da yayi,kinsan a Abuja me sai da kayan take shine ya je wajenta ya amsa bayan ya tura mata kuɗin,guda biyu fa na zaɓa amma kin ga guda 4 ya siyo."


Basmah tana maganan ne tana ɗagawa Umma rigunan tana ganin kyawunsu.Umman ta dubi Basmah bayan ta kammala gani tace, "Masha Allah,gaskiya wannan za a je da shi da alamu hannunsa a sake yake ba a dunƙule kamar na ƴan dambe ba,to ya maganan turo manyan nasa? Don ni fa na fiso ai komi gaba ɗaya tare dana Zuhurah ko na

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login