Showing 135001 words to 138000 words out of 186776 words
Chapter 46 - TAIMIYAH Book Complete Document by Ayshat Dansabo Lemu .txt
ki fita bana son wani zancen banza."
TAIMIYYAH ta shagwaɓe fuska tare da narke murya tana cewa Iyah, "Gaskiya Iyah ni dai da kin bar sa a waje,miye na wani cewa a kaisa can sasan kamar wanda ki ka sani,ko ki ka san da zuwansa, ni waima waye zai zo da yamman nan yace wani ana sallama da ni?"
Iyah ta zabga mata harara tana cewa, "Zainabu ki fita ido na,zaki tashi ki wuce ki kintsa kanki ki fita, ko sai anji kan mu ni da ke?"
TAIMIYYAH sai ta tashi tana dafa ƙafarta ta nufi hanyar ɗakinta,sai faman mita take yi a zuciyarta ,ga wani faɗuwar gaba da take ji tunda Tukur ya zo ya sanar cewa wani na sallama da ita a waje.
Wajen kayanta ta nufa ta ciro dogon Hijab red ta sanya,tsayinsa ya sauka mata har ƙasa dai dai ƙwaurinta.Ta ƙarisa gaban madubi bayan ta sanya takalmi tana gyara wuyan hijab ɗin ya zauna dai dai,ta kalli face ɗinta da babu komi a kai sai kwalli da ta sanya tun wankan safe,sai ta ɗan goga man leɓe me taushi, ta juya ta dafe guiwarta ta fara takawa don barin ɗakin.
Tana ratsowa cikin falon Iyah ta tsareta da idanu,tana kallon yadda jan Hijabin ya haske farar face ɗin TAIMIYYAN ya yi mata mugun kyau.
Manyan fararen idanunta na haskawa, da ƙyallin baƙin kwalliin da ta sanya a idanun, yana ƙara ƙawata kyawun fuskarta.
"Masha Allah! Zainabu kin yi kyau matuƙa, sai dai ki saki fuskar mana TAIMIYYAH,wannan irin ɗaure fuska kamar wacce aka ce ga maƙiyinki na jiran ki,ki sawa zuciyarki salama duk wanda ki ka ga yazo gare, ki yi fata cewa Allah sa alkhairy ne ya kawo sa,amma ba ki dinga ɓata rai kina cuskune fuska ba,kin kai munzalin aure Zainab, kuma duk masoyinki zai miki fatan kiyi auren, don shine cikar mutuncin ƴa mace, don haka ki saki ranki don Allah,ki je an bar shi yana jira tun ɗazu,zan bai wa Ladi ɗan lemu da ruwa ta kawo masa."
Iyah tayi maganar idanunta akan TAIMIYYAH da ke ta faman zumbure baki,ta dubi Iyah da muryar shagwaɓa tana cewa, "Ni Iyah wallahi tsoran fita nake yi,bana son abinda ya faru ya sake faruwa,shiyasa bani sha'awan sake kula kowa a yanzu."
TAIMIYYAH tayi maganar cikin sanyin murya sosai,wani abu na taɓa zuciyarta sosai.Iyah ta dubeta da fuskar tausayi tana cewa, "A'a Zainabu kada ki karaya komi da ki kaga ya faru da bawa muƙaddari ne,don uwar Nass ta gujeki don kina gurguwa,hakan ba shi ke nufin ba za ki samu wanda za su amsheki a yadda Ubangiji ya so ganinki ba.Ki je babu abinda zai biyo baya sai alkhairy Insha Allah."
Da wannan ƙwarin guiwar na kalaman Iyah,TAIMIYYAH ta fito daga sasan ta nufi na Ummie.Cikin tafiyarta me cike da nutsuwa dafe da guiwar ƙafarta take takawa,har ta isa cikin sasan Ummien,tana karya kwana zuwa hanyar da zai sada ta da ƙofar falon Abie ta waje.
Ta tsaya daga bakin ƙofar shiga falon, tana kallon takalmar da ke zube daga bakin ƙofar,wani irin faɗuwar gaba ke cigaba da riskar zuciyarta.
Ta yi ƙarfin halin yin sallama cikin siririyar muryarta,kafin tayi jim! Don jiran ya bata izinin shiga amma sai taji tsit! Da alamun ko sallamar nata ma da wuya idan an amsa,don bata ji alamun hakan ba ko kaɗan.
Ta sake doka wata sallamar nan ma shiru babu amsa,hakan yasa ta yin ƙundubala ta ɗaga labulen ƙofar ta sanya kanta ciki.
A.Maleek Ado dake zaune yana facing ƙofar shigowa falon,tun sallamar farko ya ji ta, ya kuma amsa a taƙaice ta yadda ba za ta iya jiyo sa ba.
Ya zubawa ƙofar shigowan idanu yana son ganin halittar da za ta kutso kanta cikin falon,don haka akan idanunsa TAIMIYYAH da ke dafe da guiwar ƙafarta tana takowa zuwa cikin falon suke.
Wani irin dokawa ƙirjinsa ke yi lokacin da take sake kusantowa cikin falon.
Maleek sai ya samu kansa da kasa ɗauke ido daga gareta, har ta samu waje ta zauna cikin kujeran da ke daura da inda yake zaune.
Amma ita TAIMIYYAH har lokacin taƙi kallon inda Maleek ɗin yake zaune, sai qamshinsa da hancinta ke shaqo mata,wanda bata taɓa jin wani mahaluki da irin qamshin ba sai yau.
Sai da ta nutsu cikin kujeran sannan ta ɗago manyan idanunta ta saci dubansa,cikin sa a shi ma na shi idanun na kanta, ba tare da ita ta san cewa yana kallonta ba.Wani irin abu ya doka a zuciyar duka su biyun, TAIMIYYAH tayi saurin janye nata idanun daga kansa,bugun ƙirjinta na ƙaruwa da sauri-sauri.
Shi ko Maleek Ado wani irin abu ne kaman tsawa,ya ji ya doka a tsakar kansa,lokacin da idanunsa su kai tozali da manyan idanun da yake cin karo dasu cikin barcinsa.Idanun da ke jefashi cikin ruɗu da tunani me tarin yawa duk lokacin da zai yi mafarki ya gansu a cikin baccinsa,bai san lokacin da ya miƙe tsaye yana sake tsareta da manyan idanunsa ba.
Jikinsa har wani irin shaking yake, na tsananin shiga ruɗu da kiɗima,ya shiga takawa a hankali don isa gaban TAIMIYYAH, wacce ta sunkuyar da kanta ƙasa,tana ji kaman ana sanya igiya ana ɗaure dukkanin jijiyoyin jikinta ne.
Har Maleek ya iso gare ta, bata sani ba sabida kanta na duƙe a ƙasa ne,sai da ta ji ƙamshin turarensa yayi yawa a hancinta,sannan ne ta ɗago manyan idanunta ,don tabbatar da ko shi ɗin ne ya taho kusa da ita,aiko sai karaf idanunsu suka sake harɗewa da juna.
Wani irin faɗuwar gaba ya sake ziyartan zuciyar Maleek Ado,wanda ke tsaye kyam a gabanta,ganin zata sake maida kanta ƙasa ,yasa yayi gaggawar kai hannu ya riƙo fuskarta baki ɗaya a tafukan lallausar fatar hannunsa.
Lamarin da ya girgiza zuciyar TAIMIYYAH,tare da haifar da matsanancin faɗuwar gaba daga ƙirjinta,tayi gaggawar lumshe idanunta jikinta da zuciyarta na wani irin rawa.
Maleek Ado da yake jin tamkar an tsaida gudun jini daga jiyoyin jikinsa,sai yayi azamar sakin face ɗin nata yana ƙoƙarin riƙe kansa.Gaba ki ɗaya kansa yayi wani irin kullewa na ban mamaki,babu tamtama ko kokonto wannan gurguwar da ke gabansa, irin idanunta yake gani kullum cikin mafarkinsa,wanda ba a taɓa nuna masa zahirin face ɗin ba illah waɗannan manyan fararen idanun kawai.
Jikinsa ya yi wani irin sanyi ƙalau, har kuma lokacin yana tsaye a gaban TAIMIYYAH ya kasa motsawa,sai da yaji ƙafafunsa na neman kasa ɗaukar gangar jikinsa, sannan ya lalubi kujeran da ke kusa da ita ya zauna, yana me kai hannu ya dafe goshinsa da hannuwa bibbiyu.
Ya lumshe idanunsa zuciyarsa na cigaba da tariyo masa, yawan mafarkan da ya dinga yi da idanun Yarinyar da ya kasa tantance wacece ita? Sai gashi yau ya ga irin idanun sak akan fuskar wannan gurguwar da Hajjah ta turo sa zuwa wajenta.
Yayi saurin buɗe idanunsa ya sake zubawa TAIMIYYAH,wacce ta kasa ɗagowa bare ta sake dubansa,gaba ɗaya itama zuciyarta ta shiga mummunan yanayin da ba za ta iya fassarawa ba.
Ƙamshinsa da laushin tafukan hannayensa da suka sauka akan face ɗinta,ke sake jefa zuciyarta cikin wani yanayi,jin shiru bai sake wani motsi ba yasa ta ɗago kanta ta saci dubansa ƙasa-ƙasa.
Idanunta su kai masa kallon sakanni kwanyarta na yaba haɗuwarsa.Tayi gaggawar ɗauke ganinta daga garesa, lokacin da idanunsu ke son sake shiga cikin na juna,sai ta buɗe baki cike da ƙarfin hali ta gaida shi.
Memakon ya amsa sai ya cigaba da zuba mata idanu,tasirin abinda yake ji a zuciyarsa na sake hauhawa kamar farashi.Zuwa wani lokaci can ya sauke wata zazzafar numfashi ,yana cigaba da kallon yadda TAIMIYYAH tayi ƙasa da kanta sosai,kamar wacce take jira yace ket...! Ta arce da gudu,sai ya buɗe baki cikin ƙasaitacciyar muryarsa yace, "Zaynabb! Ɗago idanunki ki kalleni please..!"
Yadda ya faɗi sunanta, da yadda muryansa ke fita cike da aji da ƙasaita,yasa TAIMIYYAH ta ɗago kanta,tare da sanya idanunta cikin nasa.Maleek ya yi saurin sake xubawa kwayar idanun TAIMIYYAH ido, zuciyarsa na cigaba da girigiza da tarin al'ajabi da shiga ruɗu,ya janye nasa idanun tare da lumshesu yana kiran sunan Allah a hankali.
Abinda ya yi matuƙar baiwa TAIMIYYAH mamaki da shiga ruɗu kenan,ta dinga mamakin yadda duk ya wani birkice,tun daga shigowarta cikin falon.Sai ta tashi tsaye tana dafe guiwar ƙafarta don ficewa daga ɗakin ta bashi waje, ko ita ma zata daina jin abinda take ji daga cikin zuciyarta,amma sai amon muryarsa a dake ya tsaida ita, inda yake faɗin,
"Koma ki zauna."
Babu musu ta koma ta zauna, tana jin tamkar ta ɗaga waya ta kira wani ya zo,don ya zauna a tsakaninsu,sabida ta fara tsorata da lamarin wannan mutumin,wanda kallo tayi masa ta ji kwarjininsa ya cika ɗakin baki ɗaya.
Maleek Ado ya fara da cewa, "Zaynabb sunana Abdulmaleek Ibrahim Ado,na kawo kaina gareki ne don mu ga juna,kuma ina fata zaki bani dama don sanin cikakken asalinki, koda a taƙaice ne."
Yadda ya yi maganar yana tsareta da manyan idanunsa,ya hana TAIMIYYAH dubansa cikin ido,amma gaba ɗaya sai ta ji duk wani musu da take son yi masa ta kasa.
Ta buɗe baki cikin sanyin muryarta me daɗin amo tace, "Sunana Zainab kamar yadda naji ka faɗi,wanda hakan ke nuna kasan sunan tun kafin ka iso zuwa gareni, zan so sanin manufarka na takowa har zuwa gidanmu."
Maleek da ya tsura mata ido yana kallon kyakykyawar fuskarta da ke cikin hijab,sai ya sake haɗe miskilalliyar face ɗinsa ,yana cigaba da ƙarewa kwayar idanunta masu haske kallo,wanda yake ji tamkar ya shekara dubu yana ganinsu ,sabida shi karan kansa ba zai iya irga adadin yawan mafarkan da ya dinga yi da waɗannan idanun ba,ba zai iya irga sau nawa ya ji irin wannan sassanyar sautin na rera masa kuka a cikin baccinsa ba.
A hankali kuma ya buɗe baki yana cewa, "Ba wannan ne abinda ya kamata ki buƙaci ji daga gare ni ba Zaynabb,koma miye ina wa Allah godia daya nuna min wani abu game da ke a zahiri.Yanzu sauri nake yi amma zan dawo idan na sake samun time, za mu yi waya sai kiji duk abinda kike son ji daga gareni ɗin."
Daga haka Maleek yayi shiru, idanunsa akan TAIMIYYAH wacce ta kwaɓe face tamkar zata saki kuka.Ta ɗago manyan idanunta ta sauke akansa tana cewa, "Ni dai don Allah kafin kabar nan,ka taimaka ka sanar dani wanda ya turo ka zuwa gare ni please!!"
Yadda tayi maganar cike da magiya, ya sanya maleek saurin miƙewa tsaye,don muryarta da idanunta ba ƙaramin kiɗima zuciyarsa suke yi ba.Yana ji tamkar yayi tsuntsune a yanzu ya gansa a gaban Hajjah,don ya sanar mata cewa Yarinyar da ake nuna masa idanunta cikin mafarkinsa,ita ce ta turosa zuwa gareta,ita ce Yarinyar da ya jima yana jin sautin kukanta,da irin dai wannan muryar da yake ji a yanzu,hakan na nufin ita ce wannan gurguwar dake gabansa.
Ya buɗe baki zai yi magana kenan, Babah Ladi ta shigo hannunta riƙe da tray, da aka ɗauro ruwa da lemun kwali na 5alive akai.Ta aje tray ɗin akan table dake tsakiyar falon, tana gaida Maleek da ke daga tsaye.
Ya amsa a gajarce yana zaro wayarsa da kira ya shigo, ya ɗauka ya yi receiving ya kai wayar kunni.
Babah Ladi ta fice daga falon, tana jinjina ƙasaitan wannan kyakykyawan ingarman najimin da ta baro a falon Abie.
Tana me tambayar kanta inda TAIMIYYAH ta samo wannan haɗaɗɗan mutumin, ma'abocin kyawu da ƙasaita tamkar jinin sarakai.
Har ta isa sasan Iyah mamaki bai bar kwanyarta ya huta ba.
Daga can falon Abie kuwa, Maleek ne yake amsa wayar da aka kirasa,yana magana cikin harshen nasara wanda ba za ka taɓa cewa ya ji hausa ba, idan ka ji yadda yake zubo tatacciyar turanci.
TAIMIYYAH sai ta samu daman ƙare masa kallo cikin tsanaki.Tana mamakin ta yadda haɗaɗɗan mutum kamarsa zai kawo kansa wajenta,tarin tambayoyi na cika kwanyarta.
'Waya turosa? Kuma wani manufa suke da shi akanta? Waɗannan sune tambayoyin da suka ɗarsa tsoro da rashin yadda a zuciyar TAIMIYYAH, game da wannan miskilin haɗaɗɗen mutumin dake gabanta.
Tayi gaggawar ɗauke idanunta daga kallonsa ,lokacin da ya sauke wayarsa daga kunni,yana ƙoƙarin maido hankalinsa gareta.
Ya yi mata kallo biyu yana fara takowa zuwa gareta,ya tsaya daf da ita sosai tamkar me shirin faɗawa kanta.Hakan yasa TAIMIYYAH sake shigewa cikin kujeran sosai,ƙirjinta na faman bugawa da ƙarfi ,cike da tsoro da mamakin ƙarfin halin wanna mutumi.
Maleek ya cigaba da kallonta kafin ya furta, "Zaynabb zan wuce, sai mun yi waya ki gaida mutan gidan,zan aje saƙo ki baiwa wannan Babar da ta fita yanzu kinji?"
TAIMIYYAH ta dubesa sau ɗaya, tana saurin ɗauke idanunta daga dubansa,ganin irin mayen kallon da yake bin face ɗinta da shi.
Ta zumbure baki kaɗan,tana gyaɗa masa kai ba tare da tayi magana ba.
Hakan yasa Maleek ja baya kaɗan,yana nuna mata hanya yace, "Oya mu je ina so ki fara yin gaba ,don na ga tsorona kike ji kada in gudu da ke ko?"
Yadda yayi maganar cikin ginshira, face ɗinsa a haɗe yasa TAIMIYYAH sake kwaɓe fuska.Ta buɗe baki murya can ƙasa take cewa, "Ok sai anjima,amma kabar abinka bama sai ka bata komi ba."
TAIMIYYAH tayi maganar tana ƙin kallon face ɗinsa,don jikinta ya gama bata idanunsa akanta suke,sai kawai ta dafe guiwar ƙafarta,ta fara tafiya don ficewa daga falon.
A.Maleek ya sarƙafe hannuwansa a ƙirji, yana zubawa tafiyarta idanu,wani irin yanayi na gewaye ilahirin zuciya da gangar jikinsa.
Har ta fice daga falon bai iya ɗauke idanunsa daga gare ta ba,kamar yadda bai fasa jin tasirin abinda yake ji na zagaye zuciyarsa ba.Sai ya saki hannuwansa, yana zura ɗaya hannun cikin aljihu,ya irgo kuɗin da baisan adadinsu ba, ya taka zuwa wajen da Babah Ladi ta aje tray ɗin,ya ɗaura kuɗin akai yana juyawa ya fara takawa don fitowa daga falon.
Can nesa ya hangi TAIMIYYAH tana takawa, cikin tsarin tafiyarta da ya taɓa zuciyarsa.Ya cigaba da takowa shi ma idanunsa nayi mata rakiya, har ta karya kwanar shiga sasan Iyah,kaman kuma ta ji ajikinta yana biye da ita da idanunsa,sai ta ɗan dakata daga tafiyar,tayi tsaye dafe da guiwar ƙafarta ta waiwaya ta dubi bayanta,karaf sai idanunta ya sauka akan Maleek ɗin, wanda yake ta kallo direction ɗin da take.
TAIMIYYAH sai tayi saurin ɗauke kanta, tana hanzarin cigaba da takawa ta shige cikin sasan su.Maleek Ado bai san lokacin da murmushi ya ƙwace a saman face ɗinsa ba,ya cigaba da takawa ya nufi hanyar gate ɗin gidan,yana ji tamkar ya bar wani ɓangare da ke tuno masa da mafarkansa na baya ne,wanda ada ya dinga ɗauka cewa aljanace yake ta mafarki da idanunta, ashe ba aljana bace mutum ce kamar kowa.
Bai gane hakan ba sai yau da ya yi arba, da irin idanun da yake gani cikin mafarkinsa, akan fuskar wannan kyakykyawar gurguwar.
Ya fice daga gate ɗin gidan bayan ya baiwa Tukur kyautan kuɗi me yawa,sai faman zuba godia Tukur yake yi har Maleek ya yi nisa da barin bakin gate ɗin.
Tukur ya turmutsa kuɗinsa a aljuhu, yana me addu'an Allah ƙullah alkhairy tsakanin wannan ƙasaitaccen mutumin da TAIMIYYAH........✍🏻
#Ɗansabo ce#
[12/14, 10:12 PM] +234 703 769 7050: Littafin TAIMIYYAH paid book ne,ga duk wanda ta tsincesa a kowani irin group ne,kiji tsoran Allah karki karanta sai kin biya 500 naira only.
Za ku iya min magana ta wannan number ɗin 08167768704, ko kuma ku turo kuɗin ku kai tsaye ta wannan account ɗin 0504192664 aisha ibrahim dansabo GTbank.*
*Sai ku tura shaidan biyanku ta wannan line ɗin 08167768704.*
Masu turo credit za ku turo katin MTN na 500 ta wannan line ɗin 08167768704.
_Ina ƴan kasuwa masu buƙatar a tallata muku hajar ku? Maza ku garzayo da kuɗi ƙalilan a tallata muku kayan siyarwanku sai dai kawai ku ji ana kiran waya don buƙatan sayan kayan ku,ku tuntuɓeni ta layina kamar haka 08167768704._
*56*
"Zainab me yafaru kika shigo kika zabga uban tagumi haka,har baƙon na ki ya wuce ne?"
Iyah ce ke tambayar TAIMIYYAH, lokacin da ta fito daga ɗaki, ta tadda TAIMIYYAH zaune a falo,ta rafka uban tagumi.
TAIMIYYAH ta ɗago manyan idanunta, ta sauke akan Iyah tana cewa, "Iyah ya tafi bada jimawa ba."
Iyah ta zauna daga cikin seater,har lokacin idanunta na kan TAIMIYYAH,wacce gabaki ɗaya kanta yake a kulle da al'amarin Maleek, wanda ba ta san daga ina yake ba.
Iyah tayi gyarar murya ta ce, "Zainab daga ina baƙon naki yake,kuma me ya kawosa zuwa gareki ina fata alkhairy ne?"
TAIMIYYAH tayi ƙwal-ƙwal da ido tana duban Iyah ta ce, "Iyah bansan me zan faɗi miki akansa ba,don ni ma sunansa kawai ya sanar da ni,sai kuma ya ce wai yazo ne kawai ya ganni,amma zai dawo idan ya sake samun time.Iyah baki gansa bane da alamu babban mutum ne daya mallaki iyali,kallo ɗaya na yi masa na gane hakan,daga yanayin kwarjini da kamewarsa.Sai dai kaina a kulle yake, sabida yadda ya dinga nuna kamar dama can, ya daɗe da sanina a wani wajen,amma kuma yaƙi sanar dani dalilin kawo kansa zuwa gare ni,Iyah ina jin tsoro me tsanani yana lulluɓe zuciyata,ina ji a jikina kamar wannan mutumin, yafi ƙarfin ya kawo kansa zuwa gareni,akwai wani abu da yake ɓoyewa."
TAIMIYYAH tana maganar ne cikin tsananin sanyin murya,wanda hakan ya sanya Iyah zuba mata ido har ta kai aya,kafin ta buɗe baki tana duban TAIMIYYAH cikin ido ta ce, "Zainabu ki nutsu don Allah,babu komi In sha Allah,koma miye za mu ji daga garesa, tunda yace zai dawo,to sai mu jira dawowar na sa aji meke tafe dashi?Amma yanzu ki nutsu ki cire duk wani tsoro daga cikin zuciyarki,in ma bada alkhairy yake tafe ba,sai muyi addu'a kada Allah ya bashi ikon dawowar ma."
TAIMIYYAH sai ta ɓata fuska ta dubi Iyah ta ce, "Shikenan Iyah,bari in shiga daga cikin ɗaki,idan Ayuba ya shigo ya je ya ɗakko abinda Babah Ladi ta kai, bai ma sha komi ba."
Daga haka ta miƙe tana dafe da ƙafarta ta nufi ɗaki,Iyah tabi bayanta da kallo tana jin wani abu na motsawa a zuciyarta game da TAIMIYYAH.
Babah Ladi Iyah ta sanya ta koma can falon Abie, ta ɗakko tray ɗin da ta kai ruwa da lemun.Sai da Babah Ladi ta kawo ne aka ga kuɗin da Maleek ya aje masu yawa,sai tashin ƙamshinsa kuɗin suke yi.
Iyah ta ciri murya ta kira TAIMIYYAH, wacce ta ƙule a cikin ɗaki,tana kwance tunani ya dabaibaye kwanyarta.Jin kiran Iyah ya sanya ta fitowa daga ɗakin zuwa falo,ta yi tsaye daga kusa da Iyah tana cewa, "Iyah gani."
Iyah ta tsura mata ido, tana nuna kuɗin