Showing 54001 words to 57000 words out of 186776 words

Chapter 19 - TAIMIYAH Book Complete Document by Ayshat Dansabo Lemu .txt

15 Dec 2024

6590

inyi bacci kinji Baby Luv?" Ya ƙare maganan cikin narke murya,yana ji kaman kada ya tafi ya bar wannan kyakykyawar halittar da ta gama sace zuciyansa.
Sai dai babu yadda ya iya haka ya aje mata kuɗin daya ciro daga aljihunsa,a saman Tray ɗin da Yasmeen ta aje,yana faɗin "Baby gashi nan ba yawa ki sayi Recharge Card."


Duk iya magiyan da TAIMIYYAH tayi akan ya ɗauki kuɗinsa, sam bai saurareta ba.Tana ji tana gani ya bar wajen ya nufi hanya isa gate,idanunta biye da bayansa tana kallon yanayin tafiyansa abin birgewa.


Zama tayi bayan ta ga fitansa,tana tunanin yadda za ta yi da kuɗin daya aje.Daga ƙarshe haka ta miƙe tana ɗaukan Tray ɗin da hannu ɗaya,ɗaya hannun na dafe da guiwan ƙafanta mara lafiyan,ta fara takawa don komawa cikin gida.


Sai dai ko taku biyar bata yi ba qamshin turaren BENTLEY ya fara isowa hancinta.Tayi saurin ɗaga manyan idanunta tana duban Yah Sadeeq daya ƙariso inda ta yi tsaye cak! Sai ta lumshe ido tana ji tamkar ta saki Tray ɗin dake hannunta.
Don wani irin faɗuwan gaba ne ya ziyarce ta da bata san daliliba.Kafin tayi wani motsi sai hannuwansa ta gani akan nata hannun da ke riƙe da Tray ɗin da ta ɗakko.Cikin wani disashshan murya yake faɗin,


"Muje part ɗina ina son magana da ke."


Daga haka yai gaba abinsa,hannunsa riƙe da Tray ɗin da ya amshe daga hannunta.Sai ya bar TAIMIYYAH da bin bayansa da kallo,tana rasa yadda zata yi,don haka kawai take ji ba ta son binsa.
Sabida ko bai faɗi ba ta san akan Nass ne zai titsiyeta ta faɗi masa lokacin da fara tsayawa zance da shi.


Ganin ya dakata daga tafiyan tare da waiwayowa yana dubanta.Yasa TAIMIYYAH fara takawa tana bin bayansa,har suka isa ɓangarensa,ya saka key ya buɗe ƙofan shiga falon nasa,yana ja baya kaɗan tare da nuna mata hanya alamun ta shiga.TAIMIYYAH jiki a mace ta raɓa shi ta shige,ya rufa mata baya hancinsa na shaqo sassayan qamshin da ke fita a jikinta,ya maida ƙofan ya rufe ba tare da ya saka key ba.


Daga hannun kujeran da ke facing ƙofan shigowa falon nasa,TAIMIYYAH ta ɗan ɗosana mazaunanta.
Kanta a ƙasa tana wasa da zoben azurfa dake yatsanta na hagu.Sam ta kasa kallonsa sai wani irin bugawa zuciyarta keyi ba bu ƙaƙƙautawa,shi ko Yah Sadeeq kallo ɗaya yai mata ya gane ba ta cikin nutsuwa.Hakan yasa shi sake haɗe fuska yana faɗin "Malama zama sosai za ki yi,ko nan ɗin baƙon kine da zaki wani zauna a hannun kujera kaman na ce zan cinyeki?"


Ya kai ƙarshe maganan cikin masifan da baima san zai iya ma TAIMIYYAN ba.Abinda ya sake tsorata TAIMIYYAH tayi saurin kallonsa,idanunta suka shige cikin nasa idanun,sai tayi saurin ɗauke kanta hawaye na taruwa a idanunta.Ta gyara zama sosai a cikin seatern muryanta na rawa take faɗin "Yah Deeku please! Bacci nake ji don Allah ka barni na koma gida." Wani harara da Sadeeq ɗin ya jefa mata yasa TAIMIYYAH saurin kauda kanta daga dubansa.Ji take yi tamkar ta saki kuka kawai ko zai barta. Amma memakon hakan sai gani tayi ya taso ya dawo kujeran da take kai na 1 seater ga zauna.
Ƙirjinta ya buga da wani irin ƙarfi lokacin da taji hannuwansa duka a jikinta,ya ɗaga ta cak! Ya zaunar saman hannun kujeran,shi kuma ya zauna daga ciki sosai yana crossing duka leg ɗinsa.
Hannuwansa riƙe da nata yana zuba mata manyan idanunsa.Da suka daɗe da canza launi ,sabida azaban kishin Nass dake cin zuciyansa,yayi magana cikin wani murya very low,


"Zaynab sanar dani waye shi? A ina ku ka haɗu kuma yaushe har ki ka ba shi zuciyanki?"
Sadeeq ya watsawa TAIMIYYAH tambayan.har lokacin yana riƙe da hannunta bai saki ba,yanayin da yai masifan ɗaga hankalin TAIMIYYAH da jefata cikin ruɗu.Don kusancin na su da juna yayi yawa matuƙa.Kuma yau ɗin shine karon farko da hannuwan Sadeeq ɗin suka ratsa jikinta,shiyasa gaba ɗaya ta firgice,daga zuciyanta har gangar jikinta rawa suke.
Matsanancin tsoro da fargaba ya hana ta duban idanunsa.Saima kuka da ta sakin masa da ƙaramin sauti,cikin muryan kukan take faɗin,


"Yah Deeku please ka sakeni zan gaya maka koma me kake son ji please!"


Ta ƙare maganan tana kuka sosai,hakan yasa Sadeeq sake hannunta,yana zuba mata mayun idanunsa,yake faɗin,


"Ina jinki Zaynab."


TAIMIYYAH ta sauke ajiyan zuciya,tare da sanar da shi komi.Tun daga randa Nass ɗin ya fara zuwa gidan,har kawo wayan da su ke yi da yadda Iyah ta matsa sai ta fita,duk bata ɓoye masa komi ba.Ta ƙare maganan da faɗin "Yah Deeku ni Allah ba ni ce na janyosa ba,kuma ina sauraransa ne sabida bana so Iyah tai fishi dani.Baba kuma yaga kaman naƙi jin maganansa na cewa infito da wani,amma ni sam babu ma Soyayyah a lissafina, sai karatu kaima kasani ai,amma kayi haƙury in ranka ya ɓaci please!"


Yadda take bashi haƙury tana kuka ne ya sake karya zuciyan Sadeeq.Wani irin soyayyanta ya motsa masa wanda har ya kasa controlling kansa,ya janyota jikinsa baki ɗaya ya rungumeta.Abinda ya tsaida bugun zuciyan TAIMIYYAH cak! Jikinta ya ɗauki wani irin rawa,kafin ta fashe masa da kuka lokacin da take jin kansa bisa kafaɗunta.Yana sauke wani irin numfashi kaman wanda yayi gudu,gaba ɗaya qamshin turarensa ya gama cika kafofin hancinta.Cikin muryan kuka take faɗin "Yah Sadeeq don Allah ka sakeni,kasan dai haramun ne hakan da kayi ko? Pleas......" Maganan TAIMIYYAH ya maƙaleni ne lokacin da Sadeeq ya sake shigar da ita jikinsa sosai,yana ƙoƙarin haɗe bakinsu waje ɗaya.Gaba ɗaya huɗuban da sheɗan ke masa ne ke aiki,don burinsa bai wuce yayi duk abinda zai bashi relief ba.Sai dai kukan da TAIMIYYAH ta saki me tsananin ƙarfi ne yasa shi janye fuskansa daga gareta,yana maida kansa ya kwantar bisa kafaɗunta,dukkaninsu jikinsu rawa yakeyi bama kaman TAIMIYYAH, da ke ji numfashinta na yin sama.
Cikin wani irin murya Sadeeq yake faɗin "Zaynab bansan ta yadda zan sanar dake nakasa cire soyayyanki daga cikin zuciyata ba.Bansan cewa duk iya ƙoƙarin da nake na danne feeling ɗina akanki shirme nakeyi ba,sai yau da dana ganki da wani namiji bani ba.Please! Zaynab mu ture duk wani ƙiyayyan da Umma ke miki,ki amince in samu Baba Sani in gaya masa muna son junanmu.Nayi miki alqawarin kare ki daga duk wani cutarwa ko tsangwama.Domin bazamu zauna anan ba bare har Umma ta ganki tai miki abinda ranki zai ɓaci,please Zaynab ki amince dani bazan iya kallo wani namiji ya aureki alhali ni zuciyata na azabtuwa da soyayyarki."


Sadeeq yayi maganan har lokacin TAIMIYYAH na jikinsa,yai mata wani irin runguma da ta kasa kwacewa.Kuka kawai takeyi me tsuma zuciya,amma Yah Deekun da alamu sam hakan baya damunsa.Cikin kuka take faɗin "Ka sakeni tuh sai muyi magana Yah Sadeeq please!"


Bai yi musu ba ya saketa tai baya tana zamewa ta sauka daga kujeran.Kaman yasan shirin da takeyi na son ta gudu,sai yayi saurin riƙo hannunta yana tsareta da rinannun idanunsa.TAIMIYYAH tayi saurin faɗin "Yah Sadeeq don girman Allah ka barni in tafi lokaci na tafiya,zamuyi magana gobe nayi maka alqawari." TAIMIYYAH tayi maganan cike da magiya,dukkanin jikinta rawa yake burinta bai wuce ta ganta a Sasan Iyah ba.


Kafin Sadeeq ɗin yace wani abu aka buɗo ƙofan shigowa falon nasa haɗe da yin sallama.Muryan Zuhurah ce ta shigo kanta tsaye tana sauke idanunta akan su TAIMIYYAH.Ta wani waro ido tsananin mamaki na cika zuciyanta,tuni TAIMIYYAH taji maranta yai wani irin ƙullewa,tana jin lokacin da fitsari ya zuba cikin pant ɗinta.Tsabagen yadda ta ruɗe da ganin irin kallon da Zuhurah ke jifanta dashi.Da ƙarfin gaske ta kwace hannunta daga nasa hawaye masu tsananin zafi na sake ɓalle mata.Dukkanin jikinta babu inda baya rawa sabida tashin hankali,shiko Sadeeq rinannun idanunsa ya ɗago ya sauke akan Zuhurah dake tsaye daga bakin ƙofan,ta zubo musu ido.


Yayi magana cikin ɓacin rai yana faɗin "Uban me kika zo yi,da zaki shigo min ɗaki ba tare da an baki iziniba,sabida ke daƙiƙiyace ko?" Ya ƙare maganan da dakawa Zuhurah tsawan daya sake ruɗa TAIMIYYAH ta sanya masa kuka.Zuhurah ko ta wani kyaɓe fuska tana faɗin "To ai Umma ce tace inzo in kira mata kai,don ta kira wayanka har sau uku baka ɗaga ba."


"Get out! Stupid kawai,idan kinje kuma ki gaya mata cewa kinga wani abu,kiga idan ban ɓaɓɓalaki ba!" Yah Sadeeq ɗin yayi magana a fusace idanunsa akan Zuhurah data juya da sassarfa tana barin ɗakin.TAIMIYYAH da gaba ɗaya ta rasa inda zata sanya kanta,itama sai miƙewa tayi tana saurin dafa ƙafatan zata fara tafiya,amma sai Yah Deekun yayi saurin isowa wajenta yana kama hannunta.Ta ɗago manyan idanunta da hawaye suka kasa daina zuba,cikin muryan kuka take faɗin "Kaga abin da ka janyo min ko Yah Deeku? Yanzu Allah ne kaɗai yasan abinda zata je ta gayawa Umma,shikenan na shiga uk....." Hannun da Sadeeq yakai bakinta yana faɗin "Shihhshhhh..!" Shiya katse TAIMIYYAH daga ƙarisa maganan data faro,cikin low voice yake faɗin "Babu abinda zai faru Zaynab calm down please! Muje in rakaki,amma ki sani duk abinda na faɗi da gaske nake yi.Bazan iya haƙura da soyayyarki ba Zaynab,don haka ki fara koyawa zuciyanki yadda za ta so ni,ki kuma dakatar da wancan gayen bana son in sake ganin ku tare."


Yadda ya ƙare maganan cikin wani irin murya,ya tabbatarwa da TAIMIYYAH cewa duk abinda yake faɗi da gaske yake yi,sam babu alamun wasa ko kaɗan.Ita dai TAIMIYYAH burinta kawai ta ganta a Sasan Iyah shine kawai samun nutsuwanta,don haka sai kawai ta gyaɗa masa kai ba tare da tayi magana ba.


Hannunta cikin nasa suka fito daga ɗakin nasa,kobi ta kan Tray ɗin lemu da ruwan TAIMIYYAH bata yi ba,bare har ta tuna da wani kuɗin da Nass ɗin ya bata.Sai da Sadeeq ya ga shigan TAIMIYYAH cikin Sasan Iyah,sannan ya juya yana nufan hanyan Sasan su,don amsa kiran Ummansa.


TAIMIYYAH dake tafiya cikin wani irin slow motion,gaba ɗaya jikinta a sanyaye yake.Zuciyanta na tsananin bugawa da tsoron abinda zai je ya dawo,don tasan tabbas sai Zuhurah ta sanar da Umma cewa ta ganta a wajen Sadeeq.Ba kuma zata rage komi akan yadda idanuwanta ya gane mata su sarƙe da hannun juna ba,har ta shiga cikin falon Iyah bakinta ɗauke da sallama,zuciyanta babu nutsuwa sam.Da idanun Guggo Bilki ta fara cin karo lokacin data sanya kai cikin falon,sai tayi saurin yin ƙasa da kanta tana takowa cikin falon.Tana shirin gota su ta wuce muryan Iyah dake zaune tare da Guggo Bilkin ya shiga kunnuwan TAIMIYYAH ,Iyah na faɗin "Sai yanzu ne ya tafi Naseerun?" TAIMIYYAH bata jiyo ba ta gyaɗa kai kawai tana yin gaba,domin bata son yin magana bare Iyah ta gano akwai matsala.Daga Iyah har Guggo Bilki suka bi bayan TAIMIYYAH da kallo,Iyah na faɗin "Anya lafiya Bilki,naga duk tayi wani sanyi ne gashi ta jima bata shigo ba." Guggo Bilki ta dubi Iyah tana faɗin "Lafiya lau Iyah,ai kinsan dama bata so fitanba,watakila daɗewan da yayin ne ya bata haushi."


Iyah sai ta saki rai tana faɗin "Hakane fa kuma,to shine kuma tabar min faranti a waje sabida taɓara,to ai sai ki kira Yasmeen ta je ta ɗakko min."


TAIMIYYAH kuwa tana shiga ɗaki toilet ta nufa direct.Yasmeen dake kwance akan gado tana kallo a System ɗin TAIMIYYAH,sai tabi bayan TAIMIYYAN da kallo kawai.


Lokacin da TAIMIYYAH ta fito kan gadon ta nufa tana aje Hijab ɗin data cire shi tun a toilet.Tayi kwance kawai tana lumshe idanunta ba tare data kula Yasmeen dake ta faman binta da kallo ba,ganin haka yasa Yasmen danna pause tana ture System ɗin gefe ɗaya.Ta matsa kusa da TAIMIYYAH da tayi rub da ciki tana faɗin "TAIMIYYAH lafiya,meyafaru?"


TAIMIYYAH kaman jira take Yasmeen tayi magana sai kawai ta saki kuka,tana gayawa Yasmeen ɗin abinda duk ya faru a part ɗin Yah Sadeeq.Sai dai ta ɓoye mata cewa ya rungumeta,ta taƙare maganan da cewa "Yasmeen bansan da wani fassara Zuhurah zatai min ba,ban kuma san iya abinda zata gayawa Umma ba.Sannan bansan me zan cewa Iyah ba idan ta tambayeni yadda akayi har na biye masa naje ɗakinsa,ni dai Yah Sadeeq na son jefani cikin masifa Yasmeen."


TAIMIYYAH ta ƙare maganan tana sake sakin kuka sosai.Hakan yasa Yasmeen fara lallashinta tana kwantar mata da hankali,akan cewa babu abinda zai faru ai Zuhuran na tsoran Yah Deekun bazata sanar da Umma komi ba.Da wannan lallashin na Yasmeen TAIMIYYAH ta ɗan kwantar da hankalinta,amma har suka kwanta bacci ta rasa wani irin tunani zatayi akan zancen Yah Sadeeq.Na cewa ta rabu da Nass ɗin,ita dai tasan ko sama da ƙasa zasu haɗe ba zata iya auren Yah Deekun ba,sannan kuma bata san ta yadda zata iya koran Nass wanda a yanzu ta fara jin zuciyanta na nutsawa dashi.......✍🏻






Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/FAuxFVUMsQhHYfF5qiGklY




Littafin TAIMIYYAH paid book ne da zai zo akan 500 naira only,ga masu buƙatan yin payment zakui min magana ta wannan number ɗin 08167768704, ko kuma ku turo kuɗin ku kai tsaye ta wannan account ɗin 0504192664 aisha ibrahim dansabo GTbank.*


*Sai ku tura shaidan biyanku ta wannan line ɗin 08167768704.*






#Ɗansabo ce#
[12/14, 10:05 PM] +234 703 769 7050: *TAIMIYYAH*❤️


©️Ayshat Ɗansabo Lemu✍🏻


*Page 30*


Yasmeen wani takaicin TAIMIYYAH ne ya kamata,da har zata zo ta kwanta tana rasgan kuka.Bata ci kutumar uban Zuhuran ba,cike da masifa ta dubi TAIMIYYAN tana faɗin, "Bama dole su rainaki ba tunda kin kasa kifa mata mari,kin wani zo kina faman kuka kaman wata wawiya mitsuuuw...!"
Yasmeen ta ƙare maganan tana juyawa fuu...! ta fito daga ɗakin TAIMIYYAN ta nufi ɗakin Iyah.


Iyah na zaune bakin gado,tana gyaran tarkacenta da ke cikin kwallah.Sai ganin Yasmeen tayi akanta tana faɗin "Iyah taso mu je kiga TAIMIYYAH,yadda ta kifa ciki tana faman kuka,kaman ance kece kika mutu,sabida kawai waccar mara mutuncin ta kirata wai karuwan Yah Sadeeq."


Iyah ta dafe ƙirji tana waro ido take duban Yasmeen, tana faɗin "Karuwa kuma ni Fatuh! Me waɗannan yara suke so su zama ne? To uban me ta kamasu suna aikatawa da zata kirata da wannan jafa'in?" Iyah tana maganan ne tana bin bayan Yasmeen da tai gaba abinta.


Lokacin da Iyah suka shigo ɗakin TAIMIYYAH har lokacin kuka take yi.Iyah ta ƙanƙance ido tana duban TAIMIYYAN,cike da bada umurni take faɗin "Maza tashi ki zauna ki sanar dani gaskiyan me yake faruwa,bana son kimin ƙarya don banyi miki wannan koyin ba kema kinsan haka." Babu musu TAIMIYYAH tabi maganan Iyah ta tashi zaune,idanunta har sun tasa sabida kuka tana ta faman ajiyan zuciya.
Daga Iyah har Yasmeen suka zuba mata mata na mujiya,lokacin da take zayyano ma Iyah abinda ya faru a jiya da daddaren.Har kawo yadda Zuhurah ta zo ta samesu Yah Sadeeq na riƙe da hunnunta,ta ƙare maganan tana cewa, "Iyah wallahi abinda ta gani kenan,dama nina san sai ta juya magana ta ƙulla min sharrin da ban ji ba ban gani ba."


Iyah da ranta ya gama ɓaci ta dubi TAIMIYYAH, tana sake tsuke fuska take faɗin ,"Shi Sadeeq ɗin ne ya jaki har ɗakinsa don yai miki gargaɗi akan ki rabu da Naseerun? Ke kuma da yake sakarya ce kika biye mishi kika bishi ɗakin nasa ko?"


Iyah tayi maganan cike da tsawa idanunta akan TAIMIYYAH,wacce ta sake rushewa da kuka.Hakan yasa Iyah ɗaura faɗanta da cewa "Kin ga laifinki na farko kenan da kika bisa ɗakinsa,da ace sheɗan yai muku huɗuba ai zaku iya aikata koma miye,tunda da sonki a cikin zuciyansa." Iyah ta cigaba da cewa, "Don haka wannan shine karo na ƙarshe,da zaki sake shiga ɓangarensa.Shi kuma Sadeeq ɗin zan kirasa inma tufkar hanci,ina ce agaban ubansa yace abashi lokaci zai fito da mata,shine yanzu don ya ga wani ya zo zai ɓullo da sabon salo,to idan so yake taƙama dashi na bi son da gudu na tattake shi ba takalmi." Iyah ta ƙare maganan cike da masifa,ta waiwaya tana duban Yasmeen da ke tsaye daga gefe,ta furta "Maza ɗakko min waya ta a ɗaki." Yasmeen ta juya ta fice ita kuma Iyah ta sake maida dubanta ga TAIMIYYAH,tana faɗin "Zaki tsaida kukan ki share hawaye ko saina saɓa miki? Ba ma dole su rainaki ba komi kuka,sai kace ke baki da bakin maida martani sakarya kawai!"


Iyah tayi maganan tamkar ta mangare TAIMIYYAH,don gani take sanyin nata har yayi yawa.Da a ce tana tsayawa ta maida musu da martani,da tuni sun gane itama ɗin TAIMIYYAN ba kanwan lasa bace,amma sai tai ta musu kuka shiyasa suka rainata har fiye da kima.


Yasmeen ce ta shigo ɗakin riƙe da wayan Iyah a hannunta,lokacin TAIMIYYAH ta share hawaye sai faman jan majina take yi.Duk takaicinta ya gama cika Yasmeen itama,don gani take da agabanta Zuhurah ta yi maganan,babu abinda zai hanata bata kyawawan tafi,ta kuma gaya mata babu daɗi itama.


"Kira min Sadeeq." Cewan Iyah lokacin da Yasmeen take miƙa mata wayan.


Babu musu Yasmeen ɗin ta kira layin Yah Sadeeq ɗin,yana fara ringing ta miƙama Iyah wayanta.Lokacin da ya ɗaga kiran gaisuwansa kawai Iyah ta amsa,ta sanar da shi idan yana cikin gidan yazo tana son magana da shi.Idan kuma baya nan da zaran ya dawo ya sameta a Sashin nata tana jiransa,daga haka ta kashe wayanta bayan ya sanar mata baya nan,sai ya dawo zai shigo.


Ita dai TAIMIYYAH tai kasaƙe tana faman satan kallon Iyah.Ita ko Iyah tashi tayi tsam ta fice daga ɗakin,bata kuma tsaya a ko'ina ba sai Sasan Baba Sani,ta shiga ciki bakinta ɗauke da sallama.


Zuhurah da Basmah sune zaune a falon,don haka suka amsa sallaman Iyah jikin Zuhurah na bata cewa TAIMIYYAH takai ƙaranta wajen Iyah kenan.Babu shiri ta miƙe zata nufi ɗakinsu Iyah tayi saurin dakatar da ita,lokacin data shigo cikin falon bata kuma jira komi ba ta fara wanke Zuhurah soso da sabulu,ta inda take shiga bata nan take fita ba.


Umma data fito daga ɗaki ne ta tari numfashin Iyah,tana tambayan Iyah ko lafiya? Aiko nan take Iyah ta haɗa da Umman ta ci mutuncin su da kyau,Zuhurah sai faman kuka take yi tana sanar da Iyah,ita sharri TAIMIYYAH tai mata,aiko bata ko rufe baki ba Iyah ta kai mata duka a baki,tana cigaba da faɗin "Yimin shiru mutuniyar banza kawai,har kece zaki kalli ƴar uwanki ta jini ki jinginata da kalmar karuwa.Idan akwai ɗan iska ma to ai Sadeeq ɗin ne ba ita ba,mu xuba daga ku har ke Zuwairah me ɗaura su akan halayya da ɗabi'un banza ina dai-dai da ku ne,kuma aure idan na so ya yiwu tsakanin

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login