Showing 12001 words to 15000 words out of 186776 words

Chapter 5 - TAIMIYAH Book Complete Document by Ayshat Dansabo Lemu .txt

15 Dec 2024

6568

sanya damuwa a zuciyanki,yanzu tashi ki koma wajen Iya zan shigo zuwa anjima,ina fata kinyi min girkin da nace?"


Kai kawai TAIMIYYAH ta gyaɗa masa,tana miƙewa tsaye,yayi saurin riƙo hannunta ɗaya har ta tsayu da kyau,kafin ta dafa ƙafanta don fara tafiya ya riƙe mata ɗaya hannun,ta ɗago manyan idanunta ta sauke akansa tana son zame hannunta daga nasa amma kallon da ya jefeta dashi yasa ta barinsa,a haka suke takawa har zuwa ƙofan shiga Sasan Iya,sannan ya sake hannunta ta shige ciki shi kuma ya juya zuwa part ɗinsu,zuciyansa na matuƙar masa ɗaci da irin halayyan mahaifiyansa,yana jiye mata ranan da ubangiji zai nuna mata ikonsa akan nata jinin watakila daga lokacin ne zata gane ubangiji ke yin yadda yaso da bawa,ya kuma halicceshi ta duk irin yadda yaso bawan ya kasance,ko kaɗan bai taɓa ganin aibun nakasan TAIMIYYAH ba,sai ma dai a kullum sake ganin irin baiwan da Allah yai mata yake, wanda ke fitowa a hankali don kaf tsakanin age mate ɗinta su Zuhura tafi so komi,tafi u Brain na karatu boko da islamiya,ta fi su iya kula da kanta da tsaftan jiki da iya girki,akwai ta da nutsuwa da kamun kai da kuma iya riƙe mutuncinta na ƴa mace,wanda duk su ba'a ba su wannan baiwan ba,shiyasa a kullum shi baya hango wata nakasa daga TAIMIYYAH sai tarin abubuwan da ta mallaka wanda ba kowace cikakkiyar me lafiyan ƙafafun aka baiwa wannan baiwan ba,amma ya rasa dalilin da Umma ta ɗauki karan tsana ta ɗaurawa TAIMIYYAH,tare da shan alwashin tsine masa idan har ya dage sai TAIMIYYAH yake so,har ya isa ɓangarensa zuciyansa bata bar masa bitan irin cin mutuncin da Umman tai masa ba alokacin da ya tare ta da maganan TAIMIYYAH sati ɗaya da suka wuce,yasa mukulli yana buɗe ƙofan shigewa ɗakinsa kenan wayansa ya fara ringing,ya dakata daga buɗe ɗakin yana zaro wayan daga aljihun gaban rigansa,ganin sunan My Mum da yayi yasa shi ɗaga kiran kai tsaye,daga ɓangaren Umman bayan ta amsa gaisuwansa tambayansa take ya iso ne? Ya bata tabbacin gashi ma acikin gidan yana ɓangarensa ne zai watsa ruwa ya kintsa ne ya shigo ɓangaren nasu,hakan yasa ta katse kiran shi ma sai ya maida wayan aljihu yana buɗe ɗakin nasa ya shige ciki.


TAIMIYYAH ko tana shiga ciki ta fara addu'an Allah sa Iya bata falo,sai dai addu'an nata bai ci ba don tana sanya kanta cikin falon bakinta ɗauke da sallama,idanunta suka sauka a fuskan Iya tayi saurin sauke kanta ƙasa tana cangala ƙafan da sauri don shigewa ɗakinta Iya ta kirayi sunanta da cewa "Zainabu zo nan." Cewan Iyan idanunta akan TAIMIYYAH wacce ta juyo ta fara takowa zuwa wajen da Iya ke zaune cikin kujera,ta kai ƙasa tana zama kusa da ƙafafun Iyan take faɗin "Iya gani."


Iya takai hannu ta ɗago fuskan TAIMIYYAH da take faman yin ƙasa da kai don kada Iyan ta gane tayi kuka,cikin wani irin murya a dake Iya ke faɗin "Me ya samu fuskanki,me sukai miki daga shiga kai saƙo maza sanar dani,kuma idan kikai min ƙarya saina saɓa miki don ban miki wannan koyin ba."


Iya ta ƙare maganan tana sake tsare TAIMIYYAH da kaifafan idanunta,hakan yasa TAIMIYYAH sake yin rau-rau da idanu tana me zayyane ma Iya yadda sukai da Umman,ta ƙare maganan da faɗin "Don Allah Iya kar kice zaki tanka mata,indai akan Yah Sadeeq ne ta kwantar da hankalinta ni ban taɓa son sa ba bakuma zan fara ba,amma ni bana so kice zaki je kice mata komi,lokaci yayi da zaki daina tankawa akan komi idan anmin Iya,tunda na kula hakan da kike kaman shi ke sake janyo min tsana a wajensu."


TAIMIYYAH ta ƙare maganan cike da magiya,abinda ya karya zuciyan Iya kenan,ta dafa kanta tana faɗin "Naji bazan je ince mata komi ba,amma ke kuma ki daina ƙyalesu akan irin cin fuskan da suke miki,bance ki tanka Zuwaira ba amma su Zuhura duk wanda ya sake miki gorin halitta,kice musu idan suke halittan ɗan Adam don Allah su sauyaki daga yadda kike su mayar dake mara naƙasu,sannan ki daina bari suna ganin hawayenki,domin baka bari maƙiyinka ya gane lagon ta inda zai dinga saranka koda da kalamai marasa daɗi ne,ko kaɗan ki tsaida zuciyanki tayi dakewan da ko sauyin fuska zasu daina gani idan sun miki gorin nakasa,hakan zaisa su daina ci miki fuska,sannan ina so ki kwantar da hankalinki indai mijin aure ne wallahi sai sun sha mamakin irin mijin da Allah zai kawo miki,ai ba ita ke bayarwa ba don tace bazaki auri ɗan ta ba sai me? Wallahi ba don bana miki sha'awan rashin kwanciyan hankali ba da saina nunawa Zuwaira cewa daga ita har ɗanta zan iya iko da su,in kuma haɗa auren da take iƙirarin in tana raye bazai yiwu ba,sai dai nafi so Allah yai ikonsa da kansa domin ina da tabbacin zaifi ni iya hukuntata,domin huruminsa take shiga don shi ya halicceki ahakan,shi kuma yasan irin ajiyan da yai don haka ki cire duk wata damuwa a ranki,ko kaɗan kada kiji cewa zaki ji ƙuncin kasancewanki a hakan kinji ko?"


Iya ta ƙare magana tana shafa kan TAIMIYYAH wacce ta kwantar bisa ƙafafun Iyan,kalaman Iyan na shiga kunnuwanta da wani irin tasirin dake ratsa ilahirin zuciya da gangar jikinta,ta gyaɗa kai alamun gamsuwa da tarin kalaman Iyan,wacce itace gatanta da ta maye mata dukkanin guraben da uwa zata cikewa ƴar ta,a hankali ta cusa hannuwanta saman fuskanta tana share hawayen dake gudu,cikin sanyin murya take faɗin "Insha Allah Iya zanyi anfani da dukkanin abinda ki ka ce nagode Allah ya bar min ke Iya har ƙarshen numfashi na."


Iya da tausayin TAIMIYYAH ya gama cika zuciyanta,ta shafa kanta tana faɗin "Ameen Zainab,Allah yai miki albarka yasa ki cigaba da biyo halayyan TAIMIYYAH,ita kuma Allah ya cigaba da kai haske kabarinta,Allah ya nuna min aurenki da zuriyyan da zaki haifa kafin ƙasa ya rufe idanuna."




Ta ƙare maganan muryanta na rawa cike da raunin zuciya,domin a duk lokacin da ta tuna da mahaifiyan TAIMIYYAH me suna Zainab sai zuciyanta ya karye,domin bata taɓa ganin haƙurarriyan mace me tarin nutsuwa da hankali irin ta ba,ga baiwan kyau kaman ita tayi kanta wanda nagartanta da kyawawan ɗabi'unta suka janyo ake kiranta da TAIMIYYAH,kaman yadda labarawa basa sakawa ƴar su ko ɗansu suna TAIMIYYAH sai ya mallaki nagarta irin na Zainab ɗin,shiyasa a lokacin da aka haifi TAIMIYYAH ta sa aka saka mata suna Zainab ɗin kaman tasan uwar mutuwa zatai,bayan rasuwan Zainab ɗin sai Iya ta cigaba da kiran abinda ta bari da irin sunan da ake kiran Zainab ɗin dashi wato TAIMIYYAH,tana me fata Zainab ɗin ta gado halayya da nagartan uwarta,sai gashi ko TAIMIYYAH babu inda ta baro halayyan mahaifiyan nata,Iya ta sauke ajiyan zuciya tare da dawowa hayyacinta daga faɗawa duniyan tuna baya da ta tafi,muryan TAIMIYYAH me sanyi tamkar na uwar ta na ratsa kunnuwanta lokacin da TAIMIYYAN ke amsa addu'an da faɗin "Ameen Iya na,insha Allah bazaki rigani mutuwa bama tare zamu tafi ko zaki mutu."




Iya ta saki murmushin su na manya,tana sake jin ƙaunar TAIMIYYAN me tsanani yana cigaba da ratsa jinin jikinta,sai dai kafin tayi magana sallamansa da shigowan sa cikin falon yasa duk suka bishi da ido,sassanya qamshin nan nasa dai na turaren BENTLEY ya fara kara kaina cikin falon,Iya gaba ɗaya sai ta koma ta tamke fuska,tana amsa sallaman ya ƙariso cikin falon yana zama kujeran dake facing Iya,ya zame ya kwashi gaisuwa idanunsa fes akan qanwar tasa da har lokacin kanta ke saman guiwan Iya,ba yabo ba fallasa Iya ta amsa gaisuwansa sai ya maida dubansa gaba ɗaya akan TAIMIYYAH yana faɗin "Sis tashi ki bani abinci da yunwa na shigo garin nan."


Yadda ya ƙare maganan idanunsa akanta yasa Iya da itama ta tsare shi da ido zabga masa harara,tana riga TAIMIYYAH da faɗin "Kaji min rashin tausayi dai,a memakon ka tashi ka isa wajen cin abincin tana zamanta sai ka tashe ta wani kawo maka abinci kaman mara ƙafafu,to bazata tashi ba in bazaka isa wajen kaci ba ka koma wajen uwar ka marasa kunyan qanninka su zuba maka kaci."


Yadda Iya ta ƙare magana tana faman juya ido ita adole harara take watsawa Yah Sadeeq ɗin,yasa daga TAIMIYYAH har shi uban gayyan sakin dariya,kafin ko wanne ya maze kaman bashi ke dariyan ba,Sadeeq ɗin ya tashi yana nufan wajen cin abincin yana faɗin "Maida wuƙan ƴar tsohuwa amma dai a taimaka ta zo tai sarving ɗina please."


Iya ta ja tsaki tana faɗin "Ka dai ji dashi fitinanne,ke kuma da kike dariya saiki tashi ki zuba masa waya sani ma kina sane nan zaici abincin shiyasa kika dage sai kinyi girkin da kanki mitsuww!"




TAIMIYYAH da dariya ke cinta arai ganin Iya zata ɗago ta yasa ta haɗe fuska,cike da shagwaɓa take faɗin "Kai Iya inda haka ne da baki ga na zuba masa a kula daban ba,ni inama nasan zai wani dawo bare har inyi girki dashi."


"Oho dai ku kuka sani."

Cewan Iya tana taɓe baki ita ko TAIMIYYAH sai ta nufi wajen cin abincin ta fara sarving ɗinsa,har lokacin Hijab ne sanye ajikinta bata cire ba,plate ɗin ta tura gabansa tana dubansa,ganin yadda ya tsareta da mayen kallon da yake addabanta dashi yanzu yasa tayi saurin ɗauke kanta tana faman turo baki,sam ta tsani yawan kallo tun kafin ta girma haka,lemun Fruity Zoɓo da tai ta zuba masa cikin dogon glass cup ta tura gabansa,kafin ta miƙe tana faɗin "Yah Deeku ni zan shiga daga ciki ina da karatun hadda kasan gobe Saturday."


Bata jira cewan sa ba tai gaba abinta yabi bayanta da kallo,yana girgiza kansa kawai tare da jin wani abu na sake fisgansa zuwa gareta,sai dai zuwa yanzu ya fara ji ajikinsa dole ya koyi juriya akan danne duk wani zazzafan son ta dake ɗawainiya dashi,matuƙar yana son ta sami farin ciki,domin shi kansa yasan idan ya dage sai ya aureta alhali Ummansa tai mata irin wannnan tsanan,bazata taɓa samun kwanciyan hankali ba,tabbas kaman yadda TAIMIYYAN ta faɗi ne haƙura da juna shine kawai mafita su cigaba da zumunci tamkar yadda suka faro,a hankali yake cin abincin daɗin girkin na ratsa shi,tare da haifar masa da kasala da mutuwan jiki,domin wani yanayi ke bin jininsa yana yamutsawa,tabbas zaiyi rashi idan ya bar TAIMIYYAH ta suɓuce masa,ya lumshe idanunsa a lokacin da sanyin Zoɓon da ya zuƙa yabi maƙoshinsa,daɗin ya ratsa har tsakiyan kansa,sai ya buɗe idanunsa yana cigaba da cin abincin har ya kammala,ya goge bakinsa tare da tashi a wajen,cikin falon ya dawo har lokacin Iya na zaune ta maida hankalinta ga kallo,sai yai mata sallama ya fice daga Sasan baki ɗaya..........✍🏻




*Littafin TAIMIYYAH paid book ne akan 500 naira only,ga masu buƙatan yin payment zakui min magana ta wannan number ɗin 08167768704, ko kuma ku turo kuɗin ku kai tsaye ta wannan account ɗin 0504192664 aisha ibrahim dansabo GTbank.*


*Sai ku tura shaidan biyanku ta wannan line ɗin 08167768704.*




_Masu account da Arewa books,zaku dinga siyan sabbin shafuka dalla-dalla akan farashi me sauƙi,ga yadda zaku siya pages a arewa books kamar haka_ 👇🏻


https://arewabooks.com/chapter?id=62d29e11aa5f8f19bc9621cb


*DANNA LINK DIN NAN KASHA KARATU👆🏽👆🏽👆🏽*


*_YADDA ZAKA SIYA LITTAFI A AREWABOOKS_*👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾


*Recharge* - inda ake shiga domin saka kudi cikin account.


*Balance* - Zai nuna kudin account dinku da zaku iya sayayyan littafai cikin kasuwar ArewaBooks.


*Credit/Debit Card* - Hanyar farko kuma mai dadi wajan Recharge din account dinku.


A inda (Enter your amount) za'a saka kudin da akeson Recharge din sai a taba "Proceed". Zaibude muku inda zaku saka bayanan katin banki, kuna gamawa kudinku zaishiga account dinku kaitsaye (instant).


--------


Akwai wasu hanyoyin saka kudi a ArewaBooks account kamar:


*Bank Transfer*
*Airtime Transfer*


Saidai su ba kaitsaye bane (instantly) sai ArewaBooks ta tabbatar da Transfer din, amman bayakai 1hour za'a gansa a Balance.




#Ɗansabo ce#
[12/14, 10:04 PM] +234 703 769 7050: *TAIMIYYAH*❤️


©️Ayshat Ɗansabo lemu ✍🏻


*Page 6*


Lokacin da ya isa gidan Hajiyan bayan ya gama yin parking a wajen da aka tanaza don adana motoci,sai ya dakata bai fito ba yana ansa call,lokacin ne kuma Bilya me gadi ya iso tare da zubewa yana kwasan gaisuwa,hannu kawai A.Maleek da har lokacin ke amsa waya ya ɗaga masa,hakan ya ankarar da Bilya cewa uban gidan nasa amsa waya yake,sai ya tashi ya bar wajen,da ido A.Maleek ya bishi tausayin dattijon na sake ratsa shi,lokacin daya kammala ansa call ɗin sai ya fito yana kulle motan ya fara takawa zuwa cikin gidan,tafiya yake cikin takunsa me cike da nutsuwa da zafin jini,kallo ɗaya za kaiwa fuskansa da ba ma'abocin fara'a sosai ba kasan cewa miskili ne na gaske,lokacin da yaiwa falon gidan tsinke bakinsa ɗauke da sallama,dai-dai lokacin ne Hajiya Aysha ta fito daga wani corridor,hannunta riƙe da waya da wani Cup,amsa sallaman nasa tayi hancinta na cigaba da shaƙo qamshin turaren RALPH LAUREN,ta ƙariso cikin falon a lokacin da A.Maleek ɗin yaiwa kansa mausaki a cikin kujeran 2 Seater,kusa da kujeran da ya zauna nan Hajiya ta zauna itama,domin indai har zatai zaman falo to wannan kujeran dake daura da inda A.Maleek yake nan ne wajen zamanta,shiyasa ma yaima kansa mazauni anan ɗin,idanunta fes akansa yake lokacin da take aje wayanta da Cup ɗin da ke hannunta,A.Maleek yayi saurin zamowa daga kan kujeran ya zube a ƙasan Carpet yana kwasan gaisuwa,Hajiya Aysha da idanunta ke kansa ta saki lallausan murmushi tana amsa gaisuwan tilon ɗan nata namiji,kafin ta ɗaura da faɗin "Ina ka baro Suhailan da ka sanyata kuka tunda farin safiya,har da ruɗata da cewa zakai mata kishiya duk awani dalilin?"


A.Maleek da ya cigaba da zama daga ƙasa ba tare da ya koma bisa kujeran ba,ya ɗaga manyan idanunsa da ya gada wajen Hajiyan yana faɗin "Hajiya har yanzu dai na lura baki daina ma Suhailah kallon ƙaramar yarinya ba,kullum cikin goya mata baya kike bakya son laifinta sam,wallahi Hajiya Suhailah bata jin maganata,sam ba ta ma ɗauki aure da wani muhimmanci ba,amma a yau ina son warware miki irin zaman da muke ko zaki daina goya mata baya."


Ya dakata da maganan yana kallon Hajiya,wacce ta nutsu tana sauraransa kafin ta gyaɗa kai tana faɗin "Ina jinka sanar dani menene ke faruwa da rayuwan auren naku?"


A.Maleek yai ƙasa da kansa kafin ya fara da faɗin "Hajiya Suhailah bata kula dani,duk wani aiki da kika san macen ƙwarai xata tsaya taiwa mijinta Suhailah bata min,ban isa ince ina son abu ka za ta tashi ta girka min da kanta ba sai dai mai aiki,gyaran ɗakina sai ta bushi iska take yi,shima ina ga a wata baifi tayi sau biyu ba,ni ne da kaina idan na shigo gari zan zage ingyara komi idan ina son ganin ɗakin yadda nake buƙatansa,sannan babban matsalata da ita rashin son haihuwa,Hajiya Suhailah ita da kanta ta kai kanta asibiti ta fara amsan Pills na tsarin iyali ba tare da sani na ba,a cewanta tana tsaka da karatu akai bikinmu baxata taɓa yadda ta ɗauki ciki ba,yanzu bikin mu shekaru biyar kenan ta gama karatun tayi Service amma bata daina amsan alluran hana ɗaukan ciki ba,na ɓoye miki gaskiyan magana cewa babu abinda muke yi ne,sabida na ga idanunki ya rufe a nuna mata soyayya,sam baki son laifinta san......"


"Dakata Abdul-Maleek kana so kace min ita Suhailan da kanta ne ta yanke ma kanta yin tsarin iyali ba tare da izininka ba ma, yaushe Suhailah tayi buɗewan ido har haka,ina tarbiyan dana bata ?"


Hajiya Aysha ta katse A.Maleek a fusace,tare da jero masa waɗannan tambayoyin,fuskanta gaba ɗaya na rinewa da zallan ɓacin rai,hakan yasa A.Maleek dubanta yana cigaba da faɗin "Nima abinda na jima ina tambayan kaina kenan Hajiya,ina ga qawaye ƴan duniya tayi da suke son sauketa akan turban da kika ɗaurata akai tun farko,to ni a gaskiya na gaji da halayyan Suhailah kuma bazan iya zama da macen da bazata haihu dani ba sai dai ƙaryan nuna min soyayyah,shiyasa nace a yau zan fayyace miki watakila ke idan kika zaunar da ita kikai mata faɗa zata ji naki,ta canza banzayen halayyan data fara koya,shiyasa na shigo da maganan sake aure kuma am very serious idan har bata sauya ba zan tabbatar mata da cewa ni ba zata maida ni sakarai ba,koma ta canza ɗin ina ji ajikina akwai abinda zai faru nan ba da jimawa ba."


A hankali A.Maleek ya zayyanewa Hajiyan nasa irin mafarkan da yake a ƴan kwanakinnan,da wata wacce sam ba'a nuna masa zahirinta illah idanunta masu haske da ake nuna masa a mafarkin,sai hannayenta da take miƙo masa tana kuka alamun neman taimako,amma da zaran yakai hannunsa don kamo nata yake farkawa daga mafarkin ,Hajiya Aysha bayan gama saurarensa tai shiru tare da shiga tarin nazari,matsalan Suhailah da mafarkin da A.Maleek ɗin ke yi suka taru suka kulle kanta,har ta rasa wani tunani ma zatayi sai zuwa wani lokaci ta numfasa,batai masa magana ba sai wayanta da ta ɗauka ta shiga neman layin Suhailah,bugu biyu ta ɗaga Hajiya bata jira komi ba ta furta "Ma za yanzu kizo nan gida ki sameni."


Daga haka ta kashe wayanta zuciyanta na cigaba da ɗaukan zafi akan lamarin Suhailah,tabbas tana ganin a wannan karon dole ta ɓata ran Suhailan don ko kaɗan bazata lamunci irin wannan sakarcin ba,sannan bata tunanin idan har Suhailah ta cigaba da nuna rashin son haihuwa da gudan jininta to tabbas ita da kanta ma zata nemo masa wata macen ya aura ko bai so ba,zaman awa ɗaya sukai suna cigaba da tattauna matsalolin Suhailah,kafin motar Suhailah ta iso gidan Hajiyan,ta shigo wurjanjan don tunda taji kiran da Hajiyan ke mata tasan ba lafiya ba,A.Maleek ya gama kwancewa Hajiyan komi,hakan yasa ta shigo jikinta a sanyaye tana faman raba ido,kallo ɗaya A.Maleek yai mata ya ɗauke kai yana sake haɗe fuskansa tsaf babu alamun wargi,kusa da Hajiya ta je ta zauna tamkar zata shige jikinta,amma sai Hajiyan ta shiga ture ta tana jifanta da wani mugun kallo take faɗin "Dallah! Matsa ki bani waje ashe ke ɗin sakaryace mara hankali Suhailah,irin tarbiyan dana baki kenan,ko ni haka kika taso kika ga inama marigayi rashin albarka da rashin biyayya? Maxa sanar dani gidan uban da kika kwaso dukkanin halayyan da Maleek ya sanar dani,har kinyi buɗewan idon da zaki tsarama

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login