Showing 42001 words to 45000 words out of 186776 words
Chapter 15 - TAIMIYAH Book Complete Document by Ayshat Dansabo Lemu .txt
ku kai tsaye ta wannan account ɗin 0504192664 aisha ibrahim dansabo GTbank.*
*Sai ku tura shaidan biyanku ta wannan line ɗin 08167768704.*
_Masu account da Arewa books,zaku dinga siyan sabbin shafuka dalla-dalla akan farashi me sauƙi,ga yadda zaku siya pages a arewa books kamar haka_ 👇🏻
https://arewabooks.com/chapter?id=62d29e11aa5f8f19bc9621cb
*DANNA LINK DIN NAN KASHA KARATU👆🏽👆🏽👆🏽*
*_YADDA ZAKA SIYA LITTAFI A AREWABOOKS_*👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾
*Recharge* - inda ake shiga domin saka kudi cikin account.
*Balance* - Zai nuna kudin account dinku da zaku iya sayayyan littafai cikin kasuwar ArewaBooks.
*Credit/Debit Card* - Hanyar farko kuma mai dadi wajan Recharge din account dinku.
A inda (Enter your amount) za'a saka kudin da akeson Recharge din sai a taba "Proceed". Zaibude muku inda zaku saka bayanan katin banki, kuna gamawa kudinku zaishiga account dinku kaitsaye (instant).
--------
Akwai wasu hanyoyin saka kudi a ArewaBooks account kamar:
*Bank Transfer*
*Airtime Transfer*
Saidai su ba kaitsaye bane (instantly) sai ArewaBooks ta tabbatar da Transfer din, amman bayakai 1hour za'a gansa a Balance.
#Ɗansabo ce#
[12/14, 10:04 PM] +234 703 769 7050: *TAIMIYYAH*❤️
©️Ayshat Ɗansabo lemu ✍🏻
*Page 24*
_______Washegary TAIMIYYAH koda ta tashi sam ta manta ma da wani zancen Naseer.Kunna wayanta tayi bayan ta idar da sallan asuba,ko mintuna biyu da kunna wayan bata yi ba ta fara jin shigowan saƙonni. Amma hankalinta sam bai kai cewa wai saƙon daga Nass ba ne,don haka bata bi takan wayan ba har sai da ta gama karatun Qur'aninta tsaf.Ta aje Qur'anin tana miƙewa ta cire Hijab ɗin sallanta ta aje ta nufi Bed ta kwanta, kaman yadda ta saba komawa baccin safe.Wayanta ta ɗauka tana buɗe saƙonnin biyu da su ka shigo,wanda duk baƙin numbobi ne ta gani.Sai ta fara buɗe na farkon da ke ɗauke da kalaman da ke nuna ƙorafi akan kashe wayan da tayi a daren jiya ne.Nan take ta gane saƙon daga wajen Naseer ya fito,don haka ba ta bi ta kan buɗe ɗayan ba tayi saurin mai da wayan a Airplane mode.Ta koma ta yi kwanciyarta tare da lumshe idanunta,sai dai a maimakon bacci ya ɗauketa kaman yadda ta saba sai tunanin yadda za tayi da fitinan Naseer ɗin wanda ya kutso cikin rayuwanta ta ke.Da ƙyar ta ture duk wani tunanin da ke kutsowa cikin ƙwaƙwalwanta ta samu bacci ya sa ce ta.Bata farka ba sai wajen takwas da rabi, don haka direct toilet ta nufa don yin wanka da Brush.Ko data fito tara har tayi don haka a gaggauce ta shirya cikin Riga da Zani na wani Batik me shegen kyau.Kalan Red and Black ne da yai asalin amsan fatar jikinta abinka da farar mace.Ɗinkin Half gown ne Rigan da ya zauna a jikinta sosai,tai simple ɗauri wanda Hijab zai zauna sosai a kanta.Bata sanya komi a fuskanta ba illa man leɓe me taushi don gudun bushewan leɓen,sai manyan idanunta da ta sanyawa kwalli kaman yadda ta saba.Ta ɗauki turarenta da tai sabo da shi a yanzu me suna GIORGIO PINK ta fesa kaɗan.Take qamshi me wani irin daɗi ya cika ɗakin,ta lumshe idanunta tana jin ƙaunar qamshin har cikin ranta.Abie ya fara siyo mata shi cikin siyayyan da yake turo mu su duk ƙarshen wata.
Tunda tai anfani da turaren ta ji qamshin yai mata shikenan ta sanar da Abie ɗin tana so.Ta kuma san tabbas da kuɗi me yawa ake saye,hakan yasa Abie ɗin dai shi ke siyan mata duk idan zai aiko musu da siyayyan da yake musun.
Ganin lokaci zai tafi sosai yasa TAIMIYYAH saurin sanya Hijab ɗinta kalan da ya shiga da kayan jikinta.Lokacin data fito falon Iyah na zaune tana kalacin safe,da alamu yau ta makara karyawan kenan.Don ita bata wuce takwas ba tayi karin safe ba.TAIMIYYAH ta isa wajen tana aje jakanta daga gefe ta durƙusa har ƙasa tana faɗin "Iyah ina kwana,dafatan mun tashi lafiya?"
"Lafiya lau Zainaba." Cewan Iyah tana cigaba da shan Tea ɗinta.TAIMIYYAH na ganin yadda Iyah ta amsa gaisuwanta a taƙaice, yasa ta gane fishi Iyah take da ita kenan.Sai kawai ta share Iyan ta zauna tana duba abinda Ladi ta yi musu yau na karin safen.
Soyayyan dankalin turawa ne da egg,sai kunu da ruwan Tea da aka dafa da kayan qamshi.Hakan yasa TAIMIYYAH zuba dankali da egg ɗin,memakon ta haɗa Tea ita sai ta zuba kunun,don ba ta faye son Tea ba.Sam bata son madara a Tea,ko zata sha Tea sai dai ruwan Lipton da kayan qamshi,ko kuma ta zuba Bounvita ko Milo kaɗai amma ba madara.Babu me magana a cikin su har suka kammala karin.TAIMIYYAH ta miƙe tana shagwaɓe fuska ta dubi Iyah tana faɗin "Iyah bari inje kila Sani na waje har ya iso,sai na dawo."
Iyah aka wani taɓe baki ana faɗin "A dawo lafiya." TAIMIYYAH ta saki murmushi me faɗi tana dafa ƙafanta ta fara takawa don fita daga falon.
A waje sukai kaciɓus da Ladi TAIMIYYAH ta gaishe ta tana mata sai ta dawo.Ladi ta amsa da fara'a tana ma TAIMIYYYAH fatan dawowa lafiya.
Tun daga nesa TAIMIYYAH ta hangi Sani zaune tare da Baba mai-gadi.Ta cigaba da takawa a hankali har ta isa bakin gate ɗin,ta gaisar da su suka amsa a lakoci guda.Tana shirin fita daga gate ɗin ta jiyo muryan Anty Laurat na ƙwalla mata kira.Sai tai tsaye tana jiran ƙarisowan Laurat ɗin, "Anty Laurat gud morning." Cewan TAIMIYYAH da murmushi saman fuskanta a lokacin da Laurat ɗin ta ƙariso wajen.Anty Laurat sai ta aikawa TAIMIYYAH da harara tana faɗin "Ban amsawa wallahi,yanxu TAIMIYYAH don rashin kirki jiya kashe wayanki kika yi duk roƙon da bawan Allahn nan ya yi akan ki barta a kunne? Ni yanzu ya kirani yana min ƙorafi wai har yanzu ma ya yi ta neman line ɗin naki a kashe.Shine fa nace masa bari inzo inga ko lafiya,haba TAIMIYYAH ya da haka please?" Anty Laurat ta kai ƙarshen maganan idanunta akan TAIMIYYAH da ta wani narke fuska.Kafin tayi magana cike da shagwaɓa tana faɗin "Anty ni fa bansan me zance masa bane idan ya kira.Shiyasa na kashe wayan kuma dama ni bana kwana da waya a kunne."
"Kin kyauta to,yanzu sai ki kunna tun da gashi ya damu ya na son yai magana da ke.Please! ki kunna wayan kafin ku isa skull ɗin,ni bari in koma dama shi ya fito dani,da yake jiya ya amsa numberta kafin ya wuce.Sai kin dawo bye." Cewan Laurat tana juyawa ta koma inda ta fito,ta bar TAIMIYYAH na taɓe baki ta juya ta fara takawa don fita daga gate ɗin.Tuni Sani ya fita har ya tada motan shiyasa tana isa bakin motan ta buɗe gidan baya ta shiga.Sani ya ja motan suna barin layin,ko kaɗan kuma TAIMIYYAH ba ta yi tunanin zata iya kunna wayan ba kaman yadda Anty Laurat ɗin ta roƙo.
__________
Suhailah ce zaune ita da qawarta ko ince aminiyarta Zubaida.A cikin falon gidan da ke sama a nan su kai masauki.
An cika gaban Zubyn da kayan motsa baki,wacce a kallon farko za kaiwa Zubyn ka san cewa irin ƴan duniyan matannan ne masu buɗewan ido.Baƙace ɗik sai dai tana da matsakaicin kyau,da kuma dirin jiki me kyau.
Suhailah ta aje cup ɗin hannunta data shanye lemun Chivita,tana faɗin "Zuby yanzu kina ganin idan Maleek ya jaji bo aure ban gama shiga uku na lalace ba kuwa? Ina cikin matsanancin tashin hankali Zuby.Burina a yanzu bai wuce in samu ciki ba.Amma ga abinda likita ke faɗi wai haihuwan ma zan iya rasa ta baki ɗaya.Zuby nayi nadaman fara shan magungunan hana ɗaukan ciki.Kece duk kika bani wannan gurgun shawaran,ga shi ina shirin shiga masifan da bansan ta yadda zan iya tinkiransa ba.Ko kaɗan bana hango wasa a idanun Maleek,da gaske yake yi akan son haihuwa zai iya auro wata macen.Ba tare da yayi la'akari da halin da zan iya shiga ba, ki sanar da ni miye mafita yanzu?"
Yadda Suhailan tayi maganan hankali a tashe,yasa Zuby aje cup ɗin hannunta da ta cika da lemu ta shanye.Ta miƙa hannu ta dafa kafaɗan Suhailah tana faɗin "Calm down babbar Yarinya! Nifa ban ga wani abin ɗaga hankali har haka ba.Ki bari ku je can Egypt ɗin kiji me likitocin can zasu faɗi.Kuma maganan ya ƙaro aure to sai me tunda ba a kan ki kishiyar za ta zauna ba.Kuma in banda abinki idan ya auro wata ai tamkar ya auro ta don samun cikar burinsa na samun haihuwa ne kaɗai.Ba wai don zai yi mata soyayya irin yake miki bane,kinga ashe soyayyar dai tana gareki ne.Ni abinda nake so da ke ki koyi iya kissa da zaman duniya Suhailah.Ki zama mace me wayo da iya janyo hankalin miji,ki kwantar da kai ki dinga masa duk abinda ya ke so.Amma ko kaɗan ki daina nuna damuwanki akan abinda ki ka aikata,domin ba zamu dawo da hannun agogo baya ba.Ki nuna masa ko auren zai yi za ki goyi bayansa,in yaso idan matar ta haifa masa ɗan sai kiyi kissan yadda riƙon ɗan zai dawo hannunki.Kin ga zaki ƙarisa janyo hankalinsa kanki ke ɗaya.Daga shi har Hajjah ki nuna musu kin amshi ƙaddara ko da ance ba za ki haihu ba kin amince Maleek ɗin ya sake wani auren."
Zuby ta kai ƙarshen maganan tana wani kashewa Suhailah idanu,wacce ita kuma jikinta gaba ɗaya yai wani irin sanyi da kalaman Zubaidan.Wani sashi na zuciyanta na gaya mata tabi shawaran aminiyan nata,sai dai tsananin soyayar da take wa Maleek da kishinsa me zafi da take yi.Bata ji zata iya gani tana raye ya auro wata mace har ta iya dannewa ta nuna rashin damuwanta.Ta tabbar idan har zanen ƙaddara ya zanawa Maleek ƙarin auren wata mace bayan ita.To tabbas za'ai bikin tana gadon asibiti ne a kwance.
Suhailah ta dubi Zubyn cikin ido kafin ta soma faɗin "Zuby baki zo da shawaran da zan iya ɗauka ba a wannan karon.Domin har yau kin kasa gane wani irin zafin kishi na ke dashi akan Maleek ba.Taya kike iya tunanin zan iya rintse ido in kalli wata mace,a matsayin kishiyata har ta haifa masa ƴaƴa ba ni ba?Ba zan iya ba Zuby idan ko har na iya to ki tabbatar da zan kwanta ciwon da zai iya zama ajali na! Ina ma Maleek wani irin so me wuyan bari, sannan baki san waye Maleek a iya kula da mace bane musamman a shinfiɗa.Tabbas da sam ba zaki kalli idanuna ki bani shawaran wai in goya masa baya ba." Yadda Suhailah ta kai ƙarshen maganan hawaye na cika idanunta,yasa Zuby taɓe baki tana jifanta da wani irin kallo.Can ƙasan zuciyanta kishi da takaicin Suhailan ne kwance sosai,amma ganin Suhailah ta zubo mata ido yasa ta sakin murmushi tana faɗin "Suhailah shiyasa na ke faɗi miki kanki baya ja har yanzu.Sunan kinyi boko ne kawai amma sam baki da buɗewan ido,irin na matan zamani da suka san kan duniya.Baki san miye kissa da iya zaman duniya ba,yanzu fa kike tambayan mafita amma na kawo miki mafitan da zata anfane ki,kina kawo min zancen kishi da wani so.Ubanwa ya gaya miki dama akwai macen da aka taɓa mata kishiya da son ranta? Babu wannan macen duk wacce kika ga anyi mawa bata so aka yi.Amma hakan baya hana matan da suka iya bariki kwantar da kai har su cika burikansu ba tare da an gano haƙiƙanin manufan da ke zukatansu ba.Kin riga kin aikata abinda ya janyo miki illa,kina tunanin da Maleek ya ƙaro aure da rashin yardan ki,ba gwara ya ƙaro da yardan ki ba? Ko banza idan kishiyan ta shigo za ta shigo ne don kawai ta haifa masa ɗa,ba wai don zai yi mata so irin wanda ke ya ke miki ba.Daga lokacin da zata haifa masa ɗan,ke kuma a lokacin zaki sake kwantar da kai a baki riƙon ɗan.Kin ga babu me zargin ki sai ma tausayin ki da zai kama zuciyan Hajjah har ta goya miki baya wajen a baki riƙon ɗan.Daga kuma lokacin da ɗan yazo hannunki kece zaki raine sa irin yadda kike da burin ya taso.Amma yanzu idan kika bari kishi ya rufe idanunki har ƙaddara ta zana masa auren wata kina nuna zafin kishi da shirme to zaki ɓata goma ne ɗaya bai gyaru miki ba.Sannan idan baki aje son jiki da sakaci kin kama mijinki da kyau ba duk wacce za ta shigo cikin ruwan sanyi za ta gama da zuciyan mijinki.Ta kuma samar da abinda ke kika kasa samarwa.Yanzu ki bani lambansa zan taya ki bashi haƙury akan cewa kinyi nadaman abinda kika aikata,sannan zan sanar da shi laifi nane duka domin nice na baki shawara ba tare da mun san hakan zai iya janyo kowace irin illa ba.Ke kuma da zaran ya diro gari ina so yaga canji,ki tarairaye shi da kyau tare da samar masa dukkanin nutsuwa.Ko a fuska kada ki sake ki nuna masa cewa abinda likita ya faɗi yana damunki.Nuna masa za kiyi kin barwa Allah komi,ina fata kin fahimce ni?"
Zubaida ta ƙare maganan da jefawa Suhailah tambaya.Wacce ta zubawa Zubyn idanu kaman me son gano gaskiyan dukkanin kalaman Zubyn akan fuskanta.Ta gyaɗa kai kafin ta buɗe baki tana faɗin "Na gane Zuby gaskiya kin fini sanin kan duniya,kuma kanki yafi nawa ja.Tabbas hakan za a yi har Hajjah bazan sake nuna mata damuwa ta ba.Zamu bi su a duk yadda suke so.Koda auren zai ƙaro akwai plan ɗin mu a ƙasa.Idan kuma Allah yayi ikonsa na samu cikin ma kin ga shikenan komi yazo cikin sauƙi.Amma fa zanyi yaƙi me girma kafin in iya duk waɗannan abubuwan da kika zano." Suhailah tayi maganan murya a maraice,Zuby da har wani ajiyan zuciyan samun nasara ta saki,tayi saurin kamo hannun Suhailah tana faɗin "Karki ji komi za ki iya Suhailah sai dai baki sakawa zuciyanki cewa zaki iyan ba.Yanzu dai bani lambar ranshi ya daɗe ɗin,da zaran na isa gida zan zauna in tsara masa kalaman da zai gamsu da shi.Ai indai muna tare kisa wa ranki baki da sauran wani matsala.Irin wannan daula da kike ciki kina fantamawa,yaushe zan miki fatan wani abu ya raba ki da Maleek ɗin ki.Gashi kuma kina sakar mana muna dangwala ta ina zamu bari wani abu ya shige gabanki da zai baki matsala?Ki sawa ranki duk wacce za ta shigo to tamkar za ta zo bautan haihuwa ne ke kuma kina amshe ƴaƴan,kin ga kenan ke ce da riba ba ita ba.Aikin ki kawai ki cigaba da gyara kanki da jikinki,kina samar da nutsuwa a zuciyansa.Wata kuma tana aikin ɗaukan ciki tana haifewa,komi nata na yin ƙasa ke kuma na ki yana gyaruwa hhhhh.....!" Ta kai ƙarshen maganan tana bushewa da wani irin dariya na ƴan duniya,ita kuma sakarya Suhailah na tayata,lokacin da take karantowa Zuby numbern Maleek ɗin,har wani rawa zuciyan Zubyn ke yi wani abu na kewaye zuciyanta.Tana gama kwashe numbern tsaf tai saving da suna *My M.Ado* Suhailah sam bata san ko da wani suna qawar nata dake a matsyin bazawara tai saving numbern mijinta ba.Zuby ta cigaba da tsarawa Suhailah kalamai son ranta,bata bar gidan ba sai data tabbatar Suhailah ta hau kan duk wani gadan zare da take ɗaura ta akai.Sannan Suhailan ta haɗa mata sha tara na arziƙi cike da leda ta raka ta har bakin gate.Sukai sallama tana ji a zuciyanta bata da aminiya me sonta irin Zubaida Halliru.
Koda ta dawo cikin gida kai tsaye wayanta ta ɗauka ta shiga neman layin Maleek ɗin,amma har wayan yai ringing ya katse bai ɗauka ba.Hakan yasa Suhailah aje wayan tana gyara kwanciyanta cikin seater ɗin.Ƙwaƙwalwanta na tariyo mata dukkanin yadda sukai da Zubyn da shawarwarin da ta bata.Ta lumshe ido tana fata kada ma Allah ya jarabceta da rashin samun haihuwan,bare har Maleek ɗin ya auro wata mace bayan ita.Sai dai can ƙasan ranta na gaya mata in kuma abinda bata so ɗin ya kasance to tabbas yadda duk Zubaidan ta tsara mata haka za ta bi...........✍🏻
_Ni dai Ɗansabo cewa na yi anya Suhailah na da man kai kuwa? 😁 amma bari dai mu cigaba da bibiyan su don ganin yadda wasan zai kaya._
Littafin TAIMIYYAH paid book ne da zai zo akan 500 naira only,ga masu buƙatan yin payment zakui min magana ta wannan number ɗin 08167768704, ko kuma ku turo kuɗin ku kai tsaye ta wannan account ɗin 0504192664 aisha ibrahim dansabo GTbank.*
*Sai ku tura shaidan biyanku ta wannan line ɗin 08167768704.*
_Masu account da Arewa books,zaku dinga siyan sabbin shafuka dalla-dalla akan farashi me sauƙi,ga yadda zaku siya pages a arewa books kamar haka_ 👇🏻
https://arewabooks.com/chapter?id=62d29e11aa5f8f19bc9621cb
*DANNA LINK DIN NAN KASHA KARATU👆🏽👆🏽👆🏽*
*_YADDA ZAKA SIYA LITTAFI A AREWABOOKS_*👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾
*Recharge* - inda ake shiga domin saka kudi cikin account.
*Balance* - Zai nuna kudin account dinku da zaku iya sayayyan littafai cikin kasuwar ArewaBooks.
*Credit/Debit Card* - Hanyar farko kuma mai dadi wajan Recharge din account dinku.
A inda (Enter your amount) za'a saka kudin da akeson Recharge din sai a taba "Proceed". Zaibude muku inda zaku saka bayanan katin banki, kuna gamawa kudinku zaishiga account dinku kaitsaye (instant).
--------
Akwai wasu hanyoyin saka kudi a ArewaBooks account kamar:
*Bank Transfer*
*Airtime Transfer*
Saidai su ba kaitsaye bane (instantly) sai ArewaBooks ta tabbatar da Transfer din, amman bayakai 1hour za'a gansa a Balance.
#Ɗansabo ce#
[12/14, 10:04 PM] +234 703 769 7050: *TAIMIYYAH*❤️
©️Ayshat Ɗansabo Lemu ✍🏻
*Page 25*
_______Lokacin dasu TAIMIYYAH suka fito wajen bakin gate,tun daga nesa idanunta ke hango mata mutum tsaye jingine da jikin mota,ya harɗe hannuwansa a ƙirji tare da kafowa ƙofar fitowa gate ɗin wajen idanu.
A cikin daƙiƙa kaɗan ƙwaƙwalwanta ya bata tabbacin cewa Naseer ne.Domin kallo ɗaya taiwa fuskansa ta gano hakan,don kamanninsa ne data gani a daren jiya kwance akan fuskar sa.Tayi saurin furta "Ya Allah!" A bayyane lokacin da ya fara takowa yana kusanto su.Zee tayi saurin duban TAIMIYYAH tana faɗin "Lafiya Namcy?" Sai dai kafin TAIMIYYAH taba Zee amsa har ya ƙariso wajen da sukai tsaye.Hakan yasa TAIMIYYAH ta gagara bai wa Zee amsa,sai kawai ma ta dafe ƙafanta ta fara tafiya don barin wajen.Hakan yasa Nass da ya ƙariso daf da Zee ɗin ya saki murmushi yana faɗin "Salamu Alaikum!" Zee ta ɗaga idanunta ta sauke a kansa tana amsa sallaman da ya yi,kafin ya ɗaura da faɗin "Qawar mu ko zaki taimakeni mu je ki taya ni rarraso waccar qawan taki please?"
Yadda yai maganan cike da magiya