Showing 162001 words to 165000 words out of 186776 words

Chapter 55 - TAIMIYAH Book Complete Document by Ayshat Dansabo Lemu .txt

15 Dec 2024

6602

buri ga kuma kayan mu can wajen ɗinki wanda zamu saka ranar."


Zee ta ƙare maganar tana sakin dariya, ganin yadda TAIMIYYAH ta wani narke face kaman za ta saki kuka. Ta dubi Zee ɗin ta ce, "Wallahi guys ɗinnan ku na da damuwa, ke dai da Yasmeen ban san wanda ya fi wani son bidi'a ba,shi kuma Uban Gayyar ne ai ya ɗaure mu ku gindi,da ya turo muku da kuɗin da za ku yi ta shirme da su,ni kam ko pics ɗin ma ba zan yi ba aje ana nuna ni a duniya ana cewa, ga wata gurguwa da neman duniya har da su yin Party a biki."


Zee ta dallawa TAIMIYYAH harara ta ce, "Ke dai wallahi ba ki yi ba Zaynab,miye na yin wannan maganar babu kan gado, to sai me don kin yi Bridal shower don kina da nakasa? baki da labarin gurguwar da ake turawa akan keken guragu ma anyi ƙasaitaccen Dinner Party da Bikinta,kuma akan keken gurugun aka turota zuwa wajen,don Allah ki daina kyarar kanki da kanki TAIMIYYAH please!"


Zee ta ƙare maganar cikin nunawa TAIMIYYAH cewa da gaske, ranta ɓaci ya ke yi idan tana jin yadda TAIMIYYAN ke zagin kanta da kanta, da an yi magana ta ce ita gurguwace kaza da kaza. TAIMIYYAH ta saki murmushi tana haɗe hannunta biyu alamun roƙo ta ce, "Sorry Namcy na daina ,wallahi shi ma Maleek ya hanani kiran kaina da sunan, amma na kasa dainawa don gani na ke ko ni ban kira kaina da sunan ba, ai dole duniya za ta kira ni da shi,tunda duk wanda ya ga ina tafiya cewa ake yi ga wata gurguwa can."


TAIMIYYAH ta ƙare maganar wani abu na motsawa cikin zuciyarta, Zee ta sake balla mata harara cikin son kawar da zancen ta ke cewa, "Su sauran Amaren miye na su shirye-shiryen? Kamata ya yi ma ku yi komi tare tunda dai duk abun ɗaya ne."


TAIMIYYAH ta ɓata fuska lokacin da ta tuno yadda suka kwashe da su Zuhurah, da irin baƙaƙen maganganun da suka danƙaramata,lokacin da ta ke tambayarsu ko za a haɗu a tsara yinin bakin duk tare da juna. Cikin takaicin kalaman da suka gaya mata lokacin ta dubi Zee ta ce, "Hmm! Zee kenan na gwada son hakan ya kasance, amma sun nuna cewa in yi sabgata su yi tasu,shiyasa ban ƙara musu magana akan me suke ciki bama,ni da kun bar ni ma iya walima kaɗai idan akayi ana gobe ɗaura aure ya wadatar."


Zee ta riga ta gama karantar cewa su Zuhurah, ba masu mutunci bane ta taɓe baki ta ce, "To shikenan sai kowa ya yi sabgar tasa waye a ƙasa? Da sun zo an haɗa kai an yi komi gaba ɗaya, da sunci arziƙi ma sun bar arziƙi in da suka gansa,don Maleek 1.5 mil abinda ya turawa Yasmeen,ko bata gaya miki bane?"


TAIMIYYAH ta jinjina kai cikin sanyin murya ta ce, "Ta gaya min ta ma turo min da receipt na Transaction ɗin da ya tura mata.Ni wallahi Zee kwana biyu ma duk jikina a sanyaye ya ke,idan ina tuna cewa yana da wata matar, da kuma girman matsayinsa sai in ji wani fargaba na lulluɓe zuciyata,sai na dinga jin cewa Maleek ya fi ƙarfin aji na nesa ba kusa ba,kawai dai Ubangine ya haɗa zukatanmu ba don na kai matsayin da zan mallaki mutum kamarsa ba,Allah dai yasa matarsa ta zama me sauƙin hali ba muguwa ba, don wallahi yana yawan gaya min akwai ta da zafin kishi."


Zee ta murmusa sabida yadda TAIMIYYAH ta yi maganar cike da zallar shagwaɓa,ta dubi TAIMIYYAH da idanunta ke kanta ta ce, "To ai tunda kin kira Allah kin gama magana Namcy,don ya fiki sanin fifikon da ke tsananinku da juna, amma a hakan ya haɗa zuciyoyinku tare da jarabtar zuciyar Maleek ɗin da matsanancin ƙaunarki,maganar matarsa kuma ni ina ga baki da case da ita, tunda ba gida ɗaya za ku zauna ba,tana Abuja kina Zaria me zai haɗa ku bare har ki ga zafin kishin nata? Ai sai dai ta yi masa can shi da ya haɗaku, amma ke kam in ba zuwa ta yi ku haɗu anan Zaria ba miye zai haɗa ki da ita? Babu."


TAIMIYYAH ta jinjina kai cike da gamsuwa, kafin ta ce komi wayarta da ke kusa da ita ya shiga ringing,ganin Anty Laurat ce me kiranta vid call yasa ta yi saurin yin receiving tana cewa, "Anty Laurat shiru kwana biyu, sai yaushe za ki iso mana ne,duk na ƙosa ki zo wallahi."


Anty Laurat ta dubi fuskar TAIMIYYAH da ya sake wani kyau da fresh ta ce, "Hey Baby na! Kin ga ko yadda ki ke ƙara tsatso kyau, wani irin gyara Iyah ta fara yi miki haka da ya amshi jikinki?"


TAIMIYYAH ta saki murmushi kafin ta shagwaɓe murya tana cewa, "Wallahi Anty Laurat Iyah ce ke min wankan nono da zuma kullum,tun ina jin ƙarnin nonon na damuna ajiki har na daina ji,haka za ta zuba zuma a cikin nonon shanu ta kwaɓa,sai ta bani in shafe duka jikina da shi,sai ya ɗauki kamar awa ɗaya sannan ta kai min ruwan lalle da ta dafa shi ya huce dai-dai wanka,sai na shiga na wanke jikina da ruwan lallin kaɗai,bayan na wanke jikin da ruwan lalli to ba zan ɗauraye jikin da kowani ruwa ba, sai wannan ruwan lallin ya bushe a jikina ya samu kamar awa ɗaya shi ma,sannan sai na je na yi wankan sabulu, to shine fa in gaya miki fatata ke wani irin laushi da glowing,ni kaina na san abin ya amshe ni matuƙa."


Anty Laurat da ke sauraren TAIMIYYAH idanunta na sake ƙarewa fuskar TAIMIYYAR kallo ta jinjina kai tana cewa, "Gaskiya Iyah ta san ta kan sanin sirrin gyara, wannan ai ko wajen gyaran jiki ki ka je iyakarta kenan,ni ma ko idan nawa bikin yazo zan jaraba yin hakan, in ga ko zai amshi fatata dama ke ai fatarki me laushi ce, shiyasa babu wuya gyara ya kama skin ɗin irinku masu sulɓin fata,su Zuhurah na ji Umma na cewa zuwa next week za a fara musu gyaran ai,ni ma zuwa next week ɗin zan shigo In sha Allah!Yasmeen ita ma bata iso ba kenan sai ta waya ake ta fafata shiri,ai na tura mata measurement na ɗinkin gown da za mu saka ranar Bridal ɗin,wallahi sun yi zaɓe me kyau Material ɗin ya haɗu matuƙa,Allah dai ya kaimu lafiya Mrs.Maleek Ado."


TAIMIYYAH ta amsa da cewa "Ameen." Tana jin wani abu na malting a zuciyarta jin sunan da Anty Laurat ɗin ta kira ta da shi. Suka cigaba da tattaunawa akan tsare-tsaren bikin,TAIMIYYAH ta miƙawa Zee wayar suka gaisa da Laurat, sannan ta amshi wayar su kai sallama da juna baki ɗaya.


Ta aje wayar tana duban Zee ta ce, "Zee don Allah da gaske gyarannan ya amshe ni? Shi ma Maleek kullum mu kai waya sai ya yi magana ,ya ce duk ya ƙosa ya zo jibi ya ga yadda na koma a zahiri,ni har kunya na ke ji idan ya fara sakin layinsa wallahi."


Zee ta saki dariya ta ce, "Wallahi da gaske ne nima baki ji ina shigowa sai da na tanka ba,ni ban san yadda za ki koma ba idan me gyaran jikin da za ta yi ta fara aikinta ita kuma,don wallahi sai kin kusa sanya Angon na ki ya zautu."


Zee ta yi maganar tana sakin dariyar tsokana,TAIMIYYAH ta kwaɓe fuska cike da shagwaɓa ta ce, "Don Allah Zee ki daina tsokanata ni fa tsoro na ke ji wallahi,kin san Ummie haka ta dinga tsoratani jiya tana cewa ,wai wannan Angon ba da wasa ya zo ba,irin su ne wata 9 matar ta haihu in dai da rabo kusa,ni banma gane me take nufi ba,kawai dai na ji gabana sai da ya faɗi a lokacin."


Zee me zata yi inba dariya ba,ta dinga sheƙa abinta TAIMIYYAH na ji tamkar ta saki ihu don takaici,cikin dariyar Zee ke faɗin, "Allah sarki Ummie! Wallahi gaskiya ta faɗi don ni kaina yadda ya ke nuna rawar ƙafa na san akwai shan drama a gaba,zan so ganin idon wata irin washegarin ranar da ake cewa Ango ya shiga ɗaki ne ko me ne?"


Zee ta ƙare maganar tana sake bushewa da dariya,TAIMIYYAH ta sake ƙulewa daf ta ke da sakin kuka ta ce , "Zee yaushe ke ma ki ka zama ƴar iska irin Yasmeen ne? Wallahi ni dai babu ruwana ita Ummie ba nan maganarta ya dosa ba fa,kuma bashi ku ke ci zan rama ne soon ni ma."
Zee ta sake kwashewa da dariya kafin ta yi magana kira ya shigo wayar TAIMIYYAH,ganin Maleek ne yasa TAIMIYYAH sake narke face lokacin da take receiving call ɗin, ta kai wayar kunni sabida ba vid call bane.


Sun ɗauki kamar mintuna goma kafin su kammala yin wayar, TAIMIYYAH sai faman zuba masa shagwaɓa ta ke yi,ita dai Zee sake baki kawai ta yi tana kallon yadda ake buga luv a waya.


"Malama kallon fa?" TAIMIYYAH ta tambayi Zee lokacin da ta ke aje wayarta daga gefenta,Zee ta saki murshi tana cewa "Ƙalau matar Maleek Ado,kawai ina course ɗin yadda zan koyi irin wannan shagwaɓar ce, ko nima na dinga yiwa Sahibi irin shi."


TAIMIYYAH ta saki murmushi tana hararan Zee ta ce , "Sanya idanu dai bai yi ba wallahi." Daga haka Zee ta miƙe don tafiya gida TAIMIYYAH ta raka ta har bakin gate sannan su kai sallama da juna,lokacin da ta juyo don komawa zuwa cikin gida ne,ta hango fitowar Nass da Basmah jere da juna. Ta yi saurin yin gaba a bin ta tana faman taɓe baki,don tuni lamarin su Basmah ya daina bata mamaki don abin na su kullum gaba yake yi ba baya ba,mussamman yadda a yanzu suke tashen jin tamkar su soketa ita da Iyah, tunda suka ji labarin irin mijin da za ta aura.


___________


*Kusfa Zaria,City.*


Hoton fuskar A.Maleek Ado da kuma na TAIMIYYAH ne, ya bayyana a madubin sihirin da ke gaban Boko Kallah. Ya ɗaga jajayen idanunsa masu girma da firgitarwa ya sauke su akan Umma da ƙawarta Hajiya Barirah,wacce ita ce ta yi wa Umman hanyar zuwa wajen Bokan. Ya saki wani gigitaccen dariya ya ce, "Ba waɗannan su ne mutanen da kike son a tarwatse maganar aurensu, wanda za a ɗaura nan da kwanaki goma masu zuwa ba?"


Umma ta yi saurin gyaɗa kai tamkar ƙadangaruwa,jikinta ko'ina rawa ya ke yi sabida yadda take kallon hotunansu TAIMIYYAH, a jikin madubin tsafin tamkar almara. Bakinta har rawa ya ke yi wajen furta cewa, "Eh Boka su ne,don Allah a hana faruwar auren idan ya so koma waye a nemo a bata a ranar, amma wannan attajirin bana son a ɗaura da shi."


Boka ya sake sheƙewa da wani dariyar,wanda kafatanin ɗakin da suke zaune a ciki sai da ya amsa,ya koma ya tsuke fuskarsa tare da zazzarowa Umma ido ya ce, "Duk duniya ban hango wani Boka ko Hatsabibin malamin duban da zai iya hana faruwar wannan auren ba,kamar yadda wancan malamin na ki ya sanar da ke sati biyu da suka wuce,to ni ma xan maimaita miki wannan cewa wannan auren haɗin Allah ne,kuma akwai rabo me ƙarfi a tsakani wanda babu Mahalukin da ya isa ya hana afkuwar hakan,akwai tarin ɗaukaka da buɗi a cikin auren,duk wanda ya ce zai cika matsawa akan hana faruwar hakan, to tabbas rabo zai iya zama ajalinsa,don haka ki kawo wata buƙatar a biya miki amma banda wanda ki ka zo dominsa."


Boka ya ƙare maganar yana sake zazzarowa Umma ido kamar zai cinye ta. Umma da dukkanin jikinta ya ɗauki rawar tashin hankalin rashin madafa,sai ta dubi Boka cikin rawar murya ta ce, "Yanzu Boka ina ji ina gani gurguwar,musaka za ta taka wani matsayin da ƴaƴan cikina ba su taka ba a rayuwa? Don girman Allah da shaharanka a Bokanci ka taimaka ka tarwatsa lamarin aurennnan ,ya ji ya tsaneta ba zai iya aurenta ba,na yi alqawarin salwantar da duk abinda na mallaka matuƙar buƙata ta za ta biya."


"Ko da a ce za ki salwantar da ranki akan hana aukuwar wannan rubutaccen auren,to ina tabbatar miki da cewa sai an ɗaura shi babu makawa,daƙiƙiya me kan kifi kawai."


Boka ya yi maganar a tsawace lokacin da Umma ta sake maimaita buƙatarta,ya cigaba da cewa, "Kina da sauran ƙalubalen da ya kamata a ce a kansa kika zo nan ba maganar waɗannan mutanen da duk iya ƙarfin tsafinmu ba za mu iya da su ba,don a jiyar Allah ne su wanda ya haɗa zukatansu, don ya gwadawa maƙiya irin ku ƙarfin iko da buwayarsa. Ko kina da labarin cewa mijinki zai auri wata bazawara kuma akwai zazzafar rabo a tsakaninsu?"


Umma ta gwalo idanu tare da dafe ƙirji,cikin kiɗima da mummunan tashin hankali ta ce, "What...?!! Boka ka san me kake faɗi kuwa,aure fa ka ce Sani zai ƙara to da wata shegiyar?"


Boka Kallah ya sake daka mata tsawar da ya girgiza ƴan hanjinta kafin ya ce, "Ko ma wace ce bata bayyana min a wannan madubin tsafin ba,don da alamu makaranta masu tsananin ƙarfi ne,amma ki je ki zuba ido tabbas mijinki zai sake aure nan kusa bada jimawa ba,kuma akwai zazzafar rabo a tsakaninsu ,wanda shine silar mutuwar mijin matar, duk lokacin da maganar ya taso ki dawo nan ki sanar dani,maza ku tashi ku ɓace daga nan asararrun duniya."


Boka ya kai ƙarshen maganar cike da tsawa me tsanani,hakan yasa Umma da ƙawarta Hajiya Barirah tashi a zabure suka nufi ƙofar fita,Hajiya Barirah na faɗin, "A tashi lafiya me gani har Hanji."


Boka ya tintsere da dariya yana rakasu da wata mummunar ashar cike da ƙaraji,hakan yasa Umma yin gaɓa tamkar zata ci tuntuɓe sabida firgita.


A cikin Napep ɗin da suka ɗauki drop don komawa da su gida ne Hajiya Barirah ta dubi Umma,wacce ke faman share hawayen tashin hankali ta ce, "Hajiya Zuwairah ya zuwa yanzu ya ci a ce kin sallama akan lamarin wannan gurguwar Yarinyar,wacce kika ɗaurawa karan tsana. So da yawa a wasu lissafe-lissafenmu mu kan lissafa har da abubuwa masu girman da ba za mu iya cinma wani buri akan su ba. Ki sa a ranki kin lissafa raba auren da babu mahalukin da zai duba lissafinki ya baki maki dai-dai, don haka ki aje batunsu ki fuskanci sabuwar ƙalubalen da ke shirin fuskanto ki,ki godewa Allah su ma su Zuhurah duka ba ƙananun gidaje za a kai su ba,don haka ki sanyawa zuciyarki salama ki cire lissafin wannan gurgurwan cikin littafin tsara-tsarenki."


Umma ta ɗago mitsi-mitsin idanunta da suka rine zuwa ja, ta ɗaurasu akan fuskar Hajiya Barirah. Ta sake share hawaye tana cewa, Hajiya Barirah ba za ki gane yadda na tsani Yarinyar da Iyah bane a cikin zuciyata,amma a yanzu tabbas dole na ginjine duk wasu lissafina akan su, in fuskanci sanin wata shegiyarce ta ke shirin kutso kanta cikin rayuwata da mijina,wanda na daɗe da lissafa cewa mijina ne ni kaɗai,kuma don ni kaɗai aka haliccesa.Tabbas idan hakan ya faru akwai babbar yaƙin da zai tashi garin Zaria baki ɗaya,don ba zan taɓa iya zuba ido in ga Sani da kowace irin mace ba in ba ni ba."


Umma ta ƙare maganar cike da jin wani matsanancin zafi a cikin zuciyarta, har suka iso gida sam bata cikin nutsuwarta, ji ta ke yi tamkar ta ari hauka ta nanawa kanta, ko za ta samu salama.


Lokacin da suka shigo cikin Compound ɗin gidan,idanunsu ne ya sauka akan danƙareriyar motar Maleek Ado, wanda ke fake a cikin Compound ɗin gidan. Driver ɗinsa Yusuf na kame daga mazaunin me tuƙi, yana kora ruwan lemun Chivita a maƙoshinsa. Umma da Hajiya suka sake kai dubansu ga hanyar Part ɗin su Iyah, dai dai lokacin da ragowar hasken yammacin ya hasko musu fuskar TAIMIYYAH da Maleek Ado,waɗanda su ke jerowa jere da juna lokacin da suka fito daga sashin Ummie.


Umma da Hajiya Barirah duka babu wacce zuciyarta ba ta yi wani irin dokawa a ƙirjinta ba. Lokacin da suka sauke ganinsu akan fuskar TAIMIYYAH,wacce fuskarta ke haskawa da wani irin tarin annuri da kyawun da ta ƙara yi,sakamakon ingantaccen gyaran jikin da ta fara amsa.


Umma ta yi saurin yin gaba tana ji wani irin duhu na lulluɓe idanunta da zuciyarta baki ɗaya. Hajiya Barirah ta rufa mata baya ita ma zuciyarta na yaba, haɗuwar wannan matashin attijirin da ya yi tsaye a zuciyar ƙawarta.


TAIMIYYAH wacce akan idanunta su Umma suka shige zuwa sasan su,sai ta ɗauke kai daga duban sashin ta mayar kan fuskar Maleek,wanda ya ke tsaye yana ƙare mata kallo. Ta shagwaɓe masa fuska tare da narke murya ta na cewa, "Yah Maleek wannan kallon ya yi yawa fa."


Maleek ya sake shigar da idanunsa cikin na TAIMIYYAH,yana ji tamkar ya rungumota zuwa ƙirjinsa ko zai samu salaman abinda ya ke ji a kanta,ya ɗan taɓe baki kaɗan kafin ya ce, "Babe! Ji na ke yi tamkar na sace ki mu tafi tare, sabida gaba ɗaya kin gama dagula duk wani lissafin da ke kaina, sannan me gyaran jikin nan ya kamata bayan biki in mata babbar kyauta,sabida yadda ta sake fito sirrin kyawun halittar ki. Please wife kar ki sake fita ko'ina daga nan har a ɗaura auren a kai min ke please! Cox bana so wani mahaluki na banin wannan kyawun, da kuma shaƙan wannan ƙamshin da don ni kaɗai aka tanadesu."


Ya ƙare maganar yana sake miskile fuskarsa, zuciyarsa na sake cika da matsanancin kishi akan TAIMIYYAH. TAIMIYYAH ta saki ƙaramin murmushi tana duban bakinsa, wanda ba za ka taɓa cewa daga nan dukkanin kalaman da ya furta suka fito ba,ta buɗe baki cike da shagwaɓar da ke narkar da zuciyar Maleek Ado ta ce, "An gama Yah Maleek ."


Maleek ya zabga mata harara zuciyarsa na sake narkewa da ƙaunarta me tsanani, ya buɗe baki ya ce, "Wife ban san meyasa baki jin maganata akan daina kira na da wannan sunan kareren ba,amma kar ki damu soon zan bambamce miki cewa ni ba Yayanki bane."


TAIMIYYAH sai ta sake narke masa murya ta ce, "Zan koma ciki Yah Maleek su Yasmeen na jirana, sai mun yi waya bye...!"


Daga haka ta juya za ta koma zuwa Sasan Iyah,Maleek ya yi saurin dakatar da

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login