Showing 144001 words to 147000 words out of 186776 words
Chapter 49 - TAIMIYAH Book Complete Document by Ayshat Dansabo Lemu .txt
kawai zai bani nutsuwa har na isa Abuja cikin kwanciyar hankali,wallahi Hajjah ba zan iya misalta miki yadda nake ji akan Zaynab daga ganinta daga jiya zuwa yau ba."
Hajjah ta dubi Maleek da fuskar tausayinsa, don ita kanta ta fahimci cewa,akwai wani ɓoyayyen lamari da ya jona zuciyar Maleek da TAIMIYYAH, tun akan labarin mafarkin da yace yana yi da ita.
Ta saki murmushi me faɗi tana miƙawa Maleek wayarta ta ce, "Ungu kirata da kanka,idan ta ɗauka sai ka bani muyi magana."
Maleek ya amsa wayar hannunsa har rawa yake, lokacin da yake dialing numbar TAIMIYYAH,bugu biyu ana uku ta ɗaga wayar cikin siriryar muryata.Maleek yayi sauri sanya wayar a speeker ya miƙawa Hajjah lokacin da TAIMIYYAH ke faɗin,
"Hello Hajiya ina kwana ,da fatan mun tashi lafiya?"
Hajjah ta amsa da cewa, "Lafiya lau Zainab ya kwana biyu, ya Iyah ina fata kuna lafiya?"
Muryar TAIMIYYAH ya sake fitowa tar lokacin da take amsa Hajjah da cewa, "Lafiya lau Hajiya,ai muna ta so mu zo ni da Iyah amma har yanzu bamu sama time ba,amma zuwa next week Saturday za mu zo In sha Allah."
Maleek da ke sauraran yadda TAIMIYYAH ke magana, cikin nutsuwa da zaƙin muryanta me daɗin amo,sai ya sake miƙe ƙafafunsa sosai yana sake matsawa kusa da Hajjah,ya ɗaura kansa a kafaɗun Hajjah,yana ji tamkar ya amsa wayar ya maida kiran vid call, ko zai samu ganin kyakykyawar face ɗinta, da waɗannan idanun da ke da wani irin tasiri akansa.Hajjah ta zabga masa harara tana cewa, "Allah sarki Zainab,kar ku damu ai komi sai Allah ya nufa,nima ina ga gobe zan shigo wajen Iyah ɗin, sai ki sanar da ita cewa ina tafe gobe In sha Allah."
TAIMIYYAH ta ce, "Okey tuh zan sanar da ita Hajiya, mun gode sosai da kulawa."
Hajjah ta murmusa ta ce, "Bakomi Zainab ina fata da wuri kike dawowa daga skull ɗin da kike zuwa?"
TAIMIYYAH ta baiwa Hajjah amsa da cewa, "Eh da wuri nake dawowa Hajiya."
"To madallah! Allah yayi albarka ya bada ilimi me anfani,sai na zo ɗin ki gaida Hajiya Fatiman da kyau."
Cewan Hajjah,daga haka kuma sukai sallama da TAIMIYYAH,ta ɗaga idanunta ta sauke akan face ɗin Maleek,wanda ya wani lumshe idanunsa,yana jin wani irin yanayi na bin ilahirin jinin jikinsa.Hajjah ta shafa kansa tana cewa, "To Maleek hankalinka ya kwanta yanzu ko?"
Maleek ya ɗago kansa yana faman yamutse fuska ya ce, "Ya kwanta amma kaɗan Hajjah,ba zai gama kwanciya ba sai kin cika ladanki, wajen ganin na mallaki gurguwarki ta zama tawa,na yi miki alƙawarin kasancewa da ita har ƙarshen numfashi,na kamu da ƙaunarta me ƙarfi Hajjah,irin ƙaunar da ban taɓa jin irinsa ba bayan naki da bashi da mahaɗi.Na kasa gane ko dama can da na ke ɓata lokaci ina tunani idan nayi mafarki da waɗannan idanun nata,cewa na kamu da ƙaunar me idanun ne tun ban san kowace ce ita ba,tun jiya dana ɗaura idanuna akanta, nake ji zuciyata na amsawa da wani irin baƙon yana yi ,wanda baki ba zai iya misaltawa ba,don Allah Hajjah ki taimakeni a bani Zainab,cikin lokaci da ba mai yawa ba,don ina ji ajikina bazan sake samun nutsuwa ba ,idan har ba na ga an ɗaura mana aure ba."
Yadda yake maganar cikin tabbatar da dukkanin kalamansa, yasa Hajjah sauke numfashi,kafin ta fara da cewa, "Maleek In sha Allah in dai Zainab rabonka ce za ka sameta,sai dai ina jin tausayin ƴa ta Suhailah, domin tana maka wani irin so me wahala,tana kuma da kishi me tsanani akanka,don haka ina roƙon alfarman ka riƙe kanka wajen danne zafin soyayyar Zaynab, don na lura tun yanzu kana neman ka dinga rasa nutsuwarka akanta."
Karon farko tun shigowarsa gidan, ƙayataccen murmushi ya ƙwace masa,sabida jin furucin Hajjah na ƙarshe,ya saki murmushin me faɗi har fararen haƙoransa na bayyana,kafin ya dubi Hajjah yana cewa, "Hajjah kar ki damu zan yi iya yi na, wajen ganin nayi controlling duk wani feeling da na ke ji akan Zaynabb,Suhailah kuma ke zaki san yadda za ki yi, ki fahimtar da ita komi Hajjah,tunda ke ce silar haɗuwata da dream gal ɗina, wacce idanunta kawai nake gani a she pretty gal ce a zahiri."
Yayi maganar yana jin wani nishaɗi a cikin zuciyarsa, lokacin da kyakykyawar fuskar TAIMIYYAH ya bayyana a idanunsa,Hajjah ta saki baki tana kallonsa da tsantsar mamaki, tare da jinjina ƙudira na Ubangiji.Ta saki murmushi me faɗi lokacin da zuciyarta ta tuno mata da Suhailah,da irin son da take wa Maleek ɗin, tabbas ta san akwai daru a gaba,idan har ya tabbata Maleek zai ƙara aure.Ta dubi Maleek cikin ido tana cewa, "Kar ka damu nan za ka taho min da ita, inyi rarrashi da ban baki tuƙuru,idan har Allah ya ƙulla wani abu a tsakaninka da Zainab ɗin,Suhailah na da zafin kishi akan ka,shiyasa har addu'a na ke mata akan Allah ya rage mata zafin kishi,don kishi idan ya cika yawa masifa ne."
Maleek ya jinjina kai yana cewa, "Hakane Hajjah,amma ai za ta fahimceki in dai daga bakinki za ta ji komi,sabida ni dai a yadda nake ji akan Zaynabb, bana ji ko Nigeria Suhailah za ta yaƙa sabida zafin kishi,hakan ba zai hana ni mallakar Zainabb ba."
Hajjah ta jinjina kai da tsantsar al'ajabin cewa,wai Maleek ne zaune a gabanta yana furta waɗannan kamalan duk akan TAIMIYYAH? Ta saki kyakykyawar murmushi tana wa Allah godia, da zai cika mata burin ta cikin sauƙi,tana kuma fata Iyah da Zainab su yi na'am da tilon ɗanta guda ɗaya, da take kwaɗayin ya haɗa jini da su,sabida tarbiyar TAIMIYYAN da kuma tausayinta da take ji,wanda ya haifar da zazzafar ƙaunarta a zuciyar Hajjan.
Sun daɗe suna cigaba da magana tsakanin Hajjah da Maleek Ado, duk akan TAIMIYYAH sai around 12:30pm yayi sallama da Hajjah,driver ɗinsa Yusuf shi ne zai wuce da shi zuwa Kano,ya bi flight zuwa Abuja sabida gobe 8 za su shiga meeting,tare da Minister of Transportation.
Hajjah ce ta sanya Lubah fita da saƙon Suhailah, aka sanya komi cikin boot,wanda ya kasance su garin kunu ne, da na ɗanwake da Maleek ɗin zai wuce da shi. Maleek sai da ya sallami su Babah Rabi da kuɗi kamar yadda ya saba,sai faman godia su ke yi masa.
Maleek suka fito tare da Hajjah har zuwa wajen mota, suna cigaba da tattaunawa akan TAIMIYYAH,ta yi masa addu'a na fatan alkhairy,da neman kariya kamar yadda ta saba,sannan ya shiga mota Yusuf ya ja,suka bar gidan yana jin zuciyarsa, na cike da wani irin nishaɗi mara misaltuwa............✍🏻
#Ɗansabo ce#
[12/14, 10:12 PM] +234 703 769 7050: Littafin TAIMIYYAH paid book ne,ga duk wanda ta tsincesa a kowani irin group ne,kiji tsoran Allah karki karanta sai kin biya 500 naira only.
Za ku iya min magana ta wannan number ɗin 08167768704, ko kuma ku turo kuɗin ku kai tsaye ta wannan account ɗin 0504192664 aisha ibrahim dansabo GTbank.*
*Sai ku tura shaidan biyanku ta wannan line ɗin 08167768704.*
Masu turo credit za ku turo katin MTN na 500 ta wannan line ɗin 08167768704.
_Ina ƴan kasuwa masu buƙatar a tallata muku hajar ku? Maza ku garzayo da kuɗi ƙalilan a tallata muku kayan siyarwanku sai dai kawai ku ji ana kiran waya don buƙatan sayan kayan ku,ku tuntuɓeni ta layina kamar haka 08167768704._
*60*
TAIMIYYAH na isa ɗaki ta nemi bakin gado ta zauna,tana me dafe kanta da hannu bibbiyu,tunani da tarin ruɗani ya yi wa zuciyarta ƙawanya, don bata san ta yadda za a yi ta iya son wannan miskilin mutumin ba.Wanda bashi da fara'a sai tarin kwarjini da yake mata a ido, ko a cikin waya ta kalli fuskarsa sai ta ji kwarjininsa ya cika zuciyarta. Ta zame ta kwanta tana me jingina jikinta da makarin gadon,dai-dai kuma lokacin da kira ya shigo wayarta,sai ta miƙa hannu ta ɗauki wayar,wanda ta barshi a ɗakin tun ɗazu. Ganin numbar Yasmeen ce yasa TAIMIYYAH saurin ɗaga wayar, ta kai kunni tana faɗin,
"Hello! Yasmeeni how far?"
Yasmeen daga ɓangarenta ta furta, "TAIMIYYAH ina ki ka bar waya ina ta kira tun ɗazu bakya picking?"
TAIMIYYAH ta gyara kwanciya tana cewa, "Sorry Sis,a ɗaki na bar wayar muna tare da Iyah ne, da Hajiyar nan a can falon Iyah."
Yasmeen ta furta, "Okey dama zan ce ne ki hau online, ki ga ashobi ɗin da Zuhurah suka fitar,don na san da wuya sun nuna miki."
TAIMIYYAH ta taɓe baki kamar tana gaban Yasmeen ɗin, sannan ta furta, "Okey zan duba zuwa anjima Yasmeen,ke ma kin san ba za su nuna min ba ai,amma sun fitar da wuri ba saura 2 month bane bikin?"
Yasmeen ma ana ta ɓangaren bakin ta taɓe, tana baiwa TAIMIYYAH amsa da faɗin, "Eh saura 2 month mana, kawai ganɗoki ne irin na su,idan kin duba ki min magana don sun ce ne idan bai yi ba za a sake, ni kuma kin san ba wani iya zaɓe nayi ba."
Daga haka Yasmeen su kai sallama da TAIMIYYAH,ta aje wayar tana sauke a jiyar zuciya,tana shirin tashi ta nufi toilet kira ya sake shigowa wayarta,sai ta maida idanunta kan wayar tana kallon numbar A.Maleek,wanda bata yi saving ba na yawo akan screen ɗin. Ta tsurawa wayar ido zuciyarta na doka mata da wani yanayi, sai daf da kiran zai tsinke ta iya ƙarfin halin ɗaga wayar ta kai kunni.
"Hello! Zaynabb."
Kalaman A.Maleek kenan da suka shiga kunnuwar TAIMIYYAH, wacce ta sake gyara zamanta da kyau akan gadon,ta buɗe baki murya can ƙasa ta ce,
"Na'am ina yini ya aiki?"
Memakon Maleek ya amsa gaisuwarta sai ya jefa mata tambayar da ke addabar zuciyarsa, "Zaynabb Hajjah ta zo gidanku ko?"
Take TAIMIYYAH ta gane wacce yake nufi ɗin, sai ta gyaɗa kai kamar yana ganinta ta furta, "Eh ga ta can ma tare da Iyah a falo."
"Ke kuma kina ina kenan?" A.Maleek ya sake jefa mata tambayar,zuciyarsa na wani irin dokawa da jin sassanyar muryarta.
TAIMIYYAH ta ɗan lumshe ido,muryar Maleek Ado me cike da ƙasaita da daɗin amo na ratsa zuciyarta,cikin ɗan shagwaɓe murya ta bashi amsa da faɗin,
"Ni ina ɗakina ne."
Maleek bai sake magana ba,illah cuting call ɗin da yayi ya kira ta vid call. TAIMIYYAH ta ware idanunta lokacin da ta fahimci vid call ya kira,sai ta yi saurin miƙa hannu ta janyo hijab ɗinta ta sanya,sannan ta yi receiving vid call ɗin, tana me cuskule fuska tare da zunɓure baki kaɗan.
A.Maleek kuwa lokacin da kyakykyawar fuskar TAIMIYYAH, ya bayyana masa cikin allon screen ɗin wayarsa,har wani a jiyar zuciya ya sauke yana me sake ƙuwarawa idanunta da ke da wani irin tasiri akansa ido,yadda ta zumɓuro baki ya sanya shi gane Yarinyar ƴar shagwaɓace ta gaske. TAIMIYYAH ita ko ƙin kallon face ɗinsa ta yi, sai ma ta duƙar da kanta ƙasa tana wasa gefen hijab ɗin da ta sanya,muryar Maleek ya ratsa kunnuwanta lokacin da ya ke faɗin, "Zaynab ina fata zuwa yanzu kin ji abinda kike da buƙatan ji akaina, sannan ina fata za ki bani dama don mu fahimci juna, sabida bana ji za a ɗauki dogon lokaci ba tare da na mallake ki ba. Ko ke ba za ki iya auren me mata ba Zaynabb?"
Yadda ya kai ƙarshen maganar da jefa mata tambayar,ya sanya zuciyarta dokawa da ƙarfi,ta yi saurin dubansa cikin sa a idanunta ya sauka cikin na A.Maleek ɗin,dukkansu sai da zuciyarsu ta doka da ƙarfin gaske, kafin TAIMIYYAH ta yi saurin janye idanunta tana bashi amsa da cewa, "Eh! bana ji zan iya kam, sabida ban san meyasa sai ni ba,duk lafiyayyun matan da ka ke gani meyasa sai ni gurguwa?"
A.Maleek zuciyarsa ne ta yi wani irin kaɗawa da jin kamalan da suka fito daga bakin TAIMIYYAH,karon farko kuma da ya ji zafin kalmar gurguwa da ta kira kanta da shi kai tsaye,ba tare da damuwa akan fuskarta ba, ya sake miskile fuskarsa da tsuketa tamau, kafin ya yi magana a dake yana cewa, "Zaynabb da kanki ki ke kiran kanki da wannan sunan ? Please kar ki sake faɗa min hakan,kuma da ki ke tambayar meyasa sai ke? Sabida ke ɗin na gani na ji ina ƙaunar kasancewa da ke, don haka ni ban damu da zaki iya ko ba za ki iya ba,ba zan damu da cewa za ki so ni ko ba za ki so ni ba, in dai har an amince za a bani ke hakan ya wadatar dani,daga lokacin dana mallakeki zan koyar da ke yadda za ki ƙaunace ni kin ji wife."
Maleek ya yi maganar idanunsa har lokacin akan fuskar TAIMIYYAH,wacce ta ƙi ɗago kai ta dubesa,gaba ɗaya kalamansa na ratsa jijiyoyin jikinta,suna aikawa da wani irin saƙo zuwa zuciya da gangar jikinta. Kalmar ƙarshe da ya kirata da shi na 'wife' yasa ta ɗaga idanunta a hankali ta sauke akan kyakykyawar fuskarsa,wanda sam babu ɗigon fara'a akai,sai ta yi gaggawar sauke kanta ƙasa,wani abu na motsawa a zuciyarta.
Ta kasa cewa komi kamar yadda shi ma Maleek bai sake magana ba, sai kallon side face ɗinta da ya cigaba da yi,tare da kallon cikin ɗakin nata da yake a tsare fes. Sun ɗauki tsawon lokaci a haka,babu wanda ya sake magana a cikinsu,shi Maleek ji ya ke yi ko za su shafe awanni a hakan, ba tare da ta yi magana ba hakan zai wadatar da shi.
Muryar Iyah TAIMIYYAH ta jiyo daga falo tana ƙwallo mata kira,wanda ta tabbatar shi ma Maleek ya ji hakan,sai ta ɗaga kanta ta sauke manyan idanunta akansa, tana me shagwaɓe murya ta ce, "Iyah na kira na zan je na amsa kiranta please!"
Maleek ya tsurawa cute mouth ɗinta ido, siririyar muryarta na ratsa zuciyarsa,tare da haifar da wani zazzafar feeling akanta,ya sauke ƙaramar ajiyar zuciya kafin ya furta, "Okey zan kira zuwa dare, saura kuma in yi ta kira ba za ki picking ba Zaynab."
TAIMIYYAH ta shagwaɓe fuska tana cewa, "To don Allah kar ka kira ni vid call please!"
Ta yi maganar cike da shagwaɓar da ya sake haifar da wani zazzafan yanayin a zuciyar Maleek,wanda idanunsa ke kanta.Ya sauke wani zazzafan a jiyar zuciya yana cewa, "Ba zan miki promise ba wife,cox ganin idanunki kawai shi ke haifar da nutsuwa a cikin zuciyata,tun daga randa idanuna suka sauka akan na ki idanun,ki ka tafi da dukkanin nutsuwar da ke zuciyata,don haka ki ma daina roƙona akan kar in kira ki vid call, in ba so kike a gobe in baro matata da tarin ayyukan da zan yi in dawo Zaria ba, don in sake ganin idanun da ke rikita dukkanin nutsuwata,ko hakan ki ke so babe!?"
TAIMIYYAH ta yi saurin girgiza kanta tana ƙin sake duban face ɗinsa,kiran da Iyah ta sake yi mata yasa ta saurin yin cuting call ɗin,tana me aje wayar daga kan gado ta amsa kiran da ƙarfi,yadda Iyah za ta jiyo ta daga can falon.
Lokacin da ta fito falon ta samu Hajiya Aysha a tsaye ne, alamun cewa tafiya za ta yi,sai ta ƙarisa cikin falon tana faman sunkuyar da kanta ƙasa,sabida wani irin nauyi da kunyar Hajjah ta ji tana ji.Hajjah da ta fahimci hakan sai ta saki murmushi,tana jin wani ƙarin ƙaunar Yarinyar da tausayinta,musamman da Iyah ta gama bata labarin yadda uwar Nass ta ƙi TAIMIYYAR,sabida kawai kasancewarta me lalura.
"Ƴa ta ni zan wuce sai kun zo ke da Iyah har gida ko? Amma don Allah ina so kar kisa wani tunani a zuciyarki game da maganar Maleek,ki tsaya ku fahimci juna idan har kin ji bai kwanta a zuciyarki ba, ki sanar da Iyah sai ta faɗi min kin ji ko Zaynab?"
TAIMIYYAH sai ta sake jin wani kunya ya lulluɓeta,ta yi saurin gyaɗawa Hajjah kai ba tare da ta iya kallon fuskarta ba. Iyah wacce ta fito daga ɗaki ta dubi TAIMIYYAH tana cewa, "Zainabu sai faman kiranki nake yi, kina mene ne baki fito ba sai yanzu?"
TAIMIYYAH ta dubi Iyah tana faɗin, "Ina amsa waya ne Iyah."
Hajjah ta murmusa tana ji ajikinta cewa Maleek ne ya kira TAIMIYYAH,sabida ta ga missed call ɗinsa har huɗu a wayarta, kafin TAIMIYYAH ta fito,sai ta dubi TAIMIYYAH tana cewa, "Hala Maleek ne ko?"
A kunyace TAIMIYYAH ta gyaɗa kai alamun tabbatarwa, Hajjah ta saki murmushi tana cewa, "Ai tunda na ga missed call ɗinsa na san yana son jin ko na zo ɗin ne.To Zaynabb sai na ga zuwan ku, Allah ya yi miki albarka ya tabbatar da alkhairy, Allah ya haɗa zuciyoyinku ko burina zai cika akan son haɗa jini da ke TAIMIYYAH,ina kwaɗayin hakan zan fi kowa murna,idan Maleek ya sake mallakar mace kamilalliya kamar ki."
Ita dai TAIMIYYAH ta yi ƙasa da kanta sosai tana jigine da jikin kujera,wani irin kunya take ji na ratsata,da ƙyar ta iya ɗaga kai ta dubi Hajjah, lokacin da Iyah ke mata rakiya don fita daga falon ta ce, "Hajiya sai anjima mun gode."
Hajjah ta waiwayo tana sakin murmushi ta ce, "To Zaynab sai anjima,ina nan ina zuba ido Iyah ta ce za ku zo cikin sati me zuwa."
Daga haka Iyah tayi wa Hajjah rakiya har waje,ita dai TAIMIYYAH ta kasa yi wa Hajjah rakiya sabida nauyi da kunya,sai ta juya ta koma zuwa ɗaki tana jin gaba ɗaya jikinta ya mutu.
Iyah ta yi wa Hajjah rakiya har zuwa wajen mota,suka gaisa da Shehu ya yiwa Iyah godian abinci da abun sha, da aka fito masa da shi waje.
Basmah ce ta fito daga sasansu za ta fita,sai idanunta ya hango mata danƙareriyar motar Hajjah,wanda ke fake a cikin compound ɗin gidan nasu, ta cigaba da takowa don nufan hanyar gate,idanunta na kan Hajjah da Iyah da ke sallama da juna.
Kamar Basmah za ta daure ta wuce sai zuciyarta ya addabeta, akan ta ƙarisa don ganin wace hamshaƙiyarce Iyah ta samo haka? Lokacin da ta ƙariso kusa da su Iyah ne, ta gane cewa Hajiyar da Iyah ta sa suka je sasanta suka gaisar ce ranar walimar TAIMIYYAH.
"Barka da zuwa Hajiya, ina yini,an zo lafiya?"
Basmah ta durƙusa ta gaida Hajiya Aysha,Hajjah ta dubi Basmah da fara'a tana amsa gaisuwar Basman.Iyah ta dubi Basmah tana bin ta da wani kallo, don ta san babu abinda ya iso da ita wajen sai gulma,amma sai ta danne ɓacin ranta har Basmah ta bar wajen, tana wa Hajjah sallama,Hajjah ta tsaida Basmah tana ɓalle bakin jaka, ta irgo sabbin kuɗin da bata rabo dasu cikin jakar hannu, ta irga 5k ta miƙawa Basmah tana faɗin, "Ungo kya sayi