Showing 45001 words to 48000 words out of 186776 words

Chapter 16 - TAIMIYAH Book Complete Document by Ayshat Dansabo Lemu .txt

15 Dec 2024

6579

yasa Zee sakin murmushi kaɗan tana faɗin "Eh mu je badamuwa." Daga haka suka rufawa TAIMIYYAH baya wacce har ta kai bakin titi, tana tsaye daga gefe guda.Ta jingina da jikin wani ƙarfe don jin daɗin tsayuwa sabida laluran ƙafanta.Lokacin da su Zee suka iso wajen qamshin turarensa na AZZARO WANTED,ya fara sanar mata da isowansu wajen.Sai ta yi saurin haɗe fuska cike da zunɓuro baki take duban Zee dake faɗin "Haba Namcy ya da haka kuma? Zaki taho babu ko jira to ai gashinan na biyo ki,ga baƙo nan kuma ki ji da shi please!"


Cikin murya me cike da shagwaɓa TAIMIYYAH ta kai dubanta kan Nass tana faɗin "Ina yini." Ya saki kyakykywan murmushi yana jin wani irin relief! Daga jin muryanta kawai da yayi a yanzu.Idanunsa a kanta sosai yake faɗin "Ba zan amsa ba Baby,sabida gaba ɗaya yau kin tashi hankalina,kin kuma shiga hakkin zuciyata ta hanyar hana mata dukkanin sukuni.Har sai yanzu dana bayyana a gaban ki sannan na samu nutsuwa,kin kyauta kenan eyim Luv?" Ya ƙare maganan cikin wani irin salo daya saka Zee murmusawa tana duban yadda TAIMIYYAH ta wani kwaɓe fuska kaman zata saki kuka,ita sai abin ma yaso bata dariya,amma ta maze tana kallon wannan drama da ake bugawa.Shi ko Nass ganin TAIMIYYAN taƙi amsa shi sai ya ɗaura da faɗin "To Baby tunda ba za ki magana ba mu ƙarisa ki shiga mota in sauke ki a gida please! Don ba zan so wannan ranan ya cigaba da taɓa min ke ba.Please! qawarmu kisa baki ko ke zata miki magana." Ya ƙare maganan yana maida dubansa kan Zee cike da magiya.Zee ta saki murmushi tana matsawa kusa da TAIMIYYAH sosai,cikin ƙasa ƙasa da murya ta ke faɗin "Qawata ya da shariya haka kuma,miye laifin wannan Handsome guy ɗin daya mato a kanki? Please mu ƙarisa in raka ki kawai ki shiga ku wuce,kin ga mutane sai kallo mu mutane suke.Amma fa gaskiya kinyi Babban kamu Namcy." Zee tayi maganan cike da tsokana,a karon farko da TAIMIYYAH ta ɗago manyan idanunta masu tsananin haske ta saukewa Zee wani hararan daya sa Zee ɗin kwashewa da dariya.Ta sake ƙasa da murya yadda Nass daya matsa gefe ya basu wuri ba zai ji ba,ta furta "Wayyo Qawata wannan harara ai sai ki sa in suma,afuwan please karki gwalesa mu je ku wuce please!"


"Amma Zee kin san ba mutunci bane aga mace a motar saurayi.Me zance idan wani a cikin ƴan gidan mu yaga na sauka a motar sa?Duka fa ban san ko shi waye ba,a jiya ɗaya da haɗuwan mu fa,kawai sai yau a ganni a motarsa gaskiya bazan iya ba.Ki je kawai ki san me zaki faɗi masa ya kama gabansa." TAIMIYYAH tai wa Zee maganan cikin ƙasa da murya itama,kuma sosai Zee ɗin ta fahimci me TAIMIYYAN ke nufi.Don ko ita bata ɗauki shiga motan saurayi a mutuncin ƴa mace ba,har gara gara ma idan ansan da shi a gida,an kuma yar je masa ixinin zuwa zance,Zee ta gyaɗa kai cike da gamsuwa tana faɗin "Na fahimce ki ina zuwa.Bari naje na san me zan sanar masa."


Daga haka Zee ɗin ta nufi wajen Nass dake faman danna waya,ya ɗago yana duban Zee ɗin bayan ya amsa sallaman da tayi masa,ya furta "Mu je ne ta amince Friend ɗin mu?"


Zee ta murmusa kaɗan tana faɗin "Ayyah! Abokin mu kayi haƙuri a she ta riga tayi da me kawo ta cewa ya zo ɗaukanta.Kaga kuma babu daɗi a ga kaine ka sauke ta hakan zai iya zama abin yi mata faɗa a gida.Kayi haƙury next time insha Allah ba zamu gwale ƙoƙarin ka ba."


"Alright! Babu damuwa,amma fa ba haka naso ba gaskiya.Kuma ina roƙon alfarma don Allah ki rarrasar min ita kice ta kunna wayanta da zaran ta isa gida.Wallahi na azabtu haka nan a taimaka min a kunna wayan." Cewan Nass cike da magiya idanunsa na kan TAIMIYYAH da tayi tsaye a inda take ko da wasa bata waiwayo in da suke tsaye shi da Zee ba.Ya ɗauke idanunsa daga kanta lokacin da Zee ɗin ke bashi tabbacin zata sanya TAIMIYYAH ta kunna wayan.Su kai sallama da Zee ɗin ya juya zuwa wajen motar sa, ita kuma Zee ta nufi wajen TAIMIYYAH tana zayyane mata yadda tayi da Nass ɗin.Ta ƙare maganan da faɗin "Don Allah Namcy ki bashi dama ki sauraresa ki ji da wacce ya zo? Ni dai a haka yayi min wallahi kaman zaiyi hankali.Ga shi kyakykyawa ga iya Dressing gaskiya gayen ya haɗu.Da alamu kuma masu gidan rana sun zauna masa.Ki dubi fa motar da yake hawa gaskiya kun dace da juna, ki bada kai kawai qawata mu sha biki nan bada jimawa ba."


TAIMIYYAH wannan karon ma harara ta aika wa Zee ɗin,tana faɗin "Wallahi baki da mutunci wato in bada kai,lallai ne ni kam tsoron ma bashi dama nake yi don da alamu zai yi baƙin naci,da takura ni kuma bani son hakan.Dadai ace ma yazo a me lalura irin tawa ne wataƙil dana bashi space kaɗan in ga ko zan iya gwada ɗanɗana ya soyayyan ta ke.Amma wannan sai ina ga kaman yafi ƙarfin me lalura iri na,gurguwa dani a ganni da wannan ke kinsan sai anyi da ni an kuma ga zaƙewata da yawa."


TAIMIYYAN ta ƙare maganan cikin wani irin sanyin murya,me cike da rauni da ya motsa zuciyan Zee sosai.Taji ƙarin ƙaunan TAIMIYYAN da tausayinta na sake kama ruhinta.Ta dubi TAIMIYYAN da kulawa sosai take faɗin "Ayyah! Qawata don Allah ki daina irin wannan maganan.Kada kiyi saɓo ko butulce ma ni'imomin da Allah yai miki,ke dai kawai ki bashi dama Allah ya fimu sanin yadda ki ke,shi kuma ya san me yasa ya jefo miki shi cikin rayuwanki a hakan.Kin ko ga yadda nake hango tsantsan ƙaunar ki cikin idanunsa kuwa? Gaskiya bana ji wannan guy ɗin da wasa ya zo.Da alamu da gaske ya kamu da son ki Namcy.Ki cire duk wani tunani mara kyau ki bashi dama ki kuma cigaba da Addu'a shi Ubangiji ya fimu sanin hikimansa na barin ki a yadda kike,ki godewa Allah TAIMIYYAH naki laluran ma mai sauƙi ne,wanda suka fiki nakasa ma Allah ya basu mijin aure bare ke da Ubangiji yai ma baiwan halitta me fisgan hankali."


Zee bata bar TAIMIYYAH cewa komi ba,ta cigaba da faɗi mata kalamai na ƙarfafawa,da kawo mata misalai na nakasassu kala kala.Wanda kuma sun yi aurensu a hakan ba kuma guragu suke aure ba da yawan su.Har Zee ta tarewa TAIMIYYAN abin hawa ƙarfafata take yi akan ta daure taba Naseer dama.TAIMIYYAH ta jinjina kai a lokacin da suka isa bakin Napep ɗin, ta shiga ta zauna tana yiwa Zee godia,me Napep ɗin ya tashe mashin ɗinsa suka harba bisa titi.TAIMIYYAH ta daɗe tana jin tasirin kalaman Zee na keta zuciyanta,har tana ji cewa za tai ƙoƙarin ganin ta fara sauraran Nass ta ga da wacce ya zo? Sun iso layin su TAIMIYYAH na jinta a gajiye sosai.Ga kanta dake ɗan mata ciwo sama sama,a haka ta fito tana zuge jaka ta baiwa Me Napep ɗin kuɗinsa,ta juya tana nufan gate ɗin shiga gidan,ta ƙaramin ƙofa inda ake shiga ta nufa bayan ta tsaya ta gaida Me gadi sai ta nufi hanyan isa Sasan su.Sam bata kula da Motar Guggo Bilki da suka iso garin a yau ba,ta nufi cikin Sasan su bakinta ɗauke da sallama.Yasmeen budurwar ƴar Guggo Bilki wacce za suyi sa'an juna da su TAIMIYYAN.Itace ta fito a guje tana wa TAIMIYYAH sannu da xuwa.Da wani irin murna TAIMIYYAH ta washe baki tana duban Yasmeen data ƙariso ta rungumeta take furta "Wash! Yasmeen sai ki yarda ni ai,kin ga yadda kika narka uban ƙiba kuwa, sannunku da xuwa." Yasmeen ta saki TAIMIYYAH tana faɗin "Sannu Sis TAIMY,kin ji yadda na ƙosa ki dawo kuwa,wayyo nayi missing zuwa Zaria irin sosai ɗinnan.Duk na ƙagu mu iso in sanya ki cikin ido na."


"To ai gashi kin sanya ni a idanun naki,ni ma na yi kewanki My Headache.Yanzu shikenan bani da sauran hutu sabida sani magana da zaki dinga yi." TAIMIYYAH tayi magana tana sakin dariya ganin yadda Yasmeen ta cuskune fuska,su ka ƙarisa falon Iyah da sallama idanun TAIMIYYAH na sauka akan Guggo Bilki.Ta ƙarisa gareta tana faɗawa jikinta tana faɗin "Oyoyo Guggo na sannu da zuwa." Guggo Bilkisu ta rungume TAIMIYYAH tana faɗin "Oyoyo! ɗiyata sannunki da dawowa,kin ga yadda kika koma wata baturiya,me Iya wai take baki ne kullum kike sake zama wata kaman baturiya?" Iyah dake kallon su murmushi yaƙi barin fuskarta sabida murnan zuwan tilon ƴarta mace sai cewa tayi "Babu abinda nake bata ni,tsabar dai kwanciyan hankali ne da hutu da take ciki yasa take ƙara kyau da cika kullum.Amma ja'iran a hakan bata ko so ayi zancen kauda ita,ki duba min yadda kullum take ƙara wani cika ƙirji kaman ya fashe,amma wai bata son zancen aure." Guggo da Yasmeen ne suka kwashe da dariyan zancen Iyah,hakan yasa TAIMIYYAH kwaɓe fuska kaman zata saki kuka take faɗin "Kai Iya! Kai Iya! Ni wallahi kinsa min ido da yawa a gidannan,kawai ki fito fili kice kin fara gajiya dani ko kin daina sona." TAIMIYYAH ta ƙare maganan tana tashi daga jikin Guggo Bilki.Iyah ta aika mata harara tana faɗin "Kya dai ji da shi,ba ɗaya cikin duk abinda kika lissafa,zancen aure ne dai sai anyi miki har sai kinyi zuciya kin tsayar da mijin,ja'ira kawai shagwaɓaɓɓa."


TAIMIYYAH ta miƙe fuu...! dafe da ƙafanta ta fara takawa ta nufi ɗaki.Tana jiyo su Yasmeen na mata dariya kafin Yasmeen ɗin ta biyo bayanta zuwa ɗakinta.Ta tadda TAIMIYYAH na cire kayan jikinta zata shiga toilet watsa ruwa,xama tayi daga bakin Bed tana faɗin "Haka kike kwasan Drama da tsohuwar can Sisi?" TAIMIYYAH ta sake kwaɓe fuska tana faɗin "Rabu da Iyah kawai ke dai Yasmeen,wallahi ta saka min ido komi maganan aure,ita ko tsoran a wulaƙanta mata ni bata yi.Ni gurguwa ina naga ta wani xancen aure in ba irina zan aura ba." Yasmeen ta zabga ma TAIMIYYAH harara tana faɗin "Bismillah! Zaki fara ƙonan rai ba,da anyi maganan aure ki fara kiran kanki gurguwa.Ke kaza da kaza,to wallahi wannan karon zamu hau sama in baki daina min banzan zance irin haka ba.Allah sa ke kika fi ko wace mace gurgunta sai mun aurar dake sai dai mijin bai zo ba."


Yasmeen ta ƙare maganan tana sake tsuke fuska.TAIMIYYAH sanin halin Yasmeen na ɗaukan zafi yasa ta sakin murmushi tana faɗawa toilet abin ta,tafi kowa sanin Yasmeen ta tsani tana kiran kanta gurguwa.Shiyasa basa shiri dasu Zuhurah sosai,sabida yadda suke kiran TAIMIYYAH gurguwa,hakan yasa in dai Yasmeen tazo hutu basa ma yin duk iskancin da suke wa TAIMIYYAN.Don sosai Yasmeen ke gwaɓa musu ba daɗi su ma,don haka nema basu damu Yasmeen ɗin ta zo garin ba.A cewan su bata ƙaunar su yadda take ƙaunar TAIMIYYAH,ita kaɗai take so.


Lokacin da TAIMIYYAH ta fito daga wanka,har lokacin Yasmeen na ɗakin.Tayi kwance akan gadon TAIMIYYAN,tana faman kallon hotunan girke-girke kala kala acikin wayan TAIMIYYAH.Da yake ita ba gwanar sanyawa waya code bane don gani take ita kaɗai take rayuwanta a sasan Iyah.Bata da me zuwa yace zai dinga mata taɓe taɓe a wayan,shiyasa sam bata sanya ma wayan Code ba.Ta wuce wajen kayanta direct tana ciro doguwar Riga mara nauyi na shan iska ta saka,ta juyo kenan don yiwa Yasmeen magana wayanta dake hannun Yasmeen ya fara kuka.Sai Yasmeen ɗin ta tashi daga kwance ta zauna tana miƙowa TAIMIYYAH data iso bakin gadon wayan tana faɗin "Ungo wani number ne ke kira." TAIMIYYAH ba tayi magana ba ta amsa wayan tana receiving ta kai wayan kunni bakinta ɗauke da sallama.Daga ɓangaren Nass har wani ɓoyayyen ajiyan zuciya ya sauke lokacin da sassanyar muryar TAIMIYYAH ta isa ga kunnuwansa.Ya lumshe ido yana faɗin "Ranki ya daɗe ina fata banyi gaggawan kira ba,na kasa samun nutsuwan zuciya ne hope kun isa gida lafiya?"


TAIMIYYAH data kai zaune a bakin gadonta,ta ɗan lumshe ido da taɓe baki tana faɗin "Lafiya lau,amma yanzu abinci zan ci, in babu damuwa later sai mu yi magana please!"


Naseer daga ɓangarensa,ji yayi ina ma suna kusa ne yana kallon yadda ƙaramin bakinta ke furta kalaman.Ya sauke ajiyan zuciya yana faɗin "To Baby zan barki kici abinci,amma sai kinyi promise ɗin cewa kina kammalawa zaki min ko da flashing ne saina kira.Inba haka ba kici abincin ina tare da ke ni bazan gaji ba,sai na dinga sauraran yanayin taunan Babyna.Hakan ya wadatar da ni." Yadda yayi maganan cikin wani irin salo na jan hankalin me sauraransa,yasa TAIMIYYAH rufe ido kaɗan tana jinjina rigima da wayo irin na Nass ɗin.Aahankali tayi magana cikin low voice ɗinta take faɗin "I will call u insha Allah bye!" Daga haka tayi cuting call ɗin tana maida wayan Silent,ta aje bisa Bed tana miƙewa ta bar ɗakin,tuni dama Yasmeen ta fita ta bata waje tunda ta fara amsa wayan,hakan kuma ba ƙaramin daɗi yaiwa TAIMIYYAN ba.Wajen cin abinci Direct ta nufa ta samu Yasmeen ta zuba tana ci itama,da alamu tun da suka iso bata kula taci abincin bane sai yanzu.TAIMIYYAH tayi joining ɗin Yasmeen suna cin abincin tare, har su ka cinye wanda Yasmeen ɗin ta ɗiba.Suka ƙara wani suna ci jefi jefi suna taɓa hiran yaushe gamo har suka kammala cin abincin,su ka tattarro zuwa cikin falon Iyah,inda Guggo Bilki da Iyah suka buɗe babin hira.......✍🏻












Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/FAuxFVUMsQhHYfF5qiGklY




Littafin TAIMIYYAH paid book ne da zai zo akan 500 naira only,ga masu buƙatan yin payment zakui min magana ta wannan number ɗin 08167768704, ko kuma ku turo kuɗin ku kai tsaye ta wannan account ɗin 0504192664 aisha ibrahim dansabo GTbank.*


*Sai ku tura shaidan biyanku ta wannan line ɗin 08167768704.*




_Masu account da Arewa books,zaku dinga siyan sabbin shafuka dalla-dalla akan farashi me sauƙi,ga yadda zaku siya pages a arewa books kamar haka_ 👇🏻


https://arewabooks.com/chapter?id=62d29e11aa5f8f19bc9621cb


*DANNA LINK DIN NAN KASHA KARATU👆🏽👆🏽👆🏽*


*_YADDA ZAKA SIYA LITTAFI A AREWABOOKS_*👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾


*Recharge* - inda ake shiga domin saka kudi cikin account.


*Balance* - Zai nuna kudin account dinku da zaku iya sayayyan littafai cikin kasuwar ArewaBooks.


*Credit/Debit Card* - Hanyar farko kuma mai dadi wajan Recharge din account dinku.


A inda (Enter your amount) za'a saka kudin da akeson Recharge din sai a taba "Proceed". Zaibude muku inda zaku saka bayanan katin banki, kuna gamawa kudinku zaishiga account dinku kaitsaye (instant).


--------


Akwai wasu hanyoyin saka kudi a ArewaBooks account kamar:


*Bank Transfer*
*Airtime Transfer*


Saidai su ba kaitsaye bane (instantly) sai ArewaBooks ta tabbatar da Transfer din, amman bayakai 1hour za'a gansa a Balance.




#Ɗansabo ce#
[12/14, 10:04 PM] +234 703 769 7050: *TAIMIYYAH* ❤️


©️Ayshat Ɗansabo Lemu ✍🏻


*Page 26*


_______Misalin takwas da rabi na dare Yasmeen ta ja TAIMIYYAH suka nufi can Sasan Baba Sani.TAIMIYYAH na sanye da Riga doguwa irin na material da ke zuwa Ready made ɗinnan,ɗinkin Boubou akai masa da yai mata kyau sosai ya fito da cikar ƙirjinta daga sama.


Yasmeen ita ma doguwar Rigan ne a jikinta na Atamfa.Ta yane kanta da ƙaramin Veil,saɓanin TAIMIYYAH da ke sanye da ƙaramin Hijab.kowannen su hannunsa riƙe da wayansa,su na tafe suna hiran su gunin ban sha'awa har suka shiga cikin Sasan.Da sallama su ka isa bakin ƙofar shiga Main-Parlor ɗin su Umman,su Zuhurah dake zaune suna kallo suka haɗa baki wajen amsa sallaman,tare da bada izinin shiga.


Yasmeen ita ce a farko sai TAIMIYYAH biye da bayanta,suka kutsa kai cikin falon.Basma ce ta nufo Yasmeen tana faɗin "Oyoyo Yah Yasmeeni,saukan yaushe haka tsidim?" Yasmeen tai Hugging ɗin Basman tana faɗin "Saukan tun ɗazu da rana mana,tunda kun daina zuwa Sasan waccar Old Woman ɗin taya zaku san isowan mu."


"Kai Yasmeen haka ma zaki ce?" Cewan Zuhurah tana isowa tare da yin Hugging Yasmeen ɗin itama,su a dole ga turawa lol.Yasmeen ta furta "Yes haka zan ce mana Sis ƙarya nayi,ba su daina zuwan bane?" Yasmeen ta yi maganan tana maida duban ta kan TAIMIYYAH,wacce gaba ɗaya hankalinta na kan kallon da su Zuhurah ke yi.Sanin da ita Yasmeen ɗin take yi yasa ta juyo ta saki smile kawai ba tare da tace komi ba.Anty Laurat ce ta fito daga ɗakin Umma,ganin su TAIMIYYAH yasa ta ƙariso da fara'anta idanunta akan TAIMIYYAH ta ke faɗin "Wow! Tawan ke ce anan yau?"


"Kai! Anty Laurat sai kace irin na daina shigowa kwata-kwata ɗinnan." Cewan TAIMIYYAH tana duban Anty Laurat ɗin dake jifanta da murmushi,kafin Anty Laurat ta juya wajen Yasmeen suna gaisawa da juna.


Fitowan Umma daga ɗaki yasa duk hankalinsu ya koma kanta.Yasmeen da TAIMIYYAH suka gaida Umman ta amsa da sakin fuska,tana duban Yasmeen take faɗin "Yasmeen saukan yaushe a gari?" Yasmeen ta amsa da cewa "Ɗazu muka iso Umma har da Mamie muke tare ai.Ta gaji ne shiyasa ba ta shigo ba ina ga sai zuwa da safe."


"Allah sarki to sannun ku da zuwa,ai bansan da zuwan ku ba da an ƙara yawan abincin dare ai,amma laifin Iya ne da sai ta aiko ko Ayuba tace ya faɗi."


Yasmeen ta ɗan taɓe baki kaɗan tana faɗin "Laah! Bakomi fa Umma abinci ya isa sosai,tunda ga wanda Ladi ta yi ma duk ya wadata har gashi can ma ba'a cinye wani ba."


Daga haka sai Yasmeen suka maida kai wajen hiransu da su Zuhurah.Ita dai TAIMIYYAH ba ta sanya baki hankalinta na kan kallo ita da Anty Laurat.
Umma kuma tashi tayi itama ta basu waje.Ta koma can ƙaramin falon dake kusa da Dining Area ɗinsu tai zamanta,tana faman danna waya abin ta.


Wayan hannun TAIMIYYAH ne ya fara haske alamun shigowan kira.Da yake a silent ta saka wayan tun ɗazu da rana bayan gama wayanta da Nass,kaman yadda tai masa alqawarin kiransa bayan ta gama cin abinci.Shine ta kira shi sai ya kashe ya kira ta,ya kuma daɗe ya na sake bayyana mata sirrin zuciyansa.
A cikin hiran da yai matan ne take jin ashe shi ɗin ɗan cikin gari ne.Gidan iyayensa na nan a Ƙwarbai can gaban Fadan Mai Martaba Sarkin Zazzau.Ya sanar da ita cewa shi ne Auta wajen Mamansa,ya kuma sanar mata ya kammala karatun Degree ɗinsa har zuwa Masters a ƙasar Dubai.Yanzu haka yana aiki da NNRA(Nigerian Nuclear Regulatory Authority.) Reshen su da ke Abuja.Don ma TAIMIYYAH ta katse hanzarinsa da taga zai dameta,ba don haka ba da hira sosai zai

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login