Showing 15001 words to 18000 words out of 186776 words

Chapter 6 - TAIMIYAH Book Complete Document by Ayshat Dansabo Lemu .txt

15 Dec 2024

6570

kanki rayuwa Suhailah,a gidan ubanwa kika taɓa ganin inda Haihuwa ya hana karatu? Har da zaki je ki cuci kanki ki fara tsarin iyali alhali ko haihuwan fari baki taɓa yi ba."


Inda Hajiya Aysha ke shiga ba tanan take fita ba,taiwa Suhailah tas wacce zuwa lokacin kuka sosai takeyi,cike da tarin nadaman Planing ɗin da tai tayi abaya,da gaske takewa Maleek ta daina shan pills ɗin da takeyi,kusan shekara guda kenan rabonta da shan komi amma ciki yaƙi samuwa,shi kuma ya kasa yadda ta daina ɗin abinda yasa suke ta samun saɓani dashi kenan,jikin Hajiyan ta koma tana cigaba da kuka sosai,Hajiyan ta sake ture kanta daga jikinta,don da gaske haushin Suhailan me zafi take ji,cikin muryan kuka Suhailah ke faɗin "Don girman Allah Hajiya kuyi haƙury ke da Yah Maleek,wallahi zan gyara duk halayyan da baya so,amma bazan iya ganinsa da wata mace ba bayan ina raye,wallahi Hajiya na daɗe da daina tsarin iyali shekara guda kenan,Allah ne bai kawo rabon ba shi kuma ya kasa yadda na daina."


"Ta ya za'ai dama ya yadda kin daina ɗin,tunda lokacin da kika faro ba da yawunsa kika fara ba,Allah yasa ba illah kikai wa kanki da kanki ba,inko har wani matsalan kika janyowa kanki,kinga maganan kice baki son ganin mijinki da wata mace ma bai taso ba,don ni da kaina zan masa wani auren don bazan zuba ido banga ƙwansa a duniya ba,alhali shi kaɗai na mallaka ɗa namiji da Allah ya bar min ya rayu,tunda ke shashashace baki san inda kanki ke miki ciwo ba,in banda ke ɗin sakaryace har wani tsoron haihuwa zakiyi don kina boko bayan gani a raye,ki gayamin wani wahalan raino zaki sani inda kin haihun alhali kinsan kuna dani a raye,to kisawa ranki zama da kishiya nan ba jimawa ba matuƙar ya tasaki agaba kuka je wajen likita aka tabbatar alluran da kikai ne ya janyo miki wani matsalan."




Hajiya Aysha ta ƙare maganan cikin fusata tana ji tamkar tun a yanzu ɗin ta rufe Sunailan da duka,Suhailah da kalaman Hajiyan ke sake kiɗima zuciyanta idan ana shigo da zancen Maleek ɗin zai iya sake aure,ta sake rushewa da kuka so take ta je ga Maleek ɗin ko shi zai tsaya ya saurareta,amma kallo ɗaya tai masa taga yadda shi ɗinma ya sake ɗinke fuska yana jifanta da wannan shu'umin kallon nasa me ɗaga hankali,ai sai ta kifa kanta jikin kujera tana cigaba da rasgan kuka,yayin da Hajiya ta cigaba da rufeta da faɗa daga baya ta koma nasiha,hakan yasa Maleek zame jikinsa yai sallama da Hajiyan ya bar gidan,zuciyansa fes don baiyi tunanin Hajiyan zata iya rufe ido taci zarafin Suhailan har haka ba,idan yana tuna irin son Suhailan da yake rufe idanun Hajiyan,sabida kawai Suhailan ta fito daga tsatson jinin qanwanta da suka fito ciki guda,ta rasu ta barwa Hajiyan Suhailan tun tana da shekaru biyar a duniya,tuƙi yake yi yana fata da addu'an Allah sa dukkanin faɗa da nasihan Hajiyan suyi tasiri a zuciyan Suhailah har ta gyara ɗabi'unta da baya so,wayansa da yake ruri ya kalla ganin sunan abokinsa Naseer ne yasa shi ɗaga wayan yana sanar da Naseer ɗin inda zasu haɗu.


___________


Tunda TAIMIYYAH ta tashi take ta tunanin ta yadda zata tsiri yiwa Yah Sadeeq ɗin girkin da ya buƙata,ba tare da Iya ta gane don shi tayi ba,bare har ta rufe ta da faɗa,dubara ne ya faɗo mata lokacin da ta kammala shirinta cikin wata rigan atamfa da akaiwa ɗinkin free gown da yai matuƙar yi mata kyau,ɗankwalin kayan ta ɗaura tana bin jikinta da turarenta me sanyi da daɗin qamshi,agogo ta kalla taga lokacin ɗaura lunch ɗinsu yayi,hakan yasa ta fita da ƙwarin guiwanta zuwa falo,kaman yadda tai tunani Iyan na hakince cikin kujera,ta tasa TV agaba tana kallon wa'azin da ake haskawa a tashar Manara,TAIMIYYAH ta cigaba da takowa cikin irin tafiyanta da sai da taimakon dafe guiwan ƙafanta me laluran take iya tafiya,ta iso kusa da Iya tana faɗin "Iya yau kuma me Ladi zata girka ne ko dai in amshi girkin tunda nayi sarai sosai,sai in dafa mana ko Rice and Stew ne,ke me son wake sai a dafa miki waken daban."


Ta ƙare maganan tana ɗauke idanunta daga kan Iya,ita kuma Iyan sai ta zubawa TAIMIYYAH ido tana jin ƙaunarta na sake zama a zuciyanta,rashin son jikin TAIMIYYAN da jajircewanta wajen iya sarrafa nau'in girke-girke na tsananin birgeta,don haka bata kawo komi ba ta gyaɗa kai cike da gamsuwa take faɗin "Hakan ma yayi TAIMI na indai zaki iya sai ki shiga Kitchen ku haɗu da Ladin kuyi girkin,amma ni ina son a dafa raguwan Kazan nan da ke cikin Freezer,ayi farfesun ta kawai ki ɗan saka dankalin turawa irin yadda kike mana yai daɗinnan a zuba kayan qamshi yaji sosai kinji ko."


TAIMIYYAH ta gyaɗa kai lokacin da take miƙewa,ta dubi Iya tana faɗin "To Iya duk za'ayi yadda kike so bari inje inga me Ladin take yi."


Daga haka TAIMIYYAH ta nufi Kitchen ɗin nasu,zuciyanta fes kaman ƙanƙara don ta san ta gama da shafin rigiman Yah Sadeeq ɗin,itace tayi komi Ladi kawai blanding kayan miya tai mata,sai ganyen Salad da ta sata yanka musu don TAIMIYYAH bata son cin abinci babu ganye,shiyasa basa rabo da aje kayan Salad ko na Coleslow,bayan kammala abincin TAIMIYYAH ta kwashe su a kulolin da suka saba zuba abinci Ladi na ɗauka tana fita dasu zuwa falon Iya,tana jerawa a ɓangaren da suke cin abinci,sam bata wani wahal da kanta ɗibarwa Yah Sadeeq ɗin daban ba,don tana da tabbacin nan Sasan nasu zai yi masauki yaci abincin,Zoɓon da ta tsaya kammalawa sawa Flavour ta ƙarisa haɗawa ta miƙawa Ladi tasa shi cikin ƙaramin fridge,ita kuma ta juya tabar Kitchen ɗin zuwa ɗakinta don yin sallan Zuhur ganin time yaja,lokacin da ta idar memakon ta fita falo taci abinci sai tayi kwanciyanta a gado,ta ɗauki wayanta tare da kunna Data ta hau online,shiga nan fita can har ta ɗauki lokaci ba tare da ta damu ba,sai da taji Iya na ƙwalla mata kira sannan ta fito,a tsaye ta samu Iya riƙe da wani leda a hannu,fitowan TAIMIYYAN yasa Iya maida dubanta gareta tana faɗin "Maza ɗakko Hijab ki zo ki miƙawa Zuwaira wannan saƙon,turaren wuta ne aka aiko min na ɗibar musu,ki kuma sanar mata yau bana buƙatan abincin daren su,Ladi zata tuƙa min tuwan dawa ne zuwa anjima."


TAIMIYYAH ta gyaɗa kai tana faɗin "To Iya bari in ɗakko Hijab ɗin."


Daga haka ta koma ɗaki ta sanyo Hijab ɗin sallanta ta fito,ledan da kwalban turaren wutan yake ta ɗauka tai waje,tana takawa a hankali har ta isa sasan Baba Sanin........✍🏻








#Ɗansabo ce#
[12/14, 10:04 PM] +234 703 769 7050: *TAIMIYYAH*❤️


©️Ayshat Ɗansabo Lemu ✍🏻

*Page 8*


________Suhailah sai yamma sosai ta koma gida daga gidan Hajiya,bayan ta sha faɗa da nasihun Hajiyan haɗi da razanarwa,tuƙi take amma gaba ɗaya tunaninta na ga yadda zasu kwashe da A.Maleek ɗin idan har ta samu matsala,bata ji zuciyanta ko da wasa zata iya ɗaukan ganinsa da wata mace da sunan matarsa,har ta isa gidanta ranta a jagule yake,mayafinta kawai ta cire ta faɗa Kitchen,samun Ameena tayi tana aikin ɗaura abincin Dinner,Suhailah ta dubi Ameenan tana faɗin "Me kike shirin girkawa ne? ina ga yau kiyi abinda zaku ci ke da megadi,ni zan yi girkin da zamuci da Ogan."


Cike da mamakin Suhailan Ameena ta dube ta,tana risinar da kai alamun girmamawa take faɗin "Okey Mah ba damuwa,dama tuwan Semo ne zanyi sai Macaroni Salad sabida Oga."


"Bar shi kawai yanzu ki ciro min kaza kiyi marinating ɗinta ki mayar cikin freezer,sai ki gyara min kayan miya ki fere Dankali kaman guda 6,yanzu zan dawo in ɗaura girkin okey."


Cewan Suhailah tana barin Kitchen ɗin don amsa kiran Raudha da ke shigowa,sun daɗe suna magana kafin ta saka wayan a silent ta dawo Kitchen ɗin,da taimakon Ameena ta shirya lafiyayyan gashin Kazan da aka wadata shi da Irish gashin yai wani irin kyau,akai raping cikin foil paper tare da saka shi a kyakykyawan mazubi,sai haɗin Macaroni Salad da yaji liver da zallan tsokan kaza shima aciki,da kanta ta ɗauki ƙaton Tray ɗin da aka jera komi ta haura zuwa up stairs,bisa dining ɗin da ke falon saman ta aje ta wuce zuwa ɗakinsa,yana nan yadda ta gansa da safe,ta fara da kwashe kayan dake kan bed ta zuba a kwandon adana kayan wanki,sannu a hankali take gyaran ɗakin tana mita,jikinta ko'ina yana ansawa da gajiya hatta toilet ta daure tai masa kyakykyawan wanki,sai da ta ga komi ya yayi fes sannan ta fito ta nufi ɗakinta ta ɗakko abun zuba turaren wuta,ta zuba ta kunna tana kaiwa ɗakin ta turare ko'ina da ina,bisa sofan dake ɗakin ta zube tana maida numfashi a fili take faɗin "Wai Allah! Anya ko zan jure wannan bautan, gaskiya da kamar wuya zan dai ta lallaɓa ka har ka yadda asake samo me aikin da zata dinga gyaran ɗakinka Hubby."


Yadda take maganan can ƙasa cike da mita zaka ɗauka wanda ake yi dominsa yana ɗakin ne,ganin lokaci na sake tafiya yasa ta miƙewa ta fito daga ɗakin,ko da ta shiga nata ɗakin direct Bathroom ta nufa tayo wanka,ta fito ana kiran magriba amma sanin fana off yasa kai tsaye ta nufi wajen mirrow don tsara kwalliya,sosai ko ta fente face ɗinta da light make-up,domin ita ɗin gwanace a iya kwalliya da son ɗaukan hutuna tana posterwa a media kai ba kace matar aure bace,duk waɗannan halayyan ke sake haɗata faɗa da Maleek ɗin domin ya tsani hakan sosai amma ta kasa dainawa,sabida yadda qawaye ke zigata tana kuma samun Followers sosai a shafukan nata musamman a Instagram,Riga da Skat na wani haɗaɗɗan Voile laces ta saka wanda ɗinkin yai asalin zama ajikinta,tare da fidda shape ɗinta sosai,tayi anfani da sirirn sarƙan gwal ɗinta da ɗan kunni wanda suka sake haske kwalliyanta,hannunta warawarai ne guda biyu suma na gwal ne ta saka,nan da nan tai wani irin kyau tamkar wacce zata wani haɗaɗɗen Dinner Party,ita da kanta ta yaba kyawun da ta zuba sai fatan miskilin mijin nata ya yaba kawai take,zama tayi bayan ta gama wadata jikinta da turaren MISS DIOR banda daddaɗan Body Mist da tai anfani dashi,daga ciki sosai haɗaɗɗen humra ne na DOLCE tai using,gaba ɗaya wani irin qamshi take fitarwa me saukar da tarin nutsuwa ga duk wanda ya shaqa,wayanta ta ɗauka ta hau online don rage lokaci,bayan tayi kiran layin Maleek ɗin har su biyu bai ɗaga ba.


A gajiye sosai ya shigo gidan misalin takwas da rabi na dare,lokacin har Suhailah ta gaji da zaman jiransa a sama ta sakko falon ƙasa,tana kallo a mamaken Smart TV dake manne jikin wani irin LUXURY TV Stand da ke falon,tunda hancinta ya shaƙo mata qamshin turaren RALPH LAUREN wanda yakan sirka da ɗayan turaren nasa na AMOUAGE tasan cewa shi ne ya shigo falon,kallo ɗaya yai mata ita da adonta ya ɗauke kai ya fara takawa zuwa hanyan da zai sada shi da Stairs ɗin da zai kaishi sama,ganin hakan da yayi yasa Suhailah tabbatar da akwai sauran ƙura kenan,Hajiya ta gama nata shi kuma yanzu zai hau nasa,cikin baiwa kanta ƙwarin guiwa ta bishi zuwa saman,samun sa tayi yana rage kayan jikinsa don shiga wanka,sai ta riga shi shiga bayin tana tara masa ruwan wankan cikin tube,abinda ta mance yaushe rabon da tayi ,shiyasa ko da ya shigo bai kalleta ba ya fara ƙarisa cire abinda ya rage a jikinsa,ganin hakan yasa ta juyawa ta ba shi waje,ya saki ƙaramin tsaki yana me jin wani haushinta na kamasa,domin shi mutum ne daya tsani ai masa abu bada zuciya ɗaya ba,ya riga ya gama sanin duk wannan tarairayan bame ɗaurewa bane ne,tana yi ne don ta sakko dashi da zaran ya fara sakin jiki zata sake komawa gidan jiya ne,shiyasa shi kuma ya shirya bata mamaki a wannan karon,lokacin da ya fito samunta yayi kwance bisa Sofa,ganin fitowansa yasa ta saurin aje wayan da ke hannunta ta nufesa,tana faɗin "My Hubby bari in taimaka maka da shafan please kar ka gwaleni,don Allah Maleek kayi haƙury wallahi zan canza dukkanin halayyan da baka so."


Har ta dasa aya bai tanka ba illa ma janye jikinsa da yayi daga gareta,ya fara shafa mansa ganin ta iso ta amsa man sai ya rabu da ita ta ƙarisa shafa masa,gaba ɗaya sai wani narke masa take tana komawa kalan tausayi,qamshinta gaba ɗaya ya gama cika hancinsa,yana taso masa da wani irin feelings akanta,yayi kewanta don rabonsa da gari sati biyu kenan sai a daren shekaran jiya ne ya dawo,amma rashin samun tarba me kyau yasa suka samu saɓanin da ko nemanta baiyi ba bare ya sauke nauyin da ya dawo dashi,sai dai ko kaɗan fuskansa ba asake yake ba,sam Suhailah ta kasa samun yadda take so,jallabiya ta ɗakko masa Milk Colour ya amsa ya saka,ta ɗauki turaren da ta fi son yai anfani dashi,wato AMOUAGE ta fesa masa tana me kwantar da kanta bisa jikinsa bayan ta aje kwalban turaren,ahankali ta kai hannunta zuwa bayansa ta rungumeshi sosai tana shaqan daddaɗan qamshin daya karaɗe ɗakin baki ɗaya, "I Luv u My Maleek." Ta furta cikin wani irin salon da ya motsa zuciyansa,hakan yasa ya zare ta daga jikinsa yana binta da wani shu'umin kallo,domin sosai ta taɓo duk wani feeling da ya danne akanta,har lokacin fuskansa a haɗe yake cikin muryansa me cike da ginshira da izza yake faɗin "Mu je ki bani abinci banci komi ba tun safe sai ruwan juice da nake ta sha."


Bai jira cewanta ba ya fara takawa don fita daga ɗakin,Suhailah ta rufa masa baya har suka fito zuwa dining ɗin,da kanta tai Sarving ɗinsu a plate ɗaya don itama bata ci komi ba ta tsaya jiransa,da farko da kansa ya fara cin abincin amma ganin ta shagwaɓe masa lallai sai ta ciyar dashi yasa ya sakar mata spoon ɗin,sai da ya nuna ya ƙoshi sannan ta maida hankali taci nata,shi ya fara barin wajen ya koma ɗaki don akwai abinda yake son aiwatarwa ta Computern sa,hakan yasa itama Suhailah komawa ɗakinta bayan ta kammala cin abincin,bata sake gigin zuwa garesa ba don ta gama ganesa idan yana wannan fisge-fisgen to gara itama ta ɗan dinga jan kanta bawai ta zaƙe ba,sai da agogo ya buga ƙarfe sha ɗaya sannan tayi shiri cikin wasu Nighties masu kyau,Rigan me transparent ce wanda ita da babu duk ɗaya ne,sai wandon wanda duka tsayinsa iya cinyanta ne,gaba ɗaya wani irin qamshi take fitarwa me motsa zuciya,wayanta ta ɗauka ta fito xuwa ɗakin Maleek ɗin,ga tsananin mamakinta har zuwa lokacin yana zaune bisa tsakiyan gadonsa,da Laptop a gabansa yana ta faman aiki,qamshinta da ya jiyo yasa shi ɗaga manyan idanunsa ya sauke akanta,ƙirjinsa yai wani irin motsawa nan take dukkanin sha'awansa ya gama tasowa,ya cigaba da kafe ƙirjinta da ke bayyane cikin Rigan da kallo babu ko ƙiftawa,har ta iso zuwa kan Bed ɗin tare da yin masauki kusa dashi sosai tamkar zata shige jikinsa,hakan yasa shi sauke ajiyan zuciya yana ji gaba ɗaya bazai iya cigaba da abinda yake ba,shiyasa yayi hanzarin kashe Computern yana janyota jikinsa gaba ɗaya ya rungumeta,Suhailah da ta tabbatar ya gama shiga tarkonta sai ta sake lafewa a jikinsa ta saki kukan kissa,cikin kukan take sake bashi haƙury akan ta tuba wallahi zata sauya ta koma yadda yake so,A.Maleek da yai nisa a aika mata da gigitattun Kisses tako'ina ya kai bakinsa ya haɗe da na ta alamun baya son surutu a wannan time ɗin,ai sai Suhailah ta fara maida martani don itama tayi missing ɗinsa sosai,don ma rashin tsarkin da take ciki dole zai takawa zalaman su birki,lokacin da Maleek ya fahimci bazai samu zuwa inda yafi muradi ba yaji babu daɗi amma da taimakonta ya samu gamsuwa,don ita ɗin ba baya bace wajen kula dashi awannan fannin,shiyasa ko yayi fishin indai aka zo nan ɗin baya ma sanin ya sauka sai komi ya lafa sannan zai cigaba da ɗauke kai da basarwa,a yanzu ɗin ma hakan ya kasance lokacin daya tabbatar ya samu gamsuwa,sai ya zareta daga jikinsa da ta kanainayesa ya nufi Bathroom don tsarkake kansa,ko da ya fito kallo ɗaya yaiwa Suhaila da tai ɗai-ɗai bisa Bed ɗin babu kaya a jikinta ya ɗauke kai,ya nufi wajen da Jallabiyansa yake ya zura yana kai manyan idanunsa ya dubi babban agogon bangon da ke ɗakin,lokacin time ke nuna 12:05am na dare,dole sai yasha ruwan zafi kafin ya kwanta hakan yasa ya nufi inda Suhailah take fuskansa a tamke kaman bashi ya gama mata kalamai da sambatu ba a ɗazu,ya tsare ta da manyan idanunsa yana faɗin "Suhailah tashi kije ki wanka ki zo ki haɗo min Shayi okey."


Ya ƙare maganan da janyota ya miƙar har ta sauka daga kan Bed ɗin,bata damu sam data nemi wani abu ba haka ta wucesa tik ɗinta ta nufi Toilet,ya bi bayanta da kallo yana wani lumshe idanunsa sabon feeling na fisgansa,sanin bazai samu abinda yake so ba har sai ta samu tsarki yasa shi danne komi,har ta fito bai sake yadda idanunsa sun sauka akanta ba,har sai da ya tabbar ta maida kaya a jikinta duk da dai babu maraba da babu wannan rigan nata,ficewa tayi tana faman zumɓure baki sam bata son takura,lokacin da ta kawo masa shayin sai ya dube ta yana faɗin "Sorry na manta bance miki i need some lemon aciki ba,jeki ɗakko min in matsa kaɗan."


Yayi maganan ne idanunsa fes akan face ɗinta,don haka akan idanunsa ta saki ƙaramin tsaki tana juyawa tai waje,ya girgiza kai ransa yana sosuwa,shi dama yasan da wuya Suhailah ta koma masa yadda yake so,duk rawan ƙafan da takeyi na yaudara ne da ɓacin ran da ta gani a wajen Hajiya,har ta kawo lemon sai faman cika take yai kaman baisan tana yi ba,yana gama shan shayinsa ya wanko baki yazo yai kwanciyansa ba tare da ya sake bi takan Suhailan ba,har bacci ya fara ɗaukansa ya jita cikin jikinsa,hakan yasa shi gyara kwanciyansa yana shigar da ita jikinsa sosai ya sake jan Duvet ya rufe su.


________


Ƙarfe 9am na safe TAIMIYYAH ta fito cikin shirin zuwa makarantan Hadda,sanye take da dogon Hijab da ya sauka ƙasa sai dai baya sharan ƙasa sabida

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login