Showing 30001 words to 33000 words out of 186776 words
Chapter 11 - TAIMIYAH Book Complete Document by Ayshat Dansabo Lemu .txt
ƴan uwa har abokanan arziƙi,ta gyaɗa kawai tana barin ɗakin ba tare da tace komi ba,shi ma sai ya saki ƙaramin tsaki bai san ranan da Suhailah zatai cikakken hankali irin yadda shi yake so yaga matar aurensa na bashi Respect sosai ba,Yusuf Drivern sa ta samu yana jiranta kaman yadda Maleek ɗin ya faɗi,tuni har yai Warming motan da zasu fita aciki,cikin hanzari ya buɗe mata Back seat ta shiga,ya maida murfin ya rufe bayan ta amsa gaisuwan da yake mata,kafin su fita shima Baba Megadi sai da ya miƙa gaisuwansa wajen Gimbiyar tasu,wacce take yawan musu ihsani don ba laifi Suhailah tana da kyauta da sakin fuska wa mutane,ko kaɗan bata da girman kai barta dai da son girma da son hutawa ta fantama yadda take so ,amma abin hannunta sam baya rufe idanunta,shi yasa qawanyenta ke ji da ita da yawa kuma acikinsu suke kishin yadda tafi su samun duniya,ta auri miji na liƙawa a goshi ga kuɗi ga kyawu ga wani irin aji da yake da shi,har suka isa Asibitin ABU da ke Shika Suhailah na Online tana aikin Chart da Friends,wani lokacin ta kan amsa call na ƴan uwansu da ke kira don taya ta murnan muƙamin da aka baiwa Maleek ɗin,lokacin da suka isa Yusuf Driver shi ya ɗaga waya ya kira Doctor Saiff ɗin bisa umurnin ubangidan nasa Maleek Ado,ba suyi jiran mintuna goma ba Doctor Saiff ya iso wajen,tare da yin ma Suhailah jagora zuwa Office ɗinsa,da taimakonsa akai duk wasu gwaji da yake buƙata aka fitar da sakamako,wanda tashin farko ya fahimci akwai babban damuwa,sabida gwajin da Scaning ɗin da akai mata ya nuna illan da Pills ɗin da ta sha yai mata,ya zaunar da ita yana mata bayani akan irin haɗarin da tun farko yin planing ke dashi musamman ga mata masu ƙarancin shekaru kamanta,daɗin daɗawama ita da sam bata taɓa ɗaukan ciki ba,ya cigaba da faɗin "Ranki da daɗe yin planing ga mace me ƙananun shekaru babban hatsarine ga mace me shekaru ƙanana kama daga 23years zuwa 24years,musamman ga macen da bata wuce haihuwa 1 zuwa 2 ba,ta saka kanta ayin family planing ta hanyar shan ƙwayoyi ko kuma yin allura ko saka roba,wannan babban hatsarine da ke illata mahaifar mace musamman ga wadda bata taɓa haihuwa ba kamar ke,illa ce da ke hana haihuwan kwata-kwata da maida mace inferlity acikin rukunnan planing da suka kasu kamar haka
1.DEPO PROVERA_wannan allurace da mata kanyi domin samun tsaikon haihuwa na wata (3)wanda kafin yinta sai an tabbatar da mace tayi haihuwa kusan 6 ko 7 sabida allurace me matuƙar ƙarfi da hatsari dake lalata mahaifa da canzawar period ga mata,wannan alluran ba'a yiwa mace me haihuwa 1 ko 2 zuwa 4 sai wacce tai haihuwa kaman 7 sannan akwai
2.NORISTERAT _wannan allurace da ake yiwa mace ta tazarar wata (2) ita ana iya yiwa mace me haihuwa 1 ko 2 sabida ita wannan alluran tana da sauƙin sha'anin akan (Depo provera) ta wata Sannan akwai
3.PILLS_Wato shine ƙwayoyin da mace ke sha don hana ɗaukar ciki,irin wanda ki kai anfani dashi wanda shima yana da kalan nasa illan na saka zubar jini koba a time ɗin period ba,sannan shima yana hana haihuwa kwata-kwata."
Doctor Saiff ya dakata yana zubawa Suhailah ido ganin yadda ta firgice,domin an taɓo tsarin da tabi wato shan pills,cikin tashin hankali ta dubi Doctor Saiff tana faɗin "Yanzu Doctor nima kana nufin zan iya rasa haihuwa kwata-kwata kenan? Na shiga uku ni Suhailah!"
Tayi maganan muryanta na wani irin rawa tuni wani irin zufa ya fara wanke ta,Doctor Saiff da tausayinta ya kama shi yayi saurin faɗin "No Madam bazan iya ce miki haka kai tsaye ba domin Allah shi ke ikonsa a duk sanda yaso,ni dai ina miki bayani ne kan ilimina da aikina,zaki iya rasa haihuwa za kuma ki iya samu idan Allah ya nufa hakan ya kasance,sai dai ina sake jaddada miki kinyi wauta me girma da kika illata kanki da kanki,domin fara planing a wajen mace irinki me ƙarancin shekaru babban illa ce da haɗari me girma,musamman ke da bakima bari kinyi ko da haihuwa 1 ba,haba Madam me zaisa ki aikata wannan wautan sabida kawai son boko da ke rufe muku ido da gayu ko? Kin ganni nan matata na aureta ko 100 level bata shiga ba,a gidana ta shiga jami'a kuma a shekaran da ta shiga ta samu cikin fari,a haka ta haife ta raini yaron tana kuma cigaba da shiga skull,kuma ko bayan ta haihu ban taɓa tunanin muyi tsarin iyali ba sabida na fi kowa sanin illan da ke tattare da shi,a haka tana karatu tana haihuwa,ni ke ɗaukan nauyin biyan masu raino don su rage mata wahalan hidima,amma har ta gama karatu bamu taɓa yin komi da sunan planing ba,bare ke da kike da Oga kuɗi ba matsalan ku bane,ko masu raino goma kike so za'a ije miki,gaskiya kinyi wauta me girman gaske,yanzu zan ɗaura ki akan wasu magunguna,da zaki anfani da su har tsayin wata biyu ko uku,daga nan kuma sai a jira a ga abinda Allah zaiyi."
Ya ƙare maganan yana kallon yadda idanun Suhailah tuni suka fara zubar da hawaye,a matsayinsa na babban likita a kuma fannin da ya shafi mata,ya sani dole sai yayi aikin lallashi da kwantar da hankalin Suhailan,yayi mata faɗa da farko ne sabida ta gane kuskuren da tayi abaya me girma ne,a hankali ya fara kwantar mata da hankali da kalamai masu kyau,yana nuna mata su likitoci ba Allah bane,da idan suka yanke kaza dole hakan zai faru,a'a Ubangiji na iya nuna ikonsa a duk sanda yaga dama,duk wani bayaninsa da kalaman da yaita anfani dasu wajen kwantar da hankalin Suhailah,kusan zan iya cewa baiyi wani tasiri ba domin zuciyanta gaba ɗaya a razane take,tana hango yadda zasu kwashe da Maleek da kuma Hajja idan har hasashen likitan ya tabbata cewa zata iya rasa haihuwan baki ɗaya,wani irin kuka ke son ƙwace mata tana dannewa,cikin hanzari ta miƙe bayan Doctor Saiff ya damƙa mata takaddan da ya rubuta mata magungunan da zatai anfani da su ɗin,ta fice da sassarfa bata ko ganin gabanta sosai,har ta isa wajen da Yusuf ya faka mota yana jiranta,tun daga nesa ya hango yanayinta ya tabbatar akwai damuwa,hakan yasa shi saurin fitowa ya buɗe mata gidan baya ta shige ya maida murfin motan ya rufe,tare da zagayawa mazaunin Driver ya tashi motan,tunda suka ɗauki hanya Suhailah kuka kawai take,sam bata da mu da cewa tana tare da Drivern mijinta bane,a can asibitin kuwa bayan fitanta Doctor Saif A.Maleek Ado ya kira kai tsaye tare da zayyane masa komi,ya kuma sanar dashi magungunan da ya rubuta da yadda zatai anfani da su,Maleek ɗin yai masa godia sukai sallama,take ya shiga neman line ɗin Suhailah amma yana ta Ringing taki ɗauka,sai ya maida akalan kiran zuwa ga Yusuf da ke Driving ɗinsa gently,jin shigowan kira yasa shi ciro wayansa ya duba,ganin sunan Oga ne yasa shi ɗaga wayan da hanzari,daga ɓangaren Maleek kai tsaye ya furta "Ka wuce da ita gidan Hajiya,ka sanar mata ta baka takaddan maganin da aka rubuta,yanzu zan saka maka kuɗi a account da zaka cire kaje ka siyo maganin."
"Okey an gama ranka ya daɗe." Cewan Yusuf bayan ya gama sauraren Maleek ɗin,wanda shi kuma bai ƙara cewa uffan ba ya kashe wayansa yana furzar da wani irin huci me zafi,tsananin takaicin abinda Suhailah ta aikata na tafasa zuciyansa matuƙa,domin a cikin ƴan watannin nan wani irin sha'awa da son haihuwa aka jarabci zuciyansa da ita,ta yadda duk inda ya hangi ƙananan yara suke bashi sha'awa ya dinga ji kaman ya buɗe ido ya gansa da nasa ɗan ko ƴar,sai dai ga matsalan da Suhailan ta janyo musu wanda a yanzu basu da tabbacin zata haihun ko bazata haihun ba kaman yadda bincike ya nuna zata iya rasa haihuwan baki ɗayama.
A ɓangaren Suhailah da ke kuka kasharɓan kuwa,har suka iso gidan Hajiya bata iya cewa Yusuf uffan ba,domin tun daga yadda yake amsa wayan ta san cewa da Maleek ɗin ne,shine kuma ya bashi umurnin ya kawo ta gidan Hajiyan,sai dai bata san manufansa na yin hakan ba,murfin motan ta ɓalle tare da zuro ƙafafunta waje,dai-dai lokacin da Yusuf ke sanar da ita saƙon Maleek ɗin,ba tayi magana ba sai hannu da ta saka ta ciro takardan maganin daga jaka ta aje masa akan seat ɗin,ta fice baki ɗaya daga motan ta nufi cikin gidan kuka me ƙarfi na ƙwace mata........✍🏻
*Littafin TAIMIYYAH paid book ne akan 500 naira only,ga masu buƙatan yin payment zakui min magana ta wannan number ɗin 08167768704, ko kuma ku turo kuɗin ku kai tsaye ta wannan account ɗin 0504192664 aisha ibrahim dansabo GTbank.*
*Sai ku tura shaidan biyanku ta wannan line ɗin 08167768704.*
_Masu account da Arewa books,zaku dinga siyan sabbin shafuka dalla-dalla akan farashi me sauƙi,ga yadda zaku siya pages a arewa books kamar haka_ 👇🏻
https://arewabooks.com/chapter?id=62d29e11aa5f8f19bc9621cb
*DANNA LINK DIN NAN KASHA KARATU👆🏽👆🏽👆🏽*
*_YADDA ZAKA SIYA LITTAFI A AREWABOOKS_*👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾
*Recharge* - inda ake shiga domin saka kudi cikin account.
*Balance* - Zai nuna kudin account dinku da zaku iya sayayyan littafai cikin kasuwar ArewaBooks.
*Credit/Debit Card* - Hanyar farko kuma mai dadi wajan Recharge din account dinku.
A inda (Enter your amount) za'a saka kudin da akeson Recharge din sai a taba "Proceed". Zaibude muku inda zaku saka bayanan katin banki, kuna gamawa kudinku zaishiga account dinku kaitsaye (instant).
--------
Akwai wasu hanyoyin saka kudi a ArewaBooks account kamar:
*Bank Transfer*
*Airtime Transfer*
Saidai su ba kaitsaye bane (instantly) sai ArewaBooks ta tabbatar da Transfer din, amman bayakai 1hour za'a gansa a Balance.
#Ɗansabo ce#
[12/14, 10:04 PM] +234 703 769 7050: *TAIMIYYAH*❤️
©️Ayshat Ɗansabo Lemu✍🏻
*Page 16 to17*
_______Ita dai Hajjah tana zaune da wata baƙuwa maƙwafciyanta da suka tare,ta shigo a gaisa kawai sai faɗowan Suhailah suka gani cikin falon tana rasgan kuka,Hajiya Aysha ta ruɗe tana faɗin "Suhailah lafiya?" Amma maimakon Suhailah ta tsaya sai wucewa tayi direct zuwa ɗakinta da tai ƴan matanci,ta faɗa gado tana cigaba da kuka sosai,bayan tayi wurgi da Hijab da jakanta bisa Bed ɗin,Hajiya Aysha da suke kira da Hajjah ta biyo bayanta tana cigaba da tambayan "Keh! Lafiya zaki shigo min gida kina kuka,meyafaru ina shi Maleek ɗin me yai miki?" Duka Hajjah ta jera mata tambayan tana kaiwa zaune bakin gadon da Suhailan ke kwance,kaman jira Suhailan take Hajjah takai aya ta sake ɓarkewa da kuka,cikin kukan take faɗin "Hajjah na shiga uku na,na cuci kaina da kaina idan har bazan haihu ba na bani Hajjah,wallahi ina son Yah Maleek irin son da bazan iya zuba ido in gansa da wata ba,bare har ta bashi abinda ni nakasa bashi,wayyo Hajjah na bani na shiga uk..."
"Kul! Suhailah bana son alkaba'ai na banza,ki faɗi min kawai meke faruwa?"
Hajjah ta katse Suhailan tana kamo hannunta ta riƙe cikin nata,burinta kawai taji meke faruwa don sosai taji ƙirjinta na bugawa sam bata son tashin hankali da duk abinda zai sata cikin damuwa,lokacin da Suhailah ta gama zayyane mata yadda sukai da Doctor Saiff,sai sakin hannun Suhailah Hajjah tayi tana jifanta da mugun kallo take faɗin "Shine zaki shigo min gida ki ruɗani kina ta faman kuka kaman anyi mutuwa, ina ce tun farko kece kika kai kanki da kanki kika fara amsan magungunan kina ɗirkawa cikin ki,ba tare da kinyi zurfin nazari da tunanin irin wannan ranan zai iya zuwa miki ba,babu abinda zan ce miki Suhailah sai dai ince kinyiwa kanki ne aduk me zai biyo bayan abinda kika aikata ba tare da amincewan mijinki da shawara da kowa ba,sannan kisa a ranki ko yau Abdul-Maleek ya kawo mata yace zai aura bazan taɓa hana shi ba."
Daga haka Hajjah ta miƙe fuu...! Ta fice daga ɗakin,ba tare da ta sake sauraran Suhailah wacce kalaman Hajjan suka sanya ta sake rushewa da kuka,danasanin da bazai mata anfani ba na lulluɓe zuciyanta,daman Hajjan take da hope akanta itace ke iya sanya Maleek yayi abu ko baya so,to gashi tana tabbatar mata da cewa ko Maleek zai mata kishiya akan matsalan rashin haihuwa bazata hana ba,ta sake ɓarkewa da kuka kanta na wani irin juwayawa,gaba ɗaya jin duniyan take tana mata ɗaurin goro.
Hajjah kuwa tsananin takaicin Suhailan da abinda ta aikata ɗin ne,ya hanata jin tausayinta ko kaɗan duk da cewa ƙasan zuciyanta da tausayin Suhailan,amma dole ta nuna mata kuskuren da ta aikata me girma ne,sannan ita da kanta idan har abinda likita ya tabbatar na cewa Suhailan zata iya rasa haihuwa baki ɗaya ya tabbata,to babu shakka ita da kanta zata sanya Maleek ɗin ya sake aure,don bazata zuba ido ya ƙare ƙuruciyansa babu haihuwa ba,bata sake bi takan Suhailah da ta kume kanta a ɗaki taƙi futowa ba,ta cigaba da sabgan gabanta da ma'aikatan ta su Rabi me aiki,lokacin da aka kammala Lunch ma Hajjah sawa tayi aka haɗa komi aka kaiwa Suhailan ɗaki,amma ga tsananin mamakinta Suhailah sai ta koro Lubah da abincin wai bata ci,Hajjah murmushi kawai tayi ta cewa Luban ta kai abincin Dining ta aje,bayan kammala cin abincin da Hajjah tayi,sai ta ɗaga waya ta kira layin Maleek,wanda a lokacin yana tare da wani abokinsa a cikin babban falon gidan nasa,bugu biyu tayi ya ɗaga wayan bayan sun gaisa ne take sanar dashi zuwan Suhailah,tare da tambayan mi yake nufi da sawa akawo ta nan ɗin,ga ta nan ta ƙule a ɗaki taƙi cin abinci sai faman kuka take,amsan da ya ba Hajjan yasa ta kashe wayanta tana sakin murmushi,domin tafi kowa sanin halin ɗan nata ciki da bai,sai dai a wannan karon sam bazata goyawa Suhailah baya akan duk matakin da Maleek ɗin zai ɗauka akanta ba,ta cigaba da harkokin gabanta ba tare da ko sau ɗaya ta sake komawa ta duba Suhailan ba,wacce ta daɗe da yin baccin wahalan kukan da ta rasga,tana baccin tana sauke ajiyan zuciya irin na wanda yaci kuka ya ƙoshi,ƙarfe uku ta farka daga baccin ta kallo agogon ɗakin tana dirowa da sauri,ta nufi toilet don ɗaura alwala don ko sallan Zuhur bata yi ba,a gurguje ta fito ta gabatar da sallan zuwa lokacin da ta idar wani irin yinwa take ji sosai,hakan yasa tana cire Hijab ta fito zuwa Dining ɗin falon Hajjan,lokacin Hajjah na daga kishingeɗe cikin kujera,littafin addu'o'i take dubawa idanunta sanye cikin medical glass da ke ƙara mata ƙarfin gani,takun fitowan Suhailah baisa ta ɗaga kai ta dube ta ba,har sai da ta tabbatar ta isa ga wajen cin abincin sannan ta ɗaga kai ta dubeta tana sakin murmushi sosai,don dama tasan za'a rina fishi da abinci badai Suhailan ta ba,Suhailah tayi nisa acin abincin Hajjah ta ɗaga murya yadda zata jiyo ta tana faɗin "Oh! Ai ni na ɗauka da gaske fishi kike da abincin ba zaki ci ba."
Suhailah ta ɗago idanunta da suka ƙanƙace sabida kuka ta dubi Hajjah,tana shagwaɓe fuska take faɗin "Wallahi ba don ina da ulcer ba banso ta tashi da bazan ci abincin ba,tunda bakya tausayina kin daina so na Hajjah."
Suhailah ta ƙare maganan tana sakin hawaye sharr...! Abinda ya motsa zuciyan Hajjah sosai,taji wani irin tausayin Suhailan ya kamata,amma bata nuna ko a fuskaba sai ma haɗe gira da tayi tana faɗin "Maza ki gama cin abincin sai ki zo muyi magana,ki faɗi min ta inda na daina son naki?"
Daga haka ta ɗauke kai daga Suhailah ta cigaba da duba littafinta,aiko Suhailah na gama cin abincin ta nufo cikin falon tare da yin masauki akan kujeran da Hajjah ke kai,cikin narke fuska take faɗin "Hajjah yanzu da gaske sai ki goyawa Yah Maleek baya ya iya sake aure,don na samu matsala bazan haihu ba,bafa tabbaci aka bayar na bazan haihun ba hasashe ne kawai,kuma ga magani anbani zan sha na tsayin wata biyu,meyasa bazaku yi addu'an kafin lokacin ma cikin ya samu ba,ni yanzu wallahi ko ƴan goma yake so in haifa zan iya na shiryawa hakan Hajjah,amma bazan iya kallonsa da wata ba don Allah karki faɗi hakan agabansa."
Suhailah tayi magana tana zubama Hajjah ido,fuska a maraice zuciyanta na cigaba da shiga ƙunci na danasanin abinda Zubaida sheɗaniyan qawanta ta zugata ta aikata,Hajjah ta dubi Suhailan tana faɗin "Suhailah bana fatan hakan nima,sai dai ina so kisani idan har abinda ake hasashe ya tabbata,to tabbas kome zakice bazan goyi da bayan ki ba, shi kuma a tauyesa ba,ina fata Allah yai ikonsa ki samu rabo ko da yau ne ko gobe ne,duka me sauƙi ne a wajen Allah,amma kisani akwai abinda muke aikatawa na son rai,wanda mun san zai cutar da mu amma sabida son zuciya mu rufe ido mu aikata abin,wanda daga baya zamu zo muna danasanin da bazai mana anfani ba,shi kuma Allah ya hanamu abin a lokacin da muke da buƙatansa,wanda hakan shine ya faru da ke ko ince zai farun,don haka maganan ki sanya damuwa ma bai taso ba,kinyi wauta kin tabka kuskure Suhailah,ni ban taɓa ganin ma sakarya irin ki ba da zaki je ki fara shan maganin hana ɗaukan ciki alhali ko haihuwan fari baki bari kinyi ba,to yanzu kinga ga samako nan sai ki koki gaba idan ma Allah ya ji ƙanki ya kawo rabon a lokacin da ake buƙatansa,don haka maganan Maleek ni bazan shiga tsakani ba,ku je can ku ƙarata ke da shi tunda lokacin da kikai abinki baki shawarceni ba,kuma maganan na daina son ki da kike faɗi ki cigaba karki fasa."
Hajjah ta ƙare maganan cikin nunawa Suhailah kalman yai mata zafi matuƙa,hakan yasa Suhailah cigaba da kuka tana baiwa Hajjah haƙury,amma sai Hajjah ta ture hannun Suhailan daga jikinta tana jifanta da harara,qamshin turaren RALPH LAUREN daya buɗe falon ya ankarar da su Hajjah wanzuwan Maleek Ado cikin falon,suka ɗaga kai kusan a tare da Suhailah suna sauke ganinsu akan kyakykyawan fuskansa,wanda take a kirne babu wani alamun fara'a,ya zube hannuwansa duka biyu cikin aljihun Rigan tsadaddiyar yadin dake jikinsa,wanda kalan yai asalin yi masa kyau matuƙa,da alamu ya jima tsaye cikin falon basu ankara da shi ba,ganin duk sun xubo masa ido yasa shi fara takowa zuwa cikin falon,yaiwa kansa masauki cikin kujeran dake kallon wanda Hajjah da Suhailah ke kai,cikin muryansa me cike da ƙasaita da daɗin amo yake sake gaida Hajjah,ta amsa da fara'a akan fuskanta,a hankali ya maida kallonsa