Showing 159001 words to 162000 words out of 186776 words
Chapter 54 - TAIMIYAH Book Complete Document by Ayshat Dansabo Lemu .txt
sake gyara zama tana fuskantarsa sosai ta ce, "Kana jina fa Baban Sadeeq,na ce da yaushe ta samu mijin har aka sanya rana da gaggawa haka,mu da muke gida ɗaya bamu taɓa ganin ko ƙyallinsa ba?sai kawai rana tsaka mu ga waɗannan uban kaya kamar za a buɗe shagon provition,ina jiye muku tsoron kar ku ɗauki nakasasshiyar marainiyar Allah ku baiwa ɗan yankan kai, bayan biki ya miƙawa ƙungiya jininta su shanye,don dai daga ganin waɗannan kaya an san dukiya ne ya ruɗeku, har kuka amsa da gaggawa za ku sallamata,wai shin ma a ina ta samo mijin ne?"
Umma ta sake jefawa Baba Sani tambayar tana kafeshi da idanunta,sam bata damu da irin mugun kallon da yake bin ta da shi ba. Ya buɗe baki ya yi magana cikin ɓacin rai yana cewa, "A gabana Zuwairah, a gabana zaki buɗe baki kina furta irin waɗannan mugayen kalaman akan jinin Sameer? To kar ki kuskura ki ƙure haƙurina don zan mugun baki mamaki, da ki ke maganar ba ku san da samun mijinba, dole ne idan Zaynab ta samu miji sai an yi shela duniya ta sani,ko kuma dole sai kin sani kafin ayi komi sabida ke ce waliyiyarta ko? To bari ki ji ba zan ɗauki duk wani shirme ba,don ina sane da irin ƙiyayyar da ki ke nuna mata tun asali,kuma maganar kada mu baiwa ɗan shan jini,idan mun ba shi ki je ki ƙwatota daga hannunsa idan ya tabbata ɗan shan jinin ne,kar ki kuskura ki sake min magana makamancin wannan Zuwairah kinji na faɗa miki."
Baba Sani ya tashi fuu..! Ya bar mata falon ya shige ɗakin baccinsa, ransa a matuƙar ɓace da kalaman da Umman ta gaggaya masa. Umma ta bi bayansa da kallo tana jin wani tashin hankali na sake rufto mata,ga takaicin rashin samun cikakken amsar tambayarta, na son sanin cikakken waye wanda za su ɗauki auren gurguwar da ta tsana su ba shi? Tana shirin tashi ta bi Baba Sani Sadeeq ya yi sallama yana shigowa cikin falon, sai ta yi saurin dubansa lokacin da yake takowa zuwa cikin falon Baba Sanin, idanunsa akan uban kayan sanya ranar auren TAIMIYYAH da su ke tsibe. Ya samu waje ya zauna yana gaida Umma, wacce gaba ɗaya take jin tamkar ta ari hauka, sabida baƙin cikin da ke damun zuciyarta. Ta amsa gaisuwar Sadeeq a lalace kafin ta dubi cikin idanunsa tana jefa masa tambayar da ke cin ranta, "Kai Sadeeq wai wa ye mutumin da waccar gurguwar za ta aura? Da har ake ɓoye mana maganar tun farko,sai kawai muka ji labarin an sanya ranar aurensu, kuma don wulaƙanci wai duk gaba ɗaya za a yi bikin da na su Basmah,sabida a tozartamu a nuna ta samo me arziƙin da ya kere mazajen da ƴaƴana za su aura,don daga ganin wannan uban kayan an san cewa ba daga ƙaramin gida suka fito ba,sanar dani ɗan gidan uban waye za ta aura a garinnan?"
Sadeeq ya yi saurin duban Umma yana mamakin yadda ta fusata, tana ɗaga murya cike da zallar tashin hankalin da ke haskawa akan fuskarta,ya ɗan cije bakinsa yana jin tsanar halayyar mahaifiyar tasa na ƙona ransa, ya buɗe baki a hankali ya ce, "Umma ni ma ban san shi ba,amma Baba ya ce ɗan gidan tsohon Asistant Controller ne da ya rasu, Marigayi Alhaji Ibrahim Ado,sunan guy ɗin Alhaji Abdulmaleek Ado, ana kiran da Maleek Ado kaɗai,gaskiya a yadda Baba ke bani labari ba ƙananun mutane ba ne, don sun tara arziƙi me ɗinbin yawa,gashi guy ɗin a yanzu haka shike riƙe da muƙamin Chairman na Shiffing Board na baki ɗaya. Kin ga ko baƙaramin mutum ba ne ,duk da cewa yaro ne ba wai Babba ba don duka bai ma kai 40yrs ba thirty something ya ke."
Sadeeq ya gama ratafawa Umma jawabin cike da basarwa, idanunsa akan uban kayan da ke tsibe cikin falon Baban nasu. Umma da tuni zufa ya gama jiƙe wani ɓangare na jikinta, sai ta dubi Sadeeq cike da ɓacin rai ta ce, "Eh lallai dole a ɓoye mana ayi komi a munafurce,sabida ni ce da ƴaƴana ba a so da alkhairy sai musaka gurguwa. Duk kuma ba kowa ke da alhakin hakan ba sai waccar tsohuwar makiran kakar ta ku Iyah. Sabida na ji ana ƙishin-ƙishin cewa wai ai uwar Mutumin ce, suka kaɗe TAIMIYYAH ɗin watannin baya,ka ga kenan Iyah ita ce ta kitsawa uwar tasa wannan munufurcin, akan su haɗa aure tsakanin gurguwarta da ɗan matar,to Allah yasa ba ɗan ƙungiya bane ya je ya sai da ita bayan auren."
Sadeeq ya yi hanzarin duban Umma yana faɗin, "Subhanallah! Umma wani irin kalami ki ke yi haka marar daɗin ji? Don Allah ki sanyawa zuciyarki salama, ki yi wa Zaynab fatan alkhairy ne ba sharri ba,ni dai ina ji a jikina cewa alkhairy ke bibiye da rayuwarta In sha Allah. Kuma ina farin ciki da wannan auren da za ta yi , Allah ya bashi ikon riƙe ta da amana ita da abokiyar zamanta."
"Au yana ma da aure shi ne za a ɗauki gurguwa a cinna masa? Eh! lallai wannan ya nuna cewa tsabagen kwaɗayi da son a nuna mana iyakarmu ace ta auri me arziƙi ne,shiyasa makirar ta ƙulla abin."
Umma ta sake kwaɓowa Sadeeq waɗannan banzayan kalaman,hakan yasa Sadeeq tashi ya baro falon Baba Sanin, ba tare da ya tsaya tambayar Umman akan cewa ko Baba Sanin na nan ba?
____________
Daga can Part ɗin Ummie kuwa TAIMIYYAH ce zaune ita da Ummie, suna magana akan Doughnut da TAIMIYYAH za ta yi a raba sadaka, ranar da Ummien za ta fita takaba nan da sati me zuwa. TAIMIYYAH ta dubi Ummie tana cewa, "Amma dai Ummie za ki zauna anan tare da mu, ba gida Kd za ki koma ba ko?"
Ummie da gaba ɗaya a ƴan kwanakinnan ta ke sake jin kewar mijinta da yaranta me tsanani na damun zuciyarta,ta yi murmushin ƙarfin hali tare da cewa, "To ganinan dai Zaynab,zan cigaba da zama dai har zuwa ayi bikinku sannan sai na tattara na koma gida,sai dai na dinga kowawa Iyah ziyara time to time,ni duk na ƙosa ma time ya zo mu sha biki in ga cewa na aurar da ɗiyata, ko kya haifomin jikokin da zan yi alfahari dasu."
TAIMIYYAH ta yi saurin kai bakin gyalenta ta rufe fuskarta, cike da tsananin jin kunyar kalaman Ummien. Ummie ta saki dariya kunyar TAIMIYYAH na sake birgeta, tare da haifar da tarin ƙaunarta me tsanani a cikin zuciyarta. Ta buɗe baki cike da son sake tsokanar TAIMIYYAH ta ce, "Haba daughter ko ke baki son ki haifo little Nahar ne ,wacce za ta dinga ɗebe mana kewar wacce muka rasa?"
TAIMIYYAH da kalaman Ummie suka motsa zuciyarta,sai ta yi saurin duban fuskar Ummie da ke faman murmushi ta ce, "Ina so Ummie in dai Allah zai bani ina so,kuma In sha Allah zan roƙa a maida min sunan Nahar ɗita da na rasa."
Yadda TAIMIYYAH ta yi maganar fuskarta na haskawa da tarin kewar ƴar uwarta,ya sanya Ummie jin zuciyarta ta taɓu,ta yi saurin kauda zancen ta hanyar faɗin, "In sha Allah Zaynab za ki haifa,Allah zai ba ki rabo da gaugawa kamar yadda auren ya zo cikin gaugawa."
Daga haka Ummie ta mai da hiran ya koma tattaunawa akan yadda za su shirya shagalin bikin, idan lokaci ya yi, ita dai TAIMIYYAH kunya ya hanata biyewa Ummien su yi maganar yadda ya dace.
Kiran Maleek da ya shigo cikin vid call ne ya sanya TAIMIYYAH tashi ta nufi bedroom ɗin Ummie don amsa wayar.
A kan Sofa da ke cikin ɗakin ta yi masauki lokacin da take receiving call ɗin, tare da gyara zaman gyalen da ta yafa ajikinta.
Ta saki kyakykyawar murmushi lokacin da face ɗin Maleek ya bayyana a allon screen ɗin sabuwar wayar da ya siya mata,wani irin soyayyarsa ta ke ji a ƴan kwanakinnan na ƙaruwa a cikin zuciyarta.
A.Maleek Ado wanda ke kwance akan doguwar kujerar 3 seater,wanda ke cikin haɗaɗɗen falon gidansa da ke can Lagos,ya sauke idanunsa akan face ɗin TAIMIYYAH, yana jin wani irin sabon feeling akanta na kewaye jinin jikinsa.
"Yaya Maleek ina yini ya aiki?"
TAIMIYYAH ta furta da muryarta me cike da shagwaɓar da ke motsa zuciyar Maleek Ado. Ya kafeta da ido yana taɓe baki kaɗan ya ke faɗin, "Wife ni fa ban san wannan sunan wai Yaya, ta ina na zama Yayanki in banda son kalar dangi, cewa za ki yi ina yini Darling."
Yadda ya yi maganar a miskile ya sanya TAIMIYYAH zunɓure baki tana sakin murmushi,cike da shagwaɓa ta narke murya ta ce, "Ni dai Yayana ne kai, tunda ni ƴar Hajjah ce ka ga kenan kai Yayana ne."
"No wife ni ban yarda ba,tunda soon za a ganki da ƙaton cikin da za ki haifo min twins, don da nayi mafarki kin yi ciki an ce twins za mu samu. Kin ga kenan ni ba Yayanki bane, ko Yayanki zai iya yi wa ƙanwarsa ciki ne ta haihu?"
Maleek Ado ya yi maganar cike da basarwa, tamkar ba sakin layi ya yi ba ko a jikinsa. TAIMIYYAH da tsananin kunya ya lulluɓeta sai ta yi saurin jan gyalenta, ta rufe face ɗinta da hannu ɗaya,cikin murya me cike da shagwaɓa ta ce, "Don Allah Yah Maleek ka bari, ni wallahi kunya na ke ji zaka sa in kashe wayata Allah kuwa."
Maleek ya saki ƙaramin smile yana saurin faɗin, "No wife wallahi kar ki fara kashe min waya,kuma a buɗe min fuskata ni banson wani gulma, wai a dole ana jin kunya ta."
TAIMIYYAH ta buɗe fuskarta har lokacin kunyar kalamansa ta ke ji, shi ko ya basar ko ajikinsa sai ma cigaba da zaro mata zance ya ke yi. Sun ɗauki lokaci suna waya,kafin Maleek ya yadda su yi sallama,ganin lokacin kiran sallar magrib ya kusa.
Lokacin da TAIMIYYAH ta koma Sasan Iyah, ta same su ne zaune ita da Baba Sani,da alamu suna tattauna magana ne me muhimmanci, hakan yasa TAIMIYYAH na gaida Baba Sani ta shige ɗaki.
Sai da daddare ne bayan sun kammmala yin dinner, Iyah ke sanar da TAIMIYYAH maganar da suka yi da Baba Sani,akan son ya nemi auren Ummie da zaran ta fita takaba nan da sati ɗaya me zuwa. TAIMIYYAH ta dubi Iyah da wani irin tarin farin ciki daya haska cikin idanunta,bakinta har rawa yake wajen faɗin, "Wow! Iyah aiko kin yi tunani me kyau, to me Baba Sanin ya ce?"
Iyah ta saki murmushi ta ce, "Cewa ya yi in bashi lokaci ya yi tunani,sannan ita ma Ummie in sameta da maganar, idan har ta amince a shirye ya ke da ya amsa aurenta." Iyah ta cigaba da cewa " Wallahi bana so ta kufce mana don sai yanzu na karanci kyawawar halayyar da ta ke da su. A da ina mata kallo wani iri sabida yadda na ke ganin tana share lamarinki,shiyasa aka ce baka sanin halin mutum sai ka zauna da shi,zan sameta da maganar zan kuma yi iyakan ƙoƙarina wajen ganin cewa ta amince da auren Sani,ko ya samu mata me hankali da ta san abinda ta ke yi, Sabida Zuwairah ba macen arziƙi ba ce sam! Don har yanzu maganar da na ke yi, bata tako ta ce ko Allah ya sanya alkhairy da sanya ranar aurenki da aka yi ba, sabida tsabar hassada da baƙin hali,daga ita har ƴaƴan na ta kallonsu kawai na ke yi,kuma baƙin ciki yanzu suka fara in dai a kan aurenki da Maleeku ne."
Iyah ta kai ƙarshen maganar cike da jin zafin baƙaƙen halayyar Umma da yaranta.TAIMIYYAH ta taɓe baki tana cewa, "Iyah kenan ni ban taɓa sawa raina cewa suna cikin jerin mutanen da za su taya ni murna, ko farin ciki don zan yi aure ba, Allah dai yasa Ummie ta amince ta auri Baba Sani Iyah,idan hakan ya kasance zan fi kowa farin ciki,wallahi har na ƙosa in ga yadda Umma za ta yi."
TAIMIYYAH ta yi maganar murmushi na blushing a samar fuskarta.......✍🏻
#Ɗansabo ce#
[12/14, 10:13 PM] +234 703 769 7050: Littafin TAIMIYYAH paid book ne,ga duk wanda ta tsincesa a kowani irin group ne,kiji tsoran Allah karki karanta sai kin biya 500 naira only.
Za ku iya min magana ta wannan number ɗin 08167768704, ko kuma ku turo kuɗin ku kai tsaye ta wannan account ɗin 0504192664 aisha ibrahim dansabo GTbank.*
*Sai ku tura shaidan biyanku ta wannan line ɗin 08167768704.*
Masu turo credit za ku turo katin MTN na 500 ta wannan line ɗin 08167768704.
_Ina ƴan kasuwa masu buƙatar a tallata muku hajar ku? Maza ku garzayo da kuɗi ƙalilan a tallata muku kayan siyarwanku sai dai kawai ku ji ana kiran waya don buƙatan sayan kayan ku,ku tuntuɓeni ta layina kamar haka 08167768704._
*64*
*Abuja*
Jawahir ta dubi Suhailah wacce ta sake ramewa, ta fita hayyacinta sabida kishi,don tunda aka sanya ranar auren Maleek da TAIMIYYAH, hankalinta ya ke a matuƙar tashe. Duk kwanakin da ta yi wajen Hajjah da irin yadda Hajjah ta dinga ƙoƙarin ganin Suhailah, ta kwantar da hankalinta ta fahimci cewa,ƙarin auren da Maleek ɗin zai yi ba yana nufin cewa ya daina sonta ko ƙaunarta bane,zai ƙara auren ne sabida haka Ubangiji ya tsaro, cikin littafin ƙaddaran kowannensu. Suhailah sam bata fahimci hakan ba,abinda kawai ta sanya a ranta shine Hajjah ta daina ƙaunarta, ta nuna mata cewa ta fi son Maleek tunda shi ta haifa ba ita ba,shiyasa ta ke jin zafin Hajjah sosai game da wannan ƙarin auren,wanda take ganin tamkar farin cikin rayuwarta ake shirin tsaidawa.
"Suhailah ki kwantar da hankalinki don Allah,wannan maganar auren fa ban ga wani big deal a cikinsa ba, tunda ma musaka zai auro,ina ke ina lalata kanki da zafin kishi akan gurguwa? Wacce na tabbatar kin fi ta diri da komi,ke da bakinki fa ki ke faɗin uwarsa ce ta haɗa abin,kin ga kenan shi kansa Maleek ɗin,ya amince ne don kawai yana kwaɗayin ya ɗirka mata ciki ta haihu,ki kwantar da hankalinki kin nuna cewa komi ya wuce,ni zan shirya miki duk yadda za ki bi da su,sannan idan akwai kuɗi a wajenki ki kawo ai miki aiki, don ki mallaki mijinki yadda sai abinda ki ka ce,yanzu an daina zama haka kara zube, ke na ga alamun kan ki har yanzu a kulle ya ke,mu ai mana kishiyar mana don uban mutum!"
Jawahir ta kai ƙarshen maganar tana wani taɓe baki,idanunta a kan Suhailah da tayi sakato da baki tana kallonta. Suhailah ta sake zubawa Jawahir idanu kafin ta buɗe baki ta ce, "Jawahir ni sai ki dinga min magana a dunƙule, ki fahimtar da ni inda kika dosa please!"
Jawahir ta saki murmushin fara samun nasara, kafin ta ɗan tsuke fuska tana kai bakinta kusa da kunnin Suhailah, ta fara yi mata raɗa a kunni, ni dai sam ban ji me Jawahir ɗin ke raɗawa Suhailah a kunnin ba.
Jawahir bayan ta gama yi wa Suhailah raɗa ne ta koma ta gyara zamanta tana cewa, "Yanzu yaushe Maleek ɗin zai shigo miki weekend?"
Suhailah ta taɓe baki kaɗan tana baiwa Jawahir amsa ta ce, "Ina ga nan zuwa jibi zai shigo tunda 2 weeks kenan bai shigo ba."
Jawahir ta yi murmushi ta ce, "Okey to ki dai yi duk yadda na ce ɗin,kar ki taɓa bari ya samu kanki cikin sauƙi, kin dai gane me na ke nufi ai?"
Suhailah ta jinjina kai tana duban yadda Jawahir ta ci serious sannan ta ce, "Eh duk na gane ƙawata,kin san yadda na ke jin haushinsa kuwa a yanzu? Hmm! Ni babu abinda ke min ciwo idan na tuna wai gurguwa Maleek zai amince ya aura, har ya ke nuna rawar ƙafa irin haka,don da gaske nuna son auren ya ke yi ,ke kya ce lafiyyyace Yarinyar,ni duk na ƙosa in ga shegiyar ma ,na ji Hajjah ta ce dai wai tana tafiyarta in ta dafa guiwa."
Jawahir ta taɓe baki tana sakin dariyar mugunta ta ce, "To ai za ki ganta ranki-ya-daɗe,kar ki wani damu da kanta ma za ta sai ta ma kanta hanya, in ta ga cewa kinfi ƙarfinta,ke dai kawai ki yi yadda na ce ki samu ya amince miki, mu kuma idan hakan ya kasance za mu aiwatar da abinda ya kamata."
Suhailah ta jinjina kai cike da gamsuwa, sannan suka cigaba da magana da Jawahir,wacce ta ke ɗaurata akan gadar zaren da ba zai kai Suhailah ko'ina ba sai tashar nadama.
____________
*Zaria*
Kwanaki sun cigaba da shurawa ana cigaba da tsare-tsaren, yadda shagulgulan bikin su TAIMIYYAH zai gudana,wanda ya rage saura sati uku dai-dai. Iyah sam ba a zama kullum cikin kai kawo ta ke, na shirye-shiryen yadda za ta fita kunyan baƙi,wanda tuni ta fara aika goro da sweet na gayyata,hatta dangin Mamar TAIMIYYAH da ke can Daura an aika musu da komi da komi.
Ta ɓangaren Hajjah uwar Ango ma tuni sun kammala duk wani shirinsu,hatta sabon gidan da za a aje TAIMIYYAH a cikin GRA ya kammala,an kuma zuba komi na more rayuwa a cikinsa ,sai ɗakuna biyu ne kacal Hajjah ta ce a barsu, kar a zuba komi sabida a bai wa su Iyah daman nuna bajintansu su ma,sabida ko yaya ne mace na son a shigo gidanta a nuna wani abu ace daga gidansu ta taho da shi. Hatta da lefe an kammala haɗawa, kuma duk abinda aka siyawa TAIMIYYAH haka ta sa aka siyawa Suhailah ita ma,sai dai bambamcin akwatuna biyu da Hajjah ta ƙarawa TAIMIYYAH, wanda cikin aljihunta ta shiga ta siya kayan da aka zuba aciki,jiran zuwan Maleek kawai ta ke yi wanda zai iso garin jibi,idan ya ga Lefen sai a ɗauka akai can Fam House ɗin su TAIMIYYAH, kamar yadda aka sanar da su Hajjan.
___________
"Zee ina ga fa za a cire wani Bridal Shower don ni bana buƙatar yin komi da ya wuce Walima."
TAIMIYYAH ta yi maganar tana duban Zee da ke zaune daga ƙasan carfet ɗin ɗakin TAIMIYYAH, Zee ta dubi TAIMIYYAH ta ce, "Haba dai Namcy meyasa za ki ce haka,don Allah mu dai ki bar mu mu raƙashe yadda mu ke so,na ki kawai ki cakare ayi pics, banda haka bamu ce ki damu kanki akan komi ba,kin san ma Yasmeen ba za ta taɓa yarda a fasa yin Birdal Shower ɗinnan ba ,yadda taci