Showing 21001 words to 24000 words out of 186776 words
Chapter 8 - TAIMIYAH Book Complete Document by Ayshat Dansabo Lemu .txt
ne a ABU da ke congo tana karantar Law,Sameer mahaifinsu Alhaji Amadu ne ya gina masa babban flat a filin da ke cikin gidan wanda ya siya ne dama sabida su biyun shi da qaninsa Sani,da aka tashi fara ginin sai aka gina duk biyun a lokaci guda kuma ginin iri ɗaya komi da komi,daga Iya har Baba Amadu kaman yadda ake kiran mahaifinsu Sameer ɗin,hankalinsu ya kwanta da auren Sameer tun abinciken farko da sukai game da nagartan Iyayen TAIMIYYAH,sai dai basu sake gasgata hakan ba sai da TAIMIYYAH ta shigo cikin gidan,sannan Iya ta sake sanin ɗanta yayi dace da mace ta gari,sam bata da hayaniya ga tsananin kunya kaman ba ƴar boko ba,tana da biyayya matuƙa agun mijinta da su Iya,hakan yasa cikin ƙanƙanin lokaci ta siye zuciyan Iya,wacce Allah ya ɗaura mata son matan ɗan nata,har yakai ta daina mata kallon suruka ta koma yi mata kallon ƴar da ta haifa,kasancewan mace ɗaya ta haifa kuma tayi nesa da ita,don Anty Bilki kaman yadda ake kiran Bilkisun sam bata cika zuwa gari ba inba da wani abu ba,mijinta me kulle ne sosan gaske shiyasa Iya da ta samu TAIMIYYAH a matsayin suruka ta gari sai ta maida ta tamkar ƴa,sam bata taɓa ganin aibun yarinyar ba sabida biyayyan da take mata da yadda ta iya kula da ɗanta,domin cikin shekaru biyu da aurensu da Sameer ɗin kowa sai tanka irin kyawun da yayi wanda ke alamta yana samun nutsuwa da kwanciyan hankali,itama TAIMIYYAH tayi wani girma da cika duk da cewa bawai jikin ƙiba can gareta ba,cikin kwanciyan hankali take cigaba da karatunta,sam Iya bata sanya musu idanu a lamuran su irin yadda wasu surukan keyi,ba ruwanta da shiga Sasan su sam sai in wani ba lafiya a cikinsu ta leƙa tace sannu,TAIMIYYAH itace me tarewa a Sashin Iyan da zaran ta dawo Skull,cikin haka Sameer ya samu aiki a Kaduna a wani ma'aikata me suna NNDC,don haka sai ya koma zuwa duk Weekend,haihuwa shiru-shiru har sun shiga shekaru uku da aure,Iya bata taɓa nuna damuwa ba sai binsu da addu'a da take yi,a cikin haka shima Baba Sani ya gabatar da Zuwaira a matsayin wacce zai aura,sun haɗu da ita tun wajen bautan ƙasa wanda shi aka tura shi Yobe,a can suka haɗu suka kamu da son juna wanda ƙarfin soyayyan duk ta wayane,don Yobe ba kusa bane baya samun zuwa,sai da Iyayen Zuwairan suka buƙaci ganinsa sannan ya wanke ƙafa yaje can Yoben,Maman ta asalinsu Shuwa ne sai Baban ne fulanin Yobe,lokacin da Sani ya gabatarwa Iya zancen sam ba haka taso ba,ta so ya samu yarinya a kusa yai aurensa ko don sauƙin bincike amma ya dage shi sai Zuwaira,Alhaji Amadu yace a barsa da zaɓinsa ya tashi qanninsa da wani abokinsa ya tura su Yobe domin bincike,aka tabbatar musu da Iyayenta mutanan kirki ne.....✍🏻
#Ɗansabo ce#
[12/14, 10:04 PM] +234 703 769 7050: *TAIMIYYAH*❤️
©️Ayshat Ɗansabo Lemu ✍🏻
*Page10*
Ba'a ɗauki wani dogon lokaci ba aka sanya ranan auren Sani da Zuwaira,kwanaki suka cigaba da shuɗawa har zuwa lokacin da aka ɗaura aure aka ɗakko Amarya daga Yobe aka kawo masa ita Zaria,Iya da ƴan uwanta sun sha hidima TAIMIYYAH ma ba'a barta abaya ba wajen hidima da baƙi,har zuwa lokacin da taro ya watse aka bar Amarya da Angonta,Amarya Zuwaira bata wani jima ba ta fara bayyana halayyanta tsaf,irin matannan ne masu hassada da baƙin hali,tunda ta fahimci matar wan mijinta wato Zainab TAIMIYYAH ta fita hutawa,mijinta yafi na ta wadata shikenan ta ɗauki karan tsanan da nuna kishinta afili akan TAIMIYYAN,kai kace sun haɗa miji ɗaya ne,Iya tun ba ta kula da yadda Zuwairan ta fara nunawa Zainab munanan halaye har ta karanci inda Zuwairan tasa gaba,hakan yasa ta zaunar da Zainab tai mata nasiha akan cewa sam ko da wasa kada ta biye ta Zuwairan har wataran aji kansu,ta kama girmanta a matsayin ta na babba kuma mijinta shine gaba dana Zuwairan,Zainab TAIMIYYAH ta ɗauki nasihan Iya da girma sosai,kuma sai akai sa'a ita ɗin me tsananin takatsantsan da kauda kaine,sam bata shiga shirgin Zuwairan tunda ta gane inda tasa gaba,ta maida hankali da kula da karatunta da Mijinta idan yana gari,a hankali watanni suka fara shuɗawa cikin da Zuwaira ke ɗauke da shi ya fara turowa,wanda sam babu wanda yasan da samuwansa daga Iya har Zainab ɗin,domin sam Zuwairan bata shiga shirginsu ko Iya bata damu da zuwa Sasanta ta gaida ta ba,sai ta busa iska wanda sam Baba Sanin bai san da hakan ba,Sosai Iya har ma da TAIMIYYAH sukai murnan samuwan cikin,Iya ta dage da yiwa TAIMIYYAH addu'an itama Allah ya kawo mata nata rabon,amma shiru kake ji har zuwa lokacin da cikin Zuwaira ya isa haihuwa,ta haifo ɗanta Namiji ƙato wanda bai baro komi ba a kamannin ubansa,Kyakykyawan gaske duk wanda ya zo barka sai yayi santin yaron kaman a ɗauke a gudu,tunda Zainab TAIMIYYAH ta ɗaura ido akan yaron taji duk wani soyayyanta akan yara da take dannewa don kada a fahimci rashin samun haihuwan su na damunta,sai ya taso gaba ɗaya ta ji wani irin son yaron ya dira a zuciyanta,duk wani motsin Zainab TAIMIYYAH akan yaron ashe Zuwaira na ankare da ita,aiko ana gama shan shagalin suna aka watse aka bar Zuwairan da wata Innar ta da zatai mata zaman Jego,sai ya zama duk lokacin da Zainab zata shiga don duba jaririn da yaci suna Abubakar Sadeeq sai Zuwaira ta tsiri ɗaukansa ta riƙe,ko ta ƙirƙiri ba shi Nono sam bata bari yaje hannun TAIMIYYAH sai idan ta shigo yana hannun Inna shine Innan zata bata ta ɗauka,tun TAIMIYYAH bata fahimci Zuwaira ba ta son ta da ɗanta ba har ta gane,hakan kuma ya taɓa zuciyanta matuƙa,har da ta koma sashinta sai da ta zubda hawaye,karon farko da taji tana tsananin son haihuwa,Iya ma ta daɗe da gane cewa Zainab ɗin tunda Zuwaira ta haihu ta fito da son haihuwanta a fili,hakan yasa watarana ta zaunar da ita tana mata nasiha da kwantar mata da hankali akan cewa komi na Duniya rabo ne kuma yana da lokaci,kada ta saka damuwa a ranta suma nasu rabon nanan zuwa,TAIMIYYAH taji kunya sosai a lokacin amma daga baya kaman yadda Iyan tace ta dagene da addu'a hakan ya kasance,duk idan tasa goshinta a ƙasa sai ta roƙi Ubangiji ya basu rabo me anfani,amma fa soyayyan da takewa Sadeeq yaƙi barin zuciyanta sai dai taja baya sosai da kai kanta Sasan Zuwairan da sunan taje ɗaukan mata yaro tunda ta nuna bata so,don tana da matuƙar gudun zuciya,takan gansa ta ɗauke shi idan Inna takaiwa Iya shi,a haka rayuwa ta cigaba da gangara musu sam Sameer bai taɓa nuna damuwansa akan rashin haihuwan su ba,kuma sosai Allah ke ƙara masa buɗi yana matuƙar samu da kasuwancinsa da yake,ga kuma ƙarin promotion da yake samu a wajen aiki,lokacin da Sadeeq ya samu shekaru biyu da watanni a lokacin Zuwaira ta sake samun ciki,a kuma lokacin ne Allah yai ikonsa akan su Zainab itama ya bata rabo,murna a wajen Iya da ita kanta Zainab ɗin ba'a magana,hatta da uban gayyan Alhaji Sameer wanda zuwa lokacin yaje Hajji,murnan ba'a magana,sai dai murnan nasu ya katsene a wani dare da Allah ya ɗauki rayuwan Alhaji Amadu mahaifin su Sameer ɗin,wanda yai mutuwan farat ɗaya domin sun kwanta da Iya lafiya-lafiya,cikin dare ciwan kai na ajali ya samesa kafin gari ya waye yace ga garinku nan,mutuwa ne da ya jijjiga duka Familyn sa,tare da gigita iyalansa domin Iya sai da akai uku ta fara gane kanta,hatta da TAIMIYYAH mutuwan surukin nasu ya taɓa ta matuƙa,haka aka share zaman makoki har kowa ya watse,aka bar Iya da takaba wacce cikin ƙanƙanin lokaci duk ta fita hayyacinta,amma cikin hukuncin Allah tana addu'a kuma ana bata rubutun dangana tana sha,har ta kwantar da hankalinta zuwa lokacin fitanta takaba,ta gama sarewa da kuma sadaukar da cewa Amadun ya tafi inda babu dawowa kuma dole rayuwa tacigaba,don haka sai ta sake miƙa wuya ta cigaba da yi masa addu'a,Alhaji Amadun na da watanni shida da rasuwa,Zuwaira ta haifo ƴar ta Zuhrah yayinda Zainab ita a lokacin cikinta ya shiga watanni shida,amma girmansa kai kace yakai watanni takwas,Zuhrah na da watanni huɗu har ta fara koyan zama,wata ranan Juma'a Allah ya sauki Zainab ta haifo ƴar ta mace ƙatuwan gaske,kyakykywan jinjiran da ta tafi da zuciyoyin mutane da yawa,ciki har da Iya wacce tunda ta ɗauki yarinyan taji wani irin ƙaunarta me zafi yana bin jininta,a ranan ne kuma Alahji Sameer ya dawo Weekend ya riski wannan farin cikin na samun ƙaruwa,lokacin da ya ɗaura ido akan yarinyan sai yaji wani irin soyayyanta na ratsa ilahirin jinin jikinsa,babu inda ta baro kamannin uwar ta sai manyan idanun ne kawai irin na Sameer ɗin,wanda suma suka gado wajen Iya,sai dai abin tausayi tunda Zainab ta haihu sai kuma ciwo sam babu lafiya,aka kwasa aka nufi asibiti da ita nan take aka basu gado,domin tana kuka da ciwan kai me tsananin gaske,wanda ake tunanin ko hawan jini ne ya sameta,amma bayan gwaje-gwaje aka gano babu wani hawan jini a tare da ita,kwananta biyar a asibitin Allah ya ɗauki a barsa,wani irin mutuwa da ya gigita ahalin Alhaji Amadu baki ɗaya,har fiye da yadda suka ji mutuwansa,Iya tayi wani irin gigicewa da wannan mutuwa da yazo musu a bazata,cikin kuma lokacin da suke tsananin buƙata da fatan Zainab ta rayu ta raini Kyakykyawan ɗiyar ta,sai dai shi Allah baya barin wani don wani,da zaran yayi kira dole a amsa kiransa,to hakan ne ta kasance aka ɗauke Zainab aka bar jinjiran ta,Alhaji Sameer wanwar aka kai shi asibiti baisan wanda ke kansa ba sabida tsaban gigita da fita hayyaci,jininsa yai wani irin hawa cikin ƙanƙani lokaci,don ko sallan janazanta bai samu ba yana asibiti aka kaita gidanta na gaskiya,duk wanda ya shiga gidan ta'aziyan Zainab dole ya fito da kuka sabida tausayin Iyayenta da danginta,da kuma baiwar Allah jaririyan da ta bari,wacce Iya ta ke riƙe da ita gam ta kankane ta hana kowa,ita ke bata madara idan tai kuka tai mata komi,Yayar Zainab ɗin ko Anty Mardiyyah ko magana bata iyawa sai kuka,har akai bakwai suna cikin wani irin yanayi na alhini me taɓa zukatan masu tsoran Allah,a kuma ranan bakwai ɗinne akai zama da ƴan uwan Zainab ɗin akan son abasu jinjiran su riƙe,amma Iya ta daka tsalle tace bata san wannan zancen ba,babu me raba ta da jikanta indai tana raye wacce tunda tai kwanaki bakwai aka sanya mata sunan Mahaifiyanta wato Zainab,kuma nan take aka cigaba da kiranta da TAIMIYYAH kaman yadda ake kiran Marigayiyan,duk yadda Anty Mardiyyah ta so abata riƙon Little TAIMIYYAH amma Iya ta ƙeƙashe ƙasa tace bata san zancen ba,shi ma kuma uban yarinya Alhaji Sameer ya nuna yafi son ƴarsa a wajen Mahaifiyansa,haka suka haƙura aka bar yarinya a wajen Iya,wanda ya zama sila da kuma tushen tasowan TAIMIYYAH a wajen kakarta Iya,wacce ta maye mata gurbin uwa ta kuma bata nagartacciyar tarbiyan da uwa tagari zata baiwa ƴar ta,Zuwaira tun TAIMIYYAH tana ƙarama ta tsane ta sabida irin yadda Iya ta ɗauki son Duniya ta ɗaura akan TAIMIYYAN,sam bata bi takan Zuhrah da suka taso kusan kai ɗaya da TAIMIYYAN,sai dai shi ma Sadeeq da zuwa lokacin ya daɗe da shiga makaranta yayi wayo yana da shekaru huɗu,duk inda yaje ya dawo zaka same sa a Sashin Iya yana nane da ita yana shafa kan TAIMIYYAH,a hankali rayuwa ya cigaba da garawa yaran suna wayo,soyayyan da Iya ke wa TAIMIYYAH na sake fitowa fili,lokacin da su TAIMIYYAH ke da shekaru biyu suna gudunsu ko'ina ita da Zuhurah wacce ta bata watanni huɗu,tare suke wasa da Zuhurah da Sadeeq ma baki ɗaya,tun Iya bata barin TAIMIYYAH zuwa Sasan Zuwairah don kada ta cutar da ita,har ta haƙura sabida yadda TAIMIYYAN kullum ke nane da su Sadeeq da Zuhurah,Alhaji Sameer da tun mutuwan matarsa yaji gaba ɗaya Zaria tai masa zafi,sai ya zamana ya ɗauke ƙafansa daga zuwa sosai,sai a haɗa sati biyu bai shigo garin ba,duk da cewa soyayyan ƴar sa nanan danƙare a zuciyansa irin soyayyan da baki bazai iya misaltawa ba,amma zuwan shi Zarian na masa wani irin fami ne idan har yazo ya buɗe Part ɗinsu ya ga babu Zainab,shi yasa duk son sa da zuwa ya ga ƴar sa da ayanzu soyayyan da yake wa uwarta ya gama komawa kanta yake dannewa,sai dai duk wani siyayya na abin buƙata ana jibgewa Iya su,har abin na zarta ƙa'ida sai dai Iya tai ta kwasan rabi tana turawa Zuwairah taiwa Zuhrah anfani dashi,hakan ya sake janyo wani irin kishi da tsanan TAIMIYYAH a zuciyan Zuwairan,tana tsananin adawa da yadda yarinyan ta taso da wani irin kyawu me fisgan hankali,da tarin farin jini, Sadeeq shi ya raɗawa Zuwairan Umma tunda ya buɗi baki,suma su TAIMIYYAH da bakinsu ya fara buɗuwa sai suka bi bakinsa suna kiranta da Umman,a wani dare lokacin su TAIMIYYAH na da shekaru uku ta farka da wani zazzafan Zazzaɓi,gari na wayewa Iya ta kira Alhaji Sameer ta sanar masa,shi kuma ya turo Sani wani yaronsa da ya barwa mota yana kai Iya anguwa da uzurorin kai TAIMIYYAH asibiti idan buƙatan hakan ya taso,cikin ƙanƙanin lokaci sai ga Sani ya iso suka wuce asibiti da TAIMIYYAH,tsananin zafin zazzaɓin yasa aka rubuta allurai biyu da xa'aiwa TAIMIYYAN,anyi na farko ranan lafiya lau Iya ta dawo da ita,a washegari aka koma akai na biyun,aiko washegari ƙafan yarinya yai lakaf sam bata iya motsa shi bare aje ga zancen takawanta,babu shiri Iya suka maida TAIMIYYAH asibiti da gaggawa,amma duk iyakan binciken likitoci an rasa gane daga ina matsalar take,domin likitan da yai alluran kowa ya shaida ƙwararrene,daga ƙarshe aka bar abin akan cewa anyi rashin sa'a ne alluran ya taɓa jijiya,duk inda tashin hankali ya kai tuh Iya ta shige shi,a washegari Alhaji Sameer ya diro Zaria hankali tashe don ganin lafiyan ƴar sa,wasa-wasa sai ƙaramar magana ya fara zama babba,TAIMIYYAH ƙafanta da akaiwa allura ya fara shanyewa,ta koma sam bata iya tafiya bare motsa ƙafan,wani likita ya bada shawaran afara mata gashin ƙashi a asibitin ABU da ke Tudun wada Zaria,cikin ikon Allah ana fara gashin ƙashin ta fara iya motsa ƙafafun,amma fa har lokacin bata iya tafiya,hankalin kowa a tashe yake da wannan tsautsayi daya gitta a rayuwan kyakykywan ɗiya irin TAIMIYYAH wacce a duk kwanan duniya kammaninta da mahaifiyanta ke sake fitowa ƙarara,Zuwaira ita ce kaɗai bata taɓa nuna damuwanta akan wannan lalura ba,wanda hakan yasa Iya sake ƙullatanta a zuciyanta da ƙinta a ranta,faɗin irin wahala da faɗi tashin da Iya da Alhaji Sameer suka sha akan TAIMIYYAH bazai misaltu ba,kafin Allah yai ikonsa a samu TAIMIYYAN ta fara taka ƙafan da taimakon dafa ƙafan da ya shanye,tun ana ganin kaman idan ancigaba da gashin da yawon asibitocin xata koma da tafiya ba tare da sai ta dafa ƙafanta me laluran ba,har Iya ta fara sarewa ta cire rai tunda ta ga irin shanyewan da ƙafan daya samu laluran yayi,tuni Zuhrah har an saka ta makaranta lokacin,ita kuma Zuwaira tana fama da laulayin ciki na uku,Alhaji Sameer a lokacin da ya sadaƙar ƙafan ƴar sa tabbas ya nakasa sai wani irin ƙaunarta da tausayinsa suka sake kama ruhinsa,kaman yadda ya kasance ga Iya wacce laluran nakasan ƙafan TAIMIYYAH,ya sake janyowa TAIMIYYAN wani irin soyayya da tausayi a zuciyan Iya,hatta da Baba Sani wanda a lokacin ya samu aiki da bankin CBN aka ajesa reshan jihar Kano,ba ƙaramin tausayin TAIMIYYAH yake ji ba idan ya dawo weekend ya ganta,rayuwa ya cigaba da garawa TAIMIYYAH na cigaba da taka ƙafanta bisa tsarin halittan da Allah ya nufa,kullum kuma tana Sasan Baba Sani wajen su Zuhrah,inda abu kaɗan zatayi Umma zata hauta da faɗa tana faɗin "Tafi can shegiya gurguwa." Tun Zuhurah bata ɗaukan abinda Umma ke faɗi har itama ta fara kiran TAIMIYYAH da suna gurguwa,Sadeeq ne kawai bai taɓa bin bakinsu ba ko da wasa,saima wani shaƙuwa da ke sake shiga tsakaninsa da qanwar tasa,don wani lokacin idan TAIMIYYAH sun haɗu da Zuhurah sun ma Umman ɓanna ta bige su,shi za ka ga ya ja TAIMIYYAH gefe yana lallashinta,shi yasa Iya tafi ji da shi a yaran Zuwairan ,lokacin da Zuwairah ta haifo Basmah lokacin Alhaji Sameer ya saka TAIMIYYAH a makarantar boko wani skull da ke tashe a Zaria me suna JETHRO ACADEMY,Sani shi ya zama Drivern TAIMIYYAH yana kaita ya ɗakko ta,su Zuhurah su THERBOW Skull Baba Sani ya sanya su,da ƙyar da faɗa da Nasiha Iya ta shawo kan Alhaji Sameer akan maganan aure,har Allah ya haɗa shi da Samha ƴar nan Kaduna Anguwan Rimi,ba'a ɗauki lokaci ba akai bikinsu ya kama mata gida anan Kadunan,don a cewansa bazai kuma sake zaman Zaria ba,sai dai su shigo Weekend ko idan wani abu ya faru su zo su koma,yaso Iya ta amince masa ya ɗauke TAIMIYYAH ya mayar gabansa,amma sai Samha ta nuna sam bazata iya riƙe yarinya alhali,ta aure shi a budurwa ɗanya sharaff basu fara moran rayuwansu ba,itama Iya ta nuna sam bata aminta ba hakan yasa Alhaji Sameer da TAIMIYYAH ke cewa Abie haƙura,ko kaɗan babu irin shaƙuwa me tsanani tsakaninsa da TAIMIYYAH sabida sunyi nesa da juna,sai dai kawai idan yazo zai ɗauke ta su je can su je nan yai mata siyayya ya zo ya aje,to haka rayuwan TAIMIYYAH ya taso Iya kawai tafi sabawa da ita suka shaƙu,sai su Zuhrah da Sadeeq wanda yake jida TAIMIYYAH sosai,ita kuma Umma ta ɗauki karan tsana ta ɗaura mata,tare da hantaranta tana sanya su Zuhurah cin xalin TAIMIYYAN wanda hakan ya fara jefa tsoransu a zuciyan TAIMIYYAH,tun tana ƙawazucin nacewa zuwa Sasan har ta haƙura,daga makarantan Boko sai zuwa islamiya ke fitar da ita daga Sasan Iya,gashi TAIMIYYAH ta taso da ƙoƙari da son karatu hakan yasa Abie ɗinta baya jin ciwon kashe kuɗi akan karatunta,tana sake girma da wayo ne Iya na sake laƙantan hankali da nutsuwan da TAIMIYYAH ta gado wajen uwar ta,gami da tsan-tsan kyawun halitta,ta taso shiru-shiru mara son haniya da miskilanci,sam in ba ta saba da mutum ba bazai fahimci halinta na son mutane