Showing 63001 words to 66000 words out of 186776 words

Chapter 22 - TAIMIYAH Book Complete Document by Ayshat Dansabo Lemu .txt

15 Dec 2024

6585

mata na ƙona zuciyanta.Tana jin Yasmeen data biyo bayanta na kiran sunanta,amma ko waiwaye bata yi ba, don burinta kawai ta isa ɗaki,ko zata kwanta tayi kukan dake neman kwace mata.Cikin Sa'a babu kowa a falon Iyah hakan yasa ta nufi ɗaki,tana faɗawa kan gado ta saki kuka me ƙarfin gaske.Dukkanin jikinta rawa yake na tsananin shiga ɓacin rai,domin ba'a taɓa jifanta da munanan kalamai irin wanda Zuhurah ta jefeta da su a yau ba.
Kalamai ne mafiya munin saurare musamman daga bakin ɗan uwanka na jini.
Har Yasmeen ta ƙariso bakin gadon TAIMIYYAH kuka take yi me asalin motsa zuciya.Daƙyar Yasmeen ɗin ta ciyo kan TAIMIYYAH ta sanar da ita yadda su ka yi da Zuhurah,ta ƙare maganan cikin muryan kuka tana faɗin "Yasmeen shikenan na shiga uku idan har Zuhurah wannan sharrin zata ƙulla min a wajen Umma.Wallahi hannuna kawai ta ga ya riƙe,baya ga haka bata ganmu muna komi ba."


TAIMIYYAH takai ƙarshen maganan tana sake rushewa da kuka.........✍🏻








Littafin TAIMIYYAH paid book ne da zai zo akan 500 naira only,ga masu buƙatan yin payment zakui min magana ta wannan number ɗin 08167768704, ko kuma ku turo kuɗin ku kai tsaye ta wannan account ɗin 0504192664 aisha ibrahim dansabo GTbank.*


*Sai ku tura shaidan biyanku ta wannan line ɗin 08167768704.*






#Ɗansabo ce#
[12/14, 10:05 PM] +234 703 769 7050: *TAIMIYYAH*❤️


©️Ayshat Ɗansabo Lemu ✍🏻


*Page 31*


___________


Umma ce zaune a cikin Bedroom ɗinta,ta tasa Sadeeq a gaba tana zazzaga masa ruwan masifa,akan cewa lallai ya fita a harkan Gurguwan yarinyar nan TAIMIYYAH.


Ta inda take shiga bata nan take fita ba,shi dai Yah Sadeeq yai ƙasa da kansa yana sauraranta,ba tare da ya tari nunfashinta ko sau ɗaya ba.Umman ta ƙare maganan da cewa "Aure zan maka tunda abin naka ya fara zama iskanci,ka fara saka Gurguwa a ɗaki kana kwanciya da ita sabida asara,in banda abinka in ma iskancin zaka yi ka rasa wanda zaka kula sai Gurguwa,Musaka! To tunda ka kasa fito da zaɓinka ni zan zaɓo maka yarinya dai-dai da ajinka,ƴar gidan qawata Hajiya Hadeeza za ka je ka nema.Tana nan da budurwar ƴa kyakykyawa me dirin jiki,ita ma fara ce ƙar kaman waccar Musakar,don haka sai ka shirya wata satin idan ka dawo Weekend za ka ku ga juna,sunan yariyar Nadeeya."


Umma ta kai ƙarshen maganan tana ɗaura idanunta akan fuskan Sadeeq ɗin,wanda ya haɗe fuska babu annuri ko kaɗan.Zuciyansa tafasa kawai yake yi yana ji da ba Umma bace ke masa wannan maganan,tana aibanta TAIMIYYAH a gaban idanunsa,tabbas da wata can dabam ne ba abinda zai hana shi nuna mata fushinsa.


Amma da yake Uwa ce hakanan ya danne ɓacin ransa,yana faɗin "Umma ni bana son wani haɗe-haɗe zan zaɓo matar aure da kaina,don Allah kada ma ki yi wa Anty Dijen maganan." Ya kai ƙarshen maganan cike da roƙo,Umma da ke kallonsa baki buɗe ta dalla masa harara tana faɗin "Ai ko baka isa ba Sadeeq,wannan umurni ne nake baka ba wai shawaran ka nake nema ba,don haka na gama magana,kana dawowa wata satin za ka ku ga juna final!"


Daga haka Umma ta miƙe ta bashi waje tana jan tsaki tsuuuw....! Hakan yasa Sadeeq bin bayanta da kallo,zuciyarsa na matuƙar sake ɗaukan zafi.Tuni idanunsa sun yi mugun kaɗawa ya miƙe yana ji tamkar ƙafafunsa ba zasu iya ɗaukansa ba,ya rasa da wani ɓacin ran zai ji,na Iyah da itama tai masa tatas a daren jiya akan lallai ya fita daga harkan TAIMIYYAH,ko kuwa da rigiman da Umma ta ɗauko yanzu na cewa zata haɗa shi da ƴar aminiyanta Anty Dije? Har ya fito falo bai san taƙamaimai inda yake jefa ƙafafunsa ba.


Lokacin da ya iso tsakiyan falon ne idanunsa ya sauka akan su Zuhurah.Take Brain ɗinsa ya tuno masa cewa Zuhuran ita ce silan duk wannan masifan da ake son jefa Zuciyarsa a ciki,sai ya nufi inda take yana damƙota tare da kifa mata lafiyayyen marin da ya ɗauke jin ta da ganin ta na wasu ƴan daƙiƙu.


Zuhurah da komi yazo mata a bazata ta ƙwallah wani uban ihu,wanda ya janyo hankalin su Umma da Anty Laurat da ke ɗaki,suka fito a guje don ganin meke faruwa.


Umma sai tai turus a tsaye tana kallon yadda Sadeeq ya dage yana jibgan Zuhurah,yana zuba mata masifa akan duk munafunci da cin mutuncin da tai wa TAIMIYYAH a jiya.Umma ganin zai raunata mata ƴa yasa ta isa wajen da sauri.Ta ɗaga hannu zata ɗauke shi da mari Anty Laurat da ta ƙariso wajen, tayi saurin shiga tsakiyansu tana faɗin, "Umma kiyi haƙury,Yah Sadeeq oya bar nan wajen please!"


Babu musu Sadeeq ya juya ya bar Sasan a fusace tamkar zai tashi sama.Zuhurah da Umma take riƙe da ita sai ta sake sakin wani uban ihu tana faɗin "Wayyo kafaɗata Umma ya karya ni!"


A rikice Umma ta zaunar da ita tana faɗin "Ke don ubanki bansan jafa'i,kar ki tara min mutane cikin Sasa,ya karya miki kafaɗa ne zaki xauna a haka? Ki yi shiru ki bar ni da shi saina saɓa masa,ba dai duk akan waccar Gurguwan yake yi ba,to zanci ubansa very soon!"


Umma ta ƙare maganan a fusace,tana juyawa ta bar Zuhurah da su Anty Laurat,wacce ita abinda Yah Sadeeq ɗin yaiwa Zuhurah ba ƙaramin birgeta ya yi ba.


A can ɓangaran Sasan Iyah kuwa,TAIMIYYAH ce zaune ita da Zee wacce ta kawo mata ziyara a yau.An cika gaban Zee ɗin da kayan motsa baki,sai hira suke yi har da Yasmeen da ke zaune daga gefe tana sanya baki cikin hiran.


Wayan TAIMIYYAH ne ya shiga ringing,ta ɗaga wayan tana miƙewa don barin wajen.Ganin Nass ne me kiran sabida kunyan amsa wayansa ta ke ji a gaban mutane,daga Yasmeen har Zee suka bi bayanta da kallo suna sakin murmushi.


Ta ɗauki tsayin 15 minutes sannan ta fito ,Zee ta dube ta cike da tsokana ta ke faɗin, "Qawata da alamu dai wannan Nass ɗin ya ci mu da yaƙi, ya yi nasaran sace zuciyar ki, dama ni na san da ƙyar zaki iya tsallake tarkon sa,don Guy ɗin ya haɗu kun kuma dace da juna,Allah dai ya tabbatar da alkhairy a tsakaninku."


Yasmeen ce ta amsa da "Ameen." Su na cigaba da tsokanan TAIMIYYAH wacce ta narke musu da shagwaɓa akan su daina tsokananta ita ba wani Soyayyan da take wa Nass ɗin.


Yasmeen ta danna mata harara tana faɗin, "To ai dukkanin reaction ɗinki akansa ya gama fallasaki yarinya,kowa ya ji yadda kike narke masa ya san kin kamu wallahi,don haka mu bawani gulman da za a mana a tuh!"


Zee ta saki dariya sosai bayan Yasmeen ta dire magananta,idanun Zee ɗin cikin na TAIMIYYAH take faɗin "Qawata kawai ki saki an riga an ci ki da yaƙi." TAIMIYYAH ta aikawa Zee ɗin harara tana faɗin,


"To na ji ƴan saka idanu a ɗakko wani topic ɗin a aje wannan." Daga haka suka shiga wata hiran har Iyah ta dawo daga anguwan da ta fita,ta tadda Zee ɗin da take jin labarinta a bakin TAIMIYYAH.Zee ta gaida Iyah cike da ladabi tana faman yi mata sannu da zuwa,Iyah ta amsa da fara'a sosai cikin Zuciyanta tana yaba nutsuwan Zee ɗin.


Sai around 3pm Zee ta tashi tafiya,Iyah ta bada sinƙin Sabulu me tsada na wanka da turare aba Zee ɗin.Ita kuma TAIMIYYAH wani Ɗan-kunni da sarƙa me kyau,da take aje da shi bata taɓa amfani da shi ba,shi ta ɗauka ta haɗa Body Mist me Qamshi,cikin turarukan da Abie ke aiko mata za ta baiwa Zee ɗin.Har bakin gate ita da Yasmeen su kaiwa Zee rakiya,sai faman godia Zee ɗin take yi lokacin da TAIMIYYAH ta bata ledan da suka zuba mata sha tara ta arziƙin.


Sai da suka ga Zee ɗin tayi nisa da tafiya,sannan suka juyo zuwa cikin gida.Yasmeen nata yaba kirkin Zee ɗin da hankalinta,hakan kuma yai wa TAIMIYYAH daɗi a rai,ta ji Zee ɗin ta sake shiga Zuciyanta musamman da Iyah itama take ta yaba nutsuwan Zee ɗin.


__________
*After One Week*


A cikin sati ɗayannan da ya biyo baya,abubuwa da yawa sun faru.Ciki har da yadda Soyayya me ƙarfi ya ƙullu tsakanin TAIMIYYAH da Naseer,wanda ke can garin Abuja wajen aiki amma kullum suna maƙale da juna a waya.


Sunyi wani irin shaƙuwa ta ban mamaki,ta yadda ɗaya baya iya yini guda sur! Bai ji muryan ɗan uwansa ba.Hatta da yin vid call da TAIMIYYAH ke ƙorafin bata so,yanzu ya fara zame mata jiki don duk dare kafin su kwanta sai sunyi vedio call da Nass ɗin.


Ita dai Yasmeen na ganin ikon Allah,tare da tasa TAIMIYYAH da tsiya kala kala.Gefe ɗaya kuma tana jin daɗin yadda TAIMIYYAH ta saki jikinta da Nass ɗin suna kwasan Soyayyah.Zuhurah da mutuminta Ameeru ɗan mutanen Bauchi itama luv suke bugawa ba kaɗan ba,don da gaske son shi take yi da dukkanin Zuciyanta.Tuni har maganan ya je kunnin Baba Sani,ya kuma ce a gayawa Ameerun ya turo manyansa su nema masa izinin fara zuwa zance,duk a bakin Anty Laurat su TAIMIYYAH ke jin hakan.


Yau ya kama Saturday tun safe su TAIMIYYAH ke shirin tarban zuwan Abie,wanda ya kira wayan Iyah tun daren jiya ya sanar da ita zai ƙariso Zarian bayan ya tsaya a Kaduna an ɗaura auren da zai kawo sa garin.


Qanwar Ummie da suke Cousine ne za'ai wa aure shine Abie ɗin zai zo ɗaura aure,ita Ummie da su Nahar tun Thursday ma suka biyo jirgi zuwa Kaduna.TAIMIYYAH haka kawai take jin duk ta ƙosa tayi ido biyu da Abie,sabida ya kwana biyu bai shigo garin ba,sai dai su gaisa ta waya wani zubin su yi vid call.Shiyasa yau ɗin daya sanar zai zo gaba ɗaya farin cikinta ya kasa ɓoyuwa,gefe guda kuma tun tashinta da safe take fama da faɗuwan gaba,sai ta dinga nanata kalmar Hasbunallahu wani'imalwakil! Shine ta ɗan samu sauƙi.


Ƙarfe 1:10pm na rana suka kammala shirya abincin da suka yi,a ɓangaren cin abincin da ke falon Iyah.TAIMIYYAH ɗaki ta nufa ta sake yin wanka,ta fito ɗaure da alwala ta nufi Pray Mat don tada Sallan Azuhur.Yasmeen ma wankan tayo ta fito ta shirya cikin doguwar rigan Material,ita ma TAIMIYYAH bayan ta idar mai ta shafawa fatarta,ta nufi wajen kayanta ta ciro wata doguwar riga na wani Swiss Voile mara nauyi ta saka.Ɗinkin ya yi mata kyau wanda akaiwa A shape,ta ɗaura ɗankwalin kayan,tana ɗaukan turarenta na GIORGIOS PINK ta fesa kaɗan,ta maida kwalban ta aje.Idanunta akan Yasmeen take faɗin "Yasmeen zo ki taɓi ƙirjina kiji yadda yake faman dokawa,na rasa dalilin wannan faɗuwar gaban da nake ji."


Yasmeen ta dubi TAIMIYYAH tana me matsowa gaban ta,ta kai hannu da dafa tsakiyan ƙirjin TAIMIYYAN, tana jin yadda ƙirjin ke bugawa fat! fat! Ta cire hannunta daga wajen tana faɗin "Sorry kiyi ta addu'a ne wani lokacin haka ne,sai kai ta jin faɗuwan gaba." TAIMIYYAH ta jinjina kai tana faɗin "Wallahi tunda safe nake jin hakan,da nayi addu'a sai inji yayi sauƙi amma yanzu kinji kuma ya dawo."


TAIMIYYAH ta kai ƙarshen maganan tana ɗaukan wayanta, da ke saman madubi dai-dai lokacin da kiran Nass ke shigowa.Sai ta koma bakin gado ta zauna tana ansa call ɗin,cikin shagwaɓe murya take masa magana,sun ɗauki wajen 20 minutes suna waya, don har Yasmeen dake jiranta su ci abinci ta gaji tai ficewanta zuwa falo.


TAIMIYYAH ta sauke wayan daga kunni lokacin da Nass ɗin yai hanging up! Ta saki murmushi kalaman daya gaya mata na luv na sake narkar da Zuciyarta.


Lokacin da TAIMIYYAH ta isa wajen cin abincin,tuni har Yasmeen ta fara cin abincinta ba tare da ta jira fitowan TAIMIYYAN ba.Suna cikin cin abincin Iyah ta fito tana amsa waya,da alamu da aminiyanta Hajiya Rabi take wayan,sabida yadda take ta faman ɗaga murya.Wajen cin abincin ta iso itama ta zauna kusa da TAIMIYYAH ,tana mata alama da hannu akan ta zuba mata abincin itama.


TAIMIYYAH ta ɗauki plate tai sarving Iyah Rice and Stew ɗin da yaji zallan tsokar naman kaza.Ta zuba mata haɗin Salad wanda ba'a riga an sanya masa Salad Cream ba,ta tura gaban Iyah da har lokacin waya take yi cike da ɗaga murya.Yasmeen tai ƙasa da murya tana cewa TAIMIYYAH, "Wai wannan tsohuwar tamu bata iya amsa waya a hankali bane halan?" TAIMIYYAH ta saki dariya tana faɗin "Gashi kuma kin gani,haka take yi indai Babah Rabi ne ta kirata,kinsan tana cewa Babah Rabin na da matsalan ji,shiyasa take wannan hayagagan."


Iyah data sauke wayan daga kunni,sai ta watsawa su Yasmeen harara don sarai ta san gulmanta suke yi.Yasmeen ta saki dariya tana faɗin, "Iyah wannan amsa waya kaman kina magana da kurma." Iyah ta ballawa Yasmeen harara tana faɗin,


"Eh! to ai kusan hakan tunda matsalan kunni gare ta ba ta ji sai anyi magana da ƙarfi."


Yadda Iyah ta kai ƙarshen maganan har lokacin tana hararan Yasmeen,yasa TAIMIYYAH sakin dariya,suka maida hankali akan cin abincin su har su ka kammala.Yasmeen da TAIMIYYAH sai suka koma ɗakinsu don TAIMIYYAH cewa tayi bacci za ta yi kafin La'asar tayi.
Suna shiga ɗaki kuwa kwanciya TAIMIYYAH tayi bada jimawa kuwa baccin ya sace ta,ita Yasmeen sai ta kwanta tana chart don bata cika yin baccin rana ba.




Ƙarfe huɗu dai-dai TAIMIYYAH ta farka daga baccin,kai tsaye toilet ta nufa don yin tsarki da alwala.Ta fito ta gabatar da Sallan La'asar ɗin,tana idarwa ta fito zuwa falo dai-dai lokacin da kira ya shigo wayan Iyah dake zaune,tana lazumi ita kuma Yasmeen hankalinta na kan kallon tashar Bollywood,da ake haska wani Film da take mutuwan so.


Iyah ta ɗaga wayan da sallama a bakinta,tana sauraren maganan da ake sanar mata daga ɓangaren me kiran.Su dai su TAIMIYYAH kawai gani suka yi Iyah ta saki wayan da ke hannunta,tana faman jero Salati da Sallallami,jikinta na wani irin rawa kafin jiri ya ɗebeta ya watsar bisa kan Carfet.TAIMIYYAH tai wani irin tsalle da ƙafa ɗaya sai gata a gaban Iyah,ta shiga girgizata da dukkanin ƙarfin da take da shi,ƙirjinta na cigaba da bugawa kaman zai fashe.Yasmeen kuma wayan da Iyah ta jefar ta ɗauka tana bin bayan kiran,TAIMIYYAH kuka take yi tana girgiza Iyah da tuni ta suma.
Dai-dai lokacin Babah Ladi ta shigo cikin falon,da hanzari ta nufo wajen Iyah dake yashe a ƙasa babu alamun numfashi,sai kuka TAIMIYYAH take tana faman kiran sunan Iyan.


Yasmeen data bi bayan kiran da aka yowa Iyah,bugu biyu muryan wani namiji ya ɗauki wayan yana sanar da ita cewa,Abie ne suka samu Accident a dai-dai kwanan Jaji,kuma nan take rai yayi halinsa sai yara biyu mata da yake tare da su,da suke cikin wani hali mummun......


Ai Yasmeen bata bari ta gama jin ƙarshen maganan ba,ta ƙwallah wani uban ihu tana xubewa ƙasa.Hakan ya sake tada hankalin TAIMIYYAH da ita ma ta fashe da kuka,Ladi dake faman shafama Iyah ruwa a fuska don a samu ta farfaɗo,ta dubi Yasmeen tana faɗin "Ƴar nan sanar damu abinda ke faruwa don Allah."


"A'.a'.a.Abie ne Babah Ladi...!" Yasmeen tayi maganan a rarrabe tana sake fashewa da kuka,TAIMIYYAH ta ƙariso wajen da Yasmeen take tana faɗin "Me ya samu su Abie Yasmeen,sanar dani me ke faruwa ne wai?" Tayi magana cikin muryan kuka cike da ƙaraji..! Sai dai kafin Yasmeen ta buɗe baki sallaman Baba Sani da shigowansa gaba ɗaya cikin falon Iyah,yasa dukansu suka maida dubansu gare sa.Kallo ɗaya xakai masa kasan cewa a kwai matsala,don idanunnan nasa sun kaɗa sunyi jajir,ya nufi wajen Iyah da yake hangowa a yashe ana faman shafa mata ruwan ƙanƙara a fuska.Amma har lokacin bata farfaɗon ba,ya tsuguna kusa da kan Iyah yana cewa Baba Ladi, "Ladi ai kwara mata ruwan za ki yi gaba ɗaya kawai,ina ga sanyin ruwan zaifi tasiri wajen sanya numfashin ya dawo cikin sauri."


Ladi nan take tayi yanda Baba Sanin yace,aiko nan da nan sai gashi Iyah ta kawo numfashi.Tana buɗe idanunta a hankali bakinta ɗauke da Salati,TAIMIYYAH ta iso wajen tana tambayan Baba Sani meya samu Abie ɗinta?Ganin Iyah ta farfaɗo sai ta nufeta tana sake rushewa da kuka.


Iyah ta rungume TAIMIYYAH tana nanata kalmar Allahummah ajjirni fih musibati wa'akliflikhairan minha! Idanunta babu alamun hawaye za su zuba,da alamu kukan na zuci take yi wanda yafi na fili illah.Baba Sani ya share hawaye yana duban Iyah yake faɗin "Iyah xamu tafi amso su,yanxu kafin in shigo aka sake kira su ma yaran lokaci yayi." Ya ƙarisa maganan yana fashewa da kuka kaman ƙaramin yaro,mutuwan ɗan uwan nasa da ƴaƴansa na dukan Zuciyarsa.
Iyah ta rintse idanunta da ƙarfi wani abu me tauri na danne Zuciyarta,bata iya cewa komi ba sai kai data gyaɗa masa kawai.Daga haka Baba Sani ya fice da sassarfa don kama hanyan Kaduna,zuwa amso gawarwakin su Abie da su Nahar da ajali ya sauka musu a rana guda.




Lokacin dasu Umma suka bazamo Sasan Iyah suna ihun kuka ne,TAIMIYYAH ta fahimci halin da ake ciki.Nan take ta faɗi ta sume gau! Bata sake sanin inda kanta yake ba sai farkawa tayi ta ganta akan gadon asibiti.........✍🏻




_Ina maraba da masu son a tallata musu hajarsu cikin wannan Littafin,sai ku tuntuɓeni ta lambar wayata kamar haka 08167768704._










Littafin TAIMIYYAH paid book ne,ga duk wanda ta tsincesa a kowani irin group ne,kiji tsoran Allah karki karanta sai kin biya 500 naira only.


Za ku iya min magana ta wannan number ɗin 08167768704, ko kuma ku turo kuɗin ku kai tsaye ta wannan account ɗin 0504192664 aisha ibrahim dansabo GTbank.*


*Sai ku tura shaidan biyanku ta wannan line ɗin 08167768704.*


Masu turo credit za ku turo katin MTN na 500 ta wannan line ɗin 08167768704.




"Ɗansabo ce#
[12/14, 10:05 PM] +234 703 769 7050: *TAIMIYYAH*❤️


©️Ayshat Ɗansabo Lemu ✍🏻


*Page 32*


__________ A hankali TAIMIYYAH take buɗe idanunta da su kai matuƙar nauyi,tana bin ɗakin Asibitin da kallo.Ta sauke ganinta akan Yasmeen da Anty Laurat,waɗanda su ma idanunsu yai luhu-luhu,ta ke kanta yai wani irin sarawa komi na dawowa Brain ɗinta.


Kukan data fashe da shi shine ya ankarar da su Yasmeen farkawanta.Yasmeen ta isa bakin gadon da sauri tana faɗin "Sannu TAIMIYYAH kin farko,sorry please! Kukan ya isa haka addu'a kawai su ke nema,don har an kaisu gidan su na gaskiya."


Yasmeen ta kai ƙarshen maganan cikin rawar murya,tana rungumo TAIMIYYAH zuwa jikinta.Wacce ta fasa wani sabon kukan,jin cewa da gaske dai ta rasa Abie ɗinta da Qanninta har biyu Raudha da Nahar,
cikin muryan kuka take faɗin,"Yanzu shikenan ba zan sake ganin Abie da su Nahar ba,don Allah ku ce min wasa ne ba su mutu ba,meyasa mutuwa za tai min haka Yasmeen? Allah nima

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login