Showing 156001 words to 159000 words out of 186776 words

Chapter 53 - TAIMIYAH Book Complete Document by Ayshat Dansabo Lemu .txt

15 Dec 2024

6601

akan kowace mace ba sai TAIMIYYAH.


Ya jima a haka idanunsa a lumshe, kafin ya buɗe baki ya ce, "Zaynabb idan na nemi a ɗaura mana aure, nan zuwa sati biyu masu zuwa ban yi gaggawa ba?"


Ya ƙare maganar yana buɗe idanunsa tare da ɗago jikinsa daga jinginan da ya yi, yana kafe TAIMIYYAH da manyan idanunsa masu shegen ƙwarjini.


TAIMIYYAH jin saukar furucinsa ta yi tamkar daga sama,cikin kaɗuwa ta yi saurin dubansa da idanunta da suka sake girma, sabida firgicin da kalamansa suka haifar a zuciyarta,muryarta har harɗewa ta ke lokacin da ta furta kalmar, "What....!?"


Maleek Ado ya jinjina kansa cike da tabbatar da kalamansa ya sake faɗin, "Zaynabb da gaske na ke yi idan za a bani ke nan da sati biyu zan so hakan, sabida abubuwan da nake ji akanki ni kaina tsoran kaina na ke yi Zaynabb,watakila shiyasa tun farko aka ɓoye min cikakkiyar siffarki,sai idanun kawai aka jarabe ni da su cikin mafarki,watakila da an nuna min ke sak ɗinki a wancan lokacin, da na jima da shiga mummunan yanayi, tare da haukacewa a nemanki a ko'ina ki ke a faɗin duniyar nan don na mallake ki. Please !Zaynab ki taimakeni in roƙi alfarma a ɗaura mana aure nan da sati biyu mas......"


Kukan da TAIMIYYAH ta sanya masa a bazata ne ya hana Maleek ƙarisa kalamansa, ya kafeta da ido yana jin zuciyarsa na sake dilmiya cikin ƙaunarta me zafi. A hankali ya kai hannu bisa lips ɗinsa ya furta, "Shishhhh...!!! Kar ki ƙarisa kunna ni da wannan sautin kukan na ki Zaynabb please!"


TAIMIYYAH ta yi saurin tsaida kukan nata, wanda dama har da taɓara a cikinsa,ta zuba masa ido cike da shagwaɓa ta ce, "Don Allah kar ka yi wa kowa wannan maganar,ni ban shirya ai min aure nan kusa ba na fi son in yi karatu."


Yadda ta yi maganar cike da zallar shagwaɓa with so much confidence, ya sanya Maleek kasa cewa komi, illa dafe goshinsa da yayi da hannu biyu, yana jinyar zazzafar gubar ƙaunarta da ta sake kwararawa a zuciyarsa.


TAIMIYYAH ko sam! Bata damu da yanayin da ya shiga ba, sai ma sake narke fuska da ta yi, tana jira ya sake mata zancen aure nan kusa ne, ta kuma sanya masa wani sabon kukan. Kamar ya san shirin ta kuwa sai bai sake maganar ba, sai ma duban side ɗin da aka jere kulolin abinci da su ruwa ya yi,ya ɗauke ido daga wajen yana mayarwa kan TAIMIYYAH ya furta, "Wife bani ruwa me sanyi please!"


TAIMIYYAH ta miƙe tare da dafa guiwar ƙafarta ta fara takawa don isa wajen table ɗin,in da aka jere komi a kai ta ɗakko goran table water da glass cup, ta juyo don kai wa Maleek Ado wanda idanunsa ke kanta, tunda ta tashi ya ke faman ƙarewa yanayin tafiyarta kallo,wani irin abu ya ke ji na danne zuciyarsa, yana sake haifar da zazzafar ƙaunarta a duk ilahirin jinin jikinsa.


TAIMIYYAH ta aje masa goran ruwan da cup ɗin,daga saman hannun kujeran da ya ke zaune,tana faman mita cikin zuciyarta na yadda ya ke bin ta da mayen kallo, kamar zai cinye ta. Ta zumɓure baki cike da shagwaɓa ta ce, "Ga ruwan ko na zuba maka ne?"


Ta ƙare maganar tana ɗaga manyan idanunta ta dubi fuskarsa,ganin ita ya ke kallo yasa ta ɗauke kai tana sake narke fuska, Maleek murya can ƙasa ya furta, "Da ni ki ke so na zuba da kaina wife?"


TAIMIYYAH ta kuma dubansa jin yadda ya yi maganar a dake,sai dai yadda fuskarsa ta ke a miskile, ba za ka taɓa cewa kaf maganganun da yayi daga bakinsa suka fito ba,ta ɗan taɓe baki kaɗan lokacin da ta ke kai kyakykyawar hunnunta, mai ɗauke da zara-zaran yatsu ta ɗauki goran ruwan ta buɗe, tare da zuba masa cikin cup ta miƙa masa. Maleek Ado ya zubawa kyawawan yatsunta ido, yana sake jin tsoran mafarkin da ya yi ta yi da irin waɗannan yatsun, a lokacin da takan miƙo masa su a cikin bacci tana neman ɗauki daga garesa,sai dai a wancan lokacin da ya miƙa hannunsa don kamata,ya ke farkawa daga baccinsa a firgice,yau ga hannun a gabansa tana miƙo masa cup ɗin ruwa a zahiri ba a cikin mafarki ba. Ya sauke zazzafar numfashi yana miƙa hannunsa, ya amshi cup ɗin ruwan ya kai bakinsa, ita kuma TAIMIYYAH ta yi saurin komawa mazauninta, tana sake yin ƙasa da kanta don haka kawai ƙamshinsa da ta sake shaƙowa da kyau, lokacin da suke daf da juna ya dinga kashe jikinta, yana haifar da wani yanayi a cikin zuciyarta.


Maleek ya shanye ruwan tas! Ya dire cup ɗin daga saman kujerar ya dubi TAIMIYYAH,ganin yadda ta sauke kanta ƙasa ya sa shi furta, "Zaynab yaushe za ku kammala Computer traning ɗin da kike zuwa?"


TAIMIYYAH ta dube sa ta ce, "Saura one week mu amsa certificate na kammalawa."


"Very good! Zan yi magana da Hajjah, bari na xo na wuce don idan ina cigaba da ganin waɗannan idanun,ina kuma jin wannan muryar a kusa da ni, to za ki cigaba da illata zuciyata ne kawai,da ƙaunarki da ke neman ƙure duk wata jarumtar Maleek."


Maleek ya yi maganar idanunsa akan TAIMIYYAH, wacce ta waro masa nata idanun cike da mamakin kalamansa,ganin sun haɗa ido yasa ta saurin maida kanta ƙasa kunya na lulluɓeta. Maleek ya saki murmushi kaɗan kafin ya ce , "Zaynabb kin cika kunya da yawa ,anya ko zan samu irin kulawar da nake buƙata daga mace a gunki?"


TAIMIYYAH ta yi saurin dubansa kamalaman da bata shirya furtasu ba,suka suɓuce akan harshenta suka yo waje inda ta ce, "Ai ita na san tana baka."


Maleek da idanunsa ke kan bakin TAIMIYYAH, bai san lokacin da murmushi ya haska a samar fuskarsa ba, yayi saurin cewa, "Ita wa ce Zaynabb?"


TAIMIYYAH da wani kishi da haushin kanta ya gama cika ta,sabida yadda tayi suɓul kalam ta furta kalaman a fili har ya ji,sai sake narke face ta ce, "Ita matarka mana."


Maleek sai ya miskile face cike da don tsokanarta ya furta, "Oh! Tana bani mana sosai ma,kin san ta iya luv shiyasa na ke so ke ma ki rage wannan kunyar,sabida ku dinga gasa da juna wajen nuna min luv ɗin, ko ba haka ba wife?"


TAIMIYYAH tayi kicin-kicin da face tare zumɓuro ɗan ƙaramin bakinta,cike da shagwaɓa ta ke duban Maleek ta ce, "Ni ban iya ba tunda ita ta iya shikenan sai ta dinga nuna maka luv ɗin."


"No Babe! It's not okey for me, cox ke ma soon za ki zama mallakina, kuma dole ina buƙatar ki dinga nuna min luv a zahiri."


Maleek ya yi maganar yana sake miskile face, amma can ƙasan zuciyarsa dariyane fal cikinsa,sabida yadda TAIMIYYAH ke yi da fuska cike da nuna kishi a zahiri,hakan ba ƙaramin sake kimsa soyayyarta ya yi a zuciyarsa ba.


TAIMIYYAH bata kuma magana ba sai tashi da ta yi,ta isa wajen da aka shirya coolers ɗin abincin da ta ɓata lokaci ta yi masa. Ta fara da buɗe cooler ɗin farko tana tambayar Maleek me za ta zuba masa? Ya ɗago manyan idanunsa ya kai kanta yana cewa, "No wife am full ,Hajjah ta cika min ciki da abincinta."


TAIMIYYAH ta tsuke fuska cike da rashin jin daɗi ta furta, "Please! A zuba maka dai ko kaɗan ne, ka ga na ɓata lokaci me yawa wajen yin girkin,in zuba please?"


Yadda ta marairaice masa cike da shagwaɓa, yasa Maleek kasa sake gwaleta a karo na biyu,sai ya ɗaga mata kai yana furta, "Amma ɗan kaɗan Zaynabb."


TAIMIYYAH ta zuba masa shinkafar ɗan kaɗan, ta zuba haɗin Salad ɗin daga gefe guda,sanna ta taso ta kawo masa tana me aje plate ɗin daga saman kujera.


Maleek kaɗan ya ci abincin amma ya ji daɗinsa ƙwarai,tare da jin mamakin cewa Zaynab ɗin ce da kanta tayi wannan haɗaɗɗan abincin.


Lokacin da ya tashi tafiya TAIMIYYAH ta shiga da shi wajen Ummie suka gaisa,ya aje mata kuɗaɗe masu yawa,Ummie ta yi masa godia bayan ta yi iya yinta ya ɗauki kuɗinsa ya ƙi, daga wajen Ummie TAIMIYYAH ta yi masa jagora zuwa wajen Hajjaju Iyah. Maleek ya zube ya kwashi gaisuwa tare ajewa Iyah kuɗaɗe ita ma masu yawa, Iyah ta yi maza ta ce TAIMIYYAH ta kwashe kuɗin ta mayar masa. Maleek ya nunawa Iyah cewa ba zai ji daɗi ba, idan har bata amshi kuɗin ba,hakan yasa Iyah haƙura ta bar kuɗin suka fito daga falon shi da TAIMIYYAH, wacce za ta yi masa rakiya zuwa bakin ƙofar fita daga Part ɗin nasu.


Maleek ya dakata daga tafiyar da ya ke yi, lokacin da ya fahimci cewa iya bakin ƙofar fitowa kawai TAIMIYYAH za ta yi masa rakiyar,ya buɗe baki cike da ƙasaita ya ke furta, "Zaynabb iya nan kawai za ki yi rakiyar?"


Ta gyaɗa masa kai tana magana cike da shagwaɓa ta ke cewa, "Sorry na gaji ne shiyasa, ka gaida Hajjah da kyau Allah ya tsare hanya."


Maleek ya ji daɗin kalamanta ƙwarai, shiyasa ya sakar mata ƙaramin smile ya ce, "Ameen wife thank u, Hajjah za ta ji sosai but ba ki ce in gaida Anty ɗinki ba, tare muka taho fa tana wajen Hajjah."


TAIMIYYAH sai ta kwaɓe face tace , "Ka gaishe ta tuh."


Maleek ya sake sakin murmushi yana yin gaba,TAIMIYYAH ta bi bayansa da kallo tana jin wani irin zazzafan feeling na kwaranya a zuciyarta,ta juya cikin slowly zuwa cikin falon Iyah.


Zamanta bada jimawa ba Tukur ya fara shigowa da manyan ledoji masu ɗauke da tambarin SAHAD STORE, daga ita har Iyah suka zubawa manyan ledojin har huɗu da Tukur ya aje a falon ido. Tukur ya juya ya fice bayan sun gaisa da Iyah, ya sanar da ita cewa Maleek da ya fita yanzu ne yasa shi shigowa da kayan.


Iyah ta jinjina kai kawai tana rasa bakin magana,don ita sam bata son irin waɗannan ɗawainiyar. TAIMIYYAH sai ta tashi tsam! Ta nufi ɗakinta ba tare da ta bi ta kan sababin da Iyah ta fara yi akan yawan kayan ba.....✍🏻


















#Ɗansabo ce#
[12/14, 10:13 PM] +234 703 769 7050: Littafin TAIMIYYAH paid book ne,ga duk wanda ta tsincesa a kowani irin group ne,kiji tsoran Allah karki karanta sai kin biya 500 naira only.


Za ku iya min magana ta wannan number ɗin 08167768704, ko kuma ku turo kuɗin ku kai tsaye ta wannan account ɗin 0504192664 aisha ibrahim dansabo GTbank.*


*Sai ku tura shaidan biyanku ta wannan line ɗin 08167768704.*


Masu turo credit za ku turo katin MTN na 500 ta wannan line ɗin 08167768704.




_Ina ƴan kasuwa masu buƙatar a tallata muku hajar ku? Maza ku garzayo da kuɗi ƙalilan a tallata muku kayan siyarwanku sai dai kawai ku ji ana kiran waya don buƙatan sayan kayan ku,ku tuntuɓeni ta layina kamar haka 08167768704._




*63*


*Gonar Ganye.*
*09:40pm*


Baka jin sautin komi cikin falon Hajjah sai na kukan da Suhailah ke yi, me taɓa zuciyar duk wani me saurarenta. Daga Maleek har Hajjah kallonta suke yi cike da tausayi me tarin yawa, Hajjah ta tashi ta isa wajen da Suhailah ke zaune, ta haɗe kanta da guiwa tana razgar kuka. Ta zauna kusa da ita tana me ɗago fuskarta ta fara faɗin, "Suhailah haƙury za ki yi, na san akwai ciwo amma bamu isa mu ja da hukuncin Ubangijiba,Maleek zai sake aure ne ba don ya daina sonki ko ya daina ƙaunarki ba,haka ba don ba ki haihu zai sake aure ba, zai sake aure ne sabida haka Allah ya rubuta masa cikin littafin ƙaddaransa, za ki fahimci hakan ne daga labarin da muka baki, tun daga kan mafarkin da yake yi da Yarinyar, har kawo haɗuwata da ita da sanadin da ya zama silar kulluwar zumunci a tsakaninmu da su.Suhailah bana so ki ga cewa ba a yi miki adalci ba, shiyasa na zaɓi ku taho nan don a buɗe miki komi, ba wai ki ji magana daga sama ba,ina baki haƙury tare da tausar zuciyarki,akan ki ɗauki ƙarin auren da Maleek zai yi a matsayin rubutacciyar ƙaddaranku ke da shi,wanda mu da ku duka bamu isa ja da hukuncin Ubangiji akan hakan ba,don haka ki nutsu ki rungumi ƙaddara tare da baiwa mijinki goyan baya, ki yi addu'a Allah ya haɗa kan ku ya ba ku dauwamammiyar zaman lafiya."


Hajjah ta ƙare maganar tana me rungumo Suhailah zuwa jikinta, ta cigaba da rarrashinta da kalamai na kwantar da hankali.


Suhailah ta ɗago kanta daga jikin Hajjah, tana kallon direction ɗin da A.Maleek ke zaune, sai kawai ta sake barkewa da kuka,babu abinda ke amsa kuwwa cikin kanta da kunnuwarta ,sai maganar ƙarin auren da zai yi nan da lokaci kaɗan, kamar yadda ya sanar mata da bakinsa.


Maleek ya ɗago manyan idanunsa ya sauke akan fuskar Suhailah, yana jin tausayinta me girma na kassara zuciyarsa. Memakon ya yi magana sai kawai ya miƙe yana barin musu falon ,ya fice baki ɗaya don ba zai iya zama yana cigaba da sauraren sautin kukan Suhailah ba.


Daga Hajjah har Suhailah suka bi bayansa da kallo, Suhailah ta sake fashewa da kuka tana ji tamkar zuciyarta za ta fashe,wani mahaukacin kishin Maleek ke sake danne zuciyarta. Duk iya yadda Hajjah ta kai da son ta ga cewa Suhailah ta fahimce ta abin ya ci tura,sai ma tashi da Suhailar ta yi ta nufi ɗakinta na tun asali a gidan, ta kulle kanta a ciki don bata son sake jin kowani irin rarrashi daga wajen Hajjah, ta kuma gama ƙudurcewa a zuciyarta ba za ta bi Maleek zuwa GRA gidansu su kwana tare ba,don haushinsa take ji daga shi har Hajjan.


Gaba ɗaya daren idan Suhailah ta ce ta rintsa to ta yi ƙarya,tsanar Hajjah da Maleek take ji me zafi a ranta, tana ganin cewa sun daina ƙaunarta ne kawai,sabida Allah ya jarabceta da rashin haihuwa.


Ko da gari ya waye duk iya bugun ƙofar da Hajjah ta dinga yi, akan Suhailah ta buɗe ta saurareta abin ya ci tura,sai ma cewa ta yi da Hajjah ta tafi abin ta don ba za ta taɓa buɗe ƙofar ba,gara su barta ta mutu su ɗauki gawarta tunda sun daina ƙaunarta, don an ga ba idon iyayenta a raye.


Waɗannan kalamai na Suhailah su suka dugunzuma zuciyar Hajjah,ta juya cikin tsananin fushi ta nufi ɗakinta don kiran Maleek,ta sanar da shi halin da take ciki da Suhailah. Lokacin da Maleek ya iso gidan Hajjah da ƙyar Suhailah ta yadda ta buɗe ƙofar ɗakin, kallo ɗaya ya yi wa idanunta ya san ko kaɗan bata samu bacci ba. Sai tausayinta ya kama zuciyarsa,ya isa gareta yana ƙoƙarin sanyata a jikinsa ya rungumeta, amma sai Suhailah ta yi gaggawar hankaɗe hannunwansa daga taɓa jikinta,ta fara gaya masa zafafan kalaman da suka hasala zuciyar Maleek. Ya ɗaga hannu zai ɗauke ta da mari sakamakon zafafan kalaman da ta faɗi na ƙarshe tana cewa, "Kar ka kuskura ka ce za ka sake taɓani,ka je can wajen gurguwar na sallama mata kai Yaya Maleek, tunda ka tsaneni ka ci amanata, ka zaɓi auren nakasasshiya sabida ban haihu ba,meyasa idan auren za ka ƙara ba za a sanyaka ka auro me lafiya ba sai gurguwa, nakasasshiya sabida ku tozarta ni...."


Hannun da ya ɗaga zai zabga mata mari ne ,ya sanya Suhailah gintse kalamanta,Maleek da idanunsa suka fara sauya launi ko me ya tuna? Sai ya sauke hannunsa ba tare da ya kai mata marin ba kamar yadda ya yi niyya. Ya juya cikin tsananin fishi ya fito daga ɗakin ya nufi ɗakin Hajjah. A zaune ya samu Hajjah ranta a matuƙar ɓace ita ma, don kalaman Suhailah sam basu yi mata daɗi ba ko kaɗan.
Ya isa kusa da ita ya zauna yana buɗe baki ya ce, "Hajjah haƙury za ki yi da Suhailah, ni da ke duka mun riga mun san sai hakan ya faru,idan har ta ji maganar aurennan,don haka ki yi biris da ita da duk wani haukar kishin da za ta nuna,ni zan wuce Lagos zuwa anjima,amma ita zan barta anan ta samu kaman 2 weeks kafin ta koma Abuja,watakila zuwa lokacin ta saduda ta haƙurewa zuciyarta, don duk wani haukanta ba su isa su hana komi ba,sannan ki gargaɗeta akan aibanta halittar Zaynab a gaban idanuna,idan har ta cigaba da hakan zan mugun saɓa mata,don ko a yanzu ma na kai zuciyata nesa ne da sai na kwaɗa mata mari."


Maleek ya yi maganar cikin fishi me tsanani, don a yanzu idan akwai abinda ya tsani ji bai wuce a kira TAIMIYYAH da suna gurguwaba,hakan na masa ciwo ko da a ce daga bakin ita TAIMIYYAR kalmar ya fita.
Hajjah ta jinjina kanta kafin ta dubi cikin idanunsa tana faɗin, "Allah ya tsare hanya Maleek, tabbas barin Suhailah a nan ɗin shi zai fi,don tana buƙatar a bata space ta huce,zan kuma san ta inda zan ɓullo mata,ai kishi ba hauka bane."


Daga haka Maleek ya yi sallama da Hajjah ya fito daga gidan, ba tare da ya sake bi ta kan Suhailah ba. Yusuf Driver shi ne zai kai shi Kaduna, ya bi flight ɗin 2 zuwa Lagos.Suna kan hanya ne ya kira TAIMIYYAH a waya su kai sallama da juna,akan cewa nan da sati biyu masu zuwa zai sake dawowa,wanda ya ke fata idan ya dawo ɗin kafin ya bar gari an kai kuɗi da kayan sanya ranar aurensu,don ba ya ji zai iya ƙara watanni biyu ba tare da ya mallaki TAIMIYYAH a matsayin halaliyarsa ba.


__________


*Bayan Sati Uku*


*Saturday, 05:56pm.*


Umma ta dubi Baba Sani hankalinta a matuƙar tashe ta ce, "Yanzu Baban Basmah kana nufin duk waɗannan uban kwalayen, kamar za a buɗe shago kayan sanya ranar auran TAIMIYYAH ne? Wai shin ma da yaushe ta samu mijin har magana yayi ƙarfi,ba tare da ko sau ɗaya bakinka ya furta hakan ba?"


Umma ta kai ƙarshen maganar da jefa masa tambaya, tana jin yadda zuciyarta ke sake rufewa da wani irin duhun ɓacin rai,idanunta na cigaba da kallon uban kwalaye zuwa katan-katan nasu ruwa da juice, da suka cinye rabin bango guda na falon daga sama har ƙasa.
Bata taɓama ganin kayan sanya ranar auren da aka haɗo kayayyaki irin wannan ba, ta sake ɗaga idanunta ta dubi Baba Sani wanda ya tamke fuska tamau, ba shi kuma da niyyar bata amsar tambayarta. hakan yasa ta

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login