Showing 9001 words to 12000 words out of 186776 words
Chapter 4 - TAIMIYAH Book Complete Document by Ayshat Dansabo Lemu .txt
san yanawa TAIMIYYAH illa ba,zuwa lokacin tayi kwance a bed tana tada kai da pillow,hannunta ɗaya dafe da wayan a kunni,yanayin salon da yai maganan kawai ya bata tabbacin rigimansa da neman magana ne kawai ya tashi,inba haka ba ita ta mance rabon daya ƙirƙiri cewa sai girkinta zai ci,sanin idan ta bijire wani sabon rigiman ne yasa ta faɗin "Baka da Matsala Yayana,faɗi me kake son ci ka ga da yin safe sai aje cefanen abinda babu."
Ya saki murmushi daga ɓangarensa,kafin ya gyara kwanciyansa yana jin tasirin muryanta da salon shagwaɓarta na kassara gaɓɓan jikinsa,tuni idanunsa ke hasko masa yadda take maganan ɗan ƙaramin bakinta na motsawa,ya lumshe idanunsa ya buɗe kafin ya furta "Bani da wani zaɓi ai kinsan duka irin abincin da nafi so,yanzu me kike yi yau ki ka kai har to 11pm baki bacci ba?"
Ya ƙare maganan da jefa mata tambaya,domin ya santa da baccin wuri wani lokacin tara ma ta daɗe da yin bacci,TAIMIYYAH ta sake yin ƙasa da murya tana faɗin "Kallo nake na wani film da ya ɗauke hankalina."
"Hala film ɗin na soyayya ne ko?"
Ya sake jafe mata tambayan,TAIMIYYAH ta waro ido waje kaman tana gabansa,kafin ta wani kwaɓe face cikin shagwaɓe murya ta furta "Kai Yah Deeku ni dai bance ba kawai dai Film ɗin na da kyau ne,kasan Korean Films akwai ɗaukan hankali."
"Shikenan Baby idan na zo kya bani labarin Film ɗin,wannan Old Woman ɗin ta jima da yin bacci kenan,ki gaisheta zuwa da safe kice wallahi idan na iso gobe rigima zamuyi sosai da ita,tunda yanzu ta daina ƙaunata so take ta zama ƴar ta'addan Soyayya."
Cewan Yah Sadeeq da wani irin salon da yasa TAIMIYYAH fashewa da dariya,sai da tayi me isanta yana sauraranta da jin kaman ya rufe ido ya ganshi gabanta,kafin ta tsaida dariyan tana faɗin "Kai Yah Deeku Iyan ce tazama ƴar ta'adda daga faɗin gaskiya."
Ta ƙare maganan da dariya a muryanta,hakan yasa Sadeeq taɓe baki kaman TAIMIYYAN na kallonsa,kafin ya furta "Okey gaskiya ma take faɗi lallai Baby,any way bye karki ɓata mood ɗina yanzu in kasa bacci."
Bai jira cewan komi ba yai hanging up,TAIMIYYAH ta sauke wayan daga kunni tana me taɓe baki,ko kaɗan bata ji duk wani salonsa zata bari yai tasiri akanta,bare ta jefa kanta acikin masifan da bazata iya fita ba,don a ganinta yin soyayyah da shi babban masifa ne a gareta domin Umma ba zata taɓa bari ta sami nutsuwan zuciya ba,aje wayan tayi tana hamma alamun baccin yazo da gaske,sanin Ladi zata kashe kayan kallon idan taji bacci yasa TAIMIYYAH nufan toilet ta ɗauro alwalan kwanciya bacci,already tana sanye da kayan bacci shiyasa tana fitowa ta kashe fitilan ɗakin ta haye bed,bata ɗauki lokaci ba kuwa baccin yai gaba da ita.
_________
Ƙarfe goma na safe(10:00am) A.Maleek Ibrahim ya fito daga wanka,tunda ya sanyo kansa cikin Bedroom ɗin nasa qamshinta daya shaƙo ya sanar dashi wacece,hakan yasa ya ɗauke kai sam bai kalli inda take ba, ya taka zuwa gaban dogon mirrow ɗin ɗakin,yana cigaba da tsane ruwan jikinsa yana jin tasirin idanunta da ke biye dashi,amma sam yaƙi duban sashin da ta zauna daga bakin Bed ɗinsa idanunta akansa "Darling good morning." Cewan Suhailah cikin narke murya,amma memakon ya amsa sai yai biris da ita yana cigaba da abinda yake,hakan yasa ta miƙewa ta isa garesa,ba tai magana sai ɗauke man da yake shafawa da tayi,ta lakuta kaɗan ta murza a tafukan hannunta,tana me kai hannu don fara shafa masa amma sai ya kama hannunta ya riƙe,manyan idanunsa masu cike da kwarjini ya zuba mata fuskansa a tsuke yake tsaf babu annuri,cikin muryan da idan yai mata magana dashi take sanin babu alamun wasa ya fara faɗin "Bana so Suhailah,sai yanzu ne kika san ki ɗakko ƙafa ki shigo ɗakina,meya hanaki zuwa ki kwana da mijinki a daren jiya?Bayan kinfi kowa sanin na tsani raba shinfiɗa,look! Suhailah wallahi kinji na rantse na fara kaiwa maƙura da halayyanki da sabbin banzayen ɗabi'un da kike shigowa dasu a zamantakewan auren mu,idan ma sabbin ƙawaye kikai da suke neman canzaki to kisani bazan ɗauka ba,don haka tun wuri ki dawo cikin hankalinki ina nan ban canxa ba daga Maleek ɗin da kika sani abaya ba,karki ga ina nuna miki so ki ɗauka na sauya ne ban sauya ba,kuma zan baki mamaki nan kusa."
Ya ƙare maganan yana sakin hannuwanta,tare da raɓa ta ya wuce zuwa wajen kayansa da ya fiddo zai saka,Suhailah ta bishi da kallo kafin ta fara faɗin "Haba My A.Maleek duk me yayi zafi haka?Ni gaba ɗaya wannan dawowan naka na rasa me ke fusata zuciyanka akaina,ni wani sauyawa nayi don Allah? Gayu iya gayu ina maka ta ina na rage ka,gyaran ɗakinka da girki su kaɗai ne nasan matsalata,kuma nace maka zan samo masu aikin da zasu dinga yi kaine ka nuna baka so,ni kuma kasan na tsani aikin gyara da girki tun ina gida,kuma a hakan idan na samu time da kaina nake zagewa in gyara ko'ina a ɗakinnan,girki kuma kai da kanka ka yaba cewa Ameena ta iya girki,to me kake so kuma dani Maleek?"
Ta ƙare maganan tamkar zata fashe masa da kuka,tana tsananin son sa bata faye son ɓata ranshi ba,amma akan wannan matsalan sam bata ji zata iya biye masa ta koma yadda yake so ɗin,bata son girki a rayuwanta sam tafi gane a girka taci ta kwanta,bata son moriya da yawan aikace-aikace amma shi Maleek so yake ta zama ƴar bautansa,komi na hidimansa yace sai itace da kanta zatai masa komi,hatta girki yafi so idan yana nan tayi masa abinci da kanta,ita kuma hakan ne take ganin bazata iya ba,wani irin kallo ya juyo ya watsa mata kafin cikin kaushin murya ya fara faɗin "Okey! Kina iya bani waje tunda baki san me nake so da ke ba,amma ina so kisa a ranki duk randa kika ji nazo da maganan sake aure kiyi kuka da kanki ne,domin na fara ji ajikina dole zan sami wata abokiyan rayuwan da zata iya sadaukar da lokacinta domin yimin hidima,tare da bin dukkanin umurnina."
Suhailah da maganansa ya mugun girgizata,game da zancen sake auren daya shigo dashi tayi saurin kallonsa a razane,za tai magana ya daka mata tsawa yana nuna mata hanyan fita,hakan yasa Suhailah fashewa da kuka tana ficewa daga ɗakin nasa,ya bita da tsaki yana cigaba da shirinsa,cikin mintuna biyar ya gama kintsa kansa cikin wani lallausan farin yadi,da yai masa mugun kyau links ɗin hannun rigan ya gama sawa,ya isa gaban madubi ya ɗauki turarensa na RALPH LAUREN yana fesawa gaba ɗakin ya sake rinewa da daddaɗan qamshinsa,wayoyinsa ya kwasa ya fito zuwa down stairs.
A ɓangaren Suhailah kuwa tana fitowa daga ɗakinsa,ta wuce ɗakinta tana ɗaukan waya ta kira Hajiyansa,kuka ta sanya mata tana sanar da ita cewa Maleek aure zai ƙara ya daina son ta da ƙaunarta,bata aje wayan ba sai da Hajiyan ta gama rarrashinta da bata tabbacin wasa A.Maleek yake kawai,sai dai sam ta kasa samun sukuni hakan yasa ta fito ta koma ɗakinsa, ganin baya nan yasa ta san ya sauka ƙasa kenan,sai kawai ta biyo bayansa zuwa falon ƙasa,direct ɓangaren dining ta nufa don tana da tabbacin wannan time ɗin yake zaman karya kumallo indai yana ƙasan ko yana gari,ilai kuwa can ta hangesa riƙe da cup ɗin Tea yana kurɓa,gabansa plate ne daya zuba chips,Suhailah ta ja kujeran dake kusa dashi ta zauna,tana sake duban yadda ya haɗe fuska kaman hadarin watan Augusta,cikin narke murya ta fara faɗin "My Maleek don girman Allah kayi haƙury,insha Allah zan gyara duka kuskurena,amma don Allah karka sake min irin wasan ɗazu wai zaka iya samo wata bayan ni,wallahi zuciyata zata iya tarwatsewa,kai min rai don Allah ka bar shigo da irin wannan wasan,in dai abinda kake son in dinga yima da kaina ne zan dingayi Allah kuwa zan daure kaji Baby."
Ta ƙare maganan tana kwantar da kanta a kafaɗansa tare da kama hannunsa ta shiga murzawa,hakan yasa ya dubi cikin idanunta tare da watsa mata harara,kafin ya sake kurɓan Tea ɗinsa ya aje cup ɗin yana faɗin "Ni ɗin ne nake wasa Suhailah?Wato a wasa kika ɗauki maganan ko Hmm! To maganan Planing ɗin da baki fasa ba kuma fa? Ko kina ɗaukata a sakarai ne bansan duk wani motsinki ba,to ki sani ni bazan iya cigaba da zama da macen da bata shirya haɗa zuri'a dani ba,in karatune ina sha kin ƙare har bautan ƙasan duk kin gama,to ina so kisa a ranki nan da wani lokaci kaɗan komai zai iya faruwa,abinda kike ɗauka wasa zai matuƙar baki mamaki."
Kafin Suhailah ta sami ƙwarin guiwan yin magana,wayan A.Maleek ɗin ya fara kiɗa alamun shigowan kira,daga yana yin ringing ɗin yasan Hajiyansa ce,don haka yayi hanzarin ɗauka yana fara gaida ta,memakon ta amsa sai kawai ta shiga tuhumansa akan cewa me zaisa ya fara ɗagawa Suhailan hankali da zancen cewa zai sake aure,ta rufesa da faɗa ba tare da ta bashi daman kare kansa ba,daga ƙarshe ta kashe wayanta ta bar Maleek da bin wayan da kallo,kafin ya maida dubansa kan Suhailah ta dai tsumu alamun rashin gaskiya,ya aika mata da mugun kallo yana faɗin "Bar kallona kinyi da ido kaman Munafuka,zan baki mamaki wallahi domin sai na sanarwa Hajiyan abinda kike aikatawa wanda sai tayi fishi da ke,xanga ƙarshen ji dake da take yi alhali ke ko haɗa jini da ita baki shirya yi ba,sai gayu da ƙaryan kina son ɗanta da kishinsa,haka ake son Suhailah?"
Suhailah dai tai ƙus zuciyanta na faman bugawa,idan akwai abinda baza ta so ba shine MALEEK ya tona mata asiri a wajen Hajiyansa ta gane cewa,itace ke anfani da maganin hana ɗaukan ciki,tasani Hajiya tafi kowa tsanan tsarin Iyali,kuma a ƙagauce take da ta samu jika daga gare su,ganin yana shirin miƙewa ya bar wajen don tuni ya kammala cin abincinsa,hakan yasa ta tashi ta ruƙunƙumeshi tana magiyan kada ya faɗiwa Hajiya,ita wallahi ta daɗe da daina anfani da komi na hana ɗaukan ciki,lokaci ne kawai baiyi ba,sam Maleek fuskansa babu sassauci ya zare ta daga jikinsa yana takawa ya bar mata wajen,wayoyinsa kawai ya kwasa a falo da mukullin mota yai waje don barin mata gidan ma baki ɗaya,zuciyansa na tunzurasa akan yaje ya fayyace wa Hajiyan irin rayuwan da yake yi da Suhailah,ko Hajiyan zata daina goyan bayanta da ɗaure mata gindi,hakan yasa ko da ya tada mota ya baro gidan kai tsaye hanyan da zai Kaishi Gonan Ganye ya nufa,inda a nan ne ya tanfatsawa Hajiyan nata ginin.........✍🏻
#Ɗansabo ce#
[12/14, 10:04 PM] +234 703 769 7050: *TAIMIYYAH*❤️
©️Ayshat Ɗansabo Lemu✍🏻
*Page 7*
Sallama TAIMIYYAH tai tayi a falon babu amsa,hakan yasa ta sanya kanta cikin falon sosai tana raba idanu,zuciyanta na tariyo mata baya kaman basuyi dadalmaya a sashin ba,gashi yanzu shigowa ma tayi hira da ƴan uwanta ya gagareta,ba don bata so ba sai don yadda su ɗin suka juye suka maida ta tamkar mujiya a cikinsu,zuciyanta yai nauyi tana jin tasirin damuwan hakan da take dannewa can ƙasan ranta na taso mata,hanyan da zai sada ta da asalin main Kitchen ɗin su Umman ta nufa,don tana hasashen samun ta acan tunda har ta fito bata ji an kaiwa Iya abincin rana ba,watakil yau ɗin sunyi ranan girki ne kaman yadda suka saba duk ranan Friday sukan yi ranan gama abincin rana,sabida yawan aikin da ke ƙaruwa tunda shi ma Baba Sanin sai Weekend yake dawowa daga can Kano inda yake aiki,kaman yadda tai hasashe haka ya kasance,tana sanya kanta cikin Kitchen ɗin bakinta ɗauke da sallama,idanunta akan Umma da ke tsaye jikin Cabinet na Kitchen ɗin ya fara sauka,su Mero me aiki nata faman hidiman kammala abinci ana kwashe su a manyan kulas,TAIMIYYAH ta gaida su Mero tana cigaba da takawa zuwa inda Umma ke tsaye,wacce sarai taji shigowan TAIMIYYAN tana kuma jin gaisuwan da take ma su Mero amma bata juyo ta dube ta ba "Sannu da aiki Umma ina yini."
Cewan TAIMIYYAH lokacin da ta isa daf da Umman,sai lokacin Umma ta juyo ta zuba mata idanu,fuskanta a haɗe tana faman yatsina,ta amsa gaisuwan da faɗin "Lafiya." A taƙaice daga haka ta cigaba da rufe tray ɗin da tai raping Salad,ganin hakan yasa kai tsaye TAIMIYYAH ta aje ledan saƙon a saman Cabinet ɗin tana faɗin "Gashi inji Iya." Daga haka sai ta juyo don baro sashin baki ɗaya,su Mero na ce mata a gaida Iya,Umma ce tayi saurin dakatar da ita tana faɗin "Ke! zo nan ki ɗauki wancan kwandon abincin ki kai min dining ɗin falo ."
TAIMIYYAH ta waiwayo tare da sauke manyan idanunta akan ƙaton Basket ɗin,ta nufesa tana ɗauka ta cigaba da tafiya ahankali dafe da ƙafanta me laluran,ɗaya hannun riƙe da Basket ɗin da aka jere kulolin abinci ta fito zuwa falo,da Zuhura taci karo wacce ta fito daga ɓangaren ɗakunan baccin su,TAIMIYYAH ta ɗauke idanunta daga kanta tana wucewa inda aka aiketa,ta aje kwandon abincin tana shirin juyawa don ficewa daga sashin nasu,sai ga Umma ta baro Kitchen ɗin ta fito falon,idanunta akan TAIMIYYAH tana dubanta daga sama har ƙasa,takaici da tsanan TAIMIYYAN na sake kamata,musamman in ta tuna yadda Sadeeq ya iya duban tsakiyan idanunta ya sanar da ita wai wannan musakan dake gabanta yake so,kuma son ma da aure hakan ba ƙaramin taɓa zuciyanta yake ba, "Koma ki zauna magana zanyi da ke shu'uma kina faman wani ƙus da kai munafuka."
Cewan Umma idanunta fes akan TAIMIYYAH,tuni TAIMIYYAH tayi saurin zama daga ƙasan tiles ɗin wajen,Umma kuma tayi zaune akan Kujeran da ke kusa da ita,yayin da Zuhura ma tayi zaune kusa da Umma domin bazata so tijaran da Umma zataiwa TAIMIYYAH akan Yayansu ya wuce taba,Umma ta soma faɗin "Wato ke dai wannan musakan baki jin magana ko,wai haka gurugu ke da taurin kai ne ni Zuwaira,yo inba taurin kai ba ke da nai miki iyaka da ɗana tun da daɗewa,shine kika cigaba da ribatan zuciyansa,har ya samu ƙwarin guiwan kallon idanuna yana sanar dani wai kece zaɓinsa,to bari kiji in gaya miki ni Zuwaira indai ni na kawo Sadeeq duniya,kuma Nono na ya tsotsa to na haramta soyayya a tsakaninku bare maganan aure ya shigo,in banda ma shi ɗin sakarai ne duk matan duniya ya rasa wacce zuciyansa zai so sai gurguwa musaka,me zaici da ke ya aure ki yace ya auri wa? Salon ya kunya tani ya zubda min aji acikin ƙawaye,to ahir ɗinki ba ki ba shi kije can ki jajibo gurgu irin ki da zaku fi dacewa da juna amma ba jinin shuwa ba,tashi ki bani waje saura kije ki sanar da Iyan ina dai-dai da kowa ne indai akanki ne shashasha kawai,sai shegen kyau da idanu kaman na jinnu."
Umma ta ƙare maganan cikin ɗaga murya,TAIMIYYAH da tai ƙasa da kanta tana zubda hawaye,tayi saurin ɗagowa tai musu kallo ɗaya tana miƙewa,tare da dafa ƙafanta ta fara takawa don fita daga falon,hatta jikinta rawa yake sabida ɓacin rai da wani irin ƙunci dake cin ranta,a haka ta fito daga sashin tana danne kukan da ke taho mata,aiko tana tabbatar da cewa ta fito daga Sashin ta samu bakin inda aka zagaye Flowers tayi zaune tana haɗe kanta da guiwa,ta saki kukan da take dannewa ko zata samu sauƙin ciwan da zuciyanta keyi,kuka take sosai irin wanda ke tasowa tun daga ƙasan zuciyan wanda ya jima yana haɗiyan baƙin cikin wani abu dake cin zuciyansa,sosai zuciyanta ke zafi kalaman Umma na sake ƙona zuciyan tamkar ana zuba tafasasshen ruwan zafi,ta rasa miye aibunta don ta kasance gurguwa,bata san miye laifinta don ta zamo a yadda Ubangiji yaso ta kasance ba,bata san meyasa Umma ta kasa gane cewa Sadeeq baya gabanta ba,ko batai mata gargaɗi akansa ba ita ɗin da kanta bazata taɓa bari zuciyanta tai gangancin faɗawa tarkonsa ba,meyasa Umma tai mata irin wannan tsanan ne? Sabida kawai ta kasance gurguwa me lalura ne ,ko kuwa akwai wani dalilinta ne na ƙinta da take ɓoyewa a ranta? Waɗannan tarin tambayoyin sune suka cigaba da cika kwanyan TAIMIYYAH tana buƙatan amsan su,kuka tayi sosai tana sauke ajiyan zuciya akai-akai,har lokacin kanta na kife cikin guiwoyinta,sam bata ji tahowan mutum inda take ba sai da hancinta ya fara shaqo mata qamshin turaren BENTLEY,sannan tayi saurin ɗago manyan idanunta waɗanda zuwa lokacin suka rine daga farinsu su ka koma jajur sabida kukan da ta sha,bata sauke idanun a ko'ina ba sai akan kyakykyawan fuskansa,hakan yasa tayi saurin sauke kanta ta maida shi inda yake tun farko,wasu hawayen na sake ɓalle mata kaman ana sake ingizo su,qamshin turaren BENTLEY da ya sake ƙarfi a cikin hancinta ya tabbatar mata Yah Sadeeq ya ƙariso daf da ita kenan,kafin tayi wani motsi sai jin saukan hannayen shi tayi a jikinta yana me ɗago fuskanta,cikin wani irin murya yake faɗin "Subhanallah! Kuka Zaynab me akai miki daga ina kike?" Duk ya furta mata tambayoyin har lokacin yana riƙe da fuskanta a tafukan hannayensa,zuwa lokacin tuni dama ya rage tsawonsa yana tsugunne gabanta ne,memakon TAIMIYYAH ta bashi amsa sai kawai takai hannunta tana cire nasa daya riƙe face ɗinta,cikin muryan kuka take faɗin "Babu komi Yah Sadeeq sannu da zuwa."
"Babu komi ne zan sameki anan kina kuka haka Zaynab,common sanar dani me akai miki kuma ke da waye?"
Cewan Sadeeq yana sake sanya idanunsa cikin nata,hakan yasa ta lumshe nata idanun tana jin wani irin ƙunci na sake mamaye zuciyanta,sam ba tayi farin ciki da wannan arangaman da sukai da shi ba,ta sani matuƙar bata ba shi amsan da zai gamsar da shi ba,zasu yi ta zama ne anan har sai wani yazo ya gansu yaje ya faɗiwa Umman,hakan yasa ta furta "Ni babu abinda ya haɗani da kowa na zo fitowa ne kawai daga part ɗinku tsautsayi ya ɗebeni na faɗi,shine naji zafi sosai dama kuma kaina na ciwo,amma yanzu bari in ƙarisa insha magani."
Yadda ta ƙare maganan cikin rauni da sanyin muryan daya motsa zuciyansa,ya bashi tabbacin daga wajen Umman sa matsalan yake,baya shakkan cewa tayi mata halin nata da ta saba,TAIMIYYAH bazata faɗi masa gaskiya bane kawai,hakan yasa shi zuba mata ido kafin ya furta "Kiyi haƙury Zaynab komi me wucewa ne,watarana Umma da kanta zatai nadaman irin halayyan da take nuna miki,bana so ko kaɗan ki dinga