Showing 141001 words to 144000 words out of 186776 words

Chapter 48 - TAIMIYAH Book Complete Document by Ayshat Dansabo Lemu .txt

15 Dec 2024

6599

na fara dokawa da ƙarfi.
Sai ta miƙe tsam! Tana duban Iyah da ke zaune cikin falon,ta nufi hanyar zuwa ɗakinta tana cewa, "Iyah bari in amsa call, idan na gama bacci bai zo ba,zan dawo na ƙarisa kallon."


Ta cigaba da dafe ƙafarta tana takawa ta nufi hanyar ɗakinta,Iyah tabi bayanta da kallon tana ɗan taɓe baki, ta miƙa hannu ta ɗakko remote,ta canza tasha daga Bollywood zuwa Sunnah TV.


TAIMIYYAH na shiga ɗakinta zama tayi daga bakin bed, lokacin da wani kiran ke shigowa,ganin wannan karon ba vid call bane,sai zuciyarta ta ingizata akan ta ɗaga wayar ta ji ko waye?


Ta yi receving call ɗin tana kai wayan kunni ba tare da tace komi ba,sai ƙirjinta da ke faman doka mata da wani irin yanayi da bata san dalilin hakan ba.


Ƙasaitacciyar muryar Maleek Ado ne ya shiga kunnuwan TAIMIYYAH, in da ya ke cewa, "Hello! Zaynabb!"


Take wani abu ya doka cikin tsakiyar kan TAIMIYYAH.
Ta yi saurin dafe wayar da ke neman suɓucewa a hannunta, tana cigaba da yin shiru ba tare da tayi magana ba,har sai da muryar Maleek ya sake kiran sunanta, cikin wani irin salo da bata taɓa jin mahalukin daya iya sarrafa harshensa, wajen iya kiran asalin sunanta kamar haka ba.


Ta saki numfashin da bata san ta riƙe ba kafin ta furta, "Na'am wa ke magana please?"


Tayi tambayar cikin sanyin murya sosai,tana jiyo yadda shi ma ya sauke numfashi daga ɓangarensa, kafin ya furta, "Maleek Ibrahim ne Zaunabb! Meyasa ba ki yi picking vid call ba,ko ba ki ga message ɗin dana turo miki before in kira ba ne ?"


Ya yi maganar cikin muryarsa me cike da izza,yana sauraran jin me TAIMIYYAH za ta ce? Ta buɗe baki murya can ƙasa take cewa, "Ban san lambar waye ba ne,sabida ban baka lambata ba,don Allah ya aka yi ka samu lambata?"


TAIMIYYAH ta jefa masa tambayar cikin wani irin sanyin muryar ta.


"Ki yi picking vid call da zan kira yanzu Zaynabb please!"


Maleek ya furta hakan yana cuting call ɗin,ya kira ta vid call ɗin.


TAIMIYYAH sai ta janyo Hijab ɗinta da ke saman gado ta sanya, kalar Hijab ɗin blue black ne,sai da ta gyara zaman wuyan Hijab ɗin sosai sannan tayi receiving vid call ɗin,tana jin yadda bugun zuciyarta ke ƙaruwa.


Kyakykyawar miskilalliyar fuskar Maleek Ado ne,ya bayyana akan allon screen ɗin wayarta,yana kwance daga kan makeken bed ɗinsa,yana sanye cikin milk ɗin pajamas da suka haske fatarsa.
TAIMIYYAH tayi saurin ɗauke face ɗinta daga dubansa.Maleek Ado da idanunsa ke kan screen ɗin wayarsa, lokacin da kyakykyawar fuskar TAIMIYYAH ta bayyana masa,sai ya samu kansa da lumshe idanunsa, wani abu na sake dokawa cikin kansa.Ya buɗe idanun ya sauke a side face ɗinta,sabida yadda ta ƙi yadda ta sake kallonsa ta cikin wayartata.Sai yayi magana very low yana cewa, "Zaynabb ki kalleni don Allah ko zan samu cikakkiyar nutsuwa,idan na sanya idanuna cikin kwayar idanunki,waɗanda suka jima suna gilmayya cikin barcina."


Waɗannan furucin da Maleek ya furtasu,su suka sanya TAIMIYYAH saurin duban fuskar wayarta.Manyan idanunta suka sake sauka akan fuskar Maleek,wanda idanunsa ke kafe akan allon screen ɗin wayarsa,ya sauke ajiyar zuciya yana kallon cikin idanun TAIMIYYAH,wani baƙon yanayi na sake lulluɓe ruhinsa,tare da aika wani irin zazzafan saƙo,cikin kowacce kafa ta sadarwa da ke jikinsa.TAIMIYYAH ta sake ƙasa da murya tana cewa, "Don Allah ka daina jefa zuciyata cikin ruɗani,tun ɗazu ka ke furta wasu kalamai da ke nuna kaman ka taɓa sanina awani waje,please! waya turo ka zuwa gareni,ko ince a ina ka taɓa ganina da har kake ganin idanuna acikin baccinka?"


TAIMIYYAH ta kai ƙarshen maganar tana duban fuskar Maleek Ado,cike da son ya fayyace mata yadda aka yi ya santa, har ya kawo kansa gareta.Sam ita ba ta san irin illar da salon maganarta ya yiwa zuciyar Maleek Ado ba,wanda tunda ta fara magana yake duban fuskarta da manyan idanunta,waɗanda suka ƙara girma bisa screen ɗin wayarsa.


Ya wani cije lips ɗinsa, yana ji tamkar ya tsinci TAIMIYYAH a kusa da shi,don kawai ya tasata a gaba ya yi ta kallon kwayar idanunta,waɗanda suka jima suna ruɗa tunaninsa a cikin mafarki.Idanun da ya gama sallamawa cewa ,na wata aljanace can daban wacce ke son kawo ruɗani cikin duniyarsa, a wancan lokacin,amma sai gashi yau Allah ya bayyana masa cikakkiyar surar mamallakiyarsu a zahiri,cikin lokacin da bai taɓa tunani ko hasashe ba, 'ta ya shi ko zai yi sakacin da wannan halittar za ta kubce masa?' Tunanin ya haska cikin kansa da wani irin tasirin da bai taɓa tunani ba.Ya sake duban fuskarta wacce ta sunkuyar da shi ƙasa,da alamu tafin hannunta take kallo,sai ya sake kiran sunanta 'Zaynabb!' TAIMIYYAH tayi firgigit! Ta ɗago manyan idanunta da suka sake girma ta sauke akan fuskarsa,tana me shagwaɓe fuskarta da muryarta duka a lokaci guda,sannan ta furta, "Na'am! Don Allah ka sanar da ni waye kai? A ina ka sanni please!?"


Maleek ya ɗan taɓe baki yana sake miskile fuskarsa ya ce, "Zaynabb meyasa na ke baki tsoro ne wai? Sunana Maleek Ado na sanar miki tun ɗazu,maganar ki san ko ni waye za ki sani amma ba yanzu ba,in da na sanki kuwa da kike magana akai,to a cikin mafarkina na fara sanin idanunki ba fuskarki ba,a cikin mafarki na fara jin wannan muryar taki me kama da magic,a cikin mafarki na san wani ɓangare naki Zaynab,shiyasa yau da idanuna suka sauka akanki,gaba ɗaya na rasa dukkanin nutsuwata.Oya tell me wacece Zainab TAIMIYYAH please?"


Maleek ya yi maganar yana duban yadda TAIMIYYAH ta zaro idanunta, cike da zallar mamakin kalamansa take dubansa,don baƙarmin tsoratata kalamansa na cewa a cikin mafarki ya fara saninta su kai ba.Ta buɗe baki muryarta na shaking take cewa, "Na ji zan sanar da kai komi game da ni, amma sai ka fara bani labarin yadda aka yi, ka ke mafarki da irin idanuna."


Karon farko da Maleek Ado ya saki murmushin da bai shirya yinsa ba,idanunsa na zube fes akan fuskar TAIMIYYAH.Kafin ya maida face ɗinsa ya miskileta kamar yadda take ada, yana farawa da faɗin. "Zaynab zai kai kaman watanni shida zuwa takwas baya, da na fara mafarki da me siffar idanunki a cikin baccina,ya zamana kusan kullum ne sai nayi mafarki da Yarinyar me irin idanunki, amma ba'a taɓa nuna min zahirin fuskar ko wace ce ba,sai dai a nuna min waɗannan idanun masu haske,suna kuka tana miƙo min hannu kamar tana buƙatan taimako daga gare ni,da zaran na miƙa hannu zan kama hannun da ta ke miƙomin, sai na mafarka daga baccin ina jin wani irin yanayi da bana iya fassara shi...."


Ya ɗan numfasa kaɗan kafin ya cigaba da cewa,
"Tun ina yin mafarkin jefi-jefi har mafarkin ya zame min jiki,kuma duk sanda na farka na kan yini cikin tunanin, wace ce wacce ake nuna min idanunta amma bana ganin zahirin surar fuskarta? Amma har in ƙaraci tunanina bana gano komi,daga ƙarshema sai na sanyawa zuciyata cewa aljana ce kawai,don inba aljana ba babu yadda za a yi mutum ya dinga ganin siffar idanu babu fuska,ban kuma taɓa gayawa kowa ina mafarkin ba sai sau ɗaya dana faɗiwa Mahaifiyata,tun kuma bayan dana sanar da ita bada daɗewa ba sai na daina mafarkin baki ɗaya,ban kuma ƙara tuhuman kaina ko meyasa na daina yawan mafarkinba,illa daɗi da naji a lokacin ina cewa addu'ata ne ya amsu, Allah ne ya rabani da ganin idanun aljanar mafarkina.Kwatsam! Sai gashi yau na ga irin idanun akan fuskarki a zahiri Zaynab,ta ya bazan ruɗe har in kasa controlling kaina ba?"


Ya kai karshen maganarsa yana duban yadda TAIMIYYAH ta nutsu tana saurarensa.....✍🏻














#Ɗansabo ce#
[12/14, 10:12 PM] +234 703 769 7050: Littafin TAIMIYYAH paid book ne,ga duk wanda ta tsincesa a kowani irin group ne,kiji tsoran Allah karki karanta sai kin biya 500 naira only.


Za ku iya min magana ta wannan number ɗin 08167768704, ko kuma ku turo kuɗin ku kai tsaye ta wannan account ɗin 0504192664 aisha ibrahim dansabo GTbank.*


*Sai ku tura shaidan biyanku ta wannan line ɗin 08167768704.*


Masu turo credit za ku turo katin MTN na 500 ta wannan line ɗin 08167768704.




_Ina ƴan kasuwa masu buƙatar a tallata muku hajar ku? Maza ku garzayo da kuɗi ƙalilan a tallata muku kayan siyarwanku sai dai kawai ku ji ana kiran waya don buƙatan sayan kayan ku,ku tuntuɓeni ta layina kamar haka 08167768704._


*58*


TAIMIYYAH gaba ɗaya kanta kullewa yayi da jin labarin mafarkin da Maleek Ado ya yi tayi a baya,kuma wai me irin idanunta Maleek ɗin ya ke gani a cikin mafarkin nasa.
Memakon ta tsaya ta cigaba da sauraransa, sai kawai ta kashe wayarta,tana me jingina jikinta da jikin gadon, ta lumshe idanunta.


Bakomi ke yawo a kanta ba, sai moment ɗin ɗazu da yamma zuwa yanzu,gaba ki ɗaya sai ta ji tana tsoran Maleek ɗin ma baki ɗaya.Tana ji yana sake kiranta amma tayi biris da wayar,har ta gama ɓurarinta ta tsinke,zuwa can sai ta ji ƙaran shigowar saƙo cikin wayartata.


Ta miƙa hannu a hankali kamar me tsoron taɓa wayar,ta janyota ta yi swiping tare da buɗo saƙon kai tsaye,don ganin me ke rubuce a ciki,idanunta suka sauka akan kalaman daya aiko kamar haka, " _Zaynabb meyasa zaki kashe min waya?Zan barki ki nutsu da kyau, amma kada ki ce za ki damu kanki da yawan tunanin,cewa sai kin san ko waye ni cikin gaggawa,soon za ki sani Zaynabb.Gud night wife to be._ "


TAIMIYYAH ta dinga karanta saƙon yafi sau goma,kanta na sake ɗaurewa tare da jin matsanancin fargaba, da tsoron wannan mutumi.Kalamansa na ƙarshe ke sake gigita tunaninta inda yace "Wife to be." Tunanin ya haska da wasu irin tarin tambayoyi da suka cika kwanyarta, 'A ina ya san ni,kuma waye ya bashi numberta har ya kirani,ba tare da na bashi ni a karan kaina ba?"


Waɗannan tambayoyin suka cika zuciyar TAIMIYYAH, tare da sake kulle mata kai,ta ƙurawa saƙon idanu tana sake karantawa a karo na goma sha ɗaya.Ta ɗauke dubanta daga karanta saƙon, tana nanata sunansa akan harshenta a bayyane, "Maleek Ado." Kamar yadda ya rubuta daga ƙasan saƙon,ta maida idanunta ta lumshe abinda ya faru ɗazu a falon Abie na dawowa kwanyarta, 'Kenan da gaske mafarkin ya ke yi da irin idanunta,shiyasa ya shiga shock lokacin da ya ganta a zahiri,har yana kasa riƙe kansa sai da ya taɓa fuskarta?" Wannan tunanin ya haska cikin kanta,tana jin wani irin abu na shiga jikinta yana ratsa ɓargonta.Ta sake rintse idanunta zuciyarta na wani irin bugu,ta buɗe idanun tana kai hannu ta shafa fuskarta,ji take yi kamar har lokacin lallausar hannunsa na kan fuskarta ne.


Da ƙyar TAIMIYYAH ta iya yakice tunanin komi, ta sakko daga kan bed ɗin ta nufi toilet,alwala ta ɗauro ta fito ta nufi kan sallaya don gabatar da shafa'i da wuturi, wanda bata yi sai za ta kwanta bacci.


Lokacin da ta idar light off kawai ta yi ta bi lafiyar gado,bayan ta canza kayan jikinta zuwa na bacci,ta jima sosai tana faman tunane-tunane duk akan Maleek Ado.Wanda ya yi mata tsaye a cikin rai, ta ke kuma da buƙatan sanin cikakken waye shi,ya akayi kuma har ya kawo kansa gidansu alhali yace mafarki ya ke kawai da me irin idanunta? Sai da TAIMIYYAH ta ga cewa tunani zai iya halaka kwanyarta, sannan ta lumshe idanunta tana fara karonto azkar na kwanciya bacci.


_____________


A ɓangaren Maleek Ado kuwa,lokacin da ya turawa TAIMIYYAH saƙon,sai ya maida kansa ya kwantar akan pillow yana me lumshe idanunsa.


Muryar TAIMIYYAH da salon maganarta ke dawo masa,yana jin wani irin feeling na dabaibaiye zuciyarsa.Idanunta yake haskowa a lokacin da take waro masa su,bayan ya gama bata labarin mafarkin da ya dinga yi da mai irin idanunta.Kyakykyawar murmushi ya bayyana a saman miskilalliyar fuskarsa,ya kai hannu zuwa kansa yana yamutsa sassalkan gashin kansa me matuƙar ɗaukar ido,sabida kuɗin da suman ke ci ba kaɗan bane.


Kiran Suhailah ne ya shigo cikin wayarsa,hakan ya dawo da shi cikin hayyacinsa,daga duniyar tunanin TAIMIYYAH da ya lula.


Ya miƙa hannu ya janyo wayar, yana receiving call ɗin tare da gyara kwanciyarsa sosai.Muryar Suhailah cikin shagwaɓa ya shiga kunnuwansa lokacin da ta ke cewa, "Hello! my Maleek kana jina?"


Maleek ya buɗe idanunsa yana cuting call ɗin,ya kirata vid call kawai don yana buƙatar ganin yanayin da take ciki.


Fuskar Suhailah zuwa gangar jikinta ne ya bayyana a allon screen ɗinsa,lokacin da Suhailah tayi receiving vid call ɗin.Maleek Ado ya sauke ganinsa a kan rigar baccin da ke jikinta kalar pink me santsi,rigar me faɗin wuya ce hakan yasa ƙirjinta ya fito sosai ta sama.Ya ɗauke idanunsa daga kallon ƙirjinta ya mayar zuwa kan fuskarta,idanunsu suka gauraya dana Suhailah, wacce ita ma nata idanun ke kan kallon face ɗinsa.Ta sakar mata kyakykyawar murmushi tana faɗin,


"My Maleek i miss u,tun ɗazu nake kiran line ɗinnan naka ina jin busy,na kira Hajjah ma bata ɗaga ba,har yanzu fa bana jin daɗin jikina Baby."


Tayi maganar cike da shagwaɓa ganin yadda Maleek ɗin ya tsura mata ido,kafin ya buɗe baki kamar mara son magana ya ce, "Sorry wife,sauƙi ai a hankali yake samuwa, hope dai kina shan magungunan yadda ya dace?" Suhailah ta gyaɗa kai cike da tabbatar masa da cewar tana sha,sai Maleek ya cigaba da cewa,


"Alright! Karki damu zazzaɓin zai tafi soon wife,but i miss u wife so much,oya kiss me wife."


Subailah sai ta saki murmushi, tana aiko masa da kiss ɗin kamar yadda ya buƙata,shi ma sai ya aiko mata da nasa kiss ɗin, suka saki murmushi a lokaci guda.Kowannensu na jin wani matsanancin kewar ɗan uwansa na danne zuciyarsa,Suhailah ta sake narke murya tana cewa, "Sweet ɗazu wata makwafciyarmu ta shigo, ta yi introducing kanta a wajena tana so mu dinga zumunci, tace su ma basu jima da tarewa ba,goben za ka taho ɗin ne my Maleek?"


A.Maleek Ado ya dubi Suhailah da manyan idanunsa ya ce, "Yes gobe zan dawo wife,na gane gidan da kike nufi,ina ga matar Captain Aliyu ce indai wanda gidansu ke jikin namu ne ko?"


Subailah ta amsa da cewa, "Yes haka tace kuwa,sunan mijin Aliyu ita kuma Jawahir,matar me fara'a da son mutane kuwa, daga gani za ta yi kirki sosai Yah Maleek."


Maleek ya ɗaure fuska tare da zama so serious lokacin da ya ce, "Okey daga gani ɗaya da ki kai mata har kin karanci halinta kenan,look Suhailah ni fa bana son saurin sakin jiki da mutanen da kike yi,u have to be very very careful akan irin wanɗanda za ki dinga mu'amala dasu,and bazan yarda da shiga gidan mutane ba,su idan sun shigo miki ba zan hanaki harka da su ba,amma ban yarda kina shiga gidan kowa ba,Abuja bariki ne ba irin Zaria bane da kika sani,so u have to be careful."


Suhailah da ke sauraren Maleek, idanunta akansa ta narke murya tana cewa, "Okey my Maleek zan kiyaye In sha Allah,dama ina gaya maka ne cox tace a gaida ka."


Daga haka suka cigaba da hiransu irin na mata da miji,kafin su yiwa juna gud night, Maleek ya kashe wayarsa yana jin kewar Suhailar me tsanani na ratsa shi,ga kuma tunanin TAIMIYYAH da ke addabar zuciyarsa.
Ya miƙe tsaye yana ɗaukar remote ɗin AC ya ƙara ƙarfin aikinsa,sannan ya nufi toilet don yin uzurinsa,yana fitowa light off yayi ya kwanta, yana ji a zuciyarsa dole gobe kafin ya wuce, ya sanar da Hajjah yadda yake ji akan wannan gurguwan, don ba zai iya jurewa ba,idan har ba mallakarta yayi da gaggawa ba.


____________


Washegary TAIMIYYAH ta tashi ne da tunanin Maleek cikin zuciyarta,amma sai ta dinga kwaɓar zuciyarta akan ta manta da tunaninsa.


Koda ta ga shigowar kiransa vid call, misalin sha ɗaya na safe ƙin ɗauka tayi,duk yadda wani sashi na zuciyarta ke kwaɗaitar da ita,ta ɗauki wayar bata ɗauka ɗin ba har kiran ya yanke,lokacin da wani kiran ya sake shigowa ma TAIMIYYAH ƙin ɗauka ta yi,sai ma ta aje wayar bisa bed tana me fita daga ɗakin baki ɗaya.


_____________


*Gonar Ganye.*


A.Maleek Ado ne zaune a tsakiyar falon Hajjah yana yin breakfast,tun wajen ƙarfe goma ya iso gidan don yana son suyi magana da Hajjah kafin ya wuce Abuja a yau ɗin.


Duk kiran da ya yiwa TAIMIYYAH suna zaune tare da Hajjan ne,hakan yasa ya dubi Hajjah lokacin da kiran ƙarshe ya tsinke ba tare da TAIMIYYAH ta ɗaga ba ya ce, "Hajjah ina ta kiran Yarinyar nan taƙi ta ɗaga wayata,na kirata sau huɗu kenan, gaskiya Hajjah ba zan iya jurar hakan ba,tun jiya da na bata labarin mafarkin dana dinga yi a baya, ta kashe min waya bata ƙara saurarata ba.Don Allah Hajjah ki je wajan kakarta ki sanar dasu halin da ake ciki,don ni ba ƙaramin yaro bane da zan tsaya soyayyar jan aji,tunda na ɗaura idanuna akanta na gane itace yarinyar cikin mafarkina,shikenan zuciyata bata sake hutawa ba,wani azababben ƙaunarta na ke ji irin wanda bazan iya misaltawa ba,sannan ina ji a jikina cewa ba zan sake samun sukunin zuciyata ba, in har ba mallakarta na yi ba Hajjah."


Maleek ya kai ƙarshen maganar cikin marairaice murya,hakan yasa Hajjah dubansa tana faman sakin murmushi ta ce, "Maleek kana da gaggawa a cikin lamuranka,kamata yayi ka yi haƙury ka bita a hankali,ina ga ta tsorota da cewa kana mafarki da ita alhali bata san ka ba,bata san ko kai waye ba. Kawai ta ganka ne rana tsaka ka je gareta,sannan kuma ka ce kana mafarki da irin siffar idanunta,ka ga hakan dole ya jefata a ruɗani.Zan je gidan zuwa jibi In sha Allah mu tattauna da Iyah ɗin,zan sanar da ita komi tare da neman alfarman a bamu dama, ka fara neman TAIMIYYAH,idan har ta ji tana sonka shikenan sai komi ya zo cikin sauƙi,in kuma bata sonka sai mu haƙura don ba za a yi mata dole ba."


Hajjah tayi maganar idanunta akan Maleek, wanda ya sake tsuke fuska,gaba ɗaya zuciyarsa na ga TAIMIYYAH,tunda ya tashi yake jin babu abinda yake son ji da gani kamar muryarta, da son ganin waɗannan sparkle eyes ɗin nata, masu tsananin haske da birgewa.Ya narke murya sosai yana duban Hajjah da fuskar tausayi yake faɗin, "Please Hajjah ki daina cewa in bata so na,ni ko bata sona tunda ni naji ina ƙaunarta to hakanan za ta amsheni,ni zan koyar da ita yadda za ta ƙaunace ni,ni dai kawai Hajjah ki je gobe ba sai jibi ba, sannan ki ɗan kira ta yanzu inji muryarta please Hajjah, hakan

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login