Showing 171001 words to 174000 words out of 186776 words

Chapter 58 - TAIMIYAH Book Complete Document by Ayshat Dansabo Lemu .txt

15 Dec 2024

6606

akira TAIMIYYAH ne don ta haɗasu su duka ukun ta yi musu faɗa da nasiha duk gaba ɗaya,don ita ma Basmah an je kiranta ta zo a haɗasu ai musu faɗan tare.


Zuhurah ta zurawa TAIMIYYAH ido lokacin da suka samu waje suka zauna kusa da Iyah,wani irin kyau ta ga TAIMIYYAH ta yi mata irin wanda bata taɓa gani ba.


TAIMIYYAH ko hankalinta na kan Iyah da su Hajiya Rabi aminanta,ta ɗaga ido ta dubi Iyah ta ce, "Iyah gani Nusaiba ta ce in zo kina nema na."


Iyah ta dubi TAIMIYYAH da murmushi a samar fuskarta ta ce, "Eh! Zauna nan ku jira Basmah ta zo,faɗan bankwana za a haɗa ku ai muku. Kin yi kyau Zainabu na Ubangiji ya sanya alkhairy,ya baku zama lafiya a gidajen mazajenku."


Sauran mutanen da ke cikin ɗakin suka amsa da cewa "Ameen." Guggo Bilki da ke zaune daga can ƙarshen gadon Iyah ta ɗago kanta ta dubi TAIMIYYAH ta ce, "Zainab kin ko gaisa da su Yayanki Anas,sun shigo nan suna tambayar ina ki ke na ce su je can Sasan Ummie,sun je ɗin ko wucewarsu su ka yi?"


TAIMIYYAH ta girgiza kai ta ce, "Aiko dai wucewansu suka yi Guggo Bilki,don ko mai kama da su ban gani ba wallahi."


"To ai sun kyauta,sa dawo ganin gida wataran ai." Cewan Guggo Bilki daidai lokacin kuma Basmah suka shigo cikin ɗakin Iyah. Aka haɗu aka fara musu faɗa da nasiha akan muhimmancin haƙury a zaman aure,TAIMIYYAH tuni idanunta suka raina fata,zuciyarta ta karye ta fara kuka me motsa zuciya. Gaba ɗaya ji ta yi tamkar a ɗaga auren a ce anfasa sai zuwa gaba,amma ta san hakan ba mai yiwuwa bane,sosai Iyah da su Guggo Bilki su kai musu nasihu masu ratsa jikin duk wani me hankali da nutsuwa. Basmah kaɗai ce zan iya cewa bata girgiza ba amma hatta Zuhurah sai da jikinta ya sake yin sanyi,zuciyarta ta karye ta cigaba da jin lamari me girma na dabaibaye zuciyarta.


Yasmeen ce ta riƙo TAIMIYYAH zuwa jikinta tana rarrashi,sabida yadda ta ke kuka me asalin motsa zuciya,kwalliyar fuskarta tuni har ya fara ɓaci.


Zuhurah ta isa gaban Iyah bayan an kammala yi musu nasihan,cikin muryar kuka ta ce da Iyah, "Iyah ki yafe min duk laifin da na taɓa yi miki don Allah."


Iyah ta dafe kanta ta ce, "Na yafe miki Zuhurah,Allah ya sanya albarka ya baku zama lafiya,ki kula sosai ki aje duk wasu huɗuba da akai miki na banza,ki kama Allah kaɗai tare da yin biyayyar aure kamar yadda addini ya shinfiɗa,Allah ya kai ku lafiya yasa ki shiga a sa a."


Daga haka aka janye Zuhurah daga gaban Iyah za a fita da ita,amma sai ta zame hannunta ta isa wajen da Yasmeen ke zaune tare da TAIMIYYAH da ke faman kuka har lokacin. Zuhurah ta tsugunna tare da kamo hannun TAIMIYYAH ta riƙe,cikin muryar kuka ta ce, "TAIMIYYAH za a tafi dani,ina roƙon ki yafe min duk wani abu da na taɓa yi miki mara kyau,sannan ina mana fatan alkhairy baki ɗayan mu."


TAIMIYYAH jin muryar Zuhurah daf da ita yasa ta buɗe idanunta da suka fara rinewa ta ɗaura akan fuskar Zuhurah,ganin yadda hawaye ke gudu akan fuskar Zuhurah da yadda ta yi laushi kamar ba ita ba,sai kawai TAIMIYYAH ta rungumeta tana magana cikin muryar kuka ta ce, "Zuhurah in ma kin ɓata min wallahi na yafe miki,ban taɓa riƙe ku a raina ba dama. Allah ya kai ku lafiya ya baki zama lafiya Ameen."


Daga haka suka saki juna kowanne a cikinsu na jin wani irin lamari me girma a cikin zuciyarsa,kowa a ɗakin sai da ya share hawayen tausayinsu.


Guggo Bilki ce ta ce da Yasmeen ta kama hannun TAIMIYYAH su koma Sasan Ummie, a gyara mata kwalliyar da ya ɓaci tunda su sai zuwa yamma za a kai su ɗakunansu ita da Basmah. Yasmeen ta miƙe tana riƙe da hannun TAIMIYYAH na dama,ita kuma TAIMIYYAH na dafe da guiwar ƙafarta da hannun hagu,suka fara takawa suna ratsowa cikin falon Iyah har suka fito daga cikin Sasan baki ɗaya.


Wayar TAIMIYYAH ne ya shiga ringing a hannun a Yasmeen,hakan yasa ta dakata da tafiyar ta dubi fuskar wayar don ganin me kiran. Idanunta ya sauka akan sunan My Maleek kamar yadda TAIMIYYAH ta yi saving.Ta saki murmushi tana maida dubanta kan TAIMIYYAH wacce ke ta faman sauke ajiyar zuciya,ta yi mata signa da ido tana nuna mata fuskar wayar ta ce, "Babyn Maleek don Allah ki bar kukan nan haka,kin ga Angonki ne ke kiran ki ungo wayar ki amsa call ɗin."


Yasmeen ta yi maganar tana miƙawa TAIMIYYAH wayarta da har lokacin ya ke kukan neman ɗauki, TAIMIYYAH ta amsa wayar tana danna receive ta kai kunni. Muryar Maleek ya shiga kunnuwanta lokacin da ya ce, "Wife gani na iso ina waje,za ki ga wata black ɗin mota daga gaban gidan kaɗan."


TAIMIYYAH ta jinjina kai kamar yana gabanta,sannan ta yi magana cikin sanyin murya sosai ta ce, "Okey gani nan zuwa In sha Allah." Daga haka ta yi cuting call ɗin tana maida idanunta akan Yasmeen ta ce, "Yasmeen wai ya zo ne yana waje,mu je a gyara fuskar sai ki rakani don ba zan iya zuwa ni kaɗai ba."


Yasmeen ta saki murmushi cike da tsokana ta ce, "Wow! Ki ce Ango ya zo ganawa da Amaryarsa, amma shi ne ya ƙi yadda ya zo a ɗauki pics bayan ɗaura aure, gaskiya wannan Angon na ki ajinsa har ya ɓaci,oya mu je a gyara wannan fuskar ta ki da kika jiƙe da hawayen gulma."


TAIMIYYAH ta wurgawa Yasmeen harara,hawaye suka sake zubo mata cike da shagwaɓa ta ce, "Yasmeen ni ce ke hawayen gulmar ma? Oya mu je kawai kafin ki sake sani a damuwa."


Daga haka suka jera da juna zuwa Sasan Ummie,bayan an gyarawa TAIMIYYAH fuskarta ne ta samu babban mayafi ta naɗe jikinta da shi. Duk yadda ta motsa wani fitinannan ƙamshine ke ratsa ko'ina a jikinta,ta zurah flat shoe a ƙafarta tana duban Yasmeen da fuskar shagwaɓa ta ce, "Yasmeen mu je please kin ga yana sake kira."


TAIMIYYAH ta yi maganar lokacin da kiran Maleek Ado ke sake shigowa wayarta,hakan yasa Yasmeen ɗaukar wayarta suka fito don yiwa TAIMIYYAH rakiya zuwa wajen Maleek Ado.


Sun fito harabar compound ɗin dai dai lokacin da ake fitowa da Zuhurah daga Sasan su, za a shiga mota don zuwa Kano su hau jirgi su wuce Bauchi,waɗanda za su bi mota irin su Anty Laurat su sun wuce tun ɗaxu.


"Yasmeen shikenan Zuhurah za a wuce,ba ki ji yadda jikina ke sake yin sanyi ba,ina jin tausayinmu mu duka don bamu san wace irin rayuwa za mu je mu taras a gidan auren ba,wallahi ji na ke yi tamkar a fasa auren a bar ni tare da Iyah ta."


Yasmeen ta saki dariya ta ce, "To sannunki sarkin wauta,don Allah ni mu je in kai ki in yi dawowata cikin gida,ni fa wallahi duk wannan kukan da wani roƙon yafiyar da Zuhurah ta dinga yi,sam bata bani tausayi ba don baka saurin sallamawa maƙiyinka,watakili wani salon munafurcin ne kawai aka shirya mata,ita ƙaramar mara kunyar baki ga ko gezau bata yi ba? Wallahi ina tausayin Basmah don rawar kan yarinyar da fitsaranta ya yi yawa,amma In sha Allah xa a gyare mata zama tsaf,ta dai shiga gidan za ta gane Allah ɗaya ne."


Yasmeen tana maganar ne suna takawa a hankali don fita daga gate ɗin gidan,ita dai TAIMIYYAH jin Yasmeen kawai ta ke yi bata iya cewa komi ba,don bata san ma me za ta ce ɗin ba,amma har cikin zuciyarta ta ji tausayin Zuhurah,domin ita tana son su a ranta don gani ta ke yi bata da tamkar su,tunda su ne dai za ta nuna a ko'ina a matsayin ƴan uwanta na jini da iyayensu suka fito ciki guda.


Lokacin da suka ƙarisa fitowa wajen gate ɗin ne, TAIMIYYAH ta shiga wurga ido don gano inda Maleek ya parker motarsa. Idanunta ya hango mata wata danƙareriyar baƙar mota daga gaban gidan kaɗan,kamar yadda ya kwatanta mata,sai ta dubi Yasmeen ta ce, "Yasmeen ina ga waccar motar ce ya ke nufi,don ya ce daga gaban gidannan kaɗan ya yi parking."


Yasmeen ta jinjina kai suna cigaba da takawa zuwa wajen motar. Maleek da tun da suka doso ya ke ƙare musu kallo ta cikin madubin motar,sai ya samu kansa da kasa ɗauke ido akan TAIMIYYAH,wacce tun daga nesa ya ke sake hango irin kyawun da ta yi,sai ya raina mayafin da ta sanyo domin irin Chantly ɗinnan ne me shara-shara. Ya ɗan lumshe idanunsa ya buɗe akansu lokacin da suka ƙariso bakin motar. TAIMIYYAH ta jingina jikinta da jikin motar,ta bar Yasmeen da ƙarisawa bakin driver seat ta yi knocking. Maleek ya sauke tint ɗin glass ɗin motar ya leƙo da kansa yana cewa, "Sis har kun iso? Ce wa wife ta zagayo front seat ta shigo please!"


Yasmeen ta jinjina kai tana komawa wajen da TAIMIYYAH ke tsaye daga baya ta ce, "Amarya Angonki na buƙatar ki ƙarisa daga front seat ki shiga."


TAIMIYYAH ta ɗan shagwaɓe fuska ta ce, "Okey mu je." Yasmeen ta balla mata harara ta ce, "Mu je ko ki je,kin dai ji Yarinya da rainin hankali,in je ina? Ni muna gaisawa yanzu zan juya idan kun gama kya kira ni in fito,idan kuma ya yo miki rakiya har gida kin ga an hutar dani."


Daga haka Yasmeen bata sake cewa komi ba, ta juya zuwa wajen Maleek suka gaisa ta yi masa fatan alkhairy ta juyo don komawa cikin gida, ta bar TAIMIYYAH na zagayawa za ta shiga front seat ɗin,in da har Maleek ya riga ya buɗe mata murfin motar.......✍🏻














#Ɗansabo ce#
[12/14, 10:14 PM] +234 703 769 7050: Littafin TAIMIYYAH paid book ne,ga duk wanda ta tsincesa a kowani irin group ne,kiji tsoran Allah karki karanta sai kin biya 500 naira only.


Za ku iya min magana ta wannan number ɗin 08167768704, ko kuma ku turo kuɗin ku kai tsaye ta wannan account ɗin 0504192664 aisha ibrahim dansabo GTbank.*


*Sai ku tura shaidan biyanku ta wannan line ɗin 08167768704.*


Masu turo credit za ku turo katin MTN na 500 ta wannan line ɗin 08167768704.




_Ina ƴan kasuwa masu buƙatar a tallata muku hajar ku? Maza ku garzayo da kuɗi ƙalilan a tallata muku kayan siyarwanku sai dai kawai ku ji ana kiran waya don buƙatan sayan kayan ku,ku tuntuɓeni ta layina kamar haka 08167768704._


*67*




A hankali TAIMIYYAH ta zura jikinta cikin motar tana me barin murfin motar a buɗe,ƙafarta ɗaya me lafiyan na daga waje sai ɗayar kawai ta aje daga cikin motar. Ta ɗaga manyan idanunta ta dubi fuskar Maleek Ado,wanda ke binta da wani irin mayataccen kallo kai ka ce bai taɓa ganinta bane sai a yau ɗin. TAIMIYYAH sai ta sake narke fuska cike da shagwaɓa ta fara gaida shi,memakon ya amsa gaisuwar sai cewa ya yi, "Wife ki shigo sosai ki rufe min murfin motar,magana kawai za mu yi in wuce ba wai cinyeki na zo yi ba."


Yadda ya ke maganar murya can ƙasa da yadda ya miskile fuska,ya sanya TAIMIYYAH bin umurninsa ta maido ƙafarta ɗaya cikin motar tare da rufo ƙofar motar baki ɗaya. Zuciyarta sai faman bugu ta ke yi tana jin ta very uncomfortable ,sabida irin kallon da Maleek ya tsareta da shi.Ta kai dubanta garesa sau ɗaya tana saurin yin ƙasa da kanta,ta fara wasa da yatsun hannunta da suka sha jan lalli da ya yi wani irin maroon. Kamar a mafarki ta ji hannuwan Maleek Ado akan jikinta,hakan yasa ta yi saurin ɗago manyan idanunta ta sauke akan fuskarsa,lokacin da ya ke warware gyalen da ta yane jikinta da shi ya sauke shi zuwa ƙasa.


Jikinta TAIMIYYAH sai ya ɗauki rawa,zuciyarta na wani irin harbawa da matsanancin fargaba,cikin rawar murya cike da shagwaɓa ta ce, "Yah Maleek a waje fa mu ke,don Allah ka bari kada wasu su zo wucewa su gan mu please!"


Yadda TAIMIYYAH ta yi maganar tamkar za ta rushe masa da kuka, ba ƙaramin motsa zuciyar Maleek Ado ya yi ba. Ya sake kafa mata mayun idanunsa yana cewa, "Wife ai babu me ganin mu,dukkanin gilasan motar tint ne ai so u have to be comfortable kina tare da mijinki ne yanxu ba wai saurayi ba okey."


TAIMIYYAH sai ta zura masa ido tana sake ɓata fuska,ƙirjinta har lokacin harbawa ya ke yi da wani irin tsoro me tsanani, ga ƙamshin turarensa da sanyin AC ɗin da ya gama buɗe motar,na sake haifar mata da wani irin yanayi mara misaltuwa. Ba ta iya cewa komi ba illah yin ƙasa da kanta da ta yi,tana ji tamkar ta sakin masa kuka ko zai ɗauke idanunsa daga mayen kallon da ya ke bin jikinta da shi.


"Wife kin yi kyau sosai,irin kyawun da ban taɓa gani akan ko wace mace ba,na gode Allah da ya mallaka min ke amatsayin halalina,ɗago ki kalle ni babe please cox ina son ganin waɗannan idanun cikin nawa."


Maleek Ado ya yi maganar da wani irin salon murya,da ya sanya TAIMIYYAH saurin ɗaga manyan idanunta ta sauke akan fuskarsa,cikin sa a idanunta suka shige cikin na Maleek ɗin. Ta ke sai wani irin maganaɗisu ya yi aikinsa zukatansu suka buga a lokaci guda,kamar yadda kowannensu wani abu ya tsirga masa tun daga yatsun ƙafarsu zuwa zuciya da gangar jikinsu baki ɗaya.


TAIMIYYAH za ta ɗauke fuskarta daga dubansa,amma sai Maleek ya yi saurin miƙa hannu ya riƙo fuskarta a tafukan hannunsa,cikin wani irin kasalalliyar murya ya ce, "No wife please! Ki barni na morewa kallon waɗannan idanun masu tasiri akaina."


Sai TAIMIYYAH ta maida ƙwayar idanun ta lumshe su,wani irin abu na gudu a cikin jini da tsokar jikinta. Zuciyarta ta cigaba da harbawa da gudun gaske,kamar yadda wani abu ke zagaye jikinta tana jin wani yamm...! A ilahirin jikinta. Bata kuma shiga ruɗu ba sai lokacin da ta ji fuskar Maleek Ado akan tata fuskar,yana me haɗe fuskarsu waje guda,tare da ɗaura bakinsa akan nata goshinsu na mannuwa da juna. TAIMIYYAH bata san lokacin da bakinta ya suɓuce ya furta kalmar 'Hasbunallah!' jikinta ya cigaba da ɗaukar wani irin rawa. Shi ko Maleek Ado ko ajikinsa bai ma san tana yi ba,burinsa kawai ya bata kiss ya ji irin ɗanɗanon da ke kan harshenta.


Ya miƙa hannuwansa duka ya riƙo TAIMIYYAH zuwa jikinsa ya rungumeta,ta ke ta sakin masa kuka jikinta na cigaba da ɗaukar rawa,cikin rawar murya ta ce, "Please Yah Maleek don Allah ka yi haƙury!"


Maleek da maganarta ya bashi dariya sai ya sake mannata da jikinsa sosai,yana me raba fuskarsa da tata amma idanunsa na kan yadda TAIMIYYAH ta rintse nata idanun ya ce, "Baki min laifi ba wife, so ki daina bani haƙury kawai ina son jin ɗumin jikin matata ce,ki daina wannan rawar jikin baby babu abinda zan miki da ya wuce inyi kissing ɗinki,just kiss kawai kin ji babe?"


Yana maganar ne yana sake ƙoƙarin haɗe fuskarsu waje guda,TAIMIYYAH ta sakar masa kuka jinkinta na kuma ɗaukar rawa.Wannan shi ne karo na biyu da ta ji ta rungume a jikin namiji,tun bayan karon ta da Yah Deeku a wancan lokacin,amma yadda ta ke ji a yanzu bata ji irinsa a wancan lokacin ba sam. Maleek Ado ya ɗaura bakinsa akan nata yana aika mata da wasu zafafan kiss,so ya ke yi ya zura harshensa cikin bakinta amma ta datse ta hana shi daman hakan.Dukkanin jikinta rawa ya ke yi don lamari ne da bata kawo faruwarsa nan kusa haka ba,ta buɗe baki za ta yi magiya amma sai Maleek ya yi anfani da wannan daman wajen zura harshensa cikin bakinta. Wani abu ya doka a tsakar kan TAIMIYYAH lokacin da ta fara amsan wani irin hot kiss daga Maleek Ado,wanda ke tsotsar harshenta cikin zalama tamkar wanda ya cafki wata alawa me tsananin zaƙi. TAIMIYYAH ta dinga mutsu-mutsun son kwace jikinta amma ta kasa,don wani irin runguma ya yi mata yadda ba za ta iya kwace jikinta ba. Ko kaɗan bai saurara mata ba sai da ya tsotsi bakinta son ransa,sannan ya zare harshensa daga bakinta yana duban yadda hawaye ke gudu akan kyakykyawar fuskar TAIMIYYAH. Wacce ta rintse idanunta tamau ta ƙi buɗewa sabida ba za ta iya kallon idanunsa ba, bayan ya gama mata wannan abun kunyar.


Maleek Ado sai ya saki wani killer smile yana sake jin tamkar ana rura masa wutar fitina akan TAIMIYYAH ne, ya miƙa hannunsa ya fara share mata hawayen da ke sakkowa daga idanunta. Cikin muryarsa da ya sauya sosai ya ce, "Sorry wife na gama,ba zan sake miki komi ba sai zuwa anjima idan an kai min ke ko? So please its okey kukan ya isa haka wife."


Memakon TAIMIYYAH ta nutsu ta yi shiru sai ta sake sakin masa kuka,da ƙyar ya rarrashi abarsa ta yi shiru tana faman sauke a jiyar zuciya,duk ta wani firgice masa sabida gaba ɗaya lamarinsa ya gigita tunaninta. Da ƙyar ya barta ta kira Yasmeen don yi mata rakiya su koma cikin gidan,bayan ya gama susuta tunaninta da wasu irin lamura masu nauyi. Lamuran da suka sanya kanta ya so buga mata,don kuwa a bazata ta ji hannunwansa a kan ƙirjinta,cikin muhallin da tuntuni ya ke da burin jin hannuwansa a wajen,sabida tun suna waya a ɗazu suka tsone idanunsa. Lokacin da Yasmeen ta iso wajen motar,har Maleek ya gama gyarawa TAIMIYYAH lulluɓinta, yana ta mitan cewa gyalen ya yi shara-shara da yawa, ba za ta sake sanya irin su ba. Yasmeen ta yi knocking ɓangaren da TAIMIYYAH ta ke domin su san ta iso,tunda glass ɗin tint ne ita bata ganinsu sai dai su suna ganinta,shiyasa ta yi knocking don ta san cewa ba lallai ne hankulansu na kan duban tahowarta ba. TAIMIYYAH ta ɗaga manyan idanunta ta dubi Maleek,wanda ya tsare ta da mayun idanunsa yana ji tamkar ya gudu da ita zuwa gidansa, tun kafin a kai masa ita ɗin zuwa anjima. Cikin murya me cike da zallar shagwaɓa ta ce, "Ta iso Yah Maleek."


Maleek ya cigaba da zura mata ido ba tare da ya yi ko motsi ba,bare ta sanya rai cewa zai yi unlocking motar. Hakan yasa TAIMIYYAH kwaɓe fuska tamkar za ta sanya masa kuka ta ce, "Please Yah Maleek ka buɗe min in fita,ga Yasmeen nan tsaye tana jira kar ta

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login