Showing 153001 words to 156000 words out of 186776 words
Chapter 52 - TAIMIYAH Book Complete Document by Ayshat Dansabo Lemu .txt
amsa na matarsa,kuma duk abu iri ɗaya take ji yana tasowa ya danne zuciyarta,ita kuma bata san ko minene ba. Tayi baya a hankali ta gyara kwanciyarta tana me lumshe idanunta,abinda da take ji na sake danne zuciyarta, tana ji sam ba ta so ya yanke wayar ba,duk da cewa ita bakomi take cewa ba,da ya wuce umm! ko a'a, ganin ranta na cigaba da shiga ƙunci ya sanya ta sake janyo wayarta, ta kunna data ta hau oline. Ganin Yasmeen a online yasa ta ji relief! Suka ɗan fara chart Yasmeen na tambayarta labarin Maleek,sabida TAIMIYYAH ta bata labarin duk halin da ake ciki. TAIMIYYAH sai ta wani ɓata fuska tamkar Yasmeen na gabanta,kafin ta danna wajen tura voice note tana faɗin, "Yana can suna soyayya da matarsa mana,muna fa cikin waya ta kira shi,shi kuma jikinsa na rawa ya yi cuting call ɗin da muke yi, yana ce min wai zai ɗaga call ɗin wife ɗinsa,wallahi haushi na ji sosai a raina, ba ki ji yadda zuciyata ke zafi ba Yasmeen,gaskiya soyayyah da me mata sai a slow."
Ta tura voice note ɗin zuwa ga Yasmeen, tana cigaba da zumbure baki,ranta duk babu daɗi. Yasmeen bayan ta gama jin voice note ɗin, sai ita ma ta aikowa TAIMIYYAH nata voice note ɗin tana cewa, "Eh! Lallai su Baby an fara zurmawa a son wannan Maleek ɗin, tunda gashi tun ba a je ko'ina ba,har kin fara jin kishi akan matarsa,to ni dai babu ruwana don Allah ki ko yi riƙe kanki,kar ki bari ya gane kin fara kishi da matarsa nan kurkusa."
TAIMIYYAH ta wani ɓata fuska lokacin da ta gama jin abinda Yasmeen tace,kafin ta sake aika mata da wani voice note ɗin in da take cewa, "Ni fa ban son sharri Yasmeen, babu wani kishinsa da na ke yi,kawai don na ji haushi matarsa ta kira muna cikin waya, sai ki ce wani son sa na fara ina kishinsa,ke fa ba a abin kirki da ke dama."
Yasmeen na gama ji abinda TAIMIYYAH ta ce,sai ta aikowa TAIMIYYAH da sticker na dariya,kafin ta aiko mata da reply tana cewa, "Sorry babyn Maleek,abar zancen na ga alamu a sama ki ke,yanzu dai muyi magana akan Abayarnan dana turo miki, ta yi in siya ko a turo wasu ki zaɓa?"
TAIMIYYAH ta baiwa Yasmeen amsa suka cigaba da magana ta chart,har sai wajen goma saura sannan TAIMIYYAH ta kashe data ta kwanta,sabida baccin da ya fara damun idanunta.
Kwanaki biyu bayan maganar Iyah da Baba Sani,game da bincike akan Maleek Ado. Alhaji Buhary ya zo har gida ya yiwa Iyah gamsasshen bayani, akan asalin waye Alhaji Ado mahaifin Maleek,tare da zayyane mata kyawawan halayyar marigayin, wanda kuma an yi ittifaƙin Maleek ya gaji dukkanin kyawawan halayyar mahaifin nasa ne.
Iyah ba ƙaramin farin ciki tayi da samun labari me daɗi, dangane da ahalin Hajiya Aysha ba,su kai sallama da Alhaji Buhary bayan tayi masa godia me tarin yawa,shi kuma ya sake ɗaukar mata alqawarin cewa zai cigaba da binciken Maleek ɗin, idan har ya ji wani hali mare kyau a tattare da shi zai sanar mata,amma a yanzu kada su taɓa bari ya suɓuce musu, don samun mutane masu karamci da halin dattako kamar Hajiya Aysha da tilon ɗanta,abu ne me wahala don irin su sun yi ƙaranci a wannan zamanin, musamman idan aka yi la'akari da ɗimbin dukiyar da suka tara, amma bai sa sun ɗaukaki kansu ba,sai ma ƙarin tausayi da taimakon talaka,da suka ɗaura daga inda Alhaji Ado ya tsaya.
Bayan tafiyar Alhaji Buhary,Iyah ta samu TAIMIYYAH tana sanar da ita yadda suka yi da Alhaji Buharyn,ita dai TAIMIYYAH bata iya cewa komi ba,amma can ƙasar zuciyarta ta ji ta sake samun nutsuwar zuciya akan Maleek Ado,wanda ba za ta iya tantance asalin feeling ɗin da take ji akansa ba.
Ranar Friday Iyah ta shirya ta je gidan Hajiya Aysha,wacce ita ce da kanta ta turo Shehu driver ya ɗauki Iyah.TAIMIYYAH babu yadda Iyah bata yi akan ta shirya su je tare ba amma TAIMIYYAH ta ƙi, ta ce wa Iyah ita kunyar Hajiyar take ji sosai a yanzu,ta dai yi Snacks me yawa ta ce akai wa Hajjah, kamar yadda Iyah ta buƙata.
Bayan fitar Iyah sai TAIMIYYAH ta tattara ta nufi sasan Ummie,suka sha hiransu sai lokacin da Iyah ta dawo sannan ta koma Part ɗin Iyah. Iyah ta zauna tana bai wa TAIMIYYAH labarin irin tarba na karamci, da karramawa da Hajiya Aysha ta yi mata. Tana sanar da ita cewa Hajiyar tace a gaida ta sosai,kuma za ta aiko a ɗaukar mata ita har gida,ta je ta yi mata yini,don ita a ƴa take ɗaukarta Maleek ba zai shiga tsakaninsu ya mai da ita suruka ba. TAIMIYYAH dai blushing tai ta yi tana jin tarin ƙaunar matar na sake ratsa ta,sabida ta sanya a ranta bayan Iyah da su Guggo Bilki,bata taɓa samun mutanen da suka nuna mata ƙauna irin Hajiya Aysha ba. Don haka matar na da wani irin ƙima da mutunci a idanunta, koda a ce bata shigo da maganar ɗan ta ya zo ya nemi aurenta ba.
Ranar Saturday Hajiya Aysha ta bugowa Iyah waya ta sanar da ita cewa,Yayan Mahaifin Maleek tare da wani Aminin Mahaifinsa Alhaji Aliyu,za su zo nemawa Maleek izinin fara zuwa zance wajen TAIMIYYAH. Iyah ta ɗaga waya ta sanar da Baba Sani don yana gari ya zo weekend,ta kuma shaida masa cewa ya sauke su a can Rimi ne, Fam house ɗin su don bata son su zo nan gidan su samesa. Baba Sani ya amsawa Iyah tare da bata tabbacin za a yi yadda take so ɗin.
___________
*Asokoro, Abuja.*
Suhailah ce zaune a falon su na ƙasa tare da Jawahir, makwaficiyarsu da suka ƙulla ƙawance da ita a yanzu,don kusan kullum sai ta shigo gidan Suhailah, sabida mijinta Captain Aliyu ba mazauni bane.
Jawahir ta dubi Suhailah tana cewa, "Matar Maleek anya ba ciki ne gare ki ba? Don na ga sai sake ɗashewa ki ke yi fa."
Suhailah ta saki murmushi lokacin da take aje cup ɗin da riƙe a hannunta,ta dubi Jawahir tana cewa, "Tabɗi! Wani ciki Jawahir bayan yanzu haka period na ke yi,kawai zazzaɓin da nayi ya doke ni shiyasa duk na ɗashe haka,ai ni matsalata babbane Jawahir don ina ma kan shan magunguna ne,ban sani ba ko kafin in gama sha Allah zai dube ni,ya bani lafiyar da zan iya ɗaukar cikin....."
A hankali Suhailah ta kwashe halin da take ciki ta zayyanewa Jawahir ɗin,Jawahir da ta sake baki tana duban Suhailah with shock! Ta yi saurin furta,
"Gaskiya Suhailah kin tafka wauta me yawa,amma In sha Allah za ki samu lafiya,maganar ƙarin aure ki ma daina damun kanki don tsokanarki kawai ya ke yi,so ya ke yi kawai ya ruɗa miki ciki sabida kin baƙanta zuciyarsa akan abinda ki ka aikata ɗin."
Suhailah ta jinjina kai tana duban Jawahir ta ce, "Hmm! Bana jin Maleek wasa ya ke yi Jawahir, don kuwa baya furta abinda ba haka ya ke a zuciyarsa ba,sannan Hajjah ta riga ta furta za ta iya goya masa baya,don daga ita har shi ba su da burin da ya wuce in haihu, sabida shi kaɗai ta mallaka tana da buƙatar ganin shi ya hayayyafa,ina jin tsoran randa hakan zai tabbata ace Maleek ya sake auren wata mace, sabida ina da tsananin kishi akansa me zafi."
Suhailah tayi maganar tana jin wani abu na matse zuciyarta,Jawahir ta jinjina kai tana duban Suhailah cikin ido ta ke cewa, "Suhailah ki kwantar da hankalinki na gama lura ke ɗin kina da ɗan duhun kai,ai yanzu mace sai ta so zama da kishiya in baki labari,idan baki so ba ko ta shigo za ki iya korata, ba tare da kowa yasan halin da ki ke ciki ba,kada ki bari kishin mijin ya dameki musamman ke da kuke da wuta a hannunku,tsayawa kawai za ki yi ki ga cewa kin samarwa kanki ƴan ci ta ƙarƙashin ƙasa....."
Jawahir ganin irin kallo na rashin fahimta da Suhailah ke jifanta da shi,ya sanya ta yin shiru bata ƙarisa maganar da ta faro ba,ta saki murmushi tana cewa, "Sorry ƙawata na ɗan saki layi ko? Kar ki damu in dai muna tare soon za ki gane karatun da nake so ki gane,yanzu kina buƙatar a biki a sannu ne don na ga kina da ƙarancin buɗewan ido, irin na ƴantattun matan zamani da suka san kansu."
Suhailah da kanta ke sake kullewa da maganganun da Jawahir ke yi,ta ɓata fuska tana cewa, "Jawahir ni fa a duhu kawai ki ke saka ni, don sam ban fahimci inda ki ka dosa ba."
"Zaki fahimta soon Mrs.Maleek Ado."
Cewar Jawahir tana sakin wani irin dariya na shaƙiyanci,don kana ganinta a kallo ɗaya kawai za ka fahimci irin matannan ne masu buɗewan ido. Haifaffiyar garin Jos ce daga can Captain Aliyu ya auro ta,sun cigaba da hira da Suhailah har sai da time ɗin ɗakko yaronta a skull ya yi, sannan ta yi sallama da Suhailah ta bar gidan.
Suhailah ta daɗe tana jujjuyawa kalaman Jawahir a cikin zuciyarta,amma ta kasa gane inda ta dosa,ganin za ta damu kanta da tunani yasa ta watsar da zancen, ta cigaba da sabgarta,daga ƙarshe layin Maleek ta nema amma sai ta ji duka wayoyinsa a kashe su ke,kewansa ta ke ji me tsanani gashi ya sanar mata ba zai shigo Abuja ba sai next week Friday.
____________
*2 Weeks Later.*
*Zaria, 1:15pm.*
Tunda TAIMIYYAH ta yi waya da Maleek Ado ya sanar mata cewa ya shigo gari, ta ke jin wani irin baƙon yanayi na lulluɓe zuciyarta, don cikin sati biyu da suka wuce, idan ta ce Maleek bai kimsa ƙaunarsa a cikin zuciyarta ba ta yi ƙarya.
Yadda ta ke jinsa a zuciyarta a yanzu, ko lokacin da suke tare da Nass bata ji irin haka ba,don wani irin zazzafan feeling ta ke ji akan Maleek Ado, irin wanda bata taɓa hasashen za ta ji akan wani ɗa namiji ba.
Ta kan alaƙanta hakan da cewa tarin kwarjininsa da ya yi yawa ne, ke sake haifar mata da jin yanayi me zafi akansa irin haka, don hatta da Iyah ta gama gane cewa TAIMIYYAH ta kamu da soyayyar Maleek Ado. Dojewa kawai TAIMIYYAH ta ke yi a gabanta, tana nuna tamkar bata jin ko wani irin feeling a kansa.
TAIMIYYAH ta ɗaga manyan idanunta ta sauke akan a gogon ɗakinta,tana ƙimanta ragowar lokacin da ta ke da shi kafin isowar sa gidan,don ya tabbatar mata da cewa ba zai iya kwana a garin, ba tare da ya zo gareta komin dare ba kuwa.
Ta yi hanzarin tashi tana ji duk jikinta ya saki,zuciyarta ya yi wani irin laushi da ɗokin son ganin miskilalliyar face ɗinsa a zahiri, a karo na biyu tun bayan zuwansa na farko,wanda lokacin ba ta samu halin yi masa cikakkiyar kallo ba.
Kitchen ta nufa kai tsaye lokacin da ta fito, tana ayyana irin abinda za ta shirya masa, wanda zai ci idan ya zo,duk da cewa bata da cikakkiyar tabbacin zai ci wani abu, ko ba zai cin ba. Tunaninta ya tsaya ne akan ta dafa masa mince meat jallof rice da haɗin chicken breast Salad.........✍🏻
#Ɗansabo ce#
[12/14, 10:13 PM] +234 703 769 7050: Littafin TAIMIYYAH paid book ne,ga duk wanda ta tsincesa a kowani irin group ne,kiji tsoran Allah karki karanta sai kin biya 500 naira only.
Za ku iya min magana ta wannan number ɗin 08167768704, ko kuma ku turo kuɗin ku kai tsaye ta wannan account ɗin 0504192664 aisha ibrahim dansabo GTbank.*
*Sai ku tura shaidan biyanku ta wannan line ɗin 08167768704.*
Masu turo credit za ku turo katin MTN na 500 ta wannan line ɗin 08167768704.
_Ina ƴan kasuwa masu buƙatar a tallata muku hajar ku? Maza ku garzayo da kuɗi ƙalilan a tallata muku kayan siyarwanku sai dai kawai ku ji ana kiran waya don buƙatan sayan kayan ku,ku tuntuɓeni ta layina kamar haka 08167768704._
*62*
TAIMIYYAH bata ɗauki awa biyu ba ta kammala komi, aka nufi sasan Ummie da shi aka shirya cikin falon Abie.
Wanka ta sake yi sabida gajiyar aikin da ta sha, lokacin da ta fito daga wankan ta jima a tsaye wajen kayanta, tana nazarin kayan da za ta saka,daga ƙarshe sai ta yanke shawaran saka sabuwar Abayar da ta siya bata taɓa anfani da shi ba.
Kalar Abayar dark gray ne da akaiwa ado da blue black and golden colour,ya yi matuƙar yi wa TAIMIYYAH kyau kamar ka sace ta ka gudu.
Bata yi kwalliya a fuskarta ba illah powder da ta shafa, sai ta yi lining idanunta da eye liner,ta ɗauki man leɓe mai ɗan maiƙo ta shafa a pink lips ɗinta. Nan da nan fuskarta ya sake yin kyau, manyan idanunta masu wani irin haske suka sake girma, ƙwayar idanun na ta sai sparkling su ke yi. Ta ɗauki turarenta na GIOGIOR PINK me sanyin qamshi ta fesa ajikinta, bayan ta yi anfani da body mist na Sugar Girl daga ciki.
Bayan ta kammala shiryawan,komawa ta yi ta zauna daga bakin bed tana kallon lokaci yadda ya ja,don har biyar ta wuce ga hadari da ke haɗuwa a garin kaɗan-kaɗan.
Wayarta ta janyo tana kunna data ta hau online, don cigaba da karanta novel ɗin da take bibiya,me suna Baƙar Inuwa na Billyn Abdul. Soyayyar Raudha da Mr. President na matuƙar birgeta, tana hango tamkar itace da Maleek Ado. Shigowar kiran Maleek cikin wayarta yasa ta dakatawa da karatun, tayi receiving call ɗin ta kai kunni,muryar Maleek me cike da ƙasaita ya shiga kunnuwanta, lokacin da ya ke sanar da ita isowar sa.
Ta shagwaɓe murya tana cewa, "Okey! Ka shigo daga ciki part ɗin da ka sauka wancan lokacin, gani nan fitowa."
Ta ɗanyi jim! Kafin ta saki ƙaramin murmushi, tana sake narke masa murya ta ce, "Alright za ta ji In sha Allah."
Daga haka ta kashe wayar tana miƙewa ta taka zuwa wajen madubi, don yin rolling gyalen Abayar a kanta,wani irin kyau ta ga tayi lokacin da ta kammala naɗe fuskarta da gyalen Abayar. Ta saki wide smile tana sake duban yadda Abayar ta yi kyau a jikinta,sai ta koma ta ɗauki wayarta daga kan bed ta nufi ƙofar fitowa falo.
"Iyah ya iso na ce ya ƙarisa can Part ɗin Ummie,ya ce in gaidaki zai shigo ku gaisa idan zai wuce."
TAIMIYYAH ta yi maganar kanta a ƙasa don kunyar haɗa ido da Iyah ta ke yi,Iyah ta saki murmushi kunyar TAIMIYYAH na sake birgeta ta dubi TAIMIYYAR ta ce, "To madallah ya yi kyau ki ce ina amsawa ƙwarai. Ki shigar da shi ya gaida har Samhar idan zai tafi."
TAIMIYYAH ta amsa da cewa, "Tuh Iyah." Daga haka ta dafe guiwar ƙafarta ta fara takawa don ficewa daga falon Iyah baki ɗaya.
Cikin nutsuwa ta ke tafiya zuciyarta cike da wani irin feeling da ba za ta iya fassarawa ba,har ta isa sasan Ummie ta nufi hanyar da zai kai ta ƙofar falon Abie ta waje, tana sake jin zuciyarta na wani irin dokawa. Lokacin da ta isa ƙofar shiga falon sai da tayi ɗan jim! Bugun zuciyarta na sake ƙaruwa,daga ƙarshe ta yi ƙarfin halin buɗe baki ta yi sallama,cikin muryar ta da ya sake yin sanyi sosai.
A.Maleek da ke kame daga cikin falon,ya na ji duk ya ƙosa ya yi tozali da kyakykyawar fuskar TAIMIYYAR. Ya buɗe baki ya amsa mata sallamar, yana sake kafe ƙofar shigowa cikin falon da ido.
TAIMIYYAH ta kai hannu ta ɗage labulen falon, tare da sanyo kanta ciki.Hancinta ya fara shaƙo mata daddaɗan qamshin Turaren AMOUAGE da ya cika ɗakin baki ɗaya,ta cigaba da takowa zuwa ciki tana jin tasirin idanunsa akanta. Hakan ya sake sawa ta yi ƙasa da kanta tana isa wajen kujeran one seater ta yi masauki a kai,sai kuma lokacin ta ɗaga manyan idanunta ta kalli direction ɗin da, Maleek ya harɗe yana me zubo mata ido babu ko ƙiftawa.
"Barka da zuwa dafatan ka iso lafiya,ya Hajjah ina fata ka same su lafiya?"
Sassayar muryar TAIMIYYAH ta ratsa kunnuwan Maleek Ado, wanda ya kasa ɗauke idanunsa daga kanta,wani irin kyawunta ya ke gani irin wanda sam a wancan lokacin, bai kula da hakan ba.Shigar Abayar ta tafi da zuciyarsa baki ɗaya, tare da haifar masa da jin wani irin zazzafar feeling irin wanda bai taɓa ji ba,ya sake ƙureta da ido lokacin da yake amsata da cewa, "Lafiya lau wife,Hajjah tana gaida ki ta ce ki kula da ni da kyau ."
Yadda ya yi maganar cikin wani salo,yasa TAIMIYYAH saurin ɗaga manyan idanunta ta sauke a kansa,sai kuma lokacin ta ga shigar da ke jikinsa. Yana sanye ne da shadda dark gray kalar Abayar jikinta, kalar ya yi masa kyau sosai. Kansa babu hula sai sumarsa me kyau da sheƙi, ke faman haskawa cikin hasken fararen fitullun da suka haske falon ƙau!
Ta yi saurin janye idanunta daga dubansa, lokacin da na shi idanun ke ƙoƙarin shigewa cikin na ta,ta cigaba da murza ƴan yatsun hannunta,tana jin ta very uncomfortable a cikin falon,sabida idanun Maleek masu cike da kwarjini,wanda suka hanata saƙat! Don har lokacin tana jin idanunsa akanta.
"Zaynabb ina jin gaba ɗaya so ki ke ki sanya ni, in rasa duk wata nutsuwar zuciya da ta gangar jikina, idan har banyi gaggawar mallakarki nan kusa ba. Please ki ɗago ki kalleni,kar kice za ki haramta min ganin waɗannan idanun, da su ke da matuƙar tasiri a gare ni."
Maleek yana maganar ne idanunsa akan TAIMIYYAH, burinsa kawai ta ɗago waɗannan manyan idanun nata, masu kama da magic ta dubesa da su. TAIMIYYAH sai ta ɗan shagwaɓe fuska,tana ɗago kanta da tayi ƙasa da shi ta dubesa, cikin sa'a idanunta suka shige cikin na Maleek Ado, tamkar wacce aka sanya mayen ƙarfe aka ɗane idanun na ta a cikin na sa,sai ta kasa janye na ta idanun. Suka zubawa juna ido, dukkaninsu wani maganaɗisu na yawo cikin zuciya da gangar jikinsu.
Sun ɗauki tsayin mintuna biyu a haka, kafin TAIMIYYAH ta janye idanunta ta mayar ƙasa,zuciyarta na cigaba da doka mata, da wani irin yanayi me wuyar fassara. Shi ko Maleek baya ya yi da jikinsa ya jinginar a jikin kujerar 3 seater da ya ke kai, ya lumshe idanunsa baki ɗaya,yana jin yadda zuciyarsa ke doka masa da wani irin baƙon yanayi,wanda bai taɓa jin irinsa