Showing 168001 words to 171000 words out of 186776 words
Chapter 57 - TAIMIYAH Book Complete Document by Ayshat Dansabo Lemu .txt
Event Centre da suka kama,wanda rabin Ƴan rimi da dangin Umma ne suka halarta,sai dangin Nass da yake shi ɗan Zaria ne duk yayyinsa mata da qawayen Hajiya Hajara duk sun halarci wajen.
Ƙarfe goma na dare su Yasmeen suka watse daga shagalin Bridal shower ɗin.
Hotuna ne suka fara bazuwa a kafofin sadarwa na su Instagram da su Twitter zuwa manhajar Whatsapp,duk su Yasmeen su kai ta ɗaura hotunansu da na Amarya TAIMIYYAH.
Ranar Thursday aka tafi yin jeran ɗakin TAIMIYYAH dana Basmah,in da mutane suka rabu biyu wasu suka tafi na TAIMIYYAH a can GRA ,wasu kuma suka tafi Gonar Ganye na Basmah tunda anan Nass ya tamfatsa gininsa daidai ƙarfin arziƙinsa.
Lokacin da aka dawo daga yin jeran ne surutai suka fara tashi , aka dinga koɗa haɗuwar gidan TAIMIYYAH ana jinjina irin daular da za a kai ta ciki ranan Asabar. Nan fa hankalinsu Umma ya sake tashi da jin irin dukiyar da aka narka a gidan TAIMIYYAH,don an tabbatar musu da cewa babu abinda ba a zuba a gidan ba. Ɗakuna biyu kacal aka bari wanda aka jera kayan da Baba Sani ya yi musu ita da su Basmah, duk wanda ya kalli Umma da su Zuhurah sai ya gane halin da xukatansu ke ciki, na tsananin damuwa da hassada da ke cin zukatansu.
Ita TAIMIYYAH da mutanen arziƙinta ba su san ma ana yi ba,don harkokin gabansu kawai suke yi na arziƙi. Iyah duk wanda ya kalleta a ƴan kwanakin nan ya san tana cikin wani irin farin ciki da ba zai misaltu ba. Kamar yadda shi ma Ya sadeeq da ya iso tun Wednesday ke cikin farin cikin taya TAIMIYYAH murnar aurenta da za a ɗaura ranar Asabar ɗin,duk da cewa yana jin kishi me tsanani a ƙasan ransa,amma hakan bai hana shi jin farin ciki da irin mijin da TAIMIYYAH ta samu ba.
Daga can ɓangaren Hajjah ma gidanta ya fara sauke baki, ƴan uwanta na kusa ne suka iso daga Katsina, don taya ta murnan ƙarin auren da tilon ɗan ta Maleek Ado zai yi. Daga ɓangaren can babban gidansu Maleek Ado kuwa komawa gefe suka yi suna gulma da tsegumin cewa Amaryar ma ashe gurguwace. Ita dai Hajjah ko a jikinta daga ita har uban gayyar murna kawai suke yi da ɗokin jiran ranar da za a shafa Fatiha,TAIMIYYAH ta zama mallakin Maleek ɗin halak malak. Daga ɓangaren uwargida Suhailah kuwa tana cikin wani matsanancin hali na kishi,da zallar baƙin ciki da taraddadin ranan da ke sake kusantowa, wanda za a sake mallakawa mijinta wata mace a matsayin mata bayan ita. Maganganun Jawahir da irin huɗubobin da ta yi mata kafin isowansu Zaria kawai take bita a cikin ranta. Gefe guda kuma jakarta na ɗauke da wani sirri da Jawahir ɗin ta damƙa mata,wanda za ta aiwatar da ƙudirinsu da zaran an ɗaura auren Maleek ɗin da TAIMIYYAH. Hakan yasa tunda ta iso ta ke kaf-kaf da babbar jakar hannunta,ko kaɗan bata son yin nesa da shi a kusa da ita. Kullum zuciyarta sake shiga tashin hankali da ruɗu ta ke yi, musamman da kwanaki suka rage saura 3 days Maleek ɗinta ya zama mallakin wata macen. Macen ma gurguwa wacce ta ke ganin ƙarshen ƙasƙanci ne a wajenta, a ce Maleek ɗinta ya auro mata kishiya musaka,gurguwa alhali ya aje mace lafiyayya kamarta,wacce bata rasa komi ba sai haihuwa kaɗai da ta rasa. Wanda a yanzu ta ke jin zafin rashinsa tamkar ta ari hauka,don ta gama sallamawa cewa rashin haihuwar shi ne silar ƙarin auren Maleek ɗin. Ba wai ƙaddaransa bace kamar yadda su Hajjah ke mata daɗin baki,shiyasa ta fita a sabgar kowa tare da ɗaukar fishi me tsanani da Hajjah, da ma duk wani me goyan bayan auren Maleek ɗinta da gurguwar matarsa. Jira kawai ta ke yi ranar Asabar ta yi a ɗaura auren,ita kuma ta aiwatar da aikin da Jawahir ta bata,wanda ta salwantar da kuɗi masu nauyi kafin saƙon ya iso gare ta. (To ko wani irin saƙo ne wannan Suhailah ta taho da shi? Sai mu zuba ido don ganin me zai faru a ranar).
____________
Ranar Asabar sha shida ga watan Satumban dubu biyu da ashirin da biyu, (16th September 2022),da misalin ƙarfe sha ɗaya da rabi na safe (11:30am). Aka shaida ɗaurin auren ƴan matan guda uku,
Zainab TAIMIYYAH da Angonta Maleek Ibrahim Ado,sai Basmah da Angonta Naseer Aliyu Ƙwarbai, sai Amarya Zuhurah da Angonta Ameeru Muhammad Bauchi. An ɗaura Aurarrakin ne a can Family House ɗin su TAIMIYYAH da ke Rimi. A kan sadaki mabambamta in da dubban nin mutane ne suka halarci ɗaurin auren. Kama daga kan ƴan siyasa zuwa mayan gwamnati da masu faɗa ajin Nigeria,duk sun halarci ɗaurin auren. Rabin manya da attajiran sun halarci wajen ne sabida Maleek Ado,wanda kallo ɗaya za ka masa kasan cewa yana cikin farin ciki mara misaltuwa. Wannan miskilalliyar fuskar tasa na haskawa da wani annuri da fara'ar da mutane kan jima ba su ga irin ta akan fuskarsa ba........✍🏻
YADDA AKE BUƊE ACCOUNT A AREWABOOKS*
Bayan kaje play store ka ɗakko ya sauka a kan wayarka. Za'a cike Form ɗin kamar haka: -
*Enter your name:* (Cikakken sunanki)
*Enter your mail:* (Email ɗinki)
*Enter an username* (Sunanki)
*Enter your password:* ( misali 12341234)
*Confirm password:* (misali 12341234)
Sai a taɓa *Sign Up* shikenan an buɗe account a ArewaBooks💃🏻😂.
*Continue with Google* - Idan kana da gmail/email akan wayarka kawai Continue with Google za'a taɓa zata buɗe maka account a ArewaBooks kaitsaye.
*Register* - Shine cike form domin buɗe account a ArewaBooks.
Masu iPhone
Zaku iya bibiyar shafinmu
https://arewabooks.com.
#Ɗansabo ce#[12/14, 10:14 PM] +234 703 769 7050: Littafin TAIMIYYAH paid book ne,ga duk wanda ta tsincesa a kowani irin group ne,kiji tsoran Allah karki karanta sai kin biya 500 naira only.
Za ku iya min magana ta wannan number ɗin 08167768704, ko kuma ku turo kuɗin ku kai tsaye ta wannan account ɗin 0504192664 aisha ibrahim dansabo GTbank.*
*Sai ku tura shaidan biyanku ta wannan line ɗin 08167768704.*
Masu turo credit za ku turo katin MTN na 500 ta wannan line ɗin 08167768704.
_Ina ƴan kasuwa masu buƙatar a tallata muku hajar ku? Maza ku garzayo da kuɗi ƙalilan a tallata muku kayan siyarwanku sai dai kawai ku ji ana kiran waya don buƙatan sayan kayan ku,ku tuntuɓeni ta layina kamar haka 08167768704._
*66*
*Gyallesu.*
Daga can uwar ɗakin na ummie ne aka saki guɗar 'Ayyiriyirii...!!!' sai na cigaba da ratsa tsirarun mutanen da suke cikin falon, na isa zuwa cikin ɗakin baccin Ummien in da ƴan matan huɗu ke zaune daga bakin gado.
Amarya TAIMIYYAH na zaune akan stool me yi mata kwalliya ta ƙare ana yi mata ɗauri, an lanƙwasa karin ɗankwali na ƙarshe tare da kalmashe shi daga can ƙarshen ƙeyar kan TAIMIYYAH, Yasmeen ta sake dagewa ta saki wata guɗar 'Ayyiriyiriii...!!!' Zee ta saki dariya ta ce "Kai Yasmeen wannan uban guɗa da ki ke saki haka ai sai ki toshe kunnuwar Amaryar ta mu."
TAIMIYYAH wacce me kwalliya ta matsa daga gabanta fuskarta ya bayyana a sarari, su Zee suka saki baki suna kallon yadda ta koma wata Princess. Tana sanye ne cikin wani rantsatstsen farin lace,wanda akai wa ado da golden ɗin zare a jikinsa,ɗinkin straight gown akai mata irin na Amare. Aka kuma yi sa a The Cicada ce ta ɗinka rigar da kanta,shiyasa ɗinkin ya zauna ajikin TAIMIYYAH tamkar a jikin nata aka halicci rigar.Fuskarta da ya sha make-up irin na Amare wanda sam ba a cika ba,kuma ƙwararriyace ta yi sa shiyasa fuskar ke haskawa da wani irin sirrin kyau mara misaltuwa. Ɗan ƙaramin bakinta da ya sha jan baki kalar da ya dace da kwalliyar kan fuskarta,ya sake ya tsukewa ya zama so cute. Manyan idanunta ya fi komi birgewa sabida yadda suke wani irin haskawa da shining ɗin baƙin eye liner, da akai lining ɗinsu da shi.Ta yi kyau har fiye da yadda zan iya misaltawa me karatu,kamar yadda rigar jikin nata ya fiddo duk wani shape da Ubangiji ya yi mata baiwarsa. Ƙirjinta da ya sha gyara ya sake cika tamkar an hura Baloon ya tsaya cak abin sha'awa. Jikinta baki ɗaya na tashin daddaɗan ƙamshinta, da ya gama kama ko'ina a jikinta na tashi.
Dukkanin ƴan matan Amaryan sai kabbara suke yi,lokacin da idanunsu ya sauka akan Amarya TAIMIYYAH. Sabida yadda suka ga tayi musu mugun kyau,har suna kasa ɗauke idanunsu daga ƙare mata kallo,Maryam Sunusi ta buɗe baki ta ce, "Fatabarakallahu ahsanulkhaliqin! Allah kai ne abin kambamawa da ka ƙagi wannan kyakykyawar halitta. Allah ka albarkace ta tare da aurenta,ka bata zama lafiya da nutsuwa a cikin gidan aurenta. Ya Ubangiji ka kunyata maƙiyanta ka bata zuriya masu albarka,Congratulation my best friend ever, may urs be among the best In sha Allah TAIMIYYAH."
Su Yasmeen dukansu suka haɗa baki wajen amsa addu'ar da Maryam tayi da cewa, "Ameen ya Hayyu ya Qayyum."
TAIMIYYAH ta ɗaga manyan idanunta ta sauke akan Maryam Sunusi,cike da jin daɗin kyakykyawar addu'ar da Maryam ɗin ta yi mata ta ce, "Ameen Maryama na gode,ku ma Allah ya yi muku zaɓi mafi alkhairy nan kurkusa."
Suka sake amsawa da faɗin, "Ameen." Yasmeen ta matso kusa da TAIMIYYAH ta sake sakin ƙaramin guɗa tana cewa, "Finally yau kin xama Mrs.Maleek Ado."
TAIMIYYAH ta saki ƙayataccen murmushi,sai dai kafin ta yi magana wayarta da ke hannun Anty Laurat,wacce ke faman kashe mata hotuna ya ɗauki ringing. Ta ta so da sauri tana miƙawa TAIMIYYAH wayar ta ce, "Mrs.Maleek ungo Angon ne da kansa ke kira."
TAIMIYYAH ta amsa wayar zuciyarta na bugawa da wani irin yanayi da ba za ta iya fassarawa ba. Ta yi receving call ɗin tare da kai wayar bisa kunni,murya can ƙasa ta yi masa sallama. Maleek Ado daga ɓangarensa ya amsa sallamar sannan ya ce, "Mrs.Maleek Ado!"
TAIMIYYAH ta lumshe idanunta tana jin wani irin abu na malting a cikin zuciyarta,yadda ya furta kalmar ba ƙaramin tasiri ya yi a zuciyarta ba.Ta buɗe idanunta ta sauke akan su Yasmeen da ke faman hiransu babu tsagaitawa,sai ta miƙe a hankali ta dafe guiwar ƙafarta ta fara takawa don barin musu ɗakin. Suka bi ta da ido rii...! Kowacce murmushi na blushing a samar fuskarta,ita ko TAIMIYYAH direct ɗaya bedroom ɗin Ummie ta nufa,in da ta ke zaton ba za ta ga kowa ba don bama kasafai ta ke buɗe ɗakin ba.
Kamar yadda ta zatan kuwa haka ya kasance babu kowa cikin ɗakin,amma a gyare ya ke sai tashin qamshin daddaɗan turaran wuta ke tashi. TAIMIYYAH ta samu bakin gado ta zauna,tana sake dafe wayar akan kunninta ta ce, "Hello!" Maleek da ya yi shiru yana sauraren takun tafiyarta tun fitowarta daga ɗakin da suke,ya saki ƙaramin numfashi ya ce, "Wife ina jin ki,kin gudu ma qawayen na ki ne sabida ke ma kina son ganin fuskar Angon ki ko?"
Bai jiran amsar da TAIMIYYAH za ta bashi ba ya yi cuting call ɗin,ya kirata vid call don dama a ƙagauce ya ke da ya ga kyakykyawar fuskarta. Ya fara kiran voice call ne sabida sanin cewa dole tana cikin mutane,amma yanzu tunda ta kaucewa mutanen dole ya kira vid call don baiwa zuciyarsa abinda ta ke so.
TAIMIYYAH ta kalli kanta kafin ta ɗaga vid call ɗin,cike da jin kunyan yadda karon farko Maleek ɗin zai fara ɗaura idanunsa akanta babu lulluɓi. Sai ta samu kanta da kasa duban fuskarsa lokacin da ta tabbatar nata fuskar, zuwa gangar jikinta ya gama bayyana a allon screen ɗin wayarsa.
Maleek Ado kuwa lokacin da fuskar TAIMIYYAH da kwalliyarta ya bayyana garesa,sai da ya ja wani dogon numfashi ya sauke,zuciyarsa na amsawa da wani baƙon yanayi da ke ratsa har ɓargonsa. Ya sake ware manyan idanunsa akan ƙirjin TAIMIYYAH,yana me saurin rintse idanunsa ya sake buɗe su akan muhallin da ya ɗaurasu akai tun farko. Cikin wata iriyar kasalalliyar murya ya kirayi sunanta 'Zaynabbb!' TAIMIYYAH ta yi saurin ɗago fuskarta jin yadda ya kira yi sunanta very low,idanunta ya sauka akan kyakykyawar fuskarsa zuwa gangar jikinsa,da ke sanye cikin dakakkiyar farar shadda mafi tsada da nauyin kuɗin. Ɗinkin ya yi masa kyau duk da cewa ya cire babbar rigar da hula,sai ƴan cikin ne kawai sanye a jikinsa,a mota ya ke zaune ya kwantar da seat ɗin baya sosai yadda zai ji daɗin yin wayan. TAIMIYYAH ta ɗauke idanunta daga dubansa tana jin wani irin matsanancin ƙaunarsa na sake malting a zuciyarta,don babu ƙarya ya yi mata mugun kyau irin wanda bata taɓa gani ba,sai ta alaƙanta hakan da yadda fuskarsa ta ke a sake ne a yau ɗin.
Cikin muryar shagwaɓa ta ce, "Ina yini ya taro,Allah ya tabbatar mana da alkhairy ya bamu zama lafiya."
Maleek da idanunsa ke kan TAIMIYYAH ya kasa ɗaukewa,ya buɗe baki cikin muryar da ta fi waccar yin sanyi ya ce, "Ameen wife, i luv u so very much don Allah ki riƙeni da amana babe!"
Jikin TAIMIYYAH sai ya yi wani irin sanyi da jin kalaman Maleek Ado,ta sake ɗaura manyan idanunta akan fuskarsa,tana kallon yadda ya ƙurawa waje ɗaya a jikinta ido. Wani haɗaɗɗan kunya ya taso ya lulluɓe zuciyarta,cikin sauri ta furta, "Yah Maleek don Allah minti biyu zan ɗan ɗakko mayafi."
Wani kallo Maleek Ado ya watso mata ta cikin wayar,kafin ya buɗe baki kaman me son yin raɗa ya ce, "No wife! Kar ki fara kashe min waya,yau ba zancen sanya mayafi kin zama mallakina halak malak! Please kar ki ce za ki haramta min kallon halas ɗina."
Ya ƙare maganar yana sake gyara kwanciyar da ya yi a jikin seat ɗin lafiyayyiyar motarsa.TAIMIYYAH da kunya ke ɗawainiya da ita sai ta sake narke murya ta ce, "To mu yi voice call please Yah Maleek,wallahi kunyanka na ke ji."
Maleek Ado ya saki wani ƙayataccen murshi kafin ya ce, "No wife! Ki bani 20 minutes gani nan tafe zuwa gidanku,idan na iso zan kiraki ki fito ki sameni a mota,but u make sure idan za ki fito kin rufe min wannan kwalliyar da Hijab,and bana son ɗaukar wasu hotuna ana yawo da ke a media,shiyasa ni ma bazan shigo ba bare a yi wasu hotuna da aka maida ɗaukarsu fashion,please tell ur friends su taimakeni kar su ba za ki a duniya ana kallemin sirrikana please!"
Yadda Maleek ya kai ƙarshen maganar cike da nuna magiya da zallar kishin da ke cin zuciyarsa, yasa TAIMIYYAH dubansa tana sake jin kunyarsa me tsanani na lulluɓeta.Cikin shagwaɓaɓɓiyar muryarta da ke sake kunna wutar fitina a zuciyar Maleek ta ce, "Zan gaya musu Yah Maleek sai ka iso ɗin." Daga haka ta yi saurin cuting call ɗin tana sauke numfashi,zuciyarta na sake cika da ƙaunarsa me tsanani.
Ɗakin da su Yasmeen suke TAIMIYYAH ta koma,suka ko rufar mata da tsiyar cewa ta gudu sun sha luv da oga Maleek kenan. TAIMIYYAH ta narke musu da shagwaɓa tana kare kanta,ana cikin haka wata Cousine ɗinsu ƴar Rimi ta shigo ɗakin. Ta dubi TAIMIYYAH tana yaba kyawun da tayi ta ce, "Ma sha Allah! Amarya kin sha kyau ki zo Iyah na nemanki yanzu."
TAIMIYYAH ta dubi Nusaiba ta ce, "Okey jira ni mu fita tare don ni kunyar shiga jama'a na ke yi,ina fata dai zuwa yanzu duk mazan da suka dawo ɗaura aure sun watse?"
Nusaiba ta saki murmushi ta ce, "Kai Yah TAIMIYYAH kin cika kunya wallahi,sun watse kam babu wasu maza a wajen tunda Baba Sani ba zama a gidan zai yi ba,ya tafi can hotel da mutanensa don su bar mata su sake a cikin gida."
TAIMIYYAH ta jinjina kai cike da gamsuwa sannan ta dubi Yasmeen ta ce, "Sis zo mu je daga can za ki rakani wani waje."
Yasmeen ta miƙe tana gyara zaman ɗaurinta na ashobin da suka cakare a cikinsa,atamfar kuma ta yi musu mugun kyau dukansu ƙawayen Amaren. Ta bi bayan TAIMIYYAH da suka rigata yin gaba,tana ɗaga murya ta cewa Anty Laurat, "Anty Laurat don Allah ga wayata nan a caji kusa da ke,idan ya cika ki cire min please."
Daga haka ta yi gaba Anty Laurat na amsa mata da cewa, "Tuh shikenan an gama Sis."
Suka cigaba da hiransu da su Zee da su Bushirah,don su kenan ƙawayen na TAIMIYYAH,sabida ita ba mai yawan ƙawaye bace tun farko.
__________
Daga can sasan Baba Sani kuwa shirin tafiya da Amarya Zuhurah Bauchi ake yi,don dama haka aka tsara ana kammala ɗaura aure za a wuce da ita. Ita da Angon da mutane huɗu ne aka biyawa kuɗin jirgi,sai sauran mutane za su bi dogayen motocin da aka zo ɗaura aure da su don kwasan ƴan rakiyar Amaryar.
Amarya Zuhurah da ta sha kyau ita ma cikin kayan da ta sanya,sai faman kuka ta ke yi lokacin da suke sallama da Ummanta. Wacce kallo ɗaya za kai wa Umman kasan cewa akwai manyan damuwoyi kwance a ƙasan zuciyarta. Ta dubi Zuhurah lokacin da wata ƙanwar su Baba Sani da suke ƴaƴa maza da ita,ta kama hannun Zuhuran ta miƙar daga gabanta ta ce, "Zuhurah Allah ya bada sa a,Ubangiji yasa ki shiga gidanki cikin nasara,ki kula da dukkanin huɗubobin da mu kai miki,sannan kar ki yi sake ba ki yi anfani da waɗannan saƙon kamar yadda aka sanar miki ba, Allah ya yi miki albarka ƴata."
Zuhurah dai ba baki sai kuka da ta ke sha kamar za ta shiɗe,bata taɓa tunanin wannan ranar za ta zo ta kasa jin ɗokin barin gida ba,sai gashi tun da aka ce an ɗaura auren hankalinta ya ke a tashe,tana ji a zuciyarta sam bata son barin gidan,wani irin fargaba ke danne zuciyarta wanda ta kasa gane dalilin jin hakan da take yi. Ita ko Amarya Basmah kuwa tunda su sai yamma can za a miƙa su ɗakunansu,sai sabgarta ta ke yi cikin shaƙiƙan ƙawayenta su Amna da Sharifa. Ko kaɗan bata jin fargaban komi a ranta,sai ma ɗokin son a kai ta gidan Nass ɗin su zama abu ɗaya ita da shi,don ita haushin Zuhurah ta dinga ji da ta ke wani faman rusa kuka, kamar wacce za a kai gidan maƙiyinta ba Ameerunta da take ta rawar ƙafa akansa ba.
Aka fito da Zuhurah daga Sasansu aka nufi Sasan Iyah da ita don yin sallama da ita,suna isa Sasan Iyah ne bada jimawa ba TAIMIYYAH suka shigo don amsa kiran Iyah. Ashe dama Iyan ta aika