Showing 180001 words to 183000 words out of 186776 words

Chapter 61 - TAIMIYAH Book Complete Document by Ayshat Dansabo Lemu .txt

15 Dec 2024

6577

tsananin kulawa,amma hakan bai sanyaya zuciyar Suhailah ba,sai ma saƙe zafafa zuciyar kalaman Maleek ɗin suka yi. Sabida ya tabbatar mata da cewa tare da watan ta za su rayu,har yana faɗin har ƙarshen numfashi. Ta saki hawaye masu zafi daga idanunta,suna sauka a jikin Maleek yana jin ɗuminsu na keto rigarsa zuwa fatar jikinsa. Ya kai hannu ya ɗago fuskar Suhailah daga jikinsa yana me tsura mata manyan idanunsa,ta ɗauke nata idanun da sauri daga dubansa domin bata so wannan kallon ya yi tasiri a kanta. Maleek sai ya rabu da ita bai matsa akan cewa sai sun haɗa idanunba,ya miƙa hannun ya fara wiffing tears ɗin da ke zirarowa daga idanunta,ganin hakan yasa Suhailah rintse idanun baki ɗaya tana me sake shigewa cikin jikinsa.


Ɗumin da jikinta ya yi sosai yasa Maleek sake matseta a jikinsa ya ce, "Please Suhailah ki taimakeni ki kuma taimaki kanki ki daina wannan kukan haka nan,kin ji jikinki na son kamuwa da zazzaɓi kuma na san duk yawan koke-koken da kike yi ne."


Nan ma Suhailah shiru ta yi bata tanka shi ba,ya cigaba da rarrashinta da duk salon da ya san zai yi tasiri akanta,amma sam Suhailah bata nuna masa cewa salonsa ya shige ta ba. Hakan ya sa Maleek zareta daga jikinsa yana bata umurnin tashi ta bi su Anty Safiya da ke jiranta a waje cikin mota.


Suhailah ta miƙe daga kan jikinsa tana balla masa harara lokacin da ya yi kissing hannunta da ke riƙe nasa, wajen taimaka mata tashi tsaye,ta zare hannun tana fara takawa don ficewa daga falon baki ɗaya. Maleek ya bi bayanta da kallo zuciyarsa na motsawa da tausayinta me tsanani,don ya fi kowa sanin yadda Suhailah ke ƙaunarsa da kishinsa,ya san dama sai an sha fama kafin zuciyarta ta risina har ta rungumi ƙaddaran ƙarin auren da ya yi.


Ya zame jikinsa ya kwantar a cikin seater ɗin yana me lumshe idanunsa,moment ɗinsu da TAIMIYYAH na ɗazu na dawo masa daki-daki. Wani irin fitinan ƙaunarta da shauƙin son kasancewa da ita na sake azalzalar zuciyarsa. Ya zaro wayarsa daga aljihu domin danna mata kira,amma sai kira ya shigo daga cikin ɗaya wayarsa,hakan yasa shi fasa kiranta ya yi receiving call ɗin da ya shigo masa.


Suhailah kuwa tana isa bakin motar Hajjah da Anty Safiya ta zo da ita,sai ta buɗe back seat ta shige zuciyarta na cigaba da shiga ruɗu da nadama me tarin yawa. Gaba ɗaya fargaba da kunyar yadda za ta iya duban idanun Hajjah ke sake dagula lissafinta da jefa zuciyarta cikin tsaka me wuya.


Har suka isa Gonar Ganye gidan Hajjah zuciyarta ba ta huta ba,suna isa ana kiran sallar la'asar a masallacin da ke ƙasan gidan Hajjah. Suhailah da ƙyar ta iya sanyo ƙafarta waje ta fito daga cikin motar,tana ji tamkar ƙafafun ba za su iya ɗaukar nauyin gangar jikinta ba, sabida yadda su kai wani mugun sanyi. A haka ta dinga tafiya cikin slow tana biye da bayan su Anty Rady zuwa cikin gidan Hajjah. Babu wasu mutane sosai sabida ita ba yau take nata taron ba,sai gobe ne za ta tara mutane ayi walima tunda a gidanta za a sauke Amarya ta kwana,sai bayan an tara mutane anyi walima ne sai a wuce da Amarya zuwa GRA ɗakinta.


_____________


Daga can Gyallesu kuwa gidan su Amarya TAIMIYYAH,bayan an idar da la'asar ne me make-up ta sake gyare fuskar Amarya TAIMIYYAH. Wacce ta sake sauya shiga a karo na uku cikin wani haɗaɗɗen lace mara nauyi, kalar red and black da ya yi masifar amsar jikinta. Bayan an kafa mata hular ɗankwalin lace ɗin kamar yadda ake yi a yanzu,sai aka yane jikinta da wani irin haɗaɗɗen mayafi tamkar naɗin da akewa sari.TAIMIYYAH ta yi kyau har ta gaji su Yasmeen sai kashe mata hotuna suke yi,suna yana yaba kyawun da ta yi cikin kayan. Anty Laurat ce kawai ba za ta samu yi mata rakiya ba sabida da ita aka tafi kai Zuhurah Bauchi,sai su Zee da su Maryam Sunusi ne kawai za su yiwa TAIMIYYAH rakiya zuwa gidan Hajjah. Dukkaninsu sun sauya shiga cikin kaya na alfarma sun sha make-up na kece raini.


Shigowar Ummie cikin ɗakin yasa TAIMIYYAH ɗaga ido ta dubi Ummien,wacce ta cake ita ma cikin rantsatstsen lace da ya yi mata mugun kyau,sai ta koma tamkar budurwa irin ƴar 25 yrs ɗinnan.


"To Amarya sai ki ta so ga motoci can sun iso,za a miƙa ki zuwa gidan miji."


Ummie ta yi maganar idanunta akan TAIMIYYAH da ta yi wa Ummien mugun kyau kamar ta yi ta kallonta. TAIMIYYAH nan da nan sai hankalinta ya tashi ta yi wani ƙwal-ƙwal da ido tana shirin sanya kuka,hakan yasa Ummie saurin fice wa daga ɗakin tana sanar da Yasmeen cewa su fito tare da TAIMIYYAH, ga su Guggo Lami can da su Anty Mardiyyah na jiran su a falo. Daga haka ta yi ficewarta don zuwa ta ɗakko mayafi don da ita za a kai TAIMIYYAH,bata son tsayawa TAIMIYYAH ta karya zuciyarta ne don ita me saurin kuka ce ,babu wuya zuciyarta ta raurawa ta fara kuka.


TAIMIYYAH lokacin da suka fito zuwa falon Ummie,sun samu duk su Anty Mardy suna jiran fitowarsu ne, don a wuce da ita zuwa part ɗin Iyah su yi sallama da juna.


Wani irin ƙaramin film ne ya gudana a part ɗin Iyah,na yadda rabuwarta da TAIMIYYAH zai kasance, wacce ta ƙanƙame Iyah tana kuka tamkar za ta shiɗe,tana kuka Iyah na kuka kuma cikin kukan Iyah ke faman rattafo ma TAIMIYYAH addu'o'in sanya albarka.Duk wanda ke ɗakin sai da ya taya su kuka,sannan kuma ya dara sabida yadda suke kuka tsakanin junansu,da ƙyar aka zare TAIMIYYAH daga jikin Iyah aka fita da ita.Yasmeen kanta tana kuka ne tana yin musu vedio don ba ƙaramin tausayin TAIMIYYAH ta ji ba,sabida kowa ya san yadda suke da Iyah zai san cewa rabuwarsu ba zai zo ta sauƙi ba dama.


Lokacin da aka fito da TAIMIYYAH ita kuma Basmah za a shiga da ita don sake yin sallama da Iyah ita ma,sabida kusan duk a tare motocin ɗaukar Amaren suka hallara. Ita Basmah can Ƙwarbai gidan Hajiyar Nass za a fara kaita ita ma ,sai a gobe za a ɗakko ta daga can a kai ta Gonar Ganye gidan Nass ɗin da ya gina.


Daga yanayin manyan motocin da ke fake a harabar gidan za ka san cewa akwai ratar arziƙi tsakanin motocin da za su ɗauki TAIMIYYAH da wanda za a ɗauki su Basmah. Ƙawayen Basmah irin su Sharifa duk sai suka raina arziƙin Nass ɗin,sabida motocin sun ruɗe su don kana kallo kasan bana ƙananun masu kuɗi bane,ko wace mota ka kallah za ka ganta sabuwa dal ce.


Kallo bai koma sama ba ma sai da motar da za ta ɗauki Amarya TAIMIYYAH ta ƙariso cikin compound ɗin gidan. Amintaccen driver ɗin Maleek Ado me suna Yusuf ke janye da motar. Wata iriyar mota da kaf su Sharifa ba su taɓa cin karo da motar da ta ɗauki hankalinsu irin ta ba,motar ba wani girma ne da ita ba amma kallo ɗaya za ka mata ka san bana ƙananun kuɗi bace,sabuwa ce dal don ranar aka fara hawanta. Maleek ne ya yi ordern su guda biyu tun daga ƙasar Amurka aka zo masa da su,domin ya mallakawa matan nasa su kyauta halak malak,shiyasa ya yanke shawaran a ɗakko masa Amaryarsa TAIMIYYAH a cikin nata.


Surutu ya dinga tashi ana zuzuta irin gidan daular da za a kai gurguwa TAIMIYYAH,kamar yadda su Sharifa suka dinga faɗin kalmar suna cewa "Kai! Yanzu gurguwace ta auri attajirin mutum irin haka?"


Suka dinga mamaki suna jinjina lamarin a tsakaninsu kai kace ita gurguwar ba mutum bace,da Ubangiji ba zai azurta ta kamar yadda ya ke azurta sauran bayinsa ba.


Ita dai TAIMIYYAH bata ma san ana yi ba don kukanta kawai ta ke sha,ko kalar motar aka tsareta ma ta faɗi ba za ta iya ba don ba abinda ke gabanta kenan ba. Haka Yusuf ya ja motar suka fice daga cikin compound ɗin gidan,Yasmeen da ke daga gefen TAIMIYYAH riƙe da hannunta na faman rarrashi,ita ma Anty Mardiyyah da Ummie da suke ta ɗaya gefen na taya Yasmeen rarrashin. Guggo Lami da ke matsayin ƙanwar su Baba Sani ita ta kame a front seat su Zee da su Maryam Sunusi suna can cikin ɗaya motar Maleek, wacce ya zo da ita gidan ɗazu. A ciki aka kwashesu su huɗu daga Maryam sai Zee da Bushira,sai Nusaiba cousine Sis ɗin su TAIMIYYAH.


Sauran motocin suka kwashe ragowar mutanen da za su yi wa TAIMIYYAH rakiya,wasu ma empty suka juya sabida ba da yawa aka je ba,tunda an rabu uku za a ce wasu za su raka Basmah ne, wasu kuma TAIMIYYAH, yayin da sauran kason ke can Bauchi wajen raka Amarya Zuhurah.


__________


*Gonar Ganye.*


Hajjah ta dubi Suhailah da tsananin mamaki da firgicin abinda ta ke ji da gani,wanda ya girmi tunaninta bayan su Anty Safiyyah sun gama zayyane mata komi. Ta ɗaga idanunta a karo na biyu ta sauke akan Layun da ke kan gadonta, tana cigaba da shiga mamakin yadda wai Suhailah ce ta iya amso su, don ta tarwatsa auren da take farin ciki da ƙulluwarsa a wannan rana. Zuciyarta ya sake matsewa da wani irin ƙunci me tsanani, ta maida dubanta kan su Inna Dije da suke faman yiwa Suhailah faɗa da nasiha. Hajjah ta yi magana cikin sanyin murya ta ce, "Yayah ina ga a barta haka nan, a kulle wannan babin don yanzu za ki ji ƴan kawo Amarya sun iso. Safiyyah ki ɗauki Layun ki je can backyard ta inda babu me sanin me za ki yi,ki ƙonasu gaba ɗaya. Ita kuma Suhailah zan dawo ta kanta amma ba yau ba, ba kuma gobe ba sai an watse wannan taron,sabida yanzu lokaci ne na tsayawa mu amshi baƙin mu bana ɓatawa akan Suhailah ba."


Daga haka Hajjah ta juya ta bar musu ɗakin,tana jiyo kukan da Suhailah ta saki zuciyarta na sake ɗaukar zafi da ita. Inna Dije ta dubi Suhailah tana me kai hannu ta bige bakin kukan, cikin zallar fushi da ɓacin rai ta ce, "Za ki mana shiru ko sai na ɗauke ki da mari, ƴar banzar Yarinya mare jin magana. Duk irin Nasihar da aka dinga miki ashe ta bayan kunninki suke bi suna fita. Kin bani kunya Suhailah sannan kin ci amanar ƙauna da tarbiyar da Hajjah ta baki,don baki taso kin ga tana aikata mummunar abu irin wannan ba,kada ki bari ƙawayen bariki su kai ki su baro Suhailah. Tun wuri ki dawo cikin hankalinki ki kama mijinki tare da rungumar ƙaddararki da hannu biyu,kishi ba hauka bane Suhailah don dukkkanmu ni da Radiya gata nan duk kishiyoyin gare mu,amma kin taɓa ji ko ganin ance ga mu a hanyar amso asiri don mu cutar da su?"


Suhailah ta girgiza kai hawayen tsananin nadama na sake biyo fuskarta,Inna Dije ta cigaba da cewa, "To ki shiga hankalinki tun wuri, duk wata ƙawa da ba za ta saki a hanyar bin Allah ba ki yi gaggawar rabuwa da ita,don ba mai ƙaunar ki bace. In da ace kina dagewa da addu'a tare da roƙon Allah akan ya rage miki wannan zafin kishin,da tuni kin samu nutsuwar zuciyarki. Maleek na ƙaunarki Suhailah don haka ki yi anfani da damarki wajen kwantar da hankalinki,tun yana bibiyarki yana rarrashi kafin ki kai shi bango ya tattaraki ke da mummunar kishin banzar ki ya watsar a gefe guda.Don yanzu sabuwar Amarya ya yi idan kika cigaba da wannan sokoncin da iskancin da ki ke yi ,wallahi tun kina bashi tausayi yana rarrashinki kina botsarewa, tuh fa zai fita daga sabgarki ne ya rungumi Amaryarsa da za ta faranta ransa, don haka ki dawo cikin hankalinki ki aje duk wani zafin kishi. Ki rumgumi mijinki tare da tarairayarsa, ki bashi goyan baya wajen tabbatar da adalci a tsakaninku. Duk lokacin da ki ka ji kishin ya taso miki ki dinga yawan nanata wannan addu'ar ' _Allahummah Atinifuh sanahtaqwaha_ wazakkiha Antah Khairumanzakkahah_ Anta waliyyuha_ wamaulahah!_ ' sannan ki dinga yawan faɗin ' _Allahummah lah sahlan_illahmaja'altuhu sahlan_wa'antah taj'alul haznah_ izahshi'itah sahlan!'_


Idan har ki ka dagewa faɗin waɗannan addu'o'in a duk lokacin da ki ka ji kishin ya taso miki,tuh ina tabbatar miki da cewa Ubangiji zai sanyaya zuciyarki. Amma bin Boka ko kauce hanya babu in da zai jefa rayuwarki sai a halaka da danasani marar iyaka. Ga ɗinbin zunubin da zai iya kai ki wuta,kuma ki daumama a cikinta idan har kika mutu kina shirka baki tuba ba, to ina riba Suhailah? Ki ji tsoran Allah ki kuma gode masa da ya yi miki baiwa da ni'imar samun miji da suruka ta gari. Wanda a wannan zamanin da muke ciki samun irin su ya yi ƙaranci. Wallahi Hajjah bata cancanci butulci daga gare ki ba,don wannan butulci ki ke son nuna mata tun da kin ɗakko hanyar cutar da gudan jininta da baiwar Allahn da bata ji ba bata gani ba. Sabida Allah ne ya ƙaddara cewa Maleek shi ne zai zamo mijinta, don haka ya rage naki ki ɗauki dukkanin huɗubobi da Nasihun da ake miki,ko kuma ki watsar ki kama hanyar da kike ganin ya dace dake. Amma fa ki sani daga randa kika jefa rayuwarki cikin wani hali kada ki nufo kowa a cikin mu,da sunan neman ɗauki ko baki shawara. Ki tashi ki je ki wanko fuskarki ki sauya shiga don baƙi ƴan kawo Amarya suna kan hanyar isowa,kuma lallai ki cigaba da roƙan Hajjah gafara akan ta yafe miki don ranta a mugun ɓace yake da wannan lamarin da k ika nemi aikatawa me muni."


Inna Dije ta kai ƙarshen maganar tana jin ɗaci da takaicin abinda Suhailah ta yi, ko da wasa bata taɓa kawo cewa za a iya zuga Suhailah ta kauce hanya sabida zafin kishi ba. Anty Rady ita ce ta cigaba da yiwa Suhailah faɗa,da nuna mata illar abinda ta so aikatawa,tare da bata misalai na waɗanda aka yi wa kishiyoyi,amma suka rungumi ƙaddararsu suka kuma zauna lafiya da mazajensu. Suhailah sosai ta ke jin tasirin Nasihun da suke mata na ratsa zuciyarta, nadama me tarin yawa na tasowa na sake mamaye zuciyarta, tana jin ɗaci da ƙunci akan yadda ta so sanya kanta cikin halaka. Burinta kawai a yanzu Hajjah ta sakko daga fishin da take hangowa a cikin ƙwayar idanunta. Domin wani irin fargaba me tarin yawa take ji, na yadda Hajjah ta ke dojewa bata so ma ana yawan matsa mata da faɗa akan abinda ta so aikatawan,ta fi kowa sanin halin Hajjah idan tana irin hakan to ba ƙaramin bango mutum ya kai ta ba,kuma matakin da za ta ɗauka ba zai yi mata kyau ba ita ta san hakan. Wasu hawaye masu zafi suka sake gangarowa daga idanun Suhailah, ta miƙe da ƙyar tana jin jiri na neman kada ita, hakan yasa Anty Rady taimaka mata ta riƙe hannunta suka nufi ƙofar shiga bathroom, don Suhailah ta sako wanka ta zo ta shirya kafin baƙi su iso.


*20 Minutes Later.*


Suhailah ce a zaune ta gama kintsawa cikin wani haɗaɗɗen Voile lace me nauyin kuɗi,wanda akai wa ɗinkin straight gown da ya zauna a jikinta. Fuskarta ya sha light make-up da ya taimaka wajen ɓoye halin da fuskarta ya shiga sabida yawan kukan da ta sha. Ta yi kyau sosai duk da cewa idanunta har lokacin basu sace daga kumburin da suka yi ba,amma hakan bai hana kyawun da ta yi bayyana ba.


Ta miƙa hannu ta ɗakko sarƙarta na gwal me asalin kyau ta sanya a wuyarta,kunninta na haskawa da ƙyallin ɗankunnin gwal ɗin. Hannunta ta zurawa bangles guda biyu duk na gwal, nan da nan ta sake haskawa da wani irin kyawu me sanyi. Rashin fara'ar da ke kan fuskarta kaɗai ne ya kawo cikas wajen sake haska annurin kyawun da ta yi ɗin, ta miƙe tana maida box ɗin sarƙarta cikin jaka, daidai kuma lokacin da wata mata me zaƙin murya ta saki wani irin guɗa, wanda sautinsa ya ratso har cikin ɗakin da Suhailah ta ke ya shiga kunnuwanta. Sai ta yi saurin sakin jakar hannunta tana me dafe ƙirjinta da ya buga da ƙarfin gaske, ko ba a faɗi ba ta san cewa Amaren ne suka iso. Sai ta rintse idanunta tana ambato sunan Allah da karanto addu'ar da Inna Dije ta horeta da yi aduk lokacin da ta ji kishin ya taso mata.


A hankali ta taka zuwa bakin sofan da ke ɗakin ta zauna,tana cigaba da nanata addu'ar cikin zuciyarta. Kunnuwanta na cigaba da jiyo guɗar da ake saki tare da jiyo hayaniyan mutanen da suka rako Amaryar,sai ta ji ina ma bata yadda ta biyo su Anty Safiya ba, da ta sani ta yi zamanta a can gidanta da yanzu duk ba za ta ji irin waɗannan ayyiyikan ba.


Ta dafe saitin zuciyarta da ke cigaba da bugawa da ƙarfi,tana cigaba da nanata 'Allummah lah sahlan' har zuwa ƙarshe. A hankali sai ta fara jin sauƙi a cikin zuciyarta, ta dinga jin ƙuncin da ya danne zuciyarta na raguwa sosai,ta cigaba da zama bisa Sofan tana cigaba da jiyo hayaniyan ƴan kawo Amaryar, har zuwa lokacin da Anty Safiya ta shigo ɗakin. Ta isa wajen da Suhailah ke zaune ta zauna tana me kamo hannunta ta riƙe tana cewa, "Kai! Ma Sha Allah! Uwargidan Maleek gaskiya kin yi kyau matuƙa, saurinki kawai ki saki ranki da zuciyarki Suhailah. Kin ga Amarya ta iso mutane sun cika gida don haka kar ki yadda ki yi wani abu da zai fallasa halin da zuciyarki ke ciki.Daurewa ake yi a nuna jarumta wajen danne duk wani kishi da za ki ji,kar ki yadda ki yi abinda za a tafi da ke a baki ana Allah wadai da zafin kishinki. Don Allah ki ba marar ɗa kunya daga nan har a watse taron da za a yi zuwa gobe,hakan zai sanyaya zuciyar Hajjah ta jin zafinki a zuciyarta kin ji ko?"


Suhailah ta gyaɗa kai cike da gamsuwa ta ce, "In Sha Allah! Anty Safiya zan yi duk yadda ku ka ce, ku taya ni ba Hajjah haƙury don Allah, wallahi na yi nadamar biyewa Jawahir

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login