Showing 123001 words to 126000 words out of 186776 words
Chapter 42 - TAIMIYAH Book Complete Document by Ayshat Dansabo Lemu .txt
huta,sai inji dana Sadeeq da zai biyo baya tunda shi namiji ne."
Basmah sai ta saki murmushi tana sanar da Umman ai Nass ɗin yace zuwa next week Saturday za a zo,yana jin ma gaba ɗaya da zuwa da sanya ranar za a yi a lokaci guda,sabida daga shi har Uwarsa a matse suke ya yi aure,musamman Uwar da take son ganin ya rabu da gurguwarcan,shiyasa yana zuwa mata da maganata ta amince babu wani dogon bincike,ita dai burinta ace ya rabu da gurguwar da bata so bata san tuni muka ɗauke tunaninsa daga kan wata gurguwa ba,ni kaɗai yake ji da gani."
Basmah tayi maganar bil hakki tana sakin dariyar mugunta Umma kuma na taya ta.Zuhura ta ɗan ja ƙaramin tsaki tana faɗin, "Wallahi Basmah ni har kin fini so kiyi aurennan ma,irin wannan rawar kan da kike yi haka kamar zaki kai kanki."
Basmah tayi fari da ido tana sakin dariya tace, "To miye a ciki aure ai abin so ne musamman idan kayi dace da wanda kake so,kinsan yadda nake jin Nass a raina kuwa? Hmm! Ba a magana ke dai kawai Allah ya ara mana lokaci mu more."
Zuhurah ta amsa da, "Ameen." Suna cigaba da tattauna yadda za su tsara bikinsu idan an sanya ranar auren Basmah nan da sati me zuwa.....
TAIMIYYAH bayan idar da sallan la'asar da tayi,cigaba da zama tayi a ɗaki tana ta tilawar Qur'ani sabida so take yi zuciyarta ta sake sanyaya, daga ƙunci da ɗacin da take ji a cikin ranta tun ganin da ta sake yiwa Nass da Basmah a tare.
Sai ana dafda kiran magriba sannan ta tashi ta fito falo wajen Iyah da ke zaune.
Ta isa kusa da Iyah ta zauna tana faɗin, "Iyah sannu kina ta kallo ne,ni tun ɗaxu ina tilawa ne kinsan an kusa yayenmu sai da tilawa sabida haddar ya zauna da kyau."
Iyah ta dubi TAIMIYYAH tana cewa, "Hakan yana da kyau,ai ina jiyo karatun naki daga nan nace to gaki can ana ta ƙoƙari,Allah yasa albarka yasa anyi na tsoran Allah ne."
TAIMIYYAH ta amsa da, "Ameen." Iyah na cigaba da jan ta hira har aka kira sallah suka nufi ɗakunansu don ɗaura alwala.
____________
*Abuja, 9:05pm.*
Suhailah ce ke tsaye a cikin kitchen ɗinta da ke upstairs,tana ƙarisa haɗawa A.Maleek haɗin Beef Salad da yace shi zai ci a daren.
Bayan ta kammala haɗawan ne kuma ta nufi Coffee maker, ta haɗa masa ruwan Coffee ta juye cikin ƙaramin Mug flask me kyau,ta haɗa komi bisa madaidaicin tray ta fito zuwa falo ta aje daga ƙasan carfet,don ta san ba zai taɓa hawa dining ba.
Tana ƙoƙarin tashi ta nufi ɗakinta don yin wanka,ya fito daga ɗakinsa sanye cikin Pajamas Ash colour da suka haske fatarsa.Suhailah tayi saurin dubansa tana cewa, "My Maleek na kammala zan je nayi wanka yanzu, ko in tsaya ka kammala ne?"
Da hannu kawai yayi mata alama ta tafi sabida yau da alamu ƴan miskilancin nasa na kusa ne,sabida haka suka yini da shi tun rana yana faman shan ƙamshi.
Suhailah ta saki smile tana yin gaba abinta,cikin zuciyarta take jinjina halayyar Maleek ɗin masu wuyar sabawa.
Lokacin da ta fito yayi nisa wajen cin Salad ɗinsa wanda yayi masa yadda yake so.Ya ɗago manyan idanunsa ya sauke akan Suhailah lokacin da take takowa zuwa garesa.Tana sanye ne cikin fararen Nighties riga da wando wanda suka lafe a jikinta tareda bayyana surarta a fili.Sabida kayan basu da kauri ko kaɗan,hatta ƙirjinta da bata sanya komi ba a na hangosa muraran ta cikin rigar.
Maleek yayi saurin ɗauke idanunsa akanta har ta ƙariso wajen da yake zaune, ta zauna kamar zata shige jikinsa ƙamshin turarenta dana Humrah da tayi amfani da shi na cika kafofin hancinsa.Ta miƙa hannu ta amsa fork ɗin da ke hannunsa tana cigaba da ciyar da shi ba tare da tayi magana ba,kamar yadda shima bai ce uffan ba ya dai sakar mata fork ɗin tana ciyar da shi yana buɗe baki a ƙasaice yana amsa har ta kammala bashi.
Ta haɗe kayan da suka ɓata ta nufi kitchen ta wanke su ta kife,don bata son kwana da plates da akai anfani dasu ba a wanke ba.
Lokacin da ta dawo cikin falon samunsa tayi ya miƙe ƙafafunsa sosai yana kallon labarai a tashar NTA Abuja.
Ta zauna kusa da shi jikinsu na gugar juna kafin tayi ƙasa da murya tace, "Yah Maleek next week ɗin za ka shiga Zarian ne?"
Bai yi magana ba ya dai ɗago manyan idanunsa ne daga kan TV ya sauke akanta,kafin ya kai hannunsa duka biyu ya kwanto da ita zuwa jikinsa, yana gyara mata zama bisa laps ɗinsa yake cewa, "No ina ga sai zuwa upper week zanyi tafiya xuwa Anambra bazan samu shiga Zaria ba, kina son wani abu ne daga can?"
Yadda yake maganar cike da ƙasaita hannunsa na lalube jikinta yasa Suhailah lumshe idanunta,dukkanin jikinta na amsan saƙon da yake isarwa a sassan jikinta.Ta buɗe baki murya can ƙasa tace, "So nake mu je tare dai my Maleek coz nayi missing Hajjah sosai."
Tayi maganar cike da marairaice masa murya,hakan yasa Maleek ɗago face ɗinta da hannu ɗaya,ɗaya hannun na cikin rigarta ya manna mata harara yana cewa, "Aiko ba za ki Zaria nan kusa ba sai kin samu kaman 3 month ina ga zaki fi ɗokin ganin Hajjan da kyau,zuwa lokacin kin daɗe da shaye magungunanki kila ma har kinyi ciki,kinga sai ki je kina mata ɗan amannan da kuke yi kina tara miyau a baki,sai ta gane cewa ɗan Abuja ya samu."
Suhailah ta waro ido tana duban Maleek sosai,wanda ya haɗe face ba za ka taɓa cewa shine ya zayyano dukkanin kalaman ba.Ya kai bakinsa yayi kissing idanun nata yana cewa, "Hey! Babe karki cinyeni da wannan kallon mana."
Yayi maganan har lokacin fuskarsa ɗaure yana jefa mata harara, Suhailah ta saki dariya tana sake shigewa jikinsa.Ta ɗaga kai tana kai bakinta bisa wuyarsa tayi kissing kafin tayi masa raɗa cikin kunni wanda sam banji me tace ba.Sai gani kawai nayi Maleek ya dungure mata kai da hannu yana magana can ƙasa-ƙasa yake cewa, "Zaki yi bayani ne yarinya amma ba a nan ba sai a Bed."
Suhailah dake faman dariya ta ɗan shagwaɓe murya tana faɗin, "Ni kam babu ruwana Yah Maleek,amma kana ganin zuwa lokacin da zan kammala da magungunan komi zai iya zama normal har in iya ɗaukar ciki?"
Tayi maganar da wani expression wanda yasa Maleek ɗagota baki ɗaya ya mannata da ƙirjinsa yana cewa, "If Allah yayi nufin hakan sai ya kasance wife,addu'a zamu cigaba da yi dai sai kuma in sake zama rigimammen da kike cewa idan rakinki ya tashi,watakila a duba ƙwazona a bamu rabo kurkusa ko Babe?"
Yayi maganan yana sanya idanunsa cikin nata,da yasan tasirin irin yadda yake dilmiyar da zuciyar Suhailah idan yayi hakan, daya sassauta mata don wani irin gubar ƙaunarsa yake zuba mata me asalin ƙarfi dake illata zuciyarta nantake.
Ta lumshe idanunta da sauri tana buɗesu akan kyakykyawar fuskarsa,ba tareda da ta bashi amsa ba ta kai bakinta saman nasa tana fara manna masa wani irin french kiss,wanda shi ya koyar da ita amma sai gashi ta fishi ƙwarewa a harkar.
Cikin lokaci kaɗan ta gama kunna zuciyar Maleek,sai da abubuwa sukai nisa ne ta fara danasani. Don da ƙyar ta kwaci kanta a hannunsa lokacin da ya nuna bai san komi ba, illah ta bashi abinda ta san shi kaɗai ne zai kashe wutar rikicin da take hangowa cikin idanunsa.
A daddafe suka kai 10:30pm anan falon suka nufi ɗakinsa bayan ya gama shan coffee ɗinsa,yana fitowa daga toilet yayi musu light up ya nufi kan Bed inda Suhailah ke kwance cikin duvet.
Ya miƙa hannu ya lalubota tare da janyota zuwa jikinsa,jin ta yayi a yadda yafi so don har ta cire kayan jikinta babu komi a tare da ita,hakan yasa shi manna mata sumba a biki cikin murya can ƙasa ya furta, "Luv u my sweet wifey."
Daga haka labarin ya fara canzawa zuwa wani salo na daban abinda ya kore ni daga ɗakin kenan na fito kamar zanyi tuntuɓe......Lol
__________
*3 Weeks Later*
TAIMIYYAH ce zaune tare da Iyah suna tattaunawa akan saka ranan auren Basmah da Nass da akayi sati biyu da suka wuce.
TAIMIYYAH ta dubi Iyah tana tana faɗin, "Ni Iyah kinsan me ke bani mamaki?" Iyah ta girgiza kai tana cewa, "Sai kin faɗa TAIMIYYAH." TAIMIYYAH ta ɗan tsuke face alamun koma me zata faɗi yana hurting ɗinta a zuciya kafin ta furta, "Wallahi Iyah randa na shiga yi musu Allah sanya alkhairy Umma cewa tayi wai ai dama ban je ba, tunda ta san daga ni har ke baƙin ciki muke yi sabida uwarsa tace bata sona don ni gurguwace,yanzu kuma mun ga ya dawowa Basmah har gashi an sanya musu rana ai ta san baƙin ciki muke yi,Allah sanya alkhairin ma na gulma ne na je yi,wallahi Iyah na ji zafin kalaman sosai a raina."
Iyah dake sauraren TAIMIYYAH ta jinjina kai tana cewa, "Kiyi haƙury Zainab akan koma me zasu ce miki,ke dai kawai ki musu fatan alkhairi,ki kuma sanya musu ido wanda hausawa kan ce maganin lalatacce,kuma maganar baƙin ciki da take faɗi da baƙin cikin muke yi,da ni da kaina na soke batun auren na tona musu asiri,don kuwa idan na sanar da Sani yadda abin ya faro har kawo dawowarsa wajen Basmah,suna ji suna gani zai yi kora da maganar sai dai kuyi biyu babu,sakarya wacce bata da lissafi ko kaɗan a cikin kanta,har abada bazan fasa yiwa Sani takaicin kasancewa da mace jahila me son zuciya irin Zuwairah ba,domin na jima da tsanar halayyarta don ba za ka ce ka ƙi mutum ba sai dai ka ƙi mugun halinsa,amma ina mata fatan shiriya idan tana da rabo."
Iyah ta kai ƙarshen maganan cike da tsananin ɓacin rai,don har cikin zuciyarta take jin ciwan irin abubuwan da sukewa TAIMIYYAH ,wacce bata taka musu ba bare ta zubar musu.
Daga wannan hiran suka koma kan shirye-shiryen walimar yayensu TAIMIYYAH da za a gudanar asabar me zuwa.
TAIMIYYAH na sanar da Iyah cewa tana son sayan sabuwar Abaya da za ta sanya a ranar. Iyah ta murmusa tana cewa, "To ai sai ki saya ɗin Zainab,nawa ne kuɗin Abayar sai in baki ai,munyi magana da Babanku Sani ma nace ina so a kayar da ko raguna biyu ne, a gasa kowa yaci naman,don taro sosai zan yi aci a sha a taya mu farin ciki."
TAIMIYYAH ta saki kyakykyawar murmushin farin ciki tana cewa, "Iyah Allah ya ƙara girma ya baki tsawon rai me anfani,bani da bakin da zan iya kwatanta adadin ƙaunar da nake miki a duniyar nan sai dai ince Ubangiji ya baki Jannatul firdaus ,ke da su Abie da Mamata dasu Nahar da mu baki ɗaya."
Sai kuma hawaye suka fara zubowa TAIMIYYAH sharr...!! Iyah tayi saurin kamo hannunta tana faɗin, "Ameen Zainabu don Allah bar kukan haka, kiyi haƙury Allah ya gafarta musu ya ƙara mana dangana,nawa ne kuɗin Abayar maza ki faɗi min kin ji Zainabu na."
TAIMIYYAH ta share hawayen da suka zubo mata tana jin kewar Abie ɗinta me tsanani yana cika zuciyarta.
Ta yi ƙarfin halin murmusawa tana sanar da Iyah adadin kuɗin Abayar.Iyah ta jinjina kai tana faɗin, "Karki damu gobe zan baki kuɗin Insha Allah."
TAIMIYYAH tayi godia tana cigaba da cewa, "Iyah ai online na siya Abayar nama tura da kuɗin ta account ɗina,kawai dai na san zaki yi faɗa ne kice meyasa ban bari kin saya min ba,wajen wata chuchu na siya na tura mata kuɗin gobe za ta sako min a mota sai Sani ya je tasha ya amso."
Iyah ta aikawa TAIMIYYAH harara tana faɗin, "To ai kin kyauta da baki sanar min ba sai da kika siya,sai ki amshi kuɗin ai ki mayar cikin asusun naki."
Kafin TAIMIYYAH tayi magana taji kira ya shigo wayarta,ganin sunan Hajiya Aysha yasa ta yi receiving call ɗin ta kai wayar kunni tana amsa sallamar da Hajiyar tayi.
TAIMIYYAH ta gaida ta cike da ladabi tamkar tana gabanta,kafin tayi jim tana sauraren abinda Hajiyar ke faɗi daga nata ɓangaren,zuwa can tai ƙasa da murya tace, "Eh Mama ranan Saturday ne idan Allah ya kaimu,ashe Iyah bata manta ba ta sanar miki."
Ta sake yin jim! Kafin ta furta, "Bakomi Mama duk abinda ake buƙata anyi nagode sosai na kulawa sai kun zo ɗin."
TAIMIYYAH ta cigaba da blushing tana sauraren abinda Hajiyan ke sake faɗi mata,kafin ta sake cewa, "To shikenan Mama nagode gama Iyan a kusa dani bari in bata wayar."
Daga haka TAIMIYYAH ta miƙawa Iyah wayar tana mata raɗa da cewa Hajiyar Gonar Ganye ce,kamar yadda suka raɗawa Hajiyar tun randa sukai waya ta sanar da Iyah cewa a Gonar Ganye suke zaune.Iyah ta amsa wayar suka gaisa ita dai TAIMIYYAH bata ji me Hajiyar ta sanar da Iyah ba,ta dai ji Iyah na godia kafin ta miƙo mata wayar sukai sallama da TAIMIYYAH.
Lokacin da TAIMIYYAH ta aje wayar a jikinta ne ta dubi Iyah tana cewa, "Iyah gaskiya Hajiyar nan akwaita da kirki cewa fa tayi lallai in faɗi me nake son ta kawo min gift ranan walima."
Iyah tayi murmushi tare da jinjina kai tana faɗin, "Wallahi Zainab nima na yaba da kirkin matarnan Allah kaɗai yasan alkhairyn da yake nufi ya haɗamu ta hanyar gitta tsautsauyi a tsakaninku,sosai kika shiga zuciyarta na ga alama,ai nina kirata ɗazu kina bacci na cika alƙawarin dana ɗauka na cewa zan sanar mata idan lokacin walimar ya kusa,shiyasa kika ji ta kira ki yanzu."
TAIMIYYAH ta jinjina kai itama tana jin ƙaunar Hajiyar har cikin ranta,sabida yadda take nuna mata ƙauna da kulawa.Suka cigaba da tattauna yadda hidiman walimar zai kasance,sai da kiran Yah Deeku ya shigo wayar TAIMIYYAH ne sannan ta tashi ta nufi ɗaki,don ta san shima dai zancen walimar yayen nasu zai mata,don tun jiya yake fama akan ta turo masa details ɗinta taƙi don bata son ɗaura masa ɗawainiyar sai ya bata wani abu.
Sun daɗe suna magana tana faman bashi haƙury da cewa yanzu zata tura masa details ɗin, sabida yadda ta ji ransa ya ɓaci.Suna ko gama wayar ta tura masa ko minti biyar ba a yi ba k sai ga alert na 50k.
TAIMIYYAH tayi ta kiransa don tai masa complain akan kuɗin yayi yawa,amma sai yaƙi ɗauka sai dai ta tura masa text message ɗauke da kalamai masu daɗi na godia.Ta fita da sauri don zuwa ta sanarwa Iyah don ta taya ta godia wajen Yah Deekun........✍🏻
#Ɗansabo ce#
[12/14, 10:11 PM] +234 703 769 7050: *Littafin TAIMIYYAH paid book ne,ga duk wanda ta tsincesa a kowani irin group ne,kiji tsoran Allah karki karanta sai kin biya 500 naira only.*
*Za ku iya min magana ta wannan number ɗin 08167768704, ko kuma ku turo kuɗin ku kai tsaye ta wannan account ɗin*👇🏻
0504192664 aisha ibrahim dansabo GTbank.
*Sai ku tura shaidan biyanku ta wannan line ɗin 08167768704.*
Masu turo credit za ku turo katin MTN na 500 ta wannan line ɗin 08167768704.
_*Ina ƴan kasuwa masu buƙatar a tallata muku hajar ku? Maza ku garzayo da kuɗi ƙalilan a tallata muku kayan siyarwanku sai dai kawai ku ji ana kiran waya don buƙatan sayan kayan ku,ku tuntuɓeni ta layina kamar haka 08167768704.*_
*52*
Kwanakin da suka biyo baya gaba ɗaya TAIMIYYAH da Iyah sun maida hankali ne wajen shirye-shiryen walimar kammala Haddar Qur'anin su TAIMIYYAH,ana gobe za a yi walimar Yasmeen da Guggo Bilki suka iso daga Kano.
TAIMIYYAH suka rungume juna ita da Yasmeen,suna murnan ganin juna tamkar ba kusan kullum sai sunyi vid call ba.
Da daddare bayan sun kammala cin abinci ne suka ƙule a ɗakin TAIMIYYAH don zantawa da juna,sabida tunda suka iso ana ta kammala shiri ne sai yanxu ne suka samu time ɗin kaɗaicewa.
Yasmeen ta dubi TAIMIYYAH tace, "Sis kinsan ni duk na ƙosa muyi ido biyu da mara kunyar Yarinyar can Basmah,ɗazu da naje sasan gaida Baba Sani ban ga kowa cikin su bane,dana tambayi Umma sai cewa tayi basa nan wai sai gobe da safe za su dawo ma,ni kuma na sha alwashin kafin in bar garinnan sai naji yadda akayi ta Ƙulla alaƙar soyayya da Nass har ga shi an sanya musu ranar aure,wannan ai cin amanace kuma ni a yadda tunanina ya bani koda ace baku rabu don mahaifiyarsa ta nuna ƙinki ba,dama can suna da wani manufa na son cin amanarki ne kawai."
TAIMIYYAH wacce take ta faman kauda kayayyakin gift data fara samu, ta dubi Yasmeen tana cewa, "Yasmeen wallahi bana son jin zancen Basmah da Nass a yanzu,sabida na sanyasu cikin wani littafi na daban na kulle dukkanin shafukansu,idan har zan iya baki shawara kema ki ɗauka to don Allah kada kiyi mata maganar koda wasa,matuƙar ba fatan alkhairy kawai zaki yi ki kulle bakinki ba,kinsan meyasa nace haka?"
Yasmeen ta girgiza kai alamun bata sani ba,TAIMIYYAH ta cigaba da faɗin, "Sabida babu wani amfanin yin maganar ko neman ƙarin haske,don komi ya riga ya faru Yasmeen, yanzu ana zancen irga kwanakin zuwan ranan aurene,don haka ni na daɗe da sallamawa tare da cire duk wani soyayyar Nass da yai saura cikin zuciyata.Na barwa Allah komi idan har da zuciya biyu aka ƙulla wannan al'amarin ina roƙo Ubangiji yayi min sakayya da sauyi mafi alkhairy cikin rayuwata,tunda na rasa su Abie na cigaba da rayuwa cikin godian Ubangiji,to na riga na sawa raina babu wani mahaluki da zai shigo ya fita cikin rayuwata da bazan iya jure rashinsa ba,tabbas na so Nass irin soyayyar da ban taɓa tunanin zan yi wa wani ɗa namiji ba,na kuma ji ciwon wannan lamarin fiye da tunaninki Yasmeen,amma a yanzu ji nake yi komi ya wuce har bani son tuna cewa wata alaƙar soyayya ya taɓa shiga tsakanina da shi,tun daga randa aka raba goran sanya ranar aurensa da Basmah na sake sallama cewa Nass ya riga da ya fita cikin rayuwata,don haka kema ina so ki kife duk wani babi nasa. Wannan lamarin ya daina baki mamaki tunda a duniya muke,duniyar ma irin wacce ake cikin wata rayuwa na son rai da fifita son zuciya,don haka kome akace ya faru mu daina mamaki Yasmeen...."
TAIMIYYAH ta dakata da maganar tana duban yadda Yasmeen ta tsura mata ido babu ko ƙiftawa.Sai ta saki smile tana cigaba da cewa, "Yasmeen duk wannan kallon fa?"
Yasmeen ta sauke numfashi kafin tace, "Hmm! Am Speechless TAIMIYYAH,ban san