Showing 87001 words to 90000 words out of 186776 words

Chapter 30 - TAIMIYAH Book Complete Document by Ayshat Dansabo Lemu .txt

15 Dec 2024

6583

ba,karka damu zamu samu abin hawan da zai maida mu gida,kuma karka damu da abinda Mum ɗinka tayi,gara data bayyanar da ƙiyayyarta don rabaka da abinda take ganin bai dace da kai ba,abu ɗaya ya ɓata raina yadda taci fuskan TAIMIYYAH agaban idanunta.Miye aibun Bawa don Allah ya jarabcesa da wata Nakasa da har zai zama abin muzantawa,da gudun a haɗa zuri'a da shi? Don haka kayi haƙuri tun yanzu ka fara yi mata biyayya akan raba hanyarka da gurguwa,musaka kamar yadda ta kira TAIMIYYAN,tun ayau ma kasawa zuciyarka cewa baka taɓa sanin Zainab ba,mun gode da soyayya daka gwadawa TAIMIYYAH a baya."


Yasmeen ta ƙare maganan tana sake jan hannun TAIMIYYAH suka matsa daga gaban Nass.Dai-dai kuma lokacin da wani me Napep ya tsaya a gabansu,Yasmeen bata jira komi ba ta tura TAIMIYYAH suka shige ciki tana baiwa me Napep ɗin umurni yayi maza ya ja su bar wajen.


Nass daya ƙariso wajen dai-dai lokacin da Napep ɗin ya harba bisa titi sai kawai ya samu kansa da dafe kansa zuciyarsa na tsananin bugawa da wani irin tashin hankali mara misaltuwa.Koda ya koma cikin motarsa kifa kansa yayi akan styering motar zuciyarsa na tsananin zafi da ƙuna, ya ɗauki lokaci me tsawo kafin ya tada motar don bin bayansu TAIMIYTAH.Sabida baya ji akan wannan dalilin na Momy zai iya janyewa ya bar abinda zuciyarsa ke tsananin so.


Daga cikin asibitin kuwa Hajiya Hajarah ce ke cigaba da nunawa ƙawayenta cewa ko sama da ƙasa zasu haɗe ne ba zata taɓa bari Nass ya auro mata Gurguwa a matsayin Suruka ba.Tunda ba ita bace uutar mata akwai lafiyayun ƴan mata da suka zarta TAIMIYYAN a kyawu da cikar halitta inma kyawun nata ne ya ruɗe Nass ɗin.


Ita dai Hajiya Murja da ranta ya gama ɓaci tashi tayi tana ɗaukar jakanta tai sallama da su Hajiya Malliya masu ziga Hajiya Hajaran.Ta fito daga ɗakin zuciyarta cike da tausayin yaran,har tana ji a ranta cewa da tana da ɗa namiji da tabbas sai ta saka shi ya auro mata TAIMIYYAN a matsayin surukarta.Ko don ta nunawa Hajiya Hajara cewa ita ɗin jahila ce da take gudun me lalura har take son yiwa Allah isgili,har ta shiga motarta ta ja abinda akaiwa su TAIMIYYAH na tsaya mata arai matuƙa don ita haka kawai yarinyar ta shiga ranta tare da jin tarin tausayinta akan jarabtan da Allah yai mata.


Tana tuƙine amma hankalinta na kan tunanin su TAIMIYYAH.Hakan yasa ta ɗauki wayarta tana kiran layin Nass tare da sanya wayan a speeker.Bugu biyu ya ɗaga yana faɗin, "Hello! Anty."


Hajiya Murja ta furta, "Naseer kana jina,kuna tare da yaran ne yanzu?"


Nass ya girgiza kai kaman Hajiya Murjan na dubansa kafin yayi magana murya cike da damuwa yake cewa, "Wallahi Anty sunƙi yadda su shiga motata na maida su gida.Napep suka tare suka hau amma gani akan hanya zan bisu har gida domin basu haƙury,a gaskiya Mama ni bata kyauta min ba ta muzantani da yawa tare da cin fuskar Zaynab.Ni sam banga aibunta ba don ta kasance gurguwa Anty."


"Karka damu ka bisu ɗin har gida ka basu haƙury,tabbas Hajiya Hajarah bata kyauta ba amma karka damu idan yarinyar rabonka ce sai ka ga ka sameta,amma koni ce a yau naji tozarcin da akai musu wallahi bazan bari ta aureka ba.Don uwarka sam bata yi anfani da kalamai na ilimi ba sai na jahilci,ai duk wanda Bawa ya gani da wata nasaka kamata yayi yasan cewa Allah ne yaso ganin wannan Bawan nasa a haka,ba shine ya siyowa kansa ba.Don babu Ɗan Adam da zai taɓa zaɓarwa kansa wata nakasa da gangar,amma bakomi ta haifa ai itama kuma Ubangiji baya gama yiwa bawansa halitta har sai randa ya koma zuwa garesa.Sam banji daɗin abinda a kaiwa Yarinya me hankali da tarin nutsuwa haka ba,ban ji daɗi ba Naseer."


Hajiya Murja ta kai ƙarshen maganan muryarta na sake bayyana irin ɓacin ran da zuciyarta ke ciki.Nass ya sauke ajiyan zuciya me ƙarfi yana faɗin, "Wallahi Anty nima ban ji daɗi ba,kar kiso ki ji yadda zuciyata ke ƙuna .Wallahi ina son TAIMIYYAH bana ji kuma zuciyata zata jure rashinta,kuma itama ta kamu da so na Anty meyasa Mummy za ta yi min haka?"


Nass yayi maganan cikin rawar murya karon farko kuma da yaji cewa ina ma Anty Murjan ce ta kawo shi duniya,tunda zata iya goya masa baya ya samu cikar burinsa.Da ƙyar Hajiya Murja ta kwantar da hankalisa sukai sallama da Nass ɗin akan duk yadda sukayi da su TAIMIYYAN ya kirata ya sanar mata........✍🏻








Littafin TAIMIYYAH paid book ne,ga duk wanda ta tsincesa a kowani irin group ne,kiji tsoran Allah karki karanta sai kin biya 500 naira only.


Za ku iya min magana ta wannan number ɗin 08167768704, ko kuma ku turo kuɗin ku kai tsaye ta wannan account ɗin 0504192664 aisha ibrahim dansabo GTbank.*


*Sai ku tura shaidan biyanku ta wannan line ɗin 08167768704.*


Masu turo credit za ku turo katin MTN na 500 ta wannan line ɗin 08167768704.




_Ina ƴan kasuwa masu buƙatar a tallata muku hajar ku? Maza ku garzayo da kuɗi ƙalilan a tallata muku kayan siyarwanku sai dai kawai ku ji ana kiran waya don buƙatan sayan kayan ku,ku tuntuɓeni ta layina kamar haka 08167768704._




#Ɗansabo ce#
[12/14, 10:09 PM] +234 703 769 7050: *Salamu alaikum! Ina ma'abota son ƙamshin su ke ne? Uwargida da Amare masu shirin shigewa daga ciki kai har ma da ƴan mata ma'abota son ƙamshi da ƙamsasa suturunku* *.To ga dama ta samu don kuwa shahararriyar mai saida turarukan wuta me asalin kyau da inganci wato RUUSCOLLLECTIONS ta zo muku da turarukan wuta na sawa a ɗaki wanda tun daga kunna shi baza ki taɓa jin ƙauri ba daga farko har karshensa.*
*Bata tsaya anan kaɗai ba don kuwa akwai jerin gwanon kalolin turarukanta masu ƙamsasa jiki da gida haɗi da ɗakuna ma baki ɗaya kamar haka* 👇🏻


*Akwai oil koleccha,da cream koleccha,Body butter, white humra,attraction humra, Mehlab humra, Dufr humra, brown humra, oil humra, golden humra da yellow humra,*
*Turaren wuta dinta kuwa Arabian black bakhoor mai kamshin harami, yemani bakhoor, hemani flakes, sandal rose, sandal flakes, Arabian spices, Senegalese kajiji, Couscous, special kajiji, Golden sand, wardrobe balls, Ruus Remix, Exclusive Dufr, cotton candy, Queen of the night, Bukhur, Alajab.*


*Akwai airfreshner, morphing mist, shampoo, hair cream, Vaseline.* *Harma da su atamfofi, less, shadda, takalma da mayafai duk zaki same su a wajen RUSS COLLECTION .*


Za ku sameta a Garin Kano ta wannan adireshin:- No:221 sarari koki quaters.


Ko ku nemeta a garin Kaduna a Unguwar kanawa.


ga handle ɗinta na Instagrm kamar haka👇🏻
@ Ruuscollections


Ga kuma lambar wayarta don kiranta kai tsaye 👇🏻


07025393114




*37*


"Lafiya TAIMIYYAH zaku shigo min kina faman rasgar kuka,Uwar Naseerun ta mutu ne halan?"


Iyah ke wannan maganan lokacin da TAIMIYYAH ta shigo cikin falon tana kuka sosai.Ta zube a jikin Iyah tana cigaba da kukan ba tare da tace komi ba,har zuwa lokacin da Yasmeen ta shigo falon,don ita ta tsaya biyan me Napep ɗin daya kawo su kuɗinsa.Allah yaso ita ta fita da kuɗi a jakarta,tana ko ƙarisowa cikin falon Iyah ta jefa mata tambaya tana cewa, "Ke Yasmeen mutuwa Uwar Naseerun tayi TAIMIYYAH ta shigo tana wannan uban kukan,ko kuwa meyafaru a Asibitin daga zuwa dubiya?"


Yasmeen tayi wurgi da gyalenta akan kujera tana faɗin, "Ai Iyah bama abinda bai faru ba,ban taɓa ganin jahilar mata irin Mum ɗin Nass ba...."


A hankali Yasmeen ta zayyanewa Iyah yadda Hajiya Hajarah taci mutuncin su,ta ƙare maganan da faɗin, "Wallahi Iyah na so rufe ido inci mata mutunci amma sai taci albarkacin son da ɗanta yakewa TAIMIYYAN da zuciya ɗaya,amma duk da haka na gasa mata magana,kuma insha Allah TAIMIYYAH zata rabu mata da ɗanta tunda ba shi ne autan maza ba."


Iyah da ranta ya gama ɓaci tayi ƙoƙarin danne ɓacin ranta tana faɗin, "Abinda ya faru kenan to madallah ta kyauta,ta kuma yi da jinin Fatima tunda ta nuna ita bamai ilimi bace to ta kwantar da hankalinta,gurguwa ba za ta zama Surukarta ba koda ace Naseerun shi ne autan maza.Ke kuma ba kuka zaki zauna kina yi ba sai ki godewa Allah da magana ma bai je kunnin Iyaye ba, ki rabu mata da ɗanta cikin ruwan sanyi Allah zai kawo miki wani wanda zai ƙaunaceki, ɗan gidan mutunci da iyayensa suka yadda cewa nasaka ba kasawa bace kuma Ubangiji ke halittan Bawa ya aje sa yadda yaso ganinsa,don haka bana son ki sake zubda hawayenki akan abinda ya faru,shi kuma Allah ya cire masa soyayyarki da gaggawa,don ba shi ikon yiwa uwar tasa biyayyah."


Iya ta kai ƙarshen maganan tana ɗago kan TAIMIYYAH daga jikinta ta share mata hawayen da ke zuba a face ɗinta.Kafin wani ya sake magana a cikin su sallaman Tukur ya shiga kunnuwansu,Iyah ta amsa sallaman tana tambayansa lafiya? Ya sanar mata cewa Nass ne yace ai masa magana da Yasmeen.Iyah ta cewa Tukur ya je yace wa Nass ɗin ya shigo za ta yi magana da shi,daga haka Tukur ya juya don zuwa ya sanar da Nass ɗin saƙon Iyah.


Ita kuma Iyah ta waiwaya tana duban su TAIMIYYAH take faɗin, "Ku tashi ku shiga daga ciki don Allah TAIMIYYAH ki tsaida wannan kukan,tun kafin ki fusata zuciyata akan hakan,idan ta kushe halittarki tare da aibanta nasakan da Allah ya jarabceki da shi ina ce da Allah take yi ba ke ba ko? Tunda shi ne ya maida ki hakan ba siyo gurgurguntan kika yi kika mannawa ƙafan naki ba.Don haka ki sawa zuciyarki salama ki kuma baiwa kanki ƙwarin guiwan cire soyayyar ɗanta a ranki."


Iyah ta ƙare maganan tana tsuke fuska don ko kaɗan bata son TAIMIYYAH ta raunata zuciyarta akan abinda Mum ɗin Nass ɗin tai musu.Yasmeen ta ɗauki jakarta da gyalenta suka jera da TAIMIYYAH zuwa ɗakinsu,dai-dai lokacin da Nass yai sallama daga bakin ƙofar ɗakin Iyah.


Iyah ta amsa sallamarsa tana bashi umurnin shigowa.Ya shigo ya zauna kansa a ƙasa yake gaida Iyah ta amsa cikin sakin fuska, ba tare da ta nuna masa ɓacin ranta akan abinda akaiwa jikokin nata a asibiti ba.
Nass ya fara da baiwa Iyah haƙury akan abinda mahaifiyarsa tayi ya ƙare maganan da cewa, "Don Allah ayi haƙury wallahi ban san abinda zai faru kenan ba da ban ɗauke su na kaisu ba,kuma ban taɓa tunanin cewa don Zaynab na da lalura Mummy zata nuna ba za ta amince da ita ba."


Yayi maganan muryansa na bayyana tsananin ɓacin ran da zuciyarsa ke ciki.Iyah ta ɗago ta dube shi kafin ta soma faɗin "A gaskiya Naseeru idan nace raina bai ɓaci akan cin mutuncin da akaiwa wannan Yarinyar ba nayi ƙarya,sai dai naji daɗi da mahaifiyarka ta nuna ƙiyayyarta da wuri ba tare da maganan tarayyanku da juna yaje kunnin manya ba,don haka abinda yafi shine ku haƙura da juna tunda ba zai yiwu ace ka bijirewa mahaifiyarka ka cigaba da son wacce ba za ta amince ku auri juna ba.Ka ga hakan zai zama ɓatama kai lokaci kenan,ina fata zaka haƙura da son da kake wa TAIMIYYAH ka samu wata lafiyayyar mara nakasa don gudun ɓacin ran Uwa.Na gode da ƙaunar daka nunawa jikata ina fata Allah ya musanya muku junanku da mafi alkhairyn abokan rayuwa."


Tunda Iyah ta fara magana jikinsa Nass yai mugun sanyi.Kamar yadda zuciyarsa ke cigaba da tsananin bugawa da matsanancin fargaba,ya rintse idanunsa yana jin ƙarshen hukuncin Iyah na girgiza duk wani kafar sadarwa na jikinsa.Cikin rawar murya yake faɗin, "Iyah don Allah kiyi haƙury kar ayi anfani da abinda Mummy tayi ace za a kawo ƙarshen alaƙar soyayyar da ke tsakanin mu da Zaynab,wallahi ina tsananin sonta da dukkanin zuciyata,in dai Mummy ce zan yi ƙoƙarin shawo kanta ta amince da ita tunda nine nace na ji na gani zan aureta a yadda take, don ita nake so ba jikinta ko halittar da Allah yai mata ba,don Allah kar kice in bar ta bazan iya ba."


Nass yayi maganan cike da magiya yana zube guiwoyinsa a ƙasa,cike da magiya ya cigaba da roƙon Iyah akan kar a ce za a raba shi da TAIMIYYAH.Iyah bata katse shi ba har sai da ya dakata don kansa,sannan ta ɗago manyan idanunta tana dubansa cike da tausayin Nass ɗin ta fara faɗin, "Naseeru bana so muyi jayayya da kai,karka yaudari kanka akan cewa zaka iya shawo kan mahaifiyarka sai ta baka goyan baya ka auri abinda bata so.Tunda har ta nuna nakasan TAIMIYYAH shine abinda zai sa ba za ta iya bari ta zama surukarta ba,to ka sani ko ka auri Zainab ba za ta samu soyayyah a wajen mahaifiyarka ba,kaga kenan za ta rayu cikin ƙunci ne da tsangwaman Uwar miji.Wanda ni bana mata fatan hakan don da ina mata sha'awar hakan da yanzu maganan aure ya yi ƙarfi tsakaninta da Yayanta da ke son ta da Zuciya ɗaya...."


Cikin sukuni Iyah ta sanar da Nass irin soyayyar da Yah Sadeeq ke wa TAIMIYYAH,da irin ƙiyayyar da Umma ke mata ta ƙare maganan da faɗin, "Don haka kayi haƙuri Allah ya haɗaka da wata a gaba,TAIMIYYAH marainiyace a yanzu da bata da uwa bata da uba Allah ne gatanta nice gatanta, don haka ina raye bazan taɓa bari ta shiga inda ba a buƙatarta ba,ka sawa ranka Allah bai jarabceku da soyayyar juna don ku mallaki juna ba,Allah yai muku zaɓi mafi alkhairy ita kuma uwarka Allah ya ganar da ita gaskiya."


Daga haka Iyah bata sake baiwa Nass daman magana ba,ta sallame shi ya bar ɗakin hawaye na zarya a face ɗinsa,ko gabansa baya gani da kyau lokacin da ya fito daga Sasan Iyan, har ya kai kansa wajen mota jin zuciyarsa yake tamkar zata fashe.


Daga cikin Sasan Iyah kuwa TAIMIYYAH da ke laɓe tana sauraren duk yadda Iyah suka yi da Nass,sai kawai ta juya ta koma ɗaki tare da faɗawa gado ta saki kuka me cin rai.Tana son Nass ƙaunarsa ya riga ya kama zuciyarta da gasken-gasken ta yadda bata iya tunanin zata iya cire son nasa nan kurkusa.
Amma ita da kanta bata ga aibun hukuncin Iyah na dagewa akan su haƙura da juna ba,don itama tana ji ko soyayyar Nass ɗin zai zama ajalinta ba za ta amince ta cusa kanta a muhallin da za a dinga aibanta halittarta ba.
Ba za ta iya auren Nass alhali mahaifiyarsa ta rufe ido ta iya mata irin wannan cin mutunci da cin fuskar ba.
Kuka take yi me asalin motsa zuciya.Yasmeen da ke sauraran kukan ranta na sake ɓaci tayi magana cikin muryan da ke nuna har lokacin a sama take tana cewa, "To wannan kukan wai na mene ne shi TAIMIYYAH,kukan ba za ki iya cire sonsa a ranki bane ko kuwa na miye ?"


TAIMIYYAH ta ɗago manyan idanunta da suka fara canza launi ta sauke akan Yasmeen, cikin muryan kukan take faɗin, "Yasmeen ina kuka ne sabida zuciyata za ta rabu da abinda take so,da gaske soyayyar Nass tayi wa zuciyata mugun kamu,meyasa mahaifiyarsa zata min haka? Miye aibuna don na kasance gurguwa? Yasmeen ban taɓa jin ɗacin kalmar gurguwa idan an kirani da shi irin yau ba,yau ɗin da kalmar ya fito daga bakin wacce ta kawo abinda zuciyata ta kamu da soyayyarsa duniya.Amma ko soyayyar Nass zai zama ajali na zan haƙura da shi har abada,zan yi duk iya ƙoƙarina wajen danne shi a can ƙarƙashin zuciyata domin bazan iya cire soyayyarsa farat ɗaya daga ƙirjina ba...."


Kuka ne yaci ƙarfin TAIMIYYAH har ta kasa ƙarisa kalamanta, sabida yadda zuciyarta ke asalin ƙuna.
Wayarta Nass ke ta faman kira babu ƙaƙƙautawa amma TAIMIYYAH ta kasa ɗauka ,don bata san me zata ce ba idan ma ta ɗaukan,hakanan ya yi ta kira har ya gaji ya turo saƙonni.
TAIMIYYAH na gama duba saƙonnin masu ɗauke da kalamai na ban haƙury da magiyan cewa ta ɗaga kiransa,sai kawai ta kashe wayan ma baki ɗaya tare da sake kifa ciki akan gado tana cigaba da kuka.


Kiran Anty Laurat ne ya shigo wayan Yasmeen,sai ta ɗaga wayan suka gaisa Anty Laurat ta fara koro mata ƙorafi akan meke faruwa tsakanin TAIMIYYAH da Nass? Don ya kirata har ta ji alamun ma kuka yake, yana sanar da ita cewa ta kira TAIMIYYAH ta roƙe ta akan ta kunna wayarta.
Ita kuma ta kira wayan TAIMIYYAH ta ji a kashe yake shine ta kira Yasmeen ɗin yanzu.Yasmeen ta numfasa bayan ta gama jin jawabin Anty Laurat ɗin,kafin ta fara zayyane mata duk yadda suka yi da Mum ɗin Nass a Asibiti.Ta ƙare maganan da cewa, "Anty Laurat na san ko kece akai haka akan idanunki ba za ki goyawa TAIMIYYAH baya ta cigaba da sauraran Nass ba,domin hakan bai da wani alfanu tunda akan idanunmu ta furta cewa abin kunya ne a wajenta ɗanta ya auri gurguwa.Don haka Ya yi haƙury TAIMIYYAH ba za ta sake sauraransa bare har ya cigaba da raunata zuciyarta,Allah ya haɗa shi da wata a gaba ita kuma Allah ya kawo wanda ƴan uwansa da iyayensa zasu amshe ta a yadda take.Babu gorin halitta bare tsangwama,Iyah ma ta gama magana ta sanar da shi cewa TAIMIYYAH ba za ta taɓa aurensa ba tunda har Uwarsa ta nuna bata amince da ita a yadda Ubangiji ya amince ta kasance ba."


Daga haka Yasmeen ta kashe maganan Nass a wajen Anty Laurat,wacce itama taji ciwon abinda ya farun.Tausayin TAIMIYYAH da na Nass ya cika zuciyarta don ita shaida ce akan cewa TAIMIYYAH ta kamu da son Nass,don shi irin mazannan da suka iya kula da abinda su ke so,amma sai tayi musu addu'an Allah yasa hakan ya zame musu alkhairy.


Kwanaki biyu da suka biyo bayan wannan ɓacin ran, TAIMIYYAH tayi matuƙar ƙoƙarin danne zuciyarta da nuna cewa komi ya wuce a idanun Yasmeen da Iyah.Amma daga gefe guda kullum sai ta tashi cikin dare ta sha kukanta ma'ishi,daga ƙarshe ta ɗaura alwala ta gabatar da sallah,ta roƙi Ubangiji akan ya cire mata soyayyar Nass daga zuciyarta.
Ga kuma maganan rabon gadon Abie da ya sake jefa zuciyoyin su TAIMIYYAH cikin alhini da sallamawa cewa da gaske dai sunyi babban rashi na har abada.
Don su Baba Sani basu dawo gari ba sai da suka tattaro duk wasu muhimman takaddu na kadarorin da Abie ɗin ya mallaka.Hatta da takaddun shaidar mallakan gidansu na can Lagos

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login