Showing 99001 words to 102000 words out of 186776 words
Chapter 34 - TAIMIYAH Book Complete Document by Ayshat Dansabo Lemu .txt
ce na matsa saina dawo yau ɗin,amma dana biyewa Yasmeen da Guggo Bilki aida sai na ƙara sati."
Ummie ta saki murmushi tana faɗin, "Gaskiya kin bamu kewa ni duk sai na ji gidan shiru,don ma yanzu su Basmah kan shigo min hira."
TAIMIYYAH ta zauna daga kujeran kusa da Ummien suka fara taɓa hira,don yanzu Ummien sosai take sakar mata fuska da son janyota ajiki,ba kaman lokacin da Abie ke raye da sam bata wani sakar mata fuska sosai ba.Amma a yanzu tana nuna kulawa akanta sosai har abin na baiwa TAIMIYYAH mamaki.
Ita ko Ummie tsakaninta da Allah yanzu son TAIMIYYAN ya shiga ranta, musamman data rasa nata ƴaƴan da mijinta,TAIMIYYAN itace kaɗai jinin Sameer da take gani taji sanyi a zuciyarta yanzu,shiyasa take jin ƙaunarta har cikin zuciyarta.
TAIMIYYAH ta daɗe sosai a sasan don ta saki jiki ana ta hira da Inna Larai,wacce take da yawan barkwanci da wasa da dariya,shiyasa take da daɗin zama sosai.
Lokacin da TAIMIYYAH zata fito daga part ɗin Ummie, su kuma su Zuhurah sun iso zasu shiga kenan,sai TAIMIYYAH ta basu hanya tana cewa, "Zuhurah sannun ku Yasmeen tace tana gaishe ku."
Ga tsananin mamakin TAIMIYYAH sai ta ga sun amsa ta cike da fara'a suna tambayarta yaushe ta dawo? ta basu amsa cewa ɗazu da rana ta iso.
Suka wuce ta zuwa ciki ita kuma ta juya ta fara takawa don komawa Sasan Iyah,koda ta shiga ta samu Iyah ta dawo suna zaune da Babah Ladi a falo suna hira.Itama TAIMIYYAH sai ta zauna aka cigaba da hiran da ita,kafin shigowan kiran Yasmeen yasa ta tashi ta nufi ɗaki suna waya,inda Yasmeen take sanar da ita wai Yah Emran har ya amsa lambarta wajen Yasmeen ɗin,shine ta kira taiwa TAIMIYYAH tsiya akan kodai ta tafi da zuciyar Yayan nasu ne? TAIMIYYAH da takaici ya isheta sai kashe wayarta tayi baki ɗaya ta zauna daga gefen gado,ta dafa goshinta tana jin wani matsanancin ɓacin rai na lulluɓe zuciyarta.
'Me yake nufi da amsar lambarta wajen Yasmeen,me xai ce mata idan ya kirata?"
Waɗannan tambayoyin suka dinga damun zuciyar TAIMIYYAH,tunaninta na komawa kan abinda ya faru tsakaninsu kwana ɗaya daya wuce.Sai ta samu kanta da zubda hawayen da ba za ta iya tantance asalin dalilin zubansu ba,ta rasa tsakananin kalamansa na raini da nuna ƙasƙanci ga nakasan dake tare da ita daya furta,da kuma abinda yai mata na son keta alfarmarta wanne yafi yi mata ciwo a zuciyarta? Ta kai hannu tana share hawayen zuciyarta na wani irin zafi da ƙuna,duk inta tuna dangantar dake tsakaninta da shi,da yadda ya iya yi mata abinda yayin,sai taji zuciyarta ya raunana, wani tsoro na lulluɓe ruhinta baki ɗaya.
Tana jin ciwo a zuciyarta,da tsoron anya ko zata samu wanda zai so ta tsakani da Allah har tayi aure wataran, kamar yadda su Iyah ke kwaɗaita mata? Tarin tunanin da suka dinga cinkushe kwanyarta da zuciyarta kenan,har lokacin da aka kira sallah sannan ta iya miƙewa ta nufi toilet.
"Yah Zuhurah mutumiyan namu na ga duk ta sake wani sanyi ne,da alamu ta gama saka rai da zata mallaki handsome Nass ɗinta ne,sai kuma uwarsa tai mata cikas, wallahi duk na ƙosa akai stage ɗin da zai tako ƙafarsa gidan nan ayi me kankat ɗin.Kin san yanzu lallaɓashi nake tayi muna chart tamkar babu wata manufa a zuciyata akansa,nuna masa nake yi ina bala'in tausayinsu daga shi har gurguwar tasa,shiyasa ya saki jiki dani har yake sanar dani irin tarin damuwan da yake ciki akan rabuwarsa da TAIMIYYAN.
Ashe wai uwarsa ce masa tayi ko a waya ya kirata bata yafe ba,don tafi so kwata-kwata ya shafe babinta a zuciyarsa.Amma fa da gaske ba ƙaramin so yake wa TAIMIYYAH ba,zan yi aiki kafin in mantar da zuciyarsa ita koda na mallakesa."
Basmah ce ke wannan maganan suna zaune tare da Zuhurah a falonsu,bayan sun kammala cin abincin dare.
Zuhurah ta ɗaga kai ta kalli Basmah tana cewa, "Ai baki sani ba,TAIMIYYAH yadda kika san tana da wani magic na farin jinine a tare da ita,ki duba kiga yadda babu wuya ta shiga ran mutane,shiyasa ai duk wanda zai so ta ba zai mata so na wasa ba,nima duk na ƙosa in ga yadda waɗannan idanun nata za su yi randa ta ganki da Nass ɗin,ba dai jibi Umma za ta tafi bikin ba,sai mu jira dawowarta mu ga yadda za a kaya.Nima cikin wata satin Ameeru yace iyayensa za su turo a tsaida lokaci kawai."
Basmah tayi wani farr...! Da ido tana cewa, "Wow! kinga idan lokacin an tunkuɗomin ƙeyarsa mun jone sai kawai a sanya lokaci ɗaya ayi bakinmu tare a huta kawai,tunda shi Yah Sadeeq ya ƙi wa Umma hannu har yau bai je wajen Nadeeyan ba bare a san abinyi."
Ta ƙare maganan da taɓe baki Zuhurah kuma ta sanya dariya,suka cigaba da tattauna yadda zasu ƙuntata zuciyar TAIMIYYAH duk randa ta gane cewa Basmah ta kwace mata Nass ɗinta.
Basmah ta lumshe idanunta azababben soyayyar Nass ɗin na sake kama zuciyarta.Tana kuma sake jinjina wayonta da kaifin ƙwaƙwalwanta, na yadda aka yi ta janyo hankalin Nass har ya saki jiki da ita.
Ta shiga tuna yadda tayi ta nuna masa cewa, ta ɗauke sa tamkar matsayin Yayanta ne tunda yana son TAIMIYYAH.Koda wasa bata taɓa nuna masa cewa suna da ƙiyayya da abar sonsa ba,sai ma nuna masa da take yi kullum cewa kar ya cire rai da samun TAIMIYYAN.......✍🏻
_Lallai Basmah kinyi ƙoƙari inji Ɗansabo,shiyasa aka ce ka rabu da mutum kawai inda ka gansa,sheɗancin wasu mutanen yafi gaban kwatance,to masu karatu kunji ta inda Basmah ta ɓulla har ta fara samo hankalin Nass yana magana da ita,ko me zai faru a gaba? Sai mu cigaba da bin labarin sannu a hankali don jin cikakken ya rayuwar TAIMIYYAH zai kasance baiwar Allah_ 😰
#Ɗansabo ce#[12/14, 10:10 PM] +234 703 769 7050: *Littafin TAIMIYYAH paid book ne,ga duk wanda ta tsincesa a kowani irin group ne,kiji tsoran Allah karki karanta sai kin biya 500 naira only.*
*Za ku iya min magana ta wannan number ɗin 08167768704, ko kuma ku turo kuɗin ku kai tsaye ta wannan account ɗin*👇🏻
0504192664 aisha ibrahim dansabo GTbank.
*Sai ku tura shaidan biyanku ta wannan line ɗin 08167768704.*
Masu turo credit za ku turo katin MTN na 500 ta wannan line ɗin 08167768704.
_*Ina ƴan kasuwa masu buƙatar a tallata muku hajar ku? Maza ku garzayo da kuɗi ƙalilan a tallata muku kayan siyarwanku sai dai kawai ku ji ana kiran waya don buƙatan sayan kayan ku,ku tuntuɓeni ta layina kamar haka 08167768704.*_
*43*
*Kano*
Kwance yake akan gadon ɗakinsa idanunsa duka a rufe, babu abinda zuciyarsa da gangar jikinsa ke kwaɗayi irin ya ji ɗumin jikin TAIMIYYAH a cikin jikinsa.
Gaba ɗaya tunda ya ɗaura ido akan tsiraicinta, hannuwansa suka jiye masa laushin fatarta,sannan bakinsa ya ɗanɗano masa wani irin ɗanɗano me garɗi a mounth ɗinta ,ya rasa dukkanin sukuni da nutsuwanrsa.
Ya fi kowa sanin sabida shine TAIMIYYAH ta tattara ta bar garin baki ɗaya, don ta tsorata da maitarsa da ya fitar a fiki akanta.Ya buɗe idanunsa yana Janyo wayansa tare da zubawa lambobin wayarta ido,wanda tun ɗazu yake gwada kiranta,amma sai yaji ya kasa don bai san me zai ce mata ba idan ya kira ɗin.
Gabaki ɗaya tunda ta bar garin kaman ana sake ninka masa, sha'awan son kasancewa da ita ne.Duk neman matansa bai taɓa jin kwaɗayin mace irin na yau ba,kuma babu wacce yake ji zata iya kashe wutan dake ci a zuciyarsa sai TAIMIYYAH.
Ya sauke wani numfashi me zafi maransa na sake wani irin ɗaurewa, tsabagen wutar jaraba dake cin zuciyarsa.Ya cije lips ɗinsa yana shahadan danna mata kira, tare da fatan ta ɗauka ko muryanta ya samu ya ji ko zai samu relief.
Sai dai har kiran ya gama ɓurarinsa ya tsinke ba a ɗaga wayar ba.Sai kawai yayi jifa da wayar yana tashi da ƙyar ya nufi toilet,bai jima ba ya fito yana nufan ƙofar fita daga ɗakin baki ɗaya,don zuwa ya haɗo tea me lemon ko zai rage masa nauyin da maransa yayi.
Zuciyarsa na kimsa masa tunanin akan kawai ya samu Mamie a gobe, ya sanar mata cewa ya amince zai iya auren TAIMIYYAH.
Har ya kai part ɗin Mamie tunanin dake yawo cikin kansa kenan....
___________
*Zee Town (Zaria)*
TAIMIYYAH na zaune tana danna system ɗinta, a lokacin da kiran Emran ya shigo wayarta.
Tunda kuma ta ɗauki wayar ta ga baƙuwar number ta ji a jikinta cewa shine,shiyasa ta share kiran bata ɗauka ba har ya tsinke.
Ta saki ƙaramin tsaki tana saka wayan a fly mode, ta cigaba da abinda take yi zuciyarta cike da ɓacin ran rainin hankalin da ke son shiga tsakaninta da Yah Emran ɗin.
Har ta gama abinda take yi ta kashe system ɗin, don yin shirin kwanciya barci zuciyarta bata daina tunani,akan abinda ya shiga tsakaninta da shi ba.
Lokacin data ɗauro alwala don kwanciya bacci, sai da ta gabatar da sallar wuturi kafin ta nufi gado ta kwanta,bata ɗauki dogon lokaci ba bacci ya sure ta.
Washegary ya kama monday tunda wuri TAIMIYYAH ta tashi, don tana son ganin Baba Sani kafin ya wuce Kano wajen aikinsa.Shiyasa ƙarfe takwas ta isa Sasan su Umma ,a ɗakin Baba Sanin suka gaisa da Umma wacce ke fifita masa tea da zai sha.
Ya gama shirinsa tsaf yana zaune yana cin chips da aka soya masa,TAIMIYYAH ta tsuguna ta kwashi gaisuwa tana sanar masa da buƙatarta.
Baba Sani ya amsa cike da kulawa,yana me kai hannu cikin aljihunsa ya irgo adadin kuɗin da take buƙata ya miƙa mata.
Ta amsa tayi godia tana miƙewa ta fito daga ɗakin,Umma na biyo bayarta da mugun kallo.
Lokacin da ta shigo Sasan Iyah ta tadda har Iyah an sha wanka an fito karyawa.Ta saki murmushi a lokacin da ta isa gaban Iyah tana cewa, "Iyah barka da fitowa ina kwana."
Iyah ta dubi TAIMIYYAH da manyan idanunta tana cewa, "Lafiya lau Zainabu, daga ina kike da wuri haka?" TAIMIYYAH ta ɗan shagwaɓe face tana ba Iyah amsa da cewa, "Daga wajen Baba Sani na amso kuɗi ne kinsan yau an koma skull, ina buƙatan kuɗi a hannuna har zuwa sati me zuwa."
Iyah ta jinjina kai tana cewa, "Hakane amma da kin min magana ma na riga na tanadar miki kuɗin duk buƙatunki, kamar yadda Sameer ya saba turo miki lokacin yana raye."
TAIMIYYAH da mood ɗinta ya sauya, fuskarta ya nuna tsananin kewan Abie ɗin, ta dubi Iyah tana cewa, "To ai ban sani bane Iyah sabida shi yace min lallai duk abinda nake buƙata in dinga sanar masa."
Iyah ta jinjina kai tana cewa,
"Hakane babu laifi ai, yanzu yau ɗin zaki fara zuwa makarantar, ba zaki bari sai zuwa gobe ba?"
TAIMIYYAH tayi saurin duban Iyah tana cewa, "Sai gobe zan fara zuwa tunda yau aka koma, bama lallai kowa ya je a yau ɗin ba,don Zee cewa tayi ma sai zuwa Wednesday za ta fara zuwa."
"A toh nima dai haka na gani gara ki bari zuwa goben,kin sake hutawa ma."
Cewan Iyah tana faman cin soyayyan dankali da egg da Babah Ladi ta soya,ta cika cup da kunun gyaɗa daga gefe guda.
TAIMIYYAH ta fara takawa don komawa ɗakinta,tana cewa Iyah, "Iyah bari in koma in kwanta zuwa tara zan tashi,yau ni zan yi mana girkin rana idan na gama kwaleman ɗakina."
Iyah ta bi bayanta da kallo tana cewa, "To madallah a tashi lafiya,sai Ladi ta taya ki kwaleman don rage miki wani wahalan."
Ita dai TAIMIYYAH tuni ta shige ɗaki abinta,kuma tana aje kuɗin da ke hannunta kwanciyar tayi,don da gaske baccin take son komawa.
Sai ƙarfe tara da rabi sannan ta tashi ,ta yo wanka ta shirya cikin doguwar riga mara nauyi na material,bata shafa komi akan face ɗinta ba, ta fito zuwa falo don yin kalacin safe.
Lokacin da ta kammala karyawan Iyah ce taiwa Ladi magana akan ta taya TAIMIYYAH suyi kwaleman ɗakinta.
Hakan ko aka yi cikin lokaci kaɗan suka kammala,wanda rabin aikin Ladin ce kawai tayi ma,don taki bari TAIMIYYAH tayi komi,in banda shirya kayanta da tayi cikin drawer.
11:30am TAIMIYYAH ta wuce zuwa kitchen don fara shirin ɗaura musu lunch,sabida da wuri suke gama girkin rana su.
Tuwo Iyah tace tana so ayi amma na dawa da miyar Kukah,don haka TAIMIYYAH ta fara da ɗaura miyan ne kafin ta ɗaura ruwan tuwan.
Cikin nutsuwa da ƙwarewa take aikinta har ta kammala tuƙa tuwan, ya silala ta sauke don fara kulla su a leda.Koda Ladi ta shigo don taya ta wani abin ,sai ta amshi kulla tuwan ita kuma TAIMIYYAH ta ƙarisa miyan ta juye shi cikin cooler.
Store ta nufa ta ɗakko doya madaidaici ta feraye shi,don tana son yin Yam balls ne.
Bayan kammala feraye doyan sai ta wanke shi tas ta ɗauka a wuta.
Ta nufi wajen fridge ta ɗebo carrot da green pepe ta aje su a gefe,sannan ta ɗebo tattasai da tarugu haɗe da albasa me yawa duk ta gyarasu.
Zuwa lokacin da doyar ya dahu duk ta gama yanke-yanken da zata yi, nasu carrot da green pepe ta aje a gefe guda,sai ta tsane doyar a colander don barinsa ya huce.
Kafin doyar ya huce ta tafasa nama ta baiwa Ladi ta ɗan daka mata,sai ta juye doyar tasa whisker ta dagargajeshi.Ta juye su carrot da green pepe haɗe da kayan miyan da tai grating,ta zuba albasa me yawa da ta yanka, duk ta haɗe su cikin doyar da ta dagargaje ta zuba spices da maggi yadda take so.
Zuwa lokacin Babah ta kawo mata dakakken naman, shima ta juye akai ta saka hannu ta motsa, naman yabi ko'ina sannan ta fara mulmulasu zuwa shape ɗin balls.
Babah Ladi dai tsaye tayi kawai tana kallon yadda TAIMIYYAH ke kominta gunin sha'awa.
Bayan ta gama maida su balls ne ta fasa egg ta kaɗashi,ta zuba garin corn flour sabida idan aka saka corn flour egg ɗin yafi kamawa ya yi kyau sosai.
Tunda TAIMIYYAH ta fara suyan yam balls ɗin,qamshi ya cika ko'ina hatta Iyah dake falo sai da ƙamshi ya fitineta,ta gane cewa bayan yin tuwon dawan sai da TAIMIYYAH ta ƙirƙira yin wani abin kenan.
Tana kammala komi ta wuce zuwa ɗaki don gabatar da sallah.Babah Ladi ita ce ta ɗauki kulolin abincin ta kai falo, ta jere su inda a ke zaman cin abinci.
TAIMIYYAH ta idar da sallah kenan tana cikin ninke Hijab ɗinta, wayarta ya fara ring ta isa wajen wayar tana kallon sunan Yah Deeku dake rubuce a jikin screen.
Tayi receiving call ɗin tana saka wayar a speeker.Muryan Yah Sadeeq ya fito tar lokacin da yake furta,
"Hello! Baby kina jina?"
TAIMIYYAH ta zauna daga gefen gadon tana cewa, "Ina jinka Yah Deeku ina yini,kana lafiya?"
Sadeeq yace "Lafiya lau Zaynab kin dawo daga Kano ɗin ne ko kina can? Dis week ban samu shigowa weekend ba."
TAIMIYYAH ta ɗan shagwaɓe murya kaman yana gabanta tace, "Na dawo jiya Yah Deeku,ai tunda na ga ban ga motarka ba na san baka samu shigowa ba."
Sadeeq da ke sauraran muryarta yana jin nutsuwa na sauka a ransa, ya lumshe ido yana faɗin, "Eh Babe! Ban shigo ba yanzu me kike yi ina so ki hau online na tura miki wani pic ne ki gani,but idan kin gani ki gaya min gaskiya tayi ko bata yi ba,tunda ke an hana min ke bayan zuciyata har yanzu ke kaɗai take muradi."
TAIMIYYAH dake saurarensa ta sake yin ƙasa da muryarta tana cewa, "Okey Yah Deeku bari in hau online ɗin."
Sadeeq zai yi magana kenan ya ji tayi cuting call ɗin,sai kawai shima ya hau online ɗin.
Lokacin da TAIMIYYAH ta buɗe pic ɗin, idanunta ne suka sauka akan kyakykyawar fuskar budurwar dake jikin hoton,ta tsura hoton ido kaman me son gano haƙiƙanin kyawun budurwar.Sai kawai ta fara typing tana tambayar ya Deeku budurwansa ce? Dai-dai lokacin shi ma ya hawo online ɗin, ganin tambayar da TAIMIYYAH turo masa yasa shi murmusawa ya fara typing shi ma,yana bata amsa da cewa,
"Yes Baby tayi ko bata yi ba?"
TAIMIYYAH ta saki murmushi kaman yana gabanta,kafin ta tura masa cewa, "She's very cute Yah Deeku,gaskiya tayi Allah tabbatar da alkhairy."
Sadeeq ya karanta abinda tace, sai ya aiko mata da emoji na kuka yana rubuta cewa, "Baby daɗi ma kike ji zan rasaki ko kishi ma ba zaki nuna ba ko?"
TAIMIYYAH ta aika masa da emoji na dariya kawai, ba tare da tace komi ba.
Sai kawai Sadeeq ya sauka daga online yana kiranta vid-call,suka jima suna magana yana sanar da ita cewa sunan yarinyar Safiyyah.
Ƙanwar wani abokin aikinsu ne suna zaune a Badarawa Kaduna.
Ita dai TAIMIYYAH sai suka gama wayar fuskarta na blushing, don har cikin zuciyarta tayi farin ciki da Yah Sadeeq zai fitar da matar aure.
Tana kammala cin tuwan da ta zuba kaɗan,ta nufi kitchen ta ɗauki bowl ɗin da ta zubawa Ummie yam balls, ta fito zuwa falon Iyah.
Bowl ɗin ta aje tana ɗaukan wayarta, sannan ta dubi Iyah tana cewa, "Iyah za ni Sasan Ummie in kai mata yam balls ɗinnan."
Iyah ta dube ta tana cewa, "Madallah ki gaishe da Inna Larai."
TAIMIYYAH amsa tana yin gaba, hannunta ɗaya dafe da ƙafarta me laluran, ɗaya hannun riƙe da bowl ɗin da wayarta.
Babu kowa cikin falon Ummien lokacin da TAIMIYYAH ta shiga,sai ta aje bowl ɗin tana zama cikin seater, dai-dai lokacin da kira ya shigo wayarta.
Ta tsurawa lambobin idanu har kiran ya yanke bata ɗaga ba,wani kiran ya sake shigowa sai ta ɗaga tana kai wayan kunni.
Jin muryan Yah Emran yasa ta saurin yin hanging up,tana yin blocking lambar baki ɗaya.
Ta aje wayan mood ɗinta na canzawa,ɓacin rai ya mamaye zuciyarta.
Ummie ce ta fito daga ɗaki ganin TAIMIYYAH yasa ta ƙariso cikin falon, fuskarta ɗauke da murmushi take cewa, "Zaynab ke ce dama kika shigo shine kika zauna a falo, maimakon ki shiga har cikin ɗaki." TAIMIYYAH ta maida mata martanin murmushin tana cewa, "Laah! Ummie yanzu na shigo ba wai na jima bane,na tsaya amsa call ne,ga yam balls na kawo miki ɗazu nayi sa."
Ta ƙare maganan tana ɗaukan bowl ɗin yam balls ɗin ta kai gaban Ummien,lokacin da Ummien ke cewa, "Kai! Aiko kin kyauta Zaynab nagode sosai,ke kam kinji daɗi kina da son girke-girke, kala-kala baki ko jin wuyan aiki duk da laluran ƙarfar taki."
TAIMIYYAH ta saki smile tana cewa, "Haka kowa ke cewa bana jin wahalar aiki,wallahi kam bana ji indai har zan haɗa komi waje ɗaya shikenan,yawan kai kawo ne kawai ke sani inji