Showing 183001 words to 186000 words out of 186776 words
Chapter 62 - TAIMIYAH Book Complete Document by Ayshat Dansabo Lemu .txt
kuma ba zan sake yin kowace irin alaƙa da ita ba."
"In Sha Allah! Suhailah za mu taya ki ba Hajjah haƙury, kuma na ji daɗin yadda ki kai saurin gane kuskuren da kika so tafkawa,sai ki roƙi Ubangiji ya yafe miki don shi ne babban wanda ki kai wa laifi,tunda shi ki kai wa kishiya wajen yadda da cewa akwai wanda zai iya miki wani abu bayan shi. Don haka ki yi gaggawar tuba izuwa gare shi,Allah ya yaye miki duk wani zafin kishi da zai kai ki ga halaka."
Suhailah ta amsa da cewa, "Ameen." Cikin sanyin murya me nuna tsananin nadamar da zuciyarta ke ciki. Daga can ƙasar zuciyarta kuwa so take yi kawai ta yi ido huɗu da Amaryar Maleek ta ga wace ce ita, da me ta fita da har ya aurota a matsayin gurguwarta?
Anty Safiya ce ta ja Suhailah suka fice zuwa can babbar kitchen ɗin Hajjah, in da ake ta hidimar kwasan nau'ikan abincin da aka shirya don tarban Amaren. Haɗaɗɗun girke-girke ne zuwa gasassun kaji da naman rago da aka kawo daga in da aka kai gashin, wajen wani shahararren me yin gashin da ke can cikin GRA. Da Suhailah akai ta hidimar kammala abubuwan ana baiwa masu aiki suna wucewa da shi ɗakin da aka sauke Amarya TAIMIYYAH. Wanda akai musu masauki a cikin ɗaya daga cikin Bedrooms ɗin Hajjah, wanda ba a ma cika amfani da shi ba, sabida 4 bedroom ne ta ke da su kuma wannan da aka sauke Amaren a ciki shi ne daga can ƙarshen cooridor ɗin da Bedrooms ɗin Hajjah su ke..........✍🏻
#Ɗansabo ce#
[12/14, 10:14 PM] +234 703 769 7050: Littafin TAIMIYYAH paid book ne,ga duk wanda ta tsincesa a kowani irin group ne,kiji tsoran Allah karki karanta sai kin biya 500 naira only.
Za ku iya min magana ta wannan number ɗin 08167768704, ko kuma ku turo kuɗin ku kai tsaye ta wannan account ɗin 0504192664 aisha ibrahim dansabo GTbank.*
*Sai ku tura shaidan biyanku ta wannan line ɗin 08167768704.*
Masu turo credit za ku turo katin MTN na 500 ta wannan line ɗin 08167768704.
_Ina ƴan kasuwa masu buƙatar a tallata muku hajar ku? Maza ku garzayo da kuɗi ƙalilan a tallata muku kayan siyarwanku sai dai kawai ku ji ana kiran waya don buƙatan sayan kayan ku,ku tuntuɓeni ta layina kamar haka 08167768704._
*70*
Daga can ɗakin da aka sauke Amarya TAIMIYYAH, ita ce zaune daga tsakiyar gadon har lokacin kuka take yi mara sauti. Su Ummie da su Anty Mardy da suka kawo ta duk sun juya sai aka barta tare da Guggo Lami, sai su Yasmeen da su Maryam su ma duk kwana za su yi sai gobe bayan an gudanar walima anyi buɗan kai sannan sai su raka TAIMIYYAH zuwa ɗakin ta.
Tarba ce aka yi musu irin na girma da karamci, wanda ya bayyanawa su Yasmeen cewa da gaske fa gidan girma da arziƙi TAIMIYYAH ta shigo. Irin gidan da suka san ƙima da darajar karrama mutane, don babu abinda ba a aje musu ba na nau'inka cima da abubuwan sha, babu ne kawai ba a aje ba ga zallar tarairayan da ake nuna musu tamkar za a ɗauki zani a goya su. Amarya TAIMIYYAH duk yadda ta dinga noƙewa tana jin kunya haka Anty Safiya ta janye ta zuwa bedroom ɗin Hajjah, aka cika gabanta da cima kala-kala da abubuwan sha na musamman da Hajjah ta tanadar dominta. Hajjah da kanta ta tsare ta akan sai ta ci wani gashin naman rago da ta sanya aka yi sa musamman domin TAIMIYYAH, wanda akai anfani da wani irin sirrin magani me inganci a cikinsa.
Duk kunyar da TAIMIYYAH ke ji haka nan ta daure ta ci naman, wanda ba mai yawa sosai bane dama aka yi sa,tunda don cin ta ita kaɗai aka gasa dominta. Bayan Hajjah ta ga cewa ta cinye naman ne ta fiddo wani ƙaramin gora me ɗauke da wani irin tsumi da aka kawo mata shi daga Sokoto, ta miƙawa TAIMIYYAH tana cewa, "Ungo shanye wannan ki bani gorar Zaynab,ni wannan kunyar duk ki aje ta gefe ni uwa ce a gareki ba suruka ba,yadda ki ka ɗauki Iyah haka na ke so ki ɗauke ni kin ji?"
TAIMIYYAH ta gyaɗa kai a hankali tana sake yin ƙasa da kanta,don ba ta ji wannan kunyar da take ji na Hajjah a yanzu zai bar ta nan kusa. Ta miƙa hannu ta amsa gorar ta kai baki kamar yadda Hajjah ta buƙata, ta fara shan tsumin da ke da wani irin daɗi akan harshe,hakan yasa ta shanye tas tana jinjina daɗinsa, rasa haƙiƙanin ko tsumi ne ko kuma wani abu ne me kama dashi ɗin? Ta dai ji ya yi mata kama da irin tsumin da Iyah ta dinga ɗura mata,amma sai dai wannnan da ta sha a yanzu ya fi na Iyah da daɗi da qamshi.
Lokacin da ta aje gorar sai Hajjah ta saki murmushi ci ke da tsokana ta ce, "Ashe dai ɗiyar tawa me son shan zaƙi ce,kar ki da mu zan san ya a yo miki shi da yawa a kawo, wannan da aka kawo ba yi da yawa ne don na raba muku biyu ne ke da abokiyar zamanki Suhailah. Zaynab ina me farin ciki da shigowarki cikin zuriyata, ina kuma fata da addu'ar Allah ya baku zaman lafiya. Sannan ina roƙon arziƙi da ki riƙe Maleek da Amana,ki zauna da kishiyarki da zuciya ɗaya, kada ki yarda da duk wani zuga na mutane wanda ba mai kyau ba. Ba gari ɗaya za ku zauna ba don haka babu ruwanki da ɗaukar duk wani ziga da maganganu irin na mutane, ki toshe kunnuwanki a duk lokacin da magauta za su nufo ki da wani zance, wanda ba mai daɗi ba akan mijinki ko abokiyar zamarki. Allah ya haɗa kanku ya baku zama lafiya tare da rabo me anfani, In Sha Allah ba za ki yi danasanin shigowa cikin zuriyata ba. Na gode Zaynab,na gode da yadda ki ka amince da auren Maleek Allah ya dauwamar da ƙauna ta har abada a tsakaninku, ina so ki saki jiki da ni sosai ta yadda duk wani damuwarki za ki iya sanar da ni kafin ki sanar da Iyah, duk abinda ya yi miki wanda ba ki ji daɗinsa ba ki sanar dani kai tsaye kin ji ko?"
Hajjah ta kai ƙarshen maganar idanunta akan TAIMIYYAH wacce ta sake yin ƙasa da kanta, kalaman Hajjah na ratsa zuciyarta da haifar mata da nutsuwa sosai a cikin ruhinta. Ta gyaɗa kai a hankali cikin sanyin muryarta da ya yi can ƙasa sosai ta ce "In Sha Allah, na gode Allah ya ƙara girma."
Hajjah ta amsa da cewa, "Ameen Zaynab, Allah ya yi miki albarka." TAIMIYYAH ta amsa da cewa "Ameen." A cikin zuciyarta ba tare da ta furta a fili ba , daga haka Hajjah ta yi kiran Anty Safiya don ta raka TAIMIYYAH zuwa cikin ƴan uwanta da ƙawayenta don ta sake,sabida yadda ta ga tana cikin tsananin jin kunyar ta.
Lokacin da Anty Safiya suka fito daga ɗakin Hajjah daidai lokacin ne Suhailah ta shigo cikin corridor ɗin, ita kuma za ta ɗakin Hajjah don kai wa Hajjah wayarta da ake kira,wanda ta bar shi a hannun Anty Rady kiran da ake yi mata yasa Anty Radyn baiwa Suhailah ta ce ta kawo wa Hajjar. Ta sauke idanunta akan yanayin tafiyar TAIMIYYAH tana jin wani abu na motsa zuciyarta, lokacin da fitinannan ƙamshin da TAIMIYYAH ke yi ya shiga hancinta. Ta haɗiye wani abu me ɗaci tana sake kafe su da ido lokacin da suke wuce ta suka nufi ɗakin da aka sauke Amaren. Duk yadda ta so ganin fuskar TAIMIYYAR ba ta samu gani ba sabida sun riga sun bata baya,sai ta juya ta nufi ɗakin Hajjah zuciyarta na cigaba da matsewa da matsanancin kishi.
*09:35pm*
Maleek Ado ne zaune a cikin ɗakin Hajjah idanunsa akan Inna Dije da ke faman masa tsiyan cewa ya biyo Amarya ne babu ko kunya? Ya saki murmushi yana me gyara zamansa bisa Sofa ɗin ɗakin ya ce, "Kai Inna Dije ni ba Amarya na biyo ba,zuwa na yi in ga Ƴar daru na ko ta kwantar da hankalinta. Sai gashi na sameta ma da su Safiya suna ta hiran su,da alamu kun danne ƙirjin ya dannu da kyau ke da Hajjah."
Maleek ya kai ƙarshen maganar yana duban side ɗin da Hajjah ke zaune tana murmushi, Inna Dije ta zabga masa harara ta ce, "Bawani nan ni ban yarda da kai ba, ba Uwargida ka biyo ba Amarya ka biyo sahu babu ko kunya."
Maleek ya sake sakin murmushi zuciyarsa na sake motsawa da kwaɗayin son sake sanya TAIMIYYAH a cikin idanunsa, ya dubi Hajjah ya ce, "Hajjah don Allah zan samu abu mara nauyi haɗe da fura,yinwa na ke ji ban ci abinci ba tun wanda na ci wajen Reception, ni kuma bana son cin abu me nauyi, idan akwai nama da fura a bani please!"
Hajjah ta dubesa cike da zallar ƙauna ta ce, "Za ka samu nama kam sai kalan wanda kake so, akwai gasasshe akwai soyayye akwai kuma ragowar farfesun kan rago da Babah Rabi ta gama yi ɗazunnan. Bari in saka Safiya ta kawo maka nan ko tafiya za ka yi da shi can gida?"
Maleek ya gyaɗa kai yana duban Hajjah ya ce, "Tafiya da shi zan yi Hajjah, ki ce mata ta yi min take away ɗin gasasshen naman ragon,sai a ɗan soya chips a zuba min akai kaɗan. Furan dai idan akwai abani da ɗan yawa please!"
Hajjah ta jinjina kai tana miƙa hannu ta janyo wayarta ta kira Safiya, lokacin da ta iso cikin ɗakin ne ta sanar da ita abinda za ta yi. Ta amsawa Hajjah tana juyawa kan Maleek ta fara masa tsiyan cewa ita fa bata gane bane, Amarya ya zo gani ba zai iya haƙuryn gobe akai masa ita ɗakinsa ba,sai ya yo tattaki ya biyo sahu. Shi dai Maleek blushing kawai ya ke yi ba tare da ya ce da Safiya komi ba, bayan fitarta ne ya dubi Inna Dije ya ce, "Wallahi Safiyya ta gama raina ni da yawa, ita ko kwarjinin nawa ba ta gani kullum cikin min shaƙiyancin da ta ga dama take yi,don ta ga cewa girman watanni na yi mata ba na shekaru ba."
Inna Dije ta sanya dariya ganin yadda Maleek ɗin ke wani kwaɓe fuska,ta tsaida dariyar nata tana cewa, "Kun dai fi kusa ni bazan ce komi ba,don ba a shiga tsakaninku yanzu sai a ganku kuna ƙus-ƙus za ku ƙulla wata tsiyar."
Maleek ya saki murmushi me faɗi don ya san gaskiya Inna Dije ta faɗi,sabida Anty Safiya mutuniyarsa ce sosai,suna mugun shiri da ita duk cikin cousines ɗinsa ta ɓangaren Hajjah jininsu ya fi jituwa da ita. Anty Safiya ta dawo ɗauke da ƙaramin kwandon ɗaukar abinci,wanda ta shiryawa Maleek coolers biyu da ta zuba gasasshen nama a ɗaya,ɗayan kuma ta zuba masa farfesun kan ragon da ya ji kayan ƙamshi,daga gefe guda kuma jug ne da ta zuba masa damammiyar Fura da ta sha kwakwa da madara wajen damun. Sa cup ɗin jug ɗin guda ɗaya da ta aje daga gefe, ta aje kwandon daga gefensa tana cewa, "Oya gashinan an zubo komi da komi,sai a tashi a tafi gida idan kuma za ka wuce tare da gimbiyar taka Uwargida ran gida ne,sai na turo maka ita yanzu don na ga wani basar da kai take yi."
Anty Safiya ta yi maganar cike da tsokana idanunta akan fuskar Maleek Ado da ke faman taɓe baki. Ya yi magana a ƙasaice ya ce, "No na bar miki ita ki sake danne min ƙirjinta da kyau sosai."
Su Hajjah suka sanya dariya baki ɗaya har Inna Dije, Anty Safiya ta tsaida dariyar tana cewa, "Ok haka ma za ka ce? Shiyasa na ce Amarya ka biyo wallahi in ba haka ba meyasa ba za ka tasa kan Uwargida ku wuce tare ba,ka je can kai ka danni ƙirjin nata da kyau."
"No ki rabani da darun Suhailah gara zamanta anan ɗin, ko ta bini ciwan kai kawai za ta bani, yanzu dai taya ni da ɗaukar kwandonnan mu je ki ɗan ji wata magana daga waje."
Inna Dije ta dubi Hajjah suka saki murmushi a tare,ta maida dubanta kan su maleek ta ce, "Ai dama na faɗi, ke Safiya ki kiyayemu wallahi Allah idan Amarya ya ke son gani kar ki biye masa, ya jira har akai masa ita gidan sa."
Anty Safiyyah ta saki dariya lokacin da ta ke ɗaukar kwandon abincin, ta bi bayan Maleek da har ya fice daga ɗakin, tana me ɗaga murya ta ce, "To Mamah ba zan biyesa ba, amma idan za a cika min jaka da bugun Abuja gaskiya zan ɗan ci amana."
Daga Hajjah har Inna Dije suka saki dariya,Hajjah na faɗin, "Allah ya shiryaki Safiyyah."
A.Maleek Ado ya ratso cikin falon Hajjah yana sake gaisawa da wasu ƴan Fam House ɗinsu, waɗanda za su kwana har zuwa gobe taro ya watse, wanda duk rabin su ƴan gulma da ɗaukar rahoto ne kawai. Ya cigaba da takawa har ya fito daga cikin falon Hajjah, ya yi tsaye daga bakin barandar waje yana jiran fitowar Anty Safiya. Wayarsa ya ke latsawa yana sake gwada kiran layin TAIMIYYAH, wanda tun ɗazu ya ke kira amma bata ɗagawa, yanzu ma ɗin har kiran ya tsinke ba a ɗaga ɗin ba. Sai ya maida wayar cikin aljihu daidai lokacin da Anty Safiya ta fito,hannunta riƙe da kwandon abincin da ta riƙo masa. Ta dube sa tana yin ƙasa da murya ta ce, "Bro ya aka yi ne, me kake so?"
Maleek ya ɗan yatsine fuska cike da zallar ƙasaitarsa da ta sani ya ce, "Sisi so nake ki taimaka ki je ɗakin Amaren can ki taho min da Zaynabb, tun ɗazu na ke son jin muryarta amma Yarinyar nan ta ƙi ɗaga wayata,na san kuma don tana cikin mutane ne take jin kunyar mu yi doguwar magana da ita. Ni kuma wallahi ba zan iya kaiwa gobe ban sanya ta a idanuna ba, please ki je ki taho min da ita amma kar ki bari Hajjah ko Suhailah su ga fitowarku, ki faɗi ko nawa ki ke so zan miki alert yanzu ba sai anjima ba."
Ya ƙare maganar idanunsa akan Anty Safiya da ta saki murmushin farin ciki,kafin ta buɗe baki ta ce, "An gama Angon Zaynabu,yanzu ko za ka ga cika aiki ni dai inji alert kawai ko na nawa ne ina so,me nema ai bashi da zaɓi sai abinda aka bashi."
Maleek ya jinjina kai yana ɗan yin blushing ya ce, "Alright! Karanto min details ɗin tuh."
Anty Safiya ta karanto masa account details ɗinta ya shigar cikin wayarsa, ta juya zuwa ciki bayan ta miƙa masa kwandon abincinsa da ke riƙe a hannunta. Maleek ya amsa yana fara takawa don isa wajen parking space inda motarsa ke jirge a wajen. Ko'ina a harabar wajen compound ɗin haske ne kau! Ya dallare ko'ina ta yadda ko allura ne ya faɗi sai ka gani. Ya buɗe mauzanin driver ya shiga yana me miƙa kwandon abincin ya aje daga back seat, ya koma ya jingina da jikin seat ɗin yana miƙa hannu ya saita mirrow ɗin motar, ta yadda zai iya hango tahowar su TAIMIYYAH idan sun fito daga cikin gidan.
Daga ciki kuwa direct Anty Safiya ɗakin da aka sauke Amaren ta nufa,ta tura ƙofar bakinta ɗauke da sallama ta shiga ciki. Amarya TAIMIYYAH na daga can ƙarshen gadon sanye da dogon Hijab,wanda ta ƙi cire sa tunda ta idar da sallar Isha'i su Zee ke mata mitan ta cire amma ta ƙi. Da suka matsa mata da mita ne ta sanar da su cewa, ita ba za ta iya zama da kayan bacci babu lulluɓi ba a gidan surukai, hakan yasa suka share ta babu wanda ya sake mata maganar cire Hijab ɗin.
Yasmeen da su Zee ne suka gaida Anty Safiya cike da fara'a, ta ƙarisa zuwa cikin ɗakin tana sake gaisawa da Guggo Lami, wacce ke kan ɗaya ƙaramin gadon da ke ɗakin ta yi lamo tana kallon ƴan matan na ta sha'aninsu.
"Guggo za ku ɗan bani aron Amarya ne zan dawo muku da ita nan bada jimawa ba."
Anty Safiya ta yi maganar idanunta akan Guggo Lami, Guggo Lami ta amsa da cewa, "Tuh ai babu damuwa ga ta can har ta yi shirin kwanciya ai."
Ta yi maganar tana nunawa Anty Safiya can ƙarshen gadon da TAIMIYYAH ke kwance, ta juyawa su Zee baya tana faman danna wayarta, akan idanunta Maleek ke ta kiran wayarta amma ta kasa ɗagawa sabida vid call ya ke kira,ita kuma ba za ta iya amsa wayarsa vid call a cikin mutane ba.
Anty Safiya ta matsa daga can direction ɗin da TAIMIYYAH ke kwance tana cewa, "Allah sarki Amarya har an yi shirin kwanciya haka da wuri, don Allah ki yi haƙury yanzu bada jimawaba za mu dawo,ta so mu je tunda ma ga Hijab nan a jikinki."
TAIMIYYAH ta tashi a kunyace sai fatam sunkuyar da kanta take yi ƙasa, kunyarta na sake birge Anty Safiyyah. Ta zura takalminta tana gyara Hijab ɗin jikinta suka fito tare da Anty Safiya. Suna isowa cikin falon Hajjah duk su Hajiya Laure suka biyo su da ido. Anty Safiya ta yi kamar ba ta gansu ba suka cigaba da ratsawa ta cikin falon suka fice waje, su Hajiya Laure suka bi su da ido suna cigaba da gulma akan cewa TAIMIYYAH a she dai gurguwarce da gaske tunda sai da taimakon dafa guiwa ta ke iya tafiya.
"Amarya wajen Angonki fa zan miki rakiya, ya ce yana ta kiranki ba ki ɗaga ba meyasa? In banda abinki sai ki shiga ko toilet ne ai ku sha wayarku idan ma kunya ki ke ji na amsa wayarsa cikin ƙawayenki Zaynab. Gaskiya kunyarki har ta yi yawa dole sai kin rage ta don Maleek shi ɗan life ne na gaske. Bai san wani abu wai shi kunya ba in dai akan abinda ya ke so ne,dole sai kin rage wannan kunyar idan kina so ki mallaki zuciyarsa yadda ya dace."
Ita dai TAIMIYYAH jin Anty