Showing 129001 words to 132000 words out of 186776 words

Chapter 44 - TAIMIYAH Book Complete Document by Ayshat Dansabo Lemu .txt

15 Dec 2024

6612

muku kayan siyarwanku sai dai kawai ku ji ana kiran waya don buƙatan sayan kayan ku,ku tuntuɓeni ta layina kamar haka 08167768704.*_


*53*


" Yanzu Hajiya Fatima waɗannan ƴan matan ma duka jikokin ki ne?"


Hajiya Aysha ta tambayi Iyah idanunta akan Zuhurah da Basmah da sai yanzu suka busa iska ,suka ga damar zuwa gaida Hajiya Ayshar bayan an tashi daga walimar.


Iyah ta dubi su Zuhurah tana balla musu hararan yadda suka tsare Hajiya Aysha da ido,kafin ta furta, "Eh duk jikokina ne ƴan wajen Sani ƙanin mahaifin TAIMIYYAH,ga part ɗinsu can na farko daga kin shigo gidan, wannan sunanta Zuhurah sai wannan Basmah."


Iyah tayi maganar tana pointing fuskar kowacce a cikinsu.Hajiya Aysha ta jinjina kai tana faɗin, "Masha Allah,Allah yai musu albarka."


Iyah ta amsa da cewa, "Ameen." Tana me sallamar su Zuhurah da suka zurawa Hajiyan ido,tace su tashi su tafi abinsu.
Bayan fitarsu ne take baiwa Hajiya Aysha labarin cewa dukansu an saka ranan aurensu watanni uku masu zuwa ,ta ƙare maganar da cewa, "Mutumiyarki ne dai har yanzu Allah bai kawo tsayayye ba,amma ina addu'a Allah ya kawo mata itama kafin nasu duk a haɗa ayi gaba ɗaya a huta."


Hajiya Aysha ta jinjina kai tana cewa, "Insha Allah,Allah zai kawo nata itama,ai aure lokaci ne kowa ka ga ya yi lokacinsa ne."


"Hakane Hajiya don da lokacin yayi ma da ita da Zuhurah za a fara sanyawa lokacin,sai aka samu akasi maganar TAIMIYYAH bai je ko'ina ba uwar yaron ta nuna bata so ya auri gurguwa,sanadin rabuwar tasu kenan,kuma cikin wani ikon Allah yaron ne wai kuma Basmah ƙanwarta za ta aura....."


Iyah ta shiga zayyanewa Hajiya Aysha abinda ya faru tas,ta ƙare maganan da cewa, "Wallahi Hajiya sai dana zubda hawayen tausayin Zainab akan wannan lamarin,da ƙyar da lallami na dinga bata ƙwarin guiwa akan tayi haƙury, ta ɗauki hakan a matsayin ƙaddara da kuma jarabawa,su kuma idan da gayya suka shirya wannan lamari Ubangiji ba zai barsu haka ba."


Hajiya da jikinta yayi wani irin sanyi, ta dubi Iyah tana faɗin, "Allah sarki Zainab baki ji yadda na sake jin tausayinta a cikin zuciyata ba,anya ko mutanennan na jin tsoron Mahaliccinsu kuwa? Meyasa duniya ya zama babu gaskiya ne sai son zuciya da cin amanar juna? Amma bakomi watakila Ubangiji yayi nufin nuna musu ikonsa ne da nuna musu cewa ita ɗin ba banza bace,Insha Allah sai ta auri miji na nunawa sa a, wanda sai sun zubda hawayen tausayin kansu da kansu tare da yin nadaman da bazai taɓa anfanar da su komi ba.Ai shi cin amana duk wanda yayisa ƙarya yake yace zai samu yadda yake so,kamar yadda kika ce ne a zuba musu ido ai Ubangiji baya bacci kuma yasan zukatan kowannan mu."


Hajiya Aysha na maganar ne cike da jin ciwo da zafin abinda ya faru da TAIMIYYAH.Iyah ta ɗaura da nata sharhin suna ta yi har Shehu ya iso don tafiya da Hajiyan,basu daina tattaunawa akan batun TAIMIYYAH da yadda tun asali dama Umma ke gwada mata ƙiyayyah ba.


Sai da Yasmeen ta shigo ta sanar da Iyah cewa driver ɗin Hajiyan yazo,sannan suka katse hiran Iyah na tashi ta fito zuwa kitchen tana kiran sunan Guggo Bilki dake zaune a falo.


Guggo Bilki ta samu Iyah a ckin kitchen suka kammala shiryawa Hajiya Aysha abubuwan da suka tanadar don bata ta tafi da shi.Iyah tayi kiran Babah Ladi ta ɗakko kulolin Hajiyan da suka taho da shi daga asibiti,aka tattara komi Yasmeen da Ladi suka kai wajen motar Hajiyar dake fake a bakin gate.


Iyah da TAIMIYYAH suka rako Hajiya Aysha har bakin mota suna mata godia,ta dubi TAIMIYYAH tana me kama hannunta tac, "Daughter yaushe zaku kawo min ziyara ke da Iyar taki?"


TAIMIYYAH ta saki murmushi tana duban Iyah dake saurarensu tace, "Insha Allah idan Iyah ta sanya lokaci sai mu kira waya."


"To Allah ya amince ya baku ikon zuwa ,don kuwa zan yi matuƙar farin ciki da hakan."


Cewan Hajiya Aysha tana duban Iyah ta cigaba da cewa, "To Iyah sai mun waya, Allah ya yi wa karatunta albarka ya bada miji me tsoran Allah."


Iyah ta amsa da cewa, "Ameen." Tana cigaba da kwararawa Hajiya Aysha godia akan abin arziƙin da tayi wa TAIMIYYAH.
Sai da suka ga tashin motar su Hajiyar suka juyo zuwa cikin gida,suna ta magana akan kirki da karamcin matar.


Zuwa magriba taron ya ida watsewa baki ɗaya,su Zee da su Maryam Sunusi duk sun tafi suma,aka bar su Yasmeen da Babah Ladi da gyaran wuri.


TAIMIYYAH ta samu tarin abin arziƙi daga ƴan uwa da abokan arziƙi.Yasmeen ta dinga bubbuɗe abubuwan da TAIMIYYAH ta samu suna sanya albarka,su Umma dai ko hanki bata cewa TAIMIYYAH gashi ba.


Washegarin ranar Guggo Bilki da Yasmeen suka juya zuwa Kano,TAIMIYYAH sai taji tamkar Yasmeen ta zauna amma babu halin hakan.


Kwanaki sun cigaba da shurawa tarin abubuwa na faruwa cikin aminci da ƙuduran Ubangiji.
TAIMIYYAH sai ta ɗauki hankalinta kacokan ta miƙa ga karatun Computer ɗin ta da take zuwa.Ta cire duk wani abu da zai damu zuciyarta ta aje sa a gefe,da zaran ta dawo skull to zaka sameta wajen Ummie, wacce a yanzu sukai wata irin shaƙuwa da TAIMIYYAH.Tana janyo ta ajiki sosai tare da nuna mata ƙauna ta ban mamaki,hakan kuma ya yiwa Iyah daɗi sosai a zuciyarta.


A bakin TAIMIYYAH Ummie ta ji cewa tsohon saurayin TAIMIYYAN ne Basmah zata aura.Abun yai matuƙar baiwa Ummie mamaki da tsoro,ta kuma ji ciwan abin aranta tare da yin Allah wadai da halayyar yaran.


Dama ita sam tunda ta fahimci basu da cikakkiyar tarbiyyah ta daina basu face.Tun suna shigowa wajenta har suka janye jiki ganin babu fuska,dama kuma Umman ce take turo su sabida su dinga sanyawa Ummien idanu, suna ganin me ke faruwa a sashin nata.Amma tunda suka ga babu fuska sai suka janye jiki suka daina shigowa kwata-kawata,Umma kuwa dama zata iya irga shigarta wajen Ummien tun dawowarta nan ɗin,sabida kamar yadda tayi kishi da uwar TAIMIYYAH haka take jin kishin Ummien a ranta,musamman yanzu da aka raba gado taji tarin dukiya da kadaran da Ummien ta janye.


Hakan sai ya sake jefa kishi da hassadar Ummien cikin zuciyar Umma,ba tayi la'akari da abinda mijinta shima ya samu ba.Idanunta na kan abinda su TAIMIYYAH suka gada ne kawai,tana sake sanya jin tsanarsu a zuciyarta me tsanani.


Lokaci ya cigaba da tafiya da tarin kwanaki mabambamta.Zumunci me ƙarfi ne ya sake ƙulluwa tsakanin Iyah da Hajiya Aysha, wacce basa kwana uku basu gaisa da juna ta waya ba.


TAIMIYYAH ma kusan duk friday sai ta kira Hajiyan sun gaisa,hakan kuma nawa Hajiya Aysha daɗi a zuciyarta.Kamar yadda kullum kwanan duniya take jin ƙarin ƙaunar TAIMIYYAH a cikin ranta,tana kuma kisima abubuwa da yawa cikin zuciyarta dangane da TAIMIYYAR,tare da addu'an Allah ya gwada mata alkhairy, akan abinda zuciyarta ke kisima mata akan yarinyar sabida yadda ta shiga ranta farat ɗaya....


____________


*1 Month Later.*


*Gonar Ganye, 1:15pm.*

Maleek Ado ne zaune daga cikin falon Hajjah,isowar sa garin kenan ko mintuna goma bai yi ba.


Daga gefensa Hajjah ce zaune tana amsa call, shi kuma yayi zaman dirshan a gabanta.
Lokacin da ta kammala amsa wayar ne ta sauke idanunta akan Maleek ɗin tana cewa, "Abdulmaleek lafiya dai na ga baka da walwala ko duk gajiya ce?"


A.Maleek ya ɗaga manyan idanunsa ya sauke akan Hajjah yana sake ɓata fuska,ya buɗe baki kaman me yin raɗa yana cewa, "Wallahi Hajjah na gaji ne, satinnan gaba ɗaya har ya ƙare ban samu wani isasshen hutu ba,ai dai ta tayamu da addu'a amma wannan muƙami da aka bani ji nake tamkar in ajesa,gaba ɗaya harka da ƴan kudu akwai haɗari, an sanya min ido sosai a wajen Hajjah."


Yadda yayi maganar cike da rauni yasa Hajjah dubansa da fuskar tausayi tana cewa, "Kayi haƙury Maleek shi ɗaukaka ya gaji haka,duk wanda Ubangiji yai wa wata baiwa ko ɗaukaka to fa kullum rayuwarsa na cikin jarabawane kala-kala,matuƙar akwai imani a zuciyarsa.Don haka kayi haƙury ka daina zancen cewa kamar a amshe muƙamin daga gareka,hakan tamkar butulcewa Ubangijin da ya baka ne.Addu'a kuma kullum cikinsa muke ba dare ba rana,muna kuma da yaƙinin Allah na jinmu kuma zai amsa mana,babu abinda zai faru zaka rabu da su lafiya da izinin Ubangiji,yanzu dai ga abinci can an shirya maka a dining idan kaci sai ka huta da kyau,don ina da wata muhimmiyar magana da nake so mu tattauna da kai,shiyasa kaga na ƙagu ka zo garin don mu tattauna gani ga gaka."


Hajjah ta kai ƙarshen maganar idanunta akan tilon ɗan nata Maleek Ado,wanda ya wani sake shagwaɓe fuska kamar ƙaramin yaro.


Cikin muryansa me cike da ƙasaita yake faɗin, "To Hajjah bari inci abincin amma a kira Lubah tazo ta sauko su nan ƙasa bazan hau dining ba."


Hajjah ta ciri murya ta kira Lubah don ta zo tai masa duk yadda yake so ɗin.Cikin ƙanƙanin lokaci Lubah ta iso cikin falon ta zube a gaban Maleek ta kwashi gaisuwa,hannu kawai ya ɗaga mata alamun ya amsa, sannan ta tashi ta fara ɗakko kulolin abincin ta jeresu nan tsakiyar carfet.


Tana kammalawa ta wuce ta basu waje,yayi saura daga Hajjah sai shi a cikin falon.
Da kansa ya zuzzuba abinda yayi masa cikin abinci kala uku da aka shirya masa.
Hajjah ta miƙe tana dubansa tace, "Ai ɗazu mun yi waya da Suhailah tana so ka wuce muku da garin kunu idan zaka juya,Allah yasa jiya Babah Rabi ta kammala tankaɗesa ya yini a rana, tunda anci sa a anyi ban iska ba ai ruwa ba."


Maleek ya dubi Hajjah kawai ba tare da yace komi ba har Hajjan ta shige ɗaki.Ya cigaba da cin abincinsa lokaci-lokaci ya kan amsa kiran da ke shigowa wayarsa, a haka har ya ƙare cin abincin ,ya tashi daga wajen ya koma kan seater ya zauna.


Lokacin da Hajjah ta fito daga ɗaki samun sa tayi yana ta faman amsa waya da harshen Nasara.
Ta ƙariso tana zama cikin seatern da ke facing ɗinsa, hankalinta na kan TV da ke ta faman aiki cikin falon,har ya kammala amsa call ɗin yana sauke ganinsa akan Hajjan yake cewa, "Hajjah ina so a sake yin garin ɗan-wakennan wanda akai mana yayi daɗi sosai,sai dai kinsan Suhailah da kyuiyan yinsa ina ga shiyasa bata sanar miki ya ƙare ba ko?"


Hajjah ta dubesa da murmushi saman fuskarta tace, "Aiko bata faɗi ba amma tunda sai zuwa jibi zaka wuce za a yi Insha Allah."


Maleek ya jinjina kai yana faɗin, "Okey Hajjah thank u,Allah ƙara muku tsawancin kwana me anfani."


"Ameen Maleek ku ma Allah ya cigaba da yiwa rayuwarku albarka ya kawo zuriya masu albarka."


Maleek ya amsa da cewa, "Ameen."


Hajjah ta kirayi sunansa kai tsaye kafin ta sake zama so serious tana cewa, "Abdulmaleek ina buƙatar dukkanin nutsuwarka anan,don abinda zan sanar da kai yana da matuƙar muhimmanci a wajena."


Maleek ya ɗaga manyan idanunsa ya sauke akan Hajjah,yana ganin yadda taci serious yasan lallai duk abinda take so su tattauna me muhimmanci ne kamar yadda ta faɗi.Sai ya nutsu sosai tare da maida dukkanin hankalinsa kanta yana cewa, "Ina jinki Hajjah Bismillah."


Hajjah ta jinjina kai tana me farawa da bashi labari tun daga kan kaɗe TAIMIYYAH da sukai da mota, har kawo aminci da zumuntar da ya shiga tsakaninta da su.Ta ƙare maganan da cewa, "Maleek ba wani abu nake so ba illah kai min alfarma ka je ka ga Zainab TAIMIYYAH,idan har ka ji tayi maka zaka iya zama da ita a matsayin mata,zan so ka nemi aurenta.Wannan shi kaɗai ne ƙarshen alfarman da nake ji zaka sake min arayuwa ka faranta zuciyata har in cigaba da alfahari da samun ɗa kamarka.Kai kaɗai na mallaka a duniya da zan iya iko da kai in kuma roƙi alfarma kayi min ba tare da raina ya ɓaci ba,na so a ce Ubangiji ya bani wani ɗan wanda bai taɓa aure ba don in saka shi ya aure ta amma Allah kai kaɗai ya mallaka min."


Hajjah ta ɗan dakata kaɗan tana duban fuskar Maleek Ado, wanda ya zuba mata ido yana sauraren dukkanin kamalamanta. Sai Hajjah ta kasa gane wani yanayi yake ciki, don shi yana cikin irin mutanen da suka iya riƙe kansu,duk iya yadda zance zai girgiza zuciyarsa zai yi wuya ka gane hakan akan fuskarsa.Hakan yasa Hajjah cigaba da cewa, "Maleek TAIMIYYAH gurguwace kuma marainiya da ta rasa uwa da uba,amma ta mallaki tarin abubuwan da duk namijin da yasan kansa zai yi alfahari da samunta a matsayin matar aurensa,Mahaddaciya Qur'anice me tarin nutsuwa da hankali,wacce ta samu tarbiyyah me kyau daga kakarta na wajen uba,wacce ta raineta tun tana taumman goyo,don haka ina so a gobe ka wanke ƙafa ka je ka ganta,dukkanin abinda zuciyarka ta yanke akanta ka zo ka sameni ka sanar dani."


Maleek da ke sauraren Hajjah yana dinga nanata kalmar gurguwa cikin kwanyansa kafin ya ɗaga manyan idanunsa yana kallon fuskar Hajjar,Yayi karfin halin fara faɗin, "Shikenan Hajjah zan yi duk yadda kika ce, amma Hajjah wannan karon kuma da gurguwa kika ga na dace?"


Hajjah ta dubi Maleek cikin ido, tana hango ruɗanin da kamalamanta suka jefa zuciyarsa a ciki.Ƙarfin hali kawai yayi wajen amsa mata buƙatarta ba tareda yayi mata musu ba,don abune da bai taɓa yi ba bata taɓa sanya kara ya tsallake ba,shi ɗin me tarin biyayyane akan dukkanin abinda ta nuna tana so.


Ta jinjina kai tana cewa, "Maleek karka bari kalmar gurguwa ya jefa wani abu a cikin zuciyarka,don kai da ita duka a wajen Ubangiji ɗaya kuke,bai jarabeta da zama gurguwa don baya ƙaunarta ba,kamar yadda kai da kake lafiyayye ba zaɓinka bane,shine ya so ka kasance a haka,don haka abinda za ka fara dubawa da tambayata shine, 'me ya ja hankalina akanta har nake sha'awar haɗa jini da ita? Wannan amsar kuma kai ne zaka baiwa kanka ita, bayan ka je kun yi ido biyu da TAIMIYYAH.


Hajjah ta kai ƙarshen maganar idanunta akan Maleek, tana jifansa da wani irin murmushi.Ya lumshe idanunsa yana jin wani abu na dokawa a cikin kansa,kalmar gurguwa da suna TAIMIYYAH na amsa-kuwwa cikin kwanyansa da ƙarfin gaske.


Ya buɗe idanun nasa yana sauke su akan Hajjah,cikin son ɓoye dukkanin ruɗanin da ya shiga yake cewa, "Shikenan Hajjah za a yi yadda kika ce,a kullum mu masu biyayyah ne akan duk abinda kuke so."


"Allah yayi maka albarka Maleek,Allah kuma ya baku zuriyar da zasu bi ku kamar yadda ku ke min biyayyah,ban yi maka tayin zuwa ka ga TAIMIYYAH don in tirsasaka aurenta akan dole ba,duk abinda ka ji a zuciyarka idan ka haɗu da ita ka sanar dani Maleek,kuma ina so ka je a matsayin kaine ka kai kanka gareta,sam bana so su san ina da alaƙa da kai har sai ka ji cewa tayi maka,kuma idan ka tashi zuwa kada ka je a motar da zai nuna matsayinka,ina fata ka gane duk yanda nake nufi?"


Maleek ya jinjina kai cike da gamsuwa yake cewa, "Na gane Hajjah,bari in shiga daga ɗaya bedroom ɗin in kwanta ina buƙatan hutu zuwa la'asar."


Daga haka ya wuce Hajjah zuwa ɗaya ɗakinta wanda Suhailah ta zauna lokacin tana gida....✍🏻














#Ɗansabo ce#
















#Ɗansabo ce"[12/14, 10:12 PM] +234 703 769 7050: Littafin TAIMIYYAH paid book ne,ga duk wanda ta tsincesa a kowani irin group ne,kiji tsoran Allah karki karanta sai kin biya 500 naira only.


Za ku iya min magana ta wannan number ɗin 08167768704, ko kuma ku turo kuɗin ku kai tsaye ta wannan account ɗin 0504192664 aisha ibrahim dansabo GTbank.*


*Sai ku tura shaidan biyanku ta wannan line ɗin 08167768704.*


Masu turo credit za ku turo katin MTN na 500 ta wannan line ɗin 08167768704.




_Ina ƴan kasuwa masu buƙatar a tallata muku hajar ku? Maza ku garzayo da kuɗi ƙalilan a tallata muku kayan siyarwanku sai dai kawai ku ji ana kiran waya don buƙatan sayan kayan ku,ku tuntuɓeni ta layina kamar haka 08167768704._


*54*




Kwanciya yayi tare da lumshe manyan idanunsa,maganganun Hajjah na dawo masa daki-daki.Ko kaɗan baccin da yayi tunanin zai iya yi bai samu yi ba,sai ma tarin tunani da suka dabaibaye kwanyarsa.


Haka ya cigaba da kwanciya time to time ya kan amsa call ɗin da ya ga zai iya ɗagawa,a haka lokaci ya ja ƙwaƙwalwarsa na cike da tarin tunanin yadda zai fuskanci gobe.
Bayan ya dawo daga masallaci sallar la'asar ne yayi wa Hajjah sallama, akan zai je wajen wani aminin mahaifinsa ya gaishe shi,daga can kuma zai wuce gidansu na GRA a can zai kwana.


Hajjah tayi masa fatan Allah tsare tare da jaddada masa maganar zuwa Gyallesu a goben,kamar yadda ta roƙi alfarma ya kuma amsa mata.


___________


TAIMIYYAH da Iyah ne a zaune suna hiran su cikin falon Iyan,daga gefe ɗaya Babah Ladi ce ta maida hankali kan kallon wa'azin da ake haskawa a tashar ManaraTV.


TAIMIYYAH na sanyene cikin wata free gown na atamfar Chiganvy Gold,kalar atamfar red and black ne da ya yi matuƙar yi mata kyau tare da haske farar fatarta.Sallamar Zuhurah da shigowarta cikin falon Iyah,ya sanya TAIMIYYAH ɗaga manyan idanunta ta sauke akan Zuhran,wacce taci uban ado kamar zata biki.
Fuskarnan ya sha make-up ,kamar yadda kayan jikin natasuka fidda shape ɗinta sosai a waje,ta ƙariso cikin falon tana gaida Iyah daga tsaye.


Iyah ta dubeta tana amsa gaisuwan a dake,Zuhurah ta ɗaura da faɗin, "Iyah dama Ameeru ne zai shigo ku gaisa yanzu."


Iyah ta dubi Zuhurah cikin ido kafin ta furta, "To madallah." Daga haka bata sake cewa komi ba har Zuhurah ta juya ta fice,ba tare da tace wa TAIMIYYAH kanzil ba.


Tsam TAIMIYYAH ta miƙe tana ɗaukar wayarta don shigewa ɗaki,amma sai Iyah ta dakatar da ita tana cewa, "Koma kiyi zamanki Zainab,kema ke gansa ku gaisa ai."


TAIMIYYAH ta buɗe baki cike da shagwaɓa tace, "Kai Iyah nina ce miki ina son ganinsa? Ni dai da kin barni na yi shigewata ɗaki."


Kafin Iyah tace komi sallamar su Zuhurah ya karaɗe bakin ƙofar shigowa falon,hakan yasa TAIMIYYAH sake ɓata face.Iyah ta amsa sallamar tana basu umurunin shigowa cikin falon,suka shigo Zuhurah na kan gaba Ameerun na biye da bayanta.


Ya zube ya kwashi gaisuwa wajen Iyah wacce take binsa da kallo tun shigowanrsu.
Ta amsa gaisuwar Ameeru cike da fara'a, tana tambayarsa iyayen nasa,ya amsawa Iyah idanunsa a kan TAIMIYYAH dake zaune cikin kujeran dake facing ɗinsa.


TAIMIYYAH ta buɗe baki ta gaida shi cikin sanyin muryarta,ya amsa yana sake binta da wani irin kallo na ƙurillah.Hakan yasa ranta ya sake ɓaci da hanata tafiya da

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login