Showing 84001 words to 87000 words out of 186776 words

Chapter 29 - TAIMIYAH Book Complete Document by Ayshat Dansabo Lemu .txt

15 Dec 2024

6597

har da ƙafafu.
Basu san ita TAIMIYYAH kunyan yadda zata buɗe ƙafarta aga ɗaya yafi ɗaya girma shi ke hanata yin Lalli a ƙafa ba.Ko zata yi tafi yarda ta siya salataf na yanka ta manna abinta tayi da kanta.
Amma hakanan ta miƙa ƙaramar ƙafar aka zana mata.Su Kausar na ta satan kallon ƙafafun nata suna jin wani tausayinta da kaɗaita ƙuduran Allah cikin zukatansu.Don banda Allah wa zai yi hakan gaka mace har mace kaman TAIMIYYAN amma gashi Allah ya jarabceta da Nasaka na ƙafa ɗaya.
Lokacin da aka gama zanawa duka ƙafafun ba ƙaramin kyau Lallin yayi ba,tun kafin ma ya kama a cire.Ita dai TAIMIYYAH na zaune bata wani sanya musu baki a hiran da suke,zuciyarta na can wajen tunanin Nass wanda har yanzu ta kasa yakice tunaninsa daga zuciyarta sai dai bata zauna waje ɗaya ba.


Basu baro gidan Lallin ba sai huɗu na yamma.Zuwa lokacin TAIMIYYAH ta gama galabaita da yinwa,don sam taƙi cin duk abinda aka siyo musu a gidan Lallin.
Sai data ga yinwa zai halakata sannan taiwa Yasmeen raɗa suka tsaya a wani shago aka amso mata Hollandia Milk da Buns ta ci a motar.
Lokacin da suka iso gidan su Kausar juyin duniya anyi TAIMIYYAH ta shiga ciki suyi sallolin da ke kansu amma taƙi.
Ta kafe ita kawai su barta Yellow driver ya sauke ta a gida,ita Yasmeen ɗin ta dawo daga baya.


Hakanan su Yasmeen suka bar TAIMIYYAH ta tafi Yellow zai sauke ta a gida.
Suna isa TAIMIYYAH ta sauka ta shige ciki.Tun a waje ta hango motar Yah Emran dama shi huɗu yake baro office ya dawo gida daga wajen da yake aiki.


Ta isa cikin gidan tana ji kanta har wani ciwo yake mata sabida rashin cin abinci akan lokaci.
Tunda tai sallama taji babu motsin kowa a falon kawai sai ta nufi ɗakin Yasmeen kai tsaye.
Tana shiga tai wurgi da Hijab ɗin data cire akan Bed ta nufi toilet ta yo wanka tare da ɗauro alwala ta fito.
Idanunta ta zuba akan yatsun hannunta da jan lallin ya kama juwur abin sha'awa,tana kallon irin kyawun da lallin yayi a yatsun hannunta.
Da sallolin da ke kanta ta fara bayan ta idar ne ta canza rigar jikinta zuwa wata doguwar rigan ta shan iska mara nauyi.Kalar rigan pich ne sai ya ƙara fito da hasken fatar ta,bata sanya hula a kanta ba sai ta bar gashinta dake ɗaure da Ribbom a tsakiyar ka.


Ta fito don zuwa ɗakin Guggo Bilki ta sanar da ita ta dawo ta kuma nema abinci.
Sai dai tana sanya kanta cikin corridor ɗin shiga ɗakin Guggo Bilki idanunta ya sauka akan takalman Yah Emren,dake xube daga bakin ƙofar shiga ɗakin.A hankali amon sautin muryar Guggo Bilki ya fara shiga kunnuwan TAIMIYYAH.
Jin Guggo Bilki ta ambato sunanta yasa ta jan birki daga bakin ƙofan.Ba tare da tayi yinƙurin shiga ɗakin ba,haka kawai taji tana son jin dalilin kiran sunanta cikin hiran Guggo Bilki da Yah Emran ɗin........✍🏻












*Salamu alaikum! Ina ma'abota son ƙamshin su ke ne? Uwargida da Amare masu shirin shigewa daga ciki kai har ma da ƴan mata ma'abota son ƙamshi da ƙamsasa suturunku* *.To ga dama ta samu don kuwa shahararriyar mai saida turarukan wuta me asalin kyau da inganci wato RUUSCOLLLECTIONS ta zo muku da turarukan wuta na sawa a ɗaki wanda tun daga kunna shi baza ki taɓa jin ƙauri ba daga farko har karshensa.*
*Bata tsaya anan kaɗai ba don kuwa akwai jerin gwanon kalolin turarukanta masu ƙamsasa jiki da gida haɗi da ɗakuna ma baki ɗaya kamar haka* 👇🏻


*Akwai oil koleccha,da cream koleccha,Body butter, white humra,attraction humra, Mehlab humra, Dufr humra, brown humra, oil humra, golden humra da yellow humra,*
*Turaren wuta dinta kuwa Arabian black bakhoor mai kamshin harami, yemani bakhoor, hemani flakes, sandal rose, sandal flakes, Arabian spices, Senegalese kajiji, Couscous, special kajiji, Golden sand, wardrobe balls, Ruus Remix, Exclusive Dufr, cotton candy, Queen of the night, Bukhur, Alajab.*


*Akwai airfreshner, morphing mist, shampoo, hair cream, Vaseline.* *Harma da su atamfofi, less, shadda, takalma da mayafai duk zaki same su a wajen RUSS COLLECTION .*


Za ku sameta a Garin Kano ta wannan adireshin:- No:221 sarari koki quaters.


Ko ku nemeta a garin Kaduna a Unguwar kanawa.


ga handle ɗinta na Instagrm kamar haka👇🏻
@ Ruuscollections


Ga kuma lambar wayarta don kiranta kai tsaye 👇🏻


07025393114
[12/14, 10:07 PM] +234 703 769 7050: *Salamu alaikum! Ina ma'abota son ƙamshin su ke ne? Uwargida da Amare masu shirin shigewa daga ciki kai har ma da ƴan mata ma'abota son ƙamshi da ƙamsasa suturunku.* *To ga dama ta samu don kuwa shahararriyar mai saida turarukan wuta me asalin kyau da inganci wato RUUSCOLLLECTIONS ta zo muku da turarukan wuta na sawa a ɗaki wanda tun daga kunna shi baza ki taɓa jin ƙauri ba daga farko har karshensa.*
*Bata tsaya anan kaɗai ba don kuwa akwai jerin gwanon kalolin turarukanta masu ƙamsasa jiki da gida haɗi da ɗakuna ma baki ɗaya kamar haka* 👇🏻


*Akwai oil koleccha,da cream koleccha,Body butter, white humra,attraction humra, Mehlab humra, Dufr humra, brown humra, oil humra, golden humra da yellow humra,*
*Turaren wuta dinta kuwa akwai Arabian black bakhoor mai kamshin harami, yemani bakhoor, hemani flakes, sandal rose, sandal flakes, Arabian spices, Senegalese kajiji, Couscous, special kajiji, Golden sand, wardrobe balls, Ruus Remix, Exclusive Dufr, cotton candy, Queen of the night, Bukhur, Alajab.*


Akwai airfreshner, morphing mist, shampoo, hair cream, Vaseline


Harma da su atamfofi, less, shadda, takalma da mayafai duk zaki same su a wajen RUSS COLLECTION .


Zaku sameta a Garin Kano ta wannan adireshin:- 221 sarari koki quaters.


Ko ku nemeta a garin Kaduna a Unguwar kanawa.


ga handle ɗinta na Instagrm kamar haka👇🏻
@ Ruuscollections


Ga kuma lambar wayarta don kiranta kai tsaye 👇🏻


07025393114




*36*


Misalin ƙarfe ɗaya da rabi na ranar asabar ɗin, su TAIMIYYAH suka gama shirin zuwa gaida Mum ɗin Nass.
TAIMIYYAH na sanye ne da wani haɗaɗɗen Egyptian Abaya kalan navy blue wanda akai ma adon zane a wuya da hannun rigar da pink and black colour.Ba ƙaramin kyau TAIMIYYAH ta zuba ba musamman da tai rolling veil ɗin abayar ya zagaye beautiful cute face ɗinta,sai ta fito tamkar wata balarabiyar ƙasar Marocco.
Fuskarta Powder ne kawai ta shafa sai man leɓe me taushi idanunta kuma ta zizara musu kwalli, tare da gyara baƙin gashin giranta da Brush ɗin kwantar da gira.
Daddaɗan ƙamshin body mist da turaren GIORGIO PINK data yi anfani da su ke tashi a jikinta duk ta yadda ta motsa.


Ta ɗaga manyan idanunta masu tsananin haske ta dubi Yasmeen wacce ta shirya cikin wata haɗaɗɗiyar gown na Material.
Ɗinkin ya zauna a jikinta sosai tare da yi mata kyau sai ta ɗauki gyalen da ya shiga da kayan ta yafa bayan ta sanya manyan ɗan-kunni da suka ƙarawa kwalliyan fuskarta armashi,itama daddaɗan ƙamshi ke tashi a jikinta.


"Yasmeen ni fa wallahi kunyan zuwa dubiyan nan nake ji,gani nake yi kaman idan ya nuna ni yace ni ce Budurwar tasa zan muzanta ne a gabansu idan suka ga ni ɗin gurguwa ce."


Yadda TAIMIYYAH ta kai ƙarshen maganan cikin rawar murya yasa Yasmeen da ke aje man leɓen dake hannunta saurin duban TAIMIYYAH tana faɗin, "Kin ga matsalarki ko TAIMIYYAH yanzu don Allah miye na sanyawa zuciyarki wannan banzar tunanin? Please kar ki ɓatan rai tun bamu kai ga fita ba,sai me don ke gurguwace? Ina sha ba shi ya kawo kansa wajenki ba ko kece kika janyosa ta ƙarfi ya zo gareki?"


Ganin yadda ran Yasmeen ya ɓaci yasa TAIMIYYAH faɗin, "Allah baki haƙury almasifatu daga gaya miki abinda ke raina sai ki hauni da masifa,to shikenan na bari bazan sake cewa komi ba har mu je mu dawo."


"Da dai yafi miki mutunci." Cewan Yasmeen tana zabgawa TAIMIYYAH harara kafin TAIMIYYAH tayi magana kiran Nass ya shigo wayarta.Sai ta ɗaga kiran tana kai wayan kunne,tsayin seconds ta ɗauka kafin ta furta, "Okey gamu nan fitowa yanzu Insha Allah."


Ta sauke wayan daga kunni tana duban Yasmeen take cewa, "Yasmeen gashi can a waje har ya iso."


Yasmeen sai ta nufi wajen takalmanta tana faɗin "Okey fara yin gaba kafin in ɗakko ledan kayan dubiyan ko?"


"A'a Yasmeen ni dai mu fita tare kawai,wani irin in fara yin gaba ya tsareni da wannan mayen kallon nasa." TAIMIYYAH tayi maganan tana sake kallon kanta a jikin mirrow ɗin ɗakin nasu,ita da kanta ta yaba da kyawun da Abayar yai mata a jiki sosai.
Ta nufi wajen takalminta kalan blue black samfurin ALDO Flat.Ta zura ƙafarta a ciki take kalan ya haske farar ƙafarta.
Wayarta ne kawai ta ɗauka tayi gaba tana fitowa daga ɗakin ta nufi ɗakin Iyah,ta sanar da ita cewa Nass ɗin ya ƙariso yana waje.Iyah ta ɗago manyan idanunta ta sauke akan TAIMIYYAH tana me yaba kyawun da tayi kafin ta furta, "To shikenan Allah kai ku lafiya ku gaida me jikin kuma ku dawo da wuri kada ku yarda daga asibitin ku je ko'ina na gaya muku."


"Insha Allah Iyah,sai mun dawo."


Cewan TAIMIYYAH tana juyowa ta fito falo dai-dai lokacin da Yasmeen ta fito daga ɗaki hannunta riƙe da ƙatuwar leda,wanda sukai siyayyan kayan dubiyan da zasu kaiwa Mum ɗin Nass ɗin.Ita ma ɗakin Iyah ta nufa tai mata sai sun dawo ta fito suka jera da TAIMIYYAH suka fito daga Sasan.


Kamar yadda TAIMIYYAH tai ta Addu'an kar su haɗu da kowa a waje.Cikin sa'a ko babu kowa a wajen Compound ɗin har suka fice daga gate ɗin,bayan sun gaisa da Tukur da ke musu adawo lafiya.


Tun daga nesa Nass ya kafawa TAIMIYYAH idanu wacce ke tahowa hannunta dafe da guiwar ƙafarta,tana takawa cikin nutsuwan da Allah ya halicceta da shi.
Gaba ɗaya shigar Abayar jikinta ya gama tafiya da zuciyarsa shiyasa har suka ƙariso wajen motar ya kasa ɗauke idanunsa akanta.
Ya fito da sauri yana buɗewa TAIMIYYAH mata front seat ta shiga ya maida murfin ƙofar ya rufe, yana komawa da baya ya rufewa Yasmeen murfin side ɗinta itama,sannan ya zagaya ya shiga mazaunin Driver ya tashi motar.


Sassanyar ƙamshin turaren AZZARO WANTED dana jikin su TAIMIYYAH ne ya haɗe da sanyin AC ɗin cikin motar ya bada wani irin lafiyayyan ƙamshi me motsa zuciya.Nass ya ɗaga idanunsa ya sauke akan Gimbiyar tasa yana faɗin, "My luv irin wannan kyau da kika yi ai sai kisa in kasa yin tuƙin da karsashi.Gaskiya kice zan je na ƙara jibga yawan Abayoyi cikin kayan lefe tunda na lura kyau suke yi a jikin Baby na ba kaɗan ba."


TAIMIYYAH da kunya ya rufeta sai tayi saurin kauda face daga gefensa tana kallon gefen hanya murmushi na Blushing saman face ɗinta,ba tare da iya cewa komi ba hakan yasa Nass ya cigaba da tsokanarta tana faman jin kunya. Yasmeen na musu dariya,har suka isa Asibitin AL-MADINAH da ke cikin GRA zaria.


Haka kawai TAIMIYYAH taji jikinta yayi mugun sanyi lokacin da Nass ya tsaida motarsa.Gabaki ɗaya sai tana ji tamkar kar ta shiga cikin asibitin, don bata san wani irin tarba zasu samu daga ahalin Nass ɗin ba idan sukai ido biyu da ita suka ga ita ɗin gurguwace.
Yasmeen ne data kula da sanyin da jikin TAIMIYYAH yayi ta ƙariso wajen da take tsaye tana me kama hannunta ta riƙe,murya can ƙasa take faɗin, "Malama don Allah ki saki ranki kinga yadda kika wani kwaɓe fuska ne miye haka kike son yi Sis?"


"Yasmeen wallahi tsoron shiga nake yi bansan wani irin tarba zamu samu a ciki ba,gaba ɗaya ƙirjina bugawa yake yi wallahi." TAIMIYYAH tayi maganan dai-dai lokacin da Nass ya ƙariso inda suke tsaye yana faɗin, "Bismillah luv mu je ko."


Yayi gaba suna biye da shi a baya har zuwa ɗakin da aka kwantar da Mum ɗin nasa a ciki.Zuciyar TAIMIYYAH babu abinda yake yi sai bugu,suka sanya kai bakinsu ɗauke da sallama.
Yasmeen ita ce a gaba biye da Nass sai TAIMIYYAH daga bayansu,har suka ƙarisa ɓangaren da Nass ɗin ya nufa.


Mutane uku suka samu a zaune daga kan ɗaya gadon da ke ɗakin,wanda babu Patient akai da alamu Mum ɗin nasa ne kaɗai mara lafiyan da aka kwantar a ɗakin.


"Sannunku da zuwa Naseer da baƙi kake tafe ne haka,ince dai surukar tamu ce aka kawo yin dubiya?Sannun ku da zuwa ƴan mata ku ƙariso ga wajen zama."


Cewar wata Farar mata ƴar gayu dake zaune daga gefen mara lafiyar.
Ta ƙare maganan tana nunawa su TAIMIYYAH kujerun roba biyu da babu kowa akai.
Yasmeen ta janyo musu suka zauna suna gaida mutanen da ke zaune a ɗakin,wanda duk manyan mata ne babu sa'ar su ko ɗaya.


Mahaifiyar Nass dake daga zaune akan gadon an jingina mata pillow ta baya don jin daɗin zama.Ta ɗaga kai tana zubawa su TAIMIYYAH idanu lokacin da suka isa bakin gadon tare da durƙusawa suka kwashi gaisuwa da yi mata sannu da jiki.
Ta amsa da sakin fuska idanunta akan Nass lokacin da su TAIMIYYAH suka koma wajen zamansu,ta buɗe baki tana cewa , "Auta wacece Surukar tawa a ciki?"


Nass da fara'arsa ya nuna mata TAIMIYYAH dake faman yin ƙasa da kai cike da jin kunya yana cewa "Gata nan Mum baki ga sai faman yin ƙasa da kai take yi ba tana jin kunya,da ƙyar fa nai convincing ɗinta ta zo sabida ta cika kunya."


Tunda Nass ya fara magana yana nuna TAIMIYYAH cewa itace zaɓin nasa fara'ar da ke kan fuskan Hajiya Hajara ya ɓace ɓat....
Dukkanin sauran ƙawayenta dake ɗakin suka tsurawa TAIMIYYAN idanu kaman masu son gano wani abu akan fuskarta, kafin muryan Mum ɗin Nass ya karaɗe kunnuwansu lokacin da take faɗin, "Kana nufin gurguwan itace yarinyar da kake sanar min ka samu matar aure Naseeru? Anya ko kanka ɗaya da zaka rakito gurguwa alhali kana lafiyayye baka da wata Nasaka,duk ƴan matan da ke yawo a gari lafiyayyu idanunka bai gane maka su ba sai musaka? To badani za a yi wannan haɗin ba sam! Ni duk ga zato na waccar itace yarinyar ai.To tun wuri ka rabu musu da ƴar mutane ta samu dai-dai ita ta aura,don bazan taɓa yarda ka auri gurguwa ana zaune ƙalau ba,tun farko ma meyasa baka sanar min da cewa me lalura ka kwaso ba?"


Hajiya Hajara ta jefa masa tambayan idanunta akan Nass wanda tuni zufa ya fara jiƙe rigarsa.
Ga wani mashahurin tashin hankali da ya taso masa,iya muzanta yana jin ya gama yinsa a yau agaban su TAIMIYYAH.Wacce tuni itama jikinta ya ɗauki wani irin rawa,idanunta har sun fara fitar da hawaye tsabagen yadda take ji ta gama muzanta.
Yasmeen da ranta ya gama ɓaci sai kawai ta miƙe tana kama hannun TAIMIYYAH ta miƙar da ita tsaye.Sannan ta ɗaga idanunta ta sauke akan Mum ɗin Nass da bakinta ya cigaba da faɗin kalamai na rashin ilimi akan TAIMIYYAH.Yasmeen ta soma furta cewa, "Allah ya ƙara lafiya mu zamu tafi,Allah ya huci zuciyarki Mama,TAIMIYYAH ba itace ta ga Naseer tace tana so ba,dama shine ya kawo kansa amma daga yau ta barshi bari na har abada Insha Allah, Allah ya baki suruka lafiyayya wacce ba gurguwa ba itama ƙaddara ce ta mayar da ita haka ba itace ta zaɓi kasancewa a gurguwan ba."


Daga haka Yasmeen taja hannun TAIMIYYAH suka baro ɗakin ranta a matuƙar ɓace da wannan muzanci da tozarcin da suka riska daga Mahaifiyar Nass ɗin.Kaman jira TAIMIYYAH take yi su fito daga ɗakin ta saki kukan da take danne tun a ciki.
Dukkanin jikinta rawa yake yi ba don ma Yasmeen na riƙe da hannunta ba da tafiyar ma gagaranta zai yi.


Daga ciki kuwa Hajiya Hajarah da ƙawayenta biyu ne suka sake rufe Nass da faɗan cewa taya xai kwaso gurguwa ya kawo a matsayin wacce zai iya aura? Hajiya Murja ce kawai me hankalin ciki da take nuna musu cewa ita bata ga aibun yarinyar ba.Kuma da alamu daga gidan mutunci da Tarbiyyah yaran suka fito,ta cigaba da cewa "Nakasa Allah ke jarabtan Bawa da shi Hajiya Hajarah sam ban jin daɗin yadda kika muzanta yarinyar agaban idanunta ba,wannan cin fuska ne da yiwa Allah isgilanci.Koda zaki nuna ƙinta bai dace kiyi akan idanun yaran ba,koba komi Naseer shine ya kai kansa kamar yadda ƴar uwar yarinyar ta faɗi.Don haka shi yakamata ki samu shi kaɗai ki zaunar da shi ki nuna masa baki amince ba in yaso shi yasan ta yadda zai yi ya zame jikinsa,amma yanzu don Allah da wani ido kike so ya kalli yarinyar? Me zai gaya mata alhali kin muzantashi kin ci mutuncin su agaban idanunsu,gaskiya baki yi kyan kai ba Hajarah ko kaɗan.Naseer maza bi su ka maida su gida,ka kuma basu haƙury don anci mutunci su."


Hajiya Murja tayi maganan idanunta akan Nass wanda idanunsa suka kaɗa sukai jajir zuciyarsa na faman tafasa kaman zai faso ƙirjinsa ya fito.Kaman jira yake Hajiya Murja ta bashi umurni ya fito daga ɗakin da sassarfa.
Tuni har su TAIMIYYAH sun kai bakin gate Yasmeen na riƙe da hannunta har lokacin kuka take yi tamkar ranta zai fita.Danasani da takaicin kanta na yadda zuciyarta tai saurin kamuwa da soyayyar Nass ɗin na sake kamata,suna ji yana ƙwalla musu kira amma ko kaɗan basu da alamun tsaya,har suka dangana da bakin gate ɗin asibitin suka fice abinsu. Allah ya taimakesu kan titi ne Asibitin ta yadda zasu iya samun abin hawa,shiyasa Yasmeen ta sauke ajiyar zuciya don yadda ranta ya gama ɓaci ɗinnan bata ji ko sama da ƙasa zasu haɗe ne zata bari su shiga motar Nass da sunan ya maida su gida.


Nass ne ya juya ya ɗakko motarsa ya fito,yana fakawa a gaban su Yasmeen da ke tsaye daga gefen titi.
Ya fito daga cikin motar yana zagayowa inda suke tsaye, idanunsa akan TAIMIYYAH dake kuka yake faɗin, "Yasmeen kuyi haƙury ku shiga mota in maida ku gida,don Allah kar kuce ba za ku shiga ba Please!"


Yayi maganan cike da magiya yana jin yadda kukan TAIMIYYAH ke sake ɗaga hankalinsa da ƙona zuciyarsa.Ji yake daya tara sanin abinda zai faru kenan da bai matsa sai ya kawo su wajen Mum ɗin sun dubata ba,ko kaɗan bai taɓa tunanin kasancewar TAIMIYYAH me laluran ƙafa zai sa Mum ɗin nasa ta rufe ido taci fuskarsu har haka ba.Yasmeen ne ta ɗaga idanunta ta dubi Nass tana son yin controlling temper ɗinta take faɗin, "Nass kayi haƙury amma ba za mu shiga motar ka

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login