Showing 69001 words to 72000 words out of 186776 words

Chapter 24 - TAIMIYAH Book Complete Document by Ayshat Dansabo Lemu .txt

15 Dec 2024

6609

rame kaɗan sabida yawan tunani da zafin mutuwan da ke dukanta.Don ma Iyah ta saka an rubuce musu Qur'ani tas an wanke suna shan ruwan kullum safe da yamma,hakan kuma ba ƙaramin dangana da nutsuwa ya samar a zukatansu ba.Domin Qur'ani maganin duk wata irin damuwa ce kuma warakace daga dukkanin wani ƙunci na rayuwa.


TAIMIYYAH ta sanya Hijab ɗin wanda tsayinsa ya wuce guiwanta da kaɗan.Kalan Hijab ɗin Army Green ne dark wanda ya haske farar fatarta,yai mata kyau sosai sai ta zura Flat Shoe ɗinta na Dior,ta dubi Yasmeen tana faɗin "Mu je Yasmeen kinsan dai bazan iya fita in shigo da shi ni kaɗai ba."


Yasmeen bata ce komi ba ta sakko daga kan gadon,ta ɗauki Hijab ta sanya suka fito don zuwa wajen Nass ɗin.A falo suka samu Iyah da wasu baƙi uku da suka shigo gaisuwa,sai Guggo Bilki da wata Innar Iyah dake nan su sai anyi Bakwai za su tafi.Yasmeen ta dubi Mamien nasu tana sanar da ita inda za su,Guggo Bilki ta jinjina kai kawai daga haka suka fice Iyah na bin bayansu da kallo.


A tsaye suka tadda Nass ya ginjina da jikin motarsa,yana sanye cikin riga da wando na fararen Shadda da sukai masa kyau matuƙa.Kansa babu hula sai ƙwantaccen Sumansa da kallo ɗaya zakai ma gashin kasan yana cin kuɗi ba kaɗan ba,idanunsa akan TAIMIYYAH ya ke tunda suka doso wajen da yake tsaye.Bayan sun gaisa da Yasmeen ne sukai masa jagora zuwa ciki,Sasan Iyah suka fara isa da shi yayi mata gaisuwa tare da su Guggo Bilki.Kafin daga nan su nufi falon Baba Sani,don Iyah tace su raka shi yai masa ta'aziyyah tunda yana nan.


Ita dai TAIMIYYAH ƙin binsu tayi zuwa Sasan Baba Sanin,tace Yasmeen ta kai shi ita zata jira su a waje.Hakan ko akayi Yasmeen ɗin ce tayi ma Nass ɗin jagora har zuwa falon Baba Sanin,amma bata yarda ta shiga ba ta tsaya daga waje.
Nass ya shige ya tsuguna har ƙasa ya kwashi gaisuwa tare da yin ta'aziyyah,Baba Sani amsa yana tambayansa daga ina yake? Nass ya bashi da cewa daga cikin gari yake Ƙwarbai.
Daga haka Baba Sanin bai sake cewa komi ba Nass yai masa sallama ya fito,Yasmeen ta sake masa jagora zuwa Sasan Ummie ita ma yai mata gaisuwa,sannan suka fito suna dosan inda TAIMIYYAH take zaune kan ɗaya daga cikin fararen kujerun da Tukur ya aje musu.


Nass ne yaja kujeran dake facing TAIMIYYAH ya zauna,idanunsa akanta yake fes lokacin da yake faɗin, "My Zee-zee Allah ya ƙara mana haƙury da juriyan rashin su Abie,amma don Allah Baby ki rage tunani kin ga har kin rame a fuska,kuma ki dinga daurewa kina cin abinci sosai kinji luv?"


Yadda yake maganan cike da kulawa, yasa TAIMIYYAH ta ɗago manyan idanunta ta sauke akansa.Murya a shagwaɓe take faɗin "Insha Allah! Nagode da kulawa."


Ta ƙare maganan tana kawar da face daga gare shi,ganin irin kallon ƙaunan da yake jifanta da shi kaman sunyi shekara basu ga juna a zahiri ba.Nass ya sake ƙasa da murya yana faɗin, "Ni bana son wannan kunyan Luv ki ɗago kawai ki kalli Babyn ki, na san kema kinyi missing ɗina a lot." Ya ƙare maganan yana son su haɗa ido amma sai TAIMIYYAH tayi saurin kai hannu ta rufe face ɗinta,tana sakin murmushi.
Yasmeen dake tsaye gefe guda tana danna waya ta saki murmushi kaɗan,lokacin da Nass ya juyo gareta yana faɗin, "Sis bari in zo in wuce zuwa gida,zan dawo gobe Insha Allah,ki kula min da Gimbiyar tawa please!"


Yasmeen tayi murmushi tana faɗin, "An gama karka ji komi zan kula maka da ita tamkar egg." Suka saki ƙaramin dariya dai-dai lokacin dasu Zuhurah ke fitowa daga Sasan Iyah,wasu mata na biye dasu abaya da alamun sunyi musu rakiya ne su kaiwa Iyah gaisuwa.
Hango su TAIMIYYAH da wani a zaune yasa Zuhurah duban Basmah da itama hankalinta ya tafi kan su TAIMIYYAN tana faɗin, "Basmah mu ƙarisa mu ga wannan Guy ɗin da Anty Laurah ke zuzuta shi ne halan."


Daga haka suka nufi wajen su Yasmeen ɗin,idanunsu akan su TAIMIYYAH da suka juya musu baya.Yasmeen ce da ke tsaye kawai take facing ɗin su Zuhuran,don haka akan idanunta suka ƙariso wajen.Zuhurah na faɗin "A'a Yasmeen kune anan shiyasa muka ji shiru da muka shiga Sasan Iyah,mun raka Friends ɗin Umma su yi mata gaisuwa."


Zuhurah ta ƙare maganan tana satan kallon su TAIMIYYAH,wanda da alama basu ma ankara da tsayuwan su Zuhurah a wajen ba,sai da Yasmeen ta furta, "Eh wallahi,Saurayin TAIMIYYAH ne yazo yiwa su Iyah ta'aziyyah,shine na raka shi har wajen Ummie da Baba Sani,ku matsa ku gaisa mana."


Yasmeen tayi maganan tana kallon yadda Basmah ta tsare Nass da ido.Dai-dai lokacin da suka waiwayo a tare shi da TAIMIYYAH,Zuhurah ta ƙarisa wajen tana faɗin, "Sannu ina yini anzo lafiya?" Nass ya amsa da "Lafiya lau ya ƙarin haƙurin mu,Allah yai musu rahama ya kyautata namu zuwan."


Duk suka amsa da "Ameen." Gaba ɗayansu har TAIMIYYAH,Basmah ta gaishe da Nass tana wani faman maƙe murya.Ya amsa ba yabo ba fallasa daga haka Yasmeen tai masa bayanin cewa,su Zuhurah Cousines ɗin TAIMIYYAH ne.


Sai ya jinjina kai kawai ba tare da yace komi ba,don haka kawai kallon da Basmah ke faman binsa da shi yake bashi haushi.Sai ya miƙe yana duban TAIMIYYAH yake cewa "Luv zan wuce sai mun yi waya,don Allah ki daure ki dinga cin abinci Baby please! Banda yawan tunani kinji ko?"


TAIMIYYAH ta shagwaɓe face murya can ƙasa take faɗin, "Insha Allah,ka gaida su Mama nagode."
Nass da yake jin wani irin feeling na sake fisgansa akanta,ya ɗan lumshe ido ya buɗe akanta,kafin ya maida dubansa ga Yasmeen da su Zuhurah yana faɗin, "Hey! Sisis zan wuce bye bye."


Yasmeen tai masa Allah tsare ya nufi hanyan gate,suna bin bayansa da kallo barin ma Basmah da duk haɗuwan Nass ɗin ya gama sace zuciyarta.
Ji take yi wani abu na malting cikin zuciyarta,tayi saurin maido dubanta kan TAIMIYYAH lokacin da Nass ɗin ya ɓacewa ganinta tana faɗin, "Wow! Gaskiya Yah TAIMIYYAH guy ɗinnan ya haɗu,ba ƙarya Anty Laurat ke yi ba,ke ko a ina kika samo sa?"


Ta ƙare maganan da jefawa TAIMIYYAH tambayan cike da rainin hankali.TAIMIYYAH da haka kawai taji zuciyarta ta sosu akan yabon Nass ɗin da Basmah tayi,ta ɗaure face tana bata amsa da faɗin "Allah ne ya kawosa ba nemosa nayi ba Basmah."


TAIMIYYAH ta ƙare maganan tana fara takawa don barin wajen ma baki ɗaya.Hakan yasa Zuhurah taɓe baki tana ballawa Basmah hararan meyasa taiwa TAIMIYYAH magana akan Nass ɗin.
Yasmeen da itama takaicin Basmah ya cika zuciyarta tun kallon da take ta jifan Nass ɗin da shi, ji tayi kaman ta kwaɗe Basman da mari,ta dubi su Zuhuran tana faɗin, "Bari mu koma daga ciki Zuhurah muna dai ta kewan tafiyan Anty Laurat wallahi,su Mama dai basu kyauta ba da suka matsa sai sun tafi da ita."


Zuhurah ta kyaɓe baki tana faɗin, "Wallahi muma ta bamu kewa,amma idan Umma ta je bikin da zasu yi a Yoben next month zasu taho tare ai."


Daga haka su Zuhurah suka nufi hanyan komawa Sasan su,ita kuma Yasmeen ta juya tabi bayan TAIMIYYAH wacce tuni ta kai Sasan Iyah ma.


"TAIMIYYAH kin ga kallon da mara kunyan yarinyan can kuwa ke bin Nass da shi?" Yasmeen ta jefawa TAIMIYYAH tambayan lokacin da suka dangana da ɗakinsu.
TAIMIYYAH dake ninke Hijab ɗin data cire ta dubi Yasmeen ɗin tana faɗin, "Na gani Yasmeen,baki ji ma tambayan rainin wayan da tai min bane ,wai ina muka haɗu hmm!"


TAIMIYYAH ta kai ƙarshen maganan cike da takaici,tana aje Hijab ɗin data gama ninkewa akan gado.Dai-dai lokacin da kira ya shigo wayarta,ganin Anty Mardiyyah ne yasa ta ɗagawa,suka gaisa.TAIMIYYAH tana tambayanta gajiyan hanya,don jiya suka juya daga Zarian sun zo sunyi gaisuwa har da mijinta,hatta da dangin Maman TAIMIYYAH da ke garin Daura duk sun zo gaisuwa cike da mota.
Bayan sun gama magana da Anty Mardiyyan ne, TAIMIYYAH ta aje wayan tana duban Yasmeen take faɗin, "Yasmeen inata so in tambayeki me Baba Sani yace da kika raka Nass wajensa,ko baki shiga ba a waje kika tsaya?"


Yasmeen ta dubi TAIMIYYAH tana murmushi ganin yadda TAIMIYYAN ta wani narke face,kafin ta furta "Ina fa na shiga daga waje na tsaya in gaya miki,amma dai ina jiyo sa yana tambayan Nass daga ina yake.Nass ɗin ya sanar dashi sunan anguwan su,daga haka bai sake tambayansa komi ba."


TAIMIYYAH sai ta sauke ajiyan zuciya tana faɗin, "Thank God,wallahi sam bana so Baba Sani ya san da maganan Nass a yanzu,sai zuwa gaba kaɗan."


Cewan TAIMIYYAH cike da shagwaɓa,Yasmeen ta aika mata harara tana faɗin "Matsoraciya, to miye abin rashin son ya sanin tunda dai kina son abinki,ko kina tsoran yace ya fito da wuri ne asa rana mu sha biki?"


TAIMIYYAH ta aikawa Yasmeen harara tana faɗin "Ko ba ku sha biki ba..! Ke wallahi ƴar rainin wayau ce Yasmeen ɗinnan."


Yasmeen dai dariya kawai tayi,tana yin gaba ta shige toilet don yin fitsarin daya cika mata mara.TAIMIYYAH sai ta ɗauki wayanta tana kiran layin Anty Laurat,wacce ta tafi tun shekaranjiya dasu Mamansu suka zo gaisuwa,sai suka tafi tare da ita.Sun daɗe suna magana Anty Laurat na sake kwantar da hankalin TAIMIYYAH da cewa ta rage tunani ta dinga cin abinci kuma,don tunda akai rasuwan bata cin wani abincin kirki sai an matsa mata.
Daga ƙarshe sukai sallama TAIMIYYAH na sauke wayan daga kunninta,memakon ta aje wayar sai ta shiga ma'ajiyar adana hotuna tana kallon pics ɗinsu Nahar.Hawaye na biyo fuskarta yana sauka akan jikinta,wani irin kewansu take ji na sake baibaye zuciyarta,lokacin data buɗo pic ɗin Abie kuwa bata san lokacin data fashe da kuka ba.
A haka Yasmeen ta fito ta samu TAIMIYYAH tana kuka sosa,sai ta zauna aikin rarrashi har zuwa lokacin da TAIMIYYAN ta tsaida kukan tana faman sauke ajiyan zuciya akai-akai.


A can Sasan su Zuhurah kuwa,Zuhuran ce zaune ita da Basmah a cikin ɗakinsu.Basmah ta dubi Yayarta tana faɗin "Yah Zuhurah a gaskiya Guy ɗinnan ya haɗu fa,ke kinji yadda yake magana cike da aji,daga gani ɗan boko ne da yasan kan gayu.Wallahi farat ɗaya naji ya shiga raina,shi ko yana da wannan haɗuwan ya tsaya kula gurguwa? Anya ko ba kyawunta kawai ke jansa ba,ko kuma sha'awanta ke fisgansa yana son cimma wata manufa akanta,amma in ba haka ba mi zai ci da gurguwa alhali ga lafiyayyun ƴan mata,da suka mallaki komi na cikar halitta,amma dai zamu zuba ido mu ga yadda lamarin zai kasance."


Basmah ta kai ƙarshen maganan tana ji ina ma ita Nass yace yana so ba TAIMIYYAH ba! Zuhurah da itama zuciyarta ke cike da mamakin wannan lamari,ta taɓe baki tana faɗin "Wallahi Basmah nima sanƙamewa nayi kawai a tsaye,don duk kwarzanta shi da Anty Laurat ke yi ban ɗauka haɗuwansa ya kai haka ba,to ai wannan ya ma fi Yah Sadeeq haɗuwa da komi.Ita kuma makiran baki ga wani narke masa da take yi ba,shi kuma duk ya wani susuce yana faman bin ta da mayen kallo,wallahi TAIMIYYAH ba ƙaramar shu'uma bace Allah ne ma kaɗai yasan meyasa ya maida ita gurguwan ma."


Zuhurah ta ƙare maganan cike da jin kishin TAIMIYYAN na sukan zuciyarta.Basmah kuwa sai cewa tayi "Ai Insha Allah wannan guy ɗin sai ya suɓuce mata,ba za ta taɓa auren kaman wannan alhali mu gamu lafiyayyun ko saurayin bamu da shi,gara ma ke kin kama Ameeru a hannu mitsuuw...!" Yadda Basmah ta ja tsaki kaman zata tsinke harshe yasa Zuhurah sakin dariya tana faɗin "Easy Sis ki kwantar da hankalinki ke ma zaki samo mana Handsome guy Soon."
Suka ɓarke da dariyan shaƙiyanci,kafin su kamo wani zancen amma sam Nass yaƙi ɓacewa a zuciyan Basmah,wani irin feeling take ji akansa na fisgan zuciyarta,gefe guda tana sake jin tsana da kishin yadda TAIMIYYAH ke kere su a komi tamkar ba Musaka ba....!


Ranan da akai addu'an Bakwai a ranan Guggo Bilki ta koma Kano,ta so ƙwarai su tafi tare da Yasmeen,amma sai TAIMIYYAH ta sanya mata kuka akan ta bar Yasmeen ɗin ta sake wasu kwanaki.Iyah ma sai ta goyawa TAIMIYYAH baya akan abar Yasmeen ta zauna,tunda ita ke sake kwantar ma TAIMIYYAH da hankali da ɗebe mata kewa.Hakanan Guggo Bilki ta koma cike da alhinin wannan rashi da suka yi me tsananin zafi da ciwo,wanda har abada ba zasu mance ba.


Ummie ita ma dukkanin ƴan uwanta sun tattara sun tafi,sai ita kaɗai da wata Innarta Dattijiya da aka bari ta zauna da ita.Ranan gaba ɗaya gidan kowa sai daya zubda hawaye, mutuwan ya sake dawowa sabo,sabida yadda Ummie da TAIMIYYAH ke faman kuka tamkar ranan ne akai mutuwan.Da ƙyar aka samu sukai shiru ana sake musu nasiha akan muhimmancin tawakkali da yadda da ƙaddara.


Iyah ce da kanta ta sake sawa akaiwa Ummie saukar Qur'ani a rubuce aka wanke tana shan ruwan.Tausayinta sosai Iyah ke ji don tasan cewa babu wanda zai kaita jin zafin wannan rashin,ko ita data kawo Sameer duniya ba zata ce tafi Ummie jin zafin rashinsa ba.


Haka kwanaki suka cigaba da shurawa,su Baba Sani duk suka koma bakin aikinsu ranan Monday.Sai kuma a ranan TAIMIYYAH ta sake sanya Yah Sadeeq a idanunta,lokacin daya shigowa yiwa Iyah sallama,sai yasa Yasmeen tai masa kiran TAIMIYYAN.Yana me sake mata nasiha akan ta kwantar da hankali tayi dangana,shima Baba Sani haka ya tasa TAIMIYYAN a gaba yayi na shi lallashin da nasiha kafin ya tafi...


Kwanakin da suka biyo baya duk su TAIMIYYAH sun yi shi ne cikin tarin kewa,da alhinin rashin su Abie ɗin,wanda kullum kwanan duniya ta kwanta bacci sai tayi mafarki da su,takan farka cikin dare tai ta salloli tana roƙon Ubangiji ya bata juriya da dangana ita dasu Ummie da Iyah,kuma a hankali ta fara samun nutsuwan zuciya da dangana.......✍🏻






Littafin TAIMIYYAH paid book ne,ga duk wanda ta tsincesa a kowani irin group ne,kiji tsoran Allah karki karanta sai kin biya 500 naira only.


Za ku iya min magana ta wannan number ɗin 08167768704, ko kuma ku turo kuɗin ku kai tsaye ta wannan account ɗin 0504192664 aisha ibrahim dansabo GTbank.*


*Sai ku tura shaidan biyanku ta wannan line ɗin 08167768704.*


Masu turo credit za ku turo katin MTN na 500 ta wannan line ɗin 08167768704.


#Ɗansabo ce#
[12/14, 10:06 PM] +234 703 769 7050: *34*


*Cairo, Egypt.*

Yau kwanan su A.Maleek uku kenan da isowa ƙasar Cairo wato ( Egypt).Sun sauka ne a wani New City cikin wani haɗaɗɗen building wanda akai renting ɗinsa da kuɗi masu nauyi.
Single Bedroom ne da babbar falo haɗe da Kichen sai toilet makeke da ke manne cikin Bedroom ɗin.
Daga yanayin yadda aka tsara ginin gidan da yadda a ka ƙawata ɗakunan,za ka fahimci cewa kama irin waɗannan wajen sai Manyan ma su Kuɗi.Don ba ƙaramin tsaruwa gidan ya yi ba musamman yadda aka tsara ɗakunan da kayan more Rayuwa ma su asalin kyau da nauyin kuɗi.


Daga cikin Bedroom ɗin Suhailah ce kwance a jikin Maleek Ado wanda ya ke amsa waya cikin harshen Nasara.Hannunsa ɗaya na shafa gashin kan Suhailah wanda bata jima da busar da shi ba,ya sauke wayan daga kunninsa lokacin da ya kammala amsa call ɗin,manyan idanunsa na sauka akan gashin da ɗaya hannunsa ke kai.Cikin ƙasaitacciyar muryarsa yake cewa, "Wife zuwa anjima kaɗan Sunusi zai ƙariso ina so mu kammala da Asibitin a yau, zuwa gobe sai mu fara zagayawa wuraren buɗe ido."


Suhailah ta ɗago idanunta ta sauke akan Maleek kafin ta ce "To Allah ya kai mu anjiman My Maleek,jikina ya riga da yayi sanyi tun bayanan da likitar tayi jikina na bani na riga na aikata babban kuskure cikin rayuwata,tunda kaf sakamakon gwaje-gwajen da aka yi babu wanda bai nuna cewa mahaifata bata samu matsala ba.Ka ga kenan duk wani hope da za a bani na cewa komi zai iya komawa normal zuciyata ba za ta gamsu ba, har sai lokacin da na ganni ɗauke da ciki a mahaifata Yah Maleek!"


Yadda Suhailah ta kai ƙarshen maganan tana sakin kuka tare da sake shigewa jikinsa.Ya sanya Maleek lumshe idanunsa yana sake rungumarta da kyau,hannunsa na shafa bayanta alamun rarrashi,kafin ya buɗe baki yana cewa "It's okey please! Kuka ba zai yi maganin komi ba Suhailah,kuskure kin riga kin yi so sai ki rungumi dukkan ƙaddaran da zai biyo baya,har yanzu kina da sauran hope idan har kin shaye magungunan da aka ce za a ɗaura ki akai,tunda ƙwararriyar likitar ta bada tabbacin watakila kafin ma ki kammala shanye dose ɗin za ki iya ɗaukan ciki,kin ga kenan akwai hope.Sai dai mu dage da addu'a tunda shi Allah ba a masa dole,zai iya bayar da rabon a lokacin da muke saka rai,zai kuma iya hanawa har zuwa wani lokaci koda a ce kuwa komi ya koma normal ɗin."


A.Maleek ya kai ƙarshen maganan yana share mata hawayen da ke zubowa daga idanunta.Suhailah tayi lamo a jikinsa tana sauke ajiyan zuciya,wani irin nadama da dana-sanin biyewa Zuby na sake kama zuciyarta.Sun jima a haka yana lallashinta da kalamai na kwantar da hankali,don Maleek har cikin zuciyarsa ya ke jin tausayin Suhailan yanzu.Sabida yadda yake hango tsananin nadaman da tayi a cikin idanunta,shi yasa yake sassauta fushinsa akan kuskuren da ta riga ta aikata shi.Fushinsa ba zai sauya komi ba amma baya ji da zaran ta shanye magangunan da za a bata ba a samu wani cigaba ba to dole zai ƙara aure,don da gaske yana buƙatan haihuwa....


Kamar yadda yace Sunusi ne zai zo ya fita da su,hakan ce ta kansance misalin 10:30am Sunusin ya iso.Cikin wata dalleliyar mota irin wanda manyan masu kuɗi ke zirga-zirga a cikinta.Sunusi wani yaron A.Maleek ɗinne da yawanci idan ya shigo ƙasar Cairo shi ke masa hidima,tun daga kan kama masa wajen zama zuwa duk wani zirga-zirgan da zai yi,duk Sunusin ke driving ɗinsa da yi masa wahalhalu.Sabida shi zaunannan ƙasar Cairo ne da yafi shekaru 15 yana zama cikin ƙasar,amma ɗan asalin Nigeria ne Bahaushen Jihar Kwantagora.


Suhailah ta shirya cikin wata haɗaɗɗiyar Abaya,Blue Black da akai wa adon zane da golden ɗin zare.Ta yane kanta da Veil ɗin Abayar wanda ya zagaye face ɗinta,tayi matuƙar yin kyau sai sassanyan qamshin Turarenta na MISS DIOR da CARROLINA HERRERA ke tashi.


A.Maleek kuma yana sanye cikin wani haɗaɗɗen yadin Filtex Dark Brown me asalin kyau da tsada.Anyi masa ɗinkin zamani da ya dace da jikinsa,haɗaɗɗan qamshin Turarensa na AMOUAGE duk ya cika ɗakin.Suhailah ta ƙariso wajen

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login